Hausa novels
Trending

Abban Sojoji Page 57 Book 2 Complete Hausa Novel

Abban Sojojin Book 2

Romantic Hausa Novel

Written By Boss Bature

 

________________________Zuba mashi ido su kayi suna jiran amsa,Omar yace”pls ka faɗa mana gaskiya kawai,wacece wani abu ya shiga tsakaninka da ita har akasha wannan Love haka?kaga dai daga ni sai Abba babu wanda zaiji abun da ya faru,”wani irin kallo sgr ya wurga yana mashi ƴar harara yace”Omar bana so, ka fara ko”?

Murmushi Abban nasu yayi kafin yace”abunda Omar ya faɗa gaskiya ne,Son bai kamata ka 6oye mana komai ba tunda Allah dai yasa yau asirikinka ya tonu munga komai,ashe kana kula mata har romance kake dasu asaman gado ko?faɗamun ƴarwa ka kwamushe acikin ɗakinka har akai abun arziƙin nan bansani ba,”cike da zolaya Abban nasu ke magana,

ɗaure fuska Sgr yayi tare da haɗe girarsa wuri guda ya tsuke small lips ɗinshi yana kallonsu,yarda suka tasa shi gaba suna tuhumarshi kamar wani ƙaramin yaro ba ƙaramin hasala shi yayi ba,gashi sam ya rasa amsar da zai basu tunda bai isa ya ƙaryata abunda suka gani ba asaman ƙirjinshi,don shi kanshi a ruɗe yake da lamarin abun ya ɗaure mashi kai,taya aka samu jan bakin mace raɗau haka asaman ƙirjinshi!?bai gama zancen zucin nashi ba muryar Omar ta katse mashi tunani,

“Abba zargi fa ya tabbata,kalli ka gani,”Omar ne yayi maganar yayin da yake ruƙo mayafin sehrish dake a ƙasan laps ɗin Sgr ya danne shi,

dafe kirji abban nasu yayi cike da razana yace”ƙalu innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Rafayet!wannan fa?ya akai yazo wurinka”?ya tambaya hankali tashe yana kallonshi,

Runtse ido sehrish tayi daga 6oyen da take bayan labulen ɗakin,hada ƴan matan hawayenta saboda tsoran hukuncin da zata kar6a,

Cikin sauri sgr ya aza eyes ɗinshi akan mayafin da Omar ya ruƙo a hannunshi just speechless,amace bakin shi ya mutu yama rasa bakin magana abun ya zarce tunaninshi,

Omar ne yace”Abba tunda kaga yayi tsit ya gaza magana,to ya aikata ɗinne kasan mara gaskiya,ni fatan da nakeyi ma Allah yasa iya mayafi ya cire mata bai……..’kasa ƙarasa maganar yayi saboda saukar pillow daya ji a saman fuskarshi,hannu yakai zai ƙara rarumar wani pillow abban nasu ya dakatar dashi da cewa”Wannan fa alamar rashin gaskiya ce,tun ɗazu kaƙi buɗe baki ka ce uffan,sai faman ƴan kame kame kakeyi mana,kaji tsoran Allah ka faɗa mana gaskiya,Rafayet yin hakan kuskure ne bai kamata don kana ra’ayin mace ka runƙa kawota har bedroom ɗinka ba asaman gadonka don ka rage zafi da ita ba,in kaga yarinya kanaso Ni zakayi ma magana sai aje masallaci ashafa fatiha kaga shikenan sai a kawo maka ita ɗakinka babu mai jin kanku,taka ce halak malak…..’

Zare blue eyes ɗinshi yayi yana kallon Abban nashi,rai a6ace ya ciji la66ansa tare da ɗago pillown hannunshi ya ɗaga sama zai jefa ma Abban nasu a saman fuskarshi,sai kuma ya saki filon a saman katifar,

Ganin ya dakata yasa Abban nasu cewa”ae fa kai yanzu komai ma zaka iya,saurayin da zai iya kawo mace ɗakinshi har saman gadonshi acikin gidan ubansa meke bazai iya ba Omar? Ya ƙarasa maganar  yana kallon Omar dake ƙumshe da dariya yace”of course Abba,ina goyon bayan maganar ka,yanzu sai dai mu bishi da addu’a don na lura yarinyar ba ƙaramin zautar dashi tayi ba tunda gashi har ya gaza buɗe bakinshi yayi mana magana,rashin gaskiya dai baiyi ba,”

gaba ɗaya sun gama hasala Sgr,yama rasa amsar da zai basu su dukansu,a ƙarshe ma daya rasa abunyi kawai sai ya fashe da dariya unexpected,tsananin mamaki ne ya kamasu ganin Sgr yana 6a66aka dariya yau shi da kanshi,yaushe rabon da suga sgr yayi dariya irin haka,white teeth ɗinsa sun fito rairasss,da wuya kaga yana dariya sai dai wannan murmushin nashi na gefen fuska shima kuma in kaga yayi wannan murmushin tofa zai bada horo ne,don ya iya murmushin mugunta,

Hannu sehrish tasa a hankali ta ɗan yaye labulen tana leƙensu,ba ƙaramin bugun zuciya taji ba,kasa janye idonta tayi daga kallon kyakkyawar fuskar sgr da yake ta faman dariya kamar zautacce,gaba ɗaya dimples ɗin fuskarshi sun lotsa sosai abun ba’a magana sai wanda ya gani,suman tsaye sehrish tayi amace ta mace wurin kallon fuskarshi,aranta tana maimaita kalmar nan”tabarakallahu ahsanun khaliqin,”

Har wani duƙar da kanshi yake yi ƙasa yana dariyar hakan yasa sumar kanshi ta ɗan yarfo ta gaban fuskarshi,

Atare Omar da Abbansu suka haɗa baki wurin cewa”ikon Allah,abun mamaki abun al’ajabi,”

Tsagaitawa yayi da dariyar lokaci guda ya ɗaure fuskarshi tamkar dariya bata ta6a wanzuwa a fuskarshi ba,takaici ne dama ya ishe shi shiyasa ya fashe da dariyar,

Cikin sanyin murya yace”joking aside pls,abba nikaina bansan ya akai nasamu zanen lips ɗin nan asaman chest ɗina ba,sannan bansan ya akai mayafin nan yazo bedroom ɗina ba,na rasa ta yarda zansa kuyi understanding ɗina,gaba ɗaya kunyi confusing ɗina,kun tsareni da tambaya kamar wasu lauyoyi,that’s why nayi shiru bance komai ba,”ya ƙarasa maganar a kasalance,

Murmushi Abban su ya saki yana kallon face ɗinshi,bakomai ya faɗo mashi araiba face Mommynsu,komai na fuskarshi irin na mahaifiyarshi ne,yafi kama da ita amma akwai wasu abubuwan daya ɗauko na Abbansu,

“Zan shiga toilet,”ya faɗi tare da saukowa daga saman gadon ya kama hanyar shiga toilet ɗin,

Bin bayanshi su kayi da kallo har ya shige cikin toilet ɗin,

Sannan Suka janye idanunsu,cikin sauri Omar ya samu wuri tare da zaunawa yana fuskantar abbansu ya ruƙo hannunshi tare da cewa”Abba,dan Allah ka aurar damu tare, nida Rafayet,kayi mun wannan alfarmar”

Murmushi Abbansu ya ɗanyi kafin yace”Omar bangane me kake nufi ba,har yanzu ɗan uwanka bai janye ra’ayin shi akan mace ba,ni kuma banson na takura mashi,duk da banda burin daya wuce wannan nima,inaso naga auran kowanne daga cikinku,musamman auran shi saboda ina tunanin cewa in soyayya ta shiga zuciyarshi zai rage wannan zafin kan nashi,zai sassauto ya zama tamkar kowa,idan har rafayet baiyi aure ba ya tsaya akan bakanshi,tabbas za’ayi asarar namiji har namiji Omar,bansan ya zanyi dashi ba,”yanayin da abban nasu yayi maganar zai tabbatar maka da cewa abun ba ƙaramin ciwo yake masa ba,

“Abba kadaina cewa bakasan yarda zaka yi dashi ba,shifa ɗanka ne halak malak Allah ya mallaka maka,kuma kana da iko Akanshi,idan yau kaso Abba gaba ɗayanmu zaka iya yi mana aure batare da son ranmu ba ko batare da saninmu ba kuma dole muyi maka biyayya,”

zuba mashi ido Abban yayi yana sauraran bayanin shi,

Ƙasa ƙasa da murya Omar yayi gudun kada Sgr yafito daga cikin toilet ɗin yaji abunda suke tattaunawa,

Yasa shi yin hakan sannan yaci gaba da cewa”Abba,namiji irin rafayet,aure akeyi masu batare da saninsu ba,sai dai kawai suji an ɗaura auran…  ”

Katse shi abban nasu yayi da cewa”baka tunanin cewa zai iya sakin matar anan take,kasan shifa ba’ayi mashi dole,”?

Murmushi Omar yayi tare da cewa”Abba ka fahimta mana,kaifa kake iko dashi,ka sama mashi mace ta gari wadda kasan cewa bazaiyi dana sanin zama da ita ba,ko kuma ni kaban za6i zan sama mashi macen data dace da rayuwarshi,ka aura mashi ita batare da sanin shi ba,sai bayan an ɗaura auran ka ware rana ɗaya ka sanar dashi cewa Umarnine ka bashi amatsayinka na mahaifinshi,in ya kuskure kuma yasan sauran,”

dariya sosai Abbansu yayi yana sauraron omar dakyar ya tsagaita da dariyar yace”Omar ka iya zolaya Allah kamar mahaifiyarku,yanzu rafayet kakeso nayima auren dole?so kake ya tashi bomb acikin gidan nan”?

“Abba baka fahimce ni ba,tunda muka taso tare da ɗan uwana,komai namu iri ɗaya muke yinshi tamkar twins haka muke,duk abunda nayi rafayet sai yayi shi,haka shima duk abunda yayi nima saina yi shi,yanzu abba aure ne zai banbanta ni da ɗan uwana”?

In serious matter Omar ke magana,wannan yasa Abban nasu ya gane cewa ba zolaya bace yake mashi,har cikin ranshi yake maganar kuma ba ƙaramin jin abun yake ba acikin zuciyarshi,bai gama zancen zucin nashi ba omar yaci gaba da cewa”Abba tuntuni ban ta6a sanar dakai ba,amma yau zan sanar dakai komai,najima inason na cika maka burinka na ganin cewa munyi aure, ba don komai ba sai don saboda farin cikinka,bakomai ne yasa nayi jinkirin yin aure ba face Rafayet!inason aure bawai banaso ba,rafayet shine dalilin dayasa naƙi yin aure,saboda ina ganin cewa kamar banyi mashi adalci ba,inna riga shi yin aure,saboda mun saba komai atare duk wani cigaban da zamu samu atare muke samun shi abba,taya zanso na samu wannan babban cigaban batare da ɗan uwana ba”? Ya ƙarasa maganar muryarshi asanyaye yana kallon Abban nasu,

Gaba ɗaya Omar ya gama kashe ma Abban nasu jiki,ba ƙaramin tausaya mashi yayi ba,lalle ba ƙaramar shaƙuwa bace a tsakanin shi da ɗan uwanshi ba,tun da har zai iya hana kanshi wani jin daɗi na rayuwarshi saboda ganin cewa tamkar baiyi mashi adalci bane,

“Abba,na jima ina jiran ganin cewa ɗan uwana ya fara soyayya koya fara maganar aure,amma har yanzu ba wani sauyi abun ba ƙaramin ta6amin zuciyata yake ba,bana faɗi ne kawai saboda nasan faɗin bashi da amfani zan 6ata bakina ne kawae,sau da yawa ina janshi da fira akan mace don na bugi cikinshi naji koya fara ra’ayin yin aure amma kullum babu wani cigaba game da haka,Abba rafayet shine yasa Omar ɗinka ƙin yin soyayya tun da jimawa kuma shine ya hana nayi aure,wanda bani da burin daya wuce wannan arayuwata….,…….’

Kasa ƙarasa maganar yayi saboda siririn hawayen daya zubo mashi a idonshi na hannun dama,

Cikin sauri abban nasu ya sanya hannunshi tare da yin saurin goge masu shi yace”Omar ban ta6a tunanin haka ba,meyasa tuntuni baka sanar dani wannan maganar ba?meyasa nagaza fahimtarku amatsayina na mahaifinku?ashe shaƙuwar dake tsakaninku har takai haka?nagode ma Allah sosai da kuka kasance masu son junanku,ina matuƙar alfahari daku ƴa’ƴana,” magana yakeyi yayin da idanunshi suke cike tab da kwalla,

Sehrish kuwa dake la6e bayan labule sai faman shessheƙar kuka takeyi ta rufe bakinta da tafukan dukkan hannuwanta,tsananin tausayinsu ne ya kamata,tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin ƴan uwa masu matuƙar ƙaunar junansu ba irin ahalin salahuddeen hussein,akwai soyayya da shaƙuwa tsakaninsu,zumuncin dake tsakaninsu mai ƙarfi ne sosai,da ace kowane ahali zasu kasance haka da ba ƙaramin cigaba za’asamu ba,amma yanzu zamanin da muke ciki,babu wannan soyayyar atsakanin shaƙiƙai ma,sai kaga na waje ma wani can yafika kusanci da ɗan uwanka shaƙiƙinka,idan kuwa akazo kan shiga matsala ko damuwa tofa zaka ga mutum indai bashi ta shafa ba,babu ruwanshi da damuwa akan halin da ɗan uwanshi yake ciki,sai ma ya kasance ɗan uwanka yana cikin ƙunci da matsanancin damuwa,amma kai kuma hankalinka kwance sai ma ajika kana ta faman tiƙar dariya,mai makon arunƙa jajantawa juna,shiyasa dayawa zaka ga na waje ma wani yafika kusanci dashi saboda yafi damuwa da ɗan uwan naka,wanda dayawa hakan ke jefa rayuwar ɗan uwan cikin hatsari,ba’a janshi ajiki cikin gida tun daga iyayen har ƴan uwan,bakamar salahuddeen hussein ba, ya ɗauki ƴa’ƴanshi tamkar abokanan shi,ƙaramin ɗanshi ma tamkar amininshi ya mayar dashi,kuma hakan yasa basa jin shakkar sanar da mahaifinsu abu in ya same su,ko neman shawara awurinshi,wanda a yanzu zaka ga cewa wani a gidansu tsoro ma yake ji ya sanar cewa wani na cutar dashi awaje,saboda wasu iyaye basa tsayawa su fahimci ƴa’ƴansu daga sun ji abu sai afara hantarar mutum in ƙarami ne kaga an haɗa mashi da bugu ma,babu wannan shaƙuwar ta iyaye,da ƴan uwantaka da har mutum zai iya faɗin damuwarshi acikin gidansu,sai dae ya nemi abokinshi ya sanar dashi halin da yake ciki instead of wani nashi nakusa dashi,daga nan kuma awajen in Allah yasa abokin ba nagari bane shine zaka ga anzo ana danasani, don mafi akasarin mutane na fadawa mugun hali ne ta sanadiyyar abokai,ku yi koyi da wannan ahalin wurin nuna ma junanku soyayya,ku zama naku ku kaɗai babu mai jin kanku👌👍

 

Sehrish bata bar bedroom ɗin sgr ba,har sai da aka kira sallar magrib suka fita tare da abbansu domin zuwa yin sallar magrib sannan ta samu cikin sauri ta ɗage curtains ɗin,da hanzarin gaske ta sungumi mayafinta sannan da sauri hadda gudu ta haɗa wurin barin part ɗinsa,

Saukowa downstairs tayi a lokacin duk sun tafi salla masallaci,kai tsaye kitchen ta nufa tunkan ta ƙarasa ta hangi Azmee da hayaam suna ta haramar kammala dinner ɗin ranar,duk sai taji babu daɗi taso ace tare da ita suka fara,jiki asanyaye ta shiga kitchen ɗin da sallama a bakinta,

Juyowa sukayi suna kallonta atare,da alama ma sun kammala aikin nasu,Azmee ce ke haɗawa Hayaam warmers acikin tray tana kaiwa dining,

“Kin kammala gyara mashi part ɗin nasa ne?azmee ce ta jefa mata tambaya,

“Eh,nagama,”

“Ya akai kika daɗe acan ne”?

Sunnar da kai tayi tana wasa da yatsun hannunta saboda ta rasa amsar da zata bata,

Hayaam kuwa sai faman wurga mata harara take yi kamar kwayar idonta zata faɗo ƙasa,

Murmushi azmee tayi tare da cewa”ki wuce kije kiyi sallah,kada ki samu damuwa,nasan cewa wani abunne ya tsayar dake,”

Ajiyar zuciya sehrish ta sauke kafin ta juya tasa kai tabar cikin kitchen ɗin,bedroom ɗinta ta nufa domin tayi sallah,

 

A 6angaren su hossana kuwa,tun bayan da suka dawo daga school suke ta faman saran zuwan Omar amma baizo ba,burin jahad ta sanar dashi cewa taga ƙaninshi a school ɗinsu,gaba ɗaya yinin ranar sunyi shi ne cike da kewar Ya omar ɗinsu musamman hossana ko lunch bata ci ba tunda suka dawo gashi ko’a school ma bataci komai ba,saboda tayi alƙawarin cewa tare da ya omar zasu ci abinci zai bata abaki,hakan yasa taƙi cin komai,duk yarda jahad taso ta fahimtar da hossana akan ta zauna taci abinci sam taƙi,har dai tagaji ta ƙyaleta,

sai faman zagaye takeyi acikin bedroom ɗinsu,fuskar nan ɗauke da murmushi ae tunda tayi arba da Romeo sam tagaza samun natsuwa wani irin tsantsar son shi da ƙaunarshi takeji kamar kamar me,fiye da yarda take jin ya omar ma lokacin da taso shi,saboda shi son da tayi mashi hada ƙarin don ta kyautata mashi ne akan irin ɗawainiyar da yake yi dasu,shi kuma kalar son da take yi ma junaid kallo ɗaya tayi ma kyakkyawar fuskarshi tabi ta rikice,kuma tunda Omar ya furta cewa ƙaninshi ne nan take taji ya kwanta mata aranta,sai dai abunda jahad bata sani ba shine,junaid ba babba bane kamar yarda take tunani,

 

**********haroon

Gaba ɗaya ya rikita ɗakin nashi wurin neman kuɗin da su Twins suka bashi,sam hankalin shi ya gaza kwanciya yama rasa inda zaisa kanshi,wata irin zufa ce ke gangaro mashi a fuskarshi saboda tsabar 6acin rai,yafi ƙarfin awa 2 yana neman jakar kuɗin amma babu ita ƙasa ko sama,an ɗauke ta daga ɗakinshi babu ita babu alamarta,yayi ma bedroom ɗin nashi kaca kaca wurin binciken inda jakar kuɗin take,kamar zaiyi hauka saboda yarda ya zauce,sun rigada sun gama tsara plan ɗinsu,

shirin tafiya kawai ya rage mashi daga zuwa ya ɗauki jakar kuɗin an ɗauketa daga ɗakinshi,gashi ya rasa wanda ya shigo har cikin bedroom ɗinshi ya ɗaukar mashi ita,komawa yayi gefen gadonshi ya zauna yana faman huci kamar wani zaki,tunani ya shiga yi wanene zai iya shigowa ɗakinshi ya ɗaukar mashi jakar kuɗin shi?kodai su twins ne suka yi mashi wayau,don sunsan cewa ya goge videon shine suka ɗauke jakar kuɗin,tabbas kuwa sune saboda su kaɗai ne suka san da kuɗin acikin bedroom ɗinshi,

Jinjina kanshi yayi yana huci yace”yara kenan harni zakuyiwa wayau,ƙananun ƴan iska kawai masu kwana da wando,saboda sun mayar dani shashasha shine suka zagayo ta bayan idona suka ɗauki jakar kuɗin,wlh sai kunyi danasani saina illata rayuwarku gaba ɗaya muddin baku maido mun da kuɗina ba,”ya faɗi a lokacin da ya miƙe tsaye zumbur yana faman naushin tafin hannunshi na dama da hannunshi na hagu,tashin hankali da ba’a sama shi date,

 

**********************Amani

Zaune take saman 3 seater,yayin da Amal ke zaune kusa da ita,ta fito fess abunta tayi wanka ta bata kaya ta canza   duk da rigar tayi mata yawa saboda kayanta ne taba ma amal ɗin ta sanya kafin zuwa gobe zata je da ita shopping mall ta zabi abunda take so,ta kuma yi mata siyayyar kayan sawa da sauran abubuwa na rayuwa wanda zata buƙata,

Hannunta na ruƙe da wayarta,shiga contact ɗinta tayi tare da nemo numbar Aunty babba ta buga mata call,nan take wayar tashiga ringing,

 

Hafsat na faman zarya acikin parlourn nasu taji shigowar kira a wayar mommynta dake ajiye saman hannun kujera,cikin sauri takai hannu tare da ɗaukar wayar,ganin sunan Amani ya bayyana ne yasa ta juya tare da tunkarar kitchen ɗin,tunkan taƙarasa aunty babba tafito daga kitchen din jin ringing ɗin wayarta,miƙa mata wayarta tayi tare da cewa”Amani ce ke kira,”

Yatsina fuska tayi tare dasa hannu ta kar6i wayar bayan tayi picking ta kara wayar a kunnanta tana cewa”Sai yau kika tuna dani”?_

on the other hand Amani tace”Am really sorry auntyna takaina,kullum kina araina,kawai abubuwane sunyi mun yawa,”

tsoki aunty babba taja tare da cewa”Abubuwa su kayi maki yawa,ciki gare ki ko goyo”?_

Amani tace”ko ɗaya daga cikinsu babu,pls mubar zancen ae nabaki haƙuri,yanzu akwai maganar da nakeso nayi maki pls,”

Aunty babba tace”kunne ke ji,”

“dama maganar Amal ne!wai har yanzu ba labarinta?ba’asan inda take ba?nagaza samun kwanciyar hankaline saboda mafarkin da nayi jiya agame da ita,”

Shu’umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa”Yawwa dama inaso nayi maki magana game da Zancen neman Amal,munyi waya da mammy ta sanar dani cewa an samu wasu malaman da zasuyi mata sauka,manyan malamai ne na addini kuma da zarar sunyi saukar nan ake cin sa’a buƙata ta biya,”

Ƙiriss ya rage Amani ta saki dariya,don tsabar takaici da ban haushi,aranta tace wai sai yaushe matar nan,zata daina ƙarya ne?

Juyawa tayi ta ɗan kalli Amal dake zaune hankalinta kwance idonta na kallon plasma tv ɗin dake facing dinsu,tana kallon tashar mbc 3,

gyara murya Amani tayi tare da cewa”Masha Allah,gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba auntyna takaina,ashe ansamu wasu malaman ae ni indai akan Amal ne ko nawa ne zan iya badawa,ko bani dasu zan nemo ne,’_

Jin haka yasa aunty babba,janye wayar daga kunnanta tana faman 6a66aka dariyar mugunta,duk hafsat na tsaye tana kallonta baki asake saboda tasan da zancen neman Amal ɗin,kuma a gabanta Jiya abra ta kira mommyn nata tana sanar da ita cewa Amal ta gudu,sarai tasan cewa yarinyar ta gudu shine kuma takeson ƙara cutar da Amani saboda tsabar son abun duniya?

“Yanzu nawa zan tura kenan”?acewar Amani,

Aunty babba tace”ba wasu kuɗine masu yawa ba,dubu ɗari takwas ne,ae ni nayi mamakin ma yarda suka faɗi kuɗin da sauƙi har haka,”

murmushin takaici amani ta saki kafin tace”okey,zanyi maki magana indae na samu kuɗin,yanzu dae mu koma zancen Hayaam,shin har yanzu tana maid ne ko tazo Abujan nan”?

“Tun jiya fa ta ƙaraso,yanzu ae ta jima da zama ƴar gida,”ta ƙarasa maganar tana washe baki,anzo inda tafi auki,

ɗan ta6e baki amani tayi tace”Okey yayi kyau,yanzu komai zai fara tafiya dai dai,akwai wani albishir da zanyi maki,”

Natsuwa Aunty babba tayi tare da cewa”ina sauraronki ƙanwata,faɗamun albishir ɗin,”

Shu’umin murmushi Amani tasaki tare da miƙewa daga saman sofa ɗin tabar Amal zaune tana kallo,takawa tayi nesa da falon,sannan tace”Nasan inna faɗa maki albishirin nan ko bacci ba zaki iya yi ba saboda tsabar farin ciki,”

A ƙagare Aunty babba tace”dan Allah shaƙamun mana kanwata wane irin albishir ne wannan,

Murmushi Amani ta kuma yi sannan tace”nasamo ma Hayaam maganin mallaka a wurin wani hamshaƙin boka,aikin shi tamkar yankan wuƙa yake,saboda Ni shaidace akan idona aka ta6a amfani da maganin kuma yaci,”

Cike da farin ciki Aunty babba tace”Wai dagaske”?

dariya amani tayi tare da cewa”dagaske mana!,wata neigbour ɗinace keson ƙanwarta ta auri ƙanin mijinta,sun rasa yarda zasu jawo hankalinshi acikin gidannan saboda mutunne mai matuƙar ji dakai,kamar dai sgr,ina baki labari kwatsam sai ga wata ƙawarmu ta bamu labari akan wani shu’umin boka,agabana aka shirya zuwa wurin bokan suka amso maganin,a yanzu dai labarin da nake baki,yarinyar na nan ta aure shi hada ciki ma sai faman shan soyayya suke abun gwanin burgewa,”_

Saboda tsabar Murna Aunty babba ta gaza rufe bakinta dakyar ta iya cewa”Yanzu ya za’ae kenan asama ma Hayaam maganin?nawa zamu nema”?

“Ko sisi basai kin bada ba Auntyna,fisabilillah na amso ma hayaam maganin da kuɗina ai nima kanwata ce ko,nidae burina shine inga ta auri sgr Abra kuma ta auri marshal Omar,”

washe baki Aunty babba tashiga yi tana cewa”Allah sarki Amani,ashe haka kika damu da ƙannen namu?gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba,yanzu kenan Hayaam zatazo ta kar6i maganin gidanki kenan”?

Amani tace”eh,in ma batasamu zuwa ba ni zanje nakai mata shi,babu damuwa,”_

Sun jima suna waya kafin daga bisani firar tasu ta ƙare anan,

Tuntsirewa da dariya Aunty babba tayi tana tafa hannu tashiga cewa”ban ta6a ganin ƴar wahala ba irin Amani,duk irin abunda nakeyi mata amma ita burinta ta taimakamun wurin ganin na cimma burina,gaskiya na tausaya mata,abun tausayi,

girgiza kai kawai hafsat tayi tare da wucewa ciki tabar mommyn nata tana ta faman sambatu,

A can 6angaren kuwa fashewa da dariya Amani tayi tare da cewa”Aunty laila kenan!ke atunaninki kinyi mun wayau bakisan cewa Amanin da kika sani ada ba ita bace ayanzu ba,ashirye nake dana kwance dukkan wasu notikan kanki,zan mayar dake kamar wata zararra,ita kuma hayaam zanyi amfani da wannan damar wurin ganin na canza mata halittar jikinta,kamar yarda kuka canzawa Amal kamanni ta tsotse ta rame ta ƙanjame haka itama nakeson ta koma,dama ance ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,that’s my plan!

 

Tana faɗin hakan ta juya tare da komawa wurin Amal ta zauna,kallonta Amal tayi tare da cewa”Aunty amani,dan Allah kiyi haƙuri da abunda zan faɗa maki,bansan ko zai 6ata maki rai ba,nasan cewa su mammy sun cutar damu sosai,amma kada kice zaki ɗauki fansa,mubarsu da Allah kawai shi zai saka mana,sannan in zamu iya mu taimaki mahaifinmu don yana cikin mawuyacin hali”

Shuru kawai amani tayi batace mata komai ba,amma fa har yanzu tana akan bakanta,maganar mahaifinsu kuwa tasan matukar mammy na numfashi bazata barshi ya sarara ba,don ba karamar shedaniyar mata bace,ita kanta yanzu tana shakkun in don Allah aka hadata da Abbas.

 

_💋Boss Bature💋_

 

______________________tunda yadawo daga masallaci yake jin jikinshi wani irin yanayi mara daɗi,bedroom dinshi ya shiga tare da nufan saman gadonshi ya haye yana faman sauke ajiyar zuciya,pillow ya jawo tare da aza kanshi a saman shi yana faman lumshe ido,yana cikin wannan yanayin yaji fitar wani abu daga hancinshi mai ruwa ruwa,cikin sauri junaid ya tashi daga zaune yana kallon pillown nashi,zuba ido yayi yana kallon jinin daya ɗigo daga hancinsa,abun yayi matuƙar ɗaure mashi kai,kafin yayi wani yunƙuri sai ga wani ɗigon jinin ya sake fitowa daga ƙopan hancinshi,abu kamar wasa jinin ya dinga ɗiɗɗigowa saman bedsheet ɗinshi,

Hankali tashe junaid ya sauko daga saman gadon da saurin gaske ya faɗa cikin toilet ɗinsa,kai tsaye ya nufi wash basin,dafa shi yayi yana kallon fuskarshi acikin mirror ɗin,hancin shi yabi da kallo ganin yarda hancinshi ke cigaba da bleeding,sam bai damu ba saboda yasan cewa yana yawan yin nose bleeding,don haka tunaninshi ha6o ne kawai,

Hannu yakai tare da kunna tap ɗin,ruwa ya soma shararowa da gudun gaske,tarba hannunshi yayi tare da ɗebo ruwan ya watsa a fuskarshi yana wanke blood ɗin,murzar wurin ya shiga yi don jinin ya tsaya amma yaƙi daina zuba,ya kusan 15mins a haka sannan jinin ya dakata da ɗigowa,ajiyar zuciya ya saki tare da kai hannu ya kashe tap din,

Sannan ya fito daga cikin toilet ɗin,yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarshi ya nufi gadonshi,wani irin jiri ya kwashe shi,hannu ya aza asaman kanshi tare da ambaton sunan Allah,yayin da idanunshi ke ganin mashi biji biji,

Yana cikin wannan yanayin Sehrish ta faɗo cikin ɗakin ambaton sunanshi ta shiga yi “junaid, junaid…..,”

ganin shi atsaye abakin ƙopar toilet ya sata tsayawa tana kallonshi tare da cewa”baby junaid meya faru ne naganka haka?baka jin daɗine,”

Jin muryarta yadinga yi acikin kanshi tamkar ana buga ganga,hakan yasa ya yanke jiki zai faɗi gadan gadan,

A wani irin slow sehrish ta ƙarasa wurin da sauri ta ruƙo shi suka faɗi ƙasa atare,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda yake kokowar fitar da numfashinsa,hankali a matuƙar tashe take faɗin”Innalillahi_!junaid!meke faruwa dakaine!me yake damunka ne?ka faɗamun dan Allah,

Ko iya ɗaga la66ansa ba yayi bare ya iya furta mata wata kalma,hannunshi dake kerma yasa tare da ƙara ƙanƙameta sosai ya kwantar da kanshi asaman ƙirjinta yana cigaba da ƙoƙarin fitar da numfashinsa,hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,tuni ta soma fitar da ƴan matan hawaye,yanke shawarar zuwa ta sanar ma wani tayi don a hanzarta zuwa aga halin da yake ciki,ƙoƙarin janye jikinta tayi daga nashi,tamkar zata rabashi da ranshi haka yaji,ƙanƙameta ya kuma yi sosai da sosai sai lokacin ya iya furta”rishi kada ki tafi ki barni a yanayin da nake ji zan iya mutuwa,”

Cikin shessheƙar kuka take cewa”junaid ka bari inje in sanar dasu,idan wani abu ya same ka fa”?

“A’a nidai kada ki tafi kibarni,”ya ambaci hakan da wata irin kasalalliyar murya,tsananin tausayinshi ne ya kamata,mayar da hannunta tayi abayanshi tare da ƙara rungumo shi ajikinta tana tofa masa addu’a,lamo yayi ajikinta yana faman sauke ajiyar zuciya,lokaci guda kuma numfashin ya daidaita kamar yarda yake ada,komai nashi yadawo normal,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,idonshi na arufe yake shaƙar ƙamshin turaren rishi ɗinsa,gaba ɗaya ya shiga yanayin da bai ta6a shigar irinsa ba,

Muryarta ce ta katse shi da cewa”junaid kana lafiya kuwa?naji ka tsit”?

shiru yayi mata,saboda bayason tasan cewa ya dawo cikin hayyacinsa,baison ta raba jikinta da nashi,ɗumin jikinta ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,yaushe rabon da yaji ɗumin mace haka akusa dashi tun yana da kananun shekaru,tunda mommynshi tabarshi,Aunty azmee ta ɗaura da shayar dashi,shima ɗin da zarar ta kammala bashi nono ƴan uwanshi ke ɗauke shi daga wurinta,don basu son rabuwa dashi kona minti ɗaya,ya saba da jikin abban shi,dana ƴan uwanshi yayi missing wannan feeling ɗin,

Jin yarda junaid ya lafe mata ajikinta kamar jinjiri,yasa tayi tunanin cewa kodai ya cika ne,cikin sauri takai hannu tare da ɗago da kanshi tana kallon fuskarshi,waro ido waje tayi ganin yarda yake ta faman sakin murmushin nan nashi,ranta ne ya bata cewa Dama duk plan ne ya tsara mata don ya tsoratar da ita,ɗaure fuska tayi tare da cewa”janaid wannan duk shirinka ne ko? don ka tsoratar dani,”

Buɗe idanunshi yayi a hankali yana kallon fuskarta data zuba mashi ido,tana mashi kallon Tuhuma,

Murmushi ya kuma saki tare da cewa”dan Allah rishi ki mayar dani a jikinki na kwanta,ba kiji wani irin daɗi dana ji ba,daɗi kamar nayi bacci,”ya ƙarasa maganar yana lumshe mata ido,tsuke fuska sehrish tayi tare da cewa”amma ka rainamin wayau junaid!wai meyasa ka fiye shiririta ne,kalli fa, ka gani hada hawaye na soma zubarma saboda halin da na sameka aciki,ashe duk plan ne ko”?

girgiza mata kai yayi tare da cewa”ba haka bane reesh,kona faɗa maki gaskiya ba zaki yarda ba,”

A hankali ta kwantar mashi da kanshi ƙasa,sannan ta matsa tare da saita fuskarta akan tashi tana kallon shi,shima binta yayi da kallo yarda ta duƙo da fuskarta asaman tashi sumar kanta kuma tayi masu rumfa,tunda ta faɗo bedroom ɗin nashi tashigo da gudu don ta tarbe shi mayafinta ya sulale ƙasa daga jikinta,

“Junaid waye uncle Abusufyan?naji abbanku na cewa zaizo nigeria,kodai shima ɗin yayanku ne”?

girgiza mata kai yayi alamar a’a yace”uncle ɗinmu ne,ƙanin mahaifinmu dake zaune a ƙasar turkey”

jinjina kanta ta ɗanyi kafin ta kuma cewa”bayan shi kuma naji Abbanku yana cewa,Mommynku zata zo itama,tare da wata goggonku ta katsina da kuma Ammi da Aunty azeema,duk zasu zo,”

Sai da ya bari takai ƙarshen maganarta sannan ya ɗan harareta tare da cewa”Ashe dama jin gulma ne ya kawoki ɗakin”?

Murmushi tayi tace”no ba haka bane junaid,inason nasansu ne saboda na koyi zama da kowannansu,bana so na samu matsala da kowa acikin family ɗinku,”

“Zan faɗa maki halin kowannansu amma bisa sharaɗi ɗaya’?ya jefa mata tambaya,

Tace”ina sauraronka wane sharaɗine wannan”?_

murmushi ya saki tare da kai hannunshi ya nuna mata red lips ɗinsa yace”kiss on lips,if u agree then saina faɗa maki,”

hannu tasa tare da ɗan buge bakinshi tace”pls junaid banason wasa fa,in zaka faɗamun ka faɗamun kawai,in ba haka ba zan tashi inyi tafiyata,”

tayi maganar tare da yunƙurawa zata miƙe cikin sauri ya ruƙo hannunta tare da cewa”rishi mommyn mu bata da sauƙi,nima haka naji ana faɗa,amma in har zaki iya zama da babban yayanmu to wannan bazai maki wuya ba,bambancin ita mace ce kinsan ku mata da tsiwa kuke,

Dariya tayi tana sauraronshi

“Uncle ɗinmu kuma Abusufyan,wayayyen mutun ne,idan yazo zakiji daɗin zama dashi,bafa wani babba bane autansu  daddynmu ne,yana da sauƙin kai sosai amma idan mutun bai kwanta mashi araiba hmmmmm bazasu ta6a jituwa ba,Aunty azeema kuma kamar abbanmu take wurin faran faran da mutane ga son ƴa’ƴa,zakisha mamaki idan tazo ta ganki sosai zata jaki ajikinta,goggon katsina kuwa……”bai ƙarasa ba ya kama dariya,

Murmushi ta saki tare da cewa”me tayi ita?ko batasan mutane”?

Girgiza kai yayi tare da cewa”a’a tanason mutane sosai,matsalarta ɗaya tana da mental illness…….’

Tunda junaid ya ambaci mental illness taji gabanta ya ɗan faɗi kaɗan kamar maison tuna wani abu acikin brain ɗinta,

“tana da ban dariya sosai,tana fa iya ganinki tace ke ɗiyar wani ce acikin family ɗinmu kuma dole ki yarda da hakan in ba haka ba ta sanya rigima hada kuka ma,’

Sai faman zuba junaid yake yi yana korama sehrish jawabi,ita kuwa tuni tayi nisa cikin tunaninta,kalmar da ya faɗi na cutar ta6in hankali ta tsaya mata arai,so take ta tuna waye ta ta6a sani da irin wannan lallurar amma sam tagaza tuna hakan,

Ganin ta tafi duniyar tunani yasa junaid kai hannu ya janyo sumar kanta yana cewa”wai menene haka reeeshi,kin barni ina ta zuba kamar rediyon da bata da saiti,”

Firgita ta ɗanyi tare da kallon shi har lokacin yana daga kwance tace”junaid thanks for the information,zan koma bedroom ɗina naji ana kiran sallar isha,kaima ka tashi kaje kayi sallar,’

Ba musu ya amsa mata da cewa”bari nayi alwala sai mu fita atare,”

Amsa mashi tayi da toh sannan ta miƙe tare da juyawa ta ɗauko mayafinta daya faɗi kasa ta rufe kanta dashi,toilet junaid ya shiga shaf shaf yayi alwala,bayan ya fito atare da ita suka saukko downstairs,

Anan ya haɗu dasu Irfan zasu masallacin suma yabi bayansu suka tafi,

Komawa bedroom ɗinta tayi kai tsaye ta fada toilet ta ɗauro alwala,bayan ta fito ta ƙarasa wurin wardrobe dinta tare da ɗaukar hijabinta da sallaya ta shimfiɗa tare da kabbara salla,anatse ta kammala sallar,fitowa tayi daga dakin nata sannan ta wuce kitchen don ta shirya ma kanta abincin da zata ci saboda yunwar data taso mata,

 

_💋Boss Bature💋_

 

A hankali Motarsu tashiga babban gate din gidan Abusufyan,major ne ke driving dinshi yayin da Omar ke hakimce a seat ɗin baya,sai faman zullumin haɗuwarshi da hossana yake saboda yasan cewa ba ƙaramin fushi take dashi ba,saboda ƙin zuwan da yayi,

Parking ɗin motar major yayi sannan ya fito tare da buɗe mashi motar,a hankali Omar yasa ƙafa tare da fitowa daga ciki,sannan cikin sauri batare da 6ata lokaci ba ya wuce cikin gidan,

Tunkan yasa ƙafarshi cikin parlourn nasu yajiyo shessheƙar kukan hossana,tsayawa ya ɗanyi yana sauraron abunda suke cewa,

“Hossana wai ba zaki daina kukannan ba?salon ki 6ata kwalliyarki ko”?

“Jahad ba zaki gane bane,bakisan yarda nake ji bane,saboda ya omar nayi kwalliyar nan,amma ta tashi a banza,yau ma bazaizo wurin mu ba…’cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar,

ƙayataccen murmushi Omar ya saki a fuskarshi,kafin yasa kai tare da shiga cikin palourn,samunsu yayi zaune asaman 3 seater,hossana ta kwantar da kanta asaman hannun sofa ɗin,yayin da jahad ke gefenta tana rarrashinta,gaba daya duk sunyi wanka sun canza kayan jikinsu,riga da skirt ne ajikin jahad,hossana kuma gown ce mai kyan gaske,

jin alamar motsin mutum yasa jahad ɗagowa tana kallon shi,cike da mamaki ta buɗe baki zatayi mashi magana,da hanzarin gaske ya dakatar da ita ta hanyar yi mata nuni da hannunshi alamar ta tashi ta tafi,murmushi jahad tayi tare da miƙewa cikin sanɗa tabar saman sofa ɗin ta koma saman 1 seater ta zauna tana kallon dramar da ya Omar ɗinsu zai shirya,cikin sanɗa ya lalla6a tare da komawa wurin da jahad ta tashi ya zauna,sannan yakai hannunshi tare da ɗan janyo wutsiyar gashinta,

A fusace tace”dan Allah jahad ki rabu dani inji da abunda ke damuna,ki tashi kiban wuri,”

Murmushi Omar yayi tare da cewa”zan tafi amma ki fara faɗamun meyasa kika damu da yaya Omar ɗinki har haka”?

Sam hossana bata gane voice ɗinshi ba saboda ranta a6ace yake,

“Saboda inason shi sosai,jahad nasan ni kawai nake haukana,yana can wurin hayatyn shi,suna shan soyayya…..’

Katse ta Omar yayi da cewa”kina kishi ne”?

A faɗace tace”saboda me bazanyi kishi ba,nima ae zuciyata ce a ƙirjina ba dutse ba,”

Wannan maganar ta hossana ba ƙaramin dariya taba marshal Omar ba,hatta jahad sai da ta murmusa daga inda take,

Kwantar da kanshi ya ɗanyi abayanta yana cewa”am really sorry babyn Omar,nayi missing ɗinki sosai,nasan nayi laifi ayimun afwa bazan ƙara ba…”jin muryar Omar raɗau a kunnanta yasa tayi hanzarin ɗagowa tana kallonshi da idanunta da suka cicciko da kwalla,

Waro ido Omar yayi yana kallonta ba ƙaramin tsorata yayi ba da ganin makeup ɗin da ke a fuskarta,ta dambara Uwar foundation kamar wata aljana,Jan bakin da ta shafa ya 6ata fuskarta har wurin cheeks ɗinta saboda uban kukan da tasha,ga maskara ta zazzago mata a ƙasan idonta,

Hankali tashe Omar yace”subhanallahi,kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Babyn Omar wannan kwalliyar fa?dama itace kwalliyar da ake cewa anyimun don inzo in gani,”cike da zolaya yayi maganar,amma tamkar ya tunzura hossana nan take ta 6are baki tare da fashewa da wani sabon kukan,

Dariya jahad ta dinga tiƙa kamar kamar me har tagaza dakatar da kanta,

Yama rasa ta inda zai fara shawo kanta don ya lallashe ta,hakan ya ƙara hasalata,kamar wata ƙaramar yarinya,ba ƙaramin tausayi ta bashi ba yasan duk don saboda rashin zuwan shi ne,hannu yasa tare da janyota jikinshi yayi hugging ɗinta sosai yana ɗan bubbuga bayanta,lokaci guda ta nemi kukan da takeyi ta rasa,sai gata tana faman sauke ajiyar zuciya,

a hankali ya furta”am really sorry hossana,bazan ƙara 6ata maki rai ba,kullum zan dinga zuwa idan ma bansamu halin zuwa ba zan kira ku awaya mu gaisa,”

Ya ƙarasa maganar tare da cewa”kin yafe mun”?

ƙasa ƙasa tace”na yafe maka,amma karka ƙara,”

murmushi yayi tare da ɗagota daga jikinshi yana kallon fuskarta,sai faman cin magani takeyi tana haɗe mashi fuska,

“Kin ci abinci kuwa”?

“A’a banci ba,”

“Why”? Ya tambaya yana kallon bakinta da take ta faman turowa irin na shagwa6a66u,

“Kai nake jira kazo ka bani abaki,”

“Really”? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

Juyawa ya ɗanyi tare da kallon jahad dake zaune tana kallonsu gwanin burgewa yace”dagaske hossana bata ci komai ba”?_

Amsa mashi tayi da eh,jinjina kai yayi sannan yace”ki kawo mata dinner ɗinta anan,sai na tabbatar da taci ta ƙoshi sannan zan tafi,”

Murmushi jahad tayi tare da miƙewa ta wuce downstairs don pta shiryo masu dinner din,”

 

_💋Boss Bature💋_

 

Yau da wuri suka dawo cikin gidan wuraren karfe goma dai dai,wani irin tsoro da fargaba sehrish taji,musamman da azmee ta sanar da ita cewa ga dinner ɗin sgr can taje takai mashi,bakomai ya faɗo mata arai ba face abunda ya faru ɗazu tasan cewa dole ya tuhumeta saboda ita kaɗai ce macen da take shiga part ɗinsa,sai faman zarya takeyi acikin bedroom ɗinta,tana tunanin yarda zata tunkare shi ayau ɗinnan,

 

Hayaaam

 

Tafiya takeyi cikin sanɗa tana waige waigen ko akwai wani a main palour din cikin sa’a taga babu kowa,murmushin mugunta ta saki tare da nufar kitchen din,tana shiga tayi arba da tray na abincin da Azmee ta shirya ma Sgr,asaman dogon table na kitchen ɗin ta ajiye mata,jinjina kai hayaam tayi tare da cewa”hmmmmm yarinya kenan yau zaki fara sanin koni wacece wurin iya makirci,”

Tana faɗin hakan ta shiga ciki kai tsaye ta tsaya wurin tray din,hannu tasa tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da chicken ppr soup,sai faman ƙamshi yake yi,murmushi hayaam tasaki tare da kai hannu cikin sumar kanta,ta cinko gashin kanta sannan ta jefa acikin chicken ɗin hadasa hannu ta motsashi aciki,sannan ta rufe murfin,duk hakan bai mata ba sai da tabi komai na abincin ta sanya gashi aciki,sannan cikin sanɗa tabar kitchen ɗin,tana faman sakin dariya don tasan cewa da zarar sgr yaga gashin nan yarda yake da tsaftar nan ba ƙaramin ƙyamatar yarinyar zaiyi ba,kuma tasan dole ya koreta daga yi mashi aiki,bama wannan ba dole ya hukuntata, tashin hankali da ba’a sama shi date,

 

💋💋💋

 

Fitowa sehrish tayi bayan ta gama zullumin nata,kitchen ɗin ta nufa batare da 6ata lokaci ba ta ɗauko tray ɗin a hannunta tare da wuce wa upstairs,hakanan tadinga jin gabanta na faɗuwa kamar wani mummunan abu zai faru da ita,tsayawa tayi abakin ƙopar shiga falon nashi,sai da ta dai²ta natsuwarta sannan ta zabga sallama,tana jiran jin amsawar shi,

Jin shiru yasa ta ƙara maimaita sallamar,har kusan sau uku ana huɗun ne tajiyo muryarshi yace”Come in,”

 

Ae tunda taji Voice ɗinsa jikinta ya shiga yin kerma,addu’o’in neman tsari tashiga karantowa abakinta,ta jima atsaye tana faman zullumin abun da zaibiyo baya kafin daga bisani ta daure tare da shiga cikin falon nashi,ƙamshin turaren nan nasa ne ya wanko mata hancinta har saida ta lumshe idanunta,tunkan taƙarasa ta hango shi kwance ya miƙe kafafunshi asaman 3 seater,jikinshi na sanye da pyjamas yellow,ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,kunnanshi na kare da wayarshi alamar waya yake yi,

Gabanta na faɗuwa haka ta nufe shi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table dinsa,saboda tsabar rashin gaskiya,tana ajiye tray ɗin ta juya cikin sauri zata bar parlourn nashi,kamar daga sama taji anyi ma mayafinta kwakkwaran ruƙo ta baya,nan take mayafin ya sulale daga jikinta,zazzare ido waje sehrish tayi jikinta na kerma,nan take tashiga haɗiyar yawu,tsayawa tayi tana jiran maizo biya baya,

Jin alamun motsin shi abayanta ya tabbatar mata da cewa shine yaja mayafinta daga jikinta,tsayawa tayi tana ambaton sunan Allah abakinta,ganin kusan minti biyar bata ji ya ƙara motsawa ba yasa tayi hanzarin juyawa a wani irin firgice sam bata tsammaci yana tsaye abayanta ba sai dai kawai taji ta kai mashi karo,ja da baya ta ɗanyi tana faman zare ido,tunkan ya tambayeta ta shiga cewa”dan Allah kayi haƙuri,nasan na 6ata maka rai,wlh nima bada son raina hakan ya faru ba,nashiga na gyara maka bedroom ɗinka ne,bayan na kammala shine na ɗan cire mayafina na ajiye asaman gadonka don naji daɗin yin aikin,ashe kafin na fito daga cikin toilet ɗin ka dawo,shine na same ka akwance kana bacci saman mayafina,saboda ina tsoran ka farka ka ganshi yasa nayi ƙoƙarin janshi daga jikinka,shine…cikin bacci batare da saninka ba ka………..’kasa ƙarasa maganar tayi saboda jin yatsun hannunshi da tayi asaman lips ɗinta,alamar tayi mashi shiru,sannan ya hankali ya ɗan ware eyes ɗin nashi akan fuskarta………..

omin Sauke Littafin book 3 Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button