NA
AISHA ALIYU GARKUWA
Murmushin Jin dadi Aunty Dijat din tayi, kana cikin sakin fuska tace.
“Alhamdulillah nidai ko yaushene ma ina jira.”
Barrister Kabir dinma murmushi yayi, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya cigaba da shan coffee d’insa.
Acan cikin tashar kuwa, zuwa yanzu kira na 15 kenan Jannart din ta amsa, wanda kuma daga kan kira na 15 dinne ta katse layin gaba d’aya, tare da d’agowa ta kalli cameras din dake jere agabansu.
“To masu kallonmu laifin dadi dai ance karewa, Domin naga lokaci yana daga mana hannu, saboda haka duka duka anan muka kawo k’arshen shirin namu Na Bak’on Mako, sai kuma wani sati Idan mai kowa mai komai ya kaimu, Insha Allah zamu sake zuwar muku da wani bak’on na musamman.”
Dan Juyowa tayi ta kalli Rayyern dake zaune, Cikin kuma sakin fuska kamar yanda ta sabayiwa kowa tace.
“Doctor ayiwa masu kallo da sauraronmu sallama.”
“Assalamu Alaikum.”
Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din ya fad’a atausashe, saboda yasan izuwa yanzu duk su Abbansa suna kallonsa.
Jannart kuwa juyowa tayi ta fuskanci Camera hadi da cewa.
“To masu kallonmu duka duka anan muka kawo k’arshen shirin namu, tare da babban bak’onmu”.
Ta ƙare mgnar da juyowa tana kallon Dr Rayyern.
Numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.
“Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara”.
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
“Sai kuma ni dana shirya na kuma gabatar JANNART IDI SALE DAKATA. Nake, mana fatan mu hade awani sati Idan Allah ya kaimu a huta gajiya.”
Cuttt haka masu d’aukan shirin suka katse tare da kashe cameras dinsu.
Dai-dai lokacin ne Kuma anan gidansu Rayyern din Zuciyar Abba tayi wani irin bugawa, saboda sunan Yarinyar da yaji acikin kunnuwansa.
“Jannart Idi Sale Dakata!!”.
Abba ya maimaita sunan acikin zuciyarsa, cikin sauri kuma ya d’ago da kansa ya kalli Mamy, wacce ita dinma shi take kallo, fuskarta dauke da tsananin mamaki.
Atare kuma suka sake maida kallonsu ga tv,n.
“Idan har sunan da yarinyar ta fad’a shine sunanta na gaskiya, To Lallai kuwa, wannan itace yarinyar da Barrister Kabir yazo musu da maganarta.”
Abban ya fad’i haka azuciyarsa, fuskarsa cike da tsananin mamaki, hadi da tu’ajjudin faruwar hakan.
Tuno wani abu da yayi ne kuma yasa Lokaci daya ya saki wani irin murmushi, mai dauke da tsananin jin dadi, hadi da cin nasara.
Tabbas ayanzu ya sake gaskatawa, cewar Nesa tazo ta kusa.
Acan TV station din kuwa Zumbur haka Dr Rayyern din ya mik’e tsaye, wanda hakan yasa cikin sauri MD da kuma sauran assistance managing director hadi da manyan masu muk’amai na tashan suka nufo wajen Rayyern din kaitsaye, hannayensu suka dinga mik’a masa daya bayan daya suna gaisawa cikin mutuntaka.
Inda MD da farinciki yasa bakinsa kasa rufuwa yace.
“Mungode Kwarai Dr. Rayyern, Allah Ubangiji yasa kafi haka, nida sauran ma’aikatan wannan tasha, muna godiya agareka, daka samu daman zuwa wannan tasha.
Tabbas zuwanka ya sake daga darajar tasharmu.”
Yar sauk’ak’ekk’iyar Murmushi kawai yayiwa MD’n, Yayinda MD kuwa yasa a daukowa Dr. Rayyern din kyauta ta musamman, wanda sukayi dan nuna godiyarsu agaresa.
Salman, Aysha Lawal da kuma Aunty Fauziy D Sulaiman dake gefe kuwa, hannayensu suka d’agawa Jannart alaman jinjina, kowannensu fuskarsa cike da farincikin, irin nasaran da Jannart din ta samu, Domin kuwa ta kafa tarihin da akab gidan television’s din dake Nigeria babu wanda ya tab’a kafawa.
Ta kawo musu babban hazikin Dan kasuwa kuma Doctor, mutumin da kowa yake fatan ganinsa, yau gashi Jannart din ta kawosa ta kuma bayyanawa duniya fuskarsa, daya jima yana b’oyeta.
Murmushi Jannart din tayi musu, tare kuma da k’arasowa ta kalli Salman, wanda azahirance yana cikin tsananin farinciki, akasin hakan kuwa, shine Sam bayajin dadin zuciyarsa, saboda tun zaman Jannart da kuma Dr. Rayyern din daya gani awaje daya, yaji zuciyarsa ta karye, badan komai ba kuwa saidan tsananin matching din da yaga sunyi, sosai suka haska tamkar wasu taurari, sai kuma ayanzun ya sake tabbatarwa da kansa, cewar kwata-kwata ma Jannart Dakata ba sa’ar sa bace, Jannart matar manyan mutane ce.
Kana kuma Jannart zara ce acikin taurari, furta wani abu daya shafi so agareta, kuwa tamkar karambani ne, saboda ya sani bashi da wannan matsayin.
Haka dai jikinsa adan sanyaye ya juya suka rufawa su MD din baya, wanda tuni sun nufi hanyar waje, Dan raka Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara mota.
Cikin masu rakiyan kuwa harda Asiya, wacce takejin kamar ta fashe da kuka, ko tasa ihu.
Badan komai ba kuwa, saidan ta samu ko kallo daya ne Dr. Rayyern din yayi mata.
Jannart kuwa kaitsaye Office dinsu ta wuce, batare da tabi yan rakiyar ba, Sam ita rakasa ma baya gabanta, hasalima mamaki take akan yanda taga, y’an Office din nasu suna karramasa, Tabbas Koda ga wahalan da tasha wajen nemansa, tasan cewar shidin babban mutum ne.
D’an tab’e bakinta tayi alokaci da ta samu waje ta zauna.
Hakanan takejin zuciyarta wasai, tamkar an zare mata wani mashi dake sukanta.
“Alhamdulillah Allah, Kai katsaramin komai, yanzu bazan rasa aikina ba, bana kuma da wata fargaba, Thanks for everything Allah.”
Ta fad’i hakan abayyane Cikin kuma tsananin farinciki, dajin dadi.
Saboda duk wata fargabanta yanzu ya yaye.
Acan compound din tv station din kuwa, har wajen mota su MD suka rako Dr. Rayyern, bayan sun bashi kyautar karramawa.
Kasancewar kuma tun kafun su isa, Hadi’nsa ya bud’e masa murfin motar tasa ne, hakan yasa yana zuwa batare da wani b’ata lokaci ba ya shiga ya zauna.
Still harya rufe murfin motar kuma godiya su MD sukeyi masa, tare dayi masa fatan sauk’a lafiya.
Anutse kuwa Hadi yaja motar suka fice daga cikin gidan tv’n.
Fuska Asiya ta had’e tamkar zata had’iyi zuciyarta haka takeji.
Lallai tayi takaicin wannan ranan, saboda ko kallo daya bata samu daga wajen Dr. Rayyern din ba, hasali mai irin halittarta ma baisan tana wajen ba.
Dan Kallon kanta tayi, can cikin zuciyarta kuma taja tsaki, tare da cewa.
“Tayaya ma zai kalleni, tunda akwai irin waccar mayyar aduniya, natsaneki wallahi Jannart natsani ma Koda ganinki, saboda ke ne zaman office dinnan ya fara yimin kunci, kinzo kin hanani sakat, wai kawai saboda kina da kyau, mcheewww.”
Tak’are maganar nata da jan tsaki tare da juyawa ta koma Cikin office din, dan zuwa yanzu ita kad’ai aka bari awajen.
Acan cikin Office din kuwa, MD dakansa ya shigo cikin Office din su Jannart din, tare da bud’e hannayensa ya soma tafa mata.
Aikuwa Ganin haka yasa duk sauran ma’aikatan suma bud’e hannayensu suka soma tafa mata.
Cike da jinjina hadi da yaba k’wazonta MD yace.
“Congratulation Jannart, Lallai kin cika hazikar yar jarida, na kuma jinjinawa kwazonki, Tabbas samun irinki acikin aikin jarida abune mai kyau, ayau ta sanadiyarki tasharmu ta sake daukaka, kin shammace mu Kwarai, dole ne mu baki lambar yabo, zaku ma muyi miki karramawa ta musamman.”
“Kwarai kuwa Jannart hakika kinyi Namijin kokari, Tabbas kin cika hazikar Mace mai kishi da kuma son aikinta congratulations.”
Cewar Aunty Fauziya D Sulaiman.
Jannart din kuwa murmushin daya bayyana kyawawan hakwaranta tayi, cikin tsananin jin dadi tace.
“Congratulations to you all my colleagues, Domin duk wannan nasaran nasa meta ne da k’arfafawar guiwanku, musamman Salman, Thank you so much Salman.”
Murmushin Jin dadi duk sukayi, Yayinda Salman kuwa ya sunkuyar da kansa kasa yana murmushi.
Asiya dake gefe kuwa ji take kaman tayi hauka, tsabar k’unci takaici da kuma bak’in Cikin daya cika zuciyarta.
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa atsakaninsu, Yayinda fuskar kowannensu ke dauke da tsananin farin ciki.
Amma banda na Asiya da har hawayen takaici saida suka tara.
MD kuwa yau din da kansa yasa akayi musu order’n delicious food, tare da kayan drinks.
Anan cikin babban falon da suke ajiye baki, suka gudanar da d’an kwarya kwaryan party.
Inda kuma sukayiwa Jannart din tanadin Karin matsa yi na musamman.
Bayan sun gama yar kwarya kwaryan Partyn nasu ne kuma ta dau Jakarta Kai tsaye ta wuce, gida zuciyarta cike da tsananin farinciki.
Yayinda daga can b’angaren Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara kuwa, daga tv station din kaitsaye gidansu ya nufa.
Suna isa bakin gate din kuwa Baba Hadi ya danna horn, cikin sauri da kuma azama Baba Maud’o ya karaso ya bude musu gate din, direct Baba Hadi ya tura motar cikin gida, tare da dai-dai-ta parking dinta a parking space.
Ahankali Rayyern din ya bud’e motar ya fito,
Kana ya juya ya nufi wurin da Baba Maud’o yake tare da ɗan longoɓar da kai alaman gaisuwa.
Murmushi Baba Mauɗo yayi tare da mishi sannu. kafun kaitsaye ya nufi babban falon gidan.
Inda Mamy da Abba dasu Ramadan ke zaune.
Shigowarsa cikin falonne kuma yasa duk suka d’ago Kai suka kalleshi, Riyyam-nsra ne ya taso da d’an hanzari ya rungumeshi, tare da cewa.
“Gaskiya ko Hamma Rayyern kaina musamman ne, ka iya amsa duk wata tambaya da akayi Ma.”
Kansa kawai ya Dan jinjina saboda duk ji yakeyi kansa a gajiye, karasa shigowa cikin falon yayi, tare da yiwa Abba da Mamy sannu da gida.
“Yauwa Rayyern sannu da dawowa.”
Mamy ta amsa masa, Yayinda Abba kuwa Da Kai ya amsa masa.
“Hamma Rayyern congratulation.” Ramadan ya fad’a k’asa k’asa yayinda yake Dan danne dariyarsa, badon komai ba kuma saidan sanin halin Yayan nasa da yayi, kwata-kwata baya son yawan magana amma kuma yau gashi wata tasashi yayi ta magantuwa.
Da kai kawai Rayyern din ya amsa masa, batare daya zauna acikinsu ba kuma kaitsaye ya wuce part d’insa.
Wanka yayi tare da dauro alwalan sallan magriba, bayan ya kimtsa kansa acikin wasu kaya marar nauyi ne kuma, ya fito inda dukansu suka had’a hanya wajen zuwa masallaci.
Koda sukaje masallacin kuwa kamar Koda yaushe basu dawo ba saida aka Sallame sallan Isha.
Suna dawowa gidan kuwa suka samu Mamy ta had’e musu lafiyayyen dinner, hakan yasa duk suka k’arasa kan dining table din suka zazzauna.
Yau din kuma Riyyam-nsra ne da kansa ya amshi Mamy wajen yin saving dinsu, shida kansa ya zubawa kowa abincin banda Abba da Mamy ta zuba mishi nashi, sannan da kansa ya had’awa Hamma Rayyern din tea.
Bayan ya kammala had’a musu ne kuma, kowa ya soma cin abincinsa, anutse Abba ya d’ago da kansa ya kalli Rayyern cikin jinjina da kuma ya bawa yace.
“Tabbas hirar da akayi da kai yau, tayi armashi da kuma ma’ana, sannan shawarwarin daka bayar shawara ne masu kyau, gaskiya na jinjina maka,”.
Sai kuma ya ɗan tsagaita kana ya ɗan kalleshi tare daci gaba da cewa. “Amma da kashawarce ni kafun hakan, To fa da bazakaje ba.”
Zazzafan tea din dake bakinsa ya had’iya, kana cikin yin kasa dakai yace.
“Kayi hakuri Abba nima banaje Dan son raina bane, naje ne kawai saboda nayi musu alk’awari, sannan banason wanda aka bawa kwangilar nema na din ya rasa aikinsa, kamar yanda manyansa suka bashi zab’i.”
Kai Abban ya jinjina, batare kuma daya ja zancen yayi tsawo ba yace.
“Shikenan To Rayyern Allah ya taimaka ya tsare min kai.”
Da Ameen duk suka amsa.
Bayan sun kammala cin abincinne kuma, kaitsaye Rayyern din ya wuce daki’n sa.
Yayinda Ramadan da Riyyam kuwa suka dawo Cikin falon suka ci gaba da hirararsu, daga karshe ma game suka had’a, suka soma yi.
Ganin hakanne kuma yasa Abba da Mamy wucewa sashinsu.
Rayyern kuwa yana shiga dakinnasa kwanciya yayi, Cikin mintuna kad’an bacci yayi nasaran daukarsa.
Acan falon kasa kuwa Ramadan da Riyyam, duk kowannensu saman kujera ya d’ale ya kwanta, su kansu ba zasu iya sanin tayaya nema bacci ya kwashesu ba, kowannensu da abun buga game din ahannunsa, haka sukayi bacci kasancewar dare ya nisa.
A sashin Jannart kuwa yau tun 9 tayi baccinta mai cike da nutsuwa, Yayinda takejin zuciyarta wasai babu sauran wani fargaba.
Washegari.
Friday.
Tun tashinsa karfe 7 ya gama shirya kansa, saidai shigarsa ta yaudin ta banbanta dana kullum.
saboda wani riga da wando mai Taushin gaske ya saka ajikinsa, sabanin suit daya saba sakawa akowacce rana.
Sosai kayan Yayi masa kyau, musamman daya daura boyfriend jacket mai kyau akan kayan.
Wasu bakaken shoe masu tsada da watch ya daura a tsintsiyar hannunsa .
Bayan ya gama kimtsa kannasa ne kuma, ya dauki wayarsa tare da duba sakonnin da suke ta shigo masa ta Twitter, saboda yanda duniyat Twitter din ta Dinke da hotunansa, gaba daya shi kawai ake watsawa, da kuma bayani akan hirar da akayi dashi.
Kashe data dinnasa yayi, tare da juyawa ya nufi k’asa kaitsaye.
Anan cikin falon ya samu su Abba, harma da Riyyam nsra wanda yake ta hamma da alama bacci bai ishesa ba.
Dan Koda asuba ma Abba ne daya fito yagansu kwance afalo, shi ya tashesu tare da saka su agaba suka wuce masallaci.
Karasowa yayi ya zauna akan dining table din, bayan kuma Mom tayi saving dinsa ne, ya soma cin abincin atsanake, saidai kuma bai wani ci sosai ba, ya mik’e tsaye.
Yaudin ma dai atare suka fita shida Ramadan, saidai kuma Riyyam-nsra ya dage kan cewar, tare zasu tafi Hospital shida Ramadan.
Hakan kuwa akayi inda Ramadan din ya dauki Riyyam din suka wuce Hospital, shikuwa Rayyern dama yau ba Hospital din zaije kaitsaye ba.
Bayan anwangale musu gate din gidan sun fito da tsalatsalan motocinsu ne, kaitsaye su Riyyam suka wuce Hospital, shikuwa Company’n sa ya nufa.
Koda ya isa company din kuwa ya samu, ma aikata madasa in juna suna ta aikinsu, Domin yau din injunan da zasuna had’a kwalaye da buhuna ake kafawa amazauninsu.
Sosai ya jinjina kansa ganin yanda aikin nasu ke tafiya yanda ya kamata.
Kasancewar kuma akwai aikin da zaiyi ne yasa, kaitsaye ya haura sama inda Office d’insa yake.
Acan gida kuwa Baba Maud’o na zaune yaji karan horn din mota, atunaninsa ko su Rayyern dinne suka dawo, hakan yasa ya wangale gate din gidan.
Barrister Kabir kuwa dake cikin motar, kaitsaye ya shigo da motar tasa cikin gidan.
Bayan ya gama dai-dai-ta parking din motar tasa ne kuma, ya bud’e ya fito, saidai kuma ayau din bashi kad’ai yazo ba, atare dashi akwai Dr.Sajo.
Karasowa wajen Baba Maud’on sukayi tare da bashi hannu sukayi musabaha.
Baba Maud’o kuwa fuska asake ya amsa musu, sannan kuma da kansa yayi musu iso zuwa cikin gidan, har cikin babban falon kuma ya kaisu.
Ganinsu ne kuma yasa Abba fadada fara’arsa, tare da sawa Mamy tayi musu tarba maikyau.
Bayan sun gaggaisa ne kuma, Barrister Kabir ya gyara zama, tare da Kallon Abban ya gabatar masa da Dr. Sajo.
Haka dai suka Dan tattauna, agame da abunda suke shirin had’awa.
Bayan kuma sunyi tattaunawa mai tsawo ne, suka yanke shawara akan cewar yau Idan an sauk’o daga sallan Jumm’a za’a daura auren.
Da wannan batun sukayi sallama.
Inda Abban ya rakosu har waje, bayan sun tafi ne kuma ya zauna anan awajen Baba Maud’o suka d’an soma tattauna wasu batu.
Acan Office din Rayyern kuwa. Ganin 11:30 am ne yasa shi mik’ewa. Tare da barin duk wani abu da yakeyi.
Kaitsaye kasa ya sauko, saboda yanason sake komawa gida saboda yin shirin zuwa masallaci.
Koda ya shiga motar tasa kuwa cewa Hadi yayi su wuce gida.
Take kuwa kaitsaye suka nufo gida.
Koda ya dawo gidan, wanka ya sakeyi inda ya shirya kansa cikin riga da wando da kuma babbar riga, ta hadaddiyar getzner’n da ak’alla kudinta ya haura sama da 100k, sosai kayan sukayi masa kyau kasan cewar kalarsu lemon green ne kana zaren da aka watsawa garen su kuma shudi ne da fari da baƙi sosai sukayi mishi kyau, musamman daya kafa hulan zanna bukar blue color Kansa, ga kuma wani tsadadden takalmin toms suma blue da agogo daya saka, Tabbas yayi kyau kwarai.
Domin shigar tasa bawai gama gari bace, shigace ta musamman, wacce ta kara bayyana kyau da kwarjininsa.
Bayan ya gama kimtsawa ne kuma, ya feshe jikinsa da turare tare da sauk’owa k’asa, saboda jiyo hayaniyar Ramadan da kuma Riyyam da yayi, wanda suma sun shirya ne tsab, Cikin sabin getzners dinsu, masu kyau.
Kallonsu Riyyam din kawai yayi kana a takaice yace.
“Ka kwaso kayanka ka dawo nan, ka dena kwana a hotel”.
Ya ƙare mgnar cikin bada umarni.
Cikin yanayin ba zata jin mgnar Riyyam-nsra ya kalleshi da alamun zaiyi mgn sai kuma yayi shiru.
Ganin tuni ya fice batare kuma daya ƙara ce musu komai ba.
kaitsaye ya fice daga cikin falon.
cikin sauri-sauri kuma ya nufi motarsa saboda bayason rasa hud’uba.
Bayan ya fita daga gidanne kuma suma suka fito inda suka shiga motar Ramadan daketa murna da farin cikin mgnar Hamma Rayyern ɗin nasu.
kaitsaye masallacin Alfruq’an suma suka wuce.
Acan gidansu Jannart kuwa hakanan tun tashinta yau din takejin zuciyarta na yawan tsinkewa, ga kuma wani irin faduwar gaba da takeji akai akai.
Sai-dai rashin sanin takamaimai abun yi, yasa ta fara ambaton sunan Allah a cikin zuciyarta.
Barrister Kabir kuwa, bayan yayi shirin zuwa masallaci, yau din ko motarsa bai dauka ba, da kafansa ya fito inda ya tako har bakin titi, taxi ya tara, tare kuma da yiwa mai taxi din bayanin inda zai kaishi.
Wanda kuma bako Ina bane face masallacin dake gefen gidan Dr. Sajo.
Koda mai taxi din ya saukesa a masallacin, kaitsaye wajen Dr. Sajo ya nufa, atare sukayi sallan Jumma’a, bayan sun idar da sallan ne kuma, Dr. Sajo ya fito musu da mota.
Kaitsaye suka nufi unguwar Nassarawa GRA.
Yayinda acan masallacin alfurq’an kuwa, bayan an sallame sallan jumma’an, Ramadan da Riyyam-nsra suka sulale, kaitsaye basu zame ko inaba kuwa sai kasuwa, saboda kafun su fita Abban ya basu kudi yace su sayo masa huhun goro da kuma katton katton na mintuna.
Sudai haka suka je suka sayo batare da sanin na meye bane.
Koda suka dawo gida, anan cikin falon Abban suka jibge huhun goron da kuma mintunan da suka sayo.
Dawowarsu kuwa yayi dai-dai da isowan su Barrister Kabir da kuma Dr. Sajo.
Inda Abba da kansa yazo yayi musu iso zuwa babban falon k’asa.
Bayan sun zazzauna ne kuma ya fita ya kira Baba Maud’o, inda yace.
“Baba Maud’o ka shigo, yau abun na musamman za’ayi acikin gidannan, Insha Allah yanzu za’a daura auren Rayyern.”
Idanu Baba Maud’o ya d’an fitar, lokaci daya kuma yaji wani irin farinciki ya lullub’e sa, wanda hakan yasa Cikin matuk’ar jin dadi yace.
“Masha Allah lokaci yayi kenan, yau dai Ranar Rayyernu ta tsaya, To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.”
Da “Ameen.” Abba ya amsa.
Dai-dai lokacin kuma suka shigo cikin falon shida Baba Maud’o.
Acan waje kuwa yanzu motar Rayyern din ke isowa, Jin sunyi horn ba a bud’e musu bane kuma, yasa Hadi fitowa da kansa ya bud’e musu gate din suka shiga ciki.
Da mamaki Rayyern yake Kallon bakuwar motar dake fake afarfajiar gidan nasu, yayinda daga gefenta kuma motar Usman PA ne wanda yazo babu jimawa, kuma shima ya shigo yana can cikin falon Abban.
Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito, Yana fitowa dinne kuma, Abba ma ya fito daga cikin falo, Kallon Rayyern din yayi, lokaci guda kuma ya hade fuskarsa, cikin tsare gida, ta yanda yasan Rayyern din bazai samu daman tambayarsa wani abuba yace.
“Hadi ka shigo daga ciki, kaima Rayyern ka biyoni.”
To Hadi yace tare da rufawa Abban baya, shima Rayyern din haka cikin daurewar Kai yabi bayan Abban nasa.
Suna shiga cikin falon kuwa, yaji zuciyarsa tayi wani irin harbawa, saboda yanda yaga mutane atare.
Daya bayan daya yake bin kowannesu da kallo, Koda ya sauke idanunsa akan Barrister Kabir, ji yayi wani irin abu ya tsarga mai.
“Oh My God meye kuma wannan mutumin ya sake zuwa yi agidan mu? Waishi bazai tab’a fahimta bane, nace masa ban shiryawa auren yartasa ba banasonta wai ko ana dole ne ai gaggawa dai bata da kyau.”
Yayi maganan azuciyarsa, tare da yin kicin kicin da fuskarsa.
Gudun kada yaji wata magana ta taso ne kuma yasa, cikin nitsuwa.
Ya ɗan motso ya gaidasu a mutunce.
Kana sauri-sauri ya soma kokarin haurawa sama.
“Rayyern zo zauna.”
Muryar Abba ta katse shi daga tafiyan da yakeyi, wanda kuma hakan yasa dolensa ya dawo cikin falon.
Zama yayi akusa da Abban nasa, tare da dago kansa ahankali yace.
“Abba Lafiya kuwa, meke faruwa?”
“Lafiya kalau sai alkhairi.”
Abban ya fad’a yana me d’an gyara zamansa, tare da fuskantar Baba Maud’o, cikin mutumtawa Hadi da karramawa yace.
“To Baba Maud’o kaine babba amatsayinka na babba kuma Kai ya kamata ka fada mana wanda zai zama waliyin Rayyern.”
Murmushi Baba Maud’o yayi, cikin muryar tausasawa yace.
“Kai ne zaka waliyancesa Alhaji, ai babu damuwa Dan uba ya waliyanci dansa.”
Baki Abban ya bud’e daniyar cewa wani abu, amma kuma saiya fasa saboda wani tunani daya fado cikin zuciyarsa.
Ajiyar zuciya yadan sauke tare da gyara zamansa yace .
“To shikenan ba matsala, wanene waliyin amarya?.”
“Gashi nan.”
Barrister Kabir ya fad’a yana mai nuna Dr Sajo, yana me fuskantar sauran mutanen dake cikin falon kuma da kyau.
Kai Abba yajinjina tare da juyawa ya kalli Rayyern.
Cikin yanayin dake nuna babu alaman wasa acikin magana ko fuskarsa yace.
“Rayyern kawo sadaki.”
Wani irin karya wuya Rayyern yayi, lokaci daya kuma ya narke fuska cike da tsananin mamaki yace.
“Sadaki kuma Abba? Sadakin menene, nifa…”
Ganin wani kallon da Abban ya watsa masa ne yasa shi yin shiru, tare da sunkuyar da kansa k’asa, asanyaye yace.
“Abba yanzu ba kudi ajikina, a daga auren sai na samu kudin.”
Cike da mmkin mgnar tasa Abba yace.
“Eh munsani fa baka da kuɗi.
Amman kada ka damu ko transfer ne kayi mana.”
Saurin dagowa yayi ya kalli Abban nasa, lokaci daya kuma ya kwab’e fuska, Murya araunace yace.
“Ni wayata ba charge, amma muje sama da Ramadan dakina in bashi kuɗin ya kawo muku.”
Ya ƙare mgnar yana yunƙurin tashi.
Alamun guduwa da yake son yi.
Murmushi ɓoye Abba yayi tare da danne kafaɗarsa kana yace.
“Zauna”.
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Abba Kudin zan bashi”.
Ya k’are maganar tamkar zai zubda hawaye.
Cikin tsare fuska yace.
“Ina kuɗin suke?”.
A sanyaye yace.
“Cikin bed side drower”.
Kallon Ramadan Abba yayi kana cikin, bada umarni yace.
“Ramadan jeka ɗebo kudin koma nawane kawosu.”
“To“ Ramadan din yace, tare da mikewa cikin sauri ya haura sama.
Inda Rayyern kuwa ya bishi da Harara kasa kasa.
Mintuna biyu kacal kuma saiga Ramadan ya dawo da bandir din yan dubu dubu, na dubu dari biyu, Dan kowani bandir dubu dari ne.
Mik’awa Abban nasu yayi.
Tare da komawa ya zauna.
Abba kuwa duka dubu dari biyun din ya mik’awa, Dr Sajo tare da cewa.
“Ni Alhaji Bashir Muhammad ina nemawa, d’ana Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara auren yar wajenka Jannart Idi Sale Dakata, akan sadaki naira dubu dari biyu.”
Karb’an kudin Dr Sajo yayi, tare da gyara zamansa cikin mutumtawa yace.
“Ni Dr Sajo Umar, na bawa danka Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara auren yata Jannart Abdulkarim Saleh Dakata akan sadaki naira dubu d’ari biyu.”
Daga nan kuma sukayi duk abinda ya dace na tsarin daurin aure bisa koyarwar musulunci.
“Alhamdulillah! Alhamdoulillah!! AURE Ya D’auru jama’a muyi salati goma ga Annabi.”
Cewar Baba Maud’o, cikin tsananin farinciki.
Adai-dai lokacin kuwa Rayyern ya rumtse idanunsa da karfi, tare da dafe dai-dai saitin zuciyarsa cikin rudu hadi da bugawar zuciya Ya……!
Danne jajayen labb’ansa.
“Innalillah wa innailaihi rajiun.
Oh ni Rayyern wannan wacce irin rayuwace? Wannan wanne irin ƙaddara ne mai tafe da jarababbe .ayataccen kuma lik’akk’en aure ne, shikenan dai ni.
Bani da freedom din kaina, dolen-dole sai an sako min wata acikin rayuwata!!!.”
Yayi maganar azuciyarsa, yana mejin tamkar ya mike tsaye, yace sam shi baiyarda da wannan auren ba.
Su Abba, Ramadan, da kuma Riyyam-nsra, kuwa gaba d’aya farinciki ne ya lullub’e zuciyoyinsu, more especially Ramadan da ayanzu yake Ganin shima ya samu chance na auren Rayhanna’n sa.
Baya ga haka kuma abun farinciki ne awajensu ace yau Hamma Rayyern din nasu yayi aure.
Barrister Kabir kuwa idanunsa ya lumshe tare da soma sauke ajiyar zuciya akai akai, Lallai yasan cewa yau din ya bawa Jannart Garkuwa, da kuma mafakar da babu wani mahaluki daya isa ketare ta, Allah Sarki Jannart marainiyar Allah, akullum Allah shike zama gatanta.
Dr. Sajo ne ya gyara zama, tare da somayin addu’a, bayan ya kammala addu’an ne kuma yace.
“Ina rokon Allah madaukakin sarki daya sanya al’barka da kuma al’khairi mai tarin yawa acikin wannan auren, Allah ya kade duk wata fitina da zata kunno Kai, Kai kuma Rayyern Allah Ubangiji ya baka ikon sauke nauyi da kuma hakkin dake kanka.”
Da “Ameen.” Duk suka amsa amma banda Rayyern wanda yakejin kamar yasa musu kuka, Dan takaici, Yayinda acikin zuciyarsa kuwa yace.
“Ni babu wani nauyi daya hau kaina.”
Barrister Kabir ne kuma ya d’an kallesu, kana. Cikin taushin murya yace.
“Nagode Kwarai da irin karamcin da kukayi mana, kun amince damu, sannan kuma kun karb’i auren y’armu da daraja, nagode Kwarai abu na karshe kuma da zan rokeku dukanku shine, Dan Allah wannan magana ta daurin auren ya zama sirri atsakaninmu, Domin nima dole ce ta sani yin hakan.”
Kai duk suka jinjina, Yayinda Abba Kuwa ya gyara zamansa tare da fuskantar Barrister Kabir din yace.
“Karka damu Barrister, nayi maka al’k’awarin bayan mu babu wani wanda zaisan da batun auren, haka kuma babu wanda zaisan da zaman Jannart acikin gidannan.”
Kai Barrister’n ya jinjina cike da gamsuwa, Yayinda Abban kuwa ya dawo da kallonsa gasu Ramadan din, cikin tsare gida yace.
“Dukanku ku tashi ku bamu waje.”
Aikuwa Rayyern kam dama kaman jiran hakan yakeyi, Domin bakin Abban ko gama rufewa baiyi ba ya mik’e zumbur, Da sauri Abba ya kalleshi har ya buɗe baki zaice banda kai.
Sai kuma kawai yayi shiru ya bishi da ido har ya haura sama.
Ramadan kuwa hannun Riyyam-nsra ya kama, suka nufi side d’insa, Tabbas suna cikin farinciki, amma daga wani b’angare tsananin mamakin yanda auren Hamman nasu ya kasance sukeyi, auren bazata, auren da ba tsammani kuma auren sirri auren shaidu goma.
Suna shiga cikin side din Ramadan din ne kuma, Riyyam-nsra ya zaro wayarsa, Yayinda shi kuwa Ramadan kaitsaye ya wuce toilet.
Riyyam kuwa numbern Mammynsa ya kira, bugu biyu kuwa ta d’auka, bayan sun gaisa ne kuma Riyyam din, ya dan jujjuya ya kalli kofar shigowa data Bathroom, tare da karyar da wuyansa gefe, bakinsa cike da tarin maganganu kala-kala yace.
“Mammy kinsan me yake faruwa?”.
Da sauri Mammy ta jujjuya mishi kai tare da cewa.
“A’a sai ka faɗa!”.
Numfashi ya ɗan fesar kana a hankali yace.
“Yau ɗinnan a yanzun nan aka d’aurawa Hamma Rayyern aure.”
Idanu Mammyn ta d’an zaro cike da tarin mamaki, tace.
“Aure kuma Riyyam, wanne irin aure haka?.”
Gyara zamanshi yayi tare da sauke nannauyan numfashin yace.
“Aure dai da kika sani Mammy irin dai wanda ake daurwa tsakanin mata da miji”.
Lumshe ido tayi cike da al’hini tace.
“Ikon Allah”.
Shi kuwa Riyyam-nsra ci gaba da cewa yayi.
“Mammy kinsan meye ma kuwa? acikin falo fa aka daura auren, kuma kwata-kwata bamu wuce mu goma ba, wa y’anda aka daura auren agabanmu”.
Da sauri tace.
“Toh wannan wanne irin aurene meke ɓoye a ƙasa, tabbas akwai manufar auren!”.
Da sauri yace.
“Uhumm ai baki sani, bama Mammy Hamma Rayyern fa bayason auren wallahi Mammy, karki ga yanda ya had’e fuska, kamar zai daki babu.
Domin shi kanshi baisan cewa za’a d’aura masa aure yau ba.”
Ajiyar zuciya Mammy’n ta sauke, cikin yanayin mamaki kuma tace.
“To Riyyam Allah Ubangiji yasan hakan shine mafi al’khairi, ya kuma basu zaman lafiya yasa kuma wani matakin nasara ne.”
“Ameen.” Ya fad’a, Ganin fitowar Ramadan daga cikin toilet ne kuma, yasa shi katse kiran, inda yacewa Mammyn nasa zai kirata anjima.
Acan falon Abba kuwa tafiyar su Rayyern dinne, yasa Usman P.A, Hadi da kuma Ari mikewa duk suka fice daga cikin falon, suna mai fadin Allah ya sanya alkhairi acikin auren.
Baba Maud’o kuwa Kallon su Barrister Kabir yayi, cikin muryar dake bayyana farin cikinsa, yace.
“Barrister mun gode da kyauta mai daraja.
Yanzu yaushe ne za’a je d’auko mana diyar tamu.”
Gyara zama Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutumtawa yace.
“Insha Allah ni dakaina zan kawo muku diyar ku, bama sai kunje d’auko ta ba.
Domin kamar yanda aka daura auren nan, asirrance haka kawo amaryar ma zai kasance asirrance, saboda nima acikin hikima zan samu na fita da ita daga cikin gidan da yake gab da zame mata kabari, bisa taimakon maigadin gidan, da kuma driver’nta, saboda mun shirya akan da misalin k’arfe sha d’aya zata fito daga gidan, Idan ta fito ni kuma zan dauketa na kawota.”
Kai duk suka jinjina, Yayinda Baba Maud’o kuwa yayi murmushi, tare da cewa.
“Masha Allah hakan ma yayi, Allah Ubangiji ya taimaka.” Da “Ameen” duk suka amsa.
Batare daya sake cewa komai ba, kuma ya tashi ya tafi.
Acan b’angaren Rayyern kuwa, yana haurawa sama, babbar rigar dake jikinsa ya zare, tare da hayewa saman gadonsa ya kwanta.
Idanunsa da sukayi ja, ya rumtse da karfi tare kuma da soma fitar da wani irin numfashi mai zafi ta bakinsa.
Shikam acikin rai da zuciyarsa ya rasa wannan wanni irin fitinannen aure ne da aka lik’a masa, gaba daya suna neman dagula masa rayuwarsa, wanda bai kuma San dalilin yin hakan ba, dududu acikin kwanaki goma da dawowarsa daga Ethiopia, acikin kwanaki takwas na cikin gomanne kuma, abubuwa mabanbanta suka faru dashi, aciki kuwa harda babban abu daya kasance Aure.
Auren da bai shirya masa ba, auren da yazo da wani irin k’ulli.
Sam arayuwarsa shi bai tab’a kawo tunani ko maganar aure cikin k’wak’walwarsa ba.
Fact Shi baima tab’aji ajikinsa cewar zaiyi aure ba.
But why yanzu suke son sanja masa rayuwa?
Yar karamar tsuka yaja, tare da gyara kwanciyarsa, cikin takaici kuma abayyane yace.
“Koma meye nidai bazan sanja tsarin rayuwata daga yanda na saba ba, babu wata mace agabana, haka kuma babu wata wanda zan tsaya kulawa da ita ehe inji da kaina ma mana.”
Ya kare maganan yana me jawo murfin bedside drawer’nsa, inda ya d’auko ledan chocolate d’insa na kinder bueno, bayan ya bare ledanne kuma yasa chocolate din abakinsa yana sha.
Acan falon kasa kuwa, su Abban suna gama tattaunawa ne, Barrister Kabir da kuma Dr. Sajo suka mik’e Daniyar tafiya, har bakin mota kuwa Abba ya rakasu.
Bayan yaga tafiyarsu ne kuma ya dawo gida, kaitsaye kuma dakin Mamy ya nufa, Dan sanar da ita abunda ke wakana.
*Jannart*
Zaune take akan lallausan carpet dake, cikin falon nasu, Yayinda ta duk’ar da kanta k’asa, nail cutter ne hannunta, tana gyara yan fara tun yatsun kafarta, Yayinda Momy da kuma Abdull ke zaune agefe.
Azahirance Idan ka kalleta zakayi tunanin, cewa hankalinta ya tafi ne Izuwa kan nails dinta da take gyarawa, saidai kuma awajenta sam ba hakan bane.
Domin tunaninta ya tafine izuwa wani waje na daban, wani abu takeji na musamman yau din, Domin kuwa abubuwa uku ne suka hade acikin rai da zuciyarta, Wanda kuma batasan dalilin jin hakan da takeyi ba.
Idanunta tad’an lumshe ahankali, saboda yanda takejin kirjinta na bugawa time to time, kuma zuciyarta na tsinkewa, Yayinda wani abu mai kama da fargaba ke yawan tasan mata.
Acan kasan zuciyarta kuwa, ji take tamkar ana zare mata wani babban kaso na daga cikin damuwarta.
Jin kanta take tamkar awata duniya sabuwa.
Bud’e kofar falon da akayi ne kuma yasa ta saurin d’ago kanta.
Inda idanunta sukayi mata tozali da Daddy.
Har zata dauke Idanunta daga kan Daddy’n ne kuma, Idanunta suka sauka akan Junaid dake bayan Dadyn, wani irin matsanancin fad’uwar gaba taji, lokaci daya kuma duk jikinta ya d’auki tsuma.
Wani irin matsanancin tsoro ne ya shigeta, wanda hakan yasa tayi saurin mik’ewa tsaye.
Ido biyu da sukayi da Junaid dinne kuma, yasa ta soma girgiza kanta, tare da jan jikinta baya baya.
Kamar wanda aka tsikara kuma, haka ta juya Cikin sauri, har k’afafunta na hard’ewa ta nufi sama.
Idanu Junaid ya zazzaro cike da haushi hadi da takaici.
Yace.
“Ke Jannart, Ki dawo nan dan Uwarki mahaukaci kika ganine da zaki gudu, ki dawo nan na fad’a miki.”
Ya k’are maganan cikin d’aga murya da tsananin b’acin rai.
Jannart kuwa duk da taji kiran da yakeyi mata din, amma Sam batajin zata tsaya ko ta juyo ta sauraresa.
Domin sosai ganin nasa ya haifar mata da tsoro, hadi da kuma tsananin fargaba, kasancewar. Ganin nasa da tayi ayanzu, ya dawo mata da duk wata bakar izaya daya gana mata.
Daddy dake tsaye kuwa, Ganin hakan bai wani dameshi ba, hasali ko damuwa baiyi ba, saima juyawa da yayi ya fice daga cikin falon, yana me amsa kiran wayan da akayi masa.
Momy da Abdull kuwa tsit sukayi, domin sunsan suna magana zai sauke abunda ke tsakiyar kanshi anasu kan.
Kwata kwata Junaid ba mutumci ne dashi ba, baya ganin darajar kowa acikin gidan, musamman ma Momy da ko kadan baya mutumtata, amatsayinta na matar Babansa.
K’wafa yaja tare da fesar da hucin sauran hayakin taban dake bakinsa, cikin haushi da kufula kuma ya zaro wayarsa tare da dannawa numbern Jannart din kira.
Jannart kuwa da bata zame ko ina ba sai cikin dakinta, tana shiga kuma ta dannawa kofar key.
Numfarfashi ta soma fitarwa, tare dasa hannunta ta dafe kirjinta dake bugawa, dai-dai lokacinne kuma kiran Junaid din ya shigo cikin wayarta.
Arazane takai dubanta ga screen din wayar, ganin sunan Junaid din dake yawo akan screen din wayar nata ne kuma, yasa tayi saurin karasawa jikin gadonta, ayunkurinta na rejecting call dinne kuma, tayi picking batare da ta sani ba, still batare kuma da ta.
Ankara da hakan ba, ta cilla wayartata kan gado, tare da daura pillow akanta ta kwanta.
Junaid dake tsaye afalo kuwa jin Jannart din ta d’aga wayarne yasa, amatukar hasale yace.
“Yau zakici uwarki wallahi, wancan karon Sumar dake kawai nayi, amma yanzu kasheki ma zanyi kawai kowa ya huta, wallahil azim kuma nayi rantsuwa, adaren yau basai gobe ba saina cika burina akanki, yar iskar yarinya kawai me zubin munafukai.”
Yana gama fad’an hakan ya kashe kiran, sai faman zuba huci yake tamkar mayunwacin zaki.
Dab da zaifita ne kuma ya juyo, ya bankawa Mom da kuma Abdull Harara, cikin halinsa na y’an shaye shaye daya saba yace.
“Mchewww munafukai kawai.”
Yana gama fadin haka yasa kai ya fice daga cikin falon.
Momy kuwa Kai ta girgiza, cike da takaicin halin Junaid din kuma tace.
“Insha Allah babu wani burinka dazai cika akan Jannart, bazaka tab’a samun nasara akants ba kowanni mugun nufinka, in banda ma halin dabbanci da hauka, ace yarinya uwarku daya ubanku daya amma baka da aiki sai musgunawa, da son b’ata rayuwarta, hmmm Allah Ya kyauta.”
Abdull dai dake zaune shiru yayi, saidai kuma har acikin zuciyarsa yana matuk’ar takaicin irin rayuwar da akeyi acikin gidan nasu, wanda kwata-kwata babu girmamawa ko tarbiya acikinsa, kiri-kiri ana zalunci amma babu wani wanda zaiyi magana.
Acan b’angaren su Abba Kabir kuwa, Koda suka baro gidansu Dr. Rayyern, abakin titi Dr Sajo ya sauk’e Abba Kabir, inda kaitsaye Abban ya Tari taxi ya nufo gidansu Jannart.
Koda ya iso cikin unguwar daga nesa, yasa mai taxi din ya sauk’eshi, bayan ya biyasa kudinsa ne kuma kaitsaye ya nufi katafaren gidan Yayan nasa.
Tura k’aramar k’ofar dake jikin gate din yayi ya shiga, bayan sun gaisa dasu Ashiru dake bakin gate dinne kuma kaitsaye, ya nufi cikin gidan.
Koda ya shigo ya samu su Momyn, bayan sun gaisa ne kuma Momyn tasa Abdull ya cika masa Dan table din dake gabansa da kayan drinks hadi da fruits.
Lemun exotic ya dan kurb’a, tare da duban Momyn.
“Yaya Baya nan ne?”
Ya tambaya da kulawa.
“Eh dazun nan ya fita babu jimawa, amma munyi waya dashi, wai wani meeting ne aka kirasa na gaggawa.” Momyn ta bashi amsa.
Shikuwa kansa ya jinjina, alaman gamsuwa, kamar zaiyi shiru kuma sai ya sake duban Mamy, tare da cewa.
“Jannart fa, kodai ta tafi wajen aiki ne? Duk da shigowa na ma naga guard dinta awaje.”
Ajiyar zuciya Momy ta sauke, cikin Dan yanayin sanyi kuma tace.
“A’a Jannart tana sama, batama jima da haurawa ba, dazu dukanmu mu nan azaune, dawowan Junaid ne yasa duk ta tsorita.”
D’an Jim Barrister Kabir din yayi, na y’an wasu daƙiƙu kafun daga bisani, ya mik’e tsaye, yana me cewa.
“Badamuwa To bari na haura saman na duba ta.”
Da “To.” Momyn ta amsa, Yayinda shikuwa kaitsaye ya wuce saman.
Koda ya karasa jikin kofar nata tsayawa yayi, tare da kwankwasawa.
Jannart dake kwance akan gadonta, Jin ana knocking kofar nata ne yasa ta zaro Idanunta da sauri tare da tashi zaune.
Kana cikin yanayi na tsoro, saboda duk atunaninta Ya Junaid dinne ya biyota.
“Jannart! Jannart ki bude nine Abba ne.”
Barrister Kabir ya fad’a, cikin dan daga murya yanda zata jiyosa.
Jin muryar Abba Kabir dinne kuma ya sata, sauke Wata irin wawiyar Ajiyar zuciya, tare da tashi cikin sauri ta nufi kofar.
Murza key din tayi ta bud’e k’ofar, wanda hakan ya bashi daman shigowa, murmushi tayi kana cikin jin wani abu na daban, acikin zuciyarta da ganin nasa ya haifar mata tace.
“Good morning Abba.”
“Morning Jannart, fatan kina lafiya.”
“Lafiya na kalau Abba.”
Ta fad’a tana me komawa kan gado ta zauna.
Shikuwa Abba Kabir din karasawa cikin dakin yayi, tare da zama akan daya daga cikin bedside carbinate dinta.
Bayan ya zauna dinne kuma, ya zura Hannunsa acikin aljihun rigarsa, tare da zaro rapper’n kud’i.
“Jannart.”
Ya kira sunanta cikin tausasawa.
“Na’am Abba.” Jannart din ta amsa tana me juyowa izuwa gareshi.
Shikuwa Abban Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauk’e, tare da d’an muskutawa ya kamo hannayenta, rappern kudin dake hannunsa ya dank’a mata acikin nata hannun.
Cikin muryar da yake fatan zata gamsar da ita yace.
“Ga sadakin ki Jannart, an d’aura miki Aure yau, bayan an idar da sallan Jumma’a.”
Amatuk’ar razane da kuma wani irin bugun zuciya ta d’ago Idanunta da suka firfito ta kalleshi, hakanan taji maganan Abban nata wata iri, duk da kuwa tasan da plan d’insa nayi mata aure, amma sam kwata-kwata bata tab’a kawowa aranta cewar, arana irin tayau za’a daura mata aure ba kana taji kalmar tayi mata nauyi.
Ganin Abba Kabir din na kallonta ne kuma yasa Ahankali ta janye Idanunta kasa, tare da kama y’an yatsun hannunta ta soma motsawa.
“Jannart.”
Again Barrister Kabir din ya sake kiran sunanta.
Idanunta da sukayi raurau ta d’ago ta kallesa, dai-dai lokacin kuwa hawayen dake cikin idanun nata suka gangaro zuwa kan k’uncinta.
Cikin sanyi da kuma raunin dake kwance acikin zuciyarta tace.
“Abba Karik’e su awajenka.”
Kai Abba Kabir din ya girgiza, tare kuma da dan gyara zamansa yace.
“Bazan karb’a ba Jannart, sadakin kine kuma halal dinki, sabida haka ki rik’e awajenki.”
Yana gama fad’in haka ya kuma saka hannayensa acikin aljihun rigarsa, sweets da kuma chewing gums ya fito dashi, tare da Mika mata Cikin kulawa yace.
“Ga goro da kuma sweets din daurin aurenki.
Alhamdulillah kin tabbata matar aure yanzu Jannart, babu wani wanda zai sake kokarin keta haddinki, ayanzu kin tabbata mai y’anci, zan kaiki inda zaki samu kariya, zan kaiki wajen way’anda nake da tabbacin cewa ko bayan ba raina, zasu zame miki Garkuwa, har abada ina al’fahari da wannan Auren naki Jannart, kuma Insha Allah yau da dare zan kaiki d’akinki, na dank’aki ga Mijinki, sannan karki damu da batun su Baba Ado da Baba Ashiru maigadi, akoda yaushe Idan kika fito zaki samesu abakin gate, sannan na sashi yasa maganin bacci acikin abincin bodyguard dinki, ta yanda za ki fita ba tare da sunsan da hakan ba, Baba Ashiru ma yasan duk wani shirin mu, sannan ki tabbatar idan zaki fita babu wanda ya ganki, ciki kuwa harda Momyn ki, Abdull da Junaid, meyene Junaid din ya miki dazu har yasa kika hawo sama.”
Ya jero mata jawabin a tare.
Idanunta ta d’an marairaice, kana asanyaye tace.
“Ni tsoronsa nakeji Abba, daya shigo nagansa shine na gudu, amma kuma ina shigo daki saida ya kirani awaya.”
Kai Abban Ya jinjina, cikin gamsuwa da samun wata sabuwar dama yace.
“Alhamdulillah dama me kyau, to kidai kiyaye idan zaki fita, Idan ba Baba Ashiru da Baba Ado ba, banason kowa ya ganki Jannart, sannan kina fita kibi layin bayan kunnan, ki tsallake layi uku ana gefe zaki sameni Ina tsaye ina jiranki, please Jannart kiyi komai da takatsantsan.
Dan inason na mikaki ga mijinki cikin aminci, wanda nake da yakini akan zamanki acan zai kawar da duk wani damuwarki.”
Kanta ta d’an jinjina, kana cikin muryarta dake rawa tace.
“Insha Allah zanyi abunda kace Abba, amma inajin wani irin acikin zuciya da gangar jikina, inajin cewa zanyi kewar Daddy Momy, da kuma Abdull, yanzu idan na tafi kuma sai yaushe zanzo na gansu?”
Tak’are maganan Idanunta suna zubda da k’walla.
Ajiyar zuciya Abban ya sauke, tare da kamo hannunta Cikin kulawa yace.
“Kada ki damu Jannart, Insha Allah Watan-warana zaki zo ki gansu, komai zai dai-dai-ta.”
Kai ta d’an jinjina, still kuma da muryar kuka tace.
“Abba kayi hakuri kawai dai inajin ba dadi ne, Ina son gidanmu sosai, inajin banason barinsa, matsalata kawai.
Yah Junaid ne, shine wanda ako da yaushe baya son farinciki na, asanadinsa ne kuma yau gashi, zan bar gidan zantafi wajen way’anda, basu sanni ba.”
Hannayenta Abban ya kama, tare da girgiza mata Kai.
“Kada kiyi kuka Jannart, gidan da zan kaiki zai samar miki da ingantaccen farinciki, mutanen cikinsa masu karamci ne kuma zasu zame miki yan uwa da yardar Allah, kinsani Jannart bazan tab’a cutar dake ko na kaiki inda za’a cutar dake ba.”
Kai Jannart din ta jinjina, alaman gamsuwa da kalamansa.
“Yauwa Jannart, Allah ya sanyawa rayuwar aurenki al’barka, sannan idan zaki fita, ki tattare duk wani abu naki mai amfani, kama daga kan laptop da kuma certificates, and duk wasu takardunki masu amfani, ki sasu ajaka ki kuma taho dasu, wayoyinki kuma ki barsu a nan a tsakiyar gadonki. Maganan kaya kuma banda kayan jikinki kada ki d’auki kaya ko kala d’aya, ni da kaina zanje na saya miki kayayyakin da zakina sawa.”
Kanta ta jinjina tana mai son tsaida hawayenta, Yayinda shi kuwa Abba Kabir din, ya mik’e ya fice daga cikin dakin.
Yana fita kuwa Jannart din ta mik’e, jiki asanyaye ta soma harhad’a takardun ta dama yan kananan abubuwan ta masu amfani.
Ab’angaren Abba Kabir kuwa yana fita daga cikin gidan, kaitsaye gidansa ya nufa.
Koda yaje ya samu Aunty Dijat zaune afalo, anan yake shaida mata cewar yau an daura Auren Jannart.
Farinciki ne ya lullub’e zuciyar Aunty Dijat, cikin jin dadi tace.
“Masha Allah, gaskiya naji dadi Allah Ya basu zaman lafiya, yaushe za’a kaita gidan Mijin?”
“Adaren yau zan kaita, amma Dijat karki manta, wannan maganan sirrine atsakaninmu, muddin ta fita daga bakinki, kada kiyi tunanin soyayyar dake tsakaninmu, da kuma irin zaman lafiyar da mukeyi, hadi da al’amarin yaya, zan watsar da ita, zan gurfanar dake agaban hukuma, ke kanki zan iya daura ayar zargi akanki.”
Kai Aunty Dijat din ta jinjina, cikin yin imani da abunda zata fad’a tace.
“Insha Allah Abban Hafeez, zaka sameni me matuk’ar sirrinta sirrinka, da izinin Ubangiji, wannan magana ba zata tab’a fita daga bakina ba.”
Kansa ya jinjina, alaman gamsuwa da bayanan nata.