Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta yi amai ta lashe, inda ta bayyana abubuwa masu fashewa ne suka fashe a Sabon Gari, ba tulun gas ba kamar yadda ta sanar da farko.
Wannan na zuwa ne bayan jama’an DSS sun kama wasu ‘yan Boko Haram biyu da mota dauke abubuwan harhada bama-bamai da bindogi.
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa fashewar da aka samu a Sabon Gari a ranar 17 ga wannan watan, hari ne aka kai ba fashewar tukunyar gas ba ne kamar yadda ta sanar da farko.
A farko’ ‘yan sanda sun sanar da cewa tunkutar gas da ake amfani da ita wajen yin walda ce ta fashe a kusa da wata makaranta, abin da ya jawo mutuwar mutane tara ciki har da yara kanana dalibai.
Amma a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai jiya Asabar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa mutumin da ke siyar da abubuwan da ake hada bambaman, Michael Adejo, yana cikin wadanda suka mutu a harin.
“A ci gaba da binciken da muka gudanar a kan fashear abin da ake zargin gas ne ko kuma abubuwa harhada bamabamai, wanda ya auku ranar 17 ga Maris 2022, a No. 01 Aba/Court Road a No. 01 Aba/Court Road, Sabon Gari, kano, wanda ya sandiyar mutuwar mutum tara da kuma rushewar gone-gone ciki har da gjnin makarantar Winners Kids Academy da ke daura da wajen da abin ya faru.
Sauran wadanda suka rasu a fashewar sun hada da; Ejike Vincent (mai walda); Michael Adejo (mai sai da sinadarai); Musa Kalla (mai sai da shayi); Christiana Abosade; Mary; Austine Dada; Madam Owoleke; Omo Ben da Bose Oladapo,” in ji shi.
Ya ce a binciken farko da suka gudanar sun gano cewa daya daga cikin mutum tara din nan da suka rasu, wato Michael Adejo, sun gano babban dilar sinadaran harhada abubuwa masu fashewa ne.
Kiyawa ya kara da cewa bayan sun gudanar da binciken kwakkwaf sun gano cewa sinadaren da ake harhada bamabamai a shagonsa. Sannan an fahimci akwai alakar kasuwanci tsakaninsa da ‘yan Boko Haram din da jami’an tsaro suka kama da abubuwa masu fashewa a makon nan.
Dama dai jama’ar yankin da fashewar ta auku, tun a lokacin suka yi watsi da ikirarin ‘yan sanda, inda suka zarge su da neman yin rufa-rufa a kan lamarin.