Matar Hariji Page 5 Romantic Hausa Novel
_________📝Tabe baki tayi ta dauki qwaryarta tace “nikam Baffana da yan gdanmu ba yar iska bane basuda bindira ni kadama ka qara cewa kasanni banasonka kuma……” Rufe mata baki yayi yace “ni kuma inasonki zan aureki idanma bakiso bazanyi miki ba kawai kallonki zantayi kiyita sani nishadi ko?” Daqa masa kai tayi tace “amma ka yarda zaka nunamin din ko?” Murmushi yayi yace “har wasa zakiyi da ita ma” Dariya tayi ta fara juye masa nonon saida ta gama dure masa a jarka sannan ta qulle masa furar a leda tasa masa a but sannan ta dawo ta tsaya kusa dashi tace. “Kayyy wannan mutum oye kwai shirgege kalla fah a saitin qugunka nike” matsawa yayi yace “aa kalla sosai a saitin qirjina dai ko? Murmushi tayi tace “yawwa Ina abuna da kace zaka siyamin?”Jan hanunta yayi ya zagaya ya sanyata a mota shima ya shiga ya zauna yace “na siyo miki amma ban gaji da ganinki ba so nake nayi miki wata tambaya inaso cikin satinnan zan turo iyayena su nemamin auranki, a yau nakeso idan na koma gda na sanar da mahaifina inason qara aure amma idan munyi aure Lagos zaa kaimin ke fah”Wata uwar harara ta galla masa tace “tabdi kaje ka saidani kwarankwatsa dubu bazanje ko inaba”Kallonta yakeyi da mamaki shikam tunda yake bai taba ganin sakaryar yarinya irin Jiddoh ba bude mata qofa yayi yace “naji jeki” wata leda ya dauko ya miqo mata yace.“Ga alqawarin da nayi miki jiya ki kula da kanki zanje Lagos May be zanyi sati daya kafin na dawo kome ke akwai zanji gurin Alhajinmu.Hannu ya sa a aljihunsa ya zaro yan dari biyar bayar da baisan adadinsu ba ya kama hannunta yasa mata tare da kissing dinta yace “ki bawa Gwaggo Koda yake muje kawai inganta da kaina banson tallan nan naki”A fari taso qin yarda suje wuronsu dashi amma yanda yayi kicin² yasata dole ta yarda sujedin bisa sharadin saidai su tafi a qafa haka kuwa akayi suna tafe yana janta da hira yana dauke da qorain nonon nata har suka iso bayan gdan cikin saa kuwa sukaci karo da Gwaggo ta debo ruwa a rafi ta tsaya tana kallonsu cike da tsoro hadi da kunya irin tasu ta fulani ta saki bokitin ta juya da sauri.Binta yayi shima yana fadin “Gwaggo ki tsaya bafa wani abu bane don Allah ki tsaya ki saurareni”a wata kwana suka hadu da Inna Jumme ta tsaya itama ta tsaya tasan halin abokiyar zaman nata duk da Jiddoh ba ita kadai bace amma itace mace ta fari to a al’adarsu ta fulani bazata taba tsayawa tayi mgn da duk wanda yace yanason Jiddoh ba balle Lameer da dama ba qaunarsa sukeyi ba.Inna Jumme ce ta tareshi tace “oye miye yake hwaruwa kaiko bazaka samawa kanka lfy ka fita harkar diyarnan ba tunda sunce bazasu baka ba” Shafa sumarsa yayi ya durqushe yace “Wlh nima nayi qoqarin hakan amma na kasa Inna nabawa Hauwah kudi ta kula da kanta sannan na bata ta kawo muku a daina dora mata tallan nono saboda bata gari Inna Hauwah tanada garin jiki kuma halittarta tana daukan hankalin maza komai zai iya faruwa ta fadamin komai da dalilin da yasa batason aurenta da Mahadi don Allah kada kuyi Mata dole kada kuja da ikon Allah wlh zan aureta kuma zan riqe muku ita amana fiye da abinda kuke tsammani”Kallonshi Inna Jumme takeyi cikin tausayawa tanaji a ranta dama Ladingon ta ce ta samu wannan dan gayun da kota tsiya² sai anyi auren tace.“amma ta yaya zaayi kace ta daina tallan nono bayan dashi muka saba?” Qasa ya sakeyi da kansa yace “eh nasani amma nasan kunayi ne domin ku samu kudin cefane to ga dubu hamsin nan ku rinqa cefane har na dawo sannan a fadawa Baffa yayi hqr yau talata to rana i ta yau magabatana zasuzo don Allah ya taimakeni ya amsheni a matsayin zabin ubangiji”………………….________📝Cikin tausayawa Inna Jumme tayi masa gdy ta nufi hanyar da zata isar da ita gda tana zuwa ta tarar da Jiddoh tsaye tana leqensu ta cafketa ta.Juyowa tayi cikin muguwar kidima tana ganin Inna Jumme ta sauke ajiyar zuciya tace “inna Kado tausayi yake bani wlh kamar nayi masa kuka yau har qwallah naga yanayi dazun fah”Kamata tayi tare da daukar ledar kayan suka shiga suka bajeshi a tsakar daki Jiddoh ta rinqa bin kayan da kallo kayane bana wasa ba ya hado Mata harda dogayen ruguna turaruka hijjabai da takalma sannan kayan kwalliya hatda relacxer ta manya guda biyu.Wani tsalle tayi tace “Aradun Allah wannan shi zan rinqa shafawa nima jikina ya koma irin nasa ya daina kaushi da kirci Inna Jumme jikinsa fa shi har wani danshi yakeyi kuma duk jikinsa gashine irin na yan majigi”Daquwa Jumme tayi mata tace “ke ar wannan ai saidai abawa Gwaggonki amma yayi miki yawa a man shafawa irin nasa farin nan nefa ke kuwa ai farace” Turo baki gaba tayi tace “aa ne yaseen shi meye yasa baiyi farin ba nidai kibani abuna na bude na gani” mangari takai mata tace “uwariyonki ko sille baki tabawa cikin kayan nan nasan baffanki bazai bari ki karba ba ki bari mu boye sai mu nunawa Gwaggnki kudin kinsan su bakinsu daya da Ardo fah”Shiru tayi kamar me nazari kafin ta kunto kudin daya bata kel kel dasu yan dari bibbiyu har na dubu ashirin ta zaro ido tace “Inna jaka dari ce mun shiga uku siyemu zaiyi fah”Karba Inna tayi ta qirga jikinta na rawa tace “mun boni Jiddoh jaka dari uku da hamsin ya bamu Ina zamu kaisu?….”“Ku kawo nan sukaji an ambata tare da bude labulen Ardo ya shigo a fusace yace “wato na lura kema kina daya daga cikin masu budewa yarinyar nan ido da kudi ko to bari kiji Jumme aradun Allah ko Moddibo ubana daya kawoni dunniya zan iya dagawa sanda akan wannan shegen yaron me idon agwagwa”Wartar kudin yayi da qarfi a hannun Inna ya fita da sauri duka suka miqe suka bisa ya nufi madafi da aka balbala wutar kashin shanu ana girki ya cusa kudin.Inna Jumme tace “Ardo sheden ka qona da wuta oye Ardo kanada hankali kuwa jaka dari uku da hamsin fah Ardo”Itakuwa Jiddoh durqushewa tayi a gurin ta rusa ihu tace “na shiga ukuna Baffa ka qona masa kudinsa wayyohh Kado dama ban karbar maka kudinka ba Baffa me zance masa….” Sanda ya daga zai maka mata Gwaggo ta tareshi tace “oye Ardo diyagga da gaskiyarta wannan qiyayya taka da yaron nan Lameeru tayi yawa koma meye ai bai kamata ka huce akan kudi ba yanzu idan yazo yace a biyashi me zaka bashi”Hayayyaqo Mata yayi yace “ya kada galkena ya tafi dasu ai dama ba yau suka saba kashe mana shanu da hada baki da barayin burtali su kada mana shanu ba aradun Allah Hari da Jumme kowacce ta sake sakan baki akan mgnr makirin yaron nan jikan sarkin noma qur’anin Allah saita tafi gdan tsohonta”Yana fadin haka ya juya ya shiga dakin ya dauko kayan kwalliyar ya fita dasu Jiddoh ta bishi da sauri cikin tashin hankali tana kuka tana fadin “ayyah Baffa kada ka rabani da kayan kwalliya na nima so yake nayi kyau na zama yar gayu….” Bai tsaya sauraronta ba ya zubasu a wata tsohuwar rijiya ta qarasa da gudu ta leqa rijiyar ko hango batayi saijin zubarsu ciki tayi ta zube a gurin ta dora hannunta akanta ta runtuma wani ihu tare da fizgar ledar ta rungume a qirjinta shi kuwa Ardo ya angijeta ya wucce abinsa ya barta rungume da leda tana kuka tana kirar “shikenan kayan kwalliya na sun tafi rijiya Kado yaushe zaka dawo ka kawomin wasu………………

