Hausa novels

Halysaah Page 139 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 139…Har Ajay ya dawo part din wajen karfe uku Yakumbo na nan tana ta yi ma Khaleesat labarai iri iri, wani na ban dariya, wani ban haushi, wani tausayi, Khaleesat really enjoyed her company and she wish Ajay zai yarda ta dawo part din nasa gaba daya, Yakumbo na ganin Ajay ya dawo ta bar bangaren bayan ta sallami Khaleesat, Sai a sannan Khaleesat ta bude package din da Yakumbo ta kawo mata inji Mami, tana budewa taga tsadadden Waist bead ne sai Musk shi ma mai kyau da tsada…..taken Hadiyah ga shi ko zuwa bangarenta ta gaisheta ta dena yi komai a walakance take mata yasa ta ajiye kawai bata bata ba, Khaleesat ta maida waist bead din cikin package dinsa sai ga Ajay ya fito alamar fita zai sake yi tana ganin haka ta marairaice tace “To ni sai a barni ni kadai?” Ya dan kalleta yace “Kin koma kin duba Mami?” Ta girgiza masa kai, zai fita ta bi sa da sauri tace “To ka rakani pls” Yace “Kin mance hanyar?” Ta gyada masa kai, dariya ma ta basa bai dai ce komai ba ya fita parlon tana biye da shi har suka isa part din Mami, tun da garin Allah ya waye sai sannan Hadiyah ta zo bangaren Mami dubata da jiki shi ma Jay ne ya tilasta ta, kuma da ta zo part din sai tayi zamanta a parlor bata shiga dakin ba, da safe dama Aunty ta sanar ma Ummi da su Hajiya A’isha cewar taga Khaleesat dakin Mami har tana mata gyaran kaya shi ne har yanxu babu wanda yago part din duba Mami cikinsu, shi kansa Jay da ya zo da safe bai dawo ba sai da azahar ya sake shigowa dubata, Ajay na shiga parlon Mami da Khaleesat Hadiyah ta dauke kai taki gaida shi, ya nufi dakin Mami Khaleesat na biye da shi, Hadiyah ta bi ta da wani matsiyacin kallo, exactly irin kallon Khaleesat ma ta mayar mata ta dauke kai, Hadiyah ta bude baki da mamaki ganin hararanta fa Khaleesat tayi, Mami na zaune ita kadai a dakin ko TV bata kunna ba, ta juya tana amsa sallaman su, Ajay ya zauna kan kujera Khaleesat ta karasa kusa da gadon ta zauna kan Carpet ta gaisheta sannan tayi mata ya jiki, Mami na kallonta tace “Jiki Alhamdulillah” Ajay ma yayi mata ya jiki tace “Da sauki” Mami tace “Ki duba kitchen ki dauko min bowl da cokali” Mikewa Khaleesat tayi ta nufi kofa ta fita zuwa kitchen din Mami, Hadiyah na aonin habe es mile to hi to tans bursi toon be dongaba da tafiya tayi banza da ita, Fixgota Hadiyah tayi tace “Magana nake maki don ubanki idan ba tsoro ba ki tanka min mana” Khaleesat ta fincikota a fusace tace “Sai dai ubanki amma ba nawa ba wallahi, kuma kece matsiyaciya mara tarbiyya not me” Ajay ne ya fito daga daki tare da Mami dake biye da shi jin hayaniyar su, Hadiyah na ganin Ajay ta sake Khaleesat bayan Khaleesat ta cikata ita ma, Mami ta hade rai sosai tana nuna ma Hadiyah kofa tace “Fita ki ban waje, kuma kada in sake ganin kafarki a sashin nan….” Hadiyah ta wani harareta ta juya fuuuu ta nufi kofar fita daga parlon sannan ta juya ta kalli Khaleesat tana nunata da yatsa tace “Zaki san kin zagi ubana kin kirani mara tarbiyya wallahi” Daga haka ta fice daga parlon, Mami na kallon Khaleesat tace “Tafi aiken da nayi maki” Khaleesat ta juya ta wucu kitchen din, bayan ta dauko bowl din ta koma dakin Mami, Mami ta nuna mata food warmer dauke da pepper soup da mai aikinta tayi tace “Dibar min kadan a ciki” Khaleesat ta zuba mata pepper soup din sannan ta mika mata bowl din, Mami ta amsa tace “Kar ki sake kulata a gidan nan” A hankali Khaleesat tace “To in sha Allah” Ajay ya mike ya fita daga dakin don dama pharmacy zai je siyo mata magani, sai bayan fitarsa Khaleesat tayi ma Mami godiyar sakon da ta ba Yakumbo ta kai mata, har kusan Magrib Khaleesat na bangaren Mami a zaune, tana son komawa part din Ajay amma tsoron haduwa da Walid ko a hanya ya hanata tafiya, Har sai da Ajay ya shigo da Drugs da ya siyo tun da rana, ta sauke ajiyar zuciya ganinsa, bayan ya nuna ma Mami prescription din drugs din yayi mata sai da safe, Mami ta kalli Khaleesat tace “Ki tashi ku je sai da safe, Nagode” A haka suka bar parlon Mai martaba kansa a kasa, Sarki dai sai kallonsa yake tun bayan da yaji abinda ya kawosa, after almost a minute sarki ya numfasa yace “Ka koma zuwa ina kenan?” Ajay bai dago kansa ba yace “Ko a nan garin ne ranka shi dade….” Sarki yace “Ohk, kawai dai ya zamto baka cikin Emirate kake nufi ko?” Ajay yayi shiru bai ce komai ba, Mai martaba yace “Isn’t it?” Ajay ya gyada kai a hankali yace “Haka ne ur highness” Sarki yace “Ohk, amma meye dalilin ka? Ko don saboda abinda ya faru recently?” Ajay yace “A’a dama ina da wannan intention din in har zaka amince min zan koma daya daga gidajenka na cikin garin nan in zauna” Calmly Sarki yace “To ban amince ba Ahmad, don bana son kayi nisa da ni, kafin ka zo da wannan batu Jawwad ne ya fara zuwa min da shi kuma na hanasa, ina son ku duka biyu a kusa da ni, and i will make sure ur wife lives comfortably in this Emirate if that’s ur fear Ahmad” Ajay ya girgiza kai da sauri yace “A’a ranka shi dade ba don abinda ya faru bane, dama tun asali kasan i prefer staying outside of the Emirate” Mai martaba yace “Learn to love staying inside of the Emirate Ahmad, babu zancen barin ka cikin gidan nan, i won’t be king forever, I won’t rule forever, wataran dole ka gaje ni, and you will rule this great Emirate in sha Allah” a hankali Ajay yace “Allah ya huci zuciyarka, ur wish is my command in sha Allah, a gafarce ni idan na bata maka rai da batun nan” Sarki bai kara cewa komai ba, bayan minti daya yace “Kuma yaushe zaka koma bakin aikin ka?” Ajay yayi shiru don babu inda tunaninsa ya tafi sai kan Khaleesat and how she will Cope in the palace idan ya koma aiki, A hankali yace zan zauna a gida. I know that, ko ka zauna gida naga ba shigowa fada kake yi ba ake yin komai da kai, baka involving kanka a abubuwa da yawa da suka shafi masarautar nan, it is as if you are not even in the House, to me yasa sai kayi shawara kafin komawa bakin aikin ka?” Ajay ya sauke idonsa yace “Ranan Litinin in sha Allah zan koma” Sarki yace “Allah ya taimaka” Ajay na ta zaune parlon har bayan wani dan lokaci Sarki dai sai kallonsa kawai yake, dai dai sanda Walid ya bude kofar parlon ya shigo, yana ganin Ajay a ciki har ya fara komawa baya zai fita sai kuma yaji yana ma Mai martaba sai da safe, hakan yasa ya tsaya, ai bai san yana ciki ba tun daxu da tuni ya tafi bangaren sa wajen Khaleesat, Ajay ya mike ya nufi kofa ya fita Walid ya bi sa da kallon gefen ido sannan ya karasa cikin parlon. Ko da ya koma part dinsa ya tarar da Khaleesat har tayi bacci a bedroom dinsa, yala kan kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran ya lumshe ido, bai yi tunanin Sarki zai yi turning down request dinsa na barin Palace ba and he really felt bad about it, yayi tunanin sarki zai yi considering abubuwan dake faruwa ya basa go ahead din barin gidan even if it’s just for a while, ga kuma maganar aiki da zai koma ranan litinin and today is Thursday, ji yayi kansa ya kulle gaba daya, bayan abubuwan dake faruwa gidan babban dalilinsa na jin bai son zaman masarautar saboda Jay ne don bai son suna haduwa in anyway ta haka kadai ne zai iya concentrating…. Washegari da asuba Ajay na tafiya masallaci Khaleesat ta je ta kulle kofar babban parlon ta ciki kamar yanda ta saba, tana idar da sallah ko azkar bata gama ba taji ana knocking kofar parlon, mamaki tayi don in ya tafi sallah sai karfe bakwai da rabi wani lokacin har da minti arha’in yake dawowa nart din ranta va hata hra all to open the door tace “Waye?” Yace “Bude min kofa” A hankali ta murda kofar ta bude tana kallonsa ya shigo parlon ya wuce parlonsa, ta kulle kofar ta juya ta bi bayansa har zuwa parlon, kafin ta shiga har ya shige Bedroom still ta bi sa, ta gansa tsaye yana kokarin cire jallabiyarsa alamar kwanciya zai yi, tun bai gama cirewa ba ta koma other bedroom din zata karasa azkar dinta sannan ta shiga wanka, Ajay ya fasa cire jallabiyan bayan ya tuna zai duba jikin Mami ya juya ya sake fita daga dakin zuwa part din Mami, Khaleesat ta daga kai jin kamar fita ya sake yi, after few minutes ta mike ta fita daga dakin, sai da ta kara shiga bangarensa ta duba don tabbatar da fitan yayi sannan ta fito ta nufi babban parlor da nufin kulle kofar da makulli taga an bude, tsabar shock kasa kwakkwaran motsi tayi a wajen ganin Walid, can ta juya da gudu ta koma daki da nufin saka makulli amma taga Ajay ya cire makullin, cikin rikicewa tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Tuni ya shigo har cikin dakin yayi kasa da murya yana bin ta tana komawa baya yace “Babu wani Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, duk ke kika jawo, da kin bani hadin kai tun a America da duk ba a zo nan ba amma ke me taurin kai kika ki bani co-operation, to yanxu dai mijinki na can masallaci suna karatu da sarki da wasu fadawa kuma shi da fitowa daga masallacin nan dai sai kusan karfe takwas, don haka kawai ki sallameni in kama gabana, kin ga kafin nan ma har mun mance mun yi wani abu, idan kuma kika ce yau ma taurin kai za ki min ko kuma ki min ihu wallahil azeem sai in kashe ki in kashe banza, bar ganin an samu CCTV camera part din Mami, nan babu ko normal camera ki ji in gaya maki halle cctv” Randa rawa hahu ahinda iikin Khaleesat ya hau rawa kamar mai jin sanyi, shi ko fisge hijab din jikinta ya fara yi kamar yasan ihu take da niyyar kurmawa ya shake wuyarta da hijab din yanda zata san da gaske fa yake sai ya iya kasheta idan bata basa hadin kai ba, hakan bai sa ta fasa kururuwa ba tana basa hakuri duk da muryarta bai fita sosai saboda shakar da yayi mata, a haka ya yage hijab din jikinta da karfi tun daga wajen wuya har kasa sannan ya jefata saman gado, da sauri ya fara cire belt dinsa jikinsa na rawa ganin alamar kayan bacci ne ma a jikinta, dai dai sanda aka bude kofar dakin, da mugun shock ya juya suka yi ido hudu da Ajay dake tsaye bakin kofar, nan ya fara mayar da belt dinsa da sauri yana zare ido, Khaleesat kuwa kuka ta dinga yi tana rufe jikinta da hijab dinta da ya yage ta sauka daga kan gadon ta tafi gun Ajay jikinta na rawa tana kuka sosai, Walid sai gwalo ido yake bayan ya gama saka belt dinsa yana kallon window din dakin ko zai samu hanya, a nan kasan dakin Ajay ya jefar da wayar hannunsa ya karasa ciki ya fincikosa yana kallonsa da idanuwansa da suka yi ja, ya fito da shi har zuwa Main parlor, ya fara masa wasu mugayen kulli a ciki, Khaleesat na ganin haka ta saka wani hijab ta taho parlon da sauri ta riko Ajay tana girgiza kai tace “Noo plsss, don girman Allah kawai kayi reporting dinsa….” Hankadata Ajay yayi sai ga ta kan kujera ta fadi, Yana jan Walid ya bude kofar parlon suka fita daga part dinsa gaba daya har suka yi nisa da bangaren nasa, Walid na kokarin guduwa Ajay yasa kafa ya kwashesa kasa sannan ya lankwashe hannunsa daya ya take da karfi, Walid ya kurma wani wagegen ihun azaba don sai da hannunsa yayi wani kara bayan Ajay ya take hannun, Ajay ya dagosa ya hau sauke masa wasu arnayen kiss ta ko ina yana yana jin wani irin yanayi ya dena ganin fuskarsa sam ya dena ganin fuskarsa saboda jinin da ke zuba a goshinsa, tuni mutanen gidan suka fara fitowa jin ihun Walid, hakan kuma bai sa Ajay ya fasa dukansa ba yana bugasa da bango yana punching dinsa, Cikin tashin hankali su Hajiya A’isha da Kilishi da Ummi suka dinga cewa “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, mun shiga uku mun lalace, kashe sa zaka yi? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, jama’a ku kawo agaji zai yi kisan kai” Daga nesa Aunty ta tsaya with shock tana kallon dukan da Ajay ke ma Walid jikinta na rawa, ta fashe da kuka ta taho da sauri ta cakumo Ajay tana jijjigasa tace “Kashe min dan nawa zaka yi Junaid? Kashe min Walid din zaka yi?” Ko kallonta Ajay bai yi ba bai kuma fasa dukan da yake ba, su Maryam da Khadijah sai rusa kuka suke, da sauri Ummi ta tafi ta saka ayi kiran Mai martaba dake Masallaci, Dogar Dogarai biyu suka zo kwace Walid hannun nun Ajay bayan Kilishi ta tafi ta kirasu…. aika anyı kıransu also stood in shock yana kallon scene din, ya karasa wajen cikin sauri ya finciko Ajay da karfi yace “Are you out of ur senses? What is this u are doing? shaye shaye ka fara??” Mukhtar da shi ma shigowarsa kenan yayi saurin Janye Walid shi da wani Dogari bayan Jay ya finciko Ajay ya hadesa da bango, Ajay ya fixge hannun Jay daga rikon da yayi masa yana huci kamar zaki, dai dai sanda Mai martaba ya karaso wajen yana kallon Ajay babu ko kiftawa, Ajay yaki yarda ya kallesa ya kauda kai yana sauke numfashi, can kuma ya juya ya bar wajen kamar zai tashi sama ya tafi part dinsa, Sarki ya bi sa da kallo, duk sauran mutanen wajen ma haka suka bi sa da kallo, Aunty na koke koke ta bi bayan wa enda suka fita da Walid su Ummi duk suka bi bayanta da sauri, Mami dai na tsaye bakin kofar part dinta ta kasa cewa komai.

Back to top button