Mijin Marigayiya Page 36 Hausa Novel
Yana shiga ya tara da ita ta fito daga wanka tana shirywa. Tun kafin ya gama shiga dakin tace ‘Allah ya sa dai an gama abinci don wallahi yunwa nake ji kamar an min sata a ciki.’‘Akwai dai bread, sai dai idan kin fito ki dafa ruwan zafi da kwai haka sai mu karya.’Da mamaki ta kalleshi tana cewa ‘Ruwan zafin ma sai na dafa? Yau ne fa kwanana na farko a gidan, haba! Kitchen din ma ban san inda yake ba.’Cikin damuwa yace ‘To ko order za a yiwo?’‘Ni ban gane ba, wai ita matar gidan bata girki ne?’Ya karasa kusa da ita yana kokarin kama dogon gashinta da take tajewa yana cewa ‘Ki bar wannan maganar, ki zo muje na nuna miki kitchen dinki sai ki samar mana ruwan zafi mu karya. Idan kuma akwai inda zaki iya yiwo mana order a kawo nan da awa daya haka to sai na tura kudin.’Ta jijjiga kai ‘Gaskiya babu, sai dai ko na rana don wallahi kwana bakwai din nan sai na yi su ba tare da na dora tukunya ba. Don ni abinda na sani matar gida ko ‘yar gwal ce idan aka yi amarya ita take girki kafin a zauna a raba.Haka yayi ta bata hakuri yana lallabata, daga karshe ta shirya suka sauko parlor dinta ta dafa musu ruwan zafi sanna ya debo kwai ta soya musu.Wajen 12pm ya hadasu a parlor dinsa yayi musu introduction; ita naja amarya sai muzurai takeyi tana wata yanga, ita kuwa khadeeja cike da walwala tayi mata maraba suka gaisa babu laifi. Ya sanar da su idan an kwana bakwai zasu raba kwana kowacce kwana biyu.Ba karamin mamakin Khadeeja yayi ba, ko da yake wannan ba bakon abu bane a wajensa. Tayi masa rashin kunya mintuna kadan kuma ta koma kamar ba ita ba. Shi yasa a lokuta da dama yake kasa fassarata.Ganin walwalarta ya saka ya sa rai cewa zata yi abincin rana da su, amma gudun kada akuma ya sa ya bita don ya tabbatar. Sai dai ta tabbatar masa da cewa ta figa ta dafa abincin rana tun da safe kuma nasu ne ita da yara, sauce ne kawai a fridge zata dumama ta hada musu salad su ci. Ko amsa bai bata ba ya fice ya barta a dakin, tabi bayansa da harara tana dariya.Don haka da rana tayi sai akwai ya yiwo order din abinci aka kawo musu har gida, haka ya kirawo yaransa gaba daya suka hadu da Naja suka ci suka koshi. Ita kuma Khadeeja ko damunta abun bai yi ba, taci abincinta ta zubawa hafsa sannan ta bayar da ragowar.A haka aka karasa wannan amarcin. Kullum Khadeeja zata dafa abincinta shi kuma zai ywo order su ci su koshi tare da amarya da yarasa. Babu wanda ya taba yiwa Khadeeja tayi ita kuma bata taba tambayarsa nata kason ba.Tayi zaton ranar da kwana zai dawo kanta zata ji tana cikin yanayin murna, sai dai ba hakan ya kasance ba. Yau ne zata karbi kwana amma sai taji kamar ma ba zata iya bari ya kusanceta ba saboda lkamar dai har yanzu kokari take ta saba da cewa su biyu ne matansa. Haka dai ta tashi ta gama duk wata hidima da takeyi. Ya riga ya sanar da su cewa da daddare za adinga karbar kwanan don haka tun yamma ta shirya abincin dare; duk da bata cikin walwala amma haka ta girka baincin da ta tabbatar yana so; tuwo miyar kubewa danya. Ta hada komai ta jera a table din sama. Sai dai ga mamakinta har wannan lokaci Naja tana dakinsa na sama, don haka ma bata ko je kusa da dakin ba tana jiran ya dawo taji ko shine zai biyota dakinta tunda dai kwananta ne.Da yake bayan ya ci abincin rana ya sake fita sai wajen 8pm ya shigo gidan.A dakinta ya sameta tana mike a kan gado da Hammad a kwance a kan cikinta yana wutsil-wutsil dinsa. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya karasa ya zauna gefen gadon.Suka dan taba hira sanna tace ‘Um ga abinci can a dinin fa, idan ka shirya sai mu je mu ci. Yara dai sun ci nasu don yau tun magriba Nas ta fara jin yunwa.’‘Oh,Ok.’ Ya amsa kamar mara gaskiya.Tace ‘Kuma na ga amarya har yanzu tana dakin naka fa, ko a nan zamu kwana ne?’Kamar wanda aka tayar daga bacci yace ‘Umm. No, umm kin gane? Dama ina so nayi miki magana don da na san zaki dafa abincin darem zan ce ki dakata.’Ta kalleshi da mamaki tana jira taji karashen bayanin, suka hada ido yayi sauri ya kawar da idonsa. Suka dan yi jim sannan ya cigaba ‘Ina ga ya kamata tunda ke kina jego ki bar mata kwnakin naki zuwa lokacin da zaki cika arba’in ko?’Ta dauke Hamma daga kan cikinta ta tashi zaune tana karewa Mustapha kallo ko zai sauya maganarsa, kamar bai fahimci sakon ba don sai ya kara hade rai yana wasu muzurai. Tayi murmushin yake tace ‘Oh, yanzu kenan kwanan gaba daya na amarya ne har sai na cika arba’in da haihuwar Hammad?’‘Eh, to ai kinga kina jego. Menene amfanin kwanan?’Ta sunkuyar da kai, ta dago ta kalleshi sanna tayi gajeran murmushi tace ‘Hakane, Allah ya kai mu arba’in din.Kamar wanda aka tsikara ya mike yana yage baki yana cewa ‘Yauwa, to bari naje sai da safe ko.’Cikin sauri ya fice daga dakin kamar wanda yake tsoron kada ta rikeshi tace ta fasa.Tabi kofar da kallo bayan ya fice; wasu hawaye masu zafi suka gangaro kan fuskarta a daidai lokacin da wani malolo ya taso ya tokare mata makogoro take neman kasa numfashi. Sautin rufe kofar ya dawo da tunaninta cikin dakin bayan da ta kifta idonta; tayi murmushi mai ciwo tare da sunkuyar da kai. Wato dai yanzu Mustapha yayi sabuwar amarya har ya fara gudunta, tunda ai lokacin da tayi bari sai da ya nuna bacin ransa a kan tafiyar da tayi gida. To me yake nufi da ita? Wato idan wahal ce taje ita kadai tayi ta sha kenan, lokacin da zai iya morarta shine lokacin da zai bata kwana. Lallai akwai aiki amma dai ba zata fasa addu’a duk da zuwa yanzu duk dan wani karsashin kyautatawa Mustapha da take so tayi ya zirare.Sai da Hammad ya fara kuka sannan tayi ajiyar zuciya ta sa bayan hannunta ta share hawayenta sanna ta mika hannu ta daukoshi daga inda yake kwance ta saka masa nono. Har ya gama shan non ya saki tana ajiyar zuciya, ta shiryashi ta goya shi sannan ta fice daga dakin. Da yake dare yayi tana jiyo muryarsu kasa-kasa sun hira tunda dakin nasa yana jikin nata dakin. Haka ta wuce da yaje a parlor dinta ta jera musu abincin daren can ta wuce taje ta kwashe ta mayar kitchen tana kwafa. Ta dawo suka kwanta ita da Hammad…
