Uncategorized

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 7

ZUCIYA DA KWANJI 

BOOK 1___7

Na Maimuna Idris Sani Beli

 Sadiya ta dinga yi masa wani kallo, kamar mai shirin tashi ta shake shi, Hindatu kanta a yau irin kallon da ta ke masa ke nan, tana ma shakkar anya shi din ne? Ko ya gansu fuskarsa ba ta nuna damuwa ba. Ya mikawa muftahu hannu suka gaida, sai muftahu ya ki sakin hannu nasa yana cewa.

 “A’ah!” 

Abdullahi ya fizge hannunsa ya zauna ya ce, “Kai dallah malam manta wannan maganar”. 

  A tunzure sadiya ta ce “Babu maganar ladatarwa, ni ma ga nawa girkin can yana jiranka”. 

 Muftahu na dariya ya ce, “Shekarar 2012” “Na karba”. Abin da Abdullahi ya ce ke nan, ya kuma canza wata hirar inda ya

hau tambayar muftahu game da saurensa da za a yi kwanan nan.

 Muftahu ya ce. “Kai aure da wuya Abu Turab, wallahi kamar na daga auren nan, ku ne auren ba ya muku wahala kake samun ‘ya’yan dattijai, kasan na yi mamaki wannan auren naka? Ban taba zaton a gidan ‘yan boko ana karbar sadaki kawai a bada aure ba.

 Sadiya da ta ke a wuya ta tari numfashinsa ta ce, “To ba gara wanda za a cajeka sosai a barka da KWANJINKA ba, yanzu don Allah ina amfanin abin da Abu Turab yake? Shi ke nan kullum a hanyar gidan abinci idan ba haka ba ya daura zani ya shiga kicin…. Kasan Allah Abu turab da wasa na kamaka kana mata girki ranar girkina sai mun yi tashin hankali da kai?”

  Budar bakinsa sai cewa ya yi, “To sai

dai kar a kuma”.

  Muftahu na murmushi ya ce “Ba a yin haka Abu turab, ai duk matsayinsu daya a gurinka…”

 Abdullahi ya tari numfashinsa ya ce “Babu ruwanka muftahu, ban tauyewa kowaccensu hakkinta ba, saboda haka babu ruwansu da dangantaka da wata ko naman jikina ta ke yanka, wai kowa ba da halinsa zaka zauna da shi ba, yanzu ke ba hakuri nake da halin kaifin harshen ki ba, ke kuma kullum kafarki a waje”.

  Wannan karon Hindatu ce ta shiga maganar.

“A’a Abu turab, maganar ka bar ni zuwa unguwa fa daban, maganar ka zama bawan wata ina ganin daban”.

 A fadace ya ce da ita “To duk ba sai ku yi abin da zaku yi”

 Da muftahu ya ga lamarin zai kwabe sai ya shiga tsakani suka shiga wata hirar daban, sai da ya fara shirin fita sannan

muftahun ya ce, “To ba zaka kirata mu gaisa ba?”

 Abdullahi ya ce, “Ka kyale wannan yarinyar muftahu, ‘yar rigima ce”.

 Cikin tsura masa ido muftahu ya ce, “Don Allah, to ba ta son auren ne?

 Ya girgiza kai ya ce, “Ko daya, akwai wata a kasa ne?”

 Cikin zulumi muftahu ya ce, “Kana ganin manya ba zasu shigo maganar nan ba Abu Turab? Wannan rayuwar fa ba zata dore ba, mace ba zata shiga kicin ta girka abin da zata ci ba ma bare kai ta baka, sannan kai ba wani amfana kake da ita ba….”

 Abdullahi ya yi fuska, ya ce, “Ya ya za ka ajiye min wadannan kunnuwan kana yi

min irin wadannan maganganun? Baka san mata ba ne rantse, sam ba a iyar musu, in ce Fatima ba ta soma su yi mitar na tsaya tana wulakanta ni, in ce in kadai nake sonta su ce abin da nake. Fice hankali ko na hada da nasu hakkin… Don Allah mu share wannan maganar zaka yi mamaki wata rana.”

 “Allah ya kai mu” Muftahu ya yanke zancen.

 Abdullahi ya ce, “Jira na yi wanka sai mu fita masallaci tare”. Ya shige toilet ya bar muftahu da su sadiya suna yi masa gutsiri tsoma. 

  Sai bayan sallar isha’I ya komawa Fatimah, ya karasa abin da ya rage ya shirya mata kan darduma a falo inda ta ke kwance tana kallo. Ya zauna a kujera yana dubanta. “Fatima kin taba cin danwake kuwa?” Ba tare da ta dube shi ba ta girgiza kai, ta ce. “Ina dai jin sunansa”. Ya ce, “to bari na zubo miki, Allah ya sa ki iya ci”. Bai jira cewarta ba, ita ma ba ta tanka ba ya zubo mata wanda ya tabbatar ya fi katfin cikinta ko da ta iya cin dan waken. Ya kawo gabanta ya ajiye, ya janyo tum tum ya zauna a gaban nata. Ta dan harare shi, sannan ta harari abincin ta ce. “Ni ba yanzu zan ci ba”. A tausashe ya ce. “Don Allah daure ki ci fati, kinga idan ba ki iya ci ba sai na nemar miki wani abincin”. Tsawon mintuna biyu sannan ta yunkura ta tashi ta janyo tasar abincin, ta tsirawa danwaken ido, sannan ta daga kai ta dube shi ta ce “Haka yake shi kuma?”

Ya kada mata kai. “Eh, ci ki ji”. Ta dauki fork ta kai daya bakinta tana juya shi a hankali ba zata iya cewa da dadi ko babu ba saboda rashin sabo, kuma mayar da cokali ta yi Abdullahi na kallonta har ta kai loma biyar. Ya ce, “Za ki iya? 

 Cikin dakewa ta dube shi ta kada kai.

 Sannu a hankali ya taso daga kan kujerar da ya ke yazo daf da ita ya dauki cokali ya saka a kwanon nata, A tausashe ya ce, “To bari na tayaki ci” Ta bata rai ta bata fuska sosai, sai dai ba ta tanka ba, kuma ba ta fasa cin abincin ba. Falon ya yi tsit, a nutse suke cin abincin, shi yake dawainiyar zuba mata lemo da ruwa har suka cinye dan waken ya zura mata ido ya ce, “Ya isa?” Ta kada kai tana janye jikinta gefe, ya zuba mata fruit salad din ya mika mata, sannan ya kwashe kwanukan zuwa kicin, ya dawo ya dafa kujera ya dan sunkuya ya ce, “Ina tafi?” Ta rufe ido ta bude ta dube shi ta ce. “Ya yi mata wani dunkulallen kallo gami da murmushi sannan a sanyaye ya ce, “To sai da safe”. Ta kokarta ta amsa. “Allah ya tashe mu lafiya”. Ya dan tsura mata ido, sannan ya juya ya fice. Ta sauke kai daga kallonsa, sai ta ji kewarsa ta darsu a ranta. Ta fara ji a jikinta Abdullahi ya samar da shakuwa a tsakaninta da shi, wanda sam ba ta so hakan ba, kuma tabbas yanayin bautar da Abu daya ke kuntata mata game da shi, shi ne yadda ta ke jin shakkarsa a duk wani abu da ya hado da shi, ko motsinsa ta ji sai gabanta ya fadi, shi yasa lokuta da dama ba ta iya ja ‘in ja da shi, sau tari karfin hali kawai take yi ta ke taya shi su yi fada, amma tsoron kaifin bakinsa ta ke, wanda yanzu ta fahimci dabi’arsa ke nan. Yau da safe da yake cikar nan yana batsewa ba karamin buguwa zuciyarta ta yi ba, shin kuwa akwai mutumin da ya taba samun irin wannan matsayin a rayuwarta? Ta nemi wayoyinta babu, ba ta zargi komai a ranta ba, da zummar duk lokacin da aka kirata zata gansu, amma har lokacin bacci babu labari, duk da haka sai ta share ta yi kwanciyarta.

   Abdullahi kuwa raba dare ya yi yana bude asiran wayarta, musamman inbox da sent msg, in da ya gano tsantsar so da kaunar da Alh ke mata, da kuma haukan kyautar da yake mata. Nata raddin ba ya wuce godiya da nuna tana kewarsa. A logs dinta ma, kiran Alh ya mamaye wayoyin, wanda suke bata mintuna har da awa akai. Duk sai ran Abdullahi ya jagule, wani garwashin kishi ya dinga babbaka masa kirji tare da yiwa Alh kallon wani dan ta’adda a soyayya, tare da cewa bai fi shi son Fatima ba, illa kawai ya fi shi sakaci da samun dama a cikin soyayyarta. Ranar da kyar ya runtsa don kunan zuciya, bayan ya yi flashing layukanta, ya yiwa wayoyin boyo na musamman.

Washegari da duku duku bayan ya dawo masallaci ya kwankwasa mata kofa, ta zo ta bude cikin yanayi na mai barci.

 Ya dube ta a nutse ya ce, “Kin yi sallah?” Ta gyada masa kai, bai ja magana a tsaninsu ba ya ce, “Zan miki karin kumallo ne saboda in son fit da wuri”. Ta ba shi hanya ya wuce kicin, ita kuma ta sake komawa dakin bacci har da murza key. Sai farkawa ta yi ta tarar da abinci a falo. Sannan falon a gyare tsab, kicin ma haka,wanke wanke ne kawai Abdullahi ba ya yi.

  Sai da ta yi wanka ta shirya, ta karya kumallo sannan ta sa dambar neman wayoyinta.

Wasa! Wasa! Har sha biyu tana fama ita da kanta ta fara zargin ko an dauki wayoyin ne, to amma wa zai dauka? Daga jiya zuwa yau ba ta yi baki ba, kuma babu mai shigowa dakinta sai Abdullahi, shi ma iyakarsa falo wanda shi din ma jiya kawai zata dorar ya sauya mazauni ya zauna. Sai gabanta ya fadi da ta tuno da wayoyin jiya ta barsu a kicin… Babu tantama shi zai dauki wayaoyin.to bisa wanne dalilin? Sai hoton bacin ran da ya shiga ranar da ta amsa wayar Alh saboda tsabar karfin hali. Ta wuni da tanadin bala’I iri iri wanda zata tari Abdul, sai kuma aka yi rashin sa’a ta shiga alwarlar sallar magariba ya shigo kawo mata abinci, bai kuma yi jiran fitowarta ba ya fice saboda sadiya ce da girkin kuma ta kafa ta tsare.

    Har karfe tara babu labarinsa, ta gama tanadin bala’inta har ya nemi fin karfinta, abincinsa kuwa ko kallonsa ba ta yi ba. Karfe goma ta gota, wanda a wannan lokaci ta gama zuwa wuya, kawai sai ta zira hijabi da silifas ta tunkari dakinsa. Lokacin yana tare da sadiya da Hindatu

wadanda suka balle littafin korafi, shi kuma yana biye musu har suna kirarin bar masa gida. Cikin su uku babu wanda cikinsa bai kada ba lokacin da fatima ta kwankwasa kofar falon, shi ya yi zargin Fati ce, to da me ta zo? Sadiya ta razana sosai, amma da Hindatu ta ce, “Ko waccan matar ce?” 

  Sai sadiyar ta wartsake, kufule ta ce, “Shigo”.

  Fatima na huci ta tura kofar ta shiga, sai ga Abdullahi zaune wanda da ya kishingida hankali kwance. Fatima ba da mu da kallon da kowa a falon ya zubo mata ido ba, musamman Abdullahi wanda gaba daya ya tsargu, wato tun ma kafin ya ji abin da ta zo da shi.

Also Read:

  Ta dan tsaya daga nesa tana kare masa kallo, ta ce, “Abdul ina wayoyina?”

  Muryarsa na rawa ya ce “Wayoyinki Fadima? Ba ki gansu ba ne?”

  Ta dakatar da shi da shakkiyar muryar da ta koshi da bacin rai. “Abdul kar ka raina min wayo don Allah, kawai ka ba ni wayoyina”. Kamar su kadai a falon, gaba daya Abdullahi ya rasa nutsuwarsa. A rikice ya karaso gabanta da muryar tausasawa ya ce, “Fatima maida hankalinki mana, me ye yake damunki haka?”

  Tana bude baki zata yi magana ya yi saurin rufe bakinta da hannusa, sannan ya ja hannunta da sauri suka nufi kofa, da ta fara turjewa ma kawai sai ya dauketa cak! Ya nufi dakinta har da murza key, sannan ya ajiye ta akan kujera ya durkusa gabanta yana rike da hannayenta cikin tarin damuwa ya ce, “Me ye haka Fatimah? Ya ya zaki nemi tona mana asiri a wajen da za a yi mana dariya alhalin Muna zamanmu lafiya ba tare da wani yasan tsakaninmu ba?

  Da nata hucin bacin ran ta ce, “To wannan kusancin da ka yi min na me ye? Don me zaka durkushe a gabana haka? Sakar min hannu”. 

   Ya girgiza mata kai yana kokarin shigar da idonsa cikin nata, “Abin da kika rasa ke nan, shi yasa kike son fitinata da zafin kai. Ga shi na ji na gani bana son damuwarki, Fatima me ya yi zafi?”

   Ta nemi kwace hannunta ta kasa, nema yake ma ya fice gona da iri, sai kawai ta sallama tare da zafafa murya ta ce, “Ban gane abin da na rasa ke nan…”

   Ya kuma tare ta da tasa muryar mai kama da rada “Haka na ce, ba ki san rashin kunsaci da masoyi yana mayar da mutum masifaffen karfi da yaji ba, batare da an ankara ba? Kadaici ya yi miki yawa Fatima, ina son nuna jarumta wajen abotakar gangar jikinki. Ba ruhinki kawai ba nake faman dawainiya da shi ba….. Ina ganin hakan zai sanyaya zafin kanki”. 

   Ranta ya yi mugun ɓaci, ga shi ba ta da matakin dauka domin ya kanainayeta! habarsa akan gwiwarta ya kuma matse tafukan hannunsu da juna…. Ita da ta kwashi masifa da neman ‘yanci ga abin da ya fi’yanci ta zungurowa kanta. Hawaye ya fara biyo kuncinta, ya bude baki yana mata kallon mamaki kamar bai san me ke akwai ba ya ce, “To wannan hawayen na me ye?”

  Ta ce, “Na wannan rungumar da kake min ne. Bisa wacce alakar zaka dinga hada jikinki da nawa?” Kai tsaye ya magantu.

  “Duk duniya babu wanda ya isa ya hada jikinsa da naki bai zama abin tir ba, duk kuwa da fuskar da kika dubi aurenmu”.

  “Ni maganar wayoyina nake maka ba maganar wani aure ba, kai ma ai kasan auren da yadda aka kullo shi babu kuma wanda ya isa warware wannan kullin…” Ta fada a gajiye,

   Shi kuma ya dora cikin karsashi. “An haɗo da kudirorin zuciya a wancan kullin? In an hado ki fada min zan yarda abin da nake ji a raina game da ke yau zuciyata ta haife shi….. Ta tari numfashisa cikin sartun hawaye

“Abdul….! Kai ka dauki wayoyina?” Ya yi zuru kawai yana kallonta, sai can ya girgiza kai yana murza tafin hannunta cikin nasa. Ta ga rikici da yawa a idanunsa, amma sai ta dauke su kanana akan wanda ke cin a cikin zuciyarta. Ta ladiye wani kududun bakin ciki sannan ta dubi tsakiyar idonsa ta ce. “Na ji zan yarda ba ka dauka wayoyina ba, idan a yanzu ka yi min abin da ka aure ni a kansa wato saki. Kwana sha hudu da sha uku ai duk daya ne. Saboda haka sallame ni… Sai zuciyata ta nutsu ba kai ka dauka ba”. Ba ta damu da sai ta ji amsarsa ba, kawai sai ta kwantar da kai a majinginin kujera. Ya saki hannunta a hankali, sannan ya koma hannun kujerar da ta ke zaune ya sunkuya ya fara lasar

labbanta har ya kai ga tsotsar, ko motsi ba ta yi

ba bare alamar zata hana shi, in ta gudu ina zata? In ta nuna masa karfi a matsayinta na wacce jarumar? Don kansa ya zabi saurara mata, sannan ya mike yana dan kai komo a tsakiyar falon, can ya dube ta yana rike da dunkullalen hannunsa ya ce, “Ni na dauki wayoyin”.

  Ta dage cikin sartun hawaye ta ce, “Abdul ina shawartarka da ka lura da zuciyarka don ba ka sa ta aiki ba, to ita zata saka, ka je ina tsumayinka gobe”. Ya yi mata duba na ‘yan sakanni sannan ya kada kai ya fice yana ce mata, “Godiya nake”.

  Ta bishi da kallo har ya bace lokacin da gaba daya duniyar ta yi mata kunci da zafi. A falonsa wayam! Babu sadiya bare Hindatu ,sai ransa ya yi masa zaki matuka, don bai ba wa kwakwalwarsa damar tanadin KWANJIN da zai karbi kalubalen sadiya ba, wadda ke takama da girki, gari banza ma ina kuma ga an taba mata shi a irin wannan lokacin? Da sauri ya garkame kofarsa don kar ta dawo, ya shige daki a gajiye ya fada gado. Yau ya zungurowa kansa fitina, ya san kuma ba zata jijiga shi da wasa ba ga sadiya ga Hindatu, ga kuma wadda ta ninke su a tashin hankali ta shanye, wato fatima. Da yake dama tuni ya shiryawa wannan yakin na fatima, sai jarumtarsa ta ba shi damar bacci a wannan daren, har ma ya sallaci karshensa tare da mikawa Ubangiji kokensa kamar yadda ya saba, ya kuma roki Allah ya ba shi sa’ar cinye jarrabawar da ya yi masa na jarrabarsa da matsanancin son Fatima duk da hatsarin da ke tattare da nuna mata so. Da ya dawo masallaci ma sai ya kara mayar da kofar dakinsa ya rufe, har karfe tara bai motsa ba. Sadiya ma da ta gaji ta kwaso masifarta ta biyo shi. Yana jinta ya yi lif, ta karaci bugunta ta kuma shakar wai kullacin ta koma. Cikin sanda ya murgina a gado ya ce, “Duk abin da zaki yi na dadi ne ‘yar nan”.

   Har sha biyu bai motsa ba kasancewar lahadi ce, tare da cewar ko su sadiyar bai sallama da maganar gida ba, bare ita uwar gayyar da sai ya girka ya kusa bata a baki. Kwasam sai ga kiran wayar kawun Fatima. Ya daga cikin zakuwa, suka gaisa ya ce masa, “Allah ya sa kana gida, yau na dauko momi zamu kawo muku ziyara, za mu biya.wani guri nan da awa daya zamu karaso”.

Haba wani matsanancin farin ciki ya kulle shi, ya dinga zubawa Allah godiya. Babu shiri ya fada wanka, cikin sanɗa ya fice daga gidan ya siyo musu abin motsa baki, don neman adalci sai ya hado da su sadiya, fatima kuwa dama ba ya maganarta yasan ta koshi da rikincin da ta tanadar masa. Ya dinga kwankwasa kofar sadiya tana sharewa, sai kawai ya rabu da ita ya koma kan Hindatu don kamar akan kaya yake, tsoro yake kar Fatima ta fito ta tsinka shi a tsakar gida.

  Kofar hindatu a bude ta ke, yana shiga suka yi kicibus, kawai sa ya mika mata ba tare da ya tanka ba, fuskarsa kuma ababu walwala, ta karba tana mamakin wannan irin mazewa. Yana fita ya ga sadiya a kofar dakinta tana cika tanabatsewa, sai ya yi kamar bai san tana yi ba, ya yi fuska ya nufeta yana cewa. “Me ya faru da tsakar ranar nan kika garkame kofa, kum don neman fitina kina jina ina bugu kika share ni?   

   Sai ta rasa ma abin da zata ce masa ta tsaya tana kallon wannan karfin hali. Bai barta haka ba sai ya mika mata nata kason yana cewa. “Ki zo ki dan gyara min falon can, baki zan yi. Ta karba a fusace ta shige daki tana cewa. “Sai ka yi kiran wadda ka kawai kwanan nawa ta zo ta gyara maka, ai ba ‘yar aiki ka ajiye ba.

   Ya ji wani sanyi ya ratsa zuciyarsa, wani lokacin da hargagi dadi ne da shi, yanzu dalallabata ya yi ya yarda ya yi laifi dai ta birkice masa. Awa daya ba ta cika ba su kawu suka karaso, ya sauke su a falonsa da karramawa, ya yi ta dawainiya da su har su momi ta kai ga zolayarsa, “Ina Zahra’une kake wannan dawainiya da kanka?”

  A ladabce ya amsa mata, “Dan baccin azahar ta kwanta, bari na tsota”. Ya fice gabansa na faduwa zuwadakin fatima bakinsa cike da addu’a kamar akan kaya ta ke, sau biyu ya rankwashi kofar sai gata ta bude tana sanye da hijabi don rainin hankali har da kit. Ya dubeta sama da kasa, fuskar nan tata dif! Babu alamar ta taba dariya. Ta miko masa hannu, sai ya ji ma dariya na neman subuce masa. Kawai sai ya yi fuska ya tureta ya wuce ciki. Ya juyo ya fuskanceta yana magana kamar ba ya so, “Kinga ban shigo ba tun safe ko? Ban ji dadin jikina ba ne”

  Ta kyaɓe baki gami da gyara rikon kit din a hannunta, ta ce, “Allah ya sauwake, ina jinka”.  

  Ya share abin da ta ke nufi cikin nuna kulawa ya ce, “Kin ci wani abin?”

  Ta kara daure fuska ta ce, “Idan na karasa gida na ci”. Ya yi murmushi yana dan ja da baya yana kallonta a kaikaice. “Fatima rigima ko? To anyi rashin sa’a yau gidan sun rigaki zuwan kuwa dan Momi sun kawo mana ziyara suna falona”.

   Alamun tsoro suka bayyana a fuskarta ƙarara, ta jefar da kit ta dafe kirji ta ce, “Na shiga uku, yanzu Abdullahi tona mana asirin zaka yi?”

  Ya yi saurin girgiza kai. “A’a fadima, Allah ne dai ya kawo su, tun wancan satin yake min maganar zasu zo.

  Ta sulale akan kujera a gajiye kamar wadda ta yi gudun famfalaki, ta rafka uban tagumi tana dubansa, sai kawai hawaye ya fara shatata aidonta, ya matsa kusa da ita yana girgiza mata kai.

  Ya ce. “To kukan fa?” Ta fara goge hawaye wani na bullowa,ta juya hannu ta ce. “Abdul su kawu ba su iya zuwa ba, da wacce dabara zaka sallame ni na bar gidan nan a yau ba tare da sun gane me ya faru ba?

  Ya dinga yi mata kallon tsabar son kanta da bata lokacinta wajen fadin maganar da ba zata yi mata amfani ba, koda yake akan sharafinta ta ke ba ta san me ye so ba, tunda ba ta taba dandanar zakinsa da dacinsa ba, shi yasa ta ke wasarere da irin wannan alakar da ke samar da shi, kuma kila ta yi amanna da cewa sai ka ga dama kake so, idan ka ga hagu sai ka ki. Amma da yake an ce yaki dan zamba ne, kuma ya yi digiri a kansa sai ya bayyanar da fuskar alhini sosai yadda duk wayonta sai ta gaskata shi ya ce. “Ni ma abin da ya dame ni yanzu ke nan. Ina ganin sai dai ki kara min lokaci…. Ko kwana biyu ne…… Ki karbi girki ke nan, akwai batutuwa da nake so mu tattauna kafin ki tafi, ba zan rufe ki ba Fatima ina shakkar dalilin da yasa kike son koma wa Alh. Shin ya isa ki salwantar da darajarki dominsa? Ban yarda gigin so ne ke dibarki ba, kuma bana yi miki mummunan zaton domin kudinsa kike so ki koma din…. 

To a amtsayina na musulmi dan uwanki ina son shawartarki kafin ki tafi din, inaso kin fahimce ni?”

  Da sauri ta girgiza kai, “Ba na so na fahimce ka, don ba na tsammanin shawarar taka zata yi min wani amfani, koma wanne irin nazari ka yi akan dalilin komawata gidansa ai dalili ne, na kudin da na soyayyar dama na wani abun daban idan ya gamsar da ni, ai shi ke nan babu abin da ya shafe ka”

   Ya amsa mata. “Shi ke nan, yanzu ina muka tsaya da maganar karin kwana biyun? Nan ma ta girgiza kai ta ce. “Ko kwana Ɗaya ba zan kara ba, idan kuwa na kara to sai ka dawo min da wayoyina”. Kawai sai ya hade rai ya nufi kofa, ya kuma watsa zancen da suke a kwandon shara ya ce, “Kin zo ku gaisa da su kawu, dan sauri suke”. Da sauri ta sha gabansa ta rike shi, sai dai ta kasa magana bakinta sai motsi yake. Ya dubi fuskarta ya dubi hannun da ta rike shi sannan ya kuma dubanta da shakakkiyar murya ya ce. “Ba zan jure shakar numfashinki ba, cika ni ki ban hanya na wuce”. 

  Ta hadiye wani tukukin takaici ko zata sami damar maganar, amma ya gagara. Ya yi tunanin ya yi maganinta sai ya tuna su kawu da ke jiransu, kawai sai ya tureta ya wuce yana cewa,  “Ya rage naki ki san da fuskar da zaki karbe su, ni dai na yi alkwarin kina kofa ni kuma zan yaga”.

Ya fice ya barta, duk da cikin rudu ta ke ba ta dauki lokacin nazarai mafita ba, da gudu ta bi bayansa tana goge hawaye, sai ya tsaya ta a hanya ya dinga goge mata hawaye da rigarsa bai damu da cewa fara ce rigar tasa ba. A karshe ya rungumeta a kirjinsa yana fada mata kalaman rarrahi. “Calm down… ki saukaka wa kanki damuwa fadima, duk wannan kuncin ina zatar masa sauki, hakuri da rashinsa kadan ne fadi”…. Ya dago kanta idanuwanta a bushe. Babu alamar hawaye… Ya kara murje fuskarta… Da hannayensa masu taushi, sannan ya ja … Hannunta suka tafi. Da nutsuwarta ta isa ga

kawu fuskarta da walwala sosai, suka gaisa sannan ta koma ga momi ta harde mata da

shagwabar nuna kewa. Ta ce, “Amma dai bawajena kuka zo ba momi, tunda kuka sauka dakin Abdul”.

  Ciki jin dadi kawu ya ce, “Ni dama ba wajenki na zo ba wallahi godiya na zo yiwa Abdullahi. Tana satar harara abdullahi ta ce,  “Da ya yi me kawu? Bayan ya kulle ni ya hana ni zuwa wajenku… Don Allah kawu gobe a kawo min motata”.

Also Read:

Zamu dakata a nan sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Ga masu bukatar Audio kuma za su iya saurara ta hanyar taɓa wannan hoton dake ƙasa. Mun gode da ziyarar Aihausanovels.


Back to top button