Uncategorized

Yadda Ake Dettol

 

Daga Aisha Muhammad AL-Tata 

Dettol sinadari ne da ake amfani da shi wajen kashe kwayoyin cututtuka. Akan zuba shi a cikin ruwan wanka domin a kashe kwayoyin cutar da yake a ruwa, sannan sau da yawa akan yi amfani da shi wajen goge ɗanyen ciwo da yake a kan fata, domin a kawar da kwayoyin cuta da yake a kan ciwon. Sau da yawa akan yi amfani da shi a ciikin ruwan wanki, domin kawar a ƙwayar cuta.

Amfani da Dettol na da matukar amfani, domin kuwa har mata masu jego kan yi amfani da shi wajen ɗaurayar kayan yaransu, duka saboda kawar da cututtuka da ke a kan fata, kaya har ma da goge-gogen kan tayels.

Abubuwan Da Ake Bukata

Sinadaran Hadin            Adadi

Pine oil                             10cl

Phenol (water based)    30cl

Carbolic acid                    30cl

Texapol                              10cl

Ruwa                                  5 liters

Kala                                    Yadda ake so

IPA / methanol                   2 liters

Preservation (formalin)    5CL

Flavor                                     Yadda ake so

Yadda Ake Haɗin

A kala da ruwa a dama.

Sannan a zuba phenol a ci gaba da damawa.

Sai a zuba IPA, texapol, carbolic acid da pine oil a ciki a ci gaba da damawa.

A zuba flavor da preservative

Daga nan kuma an kammala hadin sai a zuba a cikin robobi domin amfanin yau da kullum.

Back to top button