Uncategorized

Sha’awar Shi Nake Chapter 1 Hot Romantic Novel

Bissimillahirrahmanirrahim

Wannan labari ƙirƙirarrene,komai kaji  yayi daidai da rayuwarka/ki arashine.

Jannat Mus’ab ƊanMusa,Matashiya ƴar kimanin shekaru goma sha bakwai a duniya,

        Fara ce me ɗan matsakaicin tsawo,tana da round face ɗauke da fararen idanu,cycle masu ɗan girma da take yawan lumshe su.se ɗan madaidaicin baki daya dace da fuskarta ɗauke da fararen haƙora,masu ratsin wushirya a tsakiyarsu,kumatunta ɗauke da dimple,kyaƙkyawace ajin farko,dan duk inda akeso mace takai jannat ɗanmusa takai.

Ƴa ce ga Attajirin ɗan kasuwannan Alhaji Mus’ab Ɗanmusa.ɗan asalin garin ɗanmusa dake jihar katsina,amma zama da yanayin kasuwancinsa ya maidashi kano da zama,a unguwar nasarawa GRA.

Alhaji Mus’ab ɗanmusa ya jima yana neman haihuwa Allah be bashi ba hakanne yasa yake ɗauko ƴaƴan ƴanuwansa yake riƙesu wasu har ya aurar dasu.Bayan shekaru sun ja,shida matarsa,sika fawwalawa Allah lamuransu,inda aƙarshe ya amshi roƙonsu,ya basu haihuwa,inda suka haifo,jannat wacce tun daga kanta basu sake haihuwa ba,so da ƙauna da gata na gidan duniya ba wanda jannat bata ganinsa,tun tasowarta zuwa girmanta.

Alhaji Musab yafi kowa gatantata,shiyasa komai tayi daidaine,duk meson ɓacin ransa ya taɓota, yanzu ze nuna ma kurenka kuma duk matsayinka agunsa ka taɓo jannat yanzu zaku saɓa

Wannan kenan.

“mamy yanzu a can australia ɗin wa ye ze dinga goyani,?”cewar jannat wacce ke goye a bayan mahaifiyarta kamar jinjira dan har da zani tasa ta ɗaureta a bayan.

Download>>> Dangin Rabi Complete Document

Murmushi mamy tayi sannan tace”ay antynki zata dinga goyaki dan na faɗa mata bana son kisha wiya,”

“Anty muniba faɗa takemin kinga ko ay bazata goyani ba,kawai muje hutun tare mamy in dake bazatamin ba”cewar jannat cike da shagwaɓa.

“kwantar da hankalinki jannati na,Abbanki ya gargaɗeta kuma tace bazata takuraki ba” cewar mamy cikin nuna kulawa.

Haka hirar tasu taci gaba da wakana kan hutun da jannat zataje gun antyn ta Muniba ɗaya daga cikim ƴaƴan da Abbanta ya riƙa kuma ya aurar da ita ga abokinshi dake gudanar da harkokinsa acan ƙasar ta Australia  Alhaji  Bukar.

“jirgin nasu na dare ne,pls muniba yazamana kina airport ze sauka,kinga bata taɓa zuwa ba se wannan lokacin”cewar daddyn jannat lokacin da suke waya da muniba kan tasowar jannat ɗin yau.

“daddy karka damu insha Allahu zamu jira isowarta,karka damu game da hakan”muniba ta bashi amsa.

“ba damuwa yanzu zamu kaita airport”ya faɗi sannan ya kashe wayar ya juyo ya dubi mamy fuskarshi ba walwala yace.

“ji nake kamar zan rasa wani sashi na jikina,hajiya,ko kaɗan banson tafiyar yarinyar nan,dan de kawai kar suga na musu ba daidai bane yasa zan barta ta tafi”

“in banda abunka Alhaji sati biyu ne fa kawai zatayi kamar yau ne zaka ga ta dawo”cewar hajiya cikin sigar rarrashi.

Jannat ce ta fito sanye da riga da wando kanta ba kallabi se gashinta da ta ɗaure da ribon ya sauka har gadon bayanta,bame kallonta ya ɗauka bahaushiyace dan tafi kala da turawa,kyakkyawa ajin farko.

Cikin Takunta na burgewa ta iso gaban iyayen nata tace a shagwaɓe “dad time is going fa,kasan by 3 zanyi caching flight akwai buƙatar in isa airport yanzu”

Ba musu suka miƙe su duka suka mara mata baya dan tuni komai nata ansa a mota.

Suna shiga mota,driver yaja suka fice zuwa airport,se hira suke a motar kamar karsu rabu.

Isowarsu tayi daidai da fara kiran fasinjoji,dan haka basu wani jima tare ba sukai sallama tana tafe,tana waigo su suna ɗagawa juna hannu har ta ɓace musu.

Su daddy na nan tsaye jirgin su jannat ya tashi,sosai kewarta ta mamaye zuciyarsu da jikinsu,fatan sauka lafiya sukai mata,sannan suka dawo gida.

Haka suka isa gidan kowa jiki asanyaye na kewar jannat ɗin,wanda suka alaƙanta hakan da  sabo.

Wayyo rayuwa,awanni biyu da  tashin jirgin,ba tare da ansan musabbabin faruwar matsalar ba ya kama da wuta tun daga sama,har dirowarsa ƙasa.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

inda ya faɗo a wani ƙaramin ƙauye,da ke yankin ƙasar ethopia,ya raunata mutane da dama mazauna ƙauyan.

Motocin agajin gaggawa ne suka iso gurin,inda akai ta ƙoƙarin kashe wutar,sede kafatanin jamaar dake cikin jirgin ba wanda ya fita da rai ciki ko harda jannat,

Se wata matashiya wacce baa cikin jirgin take ba,hatsarin ne ya rutsa da ita,bata mutu ba,sede ta ƙone sosai,itako jannat tuni rai yayi halinsa😭

Tashin hankali ba’a sa maka rana.

WRITTEN BY:  ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO

NOVEL NAME:   SHA’AWAR SHI NAKE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         200KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:    18- SEPTEMBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Sha’awar Shi Nake Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Download>>> Yar Harka Complete Document

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button