Uncategorized

Radadi Complete Novel By Sa’adatu Waziri Gombe

 Lumshe ido tayi ruwan dake zuba a shawa tana sauka a jikinta sai a lokacin tasamu hawayen data rike suka fara zuba,tana jin radadi a cikin jiki da zuciyarta a nan tayi kuka mai isarta ta gaji Wanda hakan ya zame mata tamkar wata al’ada ko wacce safiya kafin ta fita aiki..bayan fitowarta ta leka daki ta hango su kwance suna bacci hankalin ta ya matukar tashi da ta tuna bata san me zata basu su ci ba..duk da haka tayi karfin Halin juyawa zuwa kicin ko zata samu wani abin da zata dafa musu…shiru tayi tana tunani, a lokacin taji motsinsa a bayanta zuciyarta ne ya tsinke amma sai ta daure…kizo ki kai min ruwan zafi, in ka ajiye wuta da gas din da zaa dafa maka ba sai kaje ka daura da kanka ba, ta fada cikin Kunar zuciya..mara kunya mara mutunci, ya fada cikin daga Murya kamar zai bigeta,in kika sake min rashin kunya sai na bibbigeki..nasaba ai ta fada cikin rashin damuwa dukan ka ba sabon abu bane wuri jikina ya…ya fin ciko ta da karfi ya hada ta da Bango sai da goshin ta ya fashe nan ta Mike batace komai ba ta wuce daki tasa kaya ta zari Jakarta ta fita..Aisha babar y’arta ta bita momi karki tafi ki barmu daddy yana dukan mu..kuma yasiyo abinci yaci yahanamu…ta mata murmushin karfin hali kiyi Hakuri Aisha yau zan dawo da wuri ta jata zuwa wani shagon kofar gidan su..ta karba musu bashin bread..fisge bread din yayi tare da jakarta ya zazzage duk abinda ke jakar ya kwashe mata kudin bus din da zata shiga zuwa office bata kulashi ba ta dauki jakarta ta fara takawa..har ta isa office din kuka take…hakika ta tsinci kanta cikin kunci bakin ciki da tsananin rayuwa…tayi saurin shiga office din oga ta gyara tare da arranging komai sannan tadawo office dinta tazauna ta kifa kai tunani….da bacin rai ya isheta…ga wahalar rayuwa ga yunwa ga physical and emotional abuse da kullum take kwana tana tashi ciki addu’a kawai take ko Allah zai kawo mata sassauci daga halin data tsinci kanta.

   Kamshin turarensa ya tabbatar mata da ya iso office din da sauri ta mike tare tare da fadin good mrng sir.. girgiza mata kai yayi ya wuce ba tare da ya kalleta ba kamar kullum yabada umarnin masinja ya kawo mata abinci..yayin da ya harde hannu a kirji yana kallonta murmushin daya gani a fuskarta ya saukar masa da wani irin farin ciki wannan murmushin yafi koma mahimmanci a rayuwarsa…yana kallonta tasa cikin jaka tana mai tsananin farin ciki zata kaima yaranta abinci..kullum ta fara kallon agogo..masinjan yayi mata sallama oga yace in kina da inda zakije ko tafi yau ba aiki…da gaske ta fada cikin jin dadi zan iya zuwa gida in dawo ya girgiza mata kai da sauri tazari jaga zata fita ya mika mata kudi ga kudin mota oga yace ki bi printing press ki karbo complementary cards din nan…tabbas Allah yakawo mata sauki ga abinci ga kudin mota da sauri ta karba ta fita tana tsananin murna..ya bita da kallo yanajin sonta na yawo a jikin sa yana bin jini da zuciyarsa yanajin Radadin sonta na konashi zai iyayin komai danganin ya sata farin ciki yakuma kawo mata sauki a rayuwa…ya rufe kansa a office yana kallon hoton ta a wayarsa wani irin jarababben so da bai taba jin irin sa a rayuwa ba shin yazaiyi da wannan so dake dawainiya dashi….

         Domin Sauke cikakken littafin sai ku danna inda aka saka Download.

WRITTEN BY:   SA’ADATU WAZIRI GOMBE

NOVEL NAME:   RADADI

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         26KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      15- JULY -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            ₦300 

Proceed To Download Radadi Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button