Uncategorized

Nana Atiku ɗiya ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa ta tafka abin kunya.

 Nana Atiku ɗiya ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa ta tafka abin kunya.

’Yan mintuna kadan da suka gabata, fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Zubby Michael, ya dora wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda aka ganshi da wasu kyawawan mata sanye da hijabi.  Daga cikin matan akwai Nana Atiku, diyar ga tsohon dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin Shugaban ƙasa a zamanin mulkin Chief Ulosegun Obasanjo, wato Atiku Abubakar.

A cikin faifan bidiyon, anga Zubby Michael wanda ya yi tattaki daga Lagos zuwa Abuja kwanan nan ya nuna jin dadinsa da kasancewar da kyawawan matan da suka ziyarce shi a dakinsa na otel.  Cikin zolaya ya kara da cewa watakila ba zai koma Legas ba saboda yadda matan suka yi kyau.

 Ita ma Nana Atiku cikin jin kunya ta ce “sannu” a cikin faifan bidiyon, yayin da Zubby Michael ke yi mata magana a matsayin “Babbar Yarinya Cikin wadanda suka ziyarceshi a dakin nasa.  Babu shakka, matan sun yi farin ciki da haduwa da fitaccen jarumin Nollywood din shima kuma yaji daɗin ziyarar.

Ga cikakken bidiyon daga ƙasa.  👇👇👇👇

Back to top button