Uncategorized

Matar Makaho Part 10 Complete Hausa Novel

MATAR MAKAHO

Chapter 10

Malamai  zan shiga,  ke koh yawo tsirara zanyi don naga bayan sumayya sai nayi

Amma dai kamila baki da imani habba don Allah kin wulakanta bawan Allah ya fita a Rayuwan ki sannan yanzun kice zaki wargaxa masa farin ciki ai wannan baso bane

Wace farin cikin bayan nice farin cikin sa har gobe ina da gurbi a zuciyar sa

Hhh hayya lallai kamila kina da gurbi a zuciyarsa ya hankad’aki akan matar sa koh an gaya miki so na dauwa mane a zuciya? duk mai sonka muddin baka kyautata masa toh fa kamar fure ka shuka baka ban ruwa tum tana bushewa aje aje wata rana zata mutu

Kee sadika na fahimci daman ke yar hassada ce shiyasa kwata kwata tafiyyar mu bata kyau dake

Nidai gaskiya nake fad’a miki kamila kuma gaskiya d’aya ce da wannan haukar ai gwara kije garesa da soyayya koh xai dawo ku daidai ta kinga sai ayi na biyu dake

Ina ma yake fita kullun yana gida,  naje inda akace min yana bude sana’a ma naje Amma shuru bantaba ganin sa ba, kuma ni nafi karfin kishi da sumayya sai dai ta fita tabar min shi

iii in kamila karkije kikai kanki a mahallaka wallahi wani rabon kashe ki zaiyi

Ya kashe ni mana indai akan Al’ameen ne kowa ma ya mutu

Wallahi badai kowa ba,  nidai mai sonki ce zan fad’a miki gaskiya koh kinki koh kinso rabuwa da bayin Allah nan shiyafi miki mutunci Akasinsa kuma bismillah zaki ga.

Bakin ki ya sari d’anyen kashi ba abinda zan gani  sai Alkhari

Ai baki neme Alkharin ba mutumin da keson kashe Auren wasu shine zaiga Alkhari?tace tana

Mikewa tayi ba tare da tajira Amsar kamila ba tayi mata sallama ta fita a asibitin

Sumayya na shiga cikin gidan kofar su ta wuce da mamaki take kallon kadija dake zaune tana rusa kuka”ke khadija lfy”?

Da gudu ta tashi zuwa wajen sumayya rungume ta tayi tana kuka’Aunty ina yaya? ina dawowa daga makaramta ake ce mini wai an tafi dake da yaya,.

“Babu inda akaje damu khadija yayan ki na waje shine  kika kama kuka koh uniform baki cire ba kika zauna haka”

Toh ni Aunty fisabililah yazanyi na cire uniform yayana da Aunty na na station

“Toh gani na dawo ki ibi ruwa kiyi wanka na baki kaya kisa dai dai yayan naki ya shigo”

Toh kawai tace tana d’aukar boket,  wanka tayi sumayya ta bata kayanta ta saka abincin da suka girka na karyawa daba su ciba shi ta ibawa khadija

Khadija na cikin cin abinci sai gashi ya shigo da sallama

Amsa wa khadija tayi hade da gaidashi, yaya  sannu da zuwa

Yauwa khadija ya makarantar

Lafiya yau subject 6 aka mana a rana d’aya Assignment biyu

Masha Allah ki gama ci sai muyi assignment in

Hhh yaya ka iyya ne?

Toh khadija ba nayi secondary ba koh azatan ki duk abinda na koya ya gudu ne?

Yi hakuri yayana

D’akin ya shiga sumayya kam daman tana kitchen

Bayan khadija taci abinci wanke uniform nata tayi ta shanya,school back nata ta d’auko ta bude Assingment ne aka busu na physics sai English,  yaya na gama inzo muyi Assingment in?

Bara na fitoh khadija, 

Toh yaya

Fitowa yayi suka zauna a dakali sumayya na kallon sa yana ma khadija bayanin assingment in  yanda zata fahimta sannan yana fad’a mata Amsa tana rubutawa

Bayan sun kammala gida khadija ta tafi tabar uniform nata a shanye, mikewa yayi ya ibi ruwan wanka ya shiga yana fita yayi Alwala ya wuce masjid

Bayan fitarsa  da ido sumayya ta bisa haka kawai yau taji tana jin shakkarsa sosai abinci ta juye a kula takai d’aki tayi sallah sanin baya dawowa sai bayan isha yasa tayin wanka d’akin ta shiga zani fille da T-shirt ta saka sai hulan bacci. TV ta kunna tana kallo gabaki d’aya yau ta rasa nutsuwar ta gabaki d’aya zuciyarta cike yake da tsoro

Bayan ya dawo sallah abinci ta gabatar masa baiyi magana ba kawai ya zauna ya fara ci 

Itakam taji ba dadi koh fad’ane ya mata akan wannnan shariyan ba karamin damunta yake ba 

Bayan sun kammala cin abincin wanke baki sukayi,  Al’ameen kwanciya yayi a gadon yayi shuru baice mata kome ba

Sumayya dake kwance a gefensa hawaye ne ya cika a idanunta itakam ta shigesu da mutumin nan

Sunfi, minutes 30 a haka baice kome ba itama batayi magana ba Amma kowa yasan d’an uwansa baiyi bacci ba

A hankali sumayya ta matso garesa kwanciya tayi a gabansa sosai ta shige jikinsa

Al’ameen yana jinta kala baice mata na shuru kawai yayi don so yake ya  mata horo ta ruwan sanyi yanda gobe baza tayi

Abinda bayaso ba.

Hannu tasa a hankali ta na cire botur in shirt insa nan ma baiyi magana ba 

“Ni da wannan fushin ai gwara duka da wannan shariyan”

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


Kala baice mata ba sai kama hannunta dayayi wanda ke yawo a jikinsa 

“Dan Allah ka kulani”

Kinsan Allah sumayya in baki rabu dani ba sai na sauka a gadon na koma kan kujera habba Ana dole ne?

“Kayi hakuri bazan kara bafa”

Sauka yayi niyar yi da sauri ta riko sa hade dasa ihu”wallahi nidai ban yarda ba kayi hakuri toh na tuba”

Fasa saukar yayi ya koma ya kwanta itama kwanciyar tayi a gabansa sosai ta mannu a jikinsa

Haka suka kwana tsakanin su babu shiri sumayya dai na makale da muhammad duk yanda yaso cireta a jikinsa taki

Washe gari haka suka tashi salam  Al’ameen yasha mata mur sosai duk yanda tad’au abin da sauki abu fa ya wuce nan don da gaske muhammad yake

Bayan sun karya ta d’aga ido tana kallon sa”yayan khadija”

Na’am

“Daman maganar make-up inda zan ma yar kanwar Deputy ne saboda tsaro bazasu iyya zuwa ba shine wai naje na musu a gida har kwana biyar ana biki”

Saikin dawo kawai yace yana fita a d’akin

Sosai shariyan Al’ameen ya damu sumayya, haka dai ta lallaba ta shirya tad’au hijab  nata ta saka rufe kofar tayi ta fita.

Bakin titi ta tsaya idonta ya sauka a kan Al’ameen ne zaune a bakin masallaci kusa da masu bara suna hira dasu, kara sowa tayi inda suke bakin ta d’auke da sallama, “Assalamu Alaikum”

Mutanen bakin masallacin gabaki d’aya suka zubawa sumayya ido suna mamakin ina zata, wa’alaikumu salam su Al’ameen suka had’a baki wajen Amsawa shikam cike da mamaki meya kawo sumayya gunsa bayam tace gidan deputy zata, tashi yayi ya matsa gefe

Binsa sumayya tayi  inda ya tsayan ba mutane, itama tsayawar tayi batace kome ba

Lafiya?

“Lafiyar kenan koh laifine in nazo wajen ka”?

Babu laifi…

“so nake ka rakani”

Rakaki ina?da mamaki a fuskar sa 

“Gidan da zanin mana”

Hala baki  gani ne?

“Ah ah ina gani so nake ka rakani”

Bazani ba, yace yana tafiya

Ai da sauri sumayya ta riko rigansa 

Keee menene haka? koh baki ganin a gaban mutane muke ne

“Toh sai me in a gaban mutane muke koh ba mijina na rike ba kuma wallahi in baka shige mun tafi ba saina rungume ka a gabansu”

Uhmm Allah ya kyauta shige mu tafi

Mutumin da ke saida ruwa kusa dasu Al’ameen ne ya dubi abokin sa, Kai Amma yariyar nan bata da kunya har masallaci zatabi miji bata maji kunyar idon mu ba muna zaune? wama yasan dalilin da yasa aka aura masa yarinya kamar  wannan?

Gaskiya ne haruna daga gani idon yarinyar a tsatsaye yake..

Haka sumayya tasa muhammand a gaba har gidan kanwar deputy har falon baki aka kai Al’ameen aka had’asa da abin motsa baki sumayya kuma ta shiga falon matan gidan

Har yamma suna gidan sallah kawai ke d’aga Al’ameen yaje yayi ya dawo  

Sai kusan 5:43 na yamma suka fitoh gida  gaskiya sumayya ta yaba da karamcin y’an gidan don Take Away na abubuwan da aka shirya  na biki aka iba mata” yanzun ina zamu”?

Sama jannati zamu, Al’ameen ya bata Amsa

“Ni kake fad’awa bakar magana”?

Eh an fad’a in ai nafi mai Ashar kuma bakar ma agunki na koya

“Badai aguna ba kuma in kayi tsiya saina gudu na barka ka bata”

Kanki kika ma Asara bani ba.

“Akan me xan ma kaina asara kuma”?

Aikan mijin da kike dambe mana

“Dambe ni banyi dambe akanka ba”

Au habba daman tabaryar ta burgane?

“Ai na razana tane, karka wani zata fad’a nake akanka”

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 2 HAUSA NOVEL”


Na nawa kuma.

“Allah ba wani”

Ke kika sabi dai mutum sai taurin kai

“Kamar kai”

Shuru ya mata don ya fahimci sumayya inya biye mata fuskar da ya d’aure bazai san lokacin da zai sake ba.

Keke suka hau suna isa gida ana kiran mangari ba masalaci ya shiga ita kuma ta wuce cikin gida

Bayan ya dawo sallah take Away in ta bude musu donut da kaza rabi sai drinks d’ayan take away in kuma fried rice ne da lafiyayyen naman shanu suna kammala ci, muhammad kam kwanciyan sa yayi

Sumayya TV ta kunna ta koma ta kwanta tana kallo a kwance”yayan khadija”ta kirasa tana kallonsa ganin ya natsu waje d’aya yana tunani, jin bai Amsa ba yasa ta dafa kafad’an sa

Da sauri yace Am Ammar kudin nan basuyi yawa ba, sai kuma da sauri ya fara kame kame don sam subutar baki ne abinda ke zuci shiya fitoh fili

“Wani kudi kuma Waye Ammar”?

Am ba kome.

Akan me zakace ba kome duk kabi kasa kanka a damuwa in ma bashi ake binka bazaka fad’amin na biya ba duk kudin da nake tarawa Wallahi tatali nake maka naga kudin yayi yawa sosai kafun na baka ka kama sana’a mai d’an kauri mu samu murufawa kan mu asiri, amma ina dalili ina dana rufin asiri kabar kanka a rikici”

Ba haka bane sumayya ba’a rikici zansa kaina ba wannan magana ne daban.

“Wace magana kenan?koh bankai naji damuwar kaba”?

Daman Ammar ne ya mini magana jiya zai bani jari dubu d’ari uku na kama shago kafun azumi tunda saura sati biyu ne ga kayan marmari a azumi akwai kasuwa.

“Bazai yuba wani ma Ammar inne d’aya? akan me zaice zai baka kudi tun da baisan zai Taimake kaba sai yanzun”

Sumayya bamu fa dade dashi ba kuma insha Allah ba abinda zai faru

“Gaskiya ban Amince ba ka bari inna gama had’a kudin saina baka kabar masa nasa”

Gaskiya sumayya gwara na karbi nasan kawai na gwada kasuwar tunda ba kyauta yace ba koh bashi saina tambaye sa in kyauta ne ni karan kaina bazan Amince ba Amma in bashine saina karba ke kuma saiki tara kudin ki wata rana zai mini Amfani.

“Yanzun ka zabi karban nasa akan nawa kenan”?

Ni bance ba Amma dai gwara nasan akan bashin tsakanin mata da mijin nan bana sha’awarsa sai in ya  zama dole

“toh ce maka akai bashi nace ne”?

Koma dai yayane kiyi hakuri bazan iyya karba ba

Sumayya juyawa kawai tayi ta kwanta bata kara magana ba  a hankali yasa hannu ya d’agota  kwantar da ita yayi a jikinsa cikin sanyi yake mata magana, don Allah badon niba sumayya ki daina Ashar koh don yaranda zamu haife su tashi da kalami mai kyau a baki banji dadin abinda ya faru ba koh kad’an yau ace anzo an d’auki matata a motar yan sanda wannan ba mutuncin matar aure bane sai in ya zamo mata dole

” insha Allah bazan sake ba”ta karasa maganar da kara kwanciya a jikinsa

Allah yasa…

“Ameen” shuru sukayi dukansu biyu ba wanda ya kara magana a hankali Al’ameen yasa hannu ya yaye hijab da sumayya tasa don yau sanyi ake sosai

“Sanyi fa nake ji”

Nima ai sanyin nakeji kinga nasa abune?

“Ai kai daban ni daban”

Nida ban,  inji wa?

“Sumayya”

Uhmm muyi bacci

“Banaji”

Saboda?

“Sanyi “

Uhmm toh bara na rufeki sai kibar jin sanyin, yana maganar yana hawa kanta

Saboda sabo da hakam yasa bai dame sumayya ba baccin ta kawai ta kamayi bata san ma yaushe yayi nasa ba 

Washe gari Ammar yazo Akan maganar su Al’ameen ya Amince, Tare da tambayar Ammar kyautane koh bashi kai tsaye Ammar yace bashine don ya fahimci muhammand kalansa daban ne mutum ne wanda baison banza damuwar sa kawai ya nemi na kansa

Cikin sati d’aya Ammar ya sama ma muhammad shago mai kyau ta tsallaken first bank kaya ya cika masa makil a shago kama daga mazar kwaila dabino kayan marmari ba wanda babu su dangin Apply duk ba’a barsu a baya ba,yaune Aka kammala had’a shagon kai masha Allah shago kam saidai makiya suji haushi

Muhammad Anya zaka iyya kasuwancin nan babu yaro a kusa dakai kaga yanzun shagon nan babba ne idanun barayi zai sauka akai bare an ganka baka da ido za’a iyya baka d’ari ace dubune, Amma in kana da yaron daka Aminta dashi mai hankali a Unguwan naku sai yazo ku zauna tare kana d’an basa nasa ladan sai inga kamar zaifi?

Gaskiya ne Ammar daman Akwai wani yaro shagari d’an wani makwancin mune daya rasu toh yaron ba boko ba Arabic tunda iyayen sa suka mutu dai abin sai a hankali ba kula dashi ake ba saina d’auko sa yazo mu zauna tare

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 3 HAUSA NOVEL”


Amma muhammad yaro irin wannan da ba boko ba arabic bazai cutar dakai ba kasan fa halin yaran yanzun?

Ba kome insha Allah bokon ma iyya secondary ya tsaya arabic in tunda iyayen sa suka rasu ya daina zuwa saboda rashin mafad’i Amma najashi a jiki kaga inda rabo sai kaga Allah ya dad’a nitsar dashi

Haka ne kam sai kaje wajen bappan nasa kuyi magana saika d’auki yaron

Insha Allah Ammar nagode Allah ya tsaka maka da Alkhari ya bani ikon biyan abinda ka bani

Ameen,  ni bara na wuce Allah ya kawo kasuwa 

Ameen, Al’ameen yace yana rufe shagon gida ya nnfa fuskar nan a washe

Bayan ya shigo gidan da sallama lokacin sumayya nama wasu lalle

Amsa masa tayi tana kallon sa ganin sai murmushi yake”yayan khadija lfy”?

Lafiya kun gama lallen ne ?

“Saura hannu d’aya meya faru”?

Babu kome ki gama dai sai muje ki gani

Toh sumayya tace da sauri sauri ta kammala musu don ta kagu taji menene” na gama muje”

Kiye wanka dai kisa kaya da hijab amma daga gama lalle sai fita

“Nidai gaskiya Ah Ah muje inna dawo zanyi”

Hannunta kawai ya kama har ban d’aki ya fitoh ruwa ya iba ya kai mata, kiyi wanka malama

Ba yanda sumayya ta iyya haka tayi wanka ta shirya ya saka ta agaba har shagon sa sosai sumayya tayi mamakin girman shagon da abubuwan da aka zuba masa gwanin sha’awa kai gaskiya “masha Allah waje yayi waje”

Gaskiya ne nima ina ji wajen ba karamin kyau zaiyi ba 

“Ya mayi Amma dai ya kamata kane mi abokin zama saboda tsaro”

Eh munyi magana da Ammar,  gidan su shagari zani koh xa’a amince ya tayani zaman shago

“Gaskiya ne hakan yayi kyau sosai wallahi Allah ya kawo kasuwa”

Ameen, muje ki rakani gidan su shagari

“Toh”sumayya tace tare suka tafi gidan su shagari kuma Alhamdulilah  sun Amince

Cikin sati d’aya ba karamin mamaki yan sintali sukayi ba ganin muhammad da babban shago gashi bai fad’awa kowa kome ba inka tambaye sama sai yace Allah ne ya rufa masa Asiri yayi shuru , sosai yake cefene yanzun kome na gidan sa ya d’aukewa sumayya duk yanda taso hanata yake gashi Allah yasawa abin Albarka Arana d’aya yana cinikin dubu goma gashi Shagari ya kaisa wajen wani mai kayan marmari ya had’asu da dilan yan gembu yanzun masa ordern kaya ake daga gona sai dai kawai ya tura shagari tasha in kaya ya sauka a d’auko masa.

yanzun kam Alhamdulilah sumayya kudi na shigo mata wallahi kowa ya ganta zai zaci daki Ac falo Ac mota AC  office Ac ne tsabar yanda ta dawo tayi kyau tayi fresh sosai har wani yellow yellow tayi yanzun koh tunanin gidan su batayi ita karan kanta tana mamakin yanda take mantawa akwai abie A duniya, wata rana har mamakin kanta take saitaji kamar ta kirasa sai kuma ta fasa

hatta shi muhammad yanzun in ka gansa zaka san kwanciyar hankali ya samu matsunguni.

 ga suturu masu kyau yanzun shima da kudin sa yake sayan kaya ya saka duk ya watsar da tarkacen kayansa hatta khadija yanzun daban ta koma kamar ba khadija ba gata ba yaya ba,  ba Aunty ba

Yaune aka ga watan Ramadan gobe  za’a tashi da azumi sumayya yau da khadija kasuwa suka shiga sosai sumayya ta musu sayayyan azumi kome buhu buhu katon katon ga kaji ka kifi, vegetables daman bata da matsalan fruit

bayan sun dawo kasuwa kowa ka gani fuskar sa a washe Adalilin gobe azumi 

Bayan isha muhammad ne da sumayya suke cin abinci a waje,  zazaune suke akan taburma don yanzun sumayya ta saya 

Assalamu Alaikum

“Wa’alaikumu salam”muhammad da sumayya suka Amsa ” sannun ki da zuwa sumayya tace tana tashi,  ta d’aukowa bakuwar kujera don a tunanin ta koh customer ne

Ah ah ba zama nazo ba magana zanyi dake

Ni kuma?sumayya ta maimaita

Eh ke dai,  ina dai kice sumayya Abdulsalam shugaba?

Eh nice

Nazone na shaida miki koh na gargade ki Akan 

Akan ibada don naga d’an changen rayuwa da kuka samu haryasa kuna sanyi da ibadan koh, toh bari kuji irin wannan daman makiyan ku suke jira sumu ku mai gabaki d’aya in kukayi sake da ibadah toh tabbas zasuga bayan ku sarkin yawa yafi sarkin karfi, watan da muka shiga   wata ne mai Albarka ni’ima da falala ku dukufa wajen neman tsari da kariya a wajen mahaliccin mu.

Sake baki sumayya tayi tana kallon matar da bata santa bama gashi dare ne ba nepa bare ta mata kallon sap”malama wani irin magana ne haka sannan suwaye makiyan mu”?

Baki bukatar ji nidai na fad’a miki tace tana fita a kofar

Sumayya kam kamar doluwa haka ta kuma sai bin hanyar da matar ta fita kawai take tana Al’ajabi”yayan khadija kaji wani magana kuwa”?

Uhmm sumayya  maganar matan nan koh bamu gaskata ba, Amma tunda ibadah tace toh mu dage koh ba makiyi Addu’a makamin mumini ne 

“Gaskiya ne” sumayya tace duk jikinta yayi sanyi sosai abincin ma kasa cigaba daci tayi

Al’ameen dake cin abinci tsayawa yayi jin sumayya shuru hannu yasa ya tabata sumayya yadai?

“Uhmm babu kome kawai dai ina mamaki ne”

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 4 HAUSA NOVEL”


 me kuma? inna matan nan ne ai ba abin mamaki bane don duniya da fad’i kika san menene Alakarta da su kedai mu rike ibadah hannu bibiyu insha Allah ba Abinda zamu gani sai Alkhari kici Abinci pls?

Toh tace tana cigaba dacin abincin”yayan khadija me zan dafa mana na sahur”?

Me kike so?

“Uhmm  aikai na tambaya koh”?

Nima saina tambaye ki

“Toh ai mata ke tambayar miji abinda za’a dafa”

Au yanzun kam an yarda ni mijine kenan?

“Oho dai nikam ka fad’a mini abinda zan dafa so nake mu kwanta da wuri samun mu tashi da wuri”

Ki mana tuwon shinkafa miyan shuwaka 

“Nama koh kifi”?

Duk wanda ya dace ki saka

“Ok” kawai tace tana tashi kitchen ta shiga ta barshi zaune akan taburma

Girki sumayya tayi sai kusan 10:30 ta kammala aikin girki juyewa tayi a kula takai d’aki tayi tatan kamu da khadija ta karbo mata a inji tana gamawa tattara taburman tayi, ta rufe kofar su zuwa lokacin Al’ameen yayi bacci tuntuni itama kwanciyar tayi bata tashesa ba don bacci takeji itama

Misalin karfe 1:30am Al’ameen ya farka jin sumayya ajikinsa yasa sa tata bata, sumayya!! sumayya!!

“Menene”?

Ki tashi mana

“asuba yayi ne”?

Baiyi ba sallah zamuyi tashi maza kinji

“Uhum”tace tana mikewa sauka tayi akan gadon ta kamo hannunsa suka fitoh waje bayan ta kunna hasken wayan ta Alwala sukayi suka tada sallah

Sai karfe uku suka sallame sosai suka dukufa suna Addu’an neman tsari wajen mahallincin mu da neman gafaran sa

3:41 sumayya ta d’auko musu tuwon ta bude da zafin sa kamar yanzun akayi zuba musu tayi sukayi sahur  basu koma bacci ba sai data cika ruwan randa a laida fari ta d’add’aure ta cika firij nata bayan asuba suka koma bacci

Dayake Cikin Ramadan ba’acika sayan kaya da safe ba sai yamma yasa Al’ameen yabiye wa sumayya suka cigaba da bacci basu suka tashi ba sai kusan 9 Al’ameen ya tafi masallaci tafsiri sumayya ma  islamiyar unguwan taje  wata babbar malama ke tafsir wa matan aure a ciki 

  sai bayan Azahar Al’ameen ya fita shago,  sumayya kam sallah tayi ta shiga kitchen abinci ta dafa dankali ne da kwai ta soya sai ruwan tie ta musu macaroni da miya duk ta zuzzuba  a kula ta zuba wasu goggo ma a manyan kula guda biyu,  kiran yaro tayi ya kira mata khadija bayan ta dama kunu cikin bokatin penti fari babba, wanka ta shiga kafun ta fitoh saiga khadija ta shigo bayan sun gaisa ta bata boket in da cups na roba wanda ta saya jiya ta had’a mata takai masallaci sadaka sai ruwan da tasa da asuba a firij  sunyi guda shima boket ta cika ta d’aurawa Almajiri yabi khadija 

Rarra bawa khadija tayi a masallaci sosai jama’a ke sawa abin Albarka don koh masu kudin unguwan basa kawo kome a azumi sai talakawa ke kokarin ciyar da masu azumi (Allah ya kyauta)

Bayan khadija ta dawo da bokata yen, kulan abinci sumayya ta bata ta kaima goggo suyi bud’a baki

Al’ameen ne ya had’a kankana da dabino sai sweet milo, yasa a laida biyu ya rike a hannunsa barin shagari yayi a shago hade da basa kudi yasai abin bud’a baki shima 

Gidan goggo ya wuce ya bata laida d’aya ya kamo hanyar gida

Tun akan hanya ake ta masa godiyan kunu da kankara sosai yayi mamaki wani kunu kuma amma baiyi magana ba amsa musu yayi ya shiga gida daidai lokacin aka kira sallan mangari ba

Assalamu Alaikum

“Wa’alaikumu salam”

Jin bakin sumayya cike da abinci ta amsa sallamar yasa sa da mamaki yace toh yau koh jira babu hajiya har an kai loma?

“Ai a azumin nan ba jira kaji in gaya maka ana kiran sallah sai ci yaushe zan jiraka kuma”

Uhmm yayi kyau yace yana zama akan dakalin da take, mika mata laidan yayi ganin yau koh karba batayi ba sai jin karan shukali kawai yake

Amsa tayi ta bude dabino ne guda biyar ta damka masa a hannu sai ruwan shayi a kofi

Karba yayi ya bude baki da addu’a bayan yaci dabinon ruwa ya kurba kawai yayi Alwala ya tafi masallaci 

Sumayya kam sai da ciki ya d’auka kafun ta zakud’a itama sallar tayi bayan ya dawo masallaci shima yaci nasa Abincin sauran kayan marmari da ya rage ta saka a firij 

Da misalin karfe 11 bayan ta gama aikace aikacen girkin asuba yake tambayar ta akan kankara da kunu

“Yanzun don zanyi aikin lada saina fad’a maka yayan khadija watan azumi ne fa” 

Allah ya karbi ibadun mu

“Ameen, FATAN MU(next novel)kenan insha Allah”

Ta bangaren kamila Alhamdulilah jiki yayi sauki sosai harma an sallame ta sai dai fa fatar hannu kam ba kamar nada ba 

Yau dai gidan kawarta ta nufa

Assalamu Alaikum

Wa’alaikumu salam wanake gani anan koh dai idanuna ne kemin gezo lallai kamila duniya ashe ana iyya tunawa damu 

Ke matsalar ki kenan Harira daga mutum yazo gunki koh wajen zama baki bani ba kin kama mini korafi

Ai dole na miki kamila tun auren ki na sake saki a idanu na? koh wayarki na daina samu sai dai inji a gari kinzo kin koma yar buru uba har zaki ce ban baki mazauni ba

Yanzun dai kiyi hakuri ki zauna wata magana ce ta kawo ni

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 5 HAUSA NOVEL”


Aikam sai ta kawo ki badai kika kawo kanki ba 

Kee habba don Allah jarabar ta isa haka 

Naji meke tafe dake kamila

Yauwa zancen dai na muhammad ne

Wani muhammad in?

Ki jiki da wani banzan tambaya muhammad nawa nake dashine wai

Nidai nasan tsohon mijinki dai ba muhammad bane 

MAKAHO…

Kwal uba yanzun kuma tsohon zuma aka koma

Ai daman tafi magani, ke Harira kinsan meya kashe min aure?

Ah ah 

Toh rashin biyamin bukata ne bayayi, don bana gamsuwa shiyasa na kashe aure na don ni yanzun duniya kaf  in dai zan samu namiji gwarzo ba ruwa na da talauci koh kyau kin gannin nan don nabisu banga da kyau ba

Amma ke dai kamila akwai shirme kece miki akai shi Al’ameen in jarabebbe ne kamar ki?

Hhh habba Harira ido fa ba mudu bane amma yasan kema 

Hhhh shegiya ta faso gari, ta karasa maganar da bawa kamila hannu suka tafa, toh yanzun me kike so ayi ne 

Yauwa MAKAHO fa aure yayi kuma wata yar iska ya aura family shugaba

😳shugaba fa kikace?

Eh nima nayi mamaki auren nan yar iska in kika ganta sai gaban ki ya fad’i tsabar kyau

Kema dai kamila aikin san zuriyan gidan daman kyawawane sai dai na wani yafi na wani

Gaskiya ne in gaya miki wai dana gama bibiyar muhammad na tataro kome nasa na samu cikeken bayani akansu shinefa naje da sunan koyan kwalliya wajen ta yar iska kinga duka da suka mini karshe ma acid inda zani makaranta dashi zamu shiga lab zuciya ya ebeni na d’auko zan watsa ma yar banza kawai in gaya miki abin mamaki muhammad ya zabi matar sa akaina da kansa ya hankad’a ni har acid ya zube a hannuna, ta karasa maganar da nunawa Harira hannun

Cap  wani mataki Dad ya d’auka akansa?

Ai ban fad’a masa gaskiya ba cewa nayi ita ta zuba mini

Aiko kinyi wauta 

Ai ma abin ba inda yaje don  bata kamu ba

Kema ai kinsan bazata kamun ba, yanzun dai me kike so ayi

Yauwa Harira wajen malaman nan naki nake so ki kaini akan maganar nan

Hhhh yar iska ba kullum fad’a kike mini akan malamai ba angaya miki ana zama hakane ai kikace zaki zauna haka toh bone ya sameki

Gaskiya kam don akansa babu abinda bazan aikata ba ke so nake inga koh kaunar ganin sumayya baya so yaji kaf duniya ba wanda yaki jini irin ta,  ba wanda yake so irina

Shegiya ba kome tashima kiga bara na d’auko mayafi muyi gaba kinsan har kauyen mutum biyu ne in bamu tafi yanzun ba sai kuma gobe saboda hanya ba kyau ga dare

Amma harira haka zaki tafi naga mai gidan baya nan gashi yara daga su sai yar aiki

Kee waya gaya miki sai na jira sa ai wallahi sai abinda nace 

Uhmm kai nima fa za’ayi tafiyar nan naku dani

Amma dai kin taho da kudi kam koh ?

Karkiji kome akwai kudi akwai mota sai ki tukamu tunda ke kika san hanya

Ok muje

  haka kamila da Harira suka d’auki hanyar mutum biyu wajen boka a watan azumi koh tsoron Allah babu

Sai la’asar suka isa cikin mutum biyu dole tasa suka faka motar su a bakin titi suka hau machine mai kafa biyu zuwa ciki cikin kauyen bayan sun iso ma sai da suka tsallake ruwa

Wani dutse ne baki kiren hayaki na fita akai tunda suka nufo wajen wani irin wari ne yake bugan hancin su da sauri kamila ta tushe hancin ta 

Cikin gaggawa Harira ta buge hannun,  kamila ke kamila ki rufa mana asiri kar muje ciki a haka kin tushe hanci wani irin iskanci ne wannan?

Amma Harira baki jin wari da doyi na tashi ne?

Ina ji amma rufe hancin ki daidai yake da rasa aikin ki 

Kamar ya?

Kamar haka tace tana kama hannun ta su koma baya

Ke Harira menene haka?

Bakin ce baki gane ba shine zan ganar dake

Yi hakuri muje

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 6 HAUSA NOVEL”


Haka suka nufi cikin kokon kamila kamar zata  mutu tsabar wari ai bata gama ganin tashin hankali ba sai data shiga kokon taga tashin hankali mutum ne a zaune kamar an sassaka sa jikinsa duk kuraje sunyi ruwa sun cika sai doyi yake dagashe sai fata kawai ya d’aura a Gabansa ga gashin kansa sa tsitsige kamar shaid’an gashi jikin kokon kadangaru ne sunfi dubu a mamman ne koh ta ina bazama kaga jikin kokon ba tsabar yawansu gasu a shure waje d’aya

Kai ku dakata ku dakata nace,  yafad’a da muryarsa mai amoi gata  muryar yar irin jarirai cikin tsawa yayi maganar 

Sosai kamila ta razana da gudu tayi hanyar fita 

Karki kuskura ki fita a nan ba tare da an gama da bukatun ki ba Tabbas zaki sami Muhammad MAKAHO…….

Aijin ya ambace zata samu muhammad yasa ta dawo da sauri jiki na rawa ta tsunguna kamar yanda Harira tayi 

Kallon ta bokan yayi sannan ya rufe idonsa yana wani irin magan ganun tsibbo na d’an wani lokaci kafun ya bude idanunsa kallon cikin kwaryar yayi nad’an wani lokaci kafun ya d’aga ido yana kallon kamila

Tabbas zaki samu muhammad amma fa rabasu da sumayya babban Had’ari ne saboda kaddarar su a manne take dana juna akwai makiya sama dake idanunsu kullum na kansu sannan asirin dake yawo akansu yafi wanda kike so a saka musu Amma akwai mafita d’aya

Jiki na rawa kamila tace kamar ya kenan Allah gafarta malam

Wani irin  tsawa ya daka mata,  keee ba’a kira mana Allah Anan kinsan akwai sane kika zo neman biyan bukata wajen mu(Wa iyyazubillah)

Tuba take na kan dutse sabuwa ce Amata afuwa

Ammata Harira amma ta kiyaye nan bama son shirme

Zan…z..nkiyaye..takara sa maganar cikin tsoro harga Allah mutumin razana ta yake

Yanzun ana tsaka da ibadan watan Azumi kuma sun tsaya dakyau wajen ibadah basu bada wani kofa da Za’a kawo musu farmaki ba sai dai akwai dama,  nan da sati biyu zata Fara jini mundin tayi sake da ibadah zamu farmata 

Kamar ya malam?kamila ta tambaye sa

Ranan juma’a 17 ga azumi da misalin karfe 1 na rana zata fara jini a lokacin zuwa kwana biyar kina da daman da maganin zai cita mundin tayi sakaci da ibadan da suke yanzun

Ok toh malam ni yanzun wani mataki koh ince wani aiki d’aya za’a mini

Akaf asirin da za’a musu don ganin yakita,  bazaici ba don an musu bakin asiri na zama tare da juna abu d’aya zan miki shine Ama sumayya kurciya tabar kasan gabaki d’aya ta manta da NIGERIA a rayuwar ta kwata kwata da rayuwar da tayi a ciki, 

Wannan damar xaki samu na auren muhammad, duk da hakan zai batawa wasu shirin su da suka dade sunayi

Na Amince wallahi na yarda ayi mata koma menene

Shikenan zaki kawo bakar tinkiya da jan tatabara sai rakuma biyar masu ciki

Malam ina zan samu wa’innan abubuwan sai dai in b

Da hali na bada kudin sai a nema asaya

Ba damuwa ki kawo

Nawa ne?

Bama yanke kudi biya kawai ake 

Kudi kamila ta basa kusan 500k 

Kije ki dawo gobe in mun had’a aiki sai kizo ki karba

Toh mungode 

Fita sukayi da Harira sosai taji dadin jin za’a mata maganin yar iska 

**************

Sosai sumayya da Al’ameen suka dage da ibada sallan dare ga sadaka duk yamma sai sumayya tayi kunu da kankara shi kuma muhammad yayi sadakar lemo ma Almajirai koh dabino

Khadija kam haryau basu kara haduwa da Ammar ba bata kuma san shiya bude ma yayanta shago ba taci gana da zuwa makaranta har azumi yakai 17  sumayya batayi sakaci da ibada ba kwanciya da Alwala in Muhammad ya tashi da dadare yana tada ta itama ta zauna tana lazimi sosai suke ibada Awatan koh bacci yanzun basu da lokacin sa sai bayan asuba

Ta bagaren kamila sun koma wajen boka washe gari a idanunsu ya kamo wata katuwar mujiya ya fade mata ciki layoyin da ya rubuta sunan sumayya ya saka ma mujiyar a cikin da Allura da zare yasaka ya dinke cikinta ya baiwa kamila tayi ta kula da ita a keji ta mata jinya nan da kwana 16 ranan da sumayya zata fara Al’ada kenan kuma ana son karta sake azumi daga ranan sai randa sumayya ta fara Jini saita saketa da tsakar dare tana mai Ambaton sunan sumayyar kafun gobe da safe zataji kyakkyawar lbr 

Duk da kamila na tsoron mujiya Amma dayake shaid’an ya buga mata ganga haka ta cici  a kwando tayi jalingo

Yau aka kai azumi 20 a daren ranan sumayya ta samu tsarki bayan isha’i tayi wanka

Al’ameen kam bayan ya dawo daga Ashan kwanciyan sa yayi don yau Tahajjud zasu shiyasa yake son kwantawa da wuri

Sumayya kam abincin asuba tayi sai kusan 9:39  ta kwanta 

Da misalin karfe 12:10 Al’ameen ya farka  Tada sumayya yayi sukayi Alwala kaya suka chanja daga na bacci zuwa  jallabiya ita kuma tasa dogon riga sai hijab sallaya ya d’auka suka rufe kofar suka fita

Gidan goggo suka wuce don khadija tayi ta rokon su zata bisu itama bayan sun isa sumayya ce ta shiga gidan da sallama jin shuru yasa ta buga kofar d’akin khadija 

tashe tayi Itama Alwalan tayi suka fita a gidan

Haka su uku suka kama hanya koh ina ka wuce group group ne na Al’umma musulmai suna tafiya manyan masallatai kamar rana ne ba dare ba

Sumayya da khadija da Al’ameen da kafa suka taka har macilin babban masallacin juma’a na Dr Ibrahim jalo jalingo 

Sai 3 aka tashi Ana fifita a masallacin,  ture ture tsabar yawan jama’a cunkoson ne yaraba sumayya da khadija 

Bayan khadija ta fitoh daker  tsaya tayi tana dube duben sumayya Amma bata ganta ba A haka ta fitoh bakin SINTALI GIOBAL ta tsaya saiga yayan ta don daman sunyi agun zasu hadu in An tashi 

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 7 HAUSA NOVEL”


Bayan isarsa da mamaki jin muryar khadija kad’ai banda sumayya ya tambaye ta,  ke khadija ina Aunty taki?

Wallahi yaya banganta ba tunda muka.

Tunda muka fitoh Banganta ba.

Wani irin baki gantaba kuma hauka kike ne khadija koh me?

Wallahi yaya da gaske nake banga Aunty ba.

Nashiga uku ni muhammad, yace yana kamo hannun khadija suka tsallaka titi zuwa cikin masallaci sosai suka dudu ba Amma basu ga koh mai kamada sumayya ba sosai abin ya gigitashi, ke khadija a daidai ina kuka rabune wai?

A kofar fitane fa yaya cunkoso yasa muka rabu.

Jingina kawai yayi da jikin ginin masallacin shikam dai ya shiga ukun sa ina sumayyar ta shiga ne wai?

Yaya koh dai aunty gida ta koma ne?

Wani irin gida kuma khadija bayan saida nace ku jirani a global xaki wanice ta koma gida nadai san sumayya bazata koma gida ba

 

Daga khadija har muhammad hankalin su ya tashi har hankalin yan agaji ya dawo kansu d’aya daga cikin su ya tambaye sa

 malam lafiya naga kana ta zaga masallaci kaje ka dawo,  tun dazun yanzun fa ana neman 4:00 bazaka tafi gida ba ga kanwarka   ma naga kuna ta yawo tun d’azun lfy kam?

Ina fa lfy wallahi ranka ya dade da matata mukazo masallaci amma ban ganta ba gabaki d’aya na gama iyya dubata amma bangan taba

Wace irin magana ce wannan ita matar taka yar yayece koh jaririya da za’a nema a rasa koh hanyar gidane bata sani ba?

Ranka shi dad’e ni nasan bazata koma gida ba tunda nace ta jirani toh tabbas zata jiranin

Kaga malam karkazo ka d’aga mana hankali a wani unguwa kuke ne?

Sintali ne..

Sintali😳A koh B?

Sintali A ne ranka ya dade

Amma dai kai d’an rainin wayo ne ina sintali A ina macilin da bazata iyya komawa da kanta ba kazo kana kokarin daga mana hankali?

Kayi hakuri ranka ya dade 

Na hakura amma ka fita kakama kanwarka kubar masallaci nan ya zakazo da maganar da hankali bazai d’auka ba matar ka ta bata,  ina macilin ina sintali?da bazata koma ba

Kayi hakuri..

Kama gabanka malam?

Haka Al’ameen ya fita kaman k’wai ya fashe masa a ciki 

Da sauri khadija tazo ta kama masa hannu haka suka fito a masallacin gwanin tausayi     

Tsallake titi sukayi suna tafiya Gabaki d’ayansu inka gansu kaga wa’inda basu da nutsuwa gabaki d’aya zuciyar Al’ameen bugawa take kamar ance masa sumayya  zata barsa   

Sunzo daidai titin doruwa kamar daga sama khadija ta hango mace da hijabi tana tsallako titi Allah yasa akwai wutan sola shiya bata daman ganin wance ta tsallakon da karfi ta kwala ma sumayya kira Aunty!!!

Ai da wani irin mugun sauri Al’amesn ke magana, kee kin ganta ne ina sumayyar take tana ina?

Kafun khadija ta basa amsa da  gudu sumayya ta karaso karesu”lafiya har yanzun baku koma gida ba”?

Kee sumayya kina da hankali kuwa banace miki kafun mu shiga masallaci,  kujirani a gidan man sintali ba koh ba haka nace ba,  shine zakisa kafa ki koma gida don tsabar kin raina min wayo gani d’an iska koh?

“Don girman Allah kayi hakuri, wallahi sace mini takalmi akayi shine na tsaya nema na jira mutane suka fifita duk ban gane ba dana fitoh wajen global, nan ma ban ganku ba shine nayi tunanin kun koma gida saina koma nima danaje kuma naga baku dawo ba, shine nabiyo ku”

Don Allah yaya kayi hakuri tsabani aka samu!

Na hakura khadija Amma sumayya karki sake mini haka Am warning you?

“Insha Allah” tace tana kama hannunsa dake cikin na khadija don baizo da sanda ba suka tsallaka titi

Bayan sun isa gida ganin sun kusa makara yasa sumayya hana khadija zuwa gida abincin sahur ta iba mata tuwo ne miyan kifi d’anye suka zauna a waje suna ci 

Al’ameen kam tuwo kawai yakeci  da miya baya cin kifin 

Da mamaki sumayya tace “yayan khadija ya bakacin kifin  gashi mun kusa makara fa”?

Sumayya bazan iyya cin kifi d’anye ba kar kashi ya makale min a wuya

” tarwad’a ne fa”

Nikam ah ah

Hannu sumayya tasa a kwanon miyan ta yago kifi tasa mai a baki”toh bude bakin nasa maka”

Da sauri khadija ta kauda kai kamar bata gansu ba don wallahi sun bata kunya

Al’ameen kam bude baki yayi sumayya sai da ta ciyar dashi kifi har yace ya isheshi kafun ta ci nata

Bayan sunyi sallan asuba khadija ta koma gida Al’ameen kam bacci suka koma suna ramakon na jiya

Yau koh tafsir basu samu zuwa ba saboda baccin dake idanun su har 12:00 suna bacci a d’aki 

Assalamu Alaikum!! wasu yan matane guda hudu ke sallama sunfi minutes 8 suna buga sallama shuru

Al’ameen kamar a mafarki yake jin sallama akai akai mikewa yai hade da amsa musu

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 8 HAUSA NOVEL”


Ina kwana?

Lafiya, ya amsa 

Am wajen sumayya mukazo

Ok lafiya kam?

Eh munzo tambayar lallen sallah ne

Ok bara na tada ta

Ah ah ka barta in bata tashi ba inyaso gobe sai mu dawo 

Ok toh Allah ya kaimu 

Ameen,  in ba damuwa inta tashi kace yaran gidan Malam yunusa ne sukazo tambayar Lalle kar wasu suzo su riga mu?

Toh yace yana d’aukar boket bayan sun fita wanka yayi ya shiga dakin dayake yanzun yasan soket in kunna TV  jin an kawo nepa ga fanka na hura d’akin danna soket in yayi daman jiya sunnah  suke kallo aka d’auke, zama yayi yana sauraron wa’azi hannun sa d’auke da calbi yana ja

Sumayya bata tashi ba sai azahar nan ma shiya tashe ta kafun ya tafi masallaci

*******************

Haka rayuwa yayi ta tafiya axumi nata karewa a hankali hankali customers na sumayya suke zuwa tambayar lalle tun sallah saura kwana goma ita karan kanta batasan adadin wa’inda suka tambaye lalle ba ita dai ta amsa zatayi amma suzo da wuri,  sannan tana musu tallan wanda zaiyi kitson sallah kanwar mijinta nayi ai kuwa khadija ma tatara customers sosai, 

kayan sallah ma bana muhammad ne ya d’auke sumayya da khadija har kasuwa sukayi sayayyan sallah duk da sumayya taki yarda ganin tana da wasu zanunuwan a akwatin ta amma ina yace na akwati daban na sallah daban, ba laifi yasai musu kaya itama ta dad’a wasu da kudin ta haka ma khadija ta kara mata har kala biyu bayan wanda ya musu she karan kansa gezena biyu yasaya sumayya ta kara masa biyu duk sunka kai dinki.

Akwana A tashi yau dai saura kwana d’aya sallah kofar sumayya makil da jama’a daga masu kitso harda masu lalle, harda su suwaiban adara yau ana bin layi a kofar, sumayya na hango sanye da riga da wando baki tana ta fama da lalle sai khadija dake ma wata yarinya kitson brazil kulu da bit 

Har yamma mutane ne makil ba ita ta rabu da mutane ba sai kusan goma na dare nan ba hakuri ta basu akan gobe su dawo da asuba

Al’ameen dake d’aki kwance yana lazimi shiya raka khadija gida 

Yau sumayya koh girkin asuba bata samu tayi ba na bud’a bakin ma watace ta mata girki tana ma yarta lalle

Yauma bayan sunje tahajjud suna dawowa ne suka samu tuwo a bakin titi na asuba suka saya,  dashi sukayi sahur

Sumayya suna komawa gida suna sallah ta kwanta ai koh gama d’aukarta bacci baiyi ba tafara jin sallaman mutane ga idonta duk bacci kin tashi tayi Al’ameen ne ya fita ya basu hakuri akan sumayya na bacci Amma haka bayin Allah nan sukaki tafiya taburma suka shimfid’a suka zazzauna🤣suna jiran sumy(masu lalle gaskiya kuna ganin abu a sallah har kwana ana muku a d’aki)

Surutun su shiya hana sumayya komawa bacci haka tanaji tana gani ta kasa bacci dole yasa ta fitoh jin jama’a sai dad’uwa suke

Ai tana fita saiga khadija da tawagar masu kitso sun tasata a gaba😎

Haka suka dukufa suna neman halal nasu, 

Al’ameen fita yayi a d’akin sumayya! yakira sunan ta 

“Na’am”ta amsa tana mai mikewa ta bisa d’akin ganin ya koma

Sumayya zan fita na karbo mana dinki,  maganar zuwa kasuwan fa muna sa ran gobe sallah fa naga bamu shirya kome ba?

“eh kam gaskiya nima naso naje kasuwan nan da kaina amma yanzun ba iyya fita zanyi ba sai dai ku tafi da khadija in yaso sai na rubuta mata list”?

Ok nace na saya mana watanda ne?(naman shanu da ake yankawa a ranan jajeberi ana saidawa a unguwa)

“Ah ah ka saya mana kaji gaskiya tunda sallah ne”

Shinkafa koh tuwo zakiyi?

“Habba tuwo ranan sallah, shinkafa zanyi da miya sai coslow da kaji sanan zanyi masa da miya”

Ok daman so nake ranan sallan nan mu kaiwa gidan su Ammar abinci kuma muje mu gaida iyayen sa sai kuma nayi tunanin kar suce don kudin su yasa muke son rabansu fa?

“Ah ah yayan khadija in zakayi abin Alkhari kayi kawai karma ka bari shaid’an ya saka maka wani tunani daban a ranka kaji”?

Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben kinyi lalle kuwa?yana maganar yana kama hannun ta

“Ina naga lalle daga ni har khadija ba lalle ba kitso”

Kai gaskiya nifa an takurani tun sallah saura kwana hudu ban sake cin abincin kiba ki taimaka ki mana girkin sallah da kanki

“Insha Allah la’asar nayi zan sallami kowa wanda ya samu da wanda bai samu ba duk sai suyi  hakuri nima na samu nayi aikin sallah”

Ok kiramin khadijan inkin gama rubuta list in mu tafi

Haka koh akayi sumayya list ta rubuta ta baiwa khadija duk yanda jama’a masu kitso suka ringa roko sai da sumayya ta d’aga khadija suka tafi kasuwa

 dinki suka fara karbowa sai cefenen da sukayi sosai sukayi cefene sai da ya cika bairo.

Bayan khadija ta dawo sumayya tashi tayi ta gyara kajin duk da wasu sunso karba mata Amma taki yarda soya kajin tayi daman guda biyar ya saya ta rabawa mutane d’aya sosai tayi ta ayyukanta wasu kamma ganin aiki take kuma ba karewa zaiyi ba, zuciya kawai sukayi suka tafi abinsu wasu kam kama mata aikin sukayi duk da ta nuna su bari amma kin bari sukayi wasu sun gyara mata tattasai wasu sunkai nika cikin kankanin lokaci ta kammala had’a abubuwan sallan ta miya ma ta soya amma bata sa ruwa ba saboda ba’a tabbatar anga wata ba vegetables ma bata yanka ba tadai sasu a firij ne 

Bayan Ansha ruwa sumayya sallamar mutane tayi wa’inda bata musu ba ta basu hakuri wasu kuma sukace gobe koh jibi zasuzo Amusu

Yau kam saida muhammad ya saya mata matsala 8 tasha tsabar yanda bayanta ke ciwo amma fa gaskiya ta samu kudi bana wasa ba a sallan nan khadija karan kanta kudi ta samu sosai 

Har dare ba’a sanar anga wata ba haka su sumayya suka kwanta da niyar inba’a gani ba zasu tashi da azumi

Aiko hakance ta faru don da asuba ji sukai ana atashi ayi sahur jama’a gobe ba sallah bane😌

Ai yau kam sanin da sumayya tayi ba karamin mutane ne zasu zo ba yasa tana sallan asuba ta tattara boron lallen ta tayi gidan goggo Al’ameen ta bari a d’aki yana bacci tace masa zata saloon gyaran gashi sai tayi lalle tama khadija  

Gidan goggo taje tayiwa khadija lalle ja da baki itama tayiwa kanta sai dai bata ma hannun dama ba manna masa gam tayi khadija tasa mata lalle akai

Lallen su na kamawa ita da khadija saloon suka wuce aka gyara ma khadija gashi don ita kam bata wanke kanta a sefe, kitso khadija ta watsa mata a saloon sai kusan la’asar sumayya suka dawo, kai taga ikon Allah jama’a ne tirem a kofar ta Al’ameen ya rufe kofar d’aki ya fita sukam suna zazzaune a baranda 

 haka ba yanda ta iyya ta hau musu lalle 

Dayake ana da tabbacin gobe sallah ne yasa khadija had’a musu miyan sallah ta d’aura zobo tana gama had’awa ta juye a robobi tasa a firij

muhammad ma ya turo kayan marmari da sumayya tace zata markad’a a blander tayi juice dashi 

Sai dare sosai mutane suka watse ita da khadija suka kai nikan shinkafa bayan sun dawo suka kwaba, yaukam khadija a gidan ta kwana da sumayya a waje yayanta na d’aki

*RANAN SALLAH*

yau take sallah ranar farin ciki ga dukan wani musulmi kowa ka gani fuskar sa d’auke da farin ciki hakan take a wajen su sumayya tun asuba khadija ta fara tuyan masa

 sumayya ma wuta ta hura ta d’aura shinkafa don yau dai ba’a gas koh hot plate za’ayi girki ba

Vegetables inta ta kama yayan kawa su green beans green pepper yellow pepper piece cabbage carrot harda k’wai ta d’aura a wuta ga babban kwalban BAMA a zaune agefe

karfe 7:30 sumayya sun gama girkin sallah, 

manyan kulolin ta masu shegen kyau,  bata taba bude suba sai a ranan mai guda biyar ne ta zuba shinkafa masa coslow miyan ganye da miyan stew sai manyan manyan kofunan zamani ta juye zobo a ciki d’aya kuma mango juice duk sunyi sanyi har suna raba ta sake maidasu firij, wannan na gidansu Ammar kenan,  sauran juyewa tayi a babban kula  haka ma miyar duk d’aki ta shigar dasu sanin halin mutanen gidan 

Wanka tayi ita da khadija suka saka kayansu mai kyau da hijab Al’ameen ma gezena insa sabo ya saka koh sanda sumayya ta hanasa rikewa ita ta kama hannunsa khadija ta rike musu sallaya rufe kofa sukayi lokacin karfe 8:30 sauri suke karsu rasa sallah

Suna fita a gidan sun tsaya a bakin titi amma ba keke koh wani keke suka tare a ciki haka suka fara takawa, kamar hadin baki saiga Ammar ya shawo kwana da motar sa packing yayi a gabasu hade da budewa ya fitoh sanye yake da wani d’anyen yadin shaddane mai kyau sai hula da takalmi agogonsa sai d’aukar ido yake.

Ashe gwara danayi sauri tun d’azun ina ta tunanin bazan same kuba taima ?

Laii Ammar kaine sannu ina kwana?

Lafiya muahmmad barka da sallah.

Ai ba’ayi sallar ba tukum, muhammad ya basa amsa

“Ina kwana”?sumayya tace tana had’a fuska ganin yauma kamar kullum idonsa akanta

Lafiya sumayya muntashi lafiya?

“Lafiya mungode Allah”

Khadija kam kuri tayi tana kallon sa toh a ina tasan bawan allah nan ne kam ta kasa tunawa, a hankali ta ma sumayya magana, aunty nikam a ina kukasan wannan ne?

“Habba khadija kin manta mutumin da yazo asibiti lokacin da za’a mini tiyata ya baki kudi ki ban”

Oh na tuna na tuna Aunty , ina kwana?tana gaida Ammar

 kin amsawa yayi hannun muhammad ya kama muje koh ku shiga mota muyi sauri karmu rasa sallah

Ba musu dukansu motar suka shiga yaja suka kama hanyan masallaci

Allahu Akbar anyi sallah lafiya jama’a kamar kasa suna ta fitoh wa a edi kowa ka gani fuskar sa a washe sai gaisawa ake da juna abin gwanin sha’awa kowa na sanye da sabin kaya sai dai na wani yafi na wani tsada

Bayan su Ammar sun fitoh a cikin cunkoson jama’ar dake masallacin, yaso kaisu muhammad gidan su amma sukace ya maidasu gida zasu d’auko abincin da zasu kai gidan nasu

Ba musu ya mai dasu gida abincin muhammad ya d’auko musu a kula ya fitoh waje dasu juice taburma ya shinfid’a musu ba kyama Ammar ya  zauna sukaci abincin da muhammad sai santi hake don gaskiya abinci ne na kece raini 

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 9 HAUSA NOVEL”


Ta bangaren sumayya abinci ta sassaka a kwanuka ta baiwa khadija ta rabawa mutanen gidan ADARA kowa da plate nasa ta zubawa goggo ma ta kai mata tana dawowa sukaci abinci tukum kafun suka sake wanka lokacin azahar yayi sallah sukayi sumayya ta watsawa khadija make-up sosai khadija tayi kyau tana sanye da dogon riga na zani holland mai shegen kyau sai gyele da jaka tare da takalmi hada agogo da su sarka masu azaban tsada sosai sumayya ta kashewa khadija kudi a sallan nan 

Ita kam les tasaka sai mayafin ta babba powder kawai ta shafa sai kwalli da man baki don A matsayin ta na matar aure hakan baidace ba tayi kwalliya ta fita tana d’aukar hankalin maza

Al’ameen ne ya shigo duba su sumayya sun gama shiryawa ne Ammar ya dawo yana jiransu 

“Don Allah yayan khadija ka sake wanka mana ka chanja kayan jikin kan nan”?

Meya samu na jikin nawa?

“Ba kome amma dai ya kamata ka chanja tunda gidan masu kudi zamu gwara mu kece raini”

Kai sumayya kin cika shirme amma dai bara na watsa ruwan shap shap yayi wanka ya fitoh sabon gezena da sumayya ta d’inka masa shiya saka mai tsadane sosai sai takalmi da agogo yau harda glass sumayya ta d’auko tasa masa lias na hannu riga duk ta makala masa,  hannunsa ta kama suka fitoh bayan khadija ta rufe kofar 

Kulolin suka d’auko guda biyar sai jup na juice da zobo duk suka jera a boot na motan Ammar 

Tunda sumayya ta fitoh idon Ammar ya sauka akanta gabaki d’aya ya tatara hankalin sa

Gareta sai kallon ta yake kamar idanunsa zasu zazzago

Sumayya kam tun fitowar ta ta lura da kallon da Ammar ke mata kamar maye duk d’aga ido da zatayi sai sun had’a ido ganin yanda duk yabi ya zuba mata na mujiya yasata juyawa da sauri cikin haushi tayi cikin gida

Khadija dake kokarin shiga motar ganin sumayya tayi cikin gida yasa ta kwala mata kira, aunty sumayya kin manta wani abune?

Sumayya koh juyowa batayi ba tayi shegewar ta ciki 

da sauri Al’ameen ya fita a motar jin khadija tace masa sumayya ta koma cikin gida yabi bayanta……….

 

Back to top button