Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 2 Complete Novel

Sakin ledar sweet ɗin yayi yana kallon ta ido waje.

Fasa shiga palourn yayi ya juya da sauri yai hanyar ɗakin shi ya bar ledar anan inda ya yarda ta, tsoro sosai ya lulluɓe shi, sauri yake kamar ze ci ta baka ya samu ya buɗe ɗakin shi ya shiga.

Yana shiga nepa na dawo da wuta, zama ya yi a gefen gadon shi yana dafe da kan shi 

Gaba ɗaya ya rasa wani tunani ma ze yi, Abdul yace “anya banci kai ba kuwa?, 

Da wannan tunanin a cikin ranshi ya  gama duk wani shirin kwanciya sannan ya hau gado yai addu’a tukun ya kwanta.

WASHE GARI

kamar jiya kafin Abdul ya dawo daga massalaci an gyara mishi ɗakin shi fes, ko tsinƙe baza ka gani ba,

Banda ƙamshi ba abunda ke tashi a ɗakin

Shaƙar ƙamshin yayi har cikin huhun shi, yace

“Hmmm, ƙamshi rahama ne”

Ba wani tunanin komi a cikin ran shi, ballanta na yaji abubuwan sun dame shi, sema wani irin shauƙi  da kamshin ke neman saka shi a ciki.

Cikin yanayi me daɗi Abdul ya koma baccin  safen da ya zame mishi jiki in dai ana hutu

Sosai baccin ke masa daɗi, 

cikin baccin yaji kamar ana ƙwanƙwasa masa ƙofa, a hankali ya buɗe idanu,

 jin an ƙara ƙwanƙwasa ƙofar ne ya bashi damar tashi ya nufi ƙofar

Yana buɗe ƙofar yaci karo da Hishma da Hisham a tsaye hannun su riƙe da sweet ɗin da yasaba siyan musu, yace

“ƴan biyun ummie ya akayi ne?

Sauri haɗa baki sukai wajen faɗin “Abbah ne yace kazo”

Abdul har ya juya cikin ɗakin ze saka riga ya waigo ya sake kallon ƴan biyu yace

“Waye ya je ya siyo muku sweet ɗin?

Be jira cewar su ba ya ƙara da “ba na hana ku fita ku kaɗai ba?

Hishma da ta fi Hisham magana tai saurin faɗin “Ba mu muka je ba fa ya Abdul, 

ummie ce ta bamu ɗazu, wai munyi bacci jiya da ka dawo”

Yankewa gaban shi yayi ya faɗi da ya tuno abinda ya faru da shi wajen zuwa siyen sweet ɗin, da kuma abunda ya faru bayan ya shigo gidan

Be ƙara ce musu komi ba se rigar shi da ya ɗauka ya saka, sannan yace “ku muje”

Abbah da ya kafe Abdul da kallo yace

“Ciwon kan yayi sauƙi?”

Kallon Abbah yayi da mamaki a fuskar shi yace

“ciwon kai kuma?” ya ƙara da “ni lafia ta lau, ba wani ciwon kan da nake”

Kallon shi Abbah ya sake yi da ɗan mamaki a fuskar shi yace

“To ƙarya kai mana kenan jiya da daddare?”

Shima Abdul da mamaki yake kallon iyayen na shi da suka kafe shi da idanu yace 

“Ban fa shigo cikin gidan nan ba jiya Abbah,”

Be gama rufe bakin shi ba ummie tace

 “kaga abunda nake gaya maka ko? Kwana biyu Abdul ya koyi rainin hankali, ƙiri-ƙiri zece abu ko kuma ya aikata abu, da zaran ka tambaya ze dawo ya nuna maka shi sam be san zance ba.

Waigawa tai inda Abdul ɗin yai ƙur yana ta wasa ƙwaƙwalwar shi akan ya tuna sanda ya shigo cikin gidan amma ya kasa, ummie tace

“Sweet ɗin da ka kawo ma ƴan biyu shima duk baka san kayi ba?

Abdul da muryar shi tai sanyi yace

“wallahi ummie na manta, ina kyautata zaton mantuwa ce ta fara kama ni da ƙananun shekaru na”

Maganar Abdul ɗin se taso basu dariya, “wai mantuwa”

Wasa Abbah ya maida maganar yace

“Aure kake buƙata, In ka ga mutum ya fara susucewa to ai mishi aure, se ka ga ya dawo saiti” 

Abbah ya ƙarashe maganar yana ƴar dariyar su ta manya

Murmushi Abdul ya yi yana miƙewa daga gabn iyayen na shi,

Ummie tai karaf tace

“breakfast fa?, ko yau ma kaci?

Sosa ƙeyar shi yai yace

“kitchen ɗin na nufa yanzu”

Tace “da dai yafi maka”

*********

Binta wai Ina Zainaban take ne?

Warda aka kira da Binta tace

“Ka ganta nan malam,  se faman nuƙu-nuƙu take kamar warce ƙwai ya fashe ma a ciki”

Wacce aka kira da Zainaban ce ta fito sanye da ɗan madedecin hijabin ta  da ya wuce gwiwar ta kaɗan, tace a shagwaɓen nan

“Gani nan fa Abie, waya ta na tsaya dubawa”

Abie yace

“Zo ki tafi maza kar ki taushe hannu Auta, Iya na can na zaman jiran ki,

 ungo nan” ya miƙa mata nera ɗari uku

Hannun ta biyu ta sa ta karɓi kuɗin sannan ɗauki ƙatuwar ledar da zata tafar ma iya da ita

 tai ma iyayen nata sallama ta fita gidan tare da addu’ar fita daga gida.

Cikin nutsuwa Zainab ke tafia har ta dangane da babban titin dake cikin unguwar tasu, 

bata wani  jima a tsaye ba ta samu ɗan keke napep tai mishi kwatancen in da ze kaita tukun ta shiga ya ja suka tafi.

Har ƙofar gidan iya ɗan keken ya kai ta, ta cire kuɗin shi ta ba shi  tai gaba abinta

“Assalama alaikum, iya! iya!, gani nan na faso”

Iya tace “to uwar azagwaigwai, sannu da zuwa”

Gira ɗaya Zainab ta ɗage ma iya, irin ya kika gani ɗin nan

Ranƙwashi iya ta kaima Zainab akai tana faɗin 

“watan ciwon kai na ya tsaya ni jikar su,

Ɓata rai Zainab ta yi tana cuno baki waje, hannun ta bisa kanta tana shafa inda Iya ta ranƙwashe ta, tace

“Allah ya jiƙan Abie na ba dan ya mutu ba iya, wannan ranƙwashin naki in aka jera sati ana ma mutum shi wallahi zarewa ze yi, dan kaf notikan kan mutum kwancewa zasu yi tas”

Dariya Iya tayi bayan ta zauna tace

“Ni ƴaƴa na ai ba kunne ƙashi ke gare su ba irin naki”

Kwashe wa da dariya Zainab tayi tace

“kin dai manta iya, kin tuna labarin nan da ki ka bani na rashin jin da su Abie sukai suna yara?

Ba ta jira cewar Iya ba taci gaba

“Allah dai yaso Abie da har ya zama babban malami, amma wannan ranƙwashin da kika rinƙa ɗirka musu suna yara tsaf ze maida su jakai”

Dariya sosai Iya keyi, wani lokacin haka nan take so su zauna da zainab ko ba komai zata sha dariya da shaƙiyan cin ta

Yanzu dai ga kwaɗon zogale can da na kwaɗa naci nai ragowa, 

na san ki sahibar cin kwaɗo ce

Zainab da ta cire hijabin jikin ta, ta ninke shi ta ɗora a kan kujera sannan ta jawo kwanon da iya ke nuna mata ta buɗe,

Lafiyayyen kwaɗon zogale ne a ciki, wanda yaji ƙuli-ƙuli da yankakken tumatir da albasa,

 kallon iya zainab tayi tace

“Iya ta, kinji yarda miyau ɗina ya tsinke kuwa, humm Allah dai ya ƙara ma zogale daɗi”

Dariya suka ƙara kwashe wa ita da iyan kafin daga baya Zainab ta saka hannun ta a kwanon ta fara ci

Tana ci tana santi, har ta gama.

Iya nata tsokanar ta wai “ko da gida da mota aka haɗa ta baza ta iya kwaɗa shi kamar haka ba

Zainab bata ce komi ba banda loma da take ta zubawa, tana kaɗa kai 

Fita tai bakin famfon tsakar gidan ta wanke hannun ta sannan ta ɗauraye kwanukan data gani a wajen.

Zainab tace

“Iya, mu fara karatun nan kafin yamma tayi ban koma gida ba”

Iya data jawo jakar da take aje litttattafan ta na addini tace

“matsalar ki kenan, da kinzo gidan nan kamar ana tsungulin ki, 

karatun ma amaja kike min dan ma Allah yasa ni ɗin akwai ni da ƙwaƙwalwa”  ta ƙarashe maganar tana buɗe hisnul muslim ɗin ta

Se da Zainab ta gama kwasar dariyar maganar iya tukun ta fara ɗora mata daga inda suka tsaya

Sosai Iya ta tsaya ta nutsu ta koya, 

Seda Zainab ta tabbatar da Addu’ar ta zauna daram a bakin iya tukun ta tashi daga kusa da ita ta koma kan kujera ta kwanta.

Iya ta kalli zainab tace

“oh ni salma jikar hadiza, kice haka muke abubuwa sakaka kamar tumaki, ashe komi da komi akwai shi a ma’ajiyar shi

“eh mana, ai ilimi daɗi ke gare shi iya,

 komi da tsarin shi, duk wani abu da zamuyi ankoya mana shi ta fannin addini, tun daga kan tsarki, alwala, sallah da dai sauran su, addu’o’in neman tsari suma duk ba’a bar su a baya ba, kedai Allah yasa mu dace kawai, sannu a hankali zamu taɓo ko’ina”

Gyaɗa kai iya tai tana ƙara gamsuwa da maganar jikar ta ta.

Bayan Iya ta gama nanata addu’ar fita da shiga gida da aka gama koya mata, 

ta aje littafin sannan ta cire gilashin da ke ƙara mata ƙarfin gani ta kalli Zainab tace

“ai da ba ƙaramin jahilci mu ke a ciki ba, duk waɗan nan adduar ba wacce aka koya mana, 

sedai in gab da lokacin da za’a kai ki ɗakin miji se a samu ƴar tsohuwa ta zaunar dake ta koya miki karatun baƙar mayya da dai sauran su.

Miƙewa Zainab tayi ta warware hijabin ta dake ninke ta saka, sannan ta janyo ledar data shigo da ita ɗazu ta aje a gaban Iya tace

“Abie yace azo miki da shi, zan ware ni kuma haj Iya” ta ƙarashe maganar da shaƙiyanci

Ranƙwashi Iya ta kai mata, Allah ya temake ta tai saurin kauce wa tana dariya

Iya tace “ja’ira, in kin kauce wannan ai baza ki kauce ma wani ba”

Zainab tace “Allah dai ya ƙwace ni wannan karon”

Har ƙofar gida Iya ta rako Zainab, sukai sallama ta juya ciki ita kuma tai gaba

********

Cikin ruɗu da mamaki Abdul ke kallon cikin kayan shi, 

Da saurin shi ya fita ɗakin ya zagaya baya inda suke aje washing machine ɗin su, basket ɗin da ya zuba kayan shi masu dauɗa ɗazu da safe ya duba, 

sama ko ƙasa babu su, 

a guje ya ƙara koma wa ɗakin shi, sake buɗe  walldrop  ɗin shi ya yi yaga tabbasa kayan dauɗar da ya fita dasu ne a wanke kuma a goge, wani razanannen ihu da ya karaɗe ɗakin da ma cikin gidan ya fasa ya zube a wajen wanwar.

Abbah da Ummie sun jima sosai akan Abdul, amma ina numfashin shi yayi nisa sosai, gaba ɗaya ummie ta ruɗe se faman sambatun kiran sunan Abdul take

Tunowa  da Muslim ɗin da Abbah yayi da azama ya ciro wayar shi yai dialing number shi,

Cikin sa’a bugu biyu Muslim ya ɗaga wayar 

Abbah be wani tsaya amsa gaisuwar shi ba yace

“kana gida muslim?”

Muslim da jikin shi ya fara bashi ba lafia ba yace 

“yanzu zan ƙarasa gidan dai Abbah”

Da sauri Abbah yace ka wuto nan gidan pls, muna zaune muka ji ihun Abdul, a sume muka zo muka iske shi, kazo ko akwai temakon da zaka iya bashi, ko kuma mu wuce hospital”

“gani nan” kawai Muslim ya iya cewa ya kashe wayar.

Ko minti goma muslim be ƙara ba ya iso gidan shima hankalin shi a tashe, 

Shigowar shi ke da wiya Abdul ya buɗe idon shi tanwar kamar ba shine kwance a ƙasa sheme ba

Dukan su kan shi sukayi suna tambayar shi me ya same shi

Da farko shiru yai musu yana kallon su ɗaya bayan ɗaya,

Seda Abbah ya sake tambayar shi a karo na biyu tukun Abdul yace

“Bafa komi Abbah, nima ban san me ya faru ba”

Da mamaki Abbah ya kalli ummie da ita ma shi take kallo, ido waje ummie tace

“kan ka ɗaya kuwa Abdul?, uban ihun da ka zunduma fa, shima duk a ba komai ɗin ne?

Abdul da ya ƙosa da maganar ummie yace

“bafa komi ummie”

Muslim da se yanzu yai magana yace “maybe ya na buƙatar hutu Abbah, ku ɗan ƙyale shi tukun mu gani”

Ummie ce ta fara miƙewa ta fita, 

bayan few minutes shima Abbah n ya bi bayan ta.

Bayan su Abbah sun fice daga ɗakin muslim ya kalli Abdul da yai zuru yana ci gaba da kallon cikin walldrop ɗin shi,  yace

“Guru, u are not normal, meke damun ka? in ka ɓoye ma su Abbah ni kam be kamata ka ɓoye min ba”

Abdul be ce mishi komi ba, se ma ci gaba da kallon walldrop ɗin shi yake, so yake ya tuna abunda ya faru, amma ƙiri-ƙiri ya kasa

Sun daɗe a haka har muslim ya haƙura da tambayoyin shi shima yai shiru ya rabu da shi ya maida hankalin shi ga TV dake kunne

Zaman shirun da suke ya ishi muslim yace

 “tafia zanzo inyi fa”

Da sauri Abdul da jikin shi yai sanyi ya kalli muslim yace

“ka kwana anan mana”

Banza da shi muslim yayi ya fara tattare yanashi yanashi, 

Seda ya gama haɗa komi nashi tukun ya waiga ya yace mishi

“Ka zauna dai ka nutsu kasan abunda ke damun ka, 

likita ne kai, kuma likitan da ake ji da kai afaɗin ƙasar nan, kar ka cuci kan ka sannan kuma ka cuci wanda suke amfana da baiwar ka man,

Ganin irin wannan yanayin da kake shiga ne yasa yallaɓai yace kaje ka ɗan huta duk a tunanin shi stress ne,  memakon ka samu hutun ka tsaya ka huce duk wata gajiya dake damun ka amma se akasin hakan ke faruwa, please man, kabi a hankali”

Numfashi me ɗan huci Abdul ya fesar, tashi yayi ya karɓi jakar hannun muslim ya aje sannan yace 

“zauna in faɗa maka abunda ke damuna guy”

Ba musu muslim  ya zauna yana baza kunnuwa yaji, shi duk a tunanin shi Abdul ya faɗa soyayya ne

Muslim da ɗan murmushin shi a fuska yace “gara dai kai magana ai, nasan labarin gizo ai be wuce na ƙoƙi”

“Humm” kawai Abdul ya iya faɗi, sannan ya zauna kusa da muslim ɗin ya kalle shi ido cikin ido yace

“Guy gane-gane na fara yi fa!”

Dariya muslim ya sheƙe da ita yace 

“wa ka gano? a”ina take?”

Dogon tsaki Abdul ya jaa shima, yace 

“matsala ta da kai kenan, 

kai baka da wata magana me muhimmanci se maganar mata, ni ba macen da na gano, kawai dai ina ganin abubuwan da be kamata ace ina gani bane, 

wani lokacin se inga kamar na fara cin kai ne”

Dariya muslim yaci gaba da yi, gaba ɗaya ya maida maganar Abdul abun taokana

Banza da shi Abdul yayi yai kwanciyar shi yana jin wani iri a cikin ran shi

Da shaƙiyancin muslim yai ma Abdul yawa, a fusace ya ce mishi

“ya isa haka guy, dan na kwashe problems ɗina na faɗa maka ba shine ze sa ka tasa ni a gaba kana min dariya

 kawai ka tashi ka tafi tunda ka maida ni mahaukaci”

Cikin dariya muslim yace “nifa ba haka nake nufi ba, kawai ina imaging abun ne wallahi, ya za’ai kace kome sedai kazo ka iake an maka, wannan baze taɓa yiwuwa ba”

Kafin Muslim ya gama rufe bakin shi suka ji magana daga kusurwar ɗakin “ABUNE ME YIWUWA IN KA SAMU ME SON KA TSAKANI DA ALLAH MANA ABOKIN MU!!!”

ASHA HUTUN ƘARSHEN MAKO LAFIA

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU

COMMENTS AND SHARE

MASU BUƘATAR A TALLATA MUSU HAJAR SU, ZASU IYA TUNTUƁATA TA WANNAN NUMBER 08145225540

MRS SULAIMAN(ZAINAB FALALU)

Back to top button