Uncategorized

Gidan Uncle Page 10 Complete Novel

 

Kallon Daddy yake da tsananin mamaki yace “amma Dad….” katseshi yayi da cewa zaka samin ciwon kai “ka tashi ka tafi gdanka nace dare yayi” yana fada masa haka ya shige dakinsa ya kullo itakam Hajiya dama ta dade da tashi a gurin ya jima yana saqawa da warwarewa kafin ya miqe a salube ya sauko daga upstairs din ya nufi dakin Umaiman ya murda ya shiga.

 Kaka ya tarar a tsaye tana ninke kayanta kallonsa tayi da sauri tace “Lfy Umbamban meye ya kawokada darenan?

Zubewa yayi a qasa ya ruqo hanunta idonsa na zubar da hawaye yace “kiyiwa girman Allah Kaka ki bani aron Baby inason yin mgn da ita….” daquwa ta watsa masa tace “qaniyarka umbamban ubanme zaka fada Mata wanda baka fads mata ba a tsayin shekara daya da kukayi kuna sheqe ayarku ta banason shirme da sakarci waima kay anya qlau kake kuwa?” 

Miqewa yayi ya hau gadon ya birkito Umaiman dake bacci ya dora bakinsa saman nata tare da dora hanunsa daya a cikinta yanayi mata wata irin tafiyar tsutsa wadda yasan duk nauyin baccin da dakeyi idan yayi Mata saita tashi.

Miqa tayi ta banqaro masa boobs dinta yaja ajiyar zuciya tare da sanya hanunsa da sauri ya cafka yace “ohhhhh! Baby dadi…” 

Bude idonta tayi da sauri ta sauke su cikin nasa lumshe idonsa yayi yana yamutsa boobs dinta, a matuqar zafafe ta tureshi ta miqe yayi saurin miqewa yabita Allah ya taimaketa qofar a bude take ta kuwa kwasa da gudu bayanta yabi yana qwala mata Kira kicibis din da sukayi da Hajiya ne ya sashi yin baya da sauri yana sosa qeya a kunyace yace “am… Hajiya Ina… Inason mgn da it…ita Baby… Kallonsa tayi tsaf tayi baya saboda ita kanta Hameed tsoro yake bata ganin yanda saitin uhum hum dinsa taga yanda take miqewa da sauri ta fuzgi hanun Umaiman ta cillata dakinta itama ta shiga ta datse qofar da key.

Shafa kansa yayi cikin tsananin feeling da jarabarsa tasashi tsokanowa kansa ya koma ya zauna a kujera yana mayar da numfashi.

Yafi 30 minutes a zaune a gurin kafin ya miqe ya fita ya shiga motarsa da Daddy ya basa key din ya tafi gda.

Yana zuwa ya fada saman gadon yana sauke numfashi tare da janyo pillow ya rungume qam a jikinsa kamar zai shigar dashi jikinsa zuciyarsa nayi masa wani tuquqi yanzun ta tuni Babynsa ce a rungume a qirjinsa amma su Daddy sun kasa fahimtarsa.

Hakanan ya kwana juyi ita kanta feeling ya yarda kwanciyar hankali ke kawota saboda gabadaya tunaninsa ya karkata yanda zai samu Babynsa ta dawo gareshi amma bai hango wata hanya ba.

Shi ji yakema da ace Daddy cewa yayi ya bashi duk abinda ya mallaka shikuma ya barshi da Babynsa da yafi masa sauqi fiye da wannan hukuncin rabasun daya dauka.

Daqyar ya it’s tashi yayi sallah ya shirya ya nufi gdannasu babban tashin hankalinsa yanda Umaimah taqi daga wayarsa ko kadan qarshema yajita a kashe.

Yana zuwa gdan sama ya hau gurin Daddy suka gaisa babu wata alama ta bacin rai a tattare da Daddy itama Hajiyan yaga sauyi a fuskarta ba kamar jiya ba hakama Kaka amma gwanar tasa ko kallon tsiya bai samu a gurinta ba balle yasa ran samun na arziki duk hankalinsa yana kanta so yake ta dago idonta amma taqi har qafa ya rinqa turawa qasan table din yana zungurin qafarta amma ko gezau batayi ba qarshema miqewa tayi ta nufi dakinta zata shiga har takai bakin qofar yace.

“Am Baby ga motarki tazo jiya kije ki gani idan tayi miki I batayi ba sai a kawo miki wata” tana gama sauraronsa ta shige dakin ta datse qofar ta fada gadon tana sauke ajiyar zuciya quru kawai tayi ta shareshi saboda famfon da Hajiya ta kwana tanayi Mata akan halayyar da namiji ita kuwa ta hau ta zauna daram.

Haka lkc yayita tafiya kullum da sabuwar rigimar da Hameed za bullo da ita duk yanda yake tunanin samun sauqi a gurin Umaimah abin ya gagara kwata² bata sakar masa fuska kayy yanzun takai ma ko a parlourn bata zama kuma kullum qofarta a garqame yabi takan qawarta Sa’ud amma abin yaci tura saboda ita kanta Sa’ud din yanzu Umaimah bata daga wayarta sai taga dama.

Tafi² cikinta kullum qara girma yakeyi gashi har ya shiga wata na shidda ya fara fitowa sosai Daddy da Hajiya sun kasa sun tsare sun hanata fita ko qofar gda saboda sun lura batason cikin idan ta samu dama zata iya barar dashi.

Sadiya zama ya miqa a gda tunda suka rabu da Hameed bai qara waiwayarta ba gashi yaqi bata damar ganin yayanta ko sau daya suna gurin Hajiya Umaimah ke kula dasu kamar ita ta haifesu kullum basu da aiki sai shafa dan qaramin cikinta daya fara turawa suna cewa “aunty Uncle yace kin kusa ki haifa mana qani mune zamu rinqa rainonshi muna goyashi muna tafiya mkrnta dashi” itadai saidai tayi yaqe wanda akace yafi kuka ciwo saboda Allah ya sani tana cike da nadama da danasanin abubuwan da shaidan yasasu aikatawa a baya qashi tunda cikin ya shiga wata na bakwai take fama da rashin lfy ciwon ciki da ciwon mara  sunje asibiti da Hajiya aka tabbatar musu da kwanciyar yarinyar ne ba daidai ba saboda haka tana buqatar kulawa sosai kallon Dr Saleem tayi tace “to amma Dr ya lfyr abinda ke cikinta?”

Murmushi yayi yace “lfyr baby qlau Hajiya amma dai a qara kulawa” da wannan kalamin suka dawo gda Hajiya tanajin so da qaunar cikin jikin Umaimah wanda tasani bata tabajin haka akan yayan Sadiya ba kodan Umaimah jininta ce oho.

Ita kuwa Umaimah a ranta ji takeyi dama ace cikin ya lalace idan taji motsin cikin ji takeyi kamar ta bigeshi daga jikinta haushi da tsanar Hameed na nunkuwa a zuciyarta saboda badan shiba da rayuwarta bata shiga wannan gararin ba.

A kuma wannan dan taqin ne Sadiya tayi aure saboda ta bibiyi  Hameed yana wulaqanta ta harta gaji ta hqr ta saduda ta auri wani abokin aikinta me Mata biyu saboda takurawar da babanta yayi Mata akan cewa saidai tabar masa gda bazai iya zama da ita suna hada kafada da matansa ba kasancewar babanta matansa uku.

Hakanan ta auri Alh Salisu badon tanasonsa ba saidon gudun korar karen da babansu yakewa duk wata yarsa bazawara da taqi aure yazo kanta musamman ita da kowa yasan ita ta kashewa kanta aure da masifa da zafin kishinta da kuma qin karbar qaddara ga uwa uba rashin daukan miji a bakin komai.

*************************

Tun farkon dawowar Umaimah gda Hajiya tayima Daddy mgn akan cigaba da karatunta to lkcn semester tayi nisa saboda haka ya biya mata Jamb ta zana ya Allah ya taimaketa ta samu abinda ake buqata ta zauna jiran lkcn da zaa koma hutu saboda komai na mkrntar an gama mata Skyline University ce Daddy ya biya mata.

Tun cikinta nada wata bakwai Hajiya tayima Hameed mgnr siyayyar kayan haihuwa yace Mata shi ya gama siyan komai da ake buqata Aunty Zarah zata kawo.

A cikin satin Aunty Zarah ta kawo kayan daya gigita tunanin kowa Kaka kam sallallami ta hau yi tana cewa “wannan yaro wanne irin mahaukaci ne ina zaakai kayannan haka saikace wanda zaa haifama yaya goma” 

A haka kwanaki suka rinqa turawa ranar wata laraba da yamma Umaimah tana kitchen ita da Hajiya da titsetsan cikinta a gaba suna girki taji bayanta ya bada wata qara qass tare da riqewa tayi qasa da sauri tana dafe cikinta da bayanta tana fadin “way…yohhh uwata wayyoh ub…ana wayyoh Hajiya bay…ana cikina shikenan mutuwa tazo Hajiya ki yafeni🤣……

Kamota Hajiya tayi da sauri na hadata da jikinta tace “subhanallahi haihuwar tazo Umah bari mu tafi Asibiti” riqota tayi a jikinta suka fito parlourn inda Kaka take zaune tana duba jarida miqewa tayi da sauri daidai lkcn da Hameed din ya shigo parlourn ganin yanda Umaiman take yatsina ana rirriqeta ai baisan sanda yayi watsi da ledar shop din dake hanunsa ba ya nufi Umaiman da gudu ya ruqota Hajiya tace “yawwa maza sata a mota haihuwa ce…” 

Ai bata I rufe bakinta ba ya sunkuceta yayi waje har yana tuntube yanakiran sunanta, sata yayi a sit din baya yashiga ya tada motar bai jira fitowar su Hajiyan ba saboda gani yake zata bata masa lkcn yaja motar a mugun guje ya fice daga gdan.

Suna fitowa sukaga tashin qurar motarsa suka shiga wata driver yaja suka rufa masa baya bai iya hqrn kaita asibitin nassarawan ba saboda nisansa yake gani daga unguwar tasu wani asibitin kudi ya nufa aka karbeta aka shiga da ita larbour room sai bayan an shiga da ita sannan su Hajiya suka qaraso Hajiya ce tabada katinta tare da fada musu matsalarta shikam gogan sai safa da marwa yake yana hada gumi kamar shine yake naqudar duk sanda ya juyo nishinta shima sai yayi kamar shine me haihuwar lamarin ba duk da halin tararrabin dasu Hajiya suke ciki basu kasa yimasa dariya ba amma shi ko a jikinsa bin likitocin kawai yakeyi da suketa kaiwa da komowa  idan kuwa yajisu shiru ya rinqa leqe kenan ta window.

Cikin ikon Allah baa bata wani dogon lkc ba Allah ya sauki Umaimah lfy ta haifo kyakkyawar yarta mace me kama da ubanta da uwarta dake dama kamar tasu dayace  kowanne ka kalla sai kace yarinyar tana kama dashi tsakanin Hameed din da Umaimah.

Kukan jaririyar ne ya ankarar dashi aikuwa tun kafin a bashi izinin shiga ya danna kai dakin ya hango Babyn tanata wutsil² a hanun wata nurse ko takan Babyn baibi ba ya nufi inda Umaiman take ya tsugunna yace “wayyohhh Allah Babyn Uncle sannu kinsha wahala ko da wahala haihuwa ko? Ni nama yafe kawai wannan kadai ta ishemu” 

Wani kallo da takeyi masa ne yasashi miqewa a sanyaye ya matsa inda nurse din take riqe da Babyn take shiryata ya tsaya ya zubawa yarinyar ido kawai sai yaji wasu hawaye sun zubo masa Allah kenan duk cikin yayansa babu wacce take tsananin kama dashi kamar jaririyar ajiyar zuciya yayi ya miqa hanu ya karbeta daidai lkcn dasu Hajiya suka shigo dakin.

Da sauri Hajiya ta nufi Umaimah ta dagota ta nufi toilet din da taga wata nurse ta fito tace “akwai ruwan da zata gyara jikinta?” 

Amsawa tayi da “eh nama hada mata gashi can a ciki” shiga sukayi Hajiyan ta gasa mata jikinta sannan suka fito ta zaunar da ita a gefen gadon dagyar saboda ta dunku kamar qwarya sai a lkcn Hajiya ta samu damar daukar jikar tata da taketa wawuran abinci ta zuba mata ido kamarta da ubanta lkcn yana jariri har tayi yawa.

Hakanan suka yini a asibitin Hameed  yana liqe dasu suna zuwa Hajiya dakinta takai Umaimah tana mata sannu har yanzu tana maqale da jikarta saida ta bawa Umaimah abinci da tea tasha sannan ta dora mata babyn a cinyarta tayi murmushi tace “yarinya kyakkyawa amma kun bata mata nasaba saboda son zuciyarku”

Hameed ne ya dago ya kalleta ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace “muma ba muso hakan ba Hajiya komai yana faruwa ne bisa buwaya da ikon ubangiji ku daina zargina wlh ba haka nakeba rabon wannan yarinyar zatazo a hakane yasa kika takura saina saki matata a halin inasonta tanasona kuma mun riga mun zama abu daya bazata iya rayuwa babu niba nima bazan iya rayuwa babu ita ba Hajiya ku taimaka ku dawomin da matata tunda ta haifemin abinda ke cikinta” 

Miqewa Hajiya tayi ta zugewa Umaimah rigar jikinta ta sanya hanunta ta ciro nononta ta dago yarinyar ta sanya mata a bakinta yarinyar ta kama tana tsotsa ya zubawa nonon nata ido yanajin wani shauqi da feeling na bijiro masa da sauri ya miqe ya fita daga dakin don ya fahimci zamansa zai iya haifae da matsala ko wanne lkc zai iya kai hanunsa ya cafki nonon ya taya yartasa sha.

Gidansa ya nufa yayi wanka sannan ya fara sanar da abokan arzikin sa anyi masa haihuwa matarsa ta haihu harda hotunan da yayi da bebyn ya dora a status dinsa na WhatsApp da Facebook aikuwa ya samu addu’a sosai zama yayi dirshen yana kallon bebyn da yayima huduba da sunan Hajiyansa Zulaiha yana kallon hoton yana hawaye yana Istigifari nadama yake da zuciya me tsarki tabbas ya aminta so masifa ne saboda sone umul aba’isin faruwar komai tsakaninsa da qanwar tasa amma meye ya sabbaba hakan? “Hajiya” ya fada a fili tare da cewa “itace taja mana komai amma yanzu laifina suke gani saboda nine mara gata” 

Wayarsa ya dauka a karo na ba adadi ya kira layin Umaimah amma a kashe yasani koda a kunne take ba dagawa zatayi ba saboda ta dade da ajiyeshi da rayuwarsa a gefe gashi shikuma sai yanzune ma yake qara gasqata cewa soyayyarta itace take sarrafa rayuwarsa komawa yayi ya kwanta a kujera ya zubawa hotonsu ido lkcn farin cikinsu nanan bai gusheba shi abin ar mamaki yake bashi yanda yake hangen tsantsar qiyayyarsa a idon Umaimah Umaimah da a baya yake sarrafata da zuciyarta yanda yake so.

Da wadannan tunane² ya kwana da safe ya tashi ya shirya domin tafiya aiki saida ya fara zuwa yaga lfyr Umaimah da bebynsa daya laqabawa Shurafah sannan ya haura sama gurin Daddy daya dawo daga tafiya jiya da dare suka gaisa yayi masa barka kamar abin arziqi sannan yace.

“Alhmdllh babana Ina tayaka murnar samun qaruwar da kayi taya mace naji karar da kayiwa mahaifiyarku ka kyauta daka sanya sunanta wa baiwar Allan nan Shurafah so kamar yanda na fada maka lissafin da mukayi a baya zai canza ne bayan haihuwar Umaimah to alhmdllh ta sauka lfy saboda haka yanzu zabi biyu gareka kodai ka karbi yarka ka nemi wacce zata shayar maka da ita ko kuma ka rinqa biyan uwarta take shayar maka da ita” 

Mamaki ne ya kusan kashe Hameed wannan fah shine tsugunu bata qareba ansai da biri ansai mage.

A sanyaye ya dago yace “amma Daddy na dauka cewa Umaimah koba itace ta haifi Shurafah ba ita me riqemin itace ta shayarmin da ita batare data nemi ko qwandala daga gurina ba….” 

Daga masa hanu Daddy yayi yace “ai wai da take uwar tata shiyasa muka fada maka haka dama da ace ba ita ta haifaba ma aida mu da kanmu zamu bata ta shayar maka da ita saboda haka zabi ya rage naka idan ka yarda zaka rinqa biyane to wajibine duk wata ka kawo min 5 million na ciyarwa”

A matuqar mamakance ya dago yace “5 million fah Daddy me Shurafah zataci da har zata cinye 5 million a duk wata Daddy duk mutanen dake gdannan ma bazasuci 2 millions a wata ba balle jaririyar da aka haifa jiya?” 

Shiru Daddy yayi ya dauki wayarsa ya fara latse² bayan yan sakanni aka daga yace “kuzo dukkanku inason ganinku a parlourn sama” yana fadin haka ya kashe wayar yaci gaba da duba wayarsa yana murmushi irin nasu na manya,

Shigowa sukayi suka hada ido ita dashi gabanta ya fadi sosai saboda wani kyau da taga yayi mata duk da ramar da yayi.

Daqyar ta iya samun guri ta zauna saman tumtum saida Daddy ya gama danne²nsa yace “Hajiya bashi yarsa” dagowa sukayi da sauri musamman Umaimah da taji mgnr kamar dirar kwarankwatsa a kanta.

Miqawa Hameed yarinyar Hajiya tayi jikinta a sanyaye hanunsa na rawa ya karba yana cije lebe wasu hawaye masu zafi suka zubo masa ya kwantar da yarinyar da taketa sharar baccinta a cinyarsa ya dago ya kalli Daddy yace.

“Na yarda zan rinqa badawa Daddy ka taimakeni kabar yarinyar nan a gurin mahaifiyarta idan na tafi da ita bansan ya zanyi da ita ba ko kuma ka mayar mana da aurenmu mu raini yarinyar nan cikin kulawar da duk wani da me gata yake samu a gurin iyayensa….” daukeshi da mari Daddy yayi yace “zaka tashi ka barmin gurin nan da shegiyar yarka kosai naci mutuncinka” 

Miqewa yayi a matuqar sanyaye ya matsa gaban Umaimah da take kallon Daddyn tana mamakin furucinsa kalmar shegiyar daya Kira Shurafah da ita tafi komai dukanta ya dora mata babyn a cinyarta cikin kuka me ban tausayi yace “Koda kowa na duniya zaiqi Shurafah bai kamata ta rasa gata biyu ba nawa da naki Umaimah ni namiji ne banida nonon dazan bawa Shurafah ta rayu dashi kada kibada qofar rabaki da yarki da qaddara ta qadarta mata zamowa me rangwamen gata duk da nasani a gurin gama garin mutane take me rangwamen gata amma a gurina me cikakken gatace saboda na yarda itadin qaddara tace Umaimah babu wanda ya isa yayi maka wannan kyautar bayan Allah kuma bakida tabbacin sake samun wani bayan ita ta yuwu ita kadaice rabon dake tsakanina dake karki manta Umaimah kinsani komai yana faruwa ne bisa buwayar buwayi gagara misali badon hakaba dasai kice ya zaayi muna matsayin ma’aurata mu samu yarda bata sunnah ba to wannan kadai ya isheki misali ganin damarsa ne hakan ta faru Umaimah na roqeki kada kibada qofar banzatar da rayuwar yarinyar da bataji ba bata gani ba laifi nawane naji ayimin hukunci a kankin kaina amma kada ya shafi Shurafah dan Allah Umaimah…..”

Wata tsawa Daddy ya sake doka masa yace “wlh tallahi Hameed idan baka bacemin da yarinyar nan a gurin nan ba sainayi maka abinda baka taba tunani ba” jikinsa har bari yake ya miqe ya dauki yarinyar ya rungume a qirjinsa yana wani kuka mecin zuciya ya juya ya kalli Daddy yace “hakan ma na gde daka bari aka raini cikinta a gidanka amma kasani Daddy wannan zata zama rana ta qarshe da zaka rasani nima zanbar maka gdanka kuma Shurafah zatabar maka gdanka bari na har abada”

Yana fadin haka ya juya zai fice Umaimah tayi saurin riqo qafarsa cikin kukan tashin hankalin abu biyu rabuwa da yarta qwaya daya tak a duniya tace ““Ina neman alfarma daya Daddy baa matsayina na mahaifiyar Shurafah ba a matsayina na yar’uwar mahaifinta ta jini wacce zan iya fansar rayuwata da tasa ina neman izinin shayar masa da yarsa batare dako sisin sa ba Daddy na roqeka kayimin wannan alfarm…..” 

Daka mata tsawa Daddy yayi yace “wlh baki isaba Umaimah saidai ki tashi kibishi tunda kin zabi farin cikinsa akan nawa kin fifita darajarsa da matsayinsa akan nawa to kitashi maza ki hada kayanki kibisa bana buqatar ganin shegiyar yarinyar nan a gdannan” bata iyajin kalmarsa ta qarsheba ta toshe kunnenta tare da sakinsa ta fashe da wani gigitaccen kuka me firgita zuciyar me imani tanaji tana gani ya juyo ya kalleta shima yana kuka daidai lkcn yarinyar itama tasa kuka da alamun nono take buqata amma ya juya ya fice da sauri ta miqe tana hada hanya zata bishi Daddy ya ruqo hanunta ta kuma rushewa da kuka tace.

“Tun safe Daddy Shurafah batasha nono ba ka taimakeni kabarni nabata koda shine na qarshe da zatasha daga jikina……” Dauketa yayi da wani gigitaccen mari tayi qasa ta zube yaraf ta qara dora hanunta a kanta ta rushe da kuka tace “shikenan Daddy ka rabani da yata qwaya daya tak a duniya….” Miqewa ta sakeyi da gudu ta nufi window daidai lkcn da Hameed ya kwantar da yarinyar a kujerar me zaman banza ya shiga ya tashi motar a guje yabar gdan har lkcn kuka yakeyi.

Zamewa tayi ta zauna a qasa tama manta da dinki akayi Mata soyayyar da da mahaifi ta mantar da ita ciwon komai sai ciwon rabuwa da yarta, saboda tsabar kuka har muryarta ta dashe Daddy ya tsallake ta ya shige dakinsa inda ta miqe tana hada hanya ta fita daga dakin ta fara taka matattakalar benen amma bata iya sauka ba jiri ya debeta tayo qasa luuuuuu daga saman ji kake tim ta fado tsakiyar parlourn qasan kamar matacciya Hajiya dake zaune take gursheqen kuka ta taso da gudu hakan yayi daidai da fitowar Kaka dake baccin asara a daki……

Da gudu sukayo kanta cikin tashin hankali Hajiya taja da baya tace “mun shiga uku Kaka jini ta bakinta da hancinta kinga wani yana fita ta qasanta zata mutu Kaka anya Adamu bashida mental problem kuwa yaraba uwa da yarta a daidai wannan lkcn da kowacce uwa tafi buqata da tausayin danta Kaka ina Hameed zaikai Shurafah yanzu idan Umaimah ta mutu akan wannan dalilin me Adamu zaice da ubangiji?” 

Riqeta Kaka tayi tace “me..mekike cewa Zulaiha maza ku tafi Asibiti ina zuwa nima” tana fadin haka tayi sama da gudu gurin Daddy ta fara buga qofar kamar zata balleta fitowa yayi ya bude ta cukuikuiyeshi tace “ina ka bari Hameed ya tafi da yarinyar nan to wlh ka fita da gaggawa ka nemoshi ka karbowa Umaimah yarta kafin fushina ya hau kanka ku baku da hankali da tunani kullum baku da aiki sai yanke hukunci cikin fushi”

Tana fadin haka ta sake juyowa ko mayafi babu a jikinta ta fito waje ta tsari  taxi ta sanar dashi inda zai sauketa suna tafiya tana cewa dashi ya qara gudu cikin saa tana zuwa qofar gdan nashi dake FRW Layout ta hangi motarsa da wata motar a qofar gdan ta cillawa driven 1k tayi ta fada cikin gdan a guje amma me sai ta rinqa jiyo wani kakari yana fitowa daga parlourn da sauri tasakai ciki idonta kan Shurafah ya fara sauka dake dauke hanun Sarah tanata kukan neman uwa shikuma yana kwance a qasa sai fitar da dafara yakeyi mijin Sarah yanata bashi taimakon gaggawa tare da danna masa.

Cikin tashin hankali Kaka tace “mun shiga uku mukam wannan wacce irin masifa ce ta nufomu ne” daidai lkcn Daddy ya shigo don cika umarninta.

Dafe bango yayi da sauri tare da furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji’un” mantuwa daya Daddy yakeyi a rayuwarsa shine matsalar zuciyar da aka haifi dannasa Hameed da ita.

Da sauri ya qarasa inda yake kwance yana fitar da wani wahalallan numfashi ya rungumoshi yana jijjigashi yana cewa “Abdulhameed! Abdulhameed!! Abdulhameed!!! Babana ka tashi kada ka fada a bakin mala’iku kada muyi irin wannan rabuwar dakai kada ka mutu kabarni babana ba qinka nakeyi ba wlh inasonka” 

Kuka yakeyi sosai kamar qaramin yaro yana girgiza dannasa Kaka itama tana kuka tace “Shikenan ai kun kashesu kun huta saura yar itama gatanan Adamu kasa wuqa ka yankata sai ayi jana’izarsu gabadaya su ukun kukuma ku rayuwa a duniyar ku dawwama babu jarabawar ubangiji amma inaso ka sani nidai bazan yafe maka haqqi yarannan ba kuma Allah bazai yafe maka ba saboda shugabanci ba hauka bane Allah ma daya haliccemu munayi masa laifi ya yafe mana balle kai abin halitta Mai tarin dauda da zunubi”

Tana gama fadin hakan Hameed yaja wani dogon numfashi komai na jikinsa ya daina motsawa, wani ihu Daddy ya saki yace.

“Shikenan na kasheshi da kaina Innanillahi wa innah ilaihir raji’un Hameed….”  Abubakar ne ya matso ya daga hanun Hameed din ya matse wata jijiya ya zubawa yatsun qafarsa ido babban yatsansa yada ya motsa yayi ajiyar zuciya yace “bai mutu ba akwai sauran numfashi a jikinsa ayi saurin kaishi asibiti” 

Ai kafin Abubakar ya ida rufe bakinsa Daddy ya hada qarfinsa ya dago Hameed din Abubakar ya taimaka masa suka sashi a mota tun a hanya ya kira likitansa ya sanar dasu abinda ke faruwa.

Suna zuwa aka rufar masa aka fara jorner masa na’urori.

*************************

Ita kuwa Umaimah tunda aka kaita asibitin batasan waye a kanta ba daqyar likitocin sukayi nasarar tsayar da jinin dake zuba ta qasanta na hancinta da bakinta kam basusha wahalar tsayar dashi ba saboda kawai buguwa ce, saida aka farke dinkin da akayi mata aka kankare aka sakeyi mata sabo sannan aka daura mata drip Hajiya tana zaune a kusa da ita ta zuba mata ido tausayinta yana qara narkar Mata da zuciya Kaka ta shigo dauke da Shurafah a hanunta.

Da sauri Hajiya ta tareta ta karbi yarinyar da tayi kukanta harta gaji ta koma bacci tanajan zuciya tayi hamdala tace.

“Hankalina yana gurin yarinyar nan Kaka ina Hameed din?” zama Kaka tayi tace “yana emergency section kunsan matsalar danku kunma fini sani tunda kune kuka haifeshi saboda haka idan kun kasheshi hankalinku zaifi kwanciya”

Da sauri Hajiya ta tare Kaka da cewa “wai kina nufin ciwonsa ne ya tashi?” girgiza kai Kaka tayi tace “abubuwa da yawa daya dade yana binnewa a zuciyarsa sune suka hadu da wannan abun da kukeyi masa akan qaddarar da baku isa ku canzata da bacin ranku ba na tabbata da ace ana dawowa da mutum  book din predestinations dinsa da Hameed yana cikin mutane na gaba² da zasuyi gaggawar sauya tasu qaddarar amma kun kasa fahimtarsa kun kasa yi masa adalci da uzuri a cikin rayuwarsa komai fa da kuka gani yana faruwa ne cikin sahalewa da buwayar ubangiji wlh na tabbata idan yaron nan ya rasa rayuwarsa ta wannan hanyar kema kina da kamasho kuma kece umul aba’isin faruwar komai Zulaiha kinada kaso me tsoka cikin abinda ya faru tsakanin Baby da Hameed saboda haka kiyi gaggawar tuba kema don basu kadaine suke cikin fushin ubangiji ba harda ku da kuka kasa sama musu mafita me kyau”

Sosai kalaman kaka suka daki zuciyar Hajiya kuma sukayi mugun sanyaya mata jiki qafafunta taji suna neman gaza daukarta ta sulale ta zauna a qasa kan tiles tana kuka me tsima zuciya tana qara shigar Shurafah jikinta tace “Allah na tuba astangafurullah ya Rabbil samawati wal ardi kaicona dana kasance me yanke hukunci cikin fushi kaicona dana zamo me gyara barna da barna kaicona dana zamo silar zuwanki duniya bata hanyar aureba Zulaihat me zan fada miki ranar da kikaji labarin nice silar zuwanki duniya ta wannan qazamar hanyar wayyoh Allah dama ka karbi rayuwata kafin wannan lkcn na zamo uwa mara amfani uwa me qoqarin rusa farin cikin yayanta da furucinta na tabbata da banyi furucin tsinuwa ga Hameed ba da babu abinda zaisa ya saki matarsa…..”

Ta qarasa mgnr cikin wani irin kuka me ban tausayi sun jima a haka kafin ta samu qwarin gwiwar miqewa ta fita ta nufi pharmacy din asibitin ta siyo madarar da zaa iya bama yarinyar ta dawo ta jorner kettle ta dafa ruwan zafi ta hadama yarinyar ta sanya a cikin feeder ta sanya cikin ruwan sanyi kafin Shurafah din ta tashi. 

Sunanan zaune zaman jiran tsammani Daddy ya budo qofar ya shigo dukkansu suka zuba masa ido guri ya samu ya zauna ya hada uban tagumi yana share hawaye, Hajiya ce ta sake fashewa da kuka tace “Nikam naga ta kaina ni Zulaihatu ya mutu ko Alh shikenan Hameed ya mutu….” Dakatar da ita yayi ta hanyar girgiza mata kai yace “bai mutu ba amma yana tsakanin mutuwa da rayuwa Zulaiha Hameed yana fama da heart attack wanda zai iya zamowa sanadin salwantar rayuwarsa yanzu haka ya shiga commar wanda ko babu heart attack zaiyi wahala mutum ya shiga commer ya tashi yaci gaba da rayuwa….” 

Ya qarashe mgnr cikin kuka tare da tashi ya bude fuskar Umaimah da taketa baccin wahala yayi ajiyar zuciya sannan ya koma ya dauki Shurafah da tunda aka haifeta sai yanzu ya dauketa ya zuba mata ido yanajin son yarinyar na ratsa jinin jikinsa ya rungumeta a jikinsa yana ajiyar zuciya.

Sun dade a zaune jugum²  kafin Daddy ya tashi ya miqawa Hajiya Shurafah ya fita daga dakin sai dare Umaimah ta farka shassheqar kukanta ne yasa Hajiya fahimtar ta farka ta tashi da sauri ta qarasa gabanta ta ruqo hanunta tayi ta bude idanunta ta zubasu a kan Hajiya qwallar naci gaba da kwarara a idonta mgn takeson yi amma ta kasa sai jujjuya ido takeyi yarta kawai takeson gani ganin babu alamar yarinyar yasata qara sautin kukanta da sauri Hajiya ta juya gadon da aka kwantar da yarinyar tanata bacci ta daukota ta kwantar Mata da ita a gabanta.

Dagowa tayi ta kalleta kawai batasan sanda wani smiling ya qwace mata ba itama Hajiyan murmushin yaqe tayi mata ta koma ta zauna tana kallonta yanda idonta yake juyawa akan yarinyar duk da babu bakin mgn amma da ganin kallon da takewa yarinyar kasan nasone da farin ciki hadi kuma da tarin tausayi na da da mahaifi lumshe idonta tayi tare da daukan hanunta ta tallafo bayan yarinyar ta hadata da qirjinta wani bacci ya dauketa itama yarinyar numfashinta saida ya canza saboda jin dumin uwarta data yini tana kukan nema ko madara taqisha saidai zamzam da ake bata.

Alhmdllh jikin Umaimah yana sauqi sosai amma fah shi Hameed abun baa cewa komai saboda ko motsa hanunsa baya iyawa komai saidai ayi masa da na’ura ga wani qarin tashin hankali penis dinsa data miqe tun ranar da abin ya faru bata kwanta ba tun Daddy yana ganin kamar sauqi zaizo har ya sallamawa ubangiji komai saboda baya hangen wani sauqi a ciwon Hameed.

Kwanaki bakwai din a asibiti sukayita saboda dinkin Umaimah daya rikice sosai saida aka tsaya a kanta kana aka samu ya koma normal suka koma gda ranar da suka koma akayima yarinyar hakika raguna uku Daddy ya yanka mawa amaryarsa Shurafah da Sa yasa akayi sadaka duka a maqota ana fada musu haihuwar babu wanda yasan abinda ake ciki aikuwa a ranar akayita tururuwar zuwa tayasu murna saboda kowa sanin da yayi Umaimah matar Hameed ce saboda haka babu wanda yasan matsayin yarinya Shurafah sai su isu.

Kayan da Daddy yayima Umaimah da Shurafah ya bawa kowa mamaki saboda babu wanda yayi tunanin yanda ya dauki zafin nan zai siyawa maijego da jaririyar ko pant, sai dare da mutane suka lafa Daddy yasa aka kira masa Umaimah gata ga Hajiya ga Aunty Zarah ga Aunty Jameelah ga Kaka duk a gurin Shurafah tana tsakaninsu sai yawo take tsakanin dangin uwa da uba Allah Sarki shima shege me asali dan gata ne gadone kawai bashi dashi yanda ake lelen yarinyar har kuka yakesa Umaimah tana nadama da danasanin abinda suka aikata da Uncle din nata musamman idan ta tuna halin da yanzu haka Hameed din yake ciki na rayuwa ko mutuwa.

Daddy  ne ya katse shirun ta hanyar bude taro da addu’a ya dubi Umaimah yace “Baby ba komai yasa na taraku ba sai akanki kinga dai abinda ya faru tsakaninki da dan’uwanki kuma kinga irin matsalolin da suka rinqa fullowa qarshe dai ga ribar abinda kuka aikata nan kun samarwa zuri’ar Alh Abdulhameed Yauri Shuwa babu yanda zamuyi daku a dan qaramin family dinnan namu tunda daga ke harshi babu wanda zamu kora amma dai kun sani bakuyiwa zuri’arku da yarku adalci ba musamman keda kike mace yakamata ki nuna kedin mace ce wacce take fatan samun zuri’ar da zatayi alfahari da ita amma qarshe sai kika bige kika lalace wajen biyewa namiji da son zuciyarki saboda rashin tunanin me gaba zata haifar todai yanzu ga abinda gari ya waya yanan Allah ya sani munyi iyakar qoqarinmu na ganin kun kasance iyaye ababan koyi ga yayanku amma hakan yaci tura Umaimah dagake har Hameed nawane babu wanda zanyiwa baki saboda haka nidai na yafe muku batamin din da kukayi bada haqqina ba”

Dakatawa yayi yaja fasali  kana ya dora da cewa “inayi muku fatan alkhairi a rayuwarku ta gaba sai Abu na biyu kamar yanda al’adata take kuma nayima yan uwanki Zarah da Jameelah lkcn da sukayi haihuwar fari to kema ga mukullin motar ki sannan ki zabi duk qasar da kikeso a duniya zan biya miki keda yarki kuje ku huta”

Tunda ya fara mgnr take wani irin kuka me ban tausayi kukan nata ba qaramin tasiri yayi a zuciyar duk wani wanda yake zaune a gurin ba har saida Jameelah da Zarah suka tayata,

Tsawa ya daka musu yace “banason shirme tanayi kunayi memakon ku rarrasheta sai ku qara turata ke mgn nakeyi miki ki fadamin qasar da kikeson zuwa nayi miki visa da passport zuwanan da sati biyu saboda saura 5 weeks hutu ya qare ki fara attend lectures”

Cikin kuka da rawar murya tace “Saudia Daddy” dagowa dukkansu sukayi suka kalleta saboda basu taba tunanin wannan zabin ba sunyi tunanin zata zabi Turkey ne saboda duk wanda ya kwana ya tashi a zuri’ar yasan burin Umaimah bai wucce taje Istanbul ba amma sai gashi lkcn da damar tazo Mata ta zabi wata qasar daban.

Kafin kowa yayi mgn Daddy yace “meyasa kika zabi Saudi Arabia Umaimah?” Cikin kuka ta bude baki tace.

“Saboda na kusanci ubangiji na na ziyarci kabarin annabi na roqeshi ya roqamin gafarar ubangiji ya yafemin wannan kayan dana daukarwa kaina nasani Daddy na take sani na aikata zunubi mafi girma wanda laifi biyune a duniya yafishi nauyi a mizani shirka da giba Daddy hukuncin kisane akaina ta hanyar jefewa meyasa bazaka kaini a yankemin hukuncin ba nasan zanfi samun sauqi idan na mutu ta wannan hanyar Daddy wanne jin dadi ne ya ragewa rayuwata Daddy da nasan wannan qaddarar tana cikin abinda zai faru dani ta haihuwa ba aure wlh dana roqi Allah na mutu na huta Daddy meyasa Mama batayi barin cikina ba? Daddy me zancewa Shurafah ranar data girma ta tsinci wannan mugun tabon da rudin zuciya yasamu mukayiwa rayuwarta…..” 

Rufe mata baki Jameelah tayi ta rungume yar uwar tata a jikinta tana kuka tana cewa “kidaina fadar haka Umaimah ki daina roqon ki mutu ke bamu da yawa a zuri’ar mu kuma tun ran gini tun ran zane Umaimah waman qaddarallahu haqqan qadarihi haka wannan mgnr take babu wanda ya isa ya canzata naku dakyau ma tunda kinsan uban yarki kuma ya karbi abarsa kuma yanasonta kuma yar dangi ce qarshen dai abin ace idan mgnr aure ta taso tunda mace ce to koda mutane a duniya ko babu indai muna raye kuma muna haihuwa Shurafah zata auru ko a tsakanin yayanmu….”

Sake rungume Aunty Jameelah tayi tana wani kuka mecin zuciyar me imani itama Zarah kwantowa tayi a jikinta itama kukan takeyi tace “mu rufe mgnr nan tsakanin mu kada ta fita waje Umaimah don Allah koba Hameed ne uban Shurafah ba a qaramin family dinmu zamu karbeta mu riqeta saboda bamu da yawa muna buqatar yawaita a duniya abu daya ya rage Daddy kayi ka mayarwa da Umaimah da Hameed aurensu su riqe yarsu cikin aminci da kulawa”

Saurin dagowa tayi ta kalli Aunty Zarah ta girgiza kai tace “na roqeku kubar mgnr nan koda son  Uncle Hameed zai kasheni na hqr da aurensa har abada kada kayimin dole Daddy hakan zaisa na rinqa kallon kaina a matsayin marainiya mara gata kuma bazan taba farin ciki a rayuwata ba Daddy bazan boye maka ba na tsani Uncle Hameed….” Ba qaramin girgiza kowa kalmarta ta qarshe tayi ba amma babu wanda yayi qoqarin sake maimata mgnr saboda suna ganin kamar ciwon abinda ya farune yasata furta haka.

Murmushi Daddy yayi yace “Shikenan Uwar masu gda tunda bakya raayin zama dashi babu meyi miki dole amma kinsan aure dolene akanki bada jimawa ba saboda haka zan baki shekara guda ki shayar da amaryarta ki fitar da miji kiyi aure sannan kamar yanda kika zaba zamu tafi Saudi dani dake da Hajiya sai Hameed da zamukai a dubashi acan saboda ciwonsa yafi qarfin asibitocinmu na nan sai kuma Yayarki Jameelah da idan kun gama umararku zaku wucce Turkey ki cika burinki na zuwa Istanbul kafin ki mutu” 

Dariya tayi me hade da kuka ta miqe cikin tafiyarta da bata koma Normal ba ta matsa kusa da Daddy tayi kissing hanunsa ta rungumeshi ta kuma fashewa da kuka tana jera masa dubun gdy murmushi yayi yace komai nayima uwata ba faduwa bane fatana dai karta qara irin kuskuren da tayi a baya” jinjina masa kai tayi ya rungumeta yace Allah yayi miki albarka yabaki miji na gari wanda zai riqemin ke amana”

Amsawa kowa yayi da amin Daddy ya sake rufe taron da addu’a tare da yima yarinya Shurafah addu’ar shiriya da kariyar ubangiji kowa ya tashi ya nemi gurin kwanciya inda Daddy ya fice ya koma asibiti gurin Hameed.

Koda suka koma daki Aunty Jameelah ce ta hauta da fada wai bata kyauta ba da tace ta tsani Hameed tanajinta tayi mata shiru taci gaba da feeding din yarta har saida taga ta qoshi ta canza mata Pampers ta kwantar da ita tare da kissing din jajayen lips dinta tace “sleep well my lovely daughter kiyi dreaming dina kinji” abin dariya yabawa Jameelah sosai tace “oh ni Jameelatu Umaimah da ya hauka ya qaru wannan ya zakiga hauka gurin uwarki” dariya tayi tace “Allah Aunty bansan haka iyaye sukeji ba sai ranar da Hameed ya tafi da yarinyar nan wlh hankalina gushewa yayi ban iya sanin komai da nayi ba saida aka bani labari Aunty wai dama haka kukeji akan yayanku tab aini wlh babu mai dukar min Shurafah gara ka bugeni daka bugarmin ita dan zan iya rufe idona na ci mutuncin uban kowa” 

Dariya sosai Aunty Jameelah da Aunty Zarah sukeyi Aunty Zarah tace “harda ubana ko?” Kunyace ta kamata don tama manta da Aunty Zarah a gurin ta kwanta tace “Allah aunty dan bakisan abinda nakeji bane” murmushi tayi tace “kafin kiji na rigaki ji Umaimah” da haka sukayi bacci.

 *UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*

Back to top button