Uncategorized

Da Ban San Shiba Chapter 2 Complete Hausa Novel

DA BAN SAN SHI BA

CHAPTER 2

DAGA FAUZIYYA D. SULAIMAN

Komai, Alu yana ta kai wa da komowa yana ɗauko mata ruwa, tunda ya tashi da asuba bai hutaba, kasancewar akwai tazar tsakanin rafin da gidan su, sai da ya cika mata kwatanniyar ta sannan ya samu ya zauna yana hutawa, can ya k’ara hangota gaban murhun duwatsun tana hura wuta da zata ɗumama tuwan safe, duk da shekarun sa ba yawa ne dasu ba amman ya fuskanci duk sanda ta zauna gaban murhun nan tana shan wahala saboda ɗurkuso, ya mike da sauri ya nufeta yana faɗin. 

    “Inna bari na hura miki.” Bata yi musu ba taja da baya tana murmushi, ya ɗurkusa ya fara hura wutar cikin sabo da yi.

     Mal. Belɗo ya shigo gidan cikin sauri kamar wanda aka koro yana sabe tsohuwar babbar rigarsa, babu ko sallama ya banko gidan, sumaye ta kalleshi da tsananin mamaki tana faɗin lafiya dai ko Malam? 

    Mal. Belɗo ya kalli Alu dake durk’ushe gaban murhu yace “kai Maisango maza shiga cikin ɗakin ka d’auko tsummokaranka, yanzu nake jin labarin Mal… Da ya zo ganin gida yana shirin komawa can binni.”

     Mamaki da tsora suka bayyana a fuskar Sumaye ammam ta kasa magaNa sai kallon malam Belɗo da take yi cikin ruɗani, Alu bai ji abin da mahaifinsa ke cewa ba, domin hankalin sa gaba daya yana kan hura wutar, don haka yaci gaba da abin da yakeyi, Lanto ta zagayo daga kewaye rike da buta a hanNu yanayinta akwai tsananin farin ciki da murna aka fuskarta ta kalli Malam Belɗo. 

    “Malam kamar magana na ji kana yi ko? Malam Belɗo ya ƙara kai kallon sa ga alu “kinga yaron dana keyi wa magana yayi kunne uwar shegu dani, kai Maisango baka ji ni ba ne? 

    Alu ya waigo da sauri ya kai kallon sa inda mahaifinsa yake tsaye gami da faɗin “Baba nazo ne? 

    Lanto ta yi dariyar jin daɗi gami da faɗin “Sarai fa yana fa jinka Malam, amman ya nuna kamar bai ji abin da ka ce ba.”

     Malam Belɗo ya ce masa “Maza ɗebo tsummokaranka nace ka taho Malamin da na ce zan haɗaka da shi zai koma binni yanzu.”

     Alu yayi narai-narai da ido kamar zai fasa kuka, ya kai kallosa ga mahaifiyarsa wacce ta Kauda kanta gefe sannan ya maida dubansa ga mahaifinsa yana fad’in Baffa sai na kara girma, sai inna ta haihu.”

     Mamaki ya bayyana akam fuskar Malam Belɗo, Lanto kuwa tafa hannu ta kama yi tana sallallami “Allah buwayi, kaji fa Malam, ai daman na gaya maka duk sanda matar nan ta sanya ɗan nan a cikin ɗaki huɗubar banza take masa kala-kala, banda haka yaya wannan karamin yaron zai san girma da wata haihuwa, ko idan ta haihun uwar me zai iya yi? 

    Hawaye ya fara kokarin zubowa daga idon sumaye, amman tayi kokarin sunkuyar da kanta k’asa tana kokarin haɗiye damuwarta, Mal. Belɗo ya maida dubansa ga Sumaye. 

    “Sumaye kina jin abin da Maisango ya faɗi ko? Yara nawa ya tashi ya tarar a gidan irinsa maza masu shekarunsa, dukkan yaran lanto maza suna can karatu ba kuma ta ta6a daga kai akan hakan ba, kosu ba ‘ya’ya bane sai naki?

   Dama zata iya faɗi data gaya masa Lanto tana da yaran dasuke taimaka mata suke maye mata gurbin sauran, amman ita bata da kowa sai Alu, shine abin da take kallo taji daɗi a rayuwarta, shine ya tabbatar mata da haihuwar rayayyan d’a ba, ya maida mata shi gaskiya, amman ba zata iya sanar da shi hakan ba, don haka cikin rawar murya tace “Ayi hak’uri Malam.”

    Lamto ta ta6e baki yayin da shi kuma yaji tausayin ta ya fara shiga ransa, sumaye ta kalli inda Alu yake tana ƙoƙarin danne fishin ta cikin tsawa ta fara yi masa magana muryar ta na rawa. 

   “Maisaugo ba ka ji abin da Baffan ka ke fad’i ba ne, maza ɗebo kayan ka, karatu shine abu mai muhimmanci a rayuwarka fiye da komai.”

    Alu bai motsa daga inda yake ba sai hawaye da suka fara wanke idon sa, k’aramin yaro ne amman kwakwalwar sa tana aiki irin ma yaron da ya kai shekaru shabiyar, Mal. Belɗo ya cika da tsananin mamaki, domin Alu bai ta6a yi masa musu ba balle har ya ce ga abin da yake so ayi yace a’a ba sai yau, hakan ya sanyaya jikin sa ya kasa ce masa komai. 

    Lanto ta kula da yanayin da malam din ya shiga kishi ya bayyana akan fuskarta har ta kasa boyewa tace Malam ko shi ɗin barin sa zaka yi kasancewar dan mai ne? 

    Mal. Belɗo ya dawo hayyacin sa cikin gaggawa yace “Shi d’in banza ai dolensa ya tafi neman ilimi, yan’uwansa duk suna ban, daga wanda yayi shekaru biyar sai wanda yayi shekaru bakwai, bazan fasa ko sauya ra’ayina akan sa ba sam.” Ya maida dubansa ga sumaye da kanta ke durkushe cikin zafin rai yana cigaba da fad’in maza tashi had’o min tsummokar sa sumaye. 

    Ba bu musu ko jayayya sumaye ta mik’e cikin tsananin sauri kamar babu komai jikinta, domin babu abin da take gudu bayan sa6a umarnin mijinta, tayi hanyar daki cikin gaggawa, mla. Beld’o yabi ta da kallo can k’asan ransa tausayin ta da sautin kukam Alu na so yin tasiri akansa, amman bai da halin janye k’udirinsa har abada, don haka ya kasa furta komai. Lanto ta dokawa Alu tsawa kai tafi can rufe mana baki, zaman gida bana maza bane sai mata, ka fita kaga duniya, duniya ta ganga yaro.” Alu ya kuma fashewa da kuka cikin damuwa yana kad’a kai “ban son tafiya inna! Ban sn barin innata cikin halin da take! Babu wanda zai d’ebo mata ruwa a rafi, babu wanda zai mata itace inna. Lanto ta kara tafa hannu tana sallalami kaji fa malam, ai daga jin kalaman yaron nan d’ora shi akayi akan su,duk yawan yaran gidan na a rasa wanda zai yi dukkan abin da yake fad’a sai shi? Wato hakan na nuna kai ne haife bata k’aunar kowa ya taimaka mata idan ba kai ba ko? Ta dinga surutai da soki burutsunta kala-kala, sai dai abin daya bata mamaki, dukkan fad’a da hargowar maigidan nasu yayi sanyi lakwas yau kamar bai son tafiyar alu din, hakan ke k’ara kona mata rai, dukkan abin da ya shafi lamarin sumaye sai ya nuna banbanci. Sumaye data shge cikin d’akin tayi tsaye cak domin k’afar ta rik’e ta kasa ko da motsawa, jikinta yana rawa hawaye ya cika idanuwanta, daga inda take tana jiyo shshekar kukan alu da kuma hargowar lanto da surutun ta. “Haba malam sai kace ba kai ba, ace kana bayar da umarni a gidan ka mace na k’ok’arin takewa, minti nawa ta kwashe cikin d’in babu labarin ta, da nice da tini ka fara kurarin na raina ka. Mal. Beld’o ya kalli lanto a fusace cikin taraddadin abin da yake shirin aikatawa, a k’asan ransa ya san abinda ta fad’i gaskiya ne amman yana k’ok’arin nuna mata ba haka bane ba,

Cikin zafin rai yace haba lanto yaya kike abukamar na marasa tinani ne, nafi kowa sanin halin sumaye bata musu belle ja da abinda na fad’i, kina kallo ina bata umarni ta shige aikata abin na sanya ta, lokacin data d’auka bata fito ba bazai zama abinda za’a yanke mata hukunci da shi ba, matar nan juna biyu gareta dole sai tabi a sannu. Tamkar ya watsawa lanto ruwan zafi cikin ranta, har taji dama ta sani bata ambaci kalmar ba, domin babu abin da ta tsana bayan ganin wani abu ko misk’ala zarratin da zai nuna kulawa ko so da kaunar sumaye ga mijinta, ta kama haki cikin baci rai ta kasa furta komai. A 6angaren sumaye maganar mijinta ta bata kwarin gwiwar aiwatar da abin da ya sanya ta duk da idaniyar ta na zubda hawaye, zuciyar ta na k’una na rabuwa da tilon d’an ta, amman bata yadda shaid’an da makircin abokiyar zamanta yayi tasiri akanta ba, cikin sauri ta janyo wani tsohon buhu da take ajiye ganyen kukar miya ta zazzage ganyen kukar a k’asa ta fara tsunta kayan alu tama watsasu cikin buho, ta d’ebi abinda

Ta d’ib kana tayi waje da azama, tana fitowa tayi ido hudu da Alu wanda ya fara ja da baya ganin ta fito rike da kayan sa cikin buhu, ya k’ara fashewa da kuka yana fad’in. “Ni ba zani ba baffa! Don allah ka barni, nibani son zuwa baffa! Sumaye ta d’uke kanta daga 6angaran da Alu yake tayi gurin mal. Beld’o kai tsaye ta durk’usa cikin girmamawa ta mik’a masa k’ullin kayan. Tun da ta fito lanto ke kallon ta da 6acin rai kamar ta rufe ta da duka, amman ta gaza furta komai, fuskar malam ta fad’ad’a da farin ciki ya mika hannu ya amshi buhun yana fad’in. Kin gani ko? Na sanar dake baza ta sa6a umarni na ba, nine mijin sumaye ninasan halin ta.” Lanto tayi tsaki gami da yin hanyar d’kin ta da gaggawa, sumaye ta yunk’ura ta mike da kyar, lokacin da malam yayi kan Alu wanda keci gaba da kuka yana ja da baya. “Kayi hak’uri baffa, ka barni gurin Innata don allah! Kalaman da Alu ke furtawa kenan cikin tsananin kuka yana kuma ci gaba da ja da baya. Wani abu mai ciwo ya soki zuciyar mal. Beldo har yaji dama ya sani

Bai sanar da tafiyar alu gaban lanto ba, tabbas da ya janye ta ya sauya lokaci ba wannan ba, amman ina babu wata dabara yanzu dole sai ya tafi, ya nufi yaron dake ja da baya yana fad’in. Haba maisango na, ilimi abin nema ne, dukkan ‘yan uwan ka suna can neman sa, shi na ke fatan ka samo, zaka dawo ka zauna da inna ka gaji da ganin ta a lokacin da ka zama abin alfahari watarana.” Alu ya ci gaba daja da baya yana kallon innar sa yana kada kai, sumaye tana kallon shi hawaye na k’ok’arin zubo mata tana karewa, har zuwa sanda hawaye ya su6uce ya zubo, wannan shine abu na karshe da alu ya gani ga mahaifiyar sa wanda ya bashi damar juyawa yayi hanyar fita da gudu, mal. Beld’o ya bishi da sauri yana kwala masa kira. “Alu? Mai sango! Yaron bai juyo ba yayi waje da gudu, mal. Beld’o ya rufa masa baya cikin gaggawa, sumaye taja baya cikin rawar jiki ta jingina da katangar gidan ta kasa tana nish sama-sama, shi ke nan ta shiga uku, an raba ta da abinda ke sanya ta farin ciki, wannan itace ranar da take kokawa kanta darayuwarta, mai ya sanya al’umar su suka zabi raba uwa da d’an tane, mai ya sanya ba’a tambayar ra’ayin mahaifiya akan komai, shin itab ta da hak’k’i akan d’an tane, wacce irin rayuwa ce wannan, lallai tana ji a jikin ta wannnan ce ranar rabuwar su, wannan ce ranar da aka raba ta da d’an ta tana ji a jikin ta sun rabu kenan har abada, tana jin baza ta k’ara ganin sa ba, domin tana baiwa kanta mutuwa, idan da hali ace ta mutu yafi komai dad’i a gareta yanzu, domin tana rayuwa saboda Alu ne, kasancewar bata da kowa a wannan duniya, mahaifiyar ta tana haihuwarta ta fad’i ta mutu, a gurin kakar ta ta girma ta gurin uwa nonon ta tasha tarayu, tun daga wannan lokacin mahaifinta bai k’ara sumun lafiya ba, mutane da dama sun yi zaton samun lafiyar ya dangata ga k’ara aure ne, don haka aka matsa masa har ya k’ara auran, amman bai k’ara samun lafiya ba har zuwa sanda ya rasu shima, lokacin tana da shekaru biyu a duniya, hakan ya sanya bazata d’orar da komai na gatan iyaye ba, sai dai ta tashi abar k’auna gurin

Kakar ta, ta jiyar da ita dukkan dad’i, kwatsam tana shekarun ‘yan matancin ta shabiyu itama kakar ta ta rasu, wannan ya fidda mata k’aunar komai na duniya, domin rik’on ta ya koma hannun kawun ta wanda matarsa ta kasance mara imani da tausayawa, hakan ya sanya da malam beld’o ya fito neman auran ta bata nuna k’in amincewa ba, domin tasan hakan ne gatan ta, duk da mutane da dama na ganin zaman gidan kawunta yafi rayuwar gidan mal. Beld’o amman a ganin ta hakan itace mafitar rayuwarta, anyi auran ta dashi, auran da bata ta6a d’orar da jin dad’in sa ba, domin ta sha wuya a cikin sa gurin abokiyar zamanta, kai tsaye ba zata ce mal. Beld’o yana azabatar da itaba, sai dai bubu wata kulawa ko wani abun tarairaiya cikin rayuwar gidan sa, a haka taci gaba da zama tana haihuwar abinda ke mutuwa, wanda jama’a da dama ke d’ora alhakin mutuwar ‘ya’yan nata akan abokiyar zamanta, sai dai bata ta6a yadda da hakan ba, har zuwa lokacin da allah ya zaunar mata da Alu wanda dukkan fatan ta da rayuwarta dogara akan sa, kuma yau gashi an raba su, tana ji ajikin ta irin rayuwar datayi ta maraici irinta d’anta ma zai yi. Lanto ta lek’o daga cikin d’akin ta, ta rik’e ha6a tana kallon sumaye wacce ke haki kamar zata sume a tsaye tana tana fad’in lkon allah? Wato idan kana raye zaka ga abubuwan mamaki, d’an guda daya tal da aka d’auka shine kike neman halaka rayuwar ki, allah yabani hakuri ni da aka kwashi ‘ya’ya na har uku ban san inda suke ba tsahon shekaru, ban kuma ta6a damuwa ba saike mai guda daya, lallai kina da aiki. Tayi hanyar girken akuyoyi tana cigaba da dariya da shewa farin ciki ya cika zuciyar ta. Sumaye tabi ta da kallo, tana son tafiya amman k’arfarta ta kasa motsawa daga gurin, ta fara karanto addu’ar dake karantawa ko da yaushe wato fatiha da kulhuwallahu bata san adadin da takaranta ba, sai ta fara jin sauki da sanyi cikin ran ta k’afar tata ta saki a hankali ta yunk’uri ta nufi cikin dakin ta, amman har lokacin cikin ta da marar ta a d’aure suke tamau. Abin dake ranta bai wuce yaya aka kare da ALU da

 Baffan sa ba, tasan halin mal. Beld’o babu abin da zai sanya ya sauya nufin sa, mutum ne shi mai magana daya, dukkan abin da zai faru bai girgiza shi kwata-kwata, a ranta taci gaba da yin addu’a ga kanta da kuma d’anta. A can waje tun da Alu ya zuba da gudu mal. Beld’o ya rufa masa baya, sai dai yana fita yaci karo da wani kato gungumen dutse ya fad’i k’asa kwance allah ya sanya bai ji mummunan ciwowa ba sai buguwar da babban yatsan k’afarsa yayi ya fara jini, mal. Beld’o ya iso gurin da gaggawa ya daga hannu a fusace ya wanka masa mari, yaron ya fashe da kuka sosai cikin fusata ya fara fad’a. “Kaga ja’irin yaro, ina binka  kana gudu. Ya k’ara daga hannu da nufin k’ara marin sa, sai dai hango ciwon dake kafarsa ya sanyayar masa da gwiwa da sauri ya kamo kafar yana fad’in. Kai maisango kaga yanda kayi wa kan ka illah ko? Ya kamo kafar yaron da tausayawa, sai ya mufi ciyayin dake zube a gurin ya sanya hanun ya fisgo su ya mutsike a hannusa ya diga ruwan akan ciwon, kamar daukewar ruwan sama sai ga jinin ya tsaya tsaf, alu har lnkacin yana ci gaba da kuka. Mal. Beld’o ya dafa kansa cikin lallashi bayan ya tsugunna a gabansa yana fad’i” daina kuka kaji maisangona, kasan ban son ganin kukan ka, wannan karatu da zaka tafi shne kawai gatan ka, idankaje can zaka gane abin dana ke son d’ora ka akai, watarana zaka zama babban mutum mai ilimin da zaka yi amfani da shi ba akan ka kad’ai ba har ga al’umma ma baki d’aya. Alu yayi shuru yana sauraran mahaifinsa, hak’ik’a maganar mahaifin sa ta shige shi, amman kuma abin dake ransa shine halin da innar sa ke ciki, don haka ya kasa hak’uri har sai da ya furta. “Baffa innata fa? Waye zai dinga d’ebo mata ruwa a rafi? Waye zai dinga iza mata wuta, waye zai dinga yo mata ice? Mamaki da tausayin yaron ya shige shi, wato duk gudu da yake yi shi ba yana yin don za’a dauke sg daga garin su zua wani gari bane kamar yanda sauran yara keyi, shi yana gudune saboda halin da zai bar mahaifiyar sa achki, ya k’ara dafa kan shi. Kar ka damu dukkan abinda kake mata zan sanya salame ta

Dinga yi mata kaji ko? Alu ya kurawa mahaifinsa ido kamar yana shakku akan abin da ya fad’a, mal. Beld’o yaci gaba da magana “kayi karatun da zan yi alfahari da kai maisango na, innarka tana nan a hannun ubangiji babu abin da zai same ta. Amman baffa kana ganin Salame zata d’ebowa Innata ruwa? Alu ya tambaya cikin fargaba. “Me zai hana ta zuwa Alu? Ai ni zan sanya ta, idan kuma batyi ba kasan bana wasa gurin bugun mutun ko? Alu ya d’ga kai alamar eh, mal. Beld’o yayi murmushi gami da fad’in yauwa yarona ta shi mu tafi maza kada mai tafiya daku ya tafi ya barka. Ya kama hannun yaron, Alu ya mike yana digisa k’afar suka nufi can wajan gidan mai gari, akwai yara da yawa wad’an daza’a tafi dasu can binni akwai na garin su da wanda aka kawo da mak’otan garin da kuma k’auyukan dake nesa da garin, wasu daga ciki yaraN suna cikin murna da jin dad’i wasu kuma suna kuka kamar Alu, mal. Beld’o ya isa gurin mai gari ya zauna, bayayan ya zaunar da Alu cikin sauran yaran, yaran da suka kasance abokan Alu suka fara fara tsokanar shi ganin yana kuka, kasancewar yana da zuciya ya sanya bai kula su ba, domin innar shi ta hana shi fad’a, saboda idan ya fara fad’a bai iya iya hak’uri sai ya jiwa mutum ciwo hakan ya sanya innarsa ke kwabar sa dayi masa nasiha akan yin fad’an shi ya sanya yakan daure kafin ya kula mutum suyi fad’a. 

Also Read:

Da Ban San Shi Ba Book 1 Chapter 1

Kusan awanni uku aka  kwashe kafin a kammala hada yaran, sannan aka fara kokarin tafiya dasu, mal. Beld’o ya kamo hannun alu ya jashi gefe ya dafa kanshi yana magana cikin kwantar da hankali. “Kiyi karatu da yawa kaji Alu Maisango, kar ka yadda ka bi yaran banza kaji ko? Alu ya daga kai alamar to, amman har lokacin yana ajiyar zuciya, yaran suka yi bankwana da iyayan su da dangin su suka d’auki hanyar tafiya, domin sai sun yi tafiya zuwa babban kauyen dake bakin hanya wacce tafiyace ta kusan kilomita biyar sannan zasu sami dotar shanu da zata shigar dasu binni, wasu na kuka wasu na murna suka dauki hanyar tafiya. Alu yana tafe yana waigen garin su wanda shi kad’ai ya sani cikin abin da ya

Shafi rayuwarsa wato garin sam6una sai sunan baban sada innarsa, har suka kule mal. Beld’o yana daga masa hannu, yaron yana yin kuka amman irin na zuciyar nan sai ajiyar zuciyar da yake hakan ne kawai zai tabbatar maka da lallai kuka yake yi har suka bacewa ganin kowa suka nausa cikin jeji, suka dai na waigawa. Kasancewar sun saba tafiyar ya sanya ba su gajiya ba har suka iso ainihin babban garin nasu, motar amalanke tana jiransu aka watsa su cikin motar aka fara tafiya, Alu yana ta kallon garin su sai da motar ta tashi sannan ya fashe da kuka, ya had’a kai da gwiwa yana kuka, shike nan bazai k’ara ganin Innar sa ba, bai san inda za’a kai shi ba. Abokinsa Idi ya dafa shi yana kuka k’asa-k’asa shima kadaina kuka Alu, Inna tace mini acan akwai shimkafa da abubuwa masu dad’i, zamu dinga ganin talbijin irin ta gidan maigari a ko’ina, zamu dinga shan ruwan sanyi muci abinci mai dad’i, sannan tace mini sau uku suke garki acan ba irin garin muba. Dukkan bayanin da Idi yake yi bubu wanda ya shiga zuciyar Alu, domin ba abubuwan da za’a taddane a ran sa ba tinanina halin da Innar sa ke ciki ne a ransa, amman ya rage kukun ya juya ya kalli Idi yana fadin. “Idi Innar ka tace maka zamu k’ara sumun wata Innar acan ne? Idi yayi shiru da rashin sanin amsar da zai baiwa abokin nasa, tabbas ko sun sami komai ba zasu sami uwa acan ba, don haka ya kad’a kai alamar a’a, Alu ya goge idon sa yana ci gaba da magana. Saboda bazan ga inna ta acan ba shi ya sanya nake kuka idi. Jikin idi yayi sanya ya jingina da karfen motar, Alu ya waiga ya k’urawa garin su ido wanda suke k’ara yin nisa, tun suna iya shaida garuwaruwan dake mak’ota dana su saboda zuwa biki ko aiken da ake musu har suka dai na shaida komai domin sun shiga cikin tskiyar daji, wasu sun yi bacci, wasu kuma idon su biyu, Alu yana daga cikin wadan da basu ko rufe idon su ba, domin yana ganin da ya rufe idon sa zai ganshi a wani gari, tinanin halin da Innar sa ke ciki a yanzu shine abin dake damunsa, Allah ya sanya ma ya d’ebo mata ruwa da safe a rafi ya cika mata

Dukkan mazubin ruwanta, sannan yayi mata kara wanda ta tura shi k’ark’ashin gadon ta, yayi murmushi da jin dadi cikin ransa, ko da salame beta debo mata ruwa ba zata kwana biyu tana amfani da wanda ya d’ebo mata…

 

Back to top button