Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 16 Book 2 Complete Novel

 

Jeje bude baki yayi yana kallon Hannah, dan yarasa meze ce mata, Hannah takuma kallon Jeje, ta nunashi da key din motarta

“wannan itace magana ta karshe dazanyi da kai, nidaku dan halak ka fasa, kome zefaru sena mallaki Jalal, indai na amsa sunana Hannah” daga nan ta dauki Jakarta tai gaba abunta. Dukan tabur jeje yayi da karfi, yasa kafa yai ball da tebur din “Why, ya haka ya za a yi abubuwa su lalacemin haka, akwai matsala muddin Hannah tace zata aikata abunda ta fada. Mukullin tasa motar ya dauka shima ya bar gurin. 

Jalal yana gama cin Abincin sa ya mike yana hutawa, anata kiransa ana masa bangajiya, wayarsa yadakko, IG yashiga yana shiga yaci karo da hotunan birthday dinsa, abunda ya bashi mamaki, hotunan shida Jalila yafi yawa, shi akafi yadawa, fitowa yayi yakoma what’s app still status din mutane hotunan ne suke yawo, shiru yayi ya kurawa hotunan ido, wani hotonsu ya tsaya akai yana kallo, yanda ta dan zumbura baki tana kallonsa, shikuma yana dariya, tsaki yayi “kalleta dan Allah se tsabar iya rashin kunya, shi mamaki yake yadda akayi tai mugun rainashi sam bata shakkarsa, kaman ba yarinyar dasuka dinga wasa da ita a zanin goyo ba, yan uwan sa mazama tsoronsa sukeji amma banda wannaan yarinyar, zuwa wani dan lokaci ya kashe wayar, ze ajiye kiran Jeje ya shigo wayarsa, kaman kar ya daga, seda ta kusa katsewa sannan ya daga

“hey man kana inane?” 

“me zakayi min kake nemana?” 

“ina wajene ina jiranka” “wajen ina kenan?” “kofar gidanku mana” “ok ina zuwa” Jalal ya duba yaga Jawwad yana toilet dan haka kawai ya fito, yana fita yaga motar Jeje a kofar gidansu, karasawa yayi ya tsaya bece komai ba, jeje ya fito yana wata shu’umar dariya da wannan katuwar muryartasa yace “man of the day, our celebrity yane?” 

“Normal, mukarasa cikin gida” Jalal ya fada a takaice, yaiwa Jeje jagora zuwa part dinsa, suna zuwa Jeje yanemi guri ya zauna, Jalal yaje fridge ya dakko wa Jeje ruwa da lemo, ya hada da giya ya aje masa, Jeje ya dan kalli Jalal yace “J man, ya gajiyar jiya” 

“gajiya tabi lafiya” “good wai ya akayi ka bar gurin nan jiya, ban san ka tafi ba?” Jalal ya danyi shiru yana tunani sannan yace “gaskiya i can’t recall, Hannah tabani wayne jiya, bansan meyakuma faruwa ba, ban san ya akayi na dawo gidaba, na tambayi Jawwad ma yace min ba shi yakawoni gida ba, i think ansamun wani abu a giyar nan. Dan zare ido Jeje yayi, dayaji statement din Jalal na karshe amma ya maze yace “anyway but J man, akwai wata cute baby da pictures dinku suke yawo social media, tagama haduwa babyn nan, nifa tayimin wallahi, inaso insata a harka” 

“wace yarinya kenan?” Jalal ya tambayeshi a takaice, Jeje ya zaro wayarsa ya nunawa Jalal hoton Jalila, tareda fadin “wallahi Jalal komai yaji ajikin yarinyar nan, zanso tayi joining insata a layi, zata kawo harka, maganar tama kawai abar sha’awa ce komai nata na birgewa ne, gaskiya ta hadu” 

Wani mugun hade rai Jalal yayi, ya kalli Jeje a fusace yace “Are you out of your sense, wai kai bunsurun inane da duk inda kaga mace jikinka har rawa yake, let me warn you, Wallahi3 na rantse maka, muddin wani abu yasameta sena daureka, kasan wacece? Kanwar Jawwad ce, yarinyar da yakeso, danme zaka dinga wannan kazamin maganar akanta, karka kuma fadin wani magana akanta kota arziki kota sharri akanta, wannan yarinyar ba irin jakan matan dazaka iya nasarar lalatawa bane, kaji na gaya maka take your leave now “ya nunawa Jeje hanyar fita, wani irin kallo Jeje yaiwa Jalal, amma seya daidaita nutsuwarsa yace” is ok j man bansan abunda ke tsakaninku bane, ashe kanwar kace, na dena bazan kuma ba kayi hakuri “

” Naji amma for now tashi kabani guri, raina yagama baci, tashi ka tafi” ba musu jeje ya mike ya fita. 

Da Jawwad yafito yaga Jalal ya tafi, kawai se shima yafito, yaga Jalila cikin flours dinta tana gyarawa, ya fuskanci tanason furanni, a hankali ya karasa inda take ya zauna, ta waigo ta kalleshi, tai murmushi “Allah yatemaki yayana na kaina” Jawwad yai murmushi yace “Ameen yar baby, ya meyasa kikeson furanni ne?” “nima ban saniba, kawai dai ina sonsu ne, na gidanmu a kaduna nasan sunyi missing dina, in bana nan ummi ke kularmun dasu” sekuma tai shiru idonta yacika da kwalla, Jawwad ya nisa sannan yace “am sorry, nagane kidena damuwa kinji kicigaba da addu a muna kan nemanta har yanzu” gyada masa kai tayi tareda murmushi, yace “Yawwa babyn Yayanta” yasa hannu a aljihunsa ya dakko chocolate yabata, hannu tasa ta karba tana murmushi, tareda kokarin maida hawayenta, tai murmushi tace “Nagode Ustaz” “yaukuma nine ustaz” “Eh mana” sukayi dariya gaba daya, Jawwad yace “yawwa baby, nace wai me yafarune jiya? Ya akayi manu ya kawo Jalal gida, dazu yake tambayata ya akayi ya dawo gida” Jalila tai ajiyar zuciya tace “Hannah ce ta kaishi wani guri suka bashi wani abu, naga yafita hayyacinsa, tasaka wani yaimata gadinsa ta tafi tana waya, kawai naji ban yadda da itaba, shine na dauke hankalin wanda tasa gadinsa nasa Manu ya daukeshi ya kaishi gida” shiru Jawwad yai na dan lokaci sannan yace “thank you for your contribution my dear, hakika kintemake shi, maybe akwai abunda sukeson yi masa, narasa meyasa Jalal yakasa gane basa kaunarsa, anyway mungode sosai Baby Amma ya akayi kikasan Hannah”? 

“A a, ban santa ba agurin naji ana fadar sunanta, Yaya Jawwad no need kaimin godiya fa, manta kawai, amma akwai wani abu da nagani yabani mamaki” 

“Mekika gani?” 

“Wannan mutumin na rannan, da ya dinga zagin Jalal, dan kun gaisa da dansa, shima fa yaje gurin nan, abunda yakara bani mamaki shida wannan Jejen naga suna magana, shiyasa nace maka shima yana kama da yan shaye2” 

“Anya kuwa shi kika gani, maybe kamace kawai, bana zaton baban Faruk a irin wannan gurin, saboda yanada tsatstsauran ra’ayi, kece dai kike masa kallon ba mutumin kirki ba ” 

“Yaya kenan shikenan tunda baka yadda ba, magariba tayi bari inje inyi salla” 

“to shikenan, dan Allah anjima ki dafo mana wannan tea din naki me dadi” 

“Hmmm yayana kwadayayye kawai” “ke kika koyamin kwadayin ai” tai murmushi ta mike ta tafi cikin gida, Jawwad kuma ya fita masallaci. 

Tunda Jeje yafita yake zancen zuci “lallai tunda Jalal yaketa masifa akan yarinyar nan to ba karamin matsayi take dashi a gurinsu ba, lallai dama tazomin akan wannan fitsararriyar yarinyar zan jefi tsuntsu biyu da dutse daya” Jeje ya kyalkyale da dariya, sekuma ya hade rai daya tuno da maganganun Hannah, dakuma abunda Jalila ta gaya masa ranar birthday din Jalal, “muje zuwa yan mata mu daku zanga wazeyi nasara” 

Bayan sallar isha’i Jawwad yasa Jalal a gaba yayi salla suka zauna suna hira, Jalal yace “Jawwad ina jin bacci, bari in tafi gida” “No karka tafi yanzu ka tsaya baby zata kawo mana tea, ka tsaya kasha seka tafi” “ok bari in jira, ina son sha, kasan wani abu” 

Jawwad yace “A a seka fada” “har yanzu ina mamakin me aka zubamin a giya wanda ya bugar dani haka tsawon lokaci” 

Jawwad yai ajiyar zuciya “Jalal shiyasa nake gaya maka tun ba yauba, hulda da mutane irin wannan be kamata ba, kasan wani abu? Jalila ce tasa aka dawo da kai gida, tunda kafita daga gurin nan, ni bansan meyafaru ba, bayan ka bugu tasa manu ya daukeka yakawoka gida” kallon Jawwad ya danyi, ya dan tabe baki irin he don’t care din nan, wayar Jawwad tafara ringing, ya kalli Jalal yace masa “excuse me please” ya daga wayar

“Hello My Jawwad ya kake?” 

Muryar Hanan ce, Jalal ya kafe Jawwad da ido, Jawwad yace “ina lafiya Hanan, ya mutan gidan” 

“Nifa fushi nake, ashe Jalal yayi birthday bako gayyata ko my Jawwad” 

“A a Hanan ba haka bane, Jalila ce ta gayamiki ko?” “A a, wannan ce zata gayamin, bata gayamin ba, hotuna nagani suna yawo a social media, kunyi kyau bama hotonta da Jalal, best couples of the year, kyanta ace wedding pictures ne” 

Ba Jawwad ba hatta Jalal dayake gefe yana jinsu seda gabansa ya fadi, amma yarinyar nan ta cuceshi, tarasa dawa zata hadashi se wannan fitsararriyar yarinyar Allah ya kiyaye, 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Hanan tace “My Jawwad ya kayi shiru ne” “bakomai Hanan, ni banga hotuna nan ba” “bari in turomaka, zaka gani sunyi kyau, idan birthday na yazo, irinsu zamuyi” Jalal yawani hade rai, Jawwad ya kashe wayar, ya dafe kai “wallahi wannan yarinyar tafi Jalila rigima” Jalal ya dan kalleshi, wa din? Kafadi son ranka dai” “ba son rai bane Jalal, hanan tafi baby rigima, banason Jalila ta gane, zataji ba dadi” dariya Jalal yayi “ganewa ta nawa sedai kar akuma, ai gara Hanan din akan wannan fitsararriyar, gara ta gane din” wani irin kallo Jawwad yai masa, ya cigaba da latsa wayarsa, hotunan da Hanan ta turo masa yake gani, wanda mafi yawa Jalila ce a jiki da Jalal, nan take yaji wani abu yazo ya tsaya masa a rai, Hanan ta turomasa “ya ka gansu, sunyi kyau sosai, sun kuma dace da juna” da sauri Jawwad ya rufe data, ya kashe wayar gaba daya yayi shiru, shikuma Jalal ya nuna ko a jikinsa, kuma yasan shima Jawwad din kishi yake, dan yasan zeji ba dadi, Jalal yai kaman besan wasu hotuna bane, ba a dadeba sega baby Jalila ta kawo musu tea, amma taga Jawwad wani iri, kaman yana cikin damuwa, ta dan kura masa ido tace

“Yaya lafiya dai, yanaganka a haka, kowane abu ne yafaru” girgiza mata kai yayi “Bakomai Jalila” gyda kai tayi, ta tashi ta tafi, Jalal ya zauna ya sha tea dinsa yayinda wanda aka hada tea din dominsa yakasa sha. Bayan Jalal yagama, ya mike abunsa ya tafi gida. Daren ranar da kyar Jawwad yayi bacci, yana matukar son Jalila, meyasa hanan takeson rikita komai ne tana kokarin hada Jalila da Jalal itakuma ta maye gurbin Jalila, sam hakan ba me yuwuwa bane haka ya kwana wannan tunanin. Bangaren Jalila kuma, ta takura kwakwalwarta gun tunanin meye alakar, baban faruk da Jeje, idan har shi yana hulda da mutumin banza kaman Jeje, to mezesa yayiwa Jalal wannan muguwar tsanar haka? Waima yanzu a gurin wa zataji waye Jalal, waze gayamata tarihinsa, Jawwad sam yaki gayamata,sannan meye burin Ilham akansa, meyasa hanna ta bugar dashi haka ranar birthday dinsa? Tarasa me bata amsar wannan tulin tambayoyin, ji tayi kanta yana neman yafara ciwo, dan haka ta hakura da tunanin tayi bacci. 

Ya zuba mata ido yana ta kallonta tana shiryawa a gaban mudubi, dan waigowa tayi, ta kalleshi tai masa murmushi “ka dena kallona” “ta yaya zan iya dena kallon ki, kowa yana son abu me kyau, ni kekadaice abu me kyan da idanuna ke iya gani, kinga babu batun dena kallonki” murmushi takumayi masa “hmmm my cwt kenan, to nagama yi maka kwalliyar zo ka daukeni” ba musu ya mike yazo gaban mirror ya tsaya ta miko masa hannu, ya dauketa kaman wata yar baby, ta makalkaleshi tana dariya, ya nufi kan gado da ita, yayinda take kallonsa tana murmushi. 

A hankali JALAL ya bude idonsa, yana kallon dakinsa, idonsa ya sauka akan agogo, karfe takwas dai2, se yanzu yagane mafarki yake, wani dogon tsaki yayi, ya tashi zaune “wannan wace irin masifa ce, shikenan kullum babu mafarkin wadda zeyi se wannan yarinyar, shi a yanayin dayake ganinsu ne shida ita yake bashi haushi” tsaki Jalal ya kumayi ya sakko daga kan gadon ya tafi toilet, domin yin wanka yai salla “

Karfe tara da rabi, Jalila tana ajinsu, an fara lectures, amma sam hankalinta baya kan malamin, tayi zurfi a cikin tunanin ta, gata a aji amma hankalinta yayi wani gurin, lecturer ya kalleta, cikin tsawa yace mata” Ke! Tunanin me kike haka ina lectures ” a hankali ta dago ido ta kalleshi, ta maida idonta kasa, ba tareda tace masa uffan ba,” ni kikewa wannan kallon ina miki magana, tashi tsaye, seda taja wasu seconds sannan ta mike, “bayanin me nagamayi yanzu?” ta daga ido, suka kalli juna itada malamin, ta dauke kanta tai masa shiru “wai ba magana nake miki ba” still dai shirun takumayi “ok get out from my class” ba musu balle bada hakuri ta dau jakarta, da wayarta ta nufi hanyar fita wasu suna kibashi hakuri, banza tayi musu, malamin yacigaba da mita “irin wannan sune jakan aji, irinsu ke kwasar carry over, se tsabar iskanci waisu yaran masu kudi” “tunda ka koreni kuma gashi na fita kacigaba da yimusu lectures din mana karka shiga lokacin su” tsit ajin yayi ana kallonta, tai ficewarta abunta” mamaki ne yacika daliban, dama tana magana haka, amma Allah yayi mata baiwar murya me dadi, sedai ana tsoron lecturer saboda masifaffe ne, da kyar in bata jawa kanta carry over ba a gurinsa, dan masifaffe ne gashi baya uzuri, yan ajin suka fara gulma, ji yadda take magana da izza, lallai wannan muguwar yar rainin hankali ce, itakam tana fita tasamu guri ta zauna ta cigaba da tunaninta

Siyama ce tafado mata a rai, kwana biyu basuyi waya ba, dan haka ta dakko wayarta ta kirata, bugu biyu Siyama ta dauka

“hajiya Jalila manyan kasa talaka najinku dama” 

Jalila tai murmushi “ke banason wulakanci fa, yakike yasu umma?” “duk muna lpy Alhamdilillah, yauba lectures ne naga kin kirani yanzu” “akwai lectures koroni akayi” Siyama tace “hali zanen dutse, har yanzu biki canza ba ko? To university ba secondary school bace, ko islamiyya, Allah sarki malam babba yanata tambayata ke” 

“Allah sarki malam, kice masa ina lafiya, ke ba ruwana da wata university, wani hakuri zan bashi ya riga ya koreni, hada wani wai irinmu ne dakikai” “hnm adinga hakuri dai sisy, nace ya mutuminki kuwa?

” waye mutumina kuma? ” 

” Jalal mana” siyama tabata amsa

Tsaki Jalila tayi “ta yaya yazama mutumina?” “knfi kowa sani, nace yafara shiryuwa kuwa? ” “tab shiriya se ta Allah, dan banga alamaba, abun se addu a, niba wannan ba ma kinsan wani abu” “a a sekin fada” “Siyama hanan ce takeson Yaya Jawwad dina, kuma fa da gaske take” “to meye a ciki, ai abun farincikine” “haba Siyama ya kike fadin haka, da wanine ba yaya Jawwad ba, se in hakura in barmata, amman kaman baki san abunda ke tsakanina da yaya Jawwad ba” 

“da kenan abunda ke tsakaninki da Yaya Jawwad, amma yanzu naga kin canza sheka zuwa Jalal” “mtseww, kinfiye wasa Siyama, wannan bugaggen uban me zanyi dashi”

“karki rainamin hankali mana, in bahakaba me yakaiki gurin birthday dinsa kukayi hotuna, hada kallon soyayya” zare ido Jalila tayi “nidin, nasan naje gurin birthday dinsa, amma wani irin kallon soyayya” siyama tai dariya tace “kai Jalila ansan madarar gogewa mutane hadda, to a status din mutane na ganku” 

lecturer da yakori Jalila ne ya taho, da wasu dalibai su hudu suna binsa, Jalila tace “hmm ke se anjima, zamuyi waya” ta kashe wayarta, lecturer yazo saitin Jalila ya tsaya ya kalli daliban “kun ganiko, na koreta daga aji, memakon tabani hakuri tazo nan tayi zamanta tana waya da samari, se karshen semester yazo tasamu carry over ace bani da mutunci” ita dai shiru tayi masa, yagama masifarsa yai gaba, wani daga cikin daliban ya dawo da baya yace” yan mata meyasa baki bashi hakuri ba ai ba a haka tunda gaba yake dake seki lallaba a rabu lafiya ” 

“akan me zan bashi hakuri, yayi kama da wanda za abawa hakuri ya hakura ne? Kuma fa dagani hakurin kuke bashi kowata alfarma kuke nema a gurinsa amma ga yadda yake wani shareku” 

“eh to kinsan Jami’ a se hakuri, kowane lecturer da irinsa, kuma ko dan kar ya kadake, ai da kin bashi hakuri ” Jalila ta kalleshi tace

” Yaya na nagode da shawararka amma bazan bashi hakuri ba, kuma koda ban taba zama a lectures dinsa ba banida test banida assignment indai zan shiga exams dinsa sena ci” tana gama fadin haka ta mike, tai tafiyarta. Ji tayi yau makarantar ta isheta dan haka ta kira manu, tace yazo ya maida ita gida , befi minti shabiyar ba sega manu yazo, ya dauketa don tafiya gida, Jalila tace “Manu wai yana ganka haka, kaman mara lafiya” manu yace “ke dai bari Mamace ba lafiya an rubuta mata maganin dubu hudu, kuma ni bani dako sisi, gashi ba adade da biyana albashi ba” 

“Allah sarki amma meyasa baka tambayi Abba ba”? “haba Jalila, idan na tambayeshi ai ban kyauta ba, kullum cinkin yimin hidima yake, sedai inkina dashi ki aramin” “Bakomai akwai kudi a account dina muje banki, se mu tsaya in ciro in baka” “kai godiya nake uwar dakina, Allah yasa kifi haka, Allah yabaki miji nagari, ya jikan magabata, Allah ya… 

” Ameen nagode, godiyar ta isa haka, yi sauri muje”suna zuwa banki Jalila ta sauka ba layi sosai, dan haka bata wani dade ba ta ciro kudin ta nufo hanyar fita taji ana fadin

” Yan mata adon gari, in baku babu gari, inkunyi yawa gari ya baci, amma kyawawa irinki dazasu cika garin nan, dayakara kawatuwa, barka da wannan lokaci” daga kai tai ta kall

i me maganar, koda tai tozali dame maganar, take gabanta ya fadi. 

A hankali ta daga idonta, tasa a cikin nasa bata manta fuskarba dukda gani biyu ta taba yimasa, baban faruk ne, bako shakka shine, wani shu’umin murmushi yayi mata irin nasu na yan duniya “ko baki gane ni bane”? wani kallon rainin hankali tayi masa” sannan tace “dukda kasancewar kwakwalwata tana rike, tareda tuno abubuwa masu mahimmanci da suka shafeni ne, amma hakan besa na manta wannan fuskar ba” 

“Kenan nima inada mahimmanci a gurinki tunda har kika tunoni? ” “sosai makuwa kanada mahimmanci, shiyasa na iya tunaka” wani murmushi ya kumayi “Amma naji dadin zama daya daga cikin masu mahimmanci a gurin wannan kyakyawar halittar, amma meyasa nazama me mahimmanci a gurinki” Jalila a zuciyarta tace saboda ka shigo cikin suspect dina amma a zahiri tace

“saboda kasancewar ka uba nagari, me kokarin kare mutuncin dansa daga hulda da mutanen dabana kwarai ba” “kinji haushin abunda nayiwa Jalal kenan, amma inkika duba ya cancanci hakan, duba da yanayin wani irin mutum neshi” Jalila ta dan kuramasa ido, kai da ganin mutumin nan kaga rikakken dan duniya, tsabar iya barikine yasashi yake acting kaman mutumin kirki, “excuse me please komai nawa a ka’ida nakeyinsa ina da abubuwan yi yanzu se anjima” yai saurin dakatar da ita ta hanyar cewa “yi hakuri dan tsaya mana dan Allah, ina so mudinga haduwa muna gaisawa ne, in bazaki damuba ga complementary card dina seki kirani, dakuma adress dina, mutane na musamman nake bawa wannan adress din” hannu tasa ta karba ta kalli katin ta juyashi, ta dan kalleshi na wasu seconds, tsaf ta haddace lambarsa da adress din jiki, sakin katin tayi a kasa tai masa wani kallo da yakasa gane me take nufi, kawai ta juya tai tafiyarta, tsayawa yayi ya zuba mata ido, “gaskiya wannan yarinyar yar rainin hankali ce, amma kota halin yaya, seya gane wacece din Jalal, kuma se yayi yadda yakeso da ita

Itakam tana fitowa ta kalli manu tace ” yi hakuri manu na dan dade, muje nagama”ta shiga mota suka tafi, ta dakko kudin tabawa manu tace gashi nan, aiwa maman sannu, kuma ita kyauta ta bashi ba rance ba” manu kaman ya yi kuka dan murna se godiya yake mata. 

Jalila na zuwa gida, ta tarar gidan ba kowa dan haka ta tafi dakinsu ta haye gado ta sha baccinta, alhalin school ana can ana lectures, se bayan azahar ta tashi, tana tashi da baban faruk ta tashi a ranta, ras take kuma ganin katin daya bata a idonta,  kabiru Idris, shine sunan dayake jikin katin, wayarta ta dakko tayi saving sunansa da lambar sa, da adress din dayabata a jiki, duk tayi saving a wayarta, sannan ta aje wayar a hankali, sannan tace kaima ban yadda da kai ba. Ta tashi ta tafi kitchen ta hado cornflakes dan tana jin yunwa, maimakon ta koma daki seta fito harabar gidan tai zamanta a kujerun harabar gidan, ta gefen Jawwad dayake gurin akwai bishiya, ta zauna tana shan cornflakes dinta, tanayi tana karanta qura’ani a hankali, tana dan kaďa kafarta, Jalal ne ya shigo yazo ya wuce ta gabanta bata kulashi ba be kulata ba, ya wuce part din Jawwad, yana zuwa ya dau laptop dinsa da yabari a dakin ya samu guri ya zauna ya fara video call da daddynsa

“My Man ka girma, naga hotuna na birthday kunyi kyau Allah yakaro tsawon rai da lafiya me inganci” “to Ameen amma ni fushi nake da kai” 

Daddy yai dariya “to menayi?” “Kaje ka makale a England kaki dawowa, bakayi attending birthday na ba” daddy yai murmushi “to ai nace ka daga birthday din indawo kaki, kuma abubuwa sunyimin yawa anan gakuma aikin daka sani, koka manta ne?” “ban manta ba daddy, ina fatan ana samun cigaba” “eh anasamu Alhamdilillah” “to hakan yayi kyau, yaushe zaka dawo?” 

“ina nan tafe next week Insha Allah” 

“To dan Allah ka dawo haka, inaso indinga ganinka” daddy ya dan girgiza kai “Allah sarki yarona, karka damu, nace kazo nan mu zauna tare kaki” Jalal cikin damuwa yace “Haba daddy, in taho nan in bar aminina dan uwana, kasan bazan iyaba” “Hakane Jalal, ina Dan nawane, ko yau bakwa tare?” “Yana makaranta” “that’s good, Allah ya nunamin ranar da zaka koma makaranta, yanzu ka zama mutum Jalal ina fatan Allah ya shiryamin kai inmaka aure” ya mutsa fuska yayi ya kalli system din “Aure kuma? Habaa daddy yaushe aka haifeni, ni banason gayyatowa kaina matsala, mata matsalane daddy kaima kasani” ya karashe maganar kaman zeyu kuka, 

“ABDUL JALAL, bakowace mace ce matsala ba, in har kayi dace da samun mace ta gari, kaga hotunan birthday dinka danagani, dana ganka tareda Takwararka abun yamin daďi, senaji dama matarka ce, yarinyar tanada nutsuwa ga tarbiyya ” wani mugun hade rai Jalal yayi “What matata kuma, Allah ya kiyaye, wannan kwailar, mara kunyar, na auri wannaan sedai kuzo ku tarar na kakkaryata” 

     A gigice Ilham ta tashi zaune, ganin hotunan da aka turomata ta what’s app, ba tareda tasan waye ya turoba, hotunan dasu Jalila sukayine, a kasa aka rubutamata “Yakika gansu, perfect match, ina musu fatan Alkhairi, da fatan kasancewa tare har abada, wannan itace matar data dace da Jalal bake ba” mikewa tsaye tayi akan gadon, “What ni za ayiwa wannan rashin hankalin, lallai Jalila tayi bal’in rainamin hankali. Ba tunanin komai, taja gyalenta tai waje, Mummy tana yimata magana amma taimata banza, ta fita se gidansu Jawwad, tana zuwa taga mutuniyar tata a hakimce a farfajiyar gidan, kusada part din Jawwad, a inuwa se kada kafa take, tana ciye2 hankali kwance, bazar2 Ilham ta tunkari Jalila taje kanta ta tsaya tana huci, Jalila kam kaman ba kowa a gurin, tacigaba da abunda take. Cikin masifa Ilham tace

“Wato gargadin danayi miki bakiji ba ko? Saboda kin rainamin hankali, abunda kukayi keda JALAL a gurin birthday dinsa be isheki ba ko? Hakan be miki ba seda kika hadani da wannan tsinanniyar yarinyar Hannah a gurin nan, Shine duk be miki ba sekin hada da turomin hotunanku, sau nawa ina gaya miki kifita harkata, ina tausayawa rayuwarki idan na tashi hukunta ki” Ita Jalila abun mamaki yake bata wai wace jarabar hotuna na ake damunta haka akai, ba tareda ta kalli Ilham ba tace 

” tunda kekika halicceni dole ki tausayawa hukuncin dazaki yimin mana, ki kasheni ki huta mana, seki tabattarmin dake kanwar Jalal ce, hakan se ya tabbatar da cewar bashi kadai yake shan giya ba” 

Takarasa maganar cikin ko in kula, tacigaba da watsa cornflakes dinta a baki, Ilham ta kawo iya wuya, wato Jalila takai karshe gurin raina mata hankali, idonta taf hawaye tace “Wallahi Jalila in baki fita hanyata data Jalal ba, kina daf da fadawa rijiyar sharrina, idan nasakoki gaba ruwa seya gagareki sha, Inakuma yimiki kashedi kinfara kaini bango, idan turn dina yazo bazaki ji dadi ba, ki kiyaye. 

Jalal ne yake tajin hayaniya, har ya basar ze kwanta seyaji hayaniyar yana kara yawa, dan haka ya yanke shawarar fitowa dan ganin meke faruwa, yana fitowa ya tsaya a kofar part din Jawwad yana kallon dramar da ake. 

Ilham tacigaba da cewa

“waike wace irin mayyace? Mara zuciya, meye hadinki da mune, baki da alaka ta kusa ta nesa damu why do you involve yourself in our family matters, nagaya miki nakuma gaya miki Jalal nawane, wace irin mara zuciya ce ke, kishiga hankalinki harni zaki turawa hotuna, kina kece kika dace da Jalal, zakiga wacece Ilham, na daga miki kafa amma baki ganeba, zakiga me zanyi” Kamshin turaren JALAL Jalila taji, hakan ya tabbatar mata da fitowa yayi, dan haka bata kula Ilham ba ta mike tsaye, ta taka a hankali, cikin takunta na isa, kunsan fa Ummi jinin sarauta ce dan haka akwai abun  a jinin Jalila, taje gaban Jalal ta tsaya, ta kalli Jalal sannan ta kalli Ilham, ta nuna Jalal sannan tace “Wannan shine mara zuciya, mara tarbiyya shiyakamata, kigayawa bakaken maganganu bani Jalila ba, shi duk abunda yake meyasa baki ja kunnensa ba dan kina tsoronsa, kokuwa dan abunda yake ranki wanda kike boyewa, to ni bana tsoron kowa se mahalicci na, aike karamar mara kunya ce, ni idan zanyi sedai aga na aikata, bana fada, idan akabari nafadi abunda zanyi komaj muninsa sena aikata, ke alwashi nawa kika dauka kika kasa cika ko daya, Tunda ABDUL JALAL yashiga rayuwar Yaya Jawwad to a cikin rayuwata yake, shi zaki Jawa kunne ya rabu da Jawwad, in har ya rabu da Jawwad, ba ruwana da shi, bari kiji in gaya miki za ayi dayan biyune ko Jalal ya fita daga rayuwar Jawwad kokuma kudirina….  Sekuma tai murmushi ta kalli Jalal

“Kagayawa wannan sokuwar yarinyar, niba abunda zanyi da kai, baka da abunda ze birgeni insoka bana cikin jerin banzayen matan da zasu zubar kimarsu da ajinsu akan namiji mara daraja irinka, wanda besan ciwon kansa ba balle yasan na wani, namijin da besan darajar iyayensa ba, namijin dabaya girmama alaka, dan da kanayi da zuwa yanzu ka tausayawa Jawwad kadena abunda kake, namijin dabe maida sabon Allah komai ba, baya kunyar sabawa mahaliccinsa agaban kowa, shikike tunanin ya cika siffa da kamalar dazan soshi a matsayin uban y’ay’a na, shi kike tunanin zan zubar da kimata ina hayagaga dake akansa “ta nuna Jalal sama da kasa da hannunta

” Ilham ki canza tunani, Jalila ba irin sauran matan da kike tunani bane, duk abunda kikaga inayi i have a mission, kawai ina kokarin rama Alkhairi ne da Alkhairi, karki manta da maganar dana yimiki abaya muddin kudirina yaci karo da na wani zan rusa kudirin ko uban waye dan cikar burina” ta waiga ta kalli Jalal, da idonsa tuni yayi ja, gashi ya kasa matsawa daga inda yake kaman an dasa shi, Ilham rasa bakin magana tayi, Jalila ta kalleshi a wulakance, kaikuma ka gayamata ta kiyayeni dan muddin takuma cin mutuncina saboda kai akanka zan rama, har sena gamsar da ita cewa bawata alaka me ma’ana tsakanina da kai” tana gama fadin haka takoma ta dau Cup dinta tai cikin gida ta barsu nan a tsaye. 

A hankali ya lumshe ido, ya tako a hankali ya nufi hanyar fita, Ilham tai sauri tace “Yaya Jalal dan Allah…  Daga mata hannu yayi alamar baya son jin mezata ce, yai gaba abunsa, maganganun Jalila na cigaba da tafarfasa zuciyar sa. Yana shiga gida ya nufi part dinsa ya samu guri ya zauna ya dafe kai yai shiru, Ilham ta biyo shi tazo ta zauna a kusa dashi, “Dan Allah yay Jalal kayi hakuri, nibani da laifi anan, kawai ina kokarin kare alakar dake tsakanina da kaine, meyasa bazaka yadda dani a in zama wani bangare na rayuwarka ba”? Tashi tsaye yayi ya tafi bedroom dinsa ya kulle kofa ya barta a palour. 

  Jalila koda ta koma dakinsu, kwanciyarta tayi ta dakko wayarta, tafara chatting, ta bude pages da take advertising kayan da Maama dakuma Mummy Jalal suke siyarwa, tana kawo musu customers sosai, daga gurare daban2, wasu suzo da kansu, wasu kuma a aika musu har garin da suke, gashi Jalila ma tana harkar catering ta iya girke2, wani lokacin ta kanyi snacks ta siyar, gashi duk karshen wata Abba yana basu kudi, wani lokacin dubu Ashirin zuwa talatin, inda me bukata tayi amfani dasu, Jalila bata da wata matsala se na kewar Ummi da har yanzu yake damunta, dan har yanzu takan kulle kanta tayi kuka me isarta, tana naan tanawa Ummi Addu”ar Inda rabo Allah ya kuma hadasu. 

Chats dinsu da siyama ta bude taga ta turomata hotuna tana dubawa taga hotunanta ne da Jalal, wani dogon tsaki taja yanzu watakila saboda wannan hotunan Ilham tazo kanta tanamata hauka, har zata rufe data dinta taga wani sako ya shigo, tana budewa taga an mata sallama, ta duba profile din taga basuda group in Common dame maganar, amma an rubuta unique zarah, batayi reply ba ta rufe data. Da Nana ta dawo tayi mamakin ganin Jalila a gida, Manu yagaya mata ai tun goma da rabi ya dawo da Jalila gida, Nana ta kalli Jalila

“Jalila ya akayi naganki a gida, manu yacemin tun safe kika dawo, kobaki da lafiya ne?” “lafiyata kalau zaman makarantar ne ya isheni, na dawo gida” dan zare ido Nana tayi to lectures dinfa? “

” Kinga ki manta kawai”

“Bangane in manta ba kefa al amuranki se a hankali” “A a nagaya miki gaskiya to meye na tuhumata” Nana tace “tabdijan, A haka zakiyi karatun sekin gadama zakiyi attending class in kika fadi fa” “Nana kidenamin fatan faduwa, ba abunda zekadani Insha Allah” “to Allah ya yadda amma dai banga ta yadda za aci jarrabawa a haka ba” Jalila ta dan tabe baki tace “ke kika ga haka” 

  Tunda Ilham takoma gida takewa Mummy kuka, “Mummy dan Allah ki gaggauta auramin Jalal, wallahi zuciyata daf take datayi bindiga in har ban mallakeshi ba, Mummy nagaji da wulakancin Yaya” Mummy ta dafata

“Kiyi hakuri mana Ilham kefa macece yakamata kija ajinki, kuma ni namiki alkawarin auren Jalal” “Mummy babu wani batun aji a fagen soyayya, Mummy dan Allah kiyi wani abu” 

“Haba Ilham wai meye hakane, kibari daddynsa ze dawo next week Insha Allah, in ya dawo semu san yadda za’yi, tashi ki tafi dakinki ki dena wannan kukan” mikewa Ilham tayi ta tafi dakinta, tana zuwa ta rufo kofa, sannan tai kwafa “Mummy kicigaba da jamin rai akan auren danki, koki sabaki ya aureni ko karkiyi sena aureshi, sena cika burin mahaifiya ta, sekin wulakanta kin dandani bakin cikin da uwata tayi, ko zan tafi tsirara bazan bari A banza Jalal ya auri wataba bayan ni, wasan ze fara nakusa kawo karshen wannan dramar, indai na haifu se nasa bakin cikin ABDUL JALAL ya kusa kasheki, sekuma ya aureni dan zan iya halaka duk wadda tai nufin aurensa ko wacece!!!!! 

Daga nan Ilham tai kwafa, ta nufi kan gadonta, tai shiru tana sake2 a ranta. 

Jalal kwata2 yarasa abunda yake masa dadi, meyasa Jalila tai masa wannan muguwar tsanar haka, bata da burin da yawuce taci mutuncin sa, tabbas maganganun da take gaya masa sun fara isarsa, dole ya hukunta ta hukuncin da suka hadu seta canza hanya, hukuncin da zata dandani abunda yakeji idan taci zarafinsa, gata kanwar kanwarsa, amma ko Ilham dasuke gida ďaya bata isa tayi masa haka ba, jiyayi zuciyarsa na wani irin zafi mussaman idan ya tuna yadda Jalila take kiransa da namiji mara daraja. Dole ya hukunta ta dai2 da abunda tayi masa, Ilham ma ze gamu da ita, duk yadda yaso ya manta abunda tayi masa kasawa yayi, karshe ma yaji zuciyarsa tayi masa wani irin nauyi haka yaita juyi akan gado.

  Jawwad kam be dawoba se bayan la’asar ya gaji matuka, dan haka benemi Jalal ba se bayan, sallar magariba, yaje gidansu ya duba dakinsa yaga baya nan ya duba bedroom dinsa se yaji shi a rufe, be kawo komai a ransa ba yakoma gida, yai trying lambar Jalal amma shiru baya dagawa, haka ya hakura ya nemi abunda zesawa cikinsa, dan yasan maybe Jalal ya tafi nasa yawon, amma ya damu da rashin daga wayarsa da Jalal beyiba.

Nana tana kwance tana waya da saurayinta, Maama ta shigo dakinsu tace dan Allah in tayi salla taje ta karbo mata laces a wajen Mummy dan in anjima hajiya Jamila zata turo yaranta su karba, dan bata fuska Nana tayi “Maama dan Allah ki aiki Jalila baby ne zezo fa, Maama ta dan bude baki” Lallai Nana, wato saurayinki yafi aikena ko? “” murmushi Jalila tayi tace “Allah ya shiryeki Nana, bari inyi sallar magariba ni se in karbo miki Maama” dan gyada kai Maama tayi ta fice

Jalal kam yanajin wayarsa na ringing yai banza dan tunda ya kulle kansa a daki be fito ba, banda jujjuya kalaman Jalila ba abunda yake, ga yunwa yakeji yanzu yana fita Jawwad ya ganshi a haka ze dameshi da tambayoyin me yake damunsa danhaka ya yanke shawarar ya shiga cikin gida yasamu abinda zeci base yaje gurin Jawwad ba. Ya mike daga kan gadon ya fara yin alwala dan sallar asuba kawai yai, gashi yanzu magariba akeyi, yayo alwala yazo yai sallar azahar da isha’i, seyaji ya gaji dan haka ya mike yace yayi magariba da isha’i anjima kokuma gobe da safe, ya bude dakinsa ya fito, cikin gida ya nufa yana shiga palour Mummy suna kallo itada Ilham bebi takansu ba ya nufi kitchen ya zubo Abinci, ya dakko madara ya fito, abun mamaki yabawa Mummy dan kwanan nan yadena cin Abincin su, Mummy ta kalleshi tace “Jalal zo mana” waigowa yai ya kalleta kaman kar yaje kome ya tuna, kawai se yadawo yasamu guri ya zauna a palourn, yafara cin Abincin sa ba tareda yace komai ba, Mummy takuma tattara hankalinta ta kalleshi “yanaga kana cin Abincin mu yau?” Jalal be dago ya kalleta ba yace

“Dame gidan yakawo Abincin yace banda nine? Yabata amsa ba tareda ya kalleta ba ajiyar zuciya Mummy tayi

” A a ni banceba kokunyi faďa da Jawwad ne? “

” No, yau abincin gidan mahaifina nakeson ci” “Hmm hakan yayi kyau dan nima bana jin dadin kauracewa abincin mu dakayi dukda tarin dukiyar mahaifinka amma ace sedai kaci Abinci a wani guri. shi Jalal mamakin yadda taketa lallabashi yakeyi, ya sha madarar sa sannan yace “Serious ashe bakya san hakan, hmm amma kinsan wani lokacin abun hannun Jawwad ya fiyemin abun cikin gidan mahaifina” Mummy tace “kaga ba wannan ba, daddynka ze dawo next week” “munyi waya, yagayamin” yabata amsa a takaice “Yawwa dama sonake in yadawo ayi maganar aurenka, tunda lokaci yayi dayakamata ace daga kai har Jawwad din kunyi aure, aure shine cikar mutum” 

Bayan Jalila ta idar da sallar magariba ta fito karbowa Maama aikenta, kaitsaye gidansu Jalal ta nufa ta tsaya suka gaisa dame gadinsu sannan ta wuce, tana zuwa ta tura kofar palourn ta jiyo hargagin Jalal yana masifa

” wakike tunanin ze auri mutum irina, wakike tunanin yabani ‘yarsa, ko sokike in auri wadda zata soni dan dukiyata? Ta aureni dan ta kasheni ta mallaki abunda nake dashi, Wace yar mutuncin ce zata auri ďan da kikayi sanadiyar lalacewarsa da kanki, lalatacce dan giya kamarni Mummy kozanyi aure a rayuwata se wadda zata soni dan Allah badan wani abu nawaba, wadda bazata kyamaci rayuwar da nake ba, meye damuwarki da dole senayi aure, ai aure ba dole bane”

Da sauri Mummy ta katseshi ta hanyar cewa “A a Jalal abun duk be kai haka ba, baga Ilham nan ba, itace me sonka tsakani da Allah meze hana ka aureta ai kanwarka ce” wani mugun kallo yayiwa Mummy “Au Ashe kinada wani ďan da kika haifa bayanni ai ban saniba se yanzu” Mummy ta kalleshi cikin rashin fahimta tace “kamar yaya?” “inba wani ďan ne dake bayanni ba ai kinsan ba amin dole ko? Ya kalli Ilham” Ke! A tsorace Ilham ta waigo ta kalleshi “tunda muke na tabacewa ina sonki” shiru tayi ba tace komaiba, ya kalli Mummy cikin masifa da tsawa yafara mata magana

“wai dan Allah yaushe zaki fara playing role dinki na uwa, kimin adalci a matsayinki na mahaifiyata, ba kya tunanin in shiryu, se kokarin kuma rusa rayuwata domin wanke laifinki a idon wanda kikayiwa, yakamata ki tausayamin ko sau dayane yakamata ki barni na huta haka, please Mummy ki tausayawa rayuwata haka, a matsayina na tilon danki” karo na farko da Jalila taji ya kira mahaifiyarsa da Mummy, itakam tana son sanin tarihin Jalal da mahaifiyarsa, amma waze gaya mata. Jalal kam yana gama fadin haka ya tashi ya bar palourn ya fito fuuuu kaman guguwa, yana fitowa be kula da Jalila ba a gurin ya wuceta, a hankali tabi bayansa, yana zuwa motarsa ya nufa, yana zuwa ya shiga motarsa yana kokarin kunnata,  seya fasa kunna motar ya jingina da kujera yayi shiruu, gefen motarsa taje ta tsaya tai knocking glass din, a hankali ya sauke glass din motar kawai yai tozali da fuskar Jalila. Kokarin kunna motar yake, saboda yasan in har ya tsaya ze iya illata yarinyar nan, dan yasan yanzunma ci masa mutunci zatayi, hannu tasa ta dafa window din motar saitin Jalal tana kallonsa, tana iya juyo yadda yake numfashi, 

“ABDUL JALAL kaji tsoron Allah kaji, karka mutu mahaifiyarka tana jin haushinka, kome tayi maka kabata matsayinta na uwa, Annabi salallahu alaihi wassalam se da yafadeta sau uku yace abita sannan yace uba, kaji tsoron Allah kadinga yafiya mana, ka tausaya mata kaimata biyayya, kaji dan gidan daddyn sa, ba daddy kawai keda hakki akanka ba, nasan yanzu mashaya zaka tafi, dan ba kunya ce da kaiba naga baka da alamar zaka dena shan giya, kayi a hankali da duniya, sannan ka kiyayi miyagun abokai, u have to focus, ka kiyayi JeJe da Hannah da sauran miyagun abokanka, basa komai banda rusa maka rayuwa, basa nufinka da alkhairi ka kiyaye, jeka Allah ya shiryeka” manyan idanunsa da suka sauya zuwa launin ja ya zuba mata, cikin idonta ya saka nasa, dukda akwai duhu se hasken fitilu be hanashi ganin fararen idanuwan taba masu kama da tana jin bacci, ji tayi kaman an daureta takasa motsawa tabar gurin, itama ta kura masa ido, ji tayi idonta yayi nauyi, ga Jalal yamata wani irin kwarjini, kamshin turarenta duk yacika masa hanci, daurewa yayi, yai mata wani mugun kallo me wuyar fassara, sannaan ya dauke kansa yace 

“ki kiyayi haduwata dake, zanyi maganin wannan shishshigin naki, sekinyi dana sanin shigowa rayuwata, zan baki mamaki, bari in tuna miki alkawarin dana taba yimiki, zan maida ke abun kwatance irina, matsa ki bani guri ko in takeki da mota. A hankali ta motsa bakinta, tafara magana a hankali cike da rainin hankali tace

“zaka iya ai, inbaka takeni da mota ba ba sunanka ABDUL JALAL ba, ni bazan fasa fadan gaskiya ba, kome za kayimin, Kuma bazan taba zama abun kwatance irinka ba, dama kwatancen kirki ne da sauki, Allah ya tsareni zama abar kwatance kamar dan giya” 

“Haka kikace?” “baka da kunne ne?” Ajiyar zuciya Jalal yayi, ya kunna motarsa, Jalila ta ja dabaya ya ja motarsa da gudun tsiya, Jalila ta juya zata shiga gidansu Jalal, taga Ilham a tsaye a bakin kofa tana mata wani irin kallo na tuhuma, fuskarta na dauke da tsantsar bacin rai, dakuma tsanar Jalila, dan tana hangen abunda yafaru, tsakanin Jalal da Jalila, a hankali Jalila ta karaso, kota kan Ilham bata biba, ta tureta gefe ta wuce cikin palourn, ta tarar da Mummy a palour ta fada mata sakon da aka aikota, Ilham ta shigo palourn taji zuciyarta tana raya mata taje ta dakko  wuka ta kashe Jalila ta huta, itako Jalila ko kallon Ilham batayi ba, tacigaba da abunda take. 

Jalal kam kaman yadda Jalila ta fada, mashayar sa ya tafi, amma yana tafe tunani kawai yakeyi, yana ta nazarin mezeyiwa Jalila wanda ze bata mata rai, soyake ya bata mata rai yadda zataji zafi sosai fiye da yadda take masa, manyan mutane ma suna shakkarsa, saboda kwarjinin sa, amma yarinya karama tana caza masa kai, wani abun takaicin jinsa yake duk jikinsa ya mutu, kamshin turarenta kawai yakeji, yai kwafa zeyi maganinta ne. Yasamu guri yai parking Ya fito daga mota

Guri yasamu ya zauna, yai shiru dayake ansan abunda yake bukata customer ne sosai, aka kawo masa giyar dayake sha, befi minti shabiyar da zuwansa ba, sega Hannah tazo , dan an kirta a waya an sanar da ita Jalal yazo, guri ta samu ta zauna tana fuskantar Jalal, “Jalal ina kashiga haka, babu ko waya nadena ganinka kwata2 tun a gurin birthday din ka bankuma ganinka ba gashi inason ganinka, nayi niyyar zuwa gidanku amma bani da lafiya ne” kallonta ya danyi yayi shiru ya cigaba da shan giyarsa. Kallonsa Hannah ta kumayi “Jalal ya kayi shiru, kayi magana mana” “mezance miki, inajinki” ta numfasa tace “Jalal dan Allah menene alakarka da wannan yarinyar me iyayin tsiya, ta fadamin sunan ta amma na manta, a zatona itace Ilham amma ranar ta nunamin Ilham tace ita ba itace Ilham ba” ajiye cup din hannunsaa yayi ya kalleta “meyasa kike tambayata wacece?” “ta damu dakai sosai” “hmm ya akayi kikasan hakan?” 

“Alamu nagani” “yayi kyau” shine amsan da Jalal yabata, “Jalal dan Allah wacece ita a gurinka” a fusace ya kalli Hannah yace “ke kin isheni, ki kyaleni dan Allah” “meyasa zakace in kyaleka bayan saboda kai nazo gurin nan, Jalal wata alfarma nake nema a gurinka” kura mata ido yayi sannan yace “ina jinki” “Jalal tuba nakeso nayi, na dena abunda nakeyi, dan Allah so nake ka aureni, aurenka ne kawai ze iya cetoni daga halakar danake ciki please Jalal. 

” Aurena ze cetoki daga halakar dakike ciki, nikuma ze janyomin halaka, ke kina tunanin zan zabi mace kamarki a matsayin matar aure, Hannah banason yarana suyi irin rayuwar danayi, dan haka uwa tagari zan zaba musu, ina miki murnar shiryuwa da kikayi, naso dan Allah kika shiryu, amma ina miki fatan alkhairi Allah yabaki miji nagari “yana gama fadan haka ya tashi ya tafi. Hanna ji tayi kaman ta fasa ihu, duk tsawon lokacin nan dasuka dauka tare ammaa ace babau soyayyarta a zuciyarsa, anya JALAL mutum ne kuwa? Aikuwa ko karfene a zuciyarsa seya soni sena aure shi, tana cikin wannan tunanin Jeje yazo, yasamu guri ya zauna a kusa da ita ya kalleta “Hannah manyan kasa, mekuma kikazo yi nan?” 

“meya dameka dame nazoyi, oppression na fito, na fito farautar abunda zuciyata ke so, kuma zanyi iyayina inga nasamu” “Hannah kenan dazaki zubar da makamanki ki dawo mucigaba da aiki tare gurin ganin munyi nasara akan Jalal” 

“Jeje meyasa kanka baya jane, ban gayamaka cewar bazan kara maka aiki ba, kaina nakewa aiki yanzu, kafita daga harkata ko inyi maganinka wallahi” ta dau Jakarta tai tafiyarta, bayanta Jeje yabi da kallon mamaki, gaskiya Hannah ba karamar mara mutunci bace, betaba zaton zata juya masa baya ba, dole yai taka tsan2 da ita dan yasan halin Hannah sarai, inta sawa ranta samun abu setayi duk yadda zatayi ta sameshi, dole yai wani abu akanta. 

Koda Jalal ya dawo gida, Gaba daya yau angama dagula masa lissafi, mussaman Jalila, yau an hada masa zafi sosai duk ransa a bace yake, yarasa me zeyi ya huce, kalmar namij mara daraja da Jalila takira shi dashi se yaji wani mugun bacin rai ya kamashi, yayi tunani sosai mezeyiwa Jalila ya huce haushinsa, gani yai yana kara batawa kansa lokaci, dan haka zuwa yayi ya kuma daukan giya 

Ya sha me isarsa, seda fita hayyacinsa ya fadi a gurin yana bacci. 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Share please 

More Comments 

more typing……………………..

Back to top button