Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 73 Complete Novel

Father of soldiers

🔥TAKUN ƘARSHE🔥

_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_

*Nagode sosai da addu’o’inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*

*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅

Bismillah

Kai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata,
Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa”Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing,”
Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour,
Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu,ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace”Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,”
on the other hand hayam tace”haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu…..’tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa”Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar,
Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace”Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba,’
cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa”Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,’
Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faɗi rasss,ƙasa ƙasa da murya tayi tace”Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai?
“Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!” tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa
“kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne….’

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi,
“Wani abusufyan din kuke magana akai,”
Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin,
Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin,Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet,
gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa”kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,’
A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruɗu yasa ta manta hanyar fita daga ɗakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiɗimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa,
Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miƙi hanyar wannan tsohon store ɗin data ta6a garƙame su hosana aciki,anan corridor ɗin ta tsaya tana sauraran Hayaam,
“Wlh Aunty laila da gaske ne,Ni shaidace,Naji komai lokacin da Uncle ɗin nasu yake korama junaid bayani,bama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakan,Babban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashe,kuma dukkansu Mata ne kyawawan gaske,kamannin su sak iri ɗaya,Kuma kina kallonsu zaki gane cewa ƴa’ƴanshi ne……’
Hannu ɗaya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kanta,yayin da dayan hannun ke ruƙe da wayarta data kara a kunnanta,
“Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki ba,Taya hakan ma zata faru!mutumin da bai ta6a yin aure ba,Shi za’ace yana da ƴa’ƴa har ƴan uku!Cikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same su!Ni ban yarda da kalamanki ba,Hayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmi,Idan wasa kike mun ki daina!!!!!

Also Download Ɗaudar Gora Page 8 By Billyn Abdul

6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar
Fashewa da kuka tayi saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshinta,ga zuciyarta dake ta faman tafarfasa,Gaba daya bata jin daɗin jikinta,
Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta,
Tsoki taja tana jinjina kai tace”dama saida raina ya bani cewa ƙarya take yi mun,tayi mun hakan ne saboda ta tsoratar dani don in saukko,Shashasha kawai,
“Mommy kin farka kenan”
Muryar hafsat ce ta katse mata zancen zucin nata,
Juyowa tayi tana kallonta,atsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi jikinta na sanye da riga da wando na jeans,ta ɗaure sumar kanta da ribbom,yayin da hannunta ke ruƙe da Cup mai ɗauke da Tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,
Tunda Aunty babba taga hafsat na murmushi tasan cewa akwai matsala,hakanan dae ba zakaga fuskar hafsat da murmushi ba tunda farar safiya,
ƙaƙalo murmushin yaƙe Aunty babba tayi tare da cewa”Lafiya naga kina murmushi”?
“Lafiya lou mommy,kawai wani abun farin ciki ne ya faru,nasan cewa muddin kema kika ji,zaki yi farin ciki sosai,’
Murya asanyaye aunty babba tace”Faɗamun daughter har na ƙosa naji wannan abun farin cikin?halan an ƙara maku albashi ne?ko matsayi aka ƙara maki wurin aiki”?
Dariya hafsat tayi tana girgiza kai tace”Mommy baki canka dai dai ba,wannan albishir ɗin da nakeso inyi maki yafi ƙarfin duk waɗannan abubuwan da kika lissafo,kar6i tea ɗin nan ki fara korawa kafin na faɗa maki,”
Hannunta na kerma ta kar6i kofin da hafsat take miƙa mata,a hankali takai cup din bakinta ta kur6i Tea ɗin,kusan sau uku tana kur6arsa,kafin ta ɗan jinkirta bayan ta janye kofin daga bakinta tace”daughter dan Allah ki faɗamun wannan wani abun farin ciki ne!wlh duk na ƙosa naji,’
“Zan faɗa maki mommy amma mu shiga daga cikin palour mu zauna,’
“Ba inda zanje,idan zaki faɗamun ki faɗamun kawai,Sae ja mun rai kikeyi,” tayi maganar tana faman tamke fuska,
Hafsat tace”bada jimawa ba,Na kira Aunty azeema,don in gaishe da ita,Anan take sanar dani cewa ƴa’ƴan uncle abusufyan Sun bayyana…!
Tunkan ta ƙarasa maganar a gigice Aunty babba ta saki kofin dake hannunta,Ya tarwatse ƙasa,Ruwan tean dake ciki ya fallatsar masu a ƙafa,
ja da baya hafsat ta ɗanyi tana kallonta tace”haba mommy,so kike ki ƙonamin ƙafa ta,daga faɗin abun farin ciki?
Rai amatuƙar 6ace tace”Ki 6ace mun da gani sakarya kawai,Maƙaryatan banza,bazan ta6a yadda da kalamanku ba,duk bakinku ɗaya da Hayaam,’
Ta faɗi hakan tare da kama hanya fuuuuu kamar zata tashi sama,ranta duk a jagule,bin bayanta hafsat tayi da kallo harta haye upstairs,ta6e baki tayi tare da watsa hannayenta tace”I don’t care, Ni dae farin ciki nakeyi,Daddy ma nake jira in tambayeshi yaushe zamu je gidan saboda a qagare nake dana ga ƴa’ƴan uncle ɗinmu Abusufyan,tunkan na gansu har naji ina sonsu sosai,in ma na tashi tafiya hada tsaraba zan tafin masu dashi,’

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Cike da farin ciki hafsat take maganar,zuƙunnawa tayi tana tattare kofin da aunty babba ta fasa,

Lokacin da Aunty babba ta ƙarasa bedroom ɗin nasu,har ta ɗaga ƙafarta zata zura acikin ɗakin taji muryar ishaq yana cewa”Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah!Abba nayi farin ciki sosai,Meyasa tun jiya ba’a sanar dani ba,ae da tunda sanyin safiya zanyi maku dirarr mikiya,Amma ina taya uncle murnar ganin ƴa’ƴanshi,kuma ina tayamu murnar samuwar ƴan uku acikin zuri’ar mu,gaskiya bazan ma iya jurewa ba,Zan shirya nazo ne kawai,saboda na qosa naga ƴan ukun mu bayin Allah….
Abba yace”wani abun ma sai kayi tozali da yaran,kyawawan ƴan mata dasu,Yadda kasan photo copy ɗin abusufyan haka suke,kamanninsu sak iri ɗaya da nashi,’
Murmushi Ishaq yayi tamkar yana agabanshi yace”Abba kafin na ƙaraso,dan Allah a isar musu da saƙon gaisuwata,Ace yayansu General ishaq yana gaishe su sosai da sosai,kuma saboda suma zaiyi zuwa na musamman,’
“Insha Allah zan sanar masu yanzun nan,Allah ya kawoka lfy,”
“Ameen Abbana,”
Sun jima suna waya kafin sukayi sallama ishaq ya ajiye wayar,
tashin hankalin da ba’a sama shi date!!!!!!!
Magana dae ta tabbata da gaske ne zancen da hayaam da hafsat suka faɗa mata,Tabɗijancan,
Dakyar ta iya shiga cikin ɗakin,lokaci guda ta rasa kuzarin jikinta kamar wadda tayi Zazza6i na sati ɗaya,
Jin takun tafiyarta yasa ishaq juyawa yana kallonta fuskarshi a washe har ya kammala shiryawa cikin haɗaɗɗiyar shadda,
Ganin yana ƙoƙarin buɗe baki yayi mata magana yasa tayi saurin katse shi da cewa”Naji abunda ya faru,Hafsat ta sanar dani komai,ina tayaku murna,’ko amsar shi bata tsaya ji ba,ta faɗa cikin toilet,
Tana juyo muryarshi daga cikin bedroom ɗin yana cewa”Ni yanzu zan wuce Abuja ne,inyaso kun biyo ni daga baya ko zuwa gobe ko jibi haka,duk dae yanda kuka yanke shawara keda hafsat,
daga cikin toilet tace”Allah ya sauke ka lpy,in anje agaishe mana da mutanen gidan,”
“zasuji insha Allah,” ya amsa mata tare da kama hanyar fita daga ɗakin.

❤🤍❤

Acan 6angaren kuwa har lokacin suna a falon kan junaid da Uncle abusufyan ya gama fahimtar dashi game da Su Hosana da jahad,
jiki asanyaye yace”Amma meyasa su ba suyi rayuwa atare damu ba?meyasa Abba?uncle why?cike da tuhuma yake maganar yana kallonsu,yayin da fuskarshi ke ɗauke da damuwa,
abban su ne yace”Junaid,mu kanmu bamu san dasu ba,da ace munsan da zamansu da bamu bari hakan ya faru ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata,”
Shiru junaid ya ɗanyi yana ƙare ma su Jahad kallo,yaso ace tun fil azal tare da yaran ya taso,da ba ƙaramin kulawa zasu samu a wurin ƴan uwansu ba,Allah sarki rayuwa kenan,Rashin sani yafi dare duhu,su kansu su Sehrish sae dama dama suke da sun san cewa suna da wannan family ɗin daba abunda zai hana su nemi danginsu,Tabbas an cuci rayuwarsu ƙiri ƙiri an rabasu da Ubansu kuma an hanasu danginsu,wata shari’ar dae sae a lahira,

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

“Nasan yanzu kowa yana jin yunwa,saboda halin da muka shiga jiya babu wanda ya samu damar cin abinci acikin mu,Yakamata yanzu komai ya wuce,Lokacin farin ciki ne,Za’a shirya gagarumar walima saboda ƴan ukun mu,munaso su manta da duk wani abu da ya faru a rayuwarsu kuma su ƙaddara cewa tamkar yau ne suka faɗo duniya,ko ba haka ba”? Ya yi maganar yana kallon matasan gidan dake atsaye,Kowannansu fuskarshi asake,su fawan ne suka haɗa baki wurin cewa”Wannan haka yake Abba,In sha Allah zamu nuna masu soyayyar ƴan uwantaka,har sai sun manta da dukkan wani ƙunci da suka fuskanta na rayuwarsu,’ murmushi kawai Abusufyan ke saki don ba ƙaramin daɗi yaji ba,
Marshal Omar yace “Sannan kuma muna ƙara baku haƙuri game da halin da kuka tsinci kanku,duk da ba laifin mu bane,amma mun ɗaura ma kanmu laifin,Muna neman afwarku,Hosana Sehrish and Jahad,forgive us pls,’
gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi,lokaci guda kuma sukaji wata irin soyayyar ƴan uwansu ta kamasu,
Jahad ce tayi ƙoƙarin cewa”duk wani abu daya faru damu dama can rubutaccen ne!Allah ya riga da ya ƙaddara faruwan hakan,mun gode ma Allah da muka cinye wannan jarabawar,da juriya kuma da haƙuri,yanzu gashi gaba ɗayanmu muna farin cikin wannan rana da Allah ya haɗamu da danginmu,Babban abun farin cikin ma da ya kasance Uncle abusufyan shine mahaifinmu ba waccen fasiƙin mutumin ba…….’kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya zo mata,Janyota Abusufyan yayi tare da rungumeta ajikinshi,yana ɗan bubbuga bayanta,
“Ya Omar,” hosana ce ta ambaci sunan shi,tana faman kumshe dariya abakinta,gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu akanta,nuna shi tayi da yatsanta sannan ta nuna kanta,kafin ta haɗe yatsun wuri guda ta ƙullasu,Alamar ita dashi sun zama  ƴan uwan juna, ƙayataccen murmushi Marshal ya saki yana kallonta,
Duk wannan abun dake wakana akan idon Sgr dake atsaye,ya goya hannayenshi asaman wide chest ɗinsa,Har lokacin bai sauko ba,hankalinsa fa bazai kwanta ba har sai yayi tozali da YA SAYYADI,

Suna cikin magana muryar azmee ta katse su da cewa”Abba an kammala shirya breakfast ɗin,yakamata ku hallara a dining ɗin,” tana magana idonta na akan su jahad fuskar nan ɗauke da murmushi,
Batare da 6ata lokaci ba,gaba ɗayansu suka hallara asaman zungureran dining table ɗin wanda ke shake cike tab maƙil da kayan makwalashe naci dana sha,mutun goma shabiyu yake ɗauka,akwai kuma wanda Abban su junaid yasa aka ƙara cikin wanda aka shirya walimar jiya dasu,Ansanya shi a gefen nasu mai mazaunin mutun shida,Aunty azmee ta jera wasu kayan kalacin asaman shi,anan Abusufyan ya zauna tare da su sehrish jahad da hosana,

Tun daga kan yadda kowa ke zuba abinci acikinshi zai tabbatar maka da cewar ba ƙaramar yunwa suke ji ba,ko azmee basu jiya tayi serving ɗinsu ba suka shiga zuba abincin da kansu,Sgr ne kawai tayi serving ɗinsa sae kuma Abbansu,amma sauran ba wanda ya tsaya jira,wurin yayi tsit bakajin hayaniyar komai,sai sautin Cokulla,kwas kwas kwakwasss,

ɗagowa Marshal omar yayi karaf idonshi yaci karo dana hosana,ta zuba mashi ido ko kyaftawa batayi,kasancewar table ɗinsu na kusa dana juna,tazarar kadan ce,
Da cokalin hannunshi yayi mata nuni da plate din gabanta,alamar ta mayar da hankalinta kan abunda take ci,
murmushi tayi tare da kai hannu ta dauki lemu tana korawa,
Junaid kuwa duk ya rasa samun natsuwa sam ya gaza cin abincin dake a gabanshi sae faman juya cokalin yake yi acikin plate,duk in ya tuna abunda yayi ma Jahad acikin mota amatsayin Sehrish sai yaji gabanshi ya faɗi rass,fargabar shi kada jahad tayi tunanin ko ɗan iska ne shi,tunda ba sanin shi tayi ba,kar kuma tace zata sanar ma wani abunda yayi mata,tunawa yayi da lokacin daya tsoma harshenshi acikin bakinta ya ƙanƙameta yana kissing lips ɗinta,ba iya nan ba ya tsaya har hannunshi saida ya zura ackin hijabinta
Hankali tashe junaid ya miƙe yana ƙoƙarin barin dining ɗin,hankalin kowa ya koma kanshi,
Har suna haɗa baki wurin tambayar shi ina zashi,

Also Download Hira Da Matattu Page 1 By Jamila Umar Tanko

fuskarshi ɗauke da damuwa yace”Abba,bana jin yunwa,dama munyi breakfast tare da Mommy,zanje wurinta yanzu” Abbansu yake ma magana amma hankalinshi na akan Jahad dake shan farfesun da azmee ta zuba mata a plate,da alama ba ƙaramin daɗi farfesun yayi mata ba,duba da yadda ta mayar da hankali akanshi,
“Okey,zaka iya tafiya,” ya bashi amsa,cikin sauri junaid ya kama hanyar zuwa bedroom ɗin Abbansu don acan ta sauka,yana tafiya yana waiwayen su jahad aranshi yana cewa”wayyo Allah na,bansan me zai biyo baya ba,nasan cewa dole ta sanar ma Uncle abunda nayi mata,idan ta faɗa mashi shi kuma zai faɗa ma Abban mu ne,Abban mu kuma zai faɗa ma Babban yayanmu ne,shi kuma zaice wuyana ya isa yanka tunda har na iya Sumbatar mace daga nan zaiyi tunanin turani aikin Soja abunda banso,shikenan tawa ta ƙare’
ranta ne ya bata cewar ana kallonta,hakan yasa ta tsagaita daga shan farfesun da takeyi,ta ɗan ɗago idanunta,kai tsaye suka sauka akan junaid dake can nesa dasu yana kallonsu,
Mamaki ne ya kamata ganin yadda ya ƙura mata ido yana kallonta,aranta tace”bansan meyasa yake kallona ba,tsorana kar ace baisan ganina ne,’
“Allah yasa halinta irin na Sehrish ne,idan takasance mai sauƙin kai irin na rishi ɗina nasan cewa zata rufa mun asiri,amma anya zatayi sauƙin kai?Nasan me zanyi daga yanzu zan dinga ɗaure mata fuska,in nuna kamar na tsane ta,nasan hakan ne kawai zaisa taji tsorona taƙi faɗa masu abunda ya faru atsakaninmu!good idea”,
Yana kai ƙarshen zancen zucin nashi ya watsa mata harara tare da murguɗa mata baki,ya juya ya nufi bedroom ɗin abbansu,
Jiki asanyaye jahad ta ɗauke idanunta daga kallon bayanshi da take yi,lokaci guda taji komai ya fita ranta ba don komai ba sai don kallon da taga junaid yayi mata,maganarta ta tabbata,Junaid baison ganinta,tunda gashi ya harare ta kuma hada murguɗa mata baki,
Muryar daddynsu ce ta katse ta da cewa”Jahad,meya faru ne?naga kin daina shan farfesun ina fata lafiya?
firgit ta ɗanyi tare da wurga eye balls ɗinta akanshi tace”Am ok daddy,’
jinjina kansa yayi kafin yace”Ku saki jikinku,kuci abinci sosai,kada kuji komai,nasan baku saba ba,don na lura akwai rashin sabo atattare daku,amma a hankali zaku saba da ƴan uwanku,’
hosana tace”Abba ae ni,nama saba da kowa,baka ga yadda nake ta cika cikina da abinci ba,jahad ce ke jin kunya,ni bana jin kunyar kowa,’
Dariya sukayi gaba ɗayansu,Sehrish na cikin sakin dariyar nan,Karaf idanunta suka haɗu dana Sgr,ɗagowar shi kenan yayi arba da ita,gabanta ne taji ya faɗi rass saboda fuskarshi a murtuke take ba annuri,nan take dariyar da takeyi ta koma ciki,ganin ta zuba mashi ido,yasa shi jefa mata harara,a hanzarce ta kawar da idanunta daga kallon fuskarshi da take yi,jikinta kuma yayi sanyi,ta shiga tambayar kanta dalilin hararar da taga big bro yayi mata,kodai baya farin ciki ne da kasancewarta JININ SA!?tabbas hakan zai iya faruwa,Wataƙil kodan ya saba ganinta a matsayin ƴar aikinsa,baiwarsa,ƙasƙantacciya shiyasa yanzu Yake nuna 6acin ranshi don yana ganinta tamkar a matsayi ɗaya suke dashi,Ƴa’ƴan Wa da ƙani,da alama hakan baiyi masa ba,
“Idan har dagaske ne abunda nake hasashe,insha Allah zan tattara na bar masu gidan,saboda bana son 6acin ranshi,zan iya yin komai don farin cikin shi,” ta ƙarasa zancen zucin nata tare da sake ɗagowa a hankali don ta saci kallonshi,adai dai lokacin shima ya ƙara ɗagowa da kyawawan idanuwanshi kai tsaye suka shiga cikin nata,nan take taji gabanta ya kuma faɗuwa rass,kasa janye idanuwanshi yayi daga kallonta da yake yi,a yayin da yake jujjuya spoon ɗin dake hannunsa acikin plate ɗin abincin gabansa,har Yanzu bai daina mamakin kasantuwarta ƴar uwarshi ba,ta jininsa,tamkar a mafarki haka yake ganin abun,ganin ta zuba mashi ido batare da ta janyesu ba yasa shi ɗaure fuskarshi yasha murrr,saboda kada ma yarinya taga fuska har tayi tunanin raina sa don tasamu matsayi,
“U will still remain who u are,wadda take aiki a ƙarƙashina,Matsayin dana baki kenan,”ya fada a ransa
Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa”bazasu kara wahala ba,bazan ta6a bari hakan ya faru ba,tunda dae har yaran nan suka bayyana a matsayin ƴa’ƴana,In sha Allah bazan ƙara bari suyi aikin wahala ba,ko cokali bazan ƙara bari ɗaya daga cikinsu ta ɗauko ba acikin gidan nan,rayuwar hutu kawai nake so suyi rayuwar ƴanci,” ya ƙarasa zancen zucin nashi a yayin da yake bin kowaccen su da kallo cike da so da ƙaunar ƴa’ƴan nashi,’

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

Janye idanunshi yayi daga kan nata,kafin ya miƙa hannu tare da ɗaukar Glass cup mai ɗauke da abun sha me sanyi ya kai shi saitin mouth dinsa yana sipping ɗinshi anatse,yayin da sanyin lemun ke ratsa throat ɗinsa,a hankali ya lumshe idanunsa tare da ɗan ware su kaɗan,again suka ƙara sauka akan na sehrish a karo na uku kenan,agaggauce tayi hanzarin janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan plate ɗin abincin dake a gabanta,

Hannu Sgr ya sanya tare da yago tissue ya goge bakinsa,kafin ya miƙe tare da juyawa ya nufi upstairs,Miƙewa Marshal yayi da alama shima ya kammala breakfast Ɗin nasa,shima upstairs ya nufa,

Fitowar Hajiya azeema keda wuya daga cikin bedroon ɗinta,ta jiyo muryar gwaggon katsina tana ta faman sambatu tana cewa”Tsiyarta kenan mutun yazo gidan ƴan gayu,Ni bazan iya rayuwar turawan nan ba,taya za akai ma mutun salalar biredi tare da tea rabin kofi kamar wata ƴar iska ace in sha”?
Tafiya take tana sambatu zaninta a hannu sai ɗan undi ajikinta,kanta kuwa ta kifa wannan ɗaurin ɗan kwalin nata mai kama da helmert,
har zata gifta hajiya azeema tayi gyaran murya tare da ambaton sunanta”Goggo,” fuska a yamutse ta juyo tana kallonta,dawowa tayi daga gefenta suna fuskantar juna tace”Yawwa azeema,wai nikam inaso in tambayeki,’
Natsuwa hajiya azeema tayi tare da cewa”ina sauraronki gwaggo,”
“Jiya nayi wani mafarki,ƴa’ƴan abusufyan sun bayyana,wasu ƴan uku kyawawan gaske,da nayi tunanin koda gaske ne abun ya faru amma daga baya na gane ba gaskiya bane,in ba haka ba,yaushe abusufyan ya ta6a yin aure”? Tayi tambayar tana kallon hajiya azeema,wadda ta saki baki tana kallon gwaggon,
Ganin azeema tayi sototo tana kallonta yasa tayi tunanin cewa ko abunda ta faɗa ya bata mata rai ne,
“Nasan dole kiyi mamaki kema,Mafarkin fa kamar dagaske,ɗaya daga cikinsu har tana sharara mana labarin ƙarya waisu ƴa’ƴan wata zainabu ne,kuma ma acikin labarin hada wata hajiya Ameena,in banda shaiɗan ina abusufyan ina ƴa’ƴa”?
Ƙiris ya rage Azeema ta fashe da dariya agaban gwaggon katsina,ganin yadda ta haƙiƙance tana kora mata bayani,kuma babu alamun wasa a fuskarta,
Ƙunshe dariyar bakinta tayi tare da basar da ita tace”Gwaggo Anya kina shan maganinki kuwa?ina Dr harris yake?gaskiya inason ganinshi,’
Tsoki gwaggon katsina taja tare da cewa”Harrisun daya zama ɗan iska,”
Waro ido waje azeema tayi tace”gwaggo harris ne ɗan iska”?
ta6e baki tayi tare da cewa”Zan masa ƙarya ne?ba ɗan cikina bane”?nasha wahalar yima yarona tarbiya amma waccen sauden…..’kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,zanin hannunta takai saitin idonta tana ƙoƙarin goge hawayenta,
Zuru harris yayi wanda fitowarshi kenan kuma atare da saude suka fito,jin maganar gwaggone ma yasa yayi hanzarin cire hannunshi daga cikin na sauden,
Hajiya azeema tace”gwaggo faɗamun me harris ɗin ya akaita,?
Hankali tashe Saude tace”ya harris pls kada ka bari gwaggo ta faɗa mata abunda muka aikata,kasan gwaggo yadda take ɗaukaka abu,inta tashi faɗi saita ƙara ma miya gishiri,’
Dr harris yace”just don’t worry ur self,insha Allah bazata faɗa mata ba,”
Faɗin hakan keda wuya gwaggon Katsina tace”Azeema abun da ciwo,yanzu yunwa nake ji,shiyasa ma kika ga nafito ina sambatu,Wurin waccen matar zani,wlh ba azmee ba Allah yasa ramadan ce ita yau saina zazzaga mata rashin mutunci!Ni zata raina ma hankali tunda safe,takawo mun tea rabin kofi da salalar biredi wai in fara da wannan,don ta raina mun hankali,nayi mata kama da kusu ne?

Also Download Idon Naira Chapter 1 By Mamuhgee

Rai a6ace tayi maganar,aikuwa atare haris da saude suka fashe da dariya,a hanzarce ta juyo sakamakon jin sautin dariyar tasu,nan take ta tsuke fuska ganin shi tare da saude,
Murmushi Hajiya azeema tayi tare da cewa”haba gwaggo baki fahimce ta bane,cewa fa tayi ki fara da wannan tana nufin kafin ki tashi fitowa zuwa yin breakfast ɗin,yanzu haka yana can an shirya mana mu kawai ake jira muje muci namu kalacin,”
Hajiya azeema ta ƙarasa maganar tare da ruƙo zanin hannun gwaggon tace”Bari na taimaka maki ki ɗaura shi,”
Girgiza kai tayi tare da cewa”Barmin shi a hannuna,nafison inji iska na shiga ta ko’ina,”murmushi hajiya azeema tayi kafin tace”hakan ma yayi gwaggo,ae under skirt din ma bamai sharashara bane,yana da kauri,amma duk da haka dae ki ɗaura zanin yadda zaki fito da kyau tunda ga rigarshi kin sanya ajikinki,Kuma kinga Abusufyan na nan,Ga kuma ƴa’ƴansa,bazasu so suga gwaggonsu a haka ba,”
wani irin ƙayataccen murmushi gwaggon katsina tasaki tare da cewa”Kenan dagaske ne Mafarkin da nayi jiya”?
Jinjina kai Azeema tayi tace”Ae suna nan,duk abunda ya faru jiya dagaske ne,ba mafarki kikayi ba,agabanki akayi komai kin dai shafa’a ne,’
Jin haka yasa tayi saurin mayar da zanin ajikinta tana ɗaure shi tana cewa”Allah sarki ƴa’ƴan abusufyan ɗina,bayin Allah,sunsha wahala a hannun wannan fasiƙin mutumin baƙin shaiɗani,Allah mutumin nan ƙaho ne kawai bai fito masa aka ba,amma ina tantama anya ba Irin shaiɗan bane”?
“gwaggo kidaina maganarsa ma,Ni wlh ko zancen shi ma bana so anayi,Na tsani mutumin nan kamar yadda natsani mutuwa ta,”acewar hajiya azeema,tayi maganar ne a yayin da take kama hanyar Zuwa Dining area ɗin nasu,bin bayanta Gwaggon tayi tana cewa”Ae ko sai dai ki toshe kunnanki,don zancen sayyadi ya zama dole,in har ba’a kawo min kansa ba,bazan daina faɗan sunan shi ba,’
Murmushi kawai hajiya azeema tayi,atare suka ƙarasa dining area din,
Gaggaisawa suka fara yi da junansu,su jahad na ganin saude suka tashi atare suka nufe ta,dama Jiya basu samu damar gaisawa da ita ba,saboda yanayin da suka shiga gaba ɗayansu,haɗasu tayi ta rungume ajikinta,cike da farin ciki tace”Ina tayaku murna sosai,nayi farin ciki sosai,Ya harris ya sanar dani komai agame daku,ashe ku jininsu ne,’ta ƙarasa maganar ayayin da take raba jikinta daga nasu,kowannansu fuskarshi ɗauke da murmushi,Jahad tace”Aunty saude kinga ikon Allah ko?munsha wahala sosai,mu kanmu bamu ta6a tunanin cewa muna da dangi ba,amma sai gashi ƙaddara ta haɗamu da ya Omar,Ita kuma ƴar uwarmu Sehrish ƙaddarar aikine ya kawota gidan nan,Muna tare da ƴan uwanmu ba tare da mun sani ba,sae gashi rana ɗaya Allah ya bayyana mana komai,’
Saude tace”Congratulations Once again,ina ƙara tayaku murna sosai da kuka fito daga tsatson wannan Family ɗin,abun alfahari ne wannan”kafin ta mayar da idanunta kan Hosana,Cike da zolaya taja kumatunta tare da cewa”Hosana Kinga yadda kika canza?kamar ba wannan Sha takwas sha taran ba,mai ɗan kai,kinyi kumatu kamar Balon balon,Ga haske gaskiya ya Omar ya Iya raino,”
Fashewa da dariya hosana tayi tana faman sunnar dakai,
“Kiyi ma sister ɗinku mana,Ita bazata taso mu gaisa ba”?tayi maganar tana kallon sehrish dake zaune,tana faman kallonsu ɗaya bayan ɗaya,
Murmushi jahad tayi tare da juyawa tayi mata alamar ta taso da hannunta,
Miƙewa sehrish tayi tare da nufar inda suke,koda ta ƙaraso saude ta sanya hannu tare da janyota ta rungumeta,kafin ta raba jikinta dana sehrish tace”Masha Allah,gaskiya ban ta6a ganin triplet,masu kama iri ɗaya sak kamar taku ba,ina taya ki murna sosai da Allah ya haɗaki da ƴan uwanki,da kuma mahaifinku,da kuma danginku,’
Fuskar sehrish ɗauke da murmushi tace”Ngde sosai,”
“Allah ya tsare mana ku,Ya Albarkaci rayuwarku ya kuma kare ku daga sharrin maƙiya,’
Atare suka amsa mata da Ameen,bama su kadae ba,hadasu Abba dake sauraron maganganun nasu,

Kamar yadda Abba yayi alƙawarin shirya gagarumar walima na bayyanar ƴa’ƴan ƙaninsa Abusufyan,Da kanshi ya fidda date ɗin da za’a gabatar da ita,Kuma tun aranar ya fara kiran Ƴan uwa da abokanan arziƙi yana sanar dasu game da ƴa’ƴan abusufyan da suka bayyana,Babu wanda bai bari ba,kowa kira yake tun daga kan danginsu na Zaria,na damaturu dana sauran states ɗin da kuma waɗanda ke zaune Ƙasashen waje,kowa saidaya sanar mawa,Bayan Abbas ya koma gidane da safe Amani ke tambayarshi meya faru ne jiya ya hanasu zuwa gidansu,Anan ya kwashe duka abunda ya faru game da su Sehrish ya sanar mata,wani irin farin ciki ne ya cika ta,Ba don komai ba sai don sanin cewa plan ɗin Aunty babba ya gama Tarwatsewa,ae tunda taji cewar ƴan mata ne kuma sun kai shekara goma sha bakwai zuwa sha takwas kyawawan gaske,Nan fa ta kwashe da dariyar mugunta aranta tana cewa Naga yadda za’ae Aunty laila ta cimma burinta,Gida bai ƙoshi ba taya za’a ba na waje,Ae tuwona maina za’ayi,Haba ae xance ya ƙare,
ita kanta Amani ta ƙosa ranar walimar tazo saboda suje gidan,saboda taji cewar Aranar Aunty babba da hafsat zasu zo Abuja,babban burinta taga tashin hankalin da aunty babba zata fuskanta inta gansu,

Ranar walimar kuma yayi dai dai da ranar da Ammi zata zo,tare da wasu daga cikin danginsu,haka zalika captain Najeeb da kuma Talal suma duk a ranar zasu dawo gida,ba don komai ba sai don su sanya ƴa’ƴan uncle ɗinsu abusufyan acikin idanunsu,Kowa ɗokin ganinsu yake yi kamar kamar me,musamman da sukaji irin rayuwar da yaran sukayi a wulaƙance sai suji wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu ya shiga cikin ransu,kuma duk aranar MG Osman da kuma Captain Adam suma zasu dawo gida,wanda tun dawowarsu daga U.s suka tafi sada zumunci,Gaskiya wannan Babbar rana ce,Hakan yasa ma Zamuyi shiri na musamman ni da makaranta littafina don mu halarci gidan amatsayin gayyar soɗi tunda ba’a gayyace mu ba,Sa kaine kawai,

Cikin ƴan kwanakin nan wata irin rayuwar farin ciki suke gudanarwa tare da Daddynsu,kullum yana manne dasu,Da kanshi ya zauna yayi masu kitson kalaba guda bibbiyu akansu kamar yadda ya ta6a yi masu suna yara,koda yazo kan Sehrish,Cike da mamaki yace”Ya akai naga gashin kanki guntu?ko kinyi wani ciwo ne dayasa aka datse maki gashin,”girgixa kai tayi tare da cewa”a’a Laifi nayi ma Babba yaya shine ya yanke mun gashin da almakashi,”
da buɗar bakin Abusufyan sai cewa yayi”Yayiwa kanshi ai,” murmushi sehrish tayi duk da batasan me daddyn nasu yake nufi da hakan ba,duk a wannan kwanakin basu je school ba,Abusufyan da kanshi yace kada su damu shi da kanshi zai kaisu makarantar don karma a tuhume su,

A 6angaren Sir Commander haroon kuwa,tamkar munafuki haka ya koma acikin gidan,ba kowa ma ke sanin lokacin da yake shigowa gidan ba,da kuma lokacin da yake fita,Da alama dae akwai wani abu da yake shiryawa a 6oye,

*AMRISH*

Zaune take acikin class ɗin gaba daya ta shiga damuwar rashin ganin Sehrish kwana biyu ko layinta ta kira bata samu,hatta wayar junaid ta jaraba kira shima ba’a ɗagawa,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tagumi tayi idonta cike tab da hawaye saboda damuwar da take ciki,taso ace sehrish na nan atlease zata ɗebe mata kewa,tana cikin wannan tunanin har malam ya shigo cikin class ɗin nasu bata sani ba,bayan ya kammala amsar gaisuwa daga wurin student din,kai tsaye ya ƙarasa seat ɗin da Amrish take,hannun shi yakai wanda ke ruƙe da maker ya ɗan bubbugi desk ɗinta,a firgice takai idanunta akanshi,Yunƙurawa tayi tare da miƙewa ganin Ya mu’allim,wanda tun ranar daya ba sehrish Ruwan addu’ar nan bai ƙara zuwa makarantar ba,duk da sun samu labarin cewar Ya tafi Umra ne,shiyasa aka musanya masu shi,
Murmushi ya ɗan saki afuskarshi yana kallonta yace”tunanin me kike yi ne?har na shigo cikin class ɗin baki sani ba?
Muryarta na rawa tace”Ayimun afwa ya mu’allim,Bana jin daɗi ne bansan ka shigo ba,
Jinjina kanshi yayi tare da ɗan kai idanunshi kan Seat ɗin sehrish yace”Ina yarinyar nan take?ƴar family ɗin Salahuddeeen hussein naga kamar bata a class ɗin”?
fuskarta ɗauke da damuwa tace”Batazo ba,yau kusan kwana huɗu kenan bata zo school ba,kuma nayi trying kiran layinta amma bana samu,har brother ɗinta na kira,shima layinsa ba’a samu,’
Jin hakan yasa shi fargabar to kodai wani abu ya faru da yarinyar?Yaso yaji ya tayi da ruwan addu’ar daya bata,shin tasha ko bata sha ba?
Jinjina kanshi yayi tare da juyawa yace”Allah yasa dae lafiya,in har batazo ba,zuwa sati mai zuwa zan je gidansu don na binciki dalilin rashin zuwan nata,’
Jiki asanyaye Amrish ta koma ta zauna,saman seat ɗin nata,jikinta har ya fara kerma saboda tsoran kar ace wani abune ya faru da Sehrish,
A ƙarshe dae ta yanke shawarar neman gidansu don taje ta ganta da kanta.

Karanta>>> Rigakafin Zubewar Nono, Lalacewa Da Kuma Yadda Mike

Back to top button