Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 70 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Chapter 70 Book 2

The Father Of Soldier

Written By: Boss Bature

*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata  zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,

❤🤍❤

Da wuri bayan an tashe su daga islamiyyar Abusufyan yazo ɗaukarta,ƙawayenta sae santin shi sukeyi,dama haka kullum suke zuzuta kyanshi da kuma gulmar wankan da yake ɗauka na tsadaddun kaya,ba ƙaramin tafiya yake yi dasu ba,

Shiga cikin motar abu tayi tare da rufe motar,sannan ta juya tana kallonshi,ya kifa kanshi asaman sitiyarin motar da alamun damuwa atattare dashi,

Hannu tasa tare da shafa sumar kanshi tace”Mijina,meya faru ne naganka kamar cikin damuwa,”

ɗagowa yayi daga kan sitiyarin ya kalli fuskarta tare da cewa”babu komai abuna,yau dai hakanan nake jin gabana na faduwa kamar wani mummunan abu zai faru dani,dan Allah ki tayani da addu’a ko zan samu zuciyata ta daina yi mun bugun da takeyi,

jin wannan maganar ta abusufyan yasa hankalinta tashi,matsawa tayi kusa dashi suna fuskantar juna tace”Insha Allah babu abunda zai faru mijina uban ƴa’ƴana,zan tayaka da addu’a kuma inaso kaci gaba da Ambaton Innalillahi wa’inna ilaihirraji’in,insha Allah komai zai tafi dai dai,’

Murmushi ya ɗan saki tare da haɗa fuskokinsu wuri guda suna shaƙar numfashin junansu,

Cikin wata irin kasalalliyar murya yace”Kiyimun alƙawarin ba zaki ta6a rabuwa dani ba abuna,wlh ina sonki sosai fiye da yadda nakeson kaina,banda burin daya wuce na ƙare rayuwata tare dake,daga ni har ke akwai ƙuruciya atattare damu,ina fatan mu girma tare,mu kara wayau atare sannan mu tsufa kuma atare,’

Kalamanshi ba ƙaramin kashe mata jiki sukayi ba,nan take taji soyayyarshi na ƙara ninkuwa acikin zuciyarta,

Cikin sanyin murya tace”bazan rabu dakai ba Abusufyan ɗina,i luv u so much,more than my life,bazan ta6a bijire maka ba,yanzu na gane cewa bani da masoyin da ya wuce kai aduniyar nan abusufyan,ina fatan Allah yabarmun kai,’ta ƙarasa maganar tare da hugging ɗinshi sosai ta kwantar da kanta asaman wide chest dinshi,dama tubarkallah duk da kananun shekarunsa yana da cikar kira ga hutu daya ratsa shi,hannunshi ya zura acikin hijabin jikinta yana shafa sumar kanta,sun jima a wannan yanayin kusan 30mins,kafin ya tashi motar ya miƙi hanyar komawa dasu gida,a kasalance yake yin driving ɗin,saboda sakonnin da abu ke aika mashi ajikinshi,duk ta jefa shi cikin wani irin yanayi,

koda suka koma gida atare Suka ci abincin da Hajiya Ameenatu ta girka masu abun gwanin burgewa,bayin Allah ashe duk na bankwana ne,sukeyi ma juna basu sani ba,

 

lokacin kiran sallar magrib,abusufyan ya fito daga cikin toilet,jikinshi da danshin ruwa alamar alwala yayi,a lokacin abu na zaune gefen gadonsu tana jiran fitowarshi,jin alamar buɗe ƙopar shi yasa ta ɗan dago ta kalleshi fuskarta ɗauke da murmushi tace”Sannu da fitowa hayatyna,”

Ƙarasawa yayi wurinta tare da zama daga gefenta yace”me kika tanadar mun yau idan nadawo gida da daddare?

Abu tace”komai kakeso,”

“To ki tanadar mun kan ki,yau zan baki mamaki,awashe gari zaki haifa mun babies bama ɗaya ba….’

Dariya tayi sosai jin abunda yace kafin ya tashi yayi mata sallama tare da fucewa,’

Lokacin da aka kira sallar isha’e bayan tayi wanka ta ɗauro da alwala,sai da ta kammala sallar sannan ta shiga shirya kanta,tun tana shafa mai ajikinta take tunano kalamam abusufyan nacewa zata haifa mashi babies awashe garin ranar,ta lura ba ƙaramin son ƴa’ƴa gare shi ba,kusan kullum ne sai yayi mata maganar yaushe zasu haihu,wani lokacin har cewa yakeyi wai ko dae basu isa haihuwa bane shiyasa bata samu ciki ba,duk irin ƙoƙarin da yakeyi, don ba ƙaramin jarababbe bane,

Murmushi tayi tare da cewa”Nikaina aƙagare nake dana ga ƴa’ƴan da zamu haifa ni da abusufyan ɗina,nasan yaran zasu zama kyawawan gaske in dai suka ɗauko kyawun fuskar kowannanmu,amma ni dae nafi son su ɗauko fuskar shi,saboda koda wata rana in yayi tafiya mai nisa,zan dinga kallon fuskarsu a matsayin tashi,hakan zai ɗebe mun kewa,

 

Gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren da abu ta feshe jikinta dashi,bayan ta gama shafe shi da haɗaɗdun mayukan jikinta,komawa tayi gaban wardrobe ɗin kayansu ta buɗe tana tunanin wasu kaya zata sanya waɗanda zasu zautar da abusufyan,ta jima atsaye tana ruwan ido kafin ta hango wata rigar bacci Babby doll black color,net ne ajikin rigar shara shara ana kallon komai na jikin mutun,tamkar ma mutun bai sanya kaya bane saboda yadda take fitar da tsiraici,ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,zubo da gashin kanta tayi ya sauko har wurin waist ɗinta,komawa tayi gaban mirror ta shafa jan baki red abakinta,

 

Bayan ta kammala shirin nata,ta shiga zagayen ɗakin tana jiran dawowar abusufyan,tana yi tana kallon wall clock dake manne a bango tana duba time,abu kamar wasa har ƙarfe 10 na dare babu abusufyan,shi da ya saba dawowa da zarar an kammala isha’e,baiwar Allah har ta fara gajiya da yawon,komawa tayi ta zauna gefen gadon tana sa ran dawowarshi,da zarar taji motsin mutun ya shigo cikin gidan sai ta miƙe jiki na rawa ta leƙa taga wanene  ashe Haris ne ya dawo,na biyu kuma data leƙa Abbansu ne ya dawo,ƙarshe dae bacci ya kwashe ta,wuraren goma sha biyu ta farka,ganin har lokacin bai dawo ba,yasa hankalinta yayi mugun tashi,saukowa tayi daga saman gadon ta ɗauko hijabi ta zura ajikinta,sannan ta fito daga ɗakin ta wuce bedroom ɗin haris,

A ƙofar ɗakin ta tsaya tana kwankwasawa,

Cikin bacci haris ya jiyo bugun ƙopar ɗakin nashi,muryarshi akasalance yace”Wanene,”

Abu tace”ni ce Zainab,’

Saukowa yayi daga saman gadonshi yazo bakin ƙopar ya buɗe mata tare da cewa”lfy,meya faru ne abu?

Abu tace”ɗan uwanka abusufyan har yanzu fa bai dawo cikin gidan nan ba,hankalina ya tashi sosai,bansan ko kana da masaniya akan inda yaje ba,”

Cike da mamaki Haris yace”wai kina nufin bro ɗina bai dawo gida ba?tare dashi fa muka je masallaci,amma ba tare muka dawo ba,saboda yace mun yana sauri yazo wurinki ne,ni kuma na biya gidansu abokinmu ne,”

Jin wannan maganar yasa hankalin abu ya ƙara tashi haikam,tuni idanunta sun cicciko da kwalla,dama bata da wuyar yin kuka,fargabarta kar ace wani abu ne ya faru da mijinta,

Lallashinta haris yayi tare da cewa”just calm down ur mind,duk inda abusufyan yake yana atare damu,bana so ki tashi su mommy daga bacci game da maganar nan,hankalinsu zai tashi ne,bari na jaraba kiran numbar shi muga in zata shiga,”ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya shiga cikin ɗakin nashi,

Sai gashi ya dawo hannun shi ruƙe da wayarshi yana dannata,numbar shi ya kira,tana fara ringing abun mamaki akayi picking kiran,

Da sauri haris ya kara wayar a kunnan shi yace”bros kana ina ne wai?har 12 baka dawo gida ba?duk ka tayar mana da hankali,”

Gaban haris ne ya faɗi rass jin muryar mace tana cewa”mai wayar ya shiga wanka ne,’

rejecting kiran yayi cikin sauri gudun kar abu tajiyo muryar macen da yaji,don ya santa da kishi,

“Me ya ce maka”! Ta tambaya tana kallonshi,

Daƙyar ya iya cewa”Am..um…kin gane wani aiki ne ya tsayar dasu a company,sai zuwa gobe ko da asuba zai dawo,dan Allah ki ƙara hakuri….’

Tunkan yakai ƙarshen maganar tashi abu ta watsa da gudu ixuwa ɗakinsu ta faɗa saman gado tana kuka,tasha kuka sosai a ƙarshe bacci ya ɗauke ta,

 

Koda ta farka sallar asuba,abusufyan bai dawo ba,bayan tayi salla ta zauna tana karatun al’qur’ani don kar bacci ya kuma ɗaukarta,wuraren ƙarfe 7:30 tayi shirin zuwa islamiyya,duk da halin da take ciki na damuwar rashinshi,

batare da sanin kowa ba ta fice ko breakfast ba tayi ba,a bakin gate suka haɗe da baba buzu,

Zuƙunnawa tayi tare da gaishe shi”ina kwana baba,kun tashi lafiya,”

Baba buzu yace”me ya faru abuna?naga fuskarki tayi jawur ta kumbura kamar kinsha kuka”?

cikin sauri tace”a’a babu komai baba,lafiya ta lou,’ta bashi amsa tare da miƙewa tsaye,

“Ina abusfyan ɗin yake ne yau bazai kai ki makarantar bane”?

Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,

Bai kawo komai aranshi ba,yace”kada ki makara ki wuce ki tafi,”

Amsa mashi tayi da toh sannan ta fito waje ta kama hanya tana tafiya ita kaɗae cike da damuwa,

Kwatsam!kamar ance ta waiga ta hango Motar abusufyan yayi parking ɗinta a gefen hanya,mamaki ne ya kamata,

Jiki na rawa ta nufi wurin motar tare da sanya hannunta ta kwankwasa glass ɗin shi,

Zuge glass ɗin akayi a slow,a gigice Abu ta zaro ido waje tana kallonsu,abun tamkar a mafarki, sun manne da juna abusufyan ɗin da take ta haukan nema tare da wata matashiyar budurwa cikin motar,budurwar ko kayan kirki babu ajikinta,inners ne kawai ta bari,da alama ma basu acikin hayyacinsu sunyi nisa cikin harkar tasu,

Hankali amatuƙar tashe abu ta aza hannunta akai tana fadin”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’una….!’

Tana ƙarasa faɗar hakan ta yanke jiki ta faɗi a sume ƙasa,zubewarta ƙasa ke da wuya,Motar nan tabar wurin tamkar bata ta6a bayyana ba,

Adai dai lokacin kuma Motar Abusufyan ta shigo layin da gudun gaske,tunkan ya ƙaraso ya hangi abu sume a ƙasa cikin uniform dinta,gabansa ne ya faɗi rass,da sauri ya tsayar da motar tare da buɗe ta ya fito yana faɗin”kai!me nake gani haka?kodai idanuna ne suke nuna mun ba dai dai ba!abuna ce kwance a ƙasa!taya akai hakan ya faru!”

ƙarasawa yayi tare da zuƙunnawa agabanta yana shafa fuskarta,ya jima yana mamakin yadda akai abu ta sume ƙasa,kuma tabbas itace,

Hannu yasa ya ɗaukota ya nufi mota da ita bayan ya kwantar da ita abayan motar ya shiga gaban motar ya tashe ta suka nufi gida,

 

Lokacin da abusufyan ya shigo da abu a hannunshi,Hajiya Ameena suna xaune saman dining chairs ita da alhaji da kuma haris suna yin breakfast,

Hankali atashe suka nufo shi suna tambayarshi lafiya!meya faru da ita!

Hajiya tace”Yaushe kuka fita tare da ita batare da sanina ba!?

Abusufyan yace”mommy ba atare muka fita ba,ni jiya ban kwana agida ba,bacci ya ɗauke ni acikin mota ban ƙara sanin inda kai na yake ba sai da safen nan,kuma wayata ma an sace ta banganta ba,”

Mamaki ne ya kamasu su duka,musamman Haris kanshi ya ɗaure jin cewa an sace wayar abusufyan hakan na nufin cewa jiya wayar bata a hannunshi wasu ne suka ɗauke wayar,to garin yaya hakan ya faru,

Hajiya tace”Haba abusufyan ɗina garin yaya har bacci ya ɗauke ka acikin mota,kuma aka sace maka waya,duk ta yaya hakan ya faru”?

Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace”wlh mommy ni kaina bansani ba,wayata tun a masallaci aka sace ta,ban tashi ankara ba sai da na shiga cikin motata bayan mun rabu da haris,na kamo hanyar zuwa gida na dinga ganin biji biji acikin idanuna,dalilin dayasa na dakatar da driving ɗin nayi parking na motar,tun daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba,sai yanzu dana farka,na biyo hanyar gida kenan naga abu a kwance ƙasa,ina tunanin wani abune ya tsoratar da ita shiyasa ta sume’

Alhaji yace”kaɗan daga cikin sakarcin kane sufyan!in ba shashasha ba taya zaka bar bacci ya ɗauke ka acikin mota har ka kwana awaje,ko tsoron wani abu ya faru dakai baka ji!salon kaja ma mutane bala’e ko!?

Ganin ya rufe shi da fada yasa mommy ta 6ata fuska tare da kallon Abusufyan tace”Ka shiga da ita ciki”

Amsa mata yayi kafin ya wuce da abu cikin ɗakinsu,

“Dama ae kin saba goya mashi baya!yaron nan yayi laifi me yasa ba zaki bari ayi mashi faɗa ba!ke kina da tabbacin cewar baccin ne ya kwashe shi akan hanya har ya kwana waje?ni ban yarda da zancen nan nashi bama,akwai dae inda yaje,”.

Rai a6ace Hajiya Ameena tace”ya isa haka Alhaji!kasan irin kalaman da zaka dinga faɗi akan abusufyan ɗina,in ba haka ba,ranmu xai 6aci ne gaba daya,

Tamkar zasuyi faɗa atsakaninsu,ganin haka yasa Haris cewa”pls mommy dan Allah kudaina mana,banaso inga kuna faɗa akan abusufyan,wai meyasa kuke haka ne?daddy kaima ka daina sanya baki akan lamarinshi mana tunda mommy bataso,ba shikenan ba,’.

Jinjina kai kawai Alhaji yayi tare da kama hanya ya wuce upstairs,haris ya ruƙo hannun mommynshi suka koma don su ƙarasa yin breakfast ɗinsu,

 

A6angarensu abu da abusufyan kuwa,bayan ya kwantar da ita saman gadonsu,ruwa ya dauko a roba ya ɗebo ya yayyafa mata a saman fuskarta,a hankali ta shiga mutsu mutsun buɗe idanunta,zuba mata ido yayi yana kallon fuskarta cike da tausayinta don yaga alamar jirwayen hawaye a fuskarta kuma ta ɗan kumbura,

 

Ware idanunta tayi akanshi koda taga shine a firgice ta miƙe zaune saman gadon tana ja da baya,ƙure ma head board ɗin gadon tayi tana faman zazzare mashi idanu,

Cikin sanyin murya yace”Abuna,am really sorry jiya nasan kinyi kewata sosai,na kwana awaje ban dawo gida ba,nima ba da son raina hakan ya faru ba,”

Yana kai ƙarshen maganar tashi abu ta fashe da matsanancin kuka tana cewa”ka cuce ni abusufyan,ka yaudare ni!kayi mun ƙaryar cewa zaka daina mu’amala da mata ashe ƙarya kakeyi,har yanzu kana tare dasu,da idona nagani kuma na shaida,hakan ya tabbatar mun da cewar a hotel ka kwana kai da karuwar daka ajiye tana biya maka buƙata,tunda ni ban isheka ba….’

Hankalin abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,a ruɗe yace”abu bangane akan me kike magana ba!dan Allah ki fahimtar dani!”

Cikin shesshekar kuka ta sake maimaita mashi abunda tace

Hannu ya aza akai yana fadin”innalillahi’wa inna ilaihirraji’un! Ya Allah kasa mafarki nake yi ba gaske ba,abu yau ke da kanki kike jifa na da waɗannan munanan kalaman!abu bani kika gani ba,wlh bani bane ni ban yi mu’amala da wata mace ba,ban haɗu da kowa ba,waɗanda kika gani acikin motar nan bani bane, wasu ne can daban,idanunki ne suka gwada maki ba dai dai ba….’

A tsiwace tace”Abusufyan!nagama yarda dakai,saboda kai maƙaryaci ne kuma fasiƙi mazinaci…….’

Bai bari taƙarasa maganarba afusace ya kwashe ta da mari,dafe kuncinta ta tayi ko gizau batayi ba taci gaba da cewa”Ni ka mara da hannunka saboda na faɗi gaskiya?koda yake yanzu har buguna ma zaka iyayi ai saboda ka samu wadda tafi ni,’

Kallonta yake yi yayin da idanunshi sukayi jawur jikinshi har rawa yakeyi saboda tsananin 6acin ran da ta sanya shi,

Muryarshi akausashe yace”Abu kada ki sake kirana da mazina ci!ban ta6a aikata zina ba arayuwata,ko sunanta bana son inji an ambata balle har nayi yunƙurin aikatata,wlh kika ƙara kirana da sunanta saina sa6a maki……’

duk wannan budurin da akeyi Hajiya da haris basu sani ba,saboda akwai tazara tsakanin bedroom ɗinsu abusufyan da kuma inda suke,

 

Harara ta wurga mashi har lokacin hawaye naci gaba da zuba a idanunta huci kawai takeyi saboda 6acin rai,

daƙyar ta iya furta”Ka sake ni!saboda bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba!kayi mun alƙawarin cewa zaka daina mu’amala da mata,kuma har rantsuwa kayi da al’qur’ani cewa in har ka sake kula mata,zaka sake ni saki uku!!!’

Tsananin 6acin rai da takaici yasa abusufyan ya fashe da matsanancin kuka yana cewa”Zainab baki a cikin hayyacinki!wlh ba ke bace,nasan cewa ba yin kanki bane,aljanune suka shiga jikinki,”

“Abusufyan ka sake ni!in ba haka ba zan illata kaina kowa ya rasa,”tayi maganar babu wasa a fuskarta,

“Wlh bazan sake ki ba abu,bazan iya ba,saboda ni banyi maki laifin komai ba,zargina kawai kikeyi amma baki da shaida akaina,dan Allah abu kidaina wannan maganar zuciyata zata iya bugawa in mutu,kiyi haƙuri mu sasanta tsakaninmu nasan zaki fahimce ni,’

Babu alamar sassauci a fuskarta,tamkar yana ƙara tunzurata haka taci gaba da faɗin ya sake ta,

Ganin yaƙi sakinta yasa ta mika hannu tare da janyo drawer chest,sabuwar reza ta ciro daga cikin drawer ɗinta,

Hankali tashe abusufyan yace”me zakiyi da ita abu?

Fuskarta aɗaure tace”zaka sake ni ko bazaka sake ni ba!” shi kanshi sai da ya tsorata da yanayin yadda take magana,ganin yadda hijabin jikinta ya jiƙe sharkaf da zufa,kuma babu zafi aɗakin nasu,ga idanuwanta sunyi jawur dasu luhu luhu,jikinta kuma sai kerma yakeyi,

Cikin sanyin murya yace”Abu pls ki saurare ni,zan fahimtar dake..kinsan ina sonki bazanso abunda zai cutar dake ba,bazan iya cin amanarki ba abu,

damƙar hijabin jikinta tayi tare da cireta tayi wurgi da ita gefe guda,a fusace ta Sanya rezar nan abakin  tafin hannunta na dama,ta tsarga wurin nan take jini ya soma tsastsafowa daga wurin

Agigice abusufyan ya yunƙura zai kwace rezar hannunta,dakatar dashi tayi da cewa”Idan har ka kuskura ka matso zan kashe kaina ne!”

Cikin shessheƙar kuka Abusufyan yashiga yi mata magiya yana roƙonta akan ta daina tsaga jikinta amma kamar yana tunzurata ne,

Saboda taurin kai da kafiya irin nata ko zafin rezar bata ji ajikinta,kafin yayi wani yunƙurin abu ta sanya rezar asaman wuyanta ta shiga tsarga wurin jini ya shiga bulbulowa,

A wannan lokacin ne abusufyan ya furta mata saki har ukku batare da saninshi ba,saboda tsoran karta kashe kanta,a gigice yace”ABU NA SAKE KI!NA SAKE KI!NA SAKE KI,” 😭

 

Adai dai lokacin Hajiya da haris suka faɗo dakin kamar an jefo su,sakamakon Sautin ƙarar da abu ta saki da kuma kukan da abusufyan ya saki na fitar hayyaci,zubewa tayi saman gadon asume tana billayi saboda radaɗin rezar daya shigeta,

 

Gaba daya suka rufar mata suna ambaton Sunanta suna tambayar meya faru,a lokacin shima abusufyan ya yanke jiki asaman gadon ya sume,

 

Bayan wannan lokacin sai da abu tayi jinya agadon asibiti,inda Allah yaso rezar bata shiga cikin wuyan sosai ba amma ta tsaga fatar wurin sosai,

 

Bayan an sallameta sun dawo gida anan fa suka hadu su duka a falon gidan don jin abunda ya haddasa faɗan daya shiga tsakaninsu,Zainab bata 6oye komai ba ta basu labari hada sakin da abusufyan yayi mata,hankali atashe Abusufyan ya shiga rantsuwar cewar shi bai sake ta ba,saboda baya acikin hayyacinshi baisan ya furta mata ba,gaba dayansu babu wanda baiyi takaicin faruwan wannan al’amarin ba,musamman mahaifinta baba buzu,tun daga ranar da aka sallameta daga asibiti ko kallonta bai ƙara yi  ba,in ma tagaishe dashi bai amsawa,ta 6ata mashi rai sosai,bai ta6a tunanin abu zata aikata abunda ta aikata ba saboda kishi daya rufe mata idanunta,

 

Abusufyan kuwa har ciwon zuciya sai da ya kusa kama shi a wannan lokacin,ba arziƙi hajiya Ameena tasa aka fitar dashi ƙasar turkey,wurin wata aminiyarta kuma abokiyar kasuwancinta,hajiya maimunatu dake zaune acan instanbul,a wurinta yaci gaba da zama,ta nisanta shi da nigeria ne saboda ta gusar da damuwar dake ƙoƙarin haddasa mashi Ciwon zuciya,

 

Bayan abusufyan ya koma ƙasar turkey da sati guda kacal,sai ga sayyadi yazo yi ma Abu jajen mutuwar aurenta,tun abakin gate ɗin gidan baba buzu yayi mashi korar kare,wannan abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yayi ba,

 

Ana haka kuma abu ta koma yar gidan jiya,soyayyar sayyadi ta dawo sabuwa fal acikin ranta,ko bacci bata iyayi batare da tayi mafarkinshi ba,ko sallah takeyi sai ta dinga kawo zancenshi acikin zuciyarta,Tashin hankali,zuciyarta ta dinga azalzalarta akan son ta sanyashi acikin idanunta gashi an hanata fita ko nan da bakin gate bata iya zuwa saboda mahaifinta dake fushi da ita,da zarar ya ganta awaje zai nufeta afusace da nufin ya bugeta sai ta watsa da gudu ta koma ciki,hajiya da alhaji nuraddeen har haƙuri suka bashi akan komai ya wuce amma yaƙiyi,burinshi ya damƙeta a hannunshi yayi mata mugun bugu,don ya huce haushinta da yake ji,Abu ta ƙumsa mashi baƙin ciki sosai,

 

Ana haka,wata rana ƙawar abu ta islamiyyarsu wadda suke kira da Maryam ta kawo mata ziyara acikin gidansu,

A falo suka fara gaisawa dasu mommy kafin suka shiga cikin ɗakin abu,anan take sanar da ita cewa Sayyadine ya aiko ta a 6oye don ta kawo mata wayar da zasu dinga gaisawa dashi,’hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma abu ba,

Nokia ce ƙarama maryam ta ciro daga cikin handbag dinta ta miƙa ma Abu,cike da farin ciki ta kar6i wayar,

Tafiyar maryam ke da wuya,sai ga kiran sayyadi ya shigo cikin wayar,jiki na rawa ta ɗaga kiran tare da yi mashi sallama,

ko amsa sallamar baiyi ba yace”Hmmmm abu kenan!yanzu kin tabbatar da abunda nake faɗa maki akan Abusufyan ko?ae tun farko saida naja kunnanki akan ki rabu dashi ba mutumin kirki bane amma kika ƙi jin maganata,’

Abu tace”dan Allah mubar wannan maganar,ni ko sunanshi ma bana son ji,yanzu kaine araina,banda burin daya wuce muyi aure yanzu,dan Allah sayyadina ka turo gidanmu asanya ranar auranmu,’

Dariya sayyadi yayi kafin yace”kin manta da cewa idda kikeyi yanzu,”

Cike da damuwa abu tace”Nasani,amma ni bansan ya zanyi ba,so nake kawai mu kasance atare amatsayin ma’aurata,”

Shu’umin murmushi sayyadi ya saki aranshi yace”yarinya kinzo hannu,”

A fili kuma yace”yanzu ya za muyi abu?nikaina aƙagare nake da naga wannan lokacin,na ƙosa naganki amatsayin matata uwar ƴa’ƴana kuma,”

Suna cikin wayar yunƙurin amai yazo mata,da gudu ta miƙe tare da faɗawa cikin toilet wayar na ahannunta,ta karasa gaban fanfo tana kwarara aman,

Hankalin sayyadi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abu na amai,wannan ya tabbatar mashi da cewa Akwai Cikin abusufyan ajikinta,kuma muddin ya bayyana kowa ya sani babu shi babu abu,kafin ya cimma burinshi za’a ɗauki tsawon lokaci ne,

Kunna fanfon tayi,ruwa ya zubo ta ɗebo tana kuskure bakinta da ɗayan hannun,

Bayan ta kammala aman tadawo ɗakin a gefen gadon ta zauna sannan ta mayar da wayar a kunnanta tace”kayi hakuri sayyadina,wlh bana jin daɗin jikina ne,”

Muryarshi har kerma takeyi wurin cewa”Faɗamun Abu!kamarya kike ji ajikin ki”?

Abu tace”zuciyata ce ke tashi,ga wata irin kasala da nake ji…..’

Tun kafin ta ƙarasa maganar sayyadi ya katse ta da cewa”Abu!banason ki fada ma kowa yanayin da kike ji ajikin ki!kinji ko”?

Amsa mashi tayi da toh bazan faɗa ba,

Yaci gaba da cewa”Ni zanyi maki maganin lalurarki,addu’a kike buƙata,insha Allah yanzu bada jimawa ba,zaki ji sauƙi ajikinki,”

‘Nagode sosai,”ta fadi kafin ta kashe wayar ta koma ta kwanta,

 

Kafin wani lokaci abu ta daina jin tashin zuciyar da take ji,kasalar nan duk babu ita komai ya dawo mata dai dai,har abu ta kammala iddarta babu ciki ajikinta,kuma aranar data kammala iddar aranar sayyadi yazo neman auranta wurin baba buzu,tun abakin gate baba buzu yace”meya kawoka gidan nan!”

Sayyadi yace”Naji cewa abu ta kammala iddarta,shine nazo neman auranta a wurinka,dan Allah kada ka hanani,tunda dae yarinyar nan ta nuna tana sona,kabarni kawai muyi auranmu,nayi maka alƙawarin zan kula maka da ƴarka,’

Wani irin kallo baba buzu yayi mashi kafin yace”har abada bazaka ta6a auran abuba,indai har nine ubanta,muddin ina numfashi bazan ta6a aura maka ita ba,”

Shu’umin murmushi sayyadi ya saki tare da jinjina kanshi yace”Idan kuma baka araye fa?ka isa ka hanani auranta?

Shiru baba buzu yayi yana kallonshi,dariya sayyadi yayi yana girgiza kai yace”shiyasa tun farko naso ace ka bini ta lalama ka auramun ita,amma saboda taurin kai da kafiya irin taka,yasa ka hanani auran abu,har marin abu kayi saboda ta sanya hannu ta mari abusufyan,sannan kayimun korar wulaƙanci saboda nazo wurin ƴarka,dama tara ka nake yi,yau zaka mutu baba buzu,kuma a sati mai zuwa zan auri abu,’_

Gabanshi ne yayi mugun bugu jin abunda sayyadi yace,nan take jikinshi ya shiga kerma yana rawa,wata irin zufa ce ta shiga gangarowa daga cikin ƙofofin hudar gashin jikinshi,

Muryarshi na kerma yace”Wanene kai!ka faɗamun!meyasa kake son abu,saboda me ka shiga rayuwarta!”

murmushi sayyadi ya saki tare da takawa ya matsa dab da Baba buzu suna fuskantar juna yace”Ni ba rayuwar zainab na shiga ba!rayuwar abusufyan nashiga,bansan zainab ba,abusufyan nasani!shisshiginka da bin ƙwaƙƙwafinka yau sun ja maka zaka rasa ranka baba buzu!kana tunanin cewa bansan bibiyata da kakeyi ba?don kawai kasan wanene ni!da wata manufa nake son ƴarka!shiyasa ba’ason mutun ya tsananta bincike wala tajassasu,da alama bakasan da hadisin ba,koda yake kaifa babu ilmin addini akanka…….’

Tunda sayyadi ya soma magana,baba buzu ya dinga jin tsigar jikinshi na tashi,tamkar ana tsige gashin jikinshi,nan take ya zube saman guiwarshi,idanunshi sukayi jawur muryarshi na rawa yace”Kada ka kashe ni,ka barni da raina!inason nasake ganin abu a idanuna,”

Fashewa da dariya sayyadi yayi tare da cewa”zaka iya ganin abu amma a lokacin da dukkan wasu kalaman bakinka suka daina aiki,ko uffan ba zaka iya furta mata ba,sae dai ka bita da ido kafin azare ranka,sannan kuma inaso nayi maka wani albishir baba buzu,Abu tana ɗauke da cikin Abusufyan,amma na 6oye hakan,zata haife shi ne acikin gidana kuma amatsayin ɗana…..’cike da shaƙiyanci sayyadi ke maganar,

Jin cewa abu nada ciki yasa baba buzu jin hawaye na sauka a idanunshi,dama yaji ma yana mamakin yadda akai babu ciki ajikin abu,ashe sayyadine ya kwantar da cikin don karsu gani su hanashi auranta,”

“Kaji tsoran Allah!kada ka cutar mun da ƴata!don Allah ka fita daga rayuwarta,wai lafin me mukayi maka ne?menene haɗinka da rayuwarmu,Ni da abu bamu ta6a cutar da kowa ba,mun taso mu biyu muke rayuwa bamu da kowa,Na roƙe ka akan ka ƙyale mun ƴa ta,koda zaka kashe ni amma kada ka ta6a abu,’

Bakomai zai baka mamaki ba face yadda ɗai-ɗaikun mutane ke giftawa a wurin amma babu wanda hankalinshi ke kaiwa wurinsu,hatta haris sai da yazo ya wuce ta gate ɗin gidan amma bai kai idonshi wurinsu ba,kuma wannan duk aikin sayyadine,

Juyawa sayyadi yayi ya nufi rugwagwar mashin ɗinshi dake ajiye inda yayi parking dinshi hawa yayi sannan yana kallon baba buzu yace”Zanyi amfani da abu ne don in ƙuntata rayuwar abusufyan,zan kuma yi amfani da yaron da abu zata haifa don in tarwatsa farin cikin zuri’arsu kamar yadda suka tarwatsa farin cikin namu family ɗin,nabarka lafiya,”yana ƙarasa maganar tashi ya tashi mashin ɗin da gudu yabar anguwar,

Barin unguwar tashi ke da wuya baba buzu ya yanke jiki ya faɗi,yana mirgina mirgina a ƙasa,kumfa na fitowa daga bakinshi,sai lokacin mutane suka dawo hayyacinsu suka lura da baba buzu dake kwance yana ta harba ƙafafunshi,

Lokaci guda mutane suka taru a kopar gidan sukayi dandazo suna kallonshi wasu na tambayar lafiya,wasu kuma nayi mashi addu’a,kafin su yanke shawarar kiran wani acikin gidan,

Koda aka sanarma su hajiya ameena abunda ke faruwa jiki na rawa suka kwaso gaba dayansu suka zo wajen gate din gidan,

Lokacin da abu tayi arba da mahaifinta dake kwance ƙasa yana ta birgima,zukunnawa tayi agabanshi tana jijjiga jikinshi tana faɗin’baba baba…meya faru dakai!baba dan Allah ka tashi….wayyo Allah na,nashiga uku……’haka ta dinga sambatu tana jijjiga,bawan Allah sai ƙoƙarin buɗe baki yake yi don ya sanar mata da cewa sayyadi ba mutumin kirki bane,kuma tana ɗauke da cikin abusufyan amma hakan ya faskara,anan dae rai yayi halinshi,baba buzu ya riga mu gidan gaskiya………’

A ranar abu kamar ta zauce saboda tsabar tashin hankalin rashin mahaifinta da tayi,haka hajiya Ameena da alhaji babu wanda baiji mutuwarshi ba,sun jima suna tunanin menene yayi silar mutuwarshi amma basu gano hakan ba,kowa ranshi na bashi cewa kamar guba ce saboda wannan kumfar da bakinshi ke fitar wa,

One week da rasuwarshi ko zaman makoki ba’a kammala ba,abu ta bijiro da maganar auran sayyadi,babu wanda baiji haushinta ba,don hajiya kamar ta rufe ta da bugu,a ƙarshe dae Alhaji nuraddeen ne ya goya mata baya,dama shi ya yarda da sayyadi kallon mutumin kirki yake yi mashi,

Batare da 6ata lokaci ba,aka ɗaura auren abu da sayyad’

Kunji yadda akai Abu ta shiga gidan sayyad da cikin abusufyan,aurensu ko One month bai cika ba sai ga ciki ya bayyana ajikinta kuma cikin ba ƙarami ba,yayi watanni,nan fa mutane suka soma tsegumi akan cikin nata,abun ya ɗaure masu kai,aure ko wata baiyi ba ciki ya bayyana,dama ƙarami ne cikin da sauƙi,amma wannan cikin da girmanshi fa,ya haura 4 months,

 

Tun zuwan da tayi gida,wurin Hajiya ameenatu don ta gaishe da ita,kallo daya hajiya tayi ma cikin nata,ranta ya bata cewa cikin abusufyan ne!duk da lokacin da suka rabu da abusufyan babu ciki ajikinta babu alamarshi,

 

“Abu wannan cikin na jikin ki,kamar na abusufyan ne!raina yana bani haka,dama mutane na kawomin tsegumin cewa cikin jikinki yayi saurin girma daga yin aure ko wata baiyi ba sai  ya bayyana kuma da girma har haka”?

Tur6une fuska abu tayi tare da cewa”Mommy dan Allah kidaina maganar nan,taya za’ace cikin abusufyan ne?idan cikinshi ne meyasa bai bayyana ba tun lokacin da muna tare dashi,sai bayan watanni kuma har nayi aure sannan zai fito”?

Hajiya ameena tace”abu kenan,kika san ikon Allah?koda yake ba zanyi maki gardama ba,amma ni raina na bani cewa cikinshi ne,Amma zamu zuba ido muga lokacin da zaki haife shi,in har cikin nan yayi wata tara toh na sayyadine,amma in har kika haifeshi nan da 5 months,to na Abusufyan ne,’

Muryarta tamkar zatayi kuka tace”Mommy nifa ba cikin abusufyan bane!na sayyadine,dan Allah mudaina maganar nan,’

Hajiya tace”naji zan bar maganar amma ina nan ina zuba ido,kuma in aka haifi yaron zamu je ayi mashi gwajin jini don a tabbatar da yaron wanene shi…………’

Bayan abu ta koma gida cike da damuwar abunda mommy ta sanar mata,sayyadi na dawowa ta kwashe duk abunda suka tattauna ita da hajiyarsu ta sanar mashi,

Aikuwa tun daga ranar bakin mutane ya mutu murus,babu wanda ya ƙara tanka mata game da cikin dake a jikinta,abun ya ɗaure mata kai,sa6anin da da mutane ke tsegumin ta amma yanzu ko maganar cikin babu maiyi,

Kuma tun daga ranar Hajiya Ameena,ta fara samun ta6in hankali,na yawan mantuwa,yawan sambatu ita kaɗae da dai sauransu,a ƙarshe ma taji ta tsani zama a kano gaba ɗaya tamkar korarta ake,haka ta tattara ta koma katsina da zama,dama suna da katafaren gidansu acan wanda suka bari amma duk in suka zo garin a gidan suke zama,ita kaɗae ta koma gidan tana rayuwa acikinshi,tare da mai aikinta,kafin daga baya haris ya dawo wurinta,mahaifinsu kuma yana zuwa akai akai don ya dubasu,

 

After 5 months

 

A tsakar dare naƙuda ta taso ma abu,gashi ita kaɗae ce a gidan babu kowa,sayyadi bai dawo ba,dama wani lokacin in ya fita sai tsakar dare yake dawowa kamar aljani,

 

Tun daga saman gadon ta faɗo ƙasa tana faman dafe cikinta tana cizon la66anta tana kuma ambaton sunan Allah abakinta,sosai cikin ya shiga murɗa mata tare da matsanancin ciwo.

 

 

Daga ƙarshe ta zube anan wurin,bata tashi farkawa ba sai asaman gadon asibiti,kukan jariran da ta haifa ne suka tashe ta daga dogon baccin daya ɗauketa sakamakon allurar baccin da Dr yayi mata,a hankali ta buɗe idanunta ta ware su akan fuskar sayyadi dake tsaye hannunshi ɗauke da jariri naɗe acikin towel,murmushi ya sakar mata tare da cewa”Barka da sauka my wife,ina tayaki murna kin haifa mana kyawawan ƴa’ƴa,” yunkurawa abu tayi ta miƙe daga zaune tana kallon yaran dake jere a gefenta guda biyu nade cikin towel ga kuma ɗaya a hannun sayyadi,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,saboda tsabar murna bakinta yaƙi rufuwa,muryarta na kerma tace”Wannan duk nawa ne?ƴa’ƴana ne ni kaɗai”?

sayyadi yace”namu dae,naji kina cewa duk ƴa’ƴanki ne,bayan duk ƙoƙarin nawa ne,nakudarsu ne kawai kikayi,”cikin zolaya yayi mata maganar,

Hannu tasa tare da daukar ɗaya daga cikin jariran ta buɗe fuskarta tana kallonta,gabanta ne taji ya faɗi rasss! ganin jaririyar na kama da Abusufyan,maimakon taga kamanninta kona sayyadi a fuskar yarinyar sai taga fuskar abusufyan,

bin fuskarta da kallo sayyadi yayi ganin kamar tana cikin damuwa yace”meya faru ne?yanzu fa naga kina farin cikin samun ƴan uku,lokaci guda kuma naga kin canza?

“Babu komai,”ta bashi amsa muryarta a kasalance,

 

Haihuwar tazo mata cikin sauƙi,a ranar aka sallame ta,suka koma gida,bakomai yafi damun abu ba face yadda mutane suka ƙi zuwa yi mata barkan samun ƴan uku,ko leƙo gidanta babu wanda yayi,tayi tsammanin danginshi zasu zo amma abun mamaki babu wanda ya leƙo da sunan ɗan uwanshi yazo duba yaranta,jikinta yayi mugun sanyi,duk taji ta tsani kanta,amma daga ta kalli ƴan ukunta sai taji farin ciki aranta,suka dae ne dangin da take dasu aduniyar nan,su take gani taji daɗi aranta,lokacin da yaran suka kai wata ɗaya aduniya,aranar wata ƴar uwarshi tazo kawo mata ziyara,ita ta taimaka wurin yi mata wankan jego,da kuma yi ma yaran wanka,duk yadda abu taso taja ta da fira don taji a ina suke da zama suna da dangi,amma matar nan da shegen wayau ko uffan bata ce mata ba,a haka har suka kammala wankan jegon matar ta koma garinsu,

 

Abu ba ƙaramar wahala tasha ba,wurin rainon ƴan ukunta,babu mai taimakonta,itace yi masu wanka har sau biyu arana safe da kuma dare in zata kwantar dasu,wankin kayansu da suka 6ata,ɗawainiyarsu da kuma ɗawainiyar kanta,abun duk ya jagule mata,ga sayyadi ko tsinke bai ta6a sanya hannu ya kawar mata ba,bayan kafin suyi aure shi da kanshi yake sanar da ita cewa in sukayi aure duk ranar da yake hutu bai aiki har girki sai yayi mata ashe duk ƙaryace yake yi mata,Abusufyan kuwa muddin yana agida bai barinta tayi aiki,sai dai yayi shi kaɗae ko kuma suyi atare,da kanshi yake cewa”Abuna idan har kika haifa mana ƴa’ƴa ni da kaina zan dinga yi masu wanka,idan mata ne zan dinga sharce masu gashin kansu ina gyara masu shi,bazan bari kisha wahala ba,’in ta tuna waɗannan kalaman nashi sai ta fashe da kuka,dama ita dana sani bata da daɗi,Allah ka rabamu da aikin dana sani,Amin

 

Kunji yadda akai Abusufyan ya auri abu,da kuma yadda akai yabar nigeria da kuma yadda akai ta haifi ƴa’ƴanshi agidan wani wanda ya taso amatsayin ubansu,

 

💋Boss Bature💋

 

Lokacin da Abusufyan yakai ƙarshen labarin nashi sai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin yaro,cikin sauri Abba ya janyoshi jikinshi yana lallashin shi,bashi kaɗae ba hatta su fawan,jabeer,irfan,khaleed dasu twins sai da idanunsu suka cicciko da kwalla,Sgr da Omar kuwa jinjina kai kawai sukeyi,Abbas ne yace”Yanzu ina ƴa’ƴan suke?suna raye ko sun mutu ne”?

“Nima abunda nakeso na tambaya kenan,”acewar hajiya azeema da jikinta ya gama mutuwa,kowa mamakinshi ta yadda akai waɗannan abubuwan suka faru batare da Abusufyan da kuma goggon katsina sun sanar ma kowa ba,

cikin sanyin murya Abba yace”ka faɗa mana ina ƴa’ƴan suke yanzu”?

ɗagowa abusufyan yayi da idanunshi waɗanda sukayi jawur yace”ni kaina bazan iya cewa ga inda suke ba,a lokacin can baya ina bibiyar rayuwarsu,ta hanyar haris shiya kira ni a waya yake sanar dani cewa abu ta haifi ƴa’ƴa kuma yaran dani suke kama sosai,tun daga lokacin na sanya shi akan ya dinga bibiyar rayuwar yaran yana sanar dani duk wani abu dake faruwa arayuwarsu,shine yake turo mun da hotunansu ina ganinsu a wulakance,yara ne mata guda ukku wani lokacin babu kallabi a kawunansu kuma babu takalma a ƙafafunsu,tun lokacin nake tsananin jin tausayinsu,kuma raina yake bani cewa tabbas ƴa’ƴana ne su…..saboda akwai wani lokaci da nazo nigeria zuwan bazata batare da sanin kowa ba………….”

 

Bai ƙarasa maganar ba suka jiyo muryar goggon katsina tana sambatu tana cewa”ƙarfen nasara ba tabbas,Allah ka tsine ma baturen daya ƙirƙiri motar harisu,shegiyar motar kamar da katako akayita,tun safe muke a hanya take ta bamu matsala mtsswwwwww haba ina dalili,tafiya daga katsina zuwa abuja sai kace mutun zashi saudia a ƙasa?ae dana san haka zata faru da a kafa na tako wlh,shegen maƙo irin nashi,maimakon ya biya mana kuɗin jirgi,ya nace sai mun hau waccen rugwagwar motar tashi……….’kasa ƙarasa maganar tayi ganin yadda matasan gidan suka taru a falon gidan,ga kuma Abusufyan ɗinta dake ta faman sharar kwalla,

Don bala’e,a hannu ta ruƙo zaninta daga ita sae dogon undi fari ajikinta,ta cire zanin gaba ɗaya,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,da alama,

Tsayawa tayi cak baki asake tace”Na shiga uku ni yau,abun dae ba sa’a,Allah yasa dae ba wani ya mutu ba,wlh yanzu inyi kwana in koma katsina don ni ban shirya ganin gawa ba,dan Allah ku faɗa mun maiya faru”?

Miƙewa sukayi gaba dayansu suna kallonta cike da tuhuma,adaidai lokacin kuma Dr haris ya shigo tare da Saude,suma duk suka tsaya cirko-cirko ana kallon kallon,

Koda Abusufyan yayi arba da goggon katsina,jiki na rawa ya tunkareta,tare da faɗawa jikinta ya rungumota sosai yana cigaba da kukan,

Nan fa hankalin goggon katsina ya tashi,hannu bibbiyu tasa tare da ɗago da fuskarshi daga jikinta tana cewa”Abusufyan ɗina meya faru?meyasa kake kuka?kai da zanga kana farin ciki?ko Omar bai nuna maka ƴa’ƴanka bane…..?

cike da mamaki kowa ya zuba ido yana kallonta,Abusufyan dake kuka nan take ya dakatar da kukan nashi yana cewa”Mommyna…ina abu take ne?ina yaran da ta haifa suke?suna ina?

Bata bashi amsa ba,sae ta kalli Omar dake tsaye yana kallonsu tace”Omaru ina kakai mashi ƴa’ƴanshi ne?yaran nan fa da kazo dasu gidana ƴa’ƴan abusufyan dina ne dama saida na faɗa maka,dan Allah ku nuna mashi ƴa’ƴanshi ya gansu yaga yadda suka girma ko hankalinshi ya kwanta banson ganinshi yana kukan nan”

Tashin hankali!

Nan fa kowa ya ruɗe yana tunanin su wanene yaran da gwaggon katsina take magana akai,

“Gwaggo kina nufin cewa hosana da jahad ƴa’ƴan abusufyan ne!”?Omar ne yayi mata tambayar fuskarshi ɗauke da mamaki,

goggo tace”Eh mana,sune ƴa’ƴan abusufyan ɗina,suna ina ne…..’

Kafin wani ya buɗe baki ya ƙara magana,sai ga Jahad da hosana sun fito da gudun gaske jin muryar gwaggon katsina data karade gidan,tana ganinsu ta washe baki tana cewa”Yawwwa ga ƴa’ƴan abusufyan ɗina nan sun ƙaraso,maza ku ƙaraso in rungume ku ajikina,’

ƙarasawa sukayi tare da faɗawa jikinta,ta hada su duka ta rungume ajikinta,tana ta faman murmushi,

Fawan ne yace”Anya gwaggo tasan me take cewa kuwa?taya waɗannan yaran zasu kasance Ƴa’ƴan uncle ɗinmu?hakan na nufin cewa Sehrish itama ƴar shi ce kuma,su jinin mu ne?

Download>>> Jinin Sarauta Complete Document

Cikin sanyin murya abusufyan ya juya tare da kallon fawan da yayi maganar yace”Tabbas su ƴa’ƴana ne!nasan zakuyi kokwanton maganarta ne saboda tana da ta6in hankali,to inaso ku sani cewa mommyna tana acikin hayyacinta,tasan me takeyi duk da akwai ta6in hankalin atare da ita,amma ba kowane lokaci bane take kasancewa dashi ba,’

Jin maganarshi yasa Hosana da jahad suka juyo suna kallonshi yayin da zuciyoyinsu ke cigaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi,

Kowa fa ya shiga ruɗani,wasu ma saboda tsabar mamaki sun gaza magana,irin su Sgr da kuma su Jahan,

“Yanzu duk ba wannan ba!dole muji ya akai kasan cewa su ɗin ƴa’ƴanka ne!kuma ya akai kuka bar rayuwarsu ta wulaƙanta batare da kun sanar mana ba!sannan dole muji ta bakin yaran game da irin ruƙon da wannan mutumin yayi masu!’acewar Abbansu junaid,ranshi a6ace yake maganar,

Gwaggo dae bata gane inda zancen nasu ya dosa ba,amma tana da tabbacin cewar abusufyan ya fasa abunda suka jima suna 6oyewa,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,dama ta gaji da 6oyon al’amarin da sukeyi,saboda ganin irin wahalar da yaran suke sha a hannun mugun mutumin nan,

Omar yace”Abunda ya kamata shine,yanzu naga anata kiran sallar isha’e yakamata muje muyi sallah,kafin mu dawo nasan gwaggo ta ɗan rage gajiya,sai mu zauna ayita taƙare kawai,in yaso sai jahad tayi mana bayanin komai tunda itace mai cikakken hankali acikinsu,Sehrish ita kanta bana tunanin tana acikin hayyacinta yanzu,

 

Kowa ya amince da maganar omar,batare da 6ata lokaci ba,suka wuje bedrooms ɗinsu domin yin alwala,hajiya azeema ce ta shigar da Gwaggon katsina cikin ɗakinta tare da saude kafin agyara masu inda zasu zauna,

 

Yau dae gidan Abban sojoji a hargitse yake,Wlh ni kaina a hargitse nake,sai addu’a kawai,

 

Abbansu na fitowa daga cikin toilet,junaid ya faɗo mashi acikin ranshi,nan fa gaban shi ya faɗi rasss,sae lokacin ya tuna da cewar babu junaid fa acikin gidan tun ɗazu,duk wannan budurin da akeyi babu shi acikinsu,

Hankalinshi amatuƙar tashe ya tunkari wayarshi dake ajiye saman side drawer ya dauketa,tare da lalubo numbar junaid ya danna mashi kira cikin sa’a wayar tashiga tana ringing amma ba’a ɗaga ba,kusan sau huɗu yana kira ba’a ɗagawa,

Download>>> Surbajo Complete Novel Document

Ana biyar ɗinne aka ɗaga wayar,kara wayar yayi kunnanshi yana cewa”Junaid ina ka shiga ne!!”shiru yaji ba’a tanka mashi na,nan fa yabi ya rikice,

“Junaid wai baka jina ina magana ne?bazaka amsa mun ba?junaid kodae wani abu ya faru da kaine?

Nan ma shiru ba’a bashi amsa ba,

Muryarshi tamkar zaiyi kuka ya kuma cewa”don Allah babyn Abbanshi kayi mun magana mana!

Muryar mace ce ta amsa mashi da cewar”ka duba whatsapp ɗinka,zaka ga video mun tura maka,”

Jikinshi har kerma yakeyi wurin katse kiran ya shiga whatsapp ɗinshi,new number ya gani tayi mashi message da video,

Saboda tsabar fargaba,tun kafin ya buɗe video ɗin zufa tashiga gangarowa a fuskarshi,dukkan ilahirin jikinshi ya shiga yin kerma,idanunshi sukayi jawur tsoranshi kar a videon yaga junaid cikin wani yanayi,bazai iya jurar wannan ba,

Runtse idanunshi yayi yana karanto addu’o’i abakinshi,kafin daga bisani ya daure ya cije ya buɗe videon,

Zazzare idanunshi yayi waje tamkar kwayar idanunshi zata faɗo ƙasa,

A ƙarshe kuma ya fashe da dariya,tare da zubewa saman guiwowinshi yana tikar dariya,

Bakomai bane acikin video ɗin nan ba,face Mommynsu junaid Alexandra rungume da junaid asaman gado,suna kwance abunsu,da alama ma kamar bacci yake yi ajikinta…….

Domin sauke Cikakken Littafin sai ku danna inda aka saka Download

Back to top button