Uncategorized

Lallai na yadda Annabi Muhammadu Shine fiyayyen Halitta-cewar Rani Mukherji sananniyar Jarumar fina-finan Indiya

Lallai na yadda Annabi Muhammadu Shine fiyayyen Halitta-cewar Rani Mukherji sananniyar Jarumar fina-finan Indiya

 Sananniya kuma dadaddiyar jarumar Masana’antar Bollywood wacce ta dauki Zamani mai tsayi tana jan zarenta,wacce ta lashe kyaututuka da dama a lokacin rayuwar ta a harkar fim ta fito ta yi wani furuci mai matukar ban mamaki ga me da fiyayyen halitta Annabi Muhammadu S.A.W duk da kasancewar ta mabiyiyar Addinin Hindu in da ta ce:

 “Annabi Muhammad mutum ne mai Nagarta wanda tun daga farkon samuwar ɗan Adam har zuwa yanzu babu mutum kamar sa, na shafe lokaci ina bibiyar litattafai masu dauke da tarihin sa tun daga kan rayuwarsa,har zuwa kyawawan halayensa, anan ne na gane cewa tabbas Annabi Muhammad mutum ne daya fi kowane dan Adam nagarta.” Inji Rani Mukerji.

 

Fitacciyar ‘yar gwagwarmaya daga Tamil Nadu, Sabarimala ta Musulunta

 Matar wani babban basaraken Yarbawa ta musulunta

 Olori Joyce Anene Balogun, matar Olubadan ɗin Ibadanland, Oba Lekan Mohood Balogun, ta ƙarbi addinin musulunci. Shafin LIB ya rahoto.

 Matar basaraken ta shiga addinin musulunci cikin watan Ramadan

 Olori Joyce Anene Balogun ta ƙarbi addinin musulunci a lokacin wata lakcar watan Ramadan wacce aka gudanar a ranar Litinin 25 ga watan Afrilu, a babban filin masallacin idi na birnin Ibadan ƙarƙashin jagorancin honorabul Ibraheem Akintayo.

 An tabbatar da shigar ta musulunci.

 Babban limamin jihar Oyo, Sheikh Abdul Ganiyy Abubakry Agbotomokekere I, ya tabbatar da labarin a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook, inda ya ƙara da cewa sabon sunan sarauniyar na yanzu shine Khadijah Mahood Lekan Balogun.

 Olori Joyce Mahood Lekan Balogun {Olori Olubadan ɗin Ibadanland} ta ƙarbi addinin musulunci a hannun babban limamin jihar Oyo mai girma Sheikh Abdul Ganiyy Abubakry Agbotomokekere a ƙaramar hukumar Ibadan ta Arewa yayin gudanar da lakcar watan Ramadan a babban masallacin Idi na Ibadan {Yidi Agodi Gate Ibadan} a ƙarƙashin jagorancin honorabul Ibraheem Akintayo {Sunan Olori na yanzu Khadijah Mahood Lekan Balogun.

 Ku cigaba da kasancewa da Tashar ta Aihausanovels domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku gami da littattafan Hausa, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

 Facebook Page

 Twitter Page

 Telegram Channel

Youtube Channel

 Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@Aihausanovels.com.ng

Back to top button