Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 11 Complete Novel

๐Ÿ… MATAR DAMISA ๐Ÿ…

(The Wife Of Tiger)

 

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ

ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ27 & 28.

Around 12:50 Junaid ya tashi daga baccin da ya kwashe shi tin sallar asuba, tashi yayi a kasalance yana duban agogon dake manne a jikin bango, yana jan ‘kafa ya nufi toilet brush yayi sannan ya had’a ruwan wanka mai ‘Dumi-d’umi ya yi wanka cikin kulawa after 30minute ya fito d’aure da white towel, tsayawa yayi a jikin mirrow kafin ya fara shafa cream d’insa mai shegen ‘kamshi ta ko’ina ya milmilka ya d’auki turare mai jikin Silva ga ‘kamshi kamar mai! Yana fesa jikinsa duk gidan sai da ya gauraya da wannan ‘kamshin turare (ma’abocin son ‘kamshi kenam) bayan ya gama da wannan ya d’auki kum yana taje suman kayin sa ya d’auki cream na gyaran gashi ya soma mulmulkawa daga suman gashin har zuwa sajen har d’an gemun daya bari shima yana bada nashi ‘kamshin, lips oil kumadu ya d’auko mai ‘kamshin chaculate ya mulka a saman maroon lips d’insa, nan fa lips d’in ya fara bada armashi yana she’ki (wal-wall) ๐Ÿ˜˜ jikin wardrobe d’insa ya nufa ya bud’e 6angaren Jeans da kuma T-shirts kala-kala sai da ya tsaya tunanin kayan da zai saka kafin ya kai hannu ya zaro wani dan’kararren Jeans skie blue sannan ya duba wata T-shirt wanda ya kasance shine mahad’insa mai zanen blue and white mai dogon hannun leaps, ya sanya kayan nan ga rigar ta kama jikinsa kayan tsaf sun kama jikinsa sosai gwanin sha’awa ya dubi takalmi white colour shima mai sawun ciki, gaskiya Yaron ya fito kamar kamar dai Indian man awesome, turare ya d’auka ya feffeshe kayan jikinsa da shi, ya kammala tsaff ya duba kan table zai d’auki phone d’insa wayam babu alamar sa saman bed d’insa yakai idonsa still ba waya ga gadon nan yayi kaca-kaca ba gyara daman Mom d’insa ce mai masa gyaran d’aki, tsayawa yayi yana nazarin wani abu kafin ya nufi hanyar fita a hankali yake taka stairs a falo ya tarar da Ayush zaune ta kafa ido akan TV star bata san da zuwan sa ba sai ji tayi ance “where’s my Mom?” atakaice ya yi maganar da sauri Ayush ta mi’ke tsaye tana fad’in “gud morning Sir” d’aga mata kai kawai yayi ya wuce ta gefen ta ya nufi d’akin Mom d’insa Ayush ce ta yi saurin tsayar da shi tana fad’in “am she went hospital” dakatawa yayi da tafiyar cike da mamaki yake furta “hospital? but Mom bata ta6a tafiya batare da tamun sallama ba, ko Ina bacci takan ajiye ‘karamin letter!” Kuma kafin ta tafi tana kai masa kayan breakfast..
Duk acikin ransa yake wannan jawabai, juyowa yayi yana facing d’inta ido ya ‘kura mata har sai da taji wani iri aranta sunkuyar da kai tayi ‘kasi, a hankali ya furta “tin yaushe ta fice” a d’an tsorace tace “in midnight”
Jinjina Kai ya yi yace “OK night duty”
Ya maida kallonsa kanta still yace “my phone โœ†” kallonnsa tayi a d’an rud’e tace “inside wardrobe” atakaice ta bada amsa
Jinjina kai yayi zai haura upstairs dakatawa yayi ya juyo yana kallonta yace “ke ce yarinyar da Mom ta kawo?” Amsawa tayi da “eh ni ce” Kai a sunkuye,
“OK je ki nemo mun abunda zanci am hungry”
Zaro ido tayi waje zuciyarta kuwa yana bugun uku3 tara9 ya had’ata da babban aiki domin tinda take bata ta6a shiga kitchen ba, ko natural tea bata iya had’awa ba balle azo ganjin girki
“Wayyo Allah na” abunda ta fad’a kenam acikin raanta, shi kuwa tin tinin ya haura upstairs ya wuce bedroom d’insa..
Jiki a sanyaye take tafiya ba kwari a haka ta shige kitchen, fuskar sa ne yake mata gizo domin ba’karamin kyau yayi ba, ga sajen nan ba’ki ‘kirin fuskar kuwa tayi fiyau sai hasken sa ya ‘Kara bayyana ga lips kuma sai she’ki yake, lokaci guda kuwa tasau kayataccen murmushi, sai dai kuma tana mungun jin tsoronsa ga kuma shakkarsa da takeji kwarjini yake mata ita har yanzu a Aljani take d’aukarsa bata yadda cewa mutum bane, tana cikin tunaninta ta dawo hayyacinta gata ga gass anan ta shiga taitayinta ko kunnawa bata iya ba! Tunanin mai zata dafa ta shiga yi kawai ta yanke hukuncin tayi indomie kawai
Murd’a gass tayi har sai da tayi highly d’isa sannan ta kunna ashana wani irin bond yayi wuta ne yake tashi da gudu taja da baya bata San yanda zatayi ta rage karfin wutar ba haka ta d’auko tower ta d’ora ta tsiyaya mangyad’a too much wutar nan haka yake shiga cikin tukunyar tsabar yawan da wutar yayi ga kuma ta zabga granut oil ta d’ebo ruwa cikin cup sau uku tana zubawa cikin tukunyar da 6are ledar indomie ta juye shima guda uku ta fasa eggs guda goma a cikin indomie d’in sannan ta Fara zuba Maggi da kayan had’in a ciki kafin ta kammala zuba Maggi har ruwan ya tsotse ya Fara ‘kona abincin ga eggs kuma a kwance saman indomie gasu Aunty Maggi kuma a saman eggs ko gaurayawa ba’ayi ba.
Ya salam kamar ‘kauri na soma ji kafin ta Ankara indomie kam ya ‘kone ga wutar gass kamar Wanda ake rura shi sai bin jikin tukunyar yake Ayush fa anaso a sau’ke pot kuma abu ya gagara ga jikin gass d’in kuma yad’au zafi sosai (ke Ayush kar fa kiyi musu gobara ๐Ÿ˜ณ )
Tsayawa tayi cak tana kallon tukunyar da abun cikin yake ta ‘konewa qauri ne ya gauraye gidan.
Jin motsin mutum a bayanta ne yasa ta waiwaya da sauri cike da tsoro da fargaba take bin Junaid da kallo Wanda shima ‘kaurin da ya jiyo ne yasa shi fitowa
Hannu yakai ya kashe gas d’in duk da yaji zafin wutar haka ya jure bai nuna ba
Ya sau’ke tukunyar da yayi ba’ki ‘kirin hannunsa har yayi jawur tsabar ‘Kunar wutar, ga kuma indomie fa shima yayi ba’ki ‘kirin gwanin ban kwad’ayi ๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹
Juyowa yayi yana kallon ta da sauri ta sunkuyar da Kai ‘kasi.
Juyawa yayi yakai hannu kan wata flass mai ruwan tea a ciki ya tsiyayi ruwan a jug ya had’a tea mai kaurin gaske ga yasha madara sai dai suger kad’an yasa saboda baya son suger sosai ya d’auki bread mai yanka-yanka rufaida bread dai,
Yayi had’insa a sau’ka’ke ya mi’kawa Ayush cup na tea da kuma bread shima ya d’auki nashi ya fice daga kitchen upstairs ya haura sai bedroom d’insa
Itama fitowa tayi ta zauna a kujerar falo da murmushi a fuskarta “wow godiya nake daman yunwa nima nake jii” Ayush ce tayi maganar tana d’an Kora tea tare da bread kunnenta har rawa yake tsabar had’in da yasha..

Shima ata 6angarensa yana cikin karyawa yayi dialing call number Mom d’insa amma sai dai switch up yayi tunanin idan ya kammala break zai samota a hospital domin bazai iya wuni baiga Mom d’insa ba abun alfaharin sa, yana cikin wannan tunanin yaji sau’kar message a wayarsa Wanda daman yana hannunsa bud’e sa’kon yayi (( *captain* *junaid* *sorry* *for* *your* *loss* *doctor* *fateemah* *she’s* *die,* *idan* *ka* *tuna* *da* *mahaifiyarka* *tana* *hospital* *kazo* *ka* *dauki* *gawarta* ))

Da sauri Junaid ya mi’ke tsaye yayi wurgi da wayarsa yana fad’in “whatttt my Mom, impossible” kafin kace mai gumi ya wanke masa ilahirin jikinsa da gudun gaske ya sau’ka falo ya wuce sai da Ayush ta tsorita kofin shayin ya zuba mata a cinya ‘Kara tayi jin zafin ruwan shayin a jikinta ..

Shi kuwa Junaid har ya fizgi motarsa ya nufi hanyar get da gudun gaske!
Shi da kansa ya sau’ka a motar ya bud’e get d’in bai tsaya sauraron mai gadi ba
Fincikar motar yayi sai tafiya hospital ga gida a wangame bai tsaya rufe get d’in ba………

Ga kuma mai gadi a cikin d’akinsa rai a hannun Allah, ya tsorita da ganin junaid a cikin Daren nan ga kuma jefo masa manya-manyan gardawa akai har su biyu, Allah sarki dattijon Allah………

Click Here To Read Matar Damisa Book 1 Complete Novel

 

Some of related Hausa Novels

*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*

*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

Back to top button