Harijin Sarki Page 38 The End Romantic Hausa Novel
Rana ta faɗi cikin salama.Iskar Amzir tana kaɗawa cikin sanyin da ke ɗauke da ƙamshin ruwa da sabuwar rayuwa. Masarauta ta canza gabaɗaya babu rawar jiki, babu tsoron duhu, babu sirrin tsafi.Ko da yake tarihi bai manta da Ameer ba, domin jama’a sun fahimci darasin babu iko sai na Allah.A yau shekaru goma sha shida ke nan da haihuwar Rayyan al-Nur.Masarauta ta shirya bikin godiya biki da ba a yi domin mulki ba, sai don yabo ga Ubangiji.Sultan ya zauna a kan kujerar sarauta, yana kallon jama’a cikin natsuwa da murmushi mai zurfi.Samha kuma tana gefensa, cikin shigar alfarma mai launin shuɗi, idonta na ɗauke da hasken da ya fi duk wani lu’u-lu’u daraja.Rayyan ya fito cikin farin Kaftan mai launin haske, hannunsa riƙe da tasbihi da mahaifiyarsa ta koya masa tun yana ƙarami.Sai ya tsaya a tsakiyar fada, ya ɗaga kai sama, yana cewa da muryar da ta cika da nutsuwa da ƙarfin ruhi:“Babu abin bautawa face Allah, Shi ne hasken sama da ƙasa. Duk wanda ya dogara ga Shi, zai haskaka koda duniya ta narke da duhu.”Cikin mamaki da natsuwa, rana ta tsaya a sararin sama, kamar tana sauraron wannan ƙaramin sarki mai haske.Sai wata iska mai ɗan sanyi ta ratsa fadar, ta busa furanni, ta shafi kowa da annashuwa.Sultan ya durƙusa a gabansa, yana cewa cikin hawaye “Na ga abin da babu sarki ya taɓa gani. Haske ya mallaki sarauta, kuma ni na zama shaida.”Samha ta riƙe hannun ɗanta, tana kallonsa da murmushi mai cike da so tace, “Haske ba ya karewa, sai dai ya koma wurin mahaliccinsa. Ka zama mai gaskiya, ɗana, ka jagoranci duniya da addu’a ba da tsafi ba.”Rayyan ya kalli mahaifiyarsa da ido mai ɗauke da salama“Ummu, zan yi hakan, saboda ke haske ne, Abiey haske ne, kuma ni haske ne daga hasken Allah.”Daga wannan rana, masarautar Morocco ta zama abin koyi ƙasar da ta tashi daga duhu zuwa gaskiya.Rayyan ya zama sarki, ba domin iko ba, sai domin hidima.Sultan ya koma mai ba da shawara, yana ƙarfafa ruhi da ilimi.Samha kuwa ta ci gaba da zama garkuwar addu’a, mai tarbiyyar ɗanta da darasi na gaskiya.Komai ya shuɗe ya zama tarihi bayan wuya Hausawa suka ce sai daɗi Sultan ya samu lafiya duk wanni Tsafi dake dawainiya da harijancinsa ya karye ya zama cikakken lafiyayyen mutum idan yayi jima’i sau ɗaya ƙwaƙƙwara a dare ya isar masa har zuwa asuba idan ya kumayi to zai kaishi wani daren ba tare da ya buƙatu ba Ruhsa mahaifiyar Samha itama ƙarshenta yazo akan tafarkin data zaɓa na Tsafi da shirka ta mutu tana ƙasƙantacciya Jalila ta karɓi addinin Musulunci Najjisa kuma ciwon data ɗorawa Samha ya koma mata tananan tsayin shekarun nan ita bata mutu ba ita bata warke ba domin ciwon bashi da makari dama saidai ya komawa wanda ya aikoshi.A shekara ta sha 17 ne bayan haihuwar Rayyan Nur Allah ya sake azurtasu da samun haihuwar ɗiya mace suka sanya mata suna Harmdan sukaci gaba da rayuwarsu cike da farin ciki da kulawa da tattalin juna suna more rayuwarsu ta hanyar bawa juna lokaci su morewa daɗin junansu…….A ƙarshe, an rubuta a littafin tarihi “Haske ya ci duhu, saboda duhu baya iya rayuwa a wurin da gaskiya take” Rana ta faɗi cikin natsuwa, kuma Morocco ta shafe duhu har abada……. _Tammat bi hamdullah__Ubangiji yasa wannan saƙo da muka isar cikin hikima ya isa ga waɗanda suka karanta kuma ya tasiranci rayuwarsu, ina godiya insha Allahu bada jimawa ba zaku jini da sabon littafi MY MELON labarin Liyana yar ƙasar yar addinin Budha a ƙasar Thailand da Rashad bafulatanin ƙasar Senegal, shin meye burinsu kuma meye ya jefa Liyana a harkar karuwanci kace kace haka har take tsananin ƙiyayya ga wanda yazo mata da maganar aure?”_


