Zakuna Biyar Page 45 By Princess Teema
WS-HOSPITAL.Daurewa ya yi game da fara pretending, ya nuna kamar bai gane me take magana a kai ba, a dake ya ce. “Waye ya ce maki 55 babys ne a wajen dama?”. Karisowa in da yake ta yi, ta riko hannunsa tana faɗin. “They’re 55 sir, we already caunt them since before”……. Nan fa ya ji kansa ta ɗan buga, bai taɓa zatan irin wannan rana ba a rayuwansa, so bai shirya mata ba. Shiru ya ɗan yi yana tinanin solution, katse mashi shirun ta yi da cewa. “Ko dai wani ya sace babys ɗin ne? Na shiga ukuna!”.Ganin yadda hankalinta ya yi mugun tashi ne yasa ya jawota jikinsa, bai san lokacin da bakinsa ya kubce wajen ce mata. “Meyasa kika damu da yaran da ba naki ba?”……. Da sauri ta ɗago da kallonta a kansa. “Because i love them all, ina jin kamar babys ɗina ne, please my Dr, help me to find them out”. Ɗan gyaran murya ya yi, ya daidaita natsuwansa kafin ya ce. “Ba jiya na ce maki wasu babys ɗin basu da lafiya ba?”…….. Kai ta jinjina alamar e. “To shi ne aka kwashesu kada su raɓawa sauran yaran dake da lafiya ciwo, akwai wata sabuwar cutar da ta shigo mana ne, yanzu muna ƙoƙarin shawo kan cutar, maganin cutar kuka ga mun yi wa wannan darling ɗin naku ai, yanzu saura kwanaki kaɗan mu gama haɗa maganin cutar, daga nan darling zai dawo wajenku, sauran yaran ma za’a dawo da su, amma yanzu a kowani lokacin zamuna zuwa mu bincika yaran, dik wanda ya kamu da cutar zamu kwashesu mu kaisu safe room dan tsaron lafiyarsu har su samu lafiya”. Ya faɗa hakan ne kawai dan bashi da mafita, kuma bai yi tinanin lallai zasu jira ranar da zai dawo masu da babys ɗin kamar yadda ya ce ba, a tinaninsa iya son fatar baki kawai suke yi wa yaran, so yana ganin ai zasu mance da yaran kafin nan da kwanaki.Ta aminta da zancensa, dan ta tina ai babyn da Maya take kiransa my boy ma sun same shi da zazzaɓi, hakan na nufin jariran basu da lafiya da gaske kenan, ajiyar zuciya ta sauke game da ɗan sakesa kafin ta ce. “My Dr, ka kula da babys ɗin sosai har zuwa su samu sauki sai ka dawo mana da su, da yamma idan muka tashi aiki ma zamu je mu dubasu”.Kirjinsa ne ya ɗan amsa jin ta ce da yamma zasu je su duba babys ɗin, amma sai ya danne. Kai ya jinjina kafin ya sumbaci cheek ɗinta. Murmushi ta ɗan yi game da juyawa, tana murna ta nufi hanyar fita. Bayanta ya bi da kallo har ya fice, nisawa ya ɗan yi game da girgiza kai yana furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa.Tana fita ya kammala shirinsa tsab. Sannan ya fito ya nufi ɗakin da zasu yi wa macen tiyata. A nan ya isko su Dr Kamal suna jiransa a waiting room. Yana zuwa suka ƙarisa ciki. Wata macece kwance a kan gadonsu na tiyata, tana sanye da blue gown irin wanda ake sanyawa waɗan da za’ayiwa tiyata, an shirya komai tsab, daga ganin wannan mata zaku san irin matan nan ne na kauye da basu waye sosai ba, basu san komai ba, cutarta aka yi da sunan ciwo za’a cire mata a mahaifa, kunga za’a cire mata shi gabaɗaya.Cike da taka tsantsan suka fara aikin. Da yake sun kware kuma sun saba yi sai basu ɗauki wani dogon lokaci ba suka kammala komai, bayan sun gama Dr Mark ya ɗauki wata glass ball aka sanya mahaifar a ciki, sannan ya fita da mahaifar ta wata kofa. Su kuma Dr Kamal ya hau haɗa gyara wajen, Dr James yai mata ɗinki tsab, sannan ya ɗauki paper da pen, a natse ya yi rubutu the seme rubutun da ya yi wa matar farko da aka cire mata mahaifa.Ya rubuta a dinga kula da ita sosai, a bata cima mai kyau har zuwa ta samu sauƙi, ta dinga shan abu mai ɗan ɗimi. Ya rubuta magungunar da yakamata a bata kafin ajiye paper kusa da hannunta, ya ƙara gyarata kafin ya kira nurses su fita da ita. Shi kuma ya bi bayansu Dr Mark. A in da suke ajiye mahaifar suka nufa, a nan suka je Dr James ya sanya cikin kwalbar, ya saita na’urar dake jikin kwalbar ta fara bada yanayi daidai da cikin mace, suka tabbatar komai yana tafiya daidai, sannan suka nufi in da suka yi sashen eggs ɗin nan.Kewaye suka fara yi a wajen suna duba dik wasu motsin eggs ɗin. Dr Kamal ne ya ce. “Wai ina Lazy ne yau? Bata bimu ɗaukar rahoto ba”………. Dr James da ya ɗan yi shiru for 2 mins ne ya amsa da. “Ban taɓa sanin Lazy bata da hankali ba sai yau, wai US zata je”. Zazzaro idanu Dr Mark ya yi. “US kuma?”. Suka haɗa baki da Dr Kamal wajen tambaya. Kai ya jinjina masu alamar e kafin ya ce. “Kila ajalinta ke kiranta, dik da Hussain baya raye, na tabbata su Zayra’an suna da labarin abin da ta aikata bayan mahaifinsu, na tabbata kafin Hussain ya mutu ya basu labarin komai, tabbas sun san cewa Farooq na WS yana rufe, na tabbata suna can suna neman Farooq ɗin kamar hauka, kunga in suka kamata tasan me zai biyo baya”.Dr Mark ne ya ce. “Wai dama Lazy tasa aka kama Farooq?”…… Kai Dr James ya jinjina game da cewa. “Ita tasa aka kamasa, a lokacin da aka kama Haiza’an aka tafi da shi ta kira Farooq a waya ta shirya mashi gadar zare da sunan an far masu ya kawo masu ɗauki, yana zuwa aka kama shi, na tabbata Mahvir ba zai kyaleta ba, kai su Zayra’an ba zasu taɓa yafe mata ba”. Murnushi Dr Kamal ya yi. “Ai dik a tsananin yunwace suke da nemanta, ta kai kanta ga mutuwa”…… Dr Mark ya ce. “Ba zasu iya ganeta ba fa”.Siririn tsaki Dr James ya ja. “Sai dai idan bata ci karo da Zayra’an Bint Haiza’an ba, ina da tabbacin jinin Haiza’an zasu ganeta tsab, domin su baiwa da ita aka haifesu, kyauta ce daga ALLAH ba daga wasu ba, kuma Lazy ta manta abu guda, jinin uwa fusgan ƴaƴa yake yi, bugu da ƙari ta canza komai amma bata canza murya da gashin kai ba! Kamal ku baku san waye Haiza’an ba, na tabbata da ba zaku yi tantamar Zayra’an zai gane Lazy ba”. Kai suka jinjina kafin Dr Kamal ya ce. “Dik ba wannan ne ma ya fi damuna ba, na damu sosai a kan IRON FIST, ka sani na samu mun sani aiki suke yi domin al’umma, a shirye suke su dakatar da nasarar da muke samu, ina tsoron abin da zasu iya aikatawa, kun san suna da mugun haɗari”……. Siririn tsaki Dr James ya ja. “Ba zasu iya yi mana komai ba, dik bala’i mutum ba zai taɓa iya gano WS-HOSPITAL ba! Ba’a haifi mahaluƙin da zai iya ganomu ko ya dakatar damu ba, dan nasara aka haifomu a duniya!”. With ho full confidence ya faɗa, yana jin tamkar dan su aka shinfiɗa kasar duniya!.Jinjina kai su Dr Kamal suka yi, dan suma sun san a irin tsaron mai masifaffen karfin da suke da shi sai dai in fita waje suka yi za’a iya kamosu, amma a cikin WS-HOSPITAL kam wane mutum ya iya kamasu, kofofin shiga masu shocking na lantarki, sai Dr James ya shigar da password shocking ke ɗaukewa, kuma shi kaɗai yasan password ɗin, ai kunga kuwa ba zasu kamu ba a ganinsu!.Haka suka cigaba da aiki suna tattaunawa game da nuna cewa IRON FIST ba su isa su dakatar da su ba, sun yarda da kansu kuma sun yi imani sune kawai masu nasara, dan nasararsu aka shinfiɗa duniya.A gefe kuwa, Sister Zinta ta koma ɗakin jariran, nan ta tarar Dr Kamal ya gaba duba boy ya bashi dik wani abin da ya dace, ta dawo rike da yaron tana lallaɓa shi tamkar kwai a faranti. Ita kuma sister Zinta ta ɗauki wannan haɗaɗɗen yaro mai blue eyes da aka kashe ɗan uwansa jiya, ta rungume yaron tana yabon kyansa, daga nan ta ce. “As from today this is my baby, kuma na bashi sunan Haiza’an”. Ɗan zazzaro idanu a kanta suka yi, sister Maya ta ce. “Ina kika samu wannan suna mai shegen daɗin kuma, Haiza’an, sunan ya yi daɗi”…… Tana ɗan murmushi ta ce. “A laptop na my Dr na ha wani folder an rubuta Haiza’an shi ne kawai na ji sunan ya kwanta mun har cikin raina”.”To waye ya ce maki suna ne? Kika sani ko wani abin ne?”. Sister Maya ta faɗa.. tana saɓa babyn a saman shoulder ɗinta ta ce. “Koma dai menene sunan ya shiga raina sosai, koma ba sunan mutum bane, ko sunan wani abin ne ni dai ya mun, in na kira sunan daɗi nike ji, dan haka sunan babyn nan Haiza’an”.Maya tana murmushi ta ce. “Kin san nima sunan ya kwanta mun a rai ya burgeni?”……. “Ai sunan yana da daɗi ne, daga yau sunan wannan baby Haiza’an, haka zaki dinga ce mashi”….. Suna murmushi gwanin sha’awa suka fara cire kayan jariran suna yi masu wanka. Bayan sun kammala suka sanya masu kayan sanyi saboda weather ta ruwan sama, a nan suka zauna zaman hira, sister Zinta ta sanar da sister Maya cewa ai sun kai babys ɗin ɗakin kula da su ne dan sun kamu da cuta, Maya ma ta gamsu da bayanin, sai suka hau addu’ar yaran su samu sauƙi.A can gefe kuwa 3D na zaune office ne Dr James suna tsara yadda zasu haɗa rigakafin cutar NEXAPOX-31 kafin su haɗa ainahin maganin cutar, Dr James ya fito masu da tsarin aikin da kuma jerin abubuwan da zasu buƙata domin haɗa wannan magani da kuma rigakafin. Suna ta faman karanta abubuwan buƙatar. Yau basu yi wani aiki sosai ba, around 1 suka je suka zuba jikin darling Dr James ya sake ɗaukansa video ya turawa World System, hakika bakina ya yi kaɗan iya zayyana maku bala’in da darling yake a ciki, ya rabb, ALLAH ya saka maka, ya bi maka hakkinka bawan ALLAH.Bayan sun duba shi suka wuce cikin ɗakin haɗa cutar NEXAPOX-31 ɗin, suka shirya kwalaben dake ɗauke da sinadarin cutar a cikin manya-manyan kwalaye, sannan suka shirya a wani ɗakin duhu dake kusa da wajen, daga nan suka fito suka nufi ɗakin kirkire-kirkiren halittunsu da ƙaƙale-ƙaƙalensu……. In Sha ALLAH a wannan kirkire-kirkiren zaku kirkirowa kanku bala’i shehu la’anannu kawai!.Wasu mugayen kwari dake cikin wasu glass suka sanya guard biyar majiya karfi suka ɗauka suka fitar masu da shi, kai tsaye a bayan motar da ake shirya jariran da Dr Mark yake fitarwa suka sanya katuwar glass ɗin. Kamar kullum Dr Mark ya ja motar ya fita da shi ta cikin wannan hanya da ta ɓulla cikin dokar dajin.Su kuma suka koma cikin asibiti, da alama an kammala wannan project na kwarin, za’a miƙawa masu shi. Ko wacce ƙasa za’a sakarwa waɗan nan kwari kuma? To koma wace ƙasa ce ALLAH ya kareku daga sharrin WS, dan waɗan nan kwari suka cijeka sai ka kwanta jinya na zazzaɓa mai mugun zafi ga ciwon kai, idan kana da rabo sai ka sha jinya ka warke, idan kuma ba saura kwana mutuwa zaka yi bayan shan azaba.Wunin wannan rana dai haka suka kasance, around 5:30 Dr Kamal and Dr James suka zo suka ɗauki sister Maya and Zinta. Yaran nan sam basa son tafiya su bar babys ɗinsu, amma ba yadda suka iya, sun gama yi masu wankar yamma suna wasanni dasu kawai 3D suka zo suka ɗaukesu, Maya har da guntun hawayenta wai bata son barin boy, ta ce zata tafi da shi Dr Kamal yaki yarda, ya yaudareta da kalamai har ta aminta ta biyosa suka tafi.Around 1 na dare Dr Kamal and Dr James suka sake fitowa suka baro ƴan matan nasu a cikin gida. Yau ranar haɗa drugs ne na jini da suka riƙa jariran jiya. Dan haka ba sai na sake yi maku bayani kan yadda suke haɗa magani da jinin ba, already kun sani, na ɓargo da ƙashi ne baku sani ba, idan na zo nan dallah-dallah zan maku. Amma yanzu dai sun haɗa maganin kamar yadda suka saba, suka shiryasu cikin sachet kamar ko yaushe. Sannan suka sa aka fitar masu zuwa ɗakin shiryasu a cikin kwalaye, sannan suka fitar zuwa General Hospital ɗin. Around 4 suka kammala, suka koma gidansu, sun isko su Zinta na barci, dan yau shayar da su maganin barci suna yi a cikin lemu da suka je yin lunch ba tare da su Zinta sun sani ba.Hankalin 3D ya fara tashi tin daren jiya da su Maya suka nemi titseyesu kan ina suka je, daga nan suka yanke shawarar rinƙa masu maganin barci cikin dare, dan basu son suga hankalin ƴan matan nasu a tashe, kuma ba zasu iya faɗa masu abin da suke yi ba. Bayan sun dawo wanka suka yi, suka shirya cikin wasu sleeping dress ɗin, a gefen matan nasu dik suka kwakkwanta tare da jawosu jikinsu, ba jimawa barci ya yi awon gaba da su. While shi kuma Dr Mark yana can yana kwasan hanya zai fitar da kaya daga cikin ƙasan ta ɓarauniyar hanya.D——-O——-L🔥Ita kuwa Angelina tana zaune kusa da Zaynish tana aikin satar kallonsa, Unays kuma yana satar kallonta, yana ta ALLAH ALLAH Zaynish ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna.Kiran Ummie ne ya shigo wayar Zaynish. Ciro wayar ya yi daga aljihunsa. Kashe kiran ya yi game da kiranta. Bugu ɗaya ta ɗauka, kara wayar a kunne ya yi game da cewa. “Assalamu alaikum”. A yadda ya yi magana ko Angelina dake kusa da shi bata ji me ya ce ba.Daga ɗayan ɓangaren Ummie dake zaune saman sabbin sofa set ɗinta da ta yi wa kanta ne ta amsa da. “Waalaikumussalam ɗan uwana”……. “Ina wuni Aunty Ummie?”…….. “Lafiya lou Alhamdllh ya aiki da abokan aikin naka?”……. “Suna nan lafiya, ya gida da Yaya Faisal? Ya dawo ne?”. Kai ta ɗan girgiza kafin ta ce. “A’a bai dawo ba, ya dai turo mana saƙo jiya, ina su Noor? Kwana biyu ban jisu ba?”….. Kallon in da Noor yake ya ɗan yi kafin ya ce. “Suna nan lafiya, Aunty Ummie kina mana addu’a sosai ko? Kin san yanzu addu’a kawai muke da buƙata”.”Sosaima, kullum sai na yi maku, ALLAH ya kare mun kai, yaushe zaka dawo ka fara aiki a nan dan ka ɗauka mana fansa? Ka kore mana ƴan ta’addan nan?”……… Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. “Sai mun kammala wannan FIVE MISSION ɗin, a wannan lokacin ne muke da zaɓi, ko mu zauna a Avaris mu yi aiki ko kuma mu yi applying Nigeria or Niger dik wanda kika zaɓa mun, so in mun gama FIVE MISSION muna dan ƴancin zaɓar ƙasar da muke son yin aiki”. Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. “Zan yi tinanin in da zaka yi aiki, amma yanzu dai yaushe zaku gama?”…… “Very soon In Sha ALLAH, ke dai ki cigaba da yi mana addu’a”. “In Sha ALLAH addu’a kam ba fashi, yanzu dik ajiye wannan magana, batun aure na kiraka mu yi”…… Kada ku manta ita bata san sun tafi mission ba, ya ɓoye mata dan kada ya ɗaga mata hankali, yanzu ta ɗauka suna barrack ne shiyasa ta ɗauko mashi batun aure.Ƙasa ya ƙara yi da murya wajen cewa. “Kai Aunty Ummie, na faɗa maki bani da zaɓi a kan mace, kawai ki bani dik wacce tai maki, ki zaɓota, na baki wuƙa da nama, ko wacece kika kawo zan aureta, na yi alkawari, amma ki kawo wacce zata girmamaki fiye da yadda zata girmamani, wacce zata soki kamar yadda nike sonki, wacce zata maki biyayya tamkar yacce zata mun, wacce zata kula dake tamkar yacce zata kula dani, idan ba mai wannan ɗabi’u ba bana so kada ki kawota!”……. Murmushi ne ya kubce mata, cike da farincikin irin yadda ya bata muhimmanci a rayuwansa ta ce. “Ina wacce ka ce ka taɓa gani? Wacce ka fara jin sonta a ranka? Bana son ka rasa soyayyarka ta farko”. Nisawa ya ɗan yi game da cewa. “Ban san in da take ba, na faɗa maki tin daga ranar ban sake ganinta ba, dan haka ni nama mance da ita, kawai ki nemo mun taki”……… “To shikenan zan kuwa nemo maka haɗaɗɗiya, kana zuwa hutu sai aure kawai”…….. Kai ya ɗan jinjina kafin ya ce. “A’a, mu ai muna da lokacin yin aure, sai mun samu umarni daga sama, idan kin samo matar ki sanar dani sai in shigar da buƙatar auren a tsare, idan manyanmu sun yarda shikenan in na dawo sai ayi komai”.Da to ta amsa kafin ta ce. “To ka kula da kanka, ka ci abinci ka yi ibada mai kyau, a dik in da kake ka sani ALLAH yana ganinka, kada ka cutar da kowa, ka zauna da kowa da zuciya ɗaya, hakance zai sanya ba zasu iya cutar da kai ba, a dik in da kake ka tausayawa mace, kaga mai raunice, ka tausayawa kanka, ka tina kai maraya ne, baka da kowa sai ni, ba zan iya jurar rashinka ba, ka tina hakan, ka rinƙa addu’a da alwala kafin kwanciya barci, ALLAH ya yi maka albarka”. Hakika kunnuwansa sun yi mugun sabo da jin kalaman Aunty Ummie na nasiha kullum, har ya haddace, dan haka da In Sha ALLAH ya amsa mata. Sai ta sake cewa. “Ina sonka sosai rabin raina”.Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, bai san daɗin iyaye ba, amma a kanta yasan ainahin menene soyayya, ta sadaukar da komai saboda shi, lallai soyayyarta ce ake cewa true love…….. “Nima ina sonki sosai Aunty Ummina, ba zan taɓa son wani abu rabin son da nike yi maki ba, ki kula da kanki, dik abin da yake damunki ki yi gaggawar sanar dani kin ji?”.Da okey ta amsa mashi, daga haka suka yi sallama, ya shiga gallery ɗinsa, hotunanta ya fitar ya fara kallon yana tina yarintarsa, lallai Aunty Ummie ita ce komai ɗinsa, tai mashi komai, a rana sai ta kirasa sau biyar ko mantawa bata yi, ga hidimar shago dana gida, amma baya sanya ta manta da shi, kome ta ɗauka zata kai baki sai ta tina shi, ta ce shin shi ya ci ko bai ci ba? Yana samun irin abin da take ci ko baya samu? Dik ta damu.Ya jima yana kallon hotonta kafin ya ɗan nisa, unexpected wayan nasa ya kubce ya faɗi ƙasa a gabansa. Da sauri Angelina ta ɗauko mashi wayan, kurawa hoton da yake kallo ɗin ido ta yi. Bata san lokaci da ta ce. “Wow, she’s so beautiful”…….. Slowly ya ɗago kallonsa a kanta wanda tin da ta zauna a wajen ko sau ɗaya bai ganta ba, har cikin ransa ya ji daɗin yadda ta furta words kan hoton.Murmushi ta ɗan yi game da miƙo mashi wayar tana faɗin. “Is she your sister?”. Ta faɗa tana mai da kallonta a kansa……… Bai amsa mata ba, kuma bai karɓi wayar ba. Bata damu da bai amsa ba ta sake cewa. “You look alike, amma tafika kyau saboda ta fika hasken fata, and ta fika big-big eyes, wow ta yi kyau sosai, anya ba zan cewa daddyna ya auro mana ita ba? Ta yi kyau sosai, na ji ina sonta”.Har cikin ransa ya ji Angelina ta burgesa, dik wacce zata so Aunty Ummie, hakika zata sace zuciyansa. Ganin bai karɓi wayar bane yasa ta zaci ya ji haushin abin da ta yi ne, sai a lokacin ta tina ashe oganta ne, taɓa wayansa ba da izininsa bama ta yi laifi, da sauri ta ce. “Sorry sir, it can’t happen again”. Ta faɗa tana sake miƙo mashi wayar, cikin muryar girmamawa tai maganar.Hannu yasa ya karɓa yana ɗauke kallonsa daga kanta. Ƙasa ta yi da kai, haka kawai sai ta ji murmushi ya kubce mata ganin yau ɗaya ya ɗaga ido ya kalleta, abin da bai taɓa yi a, ba zata mance wannan rana ba, kuma haka kawai har cikin ranta ta ji Aunty Ummie ta shiga ranta, ta yi matuƙar burgeta, har ta ji cewa lallai tana son yin magana da ita. Zanen heart ta yi a ƙasa tare da zana dogon kifiya a tsakiyar heart ɗin kafin ta yi rubutu da yaren daddynta a saman heart ɗin, a ƙasa kuma da turanci ta rubuta. “Zuciyata ta makance kan mutum ɗaya, ta rufe ruff kan mutum ɗaya, bana ji, kuma bana ganin kowa sai shi, shi kaɗai ne zaɓina, shikaɗai nike gani in ji daɗi, i love you forever and ever”…… Ta gama rubutun tare da miƙewa ta bar wajen, ta koma kusa da Manassa ta zauna zuciyarta cike tab da tsananin begensa, tana fatan ace ya ga wannan zane.Shi kuwa cigaba da dannar wayansa ya yi ba tare da ya sake ɗagowa ya kalli in da take bama bare ta ji sanyi a ranta. ——————-Tsaye Lion yake a tsakiyar room ɗinsa rike da rigar pjs ɗinsa daya cire, ya kunna light bolb da suka ɗaura a saman tantin wanda ke amfani da solar, haske ya gauraye ko’ina a cikin ɗakin, yana ƙoƙarin ɓalle botiran rigan zai sanya a jikinsa ya fita. Bakinta a ɗauke da excuse Arya ta shigo cikin tantin rike da hannun yarinyar nan, zata fita ne yarinyar ta ce sam ita ba zata zauna a ɗakin ita kaɗai ba, shi ne Arya ta kamata suka taho tare. Sake hannunta Arya ta yi game da kamewa ta sarawa Lion tana ɗan yin ƙasa da kai, gabanta sai faɗuwa yake yi na ganin kyakkyawan kakkarfar surar jikinsa, his sixpack was so Masha ALLAH, dole nema ya tafi da tinanin dik wacce ta gansa, gabaɗaya sai ta nemi natsuwarta ta rasa, ai a miliyan ta ɗauke kallonta daga kansa game da sauƙe hannun nata ƙasa.”Sir akwai abin da yakamata ka zo ka gani, dan bayani da baki ba zai yiwu ba”. A dake ta faɗa cikin girmamawa. Kai ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. Sake sara mashi ta yi kafin ta kama hannun Jehan su nufi waje tana ɗan waigosa. Cikin tantinsu suka koma, ta zauna a gaban laptop ɗinta game da cewa Jehan ta zauna a saman electric mattress ɗinsu. Hayewa kai Jehan ta yi tana kallon Arya cike da so, tana son Arya sosai…. Cigaba da abin da take yi Arya ta yi, ita kaɗai a cikin tantin, su V dik suna wajen wutar da suka kunna. After 5mins da kiransa sai ga shi ya shigo sanye da pjs ɗin da yake rike da shi ɗazun, hannunsa rike da wayansa yana pressing, da alama saƙo yake rubutawa. A dab saitinta ta baya ya ɗan tsaya, sai da ya kammala rubuta saƙon da yake yi ya tura sannan ya sunkuyo kanta game da maido da kallonsa kan laptop ɗin. Kallon 1 minute ya yi wa laptop ɗin sai kuma ya kai hannunsa sama mouse ɗinta, already hannunta na kai. Ai wani irin yanayin da ta ji ya ziyarce a lokacin da skin ɗinsa ya taɓata ba zai misiltu ba, da sauri ta janye hannunta tana sauke numfashi a hankali-hankali, ga daddaɗar kamshin perfume ɗinsa na kamfanin su Noor dake ta faman tashin kofofin hancinta.”Wannan ina ne?”. Ya faɗa a natse yana mai da kallonsa kan face ɗinsa, ta tsare ƙashin wuyan nan nasa da kallo. Ɗan ɗauke kallonta ta yi game da cewa. “Jiya V ta tura drone mai ɗan girma wajen ne sai suka harbesa, shi ne na tura ƙarami ɗazun dan in ga me yake ɓoye. Waɗan nan mutane sune abin dake wajen”.Cike da mamaki Leo ya sake mai da kallonsa kansu. Wajen tamkar rana, wutar lantarki zaku zaci rana ne, tantuna ne dayawa a kafe a wajen, wlh ya fi sansanin soja haɗuwa, ga wayarin na wutar lantarki da aka yi, amma su sojoji an basu kaya masu amfani sa solar, a wani sashe na wajen mutanen ma gini ne na ɗaki da block da sementi, ta ko’ina matasa ne suke yawo rike da muggan makamai masu rai da lafiyan da babu irinsu a hannun sojoji. Abin mamaki kuma wlh dik matasan nan yara ne da basu kai 20 years ba, suna sanye da rawani a fuska da jallaniya a jikinsu, wasu kuma da irin pakistan riga da wandon nan, sai sha’aninsu suke yi a wajen tamkar a cikin gari.Riƙaƙƙun ƴan ta’adda ne dake arewacin ƙasar waɗan da suka samu lasisi a ta’addanci, waɗan da manyan ƙasar ke ɗaure masu gindi, suke jin tamkar sun fi karfin kowa da kowa. Motsa done ɗin Leo ya yi, ya fara controlling ɗinsa yana bin sassan wajen, ta ko’ina matasa ne ke shawagi, a kallah zasu kai matasa 300 kam. Gabaɗaya mamaki ya hana Leo yin dogon tinani a kansu, mai da kallonsa a kan kilomita nawa ne tsakaninsu da mutanen ya yi, a gaskiya suna da nisa sosai.Cigaba da kutsawa lungu da saƙo na wajen ya yi, fili ne mai girman gaske, tamkar gari, ga lunguna da wajajen ɓoya ba adadi. Juya akalar drone ɗin Leo ya yi ya nufi wani wajen wanda ya ga lantarki yafi yawaita a wajen dan yaga menene. Bolb na wuta ya yawaita a wannan waje. Tura drone ɗin ciki ya yi dan yaga menene.Ya ilahi ya lillahi, ai Leo bai san lokacin da ya zabura ya miƙe tsaye daga sunkuyon da yake ba. Jama’a, ta’addaci ya yi mugun karfi a arewacin kasar fiye da yadda kuke zato, wannan ɗakin cike yake tab da computers masu inganci, karfin intanet dake wannan waje kusan za’a ce yafi na cikin gari karfi, ashe shiyasa suka iya gano drone na farko suka harbesa, lallai ƴan ƙasa sun yi mugun sake ta’addaci ya yi girman da in ba ALLAH ba babu mai iya kwatarsu.Wannan abu ya yi matuƙar gigita Leo, kuma ƴan ta’addan aka horar kan sanin computer da iya sarrafata. TO WAYE YA HORAR DA SU A WANNAN FANNI?. A wannan waje suna da likitocinsu, suna da masu yi masu girki, suna da dik wani abin da ɗan adam zai buƙata dan more rayuwa, dik yadda kuke tinaninsu wlh sun zarce hakan, wannan shi ne ainahin taddacin arewacin ƙasar ba wata rufa-rufa ko sakayawa, ƴan ta’addan suna rayuwar jin daɗi da ƴanci fiye da ƴan ƙasa, abinci available, ga likita, kuma kullum ƙara yawa suke yi, ga karfin internet da aka ja masu har cikin wannan kungurmin dajin, shiyasa zasu kafa waya su yi video son ransu, su saki baya slow na network saboda karfin intanet na kasar rabi dik su aka baiwa, idan sun tashi zuwa yin ta’addaci sai su tura kalilan daga cikinsu da su matsa daga in da suke zuwa gaba ta bakin fita cikin gari su kafa wasu tantunan, sai su yi shiri su shiga gari, su kashe na kashewa su kwashi na kwasa, su dawo dasu sansanin da suka kafa, bayan kwanaki biyu in komai ya lafa su zaɓi waɗan da aka tsara masu kan ba yanzu zasu sakesu ba, su kutsa dasu cikin daji su kaisu babban sassani wajen babban shugabansu.Saura kuma su barsu a wannan karamin sansani da suka kafa su karɓi kuɗin fansa, waɗan da aka wuce da su babban sansani sai su haura watanni 6-7 a wajen, wasu ma ko an kawo kuɗin fansa basa sakesu, saboda ba’a basu umarnin su sake su ɗin ba, daga sama ake juyasu suma, haka zasu ajiye mutane suna lalata da su, basa zuwa kama mutane haka kawai sai an gama tsara masu ga waɗan da zaku kama, idan kun kamasu ku ware kaza ku turasu babban sansani, kaza ku karɓi kuɗin fansa daga ƙaramin sansani, dik karshen wata waɗan da suke basu umarni suna kiransu su yi lissafi da su, dama already sun san adadin kuɗin da suke baiwa masu basu umarni dik wata. Dik watan ALLAH akwai adadin kuɗin da suke baiwa manyan ƙasar masu ɗaure masu gindi, miliyoyin miliyoyi suke basu, su kuma manyan su basu kayan aiki, bindigu masu inganci, kayan abinci, kayan more rayuwa da kuma wayoyi masu tsada, sannan ga kayan shaye-shaye da suke basu kala-kala, komai ana zuwa da jirgi helicopter a sauke masu kayan abinci, jirgin bata sauƙa ƙasa, a sama take tsayawa ta sake masu makamai da kayan abinci game da dik abin da zasu buƙata. ———————–Bin dik wani lungu da saƙo na wannan ɗaki da drone ɗin Leo ya yi, basu gane cewa drone bane, dan na faɗa maku kamar ƙuda yake……. Ya jima a wannan ɗaki yana kallon irin manyan ingantattun kayan aikin da suke da shi kafin ya fita ya sake shiga ɗakin kusa da wannan. A nan kuwa mata ya gani, mata dayawan da a kallah zasu kai 250 haka, dik sun yi shunfuɗa dun kwakkwanta. Fita ya yi ya cigaba da yawace wajen da girmansa ya zarce yadda kuke tinani, nan yaga wasu matan suna zaune bakin wuta suna girki sanye da manyan hijabai har ƙasa, daga gani ba tambaya kasan waɗan nan sun zama ƴan gida, sun yi jimawar da duniya ta manta da su a wajen, sun sadaukar da rayuwarsu sun mance da iyalansu ma bakiɗaya, ALLAH sarki, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ALLAH yai maku sakayya, ya bi maku hakkinku, dan na tabbatar kuna da yara da ƴan uwa.Leo bai san lokacin da ya ɗaura ɗayan hannunsa a kan bakinsa ba, ya kusa suman tsaye saboda tashin hankali, yana jin ta’addanci ta’addanci bai taɓa zaton karfin ta’addancin ya kai har haka a arewacin ƙasar ba, a wannan waje yaushe ƙananan sojoji ƴan bar one zasu iya fito na fito da su? Tsakiyar wannan dokar daji, gaba daji baya daji, ba zaka taɓa zatan akwai ran ɗan adam a wajen ba, ia ilahi, sun kafa wajen kafawar da suna iya ganin dik motsin da zai shigo masu, kafin sojojin su iso in da suke already suna ganinsu ta computers ɗinsu, kafin sojojin su farga sun kewayesu sun masu rubdugu.Wannan ai sai sojojin da suka samu horo biyu suka amsa sunansu sojoji, sannan a haɗa da air force, a masu ɓarin makauniya na wuta sama da ƙasa, ai masu ruwan boma-bomai sau ɗaya shi ne za’a iya masu ba’a zauna tura ƙananan sojoji masu tasowa ana kashesu a banza ba.Miƙewa tsaye gabaɗaya Leo ya yi tare da juyawa Arya baya, ya ɗan dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi saboda tsananin ciwo da sara mashi da yake yi, musifar ta zarce tinaninsa. Sai da ya ɗauki good 5 mins a haka, ya saita natsuwansa kafin nan ya juyo, ya dawo ya sunkuyo kanta, ya sauke ajiyar zuciya ya fi sau uku, damtsen hannunta ya ɗan buga kaɗan game da cewa. “You really try, and i really appreciate”. Sosai ta ji daɗi har cikin ranta ganin yau ya yabawa aikinta…… Ni kam na ce bama dole ya yaba maki ba, irin wannan ɓarna da kika bankaɗo ai wlh ba dik kai ba, za’a tara sojoji 1000 ba’a samu biyu masu kwazonki ba ɗiyar daddynta.Mai da kallonsa a kan laptop ɗin ya yi yana tunanin lallai zai yi aiki tare da Arya, dan ta fi dik mazan nan amfani, team 1 ne kawai suka ɗarata kwazo a wannan tafiya, amma dik sauran wlh ta fisu jajircewa, lallai zai yi aiki da ita, yana son mutum mai jajircewa.Cigaba da kallon wajen ya yi, a cikin wani tanti suka gano wani waje tamkar makaranta, ga board da komai, kuma ga alamar rubutu a jikin board ɗin, amma ya gogge ba su iya gane me ake karantarwa a wajen ba, amma tabbas makaranta ce wajen karantar da ƴan ta’adda.Babban abin da ya ƙara baiwa Leo mamaki shi ne yadda suke pacaka da ruwar roba bama pure water ba, sun fi bayin ALLAH na cikin gari yin rayuwar ƴanci da jin daɗi. Dik da basu ga ainahin cimarsu ba, amma sun fahimci cima mai kyau suke samu, dan sun ga buhu-buhun shinka ta waje, foreign rice kenan.Tin Leo na mamaki har ya daina, ɗan ƙara rage tsawonsa ya yi game da cewa. “Keep watching they’re movements, idan wani sabon abu ya bayyana ki sanar dani, and dik abin da kika gani wanda bamu gani a tare ba make sure you write it down for me, bari in yi meeting da su Zaynish, i will be back in the next 2 hours”. Ya kai karshen maganar game da miƙewa tsaye. Waje ya nufa cikin zafa. Bayansa ta bi da kallo tana jin tamkar ta jawosa ta dawo da shi ya cigaba da magana a kurkusa da ita kada ya dakata, amma ba yadda ta iya, tana gani har ya fita. Yana fita ta ce. “Jehan come close to me in baki yi barci ba”.Da sauri ta ɗago kai jin ta ambaci sunanta, bata jin turanci, bata gane me Arya ta ce ba, sai da ta nuna mata alama da hannu sannan ta miƙe ta zo kusa da ita, a gefenta ta zauna, Arya ta ɗan jawota jikinta tana faɗin. “Zan koya maki computer my girl”…… Ita dai Jehan bata ji komai ba, kallon laptop ɗin kawai take yi. Arya kuwa ta cigaba da aiki, wani lokaci idan ta yi pressing wani abin sai ta cewa Jehan wannan abu kaza yake nufi, dik da yanrinyar bata jin yaren amma tana fahimtar nufin Arya tin da in tana mata bayani tana gwadawa da hannu.A can kuwa, Leo ya yi wa Noor message kan ya kira Vash and Zaynish su same shi a ɗaki yanzun nan. Ba’afi 5 mins ba sai gasu sun bayyana. Umarni ya basu kan su zazzauna, a dake suka karɓi umarni, suka zazzauna suna fuskantar juna. Cikin natsuwa ya zayyana masu dik abin da ya gani a cikin wannan daji ɓangaren aikin su Arya. Hakika hankulansu ya yi mugun tashi, amma sai suka daidaita natsuwarsu, Noor ya ce. “Okey, the reason why our seniors always saying North is different? Oh, kenan they already knows that akwai gagarumin matsala?”.Vash ya amsa da. “Of course, but keep all this aside, let’s focus on wancan hayakin, mu gano menene, wannan case ɗin babba ne, sai mun fara gano hayakin mecece a wajen can before mu takalo faɗa da waɗan can riƙaƙƙun yan ta’addan”.Jinjina kai suka yi, sun gamsu da kalaman Vash, dole su fara da batun hayakin nan, dan waɗan nan riƙaƙƙun ƴan ta’addan sai sun shirya masu. Gyaran murya Leo ya ɗan yi wanda yasa dik suka ƙara natsuwa suka kuma yi tsit. A natse sosai ya ce. “Zamu raba aikin nan yadda zai fi yi mana sauri da kuma sauƙi”……… Basu gane nufinsa ba, sai suka bisa da kallo suna jiran dogon bayani.”Kowani soja a cikinmu zai ɗauki jami’a ɗaya su yi aiki a tare, hakan zai tafi daidai, zamu tafi da fly drone ɗinsu na sirri, idan mun je wajen hayakin zamu rabu ne kashi huɗu, kowanne zai kama hanyar da zai bi, a kan hanyar da zai bi zai saki wannan drone, jami’ar da suke aiki da ita zata na duba mashi hanyar da yake bi ɗin tana bashi information a kai, hakan zai sa suma matan su bada himma, for now kunga su ukun dik basu bada himma ba, ɗaya ce mai fafutuka”.Jinjina kai suka yi, sun yi na’am da wannan shawara……. A kan Noor Leo ya tsayar da idanunsa kafin ya ce. “Bayan aiki ban ce ku ɓige da wani abin ba, dan ma dai an ɗaura ne ba halin in haɗata da wani da na maka canji”. Noor ya gane karatun, watau Leo ya gano cewa shi lover boy ne, shi ne har da yi mashi gargaɗi, siririn murmushi ya ɗan yi kafin ya ce. “Amma ai ya halatta idan ta binciko mun abu mai ma’ana in na ji daɗi in bata sumbata a cheek ko?”…… Kunnensa Zaynish ya kama, ya ɗan murɗa kafin ya ce. “Da a iya wannan zaka tsaya to da sauƙi, nasan halinka sarai, zama ka iya mantawa da aiki kuke yi ka zarce wani wajen, ni shawarata a rabasu, a haɗata da wani ɗin kawai tin da a bakin aiki muke, shi ma a haɗa shi da wata”.Vash na murmushi ya ce. “Wannan shawara ta yi, kawai a rabasu”…… Buge hannun Zaynish Noor ya yi game da cewa. “In ga yadda za’ayi a haɗa matata da wani kato! Ni da kayana? A ina aka taɓa hakan?”. Yana tamke fuska ya faɗa, wai dan ma su san ba da wasa yake yi ba. Shi dai Leo bai ce masu komai ba, ya jawo laptop ɗinsa, ya fito da sunan dikka sojojin da suka zo da su wannan Mission ɗin, sojoji bar one su 34 ne, sai bar 2 team 1 and team 2 su 8, sai kuma su Arya su 4, dik in an haɗa su 46 kenan.Fito da information a kan su Arya ya yi, ya zari V daga cikinsu ya turawa Noor Information ɗinta ta email ɗinsa kai tsaye ta sauƙa a laptop ɗin, a ƙasan information ɗin ya zayyana mashi aikin da zasu yi tare, dokokin aiki da tsare-tsaren da ya dace!. Kada ku manta team 1 dik suna da laptop a halin yanzu…… Daga nan ya zaƙulo bayanan Angelina ya turawa Zaynish da nashi bayanin shi ma. Fito da bayanan Manassa ya yi, ya san ba jami’a bace, surgeon division general ce, amma dik da takasance likitar sojoji a jikinsa yana jin tana da sani kan aiki irin nasu Arya, kuma ya san dik da take surgeon general to fa anbata horon kare kai, dan wannan dokar AZURE ce, harta likitocin sojoji suna karɓar hoto dan kare kansu.Dan haka sai ya ce. “Arvash kira mun Manassa yanzu”……. Miƙewa Vash ya yi, ya fito. Zaune ya iskota suna hira da Juraiz, ta ɗan saki jiki tana biye mashi, a tinanin Juraiz V ce ba Manassa ba, dan shi baya iya rabesu fa, shiyasa ya tsaya sai tsarata yake yi.Take kishin larabawan ta motsa, tamke fuska ya yi sosai game da cewa. “Ke! Sir Nirash na kiranki”. Yana faɗa ya juya ba tare da ya kalli in da Juraiz yake ba. A hanzarce ta miƙe, bata lura da yanayin face ɗinsa ba, da sauri ta rufa mashi baya suka shiga tantin Leo.Kamewa ta yi ta sara mashi kafin ta ce gatan nan……… A dake ya tambayeta game da aiki irin nasu Arya shin tana da kwarewa a kai?….. Kai ta gyaɗa game da sanar dashi cewa dik abin da su Arya suka sani ita ma ta sani kamar yadda dik abinda ta sani a ɓangaren nata aikin suma sun sani. Ya ji daɗin jin hakan, sai ya ce. “You can go”. Ya faɗa game da dawo da kallonsa a kan laptop ɗinsa.Take ya kwashi bayananta ya turawa Vash da bayanin yadda zasu yi aiki a tare…….. Ita kuwa ta zo dab zata fita Vash ya ce. “Daga nan ki wuce cikin tantinku! Dare ya yi”. Yana tamke fuska ya faɗa, babu wasa a tattare da shi. Cikin girmamawa ta ce. “Okey sir”. Ta faɗa tare da ficewa.Duka Noor ya kai mashi a damtsen hannunsa yana faɗin. “Ya da tamke fuska mutumin, ko dai ko dai?”….. Kara tamke fuskan ya yi. “Ko dai ko dai me?”. Ya tambaya irin ban gane komai ɗin nan ba. Noor ya ce. “Ko dai kana ciki da sister ɗin tamu ce?”….…… Kai ya girgiza game da cewa. “Kawai dare ya yi ne, amma ni bana cikin komai”…….. Zaynish ya ce. “In ta yi wari zamu ji”……. Murmushi Noor ya yi. “Kyalesa my Tiger, zai yi bayani ne”. Cewar Noor ɗin.Leo dai aikinsa ya cigaba da yi a laptop ɗinsa, ya fito da email na Arya, ta nan ya yi mata hello game da cewa it’s Nirash, dik wani information ki saka mun shi tanan, zan duba…… Sosai Arya ta ji babu daɗin ganin ya ce ta tura mashi ta email, hakan na nufin ba zai dawo tantinsu ba, ta so ne ya dawo ko kallonsa ta sake yi kafin ta yi barci, to amma ya zata yi? Haka ta danne tana shafa kan Jehan da ta tada kai da cinyarta tana aiki da hannu ɗaya, dik wani sabon abu da zata gani sai ta yi screen record ta tura mashi. Shi ma ya tasa laptop gaba yana aiki ba kama hannun yaro, tin yana ɗan jiyo hiransu Noor sama-sama na shakiyancin da suke yi wa juna har hankalinsa gabaɗaya ya bar kansu, bai ma san time ɗin da suka fice daga tantin kowanne ya wuce nasa tantin ba……. Wajen wuta Noor ya nufa, yana zuwa yasa hannu ya ɗauki V cak a yadda take zaune ɗin, ta baya ya ɗauketa. Bai direta a ko’ina ba sai cikin tantinsa. A tsakiyar electric mattress ɗinsa ya direta game da sauƙowa, ya zare rigan jikinsa ya ajiye kafin ya haye. Kwanciya ya yi a miƙe, cike da shagwaɓa sosai a muryansa ya ce. “My Juliet, tausa nike so, jikina na mun zafi”.Miƙewa zaune V ta yi, ta haye kan flat tummy ɗinsa, damatsan hannunsa dake a murɗen nan ta fara matsa mashi da lausasan tafukanta tana faɗin. “Sorry my Romeo”…….. Lumshe idanu ya yi laushin tafukanta na ratsa shi.Ganin haka yasa ta dage ta kara yi mashi sosai tana ta faman yi mashi sannu, ya ɗaura hannunsa ɗaya a kan mazaunanta ta baya yana aikin shafe mata su. Ta jima tana matsa mashi jikin kafin ya juya da ita, ta koma ƙasa shi ya dawo sama, kurawa juna ido suka yi, ya ɗan turo mata baki, a shagwaɓe sosai ya ce. “Julie, I’m in need of something very urgen”. Tana binsa da wani irin kallon ƙauna ta amsa da. “What’s that?”…… Sumbatar ɗan bakinta ya yi kafin ya amsa da. “You”……….. Lumshe ido ta ɗan yi game da sake buɗewa. “I’m yours already”….. “Sure?”. Yana shagwaɓe fuska ya faɗa. Kai ta gyaɗa mashi alamar very sure ma kuwa. Sumbatar gefen kumatunta ya yi game da komawa gefe ya kwanta, sai ya kawota jikinsa ya rungume. Daga nan ya ce su yi barci.Ba musu ta lafe luff a kirjinsa, ba jimawa barci yai awon gaba da su. A ɓangare Leo da Arya kuwa, tamkar yadda dare yake matsayin rana a wajen ƴan ta’addan nan, haka yakasance a wajensu. Aiki suka sha har karfe 3, tana tare da laptop ɗinta shima yana tare da na shi, sai da nasa ta ɗauke caji ya kare, sannan ya hakura, yai mata dropping messages through sms kan da safe zasu cigaba, da yake dik suna da number abokan aikin nasu, sai ya laluɓo nata ya turo mata saƙon.Yana tura mata ya kashe wayar, yai addu’ar barci ya kwanta. Ba jimawa barci tai awon gaba da shi. Ita ma kashe nata laptop ɗin ta yi, dama ba caji sosai, batteryn solar takusa ɗaukewa, tana kashewa ta miƙe ta ɗauki Jehan da ta yi barci a jikinta ta kwantar da ita saman mattress, ta gyara ta kwanta a gefenta, already su Angelina sun jima da yin barci.Saura sojojin dake sansanin suna bakin wuta suna ta hira tamkar rana ce ba dare ba, su Juraiz dik sun shiga tantunansu. ASUBA TA GARI.MORNING D—-O—-L 🌅🔥Asubarsu ta fara ne da farar asuba, shirin yin sallah suka yi, suka yi zaman karatun Alkur’ani mai girma kafin su yi askar ɗin safiya, Leo ya koyawa Noor karatun Alkur’ani na surori biyu daga ta ƙasa, ya fara ɗaukar haddarsu.Around 7 daidai suka tashi daga wajen sallar, suka nufi cikin tantunansu, a nan ne kowanne ya buƙaci ganin macen da zai yi aiki da ita.A can gefe kuwa, safiyar Arya ta fara ne da yi wa Jehan wanka, ta shafeta da mai, sai ta sanya mata kayanta tin da Jehan ɗin bata da kaya, wandon jeans baki da top fari, kayan sun ɗan yi mata yawa, amma haka ta sanya. Arya zata fita zuwa wajen koramarta Jehan ta ce zata bita. Hannunta takama suka nufi wajen koramar.Da zuwansu Arya ta shiga ruwa, Jehan ta tsaya bakin ruwa tana ta faman kallonta, tana murnushin dake kara mata kyau sosai. Watso mata ruwa a fuska Arya ta yi tana faɗin. “Zaki shiga ne?”. Ta faɗa game da yi mata nuni da hannu ta alama tana ɗaga mata gera guda Da sauri Jehan ga jinjina kai, dan mayyar son ruwa ce. Alama Arya tai mata da hannu kan ta shigo, da sauri ta cire wandon jeans ɗinta, sai taki cire riga dan an fara kirgan dangi, girma ya fara zuwa, dik tana kunyar cire rigarta a gaba kowa, idan Arya zata yi mata wanka sosai take jin kunya, kawai daurewa takeyi.Arya ta fahimci hakan shiyasa bata takura mata kan ta cire rigar ba. Da rigar ta faɗo cikin ruwa. Angelina dake tsaye a can nesa ne take mamakin yadda Arya take wasa da Jehan, sun dai san Arya macece miskisla mai mugun shariya ga mutane, ko su da suke ƴan huɗunta ma bata sakewa da su har haka bare mutanen waje, makaranta wannan ba’a gani a waje sai dole, bata murmushi bata magana sai aiki, abin ya yi mugun basu mamaki, lallai sun yarda so gamon jini ne. ALLAH ne ya haɗa jinin Arya da Jehan.Jawota kusa da ita Arya ta yi tana faɗin. “Kada ki je ta bakin nan ruwa ya tafi mun dake”. Riko hannun Arya ɗin ita ma ta yi suka cigaba da juyi a cikin ruwan….. Unexpected suka ji hayaniya ya fara tashi daga cikin sansaninsu, Arya na ƙoƙarin saurarawa ta gano menene sai ga Manassa da gudu tana faɗin. “Bloody, waɗan nan masu kiwon shanun da kika ɗauko Jehan a wajensu har kika daki mutanensu ne suka yi gangami da sanduna suka shigo sansaninmu wai zasu kashemu”………. Toh fah, Fulani sun biyo sahu, sun zo ɗaukar fansa.*Jama’ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba’ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*



