Hausa novels

Zakuna Biyar Page 29 By Princess Teema

“Daddy ka yi kyau sosai yau”. Ta faɗa tana riko hannunsa. Nisawa ya ɗan yi tare da cewa….. “Dik kyan daddy bai kai rabin baby Cherry Bloom ba, kin fini kyau ai”…….. Juyawa tai, ta kifa a saman mattress ɗin tare da kwantar da kanta da kyau a kan laps ɗinsa, tana ɗan wuwwurga kafafunta ta ce. “Daddy da gaske na fika kyau?”. Shiru ya ɗan yi for almost 2 mins kafin ya ce. “Seraphina tashi mu yi magana”. On a serious note yai maganar, hakan yasa ta miƙe zaune tana ɗan turo baki. Ɗan lumshe idanu ya yi saboda dafa laps ɗinsa da ta yi ta miƙe, zama ta yi suna fuskantar juna, ta natsu tsit.Hannunta ya kama cikin nasa, a natse ya fara gwada mata haramcin shiga toilet mutane biyu, ya ce haramun ne ma kallon tsiraicin juna. Ya so ce mata ma’aurata kawai aka halattawa ganin tsiraicin juna, amma sai ya fasa saboda shirmen da tai mashi ranar, kada tasa yau ma yai suɓutar baki, maganin kada ayi kada a fara, da yanzu yasan karamin aikinta ne ta jefa mashi tambayar da zai hana shi barci.Da yake tana son shi sosai, sai ta ce. “Ka yi hakuri daddy, ba zan sake ba, dama a school ne muke yi tare har da su sister Aana idan muka yi lattin zuwa class, amma ba zan sake ba”…… Ajiyar zuciya ya sauke tare da sake hannayen nata kafin ya ce. “To kada ku sake”. Faɗowa jikinsa ta yi tare da cewa. “Daddy baka zo kun gaisa da Rimsha bafa, ta zo har gidan nan”…….. Ɗan ɗauke wuta ya yi na ɗan sekonnin jinta a jikinsa kafin ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, tsintar kansa yai a wani irin yanayi, ɗan gyaran murya ya yi kafin ya ce. “Cherry ba kin ce kina son daddy ya aureki ba?”. Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e……… “To tashi in faɗa maki wani abin”. Da sauri ta raba jikinta da nasa, tana kallon kyakkyawan fuskansa…….. “Cherry, idan har kina son daddy ya aureki to ki daina hawa jikina”.Cike da mamaki ta ce. “But daddy why? Are you not my daddy?”…….. Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi, on a serious note ya ce. “Idan kina hawa jikina yanzu to aure zai haramta ne a tsakaninmu, ki bari sai mun yi auren tukun nan, ko oyoyo daga yau na hana, and in kina son in aureki ki dinga sanya ɗan kwali, ki kuma koyi sirri, kada ki sake faɗawa Rimsha abin dake tsakaninmu, dan babu kyau ki dinga faɗawa wata wani abu a kan mijinki”. Ya so ce mata idan tana kwanciya a jikinsa tana jefasa cikin wani yanayi, amma ya yi saurin kama bakinsa gudun ta jefesa da wata tambayar da ba zai iya amsawa ba, dan Seraphina kam hankalin da sauƙi.Hannu ta sanya ta toshe baki, tana ɗan murmushi ta ce. “Daddy waye ya faɗa maka ina faɗawa Rimsha maganarka?”……… Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa ya watsa mata kafin ya ce. “Kina faɗa mata ko baki faɗa?”….. Ɗan turo baki ta yi. “Ai kaɗan nike faɗa mata ba dayawa ba”……. “Awwe ashe dai kina faɗar”……. Murmshi ta ɗan yi ta sanya tafukanta ta rufe fuska. Wani irin kallon kauna ya wurga mata da waɗan nan dara-daran eyes ɗin nasa. “Dubeta a wajen”. Ya faɗa yana ɗan ciza harshe……… “Kai daddy kai daddy ka bari mana”. Ta faɗa tana kai mashi dukar wasa a kirji. Wani irin yanayi mai mugun daɗi ya tsinci kansa a ciki, sai kuma ya miƙe ya koma saman sofa, ya zauna yana cigaba da kallonta, ALLAH ne kaɗai yasan irin son da yakewa babyn Cherry ɗin nan nasa, kome take yi kyau take ƙara mashi, yarinyar ga shiga rai. Haka suka kasance, har around 10 na dare, yai mata sallama ya fito, tamkar zata yi kuka, bata son rabuwa da shi, to amma ya zata yi? Dole ta hakura. Yana fita ta kira Rimsha, Rimsha na ɗagawa ta ce. “My Nisha kin san me?”. Rimsha dake kwance a room na Faryan ta tada kai da laps ɗinsa suna kallo a laptop ɗinsa ce ta amsa da. “Ina zan sani tin da baki faɗa mun ba, meyafaru?”.Cike da farincini ta ce. “Daddy ya ce idan ina son ya aureni wai in daina faɗa maki tsakanina da shi, kuma wai in daina hugging ɗinsa, mu daina wanka tare”. Sai murmushi take yi ta faɗa, tamkar ba yanzu ya gama ce mata kada ta sake faɗa ba…….. Miƙewa zaune Rimsha ta yi tare da cewa. “To amma waye ya faɗa mashi kina faɗa mun?”…….. “Ni ma ban sani ba, kawai ya ce in daina faɗa maki ne”…….. Dariya Rimsha ta yi tare da cewa. “Daddyn nan naki daga gani rigimamme ne, to ba zaki daina faɗa mun ɗin ba, mu ba aminai bane? Mun zama one blood ma yanzu”. Tana murmushi ita ma ta ce. “Ai na ce mashi to ba zan sake faɗa maki ba, amma ba zan daina ba, kuma ba zai san na faɗa maki ba, yanzu ki bani shawarar yadda zan sa ya so ni sosai kin ji?”…… Satar kallon Faryan dake kallonsa ta yi kafin ta ce. “Ina room ɗin uncle Faryan, ki bari anjuma idan na koma ɗaki”…….. Hararar wasa Faryan ya dallah mata kafin ya ce. “Me kuke ɓoyewa?”……. Da sauri ta ce. “Uncle wannan da muka je gidansu ɗazun ɗin ne fa! Star ladyta! Ka tina?”. Da sauri ya ce. “Yauwa bani ita mu gaisa”. Bata kawo komai a ranta ba ta miƙa mashi wayar, karɓa ya yi suka gaisa, bayan sun gaisa ya dinga yabon kyanta, sai murmushi take yi, daga bisani ya ce. Bai so daina kallonta ba, dole ce kawai tasa, amma please ta turo mashi pics ɗinta dayawa bari ya dinga gani. Cike da murna ta ce mashi to zata turowa Rimsha ta turo mashi, daga haka suka yi sallama, ya katse kiran tare da dawo da kallonsa a kan Rimsha da ta tsaresa da ido. “Kai Nisha wannan kawar taki akwai kyau, kina ga eyes ɗinta, i wish in sameta matsayin mata, kai Nisha ina ganin ina sonta fa”. Hannu bibbiyu Rimsha tasa ta toshe baki tana murmushi kafin ta ce. “Uncle yau da kanka kake son mace?”. Gerarsa irin na Aryan ɗin nan ya ɗaga mata, cikin salon son Seraphina dake ratsa zuciyansa ya ce. “Wlh wani irin sonta ne ya shigeni tin da na fara kallonta, please Nisha help your uncle kin ji? Kinga kawarki ce, zaki iya koya mata sona”. Aikuwa cike da farinciki ta ce. “Uncle ko dan yadda ka kasance kai ɗaya ne mai sanyani farinciki a gidan nan dole in tayata samo zuciyar Seraphina, nima ina kaunarta sosai, zan so ta shigo zuriarmu kuma gidanka, ba zata yi wahalar samu ba, tana sona, tana da saukin kai, zata so dik abin da nike so, and zan baka numberta, kai ma ka dinga kiranta”……. Ya ji daɗin wannan kalamai, bai san time ɗin da ya bawa cheek ɗinta haɗaɗɗen sumbata ba, cike da farinciki ya ce. “In dai kika tayani shawo kanta nai maki alkawarin sabuwar waya da sabowar mota and laptop”. Wani irin tsalle ta daka ta rumgumesa tana murna, shi ma rungumeta ya yi yana murmushi.A yayin da haka yake faruwa, shi kuma Aryan yana master room na Abba suna magana da Abba a kan Rimsha, bai samu damar sauraren voice na wayar da su Rimsha suka yi yanzu ba.Yana zaune a gefen gadon Abba, while Abba yana kwance saman bed. Dik abin dake faruwa Aryan ya zayyanewa Abba game da Rimsha, abin da ya gani da idanunsa na abin da aka koya masu a school. Daga karshe ya ce. “Abba aurar da ita zan yi, zan haɗata aure da Vash in the next 2 months masu zuwa!”. Babu wasa a kan fuskansa.Miƙewa zaune Abba ya yi, hakika ya kiɗima da jin zancen nan, sai da ya fara maimaita hasbiyallahu wani’imal wakil kafa goma sannan ya ce. “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, a zamanin nan na yanzu kawai ALLAH ne zai iya kare maka zuri’a, wannan wace iriyar musifa ce?”.Shiru suka ɗan yi, can kuma Abba ya ce. “Aurar da ita ai ya zama dole ne, wannan musifa dole ai, sai ka shirya biyawa Vash ɗin sadaki, wata biyu ma ta yi nisa, gara a aura mashi ita nan da sati guda, dama zai zo ya yi kwana biyu kafin su tafi next mission kaga komai zai tafi daidai”………. “Haka ne Abba, amma a bari nan da two months ɗin”. Aryan ya faɗa, so yake a ranar da za’a ɗaura auren a haɗa da nasa shi da Cherrynsa, shiyasa yake son nan da 2 months.Da farko Abba ya so ja, amma daga baya ya hakura ya bar batun, nan da wata biyu za’a yi bikin. Sosai Abba ya shiga damuwa, a daren ranar wlh bai rintsa ba, Aryan na fita Abban yasa aka kira mashi Rimsha, tana shigowa zata hau jikinsa ya ce ta zauna a ƙasa magana zasu yi, ai tana ganin yanayin fuskansa ta natsu tsit.A ƙasa ta zauna, ta sha jinin jikinta, fuskansa babu alamar wasa ya ce. “Tambaya zan yi maki, ki faɗa mun tsakaninki da ALLAH”…… Cike da mamaki ta ɗago ta kallesa, bai taɓa yi mata magana irin haka ba, amma sai ta ce to zata bashi amsa tsakaninta da ALLAH.Kai ya jinjina game da cewa. “Kin taɓa kwanciya da wani ɗa namiji ko kin taɓa da wata ɗiya mace?”…… A zabure ta zazzaro idanu a kansa, ganin ya kara murtuƙe fuska ne yasa ta yi ƙasa da kai game da cewa. “A’a Abba, ban taɓa wlh”….. “Ki mun bayani da kyau!”. Ya faɗa in a harsh way, dan yana da mugun zafi, yanzu ne ma da tsufa tasa ya ɗan yi sanyi, amma da! Tab!……… Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. “Wlh Abba ban taɓa aikata ko ɗaya daga ciki ba, amma roommate ɗinmu suna yi, classmates ɗinmu ma suna yi, ni da Seraphina ne bamu taɓa yi ba”.Tarar numfashinta ya yi da cewa. “Meyasa kuke wanka a tare a toilet ku dayawa matsayinku na matasan ƴan mata?”…….. Jikinta ne ya soma rawa, cikin sanyin murya ta ce. “Abba wani lokaci ne idan mun yi lattin zuwa class muke wanka tare dan mu yi sauri, amma bayan haka ALLAH babu wani abin”…… Daga kalamanta yasan iya gaskiyarta take faɗe, dan haka sai ya ce ta tashi ta tafi ba tare da ya faɗa mata hukuncin da uncle ɗinta ya yanke kan aurar da ita ba…… Da sauri ta miƙe ta fito, a ransa ya ce yakamata ya fahimtar da Aryan cewa Rimsha bata taɓa aikatawa ba, dan ya kara tsanarta sosai, a bayanan da ya yi wa Abba ma ya yi kamar ya yarda ta taɓa aikatawa.Abin da yasa Aryan ya ce ta taɓa aikatawa kuma shi ne, ya fahimci bayanin Seraphina a baibai, da ta ce mashi sister Aana ta ce ita kirjinta basu girma ba, ba zasu yi komai da ita ba, kirjin Rimsha ya fi nata girma, to shi ne yake tinanin kenan tin da na Rimsha yafi nata girma suna aikatawa da ita kenan ai, bai san ba haka bane, bai fahimta bane, shi ne har da ƙara tsananta zai aurar da ita.Kwana tinane-tinane Abba ya yi, ya yi nadamar turata boarding school tana ɗiya mace, a zamanin yanzu da komai ya lalacen nan, gaskiya ya yi babban kuskure. Wannan damuwa ta hanasa rintsawa, washegari da sassafe ya haɗa kan Faryan da Harleen ya ce su rakasa benen kusa da su aje batun nemowa Aryan da Harleen auren Aunty Lusi da Aunty Luna, dan fa bai manta da zancen ba. Faryan ɗan auta kam ba ta shi ake yi ba, shi ance da sauran shi, basu san shi yana can yana ƙoƙarin sace zuciyar Baby Cherry bloom ɗin Aryan ba, ya samu numberta wajen Rimsha, jiya sun kwana chatting while Aryan sun kwana aikin IRON FIST, bai bi ta kan wayar Seraphina ba bare yasan abin da suke tattaunawa, ita kuwa tana nan Faryan ya tsarata son ransa, ya zuba mata kalaman da ta dinga murmushi har ta yi barci fuska ɗauke da murmushi. ……. Hmmmm ga shi da Aryan da Faryan sun fi shaƙuwa da juna, Aryan ya fi kaunar Faryan fiye da Harleen, akwai case kenan.Faryan sai dariya yake yi yana murna za’ayi wa Harleen auren dole, baya murnar za’ayi wa Aryan auren dole, amma yana murnar na Harleen, dan dama yana son a kuntatawa Harleen ko dan kuntatawa Rimsha da yake yi.Shiga ta mutunci suka yi, Abba thobe and bisht ya sanya, ya naɗa rawani, while Harleen and Faryan tail coat suka sanya. Kai tsaye suka nufi benensu Noor, sai haɗe rai Harleen yake yi. Ko da suka je daddyn Noor baya nan, amma sun samu uncle da su Aunty Luna, kuma sun karɓesu hannu bibbiyu saboda kirkinsu, yadda suka mutuntasu yasa Abba ya ji ya ƙara kwaɗayin su haɗa zuri’a, musamman yadda Aunty Luna ta gwada masu kulawa, da kanta ta kawo masu ruwa da abin taɓawa, ta zauna tana ta kula da su, uncle ɗin Noor ma akwai kirki da son mutane.Ya zauna kusa da Abba sai jansu da hira yake yi, musamman ma da ya ji ai maƙotansu ne, sai ya saki jiki da su sosai, ya girmama Abba sosai, ba ƙaramin daɗi Abba ya ji ba, hakan yasa ya furta buƙatarsa ga uncle kai tsaye. Aikuwa cike da murna uncle ya ce ai wannan ba wani abu bane, dan suna addini daban-daban ba zai hana su auratayya ba matuƙar su Aunty Luna suna so, bari yayansa ya dawo zasu yi magana, zasu tattauna, kada Abba ya wani damu zai ji amsa mai daɗi.Sosai Abba ya ƙara girmana dattakunsu, ya yi matuƙar farinciki, ya masu godiya sannan ya ce idan ba damuwa Aunty Luna su gaisa da Harleen, fuska ɗauke da fara’a ta ce ba komai, ta miƙe ta fita zuwa balcony, kin bin bayanta Harleen ya yi har sai da Abba ya ce. “Ka je tana jiranka”. Sannan ya miƙe yana haɗe rai ya fito balcony ɗin. Tana tsaye tana kallon cikin CP ya ƙariso wajen. Bai ce mata sannu ba sai da ita ta ce mashi. “Hy”. Sannan ne ya amsa game da ce mata. “Well-done”. Daga haka bai sake magana ba, har suka ɗauki 20 mins a wajen, sannan ya wuce ya dawo parlo, ga mamakinsa sai bai samu su Abba a wajen ba, sun koma gida.Siririn tsaki ya ja tare da bin bayansu, ita kuwa Aunty Luna ko a jikinta, sai ma son shi da ta ji ya shigeta, dan tana son namiji miskili, bata san wannan ba iya miskili bane, ɗan duniya ne.A ɓangaren shi kuwa Aryan, yana barin gidan Abba ya koma wajen Lion. A lokacin Lion ya dawo daga Ring Of Power, yana tsaye a balcony sanye da pj’s farare ƙal, ya saki kitson dake kansa wanda suka ƙasa mashi matuƙar kyau, hannunsa rike da cup of americano yana sha, ya zura hannu guda cikin aljihu, yana kallon yadda CRYSTAL PALACE ke a cikin dare, yana da matuƙar kyau da ɗaukar hankali, haske ta ko’ina tamkar rana, wani irin ni’imantaccen iska na kaɗawa a hankali-hankali wanda ke kaɗa kitson kansa suna motsawa, iskan gwanin daɗi.Wajen sky blue light ne, hakan ta ƙara fito da tsantsar kyan fuskansa, waɗan nan jade eyes ɗin nasa sun kara wani irin cool sun ciza, zaku ce barci yake ji, in baku manta ba shi da Leo idanunsa sun yi zubin sleeping eyes ai, to da yake yanzu yana cikin kwaciyar hankali sai idanun suka ƙara zama sak sleeping eyes sosai, pink lips ɗin nan nasa ya ciza kala matuƙa, yana ɗan ciza laɓɓan nasa a hankali alamar yana tinanin wani abin.Aryan ya ɗan jima yana kallon haɗuwar Lion, da dai ya ga bafa zai gaji da kallon kyan nan nasa ba sai ya kariso wajen, a kusa da shi ya tsaya, hannu yasa ya fara tattare kitson dake kan nasa, yana tarawa wajen guda kafin ya ce. “What a special day today! My man yana cikin farinciki”……. Aryan ya san idan Lion yana cikin farinciki ne yake sake kitson kansa a watse. Shiru babu alamar Lion zai yi magana. Ɗaure mashi gashin Aryan ya yi game da cewa. “Yakamata mu binciki meyasa ake cire mahaifar mata a asibitoci a hankalin yanzu? The case is getting out of hand, anywhere ka juya wannan magana ake yi, i think there is something behind all this”. Kai Lion ya ɗan jinjina ba tare da ya yi magana ba, hannu Arya ya miƙa ya karɓi Americanon dake hannunsa, sipping ya ɗan yi tare da cirewa, ya nisa before ya ce. “A Avaris abin yafi worst! But why, meyasa dik wata musifa a wannan ƙasar tafi yawaita kuma mutanen cikinta suka fi shan wahala”. Sai da Lion ya ɗauki good 2 mins kafin in a cool way ya amsa da. “Saboda Avaris tana da mutane irin IRON FIST”…….. Watau saboda tana da mutane ƴan baiwa, masu hazaƙa da basira, waɗan da idan suka samu dama a ƙasa da kwanaki suna iya saita duniya bakiɗaya ba iya Avaris ba, shiyasa ake dakushesu, ake hanasu motsi bare su ci ribar baiwar da ALLAH yai masu.Jinjina kai Aryan ya yi, zai sake yin magana guru ya hauro wajen da juggling, alamar yana cikin farinciki, cike da murna yai hugging na Lion kafin ya sake shi yai hugging na Aryan, daidau lokacin Zakinsu ma ya hauro da gudu yana wani numfashi alamar yana farinciki shi ma.Kai tsaye jikin takwaransa watau Lion zaki ya nufa, sai hayesa Lion ya ja baya yana ɗan marin fuskan zakin, ya ɗaure fuska kafin ya ɗaga mashi hannu alamar kada ya hau mashi jiki……. Hannu zakin ya ɗaga ko in ce kafafunsa na gaba, ya ɗaga duka biyu ya fara gurnani alamar Lion ya ɓata mashi rai.Hannu Aryan ya ɗaura a kan zakin yana ɗan shafasa alamar rareashi, guru kuma ya fara shafa ƙasan wuyan zakin. Harara Lion ya dallawa zakin irin ka daɗe baka yi fushi ba, sun ɓata ne yau, ta kwaɓe masu. Gurnani da karfi zakin ya yi irin zamu haɗu ne, zaka zo nemana wani lokaci. Lion bai dena hararansa ba yasa hannu zai kai mashi wata marin Aryan ya tare yana faɗin. “Kaga kada ka takurawa bawan ALLAH, ka ce kai haka kake wannan hali, bawan ALLAH bai maka komai ba ka nemi kuntata mashi, ka manta amanarsa aka bamu ne?”. Hararansu dikkansu Lion ya yi kafin ya matsa ya sauƙa ƙasa izuwa room na aikinsu, dan ya duba meyasa ake ta samin cases a kan cire mahaifa this year, me ake yi da su ne? And me yake jawo lalacewar mahaifar da za’a dinga cewa mata mahaifarki ya lalace sai an cire! Meyasa mace ta yi haihuwa ɗaya biyu wata ma har uku dik da kanta take haihuwa sai na kwanakin nan ne za’a dinga cewa ba zata iya haihuwa da kanta ba sai an mata aiki? Yanzu abin is getting out of sense, ya fara zama ruwan dare, ko’ina koken da jama’a suke yi kenan, so yakama IRON FIST su shiga wannan case ɗin su dakatar da koma menene ake shirin yi!.While Aryan ya kalli guru kafin ya ce. “Murnar me kake yi?”. Ƙara ɗaure fuska ya yi kafin ya amsa da. “Wasu banks na ƴan damfara ne suka kwashe kuɗin mutane zasu gudu, ina hawa media yanzu naga batun, al’umma sai kuka suke yi, shi ne na datsi tsaron banking, na fasa security ɗinsu, na sakewa al’umma kuɗinsu har ma da ƙari da na kwaso daga account na CEO na banking, na zubawa kowa ƙari ya fantama, yanzu koya banking zasu yi dan su dakatar da kuɗin al’ummar dake wannan banking ba zai yiwu ba, dan na sanyawa bakin tsaro nawa na kaina”.Aryan ya tari numfashinsa da cewa. “Ka ce kawai ka kwace banking, to ALLAH yai maka albarka, ai naga kwana biyun nan suna tinanin IRON FIST ta yi sanyi shi ne suka fara dawo da damfara da cutar mutane, dole mu koma bakin aiki dan kakkaɓe gurɓatattu, ni yanzu ma akwai in da zan je, sai 3 na dare zan dawo”. ……… Guru da yasan hali sai ya ce. “Kada ka masu kisan sauki, ka gana masu azaba kafin kashesu”. Kashe mashi ido ɗaya Aryan ya yi alamar ya gano komai, sannan ya wuce ya bi bayan Lion. Bayansa guru ya bi kafin zakinsu ya rufa masu baya da gudu. A ɗakin aikinsu suka isko Lion yana bincike, a kusa da shi Aryan ya tsaya, sai da ya manna mashi sumbata a cheek kafin ya sanar da shi zai fita sai karfe 3 na dare zai dawo. Kai kawai Lion ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. Wucewa ya yi izuwa room ɗinsu dan ya shirya. While shi ma guru ya bi bayan Aryan dan ya tayasa shiryawa, Lion kuma ya cigaba da aikinsa cikin kwanciyar hankali da natsuwa. ——————————-🔥AZURE.🔥A maimakon ta fara bashi labari sai ta shige jikinsa, ta lafe tana zuba mashi shagwaɓa. Hannu ya tura cikin gashin kanta, ya warware kullin da tai wa gashin, ya watsa har saman bayanta zuwa mazaunanta, bayanta ya cigaba da shafawa yana biyewa shirirtarta.Hannu ta tura ta baya ta rungumesa sosai, cikin shagwaɓa ta ce. “My Romeo yaushe zamu yi first night ɗinmu”…….. Idanunsa ya ɗan ɗaga sama, sai kuma ya ce. “Ba’a gidan nan ba, a gidanmu ko a wajen Mission”. “Why not a gidan nan?”. Ta tambaya tana ɗago kai, kunsan Angelina ta ɓata ta da kalle kallen banza, sannan yanzu ta gama kallon video ɗin in baku manta ba, gabaɗaya cike take da feeling shiyasa take mashi waɗan nan surutan da bata san tana yi ba.Matso da face ɗinsa dab ita ya yi, tamkar zai haɗe bakinsu sai kuma ya dakata game da cewa. “Kina buƙatata ne? Kina buƙatar mijinki?”. A shagwaɓe sosai ya yi magana……. Ɗan lumshe idanu ta yi tare da sake warosu a kansa. Slowly ta gyaɗa mashi kai alamar e tana buƙata. Tongue ɗinsa ya fitar ya ɗan lashi lips ɗinta da suka ciza kala saboda yanayin da take ciki. “Na fiki buƙata, amma ba’a gidan nan ba”….. Cikin wani irin murya tamkar ƴar maye ta ce. “Kana tsoron daddy ne?”…….. Kai ya girgiza mata alamar a’a kafin ya ce. “Bana son yin dis virgin ɗinki a gidanku ne kawai, na fi son a gidanmu ko a wani waje”. …… “Why?”. Ta faɗa tana saƙalo wuyansa ta ƙara shigewa jininsa sosai.Yana ɗan lumshe idanunsa da suka yi jajir da su ya amsa da. “Haka kawai, zan fi jin daɗi da samun peace of mind”…….. Nisawa ta yi kafin ta matsa ta haɗe bakinsu. Kissing ɗinsa ta fara yi in a romantic way. Moving hannunsa ya yi from her waist to her back. Ɗan tallabota ya yi tare da juyawa, ya kwantar da ita a saman sofar kafin yai mata runfa da buɗaɗɗiyar kirjinsa.Wani irin hot kiss ya shiga bata, cikin dabara ya sake moving hands ɗinsa izuwa saman botiran sleeping dress ɗinta. Ɓallesu yai ya cire, sai ya ɗan raba jikinsu tare da zame ɗan bakinsa daga nata. Ɗan lumshe idanu yai tare da sake warosu a kan tula-tulanta dake tamkar an bura balo-balo.Da kyar ya iya ce mata. “Where’s your bra?”… Kashe mashi ido ɗaya ta yi before ta amsa da. “Bana sanyawa da daddare”……. Hannu ɗaya ya kai ya shafi tula-tulan nata, cikin tsananin shgawaɓa in a romantic mood and voice ya ce. “Ohhhhh sh**** my Juliet, now all this is mine?”. Yana wani lumshe idanu ya faɗa. Ɗan turo mashi baki ta yi kafin ta amsa da. “Yeah is yours”…….. Kwantowa kanta kaɗan ya yi, baya son taɓata sosai saboda baya son yi mata komai a gidansu, shi ganinta kawai ya zo yi ya koma cikin barrack. A gefen wuyarta ya kwantar da kansa, yana shaƙar kamahin shampoo ɗinta na kamfaninsu mai kwantar da hankali, ya ɗaura hannunsa ɗaya a kan tula-tulan nata, yana shafawa a hankali yana ɗan lasan wuyanta.Gabaɗaya ya kara kiɗimata ga shi babu alamar zai yi abin da take so, juyawa ta yi ta kara shiga jikinsa sosai. Da ɗan karfi ya furta wash saboda yadda ya ji kirjinsa a jikinsa, ya ALLAH. Daurewa ya yi, ya rungumeta ba tare da ya sake taɓa wani abin daga jikinta ba, a hankali ya dinga shafa bayanta zuwa mazaunanta har barci ɓarawo ya saceta.Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara mata kwanciya, ya zareta daga jikinsa kafin ya miƙe, ya sauƙo ƙasa, a gaban sofar ya tsuguna game da sanya hannu ya rufe mata botiran da ya buɗe, sumbatar ɗan bakinta ya yi kafin ya miƙe, cak ya ɗauketa sai saman shoulder ɗinsa.Waje ya fito da ita, dik sojojin dake gidan basu lura da shi ba, da yake bq yana ta baya ne, so ta kofar kitchen da ya huda ta bayan ya bi izuwa cikin parlo. Nan ya isko Aunty Lisa tsaye shiru tamkar mai tinanin wani abin, ga alamar damuwa a kan face ɗinta.A saman sofa ya shinfiɗe V kafin ya dawo kusa da Aunty ya tsaya, sai da ya ja dogon hancinta, yana wani lumshe idanu saboda bai wastsake ba ya ce. “Lafiya kike tsaye a nan haka?”. Ɗago da eyes ɗinta irin nasa ta yi, kallo ɗaya tai mashi ta ɗauke kai tare da cewa. “Ango har an gama cin amarcin ne?”. ……. Ɗan shagwaɓe fuska ya yi. “Kai Aunty ki bari, my Juliet special ce, a special time and place zan yi abin da ya dace, yanzu dai faɗa mun menene yake damunki?”.Tamkar zata yi kuka ta ce. “Our pleasure ina cikin damuwa”….. Ɗan zazzare eyes ɗinsa a kanta ya yi kafin ya ce. “Wani irin damuwa kuma?”……. Hannunsa ta ja suka fito parlo ta kofar baya wajen kitchen, suka tsaya ta wajen tank na ruwan gidan, cikin sanyin murya ta ce. “Damuwata guda biyu ne”……. “Okey I’m listening”. “Na farko ina fargaban yaran honey ba zaku karɓeni a matsayin uwa ba, musamman Arya, dan ya faɗa mun sau da dama yana yunkurin yin aure su Arya suna hanawa, baya son ɓacin ransu saboda maraicinsu, shiyasa ya ce kada in faɗa masu cewa ni matarsa ce, yanzu dai ƴar ɓuya muke yi da su, ko ɗakinsa bana zuwa sai sun yi barci, hakan yana damuna”. Zuba mata idanu kawai ya yi yana mamakinta ita ɗinma tukunan……… “Damuwata ta biyu shi ne, a fannin aikina na gano wani waje da ake safaran yara mata ƙanana ana kaisu ana ɓuyewa, sai a dinga kaiwa manyan shuwagabanninsu suna lalata da su a gidajen shaƙatawarsu da manyan hotels a nan AVARIS, wannan abu ya yi matuƙar ɗaga mun hankali, amma na rasa yadda zan fito da maganar, dan manya daga cikin ƙasar nan ta AVARIS suna da sa hannu a wannan al’amarin, na ji ina tsoron yin magana”.Tin da ta fara wannan magana jikinsa ya fara tsuma, ɗan rintse idanunsa ya yi, ya sake warosu a kanta, ai take ya wastsake daga mayen da V ta sanya shi, a dake ya ce. “Wani irin lalata ne wannan? Ai wannan ba abin ayi shiru bane, ba kina da evidance ba?”……. Kai ta gyaɗa mashi da sauri alamar e.Hannu ya miƙa ya riko shoulders ɗinta, cike da jarumta ya ce. “Rayuwar yaran da basu ji ba basu gani, yaran da basu san komai ba, rayuwarsu zaki taimaka, buɗe wannan sirri wa duniya tamkar taimakon al’umma ne, please aunty kada ki ji tsoron kowa, ki fitar da sirrin kuma ki takurawa GAT da ya bawa sojojinmu umarni su tarwatsa wannan waje su ceto yaran nan da ake kawalcinsu zuwa manyan hotels da manyan wajen shaƙatawa, mu muna gab da tafiya MISSION, ba lallai su yarda su turamu wajen ba, amma naso ace mu aka tura”. Kalamansa sun kwarara mata gwiwa, sai ta ji cewa zata iya haska wannan labaran, zata haska video ɗin da ta ɗauka, dan haka sai ta ce. “I really love you my pleasure, zan yi dik abin da ka ce “……… “Love you too Aunty”.A daidai lokacin comboi na motocin daddy GAT suka danno cikin gidan, dole ba dan yana so ba yai wa sister ɗinsa sallama, ya nufi hanyar fita, sai da ya tsaya ya sarawa GAT, suka gaisa, sannan ya koma cikin barrack. Gidansu na cikin senior staff area ya koma, a parlo ya isko Vash, Unays, Juraiz and Zaynish suna zazzaune, Vash ya gama samun sauki sosai, dukkansu suna rike da cup na black tea suna sha. Kamar Noor zai wucesu, sai kuma ya zauna a kusa da Zaynish yana faɗin.”Bro what’s going on?”….. Zaynish da fuska yake a murtuƙe tamkar hadari ne ya amsa da. “Vash ke bani wani banzan labari wai yai gamo da demon”…….. Siririn tsaki Noor ya ja kafin ya ce. “Ina demon ɗin? Bata san sojojin AZURE ne a gabanta ba ne?”. Da sauri Vash ya ciro wayarsa ya fara nuna mashi chatting ɗinsu. Karɓa Noor ya yi, a kallon farko ya gane ɗaya daga cikin yaran GAT ne, dan yadda suke typing dikkansu iri ɗaya ne, yana chat da Angelina da V, dik typing ɗinsu iri ɗaya, kuma yanayin turancinsu iri ɗaya ne, sun fi amfani da turancin England sama da na America, kun san turanci kala biyu ne, akwai Europe akwai kuma na America, kowacce kika yi daidaitacciya ce, amma fa su dai masu jin turancin America idan kika masu turancin England zasu yi ƙoƙarin gyara maki ne, su ce ba daidai bane, amma masu jin European English kat ne, su idan kika yi American English zasu gane kin yi daidai, saboda su ne kat a turanci, su ne suka iya daidai, kamar yadda a hausa akwai na Zanfaranci, Sakotanci, Kanawa, Zazzagawa, Katsinawa da sauransu, to haka suma Europe and America. Ai kunga wata kalma idan bakano ya faɗa kuma basokwace ya faɗa sai ku ji sun banbanta sosai, alhalin su abu guda suke nufi, to haka American and European English suke, ku su America English ɗinsu ba shi ne ainahin turanci ba, amma kuma a yau da turancinsu duniya tafi amfani.A yau idan zaki yi European English wanda ke jin American English sai ya gyara maki, ya ce ba daidai bane, bai san nasa bane fake! Bari in baku ƙaramar misali ku gani American English zasu ce Color, Organize, Defense, amma European English zasu ce Colour, Organise, Defence , kunga spelling ɗin akwai banbanci, to idan kika rubuta haka ga wanda yake jin American English zai ce sam ba daidai kika yi ba.Kari misali, American English zasu ce. I just ate. European zasu ce I’ve just eaten, American zasu ce on the weekend, European za su ce at the weekend, spelling ɗin yana zuwa daban-daban, ƴan iyayi sai su ce zasu maki gyara saboda su fake ɗin suka iya, kunga yanzu America ta fi karfi a idanun duniya, shiyasa turancinta ya fi karfi a duniya aka bar ainahin daidaitaciyar turancin.So yaran GAT da European English suke amfani, shiyasa Noor na karɓa ya gano sune, amma bai nunawa Vash ya gane ba, saboda surakannensa ne, kada ya ɓata masu niyarsu a kan Vash, kuma ya ga yadda take cika baki har da cewa ko motsi Vash ya yi a tafin hannunta yake, so ba zai so tona mata asiri ba, ya ce bari ya kyale ta tonawa kanta asiri da kanta.Miƙawa Vash wayar ya yi yana faɗin. “Gaskiya demon ce, amma ka jajirce kada ka tsorara da lamarinta, babu wani abin da ta isa tai maka”. Jinjiina kai kawai ya yi, shi kaɗai yasan me yake ji a ransa, yana tsananin son Manassa da ya gani, amma yasan tafi karfinsa, yana fama da wannan ciwon a zuciya ga demon ta zo zata ƙara mashi wahala wai son shi take yi, kuma kada ya kuskura ya kula wata macen. Kai Manassa ƴar duniya ce yarinyar nan, kuna ganinta shiru-shiru, wai in ya kula wata macen sai ta kashe yarinyar dan ita bata kishi da mace! Ku ji wani lukutar balai.Miƙewa Noor ya yi ya nufi sama room ɗinsa shi da Leo. Yana shigowa ya isko Leo kwance yana waya da Aryan, a gefensa ya zauna yana ganin yadda guy ɗin nan ke magana a natse, one after the other, cikin kwanciyar hankali ga sanyin murya, yana waya yana ɗan murza dogayen natsun hannayensa, yana kuma ɗan jujjuya jade eyes ɗinsa sama tamkar mai tinanin wani abin.Can ya ce. “Yah Champion na fi kewarka sama da kowa, amma ba zan zo ba, saura sati ɗaya ne mu tafi Mission na gaba, lokaci ya kure, na so in zo ko kwana guda in yi, amma ba lokaci”. Ya kai karshe tare da dawo da kallonsa a kan Noor. Shafa lallausan kumatunsa Noor ya yi, a ransa ya ce dole ƴan mata idan suka ganka su bi su rikice ai, haɗuwa iya haɗuwa.Daga can ɓangaren Aryan ya ce. “A ranar da zaku tafi dole zan zo in ganka, ba zan iya ka shiga Mission na uku ban ganka ba our heartbeat”………… “Ni kaina kewarka kamar zan yi hauka, amma ba yadda na iya”….. Gyara zama Aryan ya yi kafin ya shiga bashi kalaman da zasu karfafa mashi gwiwa, ya dinga nuna mashi jarumta. Sun shafe awa biyu suna waya kafin su yi sallama. Kuma dik wayar nan da suke yi fa Aryan yana zaune gaban wasu mutane uku da ya ɗaure da chain, yana ta faman shirya kayan da zai yi amfani da su wajen gana masu azaba, mutanen da suka baiwa Aunty Safiyya aikin kamo masu Seraphina ne ya damko, in baku manta ba dama ba ya cewa su guru zai fita sai 3 ma dare zai dawo ba? To ga in da ya tafi nan, ya yi shirin gana masu azaba har sai sun faɗa mashi meyasa suke neman Seraphina.Ita kuwa Aunty Safiyya tana can tana shirya yadda zata fito da Seraphina ta kaiwa mutanen ta ci makudan kuɗin da ta karɓo, bata san a hannun Aryan take ba. Yanzu dai mu koma kan Leo, mun baro su Aryan, zamu waiwayesu mu ji yadda zai yi da mutanen, yanzu muna Barrack ne, kada na ruɗaku! ————————-Leo yana katse wayar ya kira guru, a lokacin guru na zaune tsakiyar bed ɗin Lion yana rike da laptop yana cigaba da kwashe kuɗin CEO na bankin yana rabawa bayin ALLAH, kai IRON FIST duniya ne, ka kuskura ka faɗo tarkonsu ka shiga uku, dik wani hau ɗinka sai sun gyara maka zama sun sanya ka shiga taitayinka! In dai kaifin ƙwaƙwalwa ne ALLAH ya basu, basirarsu sai dai ayi shiru kawai, ku duba fa, yana kwance a gado cikin kwanciyar hankali yana rabawa al’umma kuɗin da azzalumai suka danfaresu, kai guru ma takadari ne wasa-wasa, ka gansa kamar ba ruwansa, amma idan ya tabka wata tsiyar sai ya gigita ƙwaƙwalwa.So guru yana zaune a saman bed ma Lion, while Lion yana balcony yana waya da mr president. Picking ya yi tare da karawa a kunne, daidai lokacin Heronsu ya shigo da gudu yana wani irin girgiza, daga balcony wajen Lion ya fito.Jikin guru ya haye yana ɗan gurnani sama-sama, shafa wuyan zakin guru ya fara yi yana amsa gaisuwar da Leo yake ɗaga mashi, shi ma sun ɗauki awa suna waya kafin su yi sallama ya kira Big Bro ɗinsa watau Lion. Sai da ya yi wa Lion kira uku yana katsewa, sai a na huɗu ne ya ɗauka, kuma wayar tana aljihunsa yana ji, kawai a lokacin kiran farko dana biyu dana ukun ne bai yi niyyar ɗauka ba ɗan duniya, bai son motsa jikinsa. Ko da ya yi picking shiru bai yi magana ba, sai da Leo ya ce. “Good evening bro”.Nan ma shiru ya yi for almost two mins, ba dan Leo ya saba da halinsa ba da ya jima da katse kiran, amma ya hakura yana jiran ya amsa mashi. Can a maimakon ya amsa gaisuwar sai dai ya ce. “Chat me on whatsapp!”. Daga haka ya katse kiran, magana tana mashi wahala, idan chatting ne lafiya lou zai maka typing komai tsawon amsa ya tura maka, amma ko voice bayayi a Whatsapp ɗin ma, dan ba zai iya wani dogon magana ba, haka guru yake da wannan ɗabia, ya gwammaci chatting, shiyasa zaku ga basa yawan magana da Leo. Shi kuma Aryan da mutum ɗaya yake dogon hira, Leo kawai, shi ma ALLAH ya haɗa jininsu ne, kuma babu wanda ya ci wahalar renon Leo biyun Aryan, ba irin goyashe da bai ba, shakuwarsu ta zarce yadda kuke tinani, shiyasa da shi zaku ga suna magana sosai, idan ba da shi ba ba zaku taɓa cewa Aryan ya iya magan ba. A fili Leo ya ce. “Dama na san hali, ni ban san meyasa ma na kiraka kai tsaye ba, let me drop you a message on Whatsapp”. Ya faɗa tare da yi wa Lion typing na gaisuwa da fatan ya wuni lafiya, daga karshe ya rufe mashi da addu’a da kuma kalaman dake nuna yana tsananin so da kaunar ɗan uwan nasa, daga haka ya kashe wayarsa gabaɗaya.Yana kashewa Noor ya faɗo jikinsa yana faɗin. “Guess what!”…….. Harara Leo ya dallah mashi kafin ya ce. “Tashi mun a jiki rigimamme kawai”……. Ɗan turo baki ya yi. “I just got married bro, what advice do you have for me?”.Wani irin harara da Leo ya dallah mashi sai da ya ji barci ta kama shi, ɗan tsuke fuska ya yi tare da sauƙa daga jikin Leo, yana haɗe rai ya nufi sauƙa ƙasan gadon. Ganin kamar ya yi fushi ne yasa Leo riko hannunsa. Ai da sauri ya juyo, dama yasan Leo ba zai barshi da fushi a cikin daren nan ba. “Okey tell me I’m listening”. Leo ya faɗa a natse……. Cike da farinciki ya fara faɗawa Leo ya yi aure, kuma Aunty Lisa ce ta shige mashi gaba. Shiru Leo ya yi yana saurarensa har barci ya ɗaukesa. Da Noor yaga ya yi barci sai ya kwanta gefensa shi ma ba jinawa barci tai awon gaba da shi.Washegari da sassafe, shirye suka cikin kakinsu tamkar kowani jami’i. Noor and Leo a tare suka fito daga room ɗinsu, sun yi matuƙar kyau cikin wannan uniform ɗin. Ku fahimci wani abu ɗaya, ita kyau daban-daban ne, masu cewa Noor ya fi kyau, wasu su ce Leo ya fi kyau, to bari in banbanta maku wani abin a nan. Noor European ne, kyansa na asalin turawa ne babu mix, yana da idanu masu zurfi, masu girma dara-dara, kuma kowa yasan idanun European farare ne kal, sai kwayar kuma zaku samu mafi akasarinsu olive green ne ko tiger brown, or blue eyes, to idanun Noor olive ne, and suna da shape na fuska mai kyau, kuma mai ɗan tsawo, sannan gashin kansu ba’a miƙe yake ba, yana nannaɗe ne sosai kamar indomie, da wuya ku samu asalin European da mikakken gashin kai, sai in sun miƙar da shi na ɗan lokaci kafin ya koma yadda yake a nannaɗe, sannan su dogaye ne sosai, haskensu irin up white ɗin nan ne mara control watau haske paw sosai, a cikinsu ana samun launin lips ja, pink and purple, ga shin gerarsu na da cika sosai, kuma yana da faɗi, to dik in da asalin European yake haka zaku gansa da waɗan nan suffa.Su kuma Pamira people suna da zubin larabawa ne, musamman mutanen Pakistan, suna da yanayi da Pakistan kaɗan, amma sun fisu kyau, kunga ko a nan kyan ya banbanta, dan dik duniya larabawa ne karshen kyau, su ne haskensu bai yi yawa ba, komai ɗinsu daidai mai control! To amma Pamira ba larabawa bane! Suna dai da zubin halitta kusan iri guda ne, a in da suke kamanceceniya kuma shi ne idanu, idanunsu manya-manyan a buɗe da tsawo ba karamar European da nasu ke da zurfi ba, kuma su farin cikin idanunsu ba fari kal bane, milk color ne, larabawa kullum bakin cikin idanunsu baki ne kirin, ko kuma brown, amma su Pamira kala uku ne ƙwayar idanunsu, olive green shi ya fi yawa a cikinsu, sai kuma jade wanda zaku iya kiransa da ash, na karshe violet, sai ɗan brown da ba a rasa ba. Pamira su farinsu irin pure white ɗin nan, kaman korean skin, su kuma larabawa farinsu sese-sese ne. Larabawa gashin kansu baki ne ko brawn, pamira golden white ne ya fi yawa, ko kuma ash or brown da ba sosai ba, Pamira suna da tsawo sosai, da mazans da matansu, suna da pink lips mafi akasari, suna da cikar halitta da zarra sosai, sannan basu da yawa sosai a duniya, in taƙaice maku kyau kam daga kansu an rufe kofa, Pamira yana iya sajewa da ƙuraishewa sai ka zaci nasu ne saboda kamanninsu yana yanayi, sai hasken fatar da pamira suka fisu, fatan yanzu kun gane banbancin? Ba zaku haɗa kyan Leo da Noor ba, dan yarensu ba ɗaya ba, kowa gwani ne a ɓangarensu, amma Leo kat ne!….👌Uniform ɗinsu yana mugun yi masu kyau, musamman tactical t-shirt and tactical trouse, ya ALLAH, idan suka sanya tamkar ka tsaya ka yi ta kallonsu kada ka dakata.Suna fitowa harabar gidan sai ga wani soja ya shigo, a gabansu ya tsaya ya sara masu kafin ya ce. “Sir GAT na kiran sir Nooriel”. Cike da mamaki Noor ya kalli Leo, sai kuma ya jinjina kai alamar he’s coming. Juyawa sojan ya yi ya fita, shi kuma Noor ya ce da Leo. “Bro meyasa GAT yake nemana?”.Shiru Leo ya ɗan yi kafin ya ce. “Jeka ji mana”……. Kai ya jinjina kafin ya wuce ya tafi cikin tsananin takun jarumta. Bayansa Leo ya bi suka fito wajen harabar gidan, cikin barrack Leo ya shiga yana ɗan kewaye, ya zura hannaye a aljihu yana ɗan tattaki. Shi kuwa Noor kai tsaye office na GAT ya nufa. Sai da ya yi excuse ya jira aka bashi izinin shiga. A natse ya shiga ciki, ya sha madarar mamakin ganin V a office ɗin, ita da Angelina suna zaune saman doguwar sofar dake cikin office ɗin, suna rike da wayoyinsu. A gaban GAT ya tsaya tare da sara mashi, bai ɗauke hannu ba har sai da GAT ya jinjina kai alamar sarawar ta yi, sannan ya sauke hannunsa ƙasa. Satar kallon in da V take ya yi, hakika ta lashe zuciyarsa a wannan safiya, ta yi fitina cikin wani haɗaɗɗen gown da ya tsaya mata iya ƙasan cinya wajen gwiwa, ga rigar ya bi shape ɗinta, hannun rigar da chain ne, while kafafunta na cikin gucci ace sneaker da ya yi balai karawa dressing ɗin nata kyau, gata fara, shigar dark purple ba karamin fito da kyanta ya kara ba, shigarsu iri ɗaya da Angelina, sun gyara ash hair ɗin nan nasu, sai sheki yake yi, na gaban goshi ƴan guntayen nan suna kwance luff. Yana sauke idanunsa a kanta sai ya ga shi take kallo tana yaba kyansa. Shammatar GAT ya yi ya ɗan mata alamar heart da hannu yana ɗan lumshe idanu irin ta haɗu ɗin nan. Kyakkyawan murmushi ta sakar mashi kafin ta haɗe babban yatsarta da manuniya tai mashi alamar perfect. Kashe mata ido ɗaya ya yi in a love mood, ya ɗan ciza laɓɓa alamar wankarta ta cijesa sosai. Ita kuwa alamar sumbata tai mashi da ɗan bakinta. Daddy GAT yana can yana cike wasu forms yana jawa Noor aji, wai sai ya barshi a tsaye kafin ya umarcesa da abin da zai mashi, bai san nan suna shan sharholiyansu ba, soyewa suke a ɓoye a office ɗinsa.Dik abin da suke yi Angelina na kallonsu, can ta matsa dab kunne V, a ɗan shagwaɓe ta ce. “V i wish in samu wanda zai kasheni da soyayya irin Romeo ɗin nan naki mana, ohhh shi***, V ya haɗu, ya iya love, ga jarumta, ga shagwaɓa, irin mijin da nike so, please help me find out someone like him”. Tana faɗa tana ɗan ciza laɓɓa irin abin ya cizata ɗin nan.Kwanciya a jikinta V ta yi game da cewa. “We will talk later, yanzu kada ki katse mun jin daɗi”. Ta faɗa tana ɗan fito da tongue ɗinta ta ɗan lashi lips ɗinta tana ɗagawa Noor gera guda. Yana ɗan tauna gefen lips ɗinsa yai mata wani alama da hannu wanda ta sanyata waro idanu waje a kan fuskansa, kashe mata ido ɗaya ya yi…….Wannan alama dai yai mata tafi karfin bakin STARLADY ɗinku shiyasa na gagara kwatanta maku alamar, Noor ya goge mun hadda ne gabaɗaya.Daidai lokacin GAT ya miƙo mashi key ɗin mota, a dake ya ce. “Take them to shopping, make sure you take good care of them, and as from today kai ne zaka dinga kula da su, dik in da zasu je kai ma aminta kawai ka kaisu, ko a wajen mission na damƙasu a hannunka”….. Ba komai ne yasa GAT yai hakan na face dan yana auren Aunty Lisa, kunga yanzu ai sun zama ɗaya, Noor ƙaninsa ne, so yana ganin babu wanda ya cancanci kula mashi da su idan ba shi ba…….. Ni kam na ce tab, V and Noor an samu promotion ai, kai kam daddy GAT sai dai mu ce sorry, sai kaga V da ciki zaka gane karatun, zaka gane kura ka baiwa ajiyar nama.Team Noor muna cikin alkhairi dumu-dumu.Sara mashi cikin zafin jini Noor ya yi bayan ya karɓi key ɗin……… “You can go with them now, this is my ATM, they know my pin”. Ya kai karshe tare da miƙo mashi ATM card ɗinsa. Karɓa Noor ya yi, cikin zafa ya nufi waje.Da sauri suka miƙe suka bi bayansa suna faɗin daddy sai mun dawo, hannu ya ɗaga masu cike da tsantsar kaunarsu. A waje suka isko Noor, yana gaba suna biye da shi har wajen motar GAT, a nan suka tsaya suna ce mashi ya jira Arya da Manassa, suna zuwa yanzu. Buɗewa V gidan gaba na motar ya yi tare da ce mata ta shiga. Fakar idanun mutane ta yi, ta gaza hakuri har sai da ta ɗaga kafafunta ta shafi lallausan kumatunsa kafin ta shige ciki. Mai da kofar ya yi ya rufe yana kallonta, ya tsaya jiransu Arya, ita kuma Angelina ta shiga gidan baya.A daidai wannan lokaci ita kuwa Arya tana cikin barrack tana faman yawon neman in da zata ga Leo, so kawai take yi ta ga fuskansa ko zata ji sanyi a ranta, ta damu sosai, tin dawowarsu Mission basu haɗu ba, sai dai hotonsa da take aukin kallah kullum.While ita ma Manassa tana can yawon neman Vash dake cikin gidansu bai fito ba, ga nan Noor na tsaye yana jiransu. —————————-🔥WS-HOSPITAL. Bari mu ɗan leƙa ya suke ciki mu dawo mu ga ya za’a ƙare da yaran GAT.A wannan rana da yamma su sister Zinta sun gane ALLAH da girma yake, sun raina kansu, domin kuwa tin suna iya ƙoƙarinsu wajen yi wa yaran nan wanka har suka gaza, babys 30 suka samu suka yi wa wanka da kyar, sauran kawai suka jiƙa towel suka gige masu jiki, suka ce ba zasu iya wannan azaba ba. Ga wannan baby sai kuma yake ta yi, Maya na ta fama da shi, ta sanya mashi suna darling, sai jijjiga shi take yi, idan ya yi shiru anjuma sai ya sake fara wani kuka.Ana haka 3D suka shigo cikin ɗakin. A tare kirjin sister Maya and sister Zinta ya buga, sai suka tsinci kansu da faɗuwar gaba na ganin 3D, sai suke jin kamar ba alkhairi bane ya kawosu.Baby hannun Maya Dr James ya karɓa, basu yi wa kowa magana ba suka wuce wani glass wall room dake gefe guda. Ɗaki ne mai cike da na’urori kala daban-daban. Gabaɗaya hankalin sister Zinta and Maya ya tattara ya koma kansu, da yake glass wall ne suna iya hango me suke yi daga in da suke tsaye.Kwantar da baby suka yi a kan wani ƙaramin bed, take yaron ya yi shiru tamkar sun rufe mashi baki. Wani na’ura mai matuƙar hasken gaske suka kunna mashi a kan fuska wanda yasa yaron ya datse idanunsa yana ɗan girgiza jikinsa kaɗan alamar baya son wannan haske.Sosai hankalin su Maya ya tashi, da yake a wurin yau sister Maya ɗin ta fi rike babyn, sun fi shakuwa sai ta ji kirjinta na bugawa da karfi, jikinta ya fara kerma, ta dakata daga goge jikin sauran babys da take yi, gabaɗaya ta tsayar da kallonta a kan 3D take ƙoƙarin tura yaron nan cikin na’urorin dake jikin gadon da yake kwance.Ko me zasu yi mashi kuma? ALLAH masani sai kuma alƙalamina.

Back to top button