Zakuna Biyar Page 22 By Princess Teema
Zame rigar ya yi tare da ajiyewa a gefe saman wani dutse. Ai kasaƙe Arya ta yi tana kallonsa, ta kuma gagara daina kallon nasa dik da rikitata da ya yi. Cikin zafin nama ya motsa izuwa dab bakin ruwan, sai a lokacin ta lura da sojojin huɗu dake bayansa wanda sun juya mashi baya suna rike da bindigu dan bashi tsaro. Ƙara rage tsawonta ta yi ta hanyar ƙara natsawa cikin ruwan saboda ta ɓoye kirjinta, dik da take bata da addini lallai bata yarda a kalle private part ɗinta ba, musamman kirjinta, a cewarta dik wanda ya kalli tsiraicinka ya gama da kai, kuma ba zai sake kallonka da wata daraja ba, kuma zancenta haka ne, ni ban ga amfanin fitar da surar jikin da wasu ƴan matan suke yi ba, dik ranar da namiji a waje ya kalli albarkatun da ALLAH yai maki shikenan kuma, ALLAH baya kuskure, ba a banza ya ce mata ku suturta jikinku ba, amma wasu suna ganin kamar wayewa ce su bar ko’ina a buɗe, wlh dik namijin da yasan ciwon kansa ya fi son macen dake cikin hijabi, yana son sanin ainahin abin dake a cikin hijabin ne.Ko sau ɗaya Leo bai ɗago ya kalleta ba, ya shige cikin ruwan abinsa, sai dai bai tsaya ta kusa da ita ba, saboda ita tana tsoron can tsakiyar ruwa, ta baki-baki ta tsaya, shi kuma wajen yai mashi kaɗan tin da ruwan ko waish ɗinsa bata kai ba.Can ya shiga har sai da ya kai in da ruwan ta zo daidai kirjinsa. Gagara motsawa Arya ta yi tamkar wacce ta sume, slowly ta juyo bayanta ta ɗan saci kallonsa. Wankansa yake yi cikin kwanciyar hankali, kirjinta dake barazanar tarwatsewa ta dafe tare da jan dogon numfashi kafin ta furzar a hankali, a idanunta kawai ta fara kallon irin yadda ya cire rigar a gabanta, ya ilahi, ita kanta ta shaida Leo ya haɗu matuƙa, jikinsa tamkar madara, ba tabo ba ciwo sai wannan tsage na gerar tasa da ta ƙara mashi kyau sosai. A takaice sai da ya yi wankansa ya fito, ya mayar da bathrobe ɗinsa ya bar wajen sannan ta samu salamar dawowa cikin hayyacinta, a lokacin ta ɗan iya samun motsawa, jikinta dik a mace, ta ji ba zata iya cigaba da wankar ba, sai kawai ta fito ita ma. Ganinsa dik ya kashe mata jiki, da kyar ta mayar da kayanta ta nufi ɗakinsu. Nan ta isko su Angelina dikkansu a ciki suna ƙoƙarin shiryawa cikin kayan aiki, sun yi wanka a tantunan da suka kafa. Da ganinta suka nufeta suna tambayar lafiya? Dan sun ganta tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki ne. A takaice ta ce masu babu komai, sannan ta wuce ta ɗauki uniform ɗinta, a gurguje ta hau shiryawa, while Angelina and V sun kammala shiri har sun fito da laptop ɗinsu dan yin aikin da ya kawosu. Tactical trouser and tactical t-shirts Arya tasa, kayan sun yi mugun yi mata kyau, ta goge gashin kanta dake zubar da ruwa, ta shirya tsab tare da zube perfume ɗinta na kamfanin STAR LADIES BODY LUSH, sannan ta nufi wajen laptop ɗinta. Ita kuma Manassa miƙewa ta yi ta nufo waje dan ba aikinta bane yanzu, tana da free time….. Sosai suka dukufa a kan aikinsu na tsawon good 30 mins, V tana duba ta kudanci, Angelina ta kudu maso gabans, Arya ta yamma maso kudu. Idan a aikin computer ne jama’a to a barwa Arya kayanta, cikin ƙankanin lokaci ta gano motsi a wajen, sannan ta yi amfani da sound-d ɗin jikin drone da ta tura dan jiyo menene a wajen, ta sanya katan Bluetooth ɗinta a kunnuwanta dan ta ji me ake cewa da kyau.Magana ta ji na mutane, amma bata iya ganinsu, sannan maganar bata iya fita sosai, amma confirm ƴan adam ne suke magana a wajen. A natse ya zare Bluetooth ɗin daga kunnenta, ta ɗaura saman table da laptop ɗin nasu yake, sannan ta miƙe ta fito waje. Kirjinta na bugawa da karfi ta isa wajen tantin su Leo, daga bakin kofa ta tsaya, yanzu dai taki shiga ƴar kaniya, tana tsoron sake ganin abin da ta gani jiya da kuma ɗazun. Sara mashi ta yi game da cewa. “Sir akwai karin haske”. Yana tsaye a tsakiyar ɗakin yana rike da wayar da ya kara a kunne alamar waya yake yi, amma shi ma maganansa irin na IRON FIST ne, ba zaka taɓa cewa yana magana ba, can ƙasa cikin sanyin murya tamkar baya motsa lips. Tsayawa ta yi daga wajen tana satar kallonsa har ya kammala wayan, yana sanye da kaya irin nata sak, shi ma tactical trouser and t-shirt ya sanya, da yake ya fita haske sosai kuma launin kayan nasu duhu ne sai ya fi yi mashi kyau, shi shi ya yi wa kayan kyau, ita kuma kayan ne suka yi mata kyau. Ita dai har yau tana mamakin kitson dake kansa, kuma mugun kara mashi kyau yake yi, sai ma idan ya sakesu, wlh ba karamin kyau yake yi ba, amma yafi yawan tara jelar kitson ya ɗaure, idan kunga ya sakesu to yana cikin yanayi mai daɗi ne suma zai barsu su shana.Bayan ya kammala wayan ne ya nufo waje, hakan yasa ta bashi hanya da sauri, a wannan karon ita ta wuce gaba ya rufa mata baya. A gaban laptop ɗinta ta zauna tare da ɗauko Bluetooth ɗin nata ta mayar kunne, hannunta ɗaya naa kan mouse na laptop ɗin, ɗayan hannunta kuma yana gefen table ɗin.Ciki Leo ya shigo wanda yasa su V kara natsuwa sosai. A gaban laptop ɗin nata ya tsaya, ta bayanta kenan, ɗan sunkuyowa kanta kaɗan ta gefen shoulder ɗinta ya yi a ƙoƙarinsa na son hango motsin dake wajen. Ai jin yadda ya sunkuyo kanta har tana jin sauƙar numfashinsa a jikinta ne yasa gabaɗaya ta birkice ta rasa natsuwarta, har wani ɗan kerma yatsun kafafunta suke yi. Shi kuwa ko kaɗan bai kawo komai ba, sai ma hannu da ya miƙa ya ciro Bluetooth na kunnen nata ya sanya a nasa kunnen dan ya ji sautin dake fitowa. A lokacin da ya sanya hannu zai cire Bluetooth ɗin nan dogayen yatsunsa suka taɓata sai da ta ji wani irin shock, shi kam bai ji komai ba, to a bakin aiki yake, dik wani tinaninsa da lissafinsa game da hankalinsa ya tafi a kan laptop ɗin, bai mashi ma kamar macece take zaune a wajen ba. Jin sautin baya fita sosai da ya sanya Bluetooth ɗin ne yasa ya ɗaura hannunsa a kansa mouse ɗin da hannunta ke kai da nufin ya gyara sautin, bai ma lura da hannunta a wajen ba. Saura kaɗan ta saki fitsa a wando saboda razana na jin skin ɗinsa ya taɓata, da sauri ta zame hannunta tana jan wani irin dogon numfashi. Bai san tana yi ba, ƙoƙarin clearing na voice ɗin ya shiga yi yana sauke mata numfashinsa mai ɗumi a gefen wuyanta, gabaɗaya ya rikita baiwar ALLAH shi bai san tana yi ba…… Ya nemi clear na laptop ɗin sama da ƙasa bai gani ba, hakan yasa ya ɗan juyo da kallonsa a kanta kaɗan. “Ina clearing voice and rash ɗinki?”. In a cool way ya faɗa. Daidai lokacin ita ma ta juyo da kallonta a kansa saboda yadda cool voice ɗinsa ya ratsa kunnuwanta ya yi mugun tafiya da ita, sai ta ji tamkar yana romantic mood ko kuma shagwaɓa yake yi mata, alhalin ba haka bane, kunnuwanta ne kawai ke jiyo mata hakan. Zuba mashi idanu ta yi, ta manta ya tambayeta ta gagara yin magana….. “Are you okey?”. Ya faɗa yana zare kallonsa daga kanta, waɗan nan jade eyes ɗin nasa masu kalar sanyi sun kara rikitata, sai da ta haɗiyi wani irin yawu gwad kafin ta iya amsa mashi da. “Bari in fitar maka dasu”. Dama ta ɓoyesu ne a wani waje saboda V dake addaba mata da clearing na wakokin soyayya..Bai yi magana ba, ya dai jinjina kai. Da sauri ta kai hannunta saman nasa dake kan mouse na laptop ɗin da tinanin idan ta ɗaura hannunta ai zai cire nasa, sai ta ga akasin haka, domin kuwa hankalinsa ya tafi kan cikin kungurmin dajin da drone da V ta tura yake ɗauko masu video, ya mayar da kallonsa kan laptop na V, ko kaɗan bai ji hannun Arya a kan nasa ba.Ita kuwa jin ɗumin hannunsa yasa ta mance me zata yi, unexpected ta tsinci kanta da fara shafa skin ɗin nasa da golden hair kalar na kansa ke kwance a hannun nasa luff. Jin ana shafa mashi hannu ne yasa ya dawo da kallonsa a kan hannun nasa, da sauri ya juyo da kallonsa a kanta wanda ya yi daidai da ta juyo dan ta saci kallonsa ita ma.Ganin angry face ɗinsa mai rikitar wannan, ga waɗan man jade eyes ɗin nasa ne yasa ta ji a take natsuwarta ta dawo, har ɗan ɗauke wuta ta yi kafin ya sha jinin jikinta, da sauri ta ɗauke kallonta daga kansa tare da fara ƙoƙarin cire hannunta a kan mouse ɗin, sai ta ga ya rigata cirewa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta haɗiyi yawu mai wuyar wucewa gwab, sannan ta fara kokarin aikinta.Bayan ta fitar masa ta ɗauke hannunta ya mai da nasa ya shiga ciki, har yanzu dai jikinta na ɗan rawa, amma ta daure har ya gama abin da yake yi, ta yi mamakin ganin yadda ya kware a computer, har ta ji kamar ta yi bincike a kansa! Me ya haɗa shi da computer da zai iya sarrafata har haka?. Tana can tana tinaninta shi ya kammala abin da zai yi har ya fita waje, da sauri ta miƙe ta nufi kofa dan ta sami damar binsa da kallo, an kuwa yi haka, ta zuba mashi idanu har ya shiga cikin tantinsa.Su Angelina dai sai kallonta suke yi a sace, sun sha mamakinta. A fili ta ce STERIOUS, MYSTERIOUS, watau sterious mutumin da ba’a iya fahimta, mai ɓoyayyen hali kenan, ta gagara fahimtar a sahun mutane kirki zata sanya shi ne ko a na banza, shiyasa kawai ta bashi wannan suna STERIOUS. Su Angelina dai suna ta kallonta, ta ɗan jima a tsaya a wajen kafin ta juyo ta dawo ciki, ta zauna a gaban laptop ɗinta tana cigaba da bibiyar abin, ta sanya Bluetooth a kunnenta, nan ta ji Leo ya gyara sautin maganar na fita sosai, lallai ƴan ta’addan ne a wajen, ga shi suna magana cikin farinciki da shanawa.Tana ƙoƙarin yin magana kenan sai ji ta yi Leo dake tsaye a bakin kofa ya ce. “Ki haɗa ƙananan bluetooth ɗin dik ki miƙo mun”…….… Da sauri ta ɗago ta kallesa, ya shirya cikin kayan yaki, waist ɗinsa ɗaure da bullets cover, yana kokarin gyara bindigar hannunsa. Sai da ta ji faɗuwar gaba, take ta ji tsoron su je su mutu a can ya kamata, ita da take cewa zata dinga basu wrong information idan sun tafi yaki sai ga ta cikin tsoron kada su je basu dawo ba, watau ita imani da tausayi a zuciya take ba’a kan fuska ba, ɗaure fuska ba shi ke gwada rashin imanin mutum ba. Jikinta dik ya mutu ta haɗa bluetooths ɗin ta yi connecting ɗinsu da sautin nata, ta yadda suna kutsawa cikin daji ita kuma tana magana, ma’ana tana directing ɗinsu a kan hanya while tana ganin rahoton da drone ɗinta ke ɗauko mata.Bluetooth uku ta ɗauka ta nufo shi, a natse ta miƙa mashi tare da cewa. “This is it”. ……. Ba tare da ya ɗago ya kalleta ba ya karɓa ya juya, da gudu su Angelina suka fito dan ganinsu, sun sha mamakin ganin dikka mazan sun yi shirin yaki, suna rike da bindigu, babu alamar wasa a tattare da su, dik sun tsaya a layi sun yi shirin mutuwa ko rayuwa.Miƙewa Noor and Zaynish bluetooth ɗin hannunsa ɗaiɗai Leo ya yi, shi kuma ya sanya ɗaya a kunnensa, cikin sirri yai mashi bayanin yadda zasu tafi, daga nan ya ce su shirya. V na tsaye tana kallon Noor da yake ƙoƙarin sanya bluetooth a kunne, ba zaka taɓa cewa shi bane, fuskan nan babu alamar wasa, lallai ya cika alkawarinsa da ya ɗauka na cewa ba zai bari soyayya ta ɗauke mashi hankali daga kan aiki ba, ko sallama bai zo sun yi ba, aikin dake gabansa kawai yasa kai. Bayan ya kammala shirinsa tsab sai ya ɗago ya kalleta. Hannu ya ɗaga yai mata alamar heart da shi, slowly ya motsa lips ɗinsa wajen cewa. “I love you”. Ko kaɗan babu fara’a a kan fuskansa, yanzu ya tashi daga Romeo ya rikiɗa zuwa AZURE SOLDIER kuma member of DOL!. Kallon shi cike da fargaba kawai take yi, ta gagara iya mayar mashi da martanin love ɗin da ya furta mata, ganin haka yasa ya ɗauke kansa daga kallonta, dan kada ma ta raunata mashi zuciya.Sojoji 20 suka tafi, suka bar 4 a tare da su Arya dan su basu tsaro, su V suna kallonsu har suka wuce cikin shirin yaki. Bayan sun ɓacewa ganinsu ne suka juya da nufin su koma cikin tantinansu sai Arya ta ji alamar kuka kamar kuma motsi ta can nesa da tantinsu. Cike da jarumta ta nufi wajen, tin daga nesa tana jiyo kukan tana bibiya har ta isa wajen, yana da nisa daga in da suke, sannan wajen bakin ruwan dake kusa da su ɗin nan ne amma ta can. Tin daga nesa ta hango mutum a bakin ruwan zaune dirshan a ƙasa tana kuka. Da sauri ta karisa wajen, yarinya ce karama da bata wuci 10 years ba, kyakkyawar gaske, irin masu kiwon shanun nan ne. Arya ta ɗan ji tsoronta kaɗan, saboda bata zaci mutum bace, gata a tsakiyar dokar daji, gata kyakkyawa, sannan tana zaune kusa da ruwa tana kuka, sai ta zaci ƴar ruwa ce kawai.Kamar zata juya, sai ta tina ba’a san sojoji da tsoro da sarewa ba, hakan yasa ta ji kwarin gwiwa, da sauri ta nufi yarinyar. A gabanta ta tsugunna tare da dafa shoulders ɗinta, a sanyayye ta ce. “Why are crying? Where’s your mom?”. Ɗago kai yarinyar ta yi ta kalleta, sai da gaban Arya ya faɗi ganin a fusge yarinyar taso yi mata kama da Leo, amma kama ta jini haka ba ta fuska ba. Ni kam na ce Arya ko dai ko dai? Ko dik damuwa da shi ne yasa kike ganin masu kama da shi?.Da hannu yarinyar tai mata nuni da wani jarka na ruwanta da take ɗeba, ta zo ɗeba ne ya kwace ya faɗa cikin ruwan, ita kuma tana tsoron shiga, shi ne ta zauna ta hau kuka. Kallon jarkan ruwan nasu Arya ta yi, ta fahimci yarinyar bata jin turanci, a ranta ta ce to wace yare yarinyar take ji?.Ganin bata da lokacin ɓatawa wajen buƙatar gane yaren yarinyar ne tin da ga su Leo sun tafi kuma dole zasu buƙaci information daga wajenta, sai ta yi saurin miƙewa, cikin zafin nama ta faɗa cikin ruwan, iyo ta yi har izuwa in da jarkan yake, ta fito da shi tare da zuwa ta miƙawa yarinyar, sai da ta miƙar da ita, dik da yakansance yarinyar jikinta dik datti Arya bata kyamaceta ba, ta sanya hannu ta kakkaɓe mata jiki sannan ta ce to ta tafi. Alama yarinyar tai mata da cewa zata ɗebi ruwa kafin ta tafi, karɓar jarkar Arya ta yi, ta cika mata da ruwa sannan ta ɗaura mata a kai, ta ce ta tafi. Wucewa ta yi tana waigo Arya, ita ma tsayuwa ta yi tana kallonta har ta kurewa ganinta, mamaki Arya take yi ta yadda aka yi mutane ke rayuwa a wannan dajin! Ganin yarinyar ta tafi yasa ita ma ta wuce da sauri ta koma wajen tantinsu.Canza kayan jikinta ta yi, sai tambayarta ina ta je ta jike su V suke yi, amma bata kula kowa ba, ta canza kaya ta zo ta hau kan aikinta, watau Arya tana da kyakkyawar zuciya, kawai halinta ne a haka na rashin son shiga mutane da ware kai, rashin son hayaniya da ɗauke kai a abu ga tsiwa da riko, amma batu na kirki a zuciya yake, kuma zuciyarta tas yake a kan hakan.Ita kuwa V sai ƙoƙarin kiran Noor take yi, ta manta basa zuwa farmaki da waya, dik wayoyinsu na tantunansu, daga su sai bullets and gun suka tafi. Angelina na ta faman kallon hotunan da tai wa su Unays ɗazun, while Manassa ta yi shiru tana tinanin guy ɗin da suka haɗu da shi ɗazun da ta je yin brush.Tana tafiya tana waige-waige kawai ta ci karo da shi, baya ya ja tare da kura mata idanu kafin ya ce mata ita ɗin kyakkyawa ce. Shiru bata mashi magana ba, ta matsa gefe ta cigaba da goge bakinta, unexpected daga bayanta ta ji ya zuro hannu ya karɓi brush ɗin, goge mata bakin ya dinga yi har sai da hakwaranta suka fita. Juyawa ta yi ta ɗan turesa ganin ba zai daina goge mata bakin ba.Ta ɗaure fuska tamau kafin ta ce. “Waye ya baka izinin ka taɓani ko wani abin nawa?”. …….. Yana kallon kyakkyawan face ɗinta ya amsa da. “No body, haɗuwarki ce kawai sila, kuma ai gaba nike dake a wajen aiki, kinga ba sai kin bani izinin yin abu ba, ni ne ma zan baki izini!!”…… Harara ta dallah mashi kafin ta ce. “Kasan wacece ni kuwa da kake maganar gaba kake dani a aiki?!”. “Soja ce ke kamar ni, ke jami’ar computer ni kuma jami’in bindiga, that’s all”……… “Haka kake tinani?!”….. Ta faɗa a fusace. Kai ya gyaɗa mata alamar kwarai haka yake tinani. Screen light na wayarta ta kunna tare da juya mashi. Ai yana kallon hoton kan wallpaper ɗinta bai san lokacin da ya saki brush na hannunsa ba.Ɗan ja baya daga kusa da ita ya yi, with do respect ya ce. “Sorry madam”. Ya ganta tare da daddynsu ne da su Arya, shi ne ya kiɗime haka, ya ga GAT. Harara ta dallah mashi tare da miƙa mashi hannu kan ya bata brush ɗinta, da sauri ya duƙa ya ɗauko ya miƙa mata, karɓa ta yi ta wuce ta nufi hanyar shiga room ɗinsu. Sai dab zata shiga ɗakin ne ta juyo ta saci kallonsa, ya yi mugun tafiya da imaninta, amma tin da yana tsoron daddynta sai ta yi ya ja mashi rai da barazana kafin ta sake da shi. A TINANINKU DA WAYE TA HAƊU?. To su Leo sai dai mu ce ALLAH ya tsare ya maido mana da ku gida lafiya, ya baku iko a kan waɗan nan ƴan ta’addan, su Arya ALLAH ya dafa maku ku naɗi information na komai da taka tsantsan ba tare da ƴan ta’addan sun gano drone na camerarku ba, ku naɗi komai ku bawa su Leo namu a kan lokaci kuma daidai ta yadda zasu yi aiki cikin hikima da kwarewa!. Kun ji halin da ƴan team DOL suke ko? To mu leƙa asibiti kafin mu wuce CP. ————————–🔥WS-HOSPITAL.💔🥲Zaune Maya ta isko Dr Kamal yana aiki a desktop computer dake gabansa, idanunsa sanye da eyes care, ga dikkan alamu ba aikin wasa yake yi ba, ya dukufa haikam. Excuse tai mashi har sai da ta jira ya bata izinin shigowa bayan ta wuce PA ɗinsa kenan. A saman visitor chair ta zauna, cikin girmamawa ta ce. “Good morning sir”……. Bai amsa ba, hasali bai ma ɗago ba, yana cigaba kawai da aikinsa. Shiru ta zuba ido tana kallon irin haɗuwar office ɗin nan, komai na cikin office ɗin luxury one ne, ga wani haɗaɗɗen kamshi dake tashi. Zaman good 30 mins ta yi kafin ya ɗauke idanunsa daga kan computer ya mai da shi gabaɗaya a kanta, slowly ya zame hannnunsa daga kan keyboard na computer kafin ya cire eyes protection dake idanunsa. Sai da ya cire ta fahimci ita yake kallo, ƙara natsuwa ta yi game da yin ƙasa da kai, tana jin kirjinta na dukan uku-uku. “Maya”. Ya ambaci sunanta can ƙasa. Da sauri ta ɗago kai. “Good evening sir”. Dan sai a yanzu ta tina ashe yamma ce ma ba safiya ba. Bai amsa gaisuwar ba sai ya fito da wasu tulin takardu ya tura mata gabanta, sannan ya ɗauki pen ya miƙo mata. “Sign here”. Ya faɗa in a low waye sosai.Da yake suna shakkarsu da tsoronsu, bata tsaya tambayar document na menene bane kawai ta karɓi pen ɗin ta hau signing, paper dake ciki dikka ya dinga buɗe mata tana signing. Sai da ta kammala sannan ya ɗauko wani document ya miƙa mata. “Wannan shi ne project da kika yi signing na kin karɓa a yanzu, 24 hours gareki ki karanta document ɗin nan jibi da safe za’a fara project ɗin, so a yanzu kin dawo karkashin office ɗin nan da aiki, kina iya tafiya”. Cikin girmamawa ta amsa tare da karɓar document ɗin sannan ta miƙe ta fito cike da farincikin ta baro side na chemical ta koma side na manyam 3D da kowa ke tsoro……… Da kallon ƙasan ido ya bita har ta fita, wayansa ya ɗauka, rubutu yai short kafin ya ajiye wayar, ya miƙe ya buɗe door dake cikin office ɗin, a tinanina toilet ne a wajen, sai da ya shiga naga wajen ya sha banban. Dan kuwa yadda kuka san bar na shaye-shaye haka wajen yake, ga wani dim light purple kala, wasu manya-manyan glass ne shake da abubuwan sha kala-kala wanda na tabbatar kuɗinsu ba zai faɗu ba, dan tsadaddun kayan drinks ne a wajen. Daga gefen glass ɗin can ɗan nesa wasu sofa set ne a wajen, ga kuma irin torch creen computer ɗin nan tangameme a wajen sofa set ɗin, da alama wajen shirya project ɗinsu ne. Ɗakin sai kamshi yake yi.Wajen sofa ɗin ya karisa, a saman ɗaya daga ciki ya zauna, yana zama sai ga Dr Mark ya shigo, kai tsaye wajen glass na drinks ɗinsu ya nufa, wani tangamemen bottle ya ɗauko da glass cup, a wajen sofar ya dawo. Abin mamaki drinks ɗin da sanyi sosai, da alama glass freezer ne a wajen. Ɓalle bakin bottle ɗin ya yi, ya zuba drink ɗin a cup, sipping ya ɗan yi tare da cewa. “In zuba maka ne?”. Kai Dr Kamal ya girgiza tare da cewa no. Zama ya yi ya cigaba da sipping a hankali cikin natsuwa, babu wanda ya sake ce da wani uppan. To mu bi sister Zinta kuma. A lokacin da suka shiga office na Dr James da sister Lazy jikinta sai kerma yake yi, umarni Lazy ta bata da ta tsaya a tsaye, ita kuma ta zauna a kan visitor chair. Tana zama Dr James ya ce. “Get out!”. Wani irin kululun bakinciki me ya turmuke zuciyanta, jikinta har kerma yake na takaici, ga shi ba yadda ta iya da shi, haka ta miƙe tsaye cike da kunyar ya walaƙantata a gaban Zinta. Tana miƙewa ya ce. “Zinta have a seat”. Ya faɗa still bai ɗago ya kallesu ba. Wucewa Zinta ta yi, ta zauna a saman kujerar da Lazy ta tashi, ita kuwa Lazy da wani mahaukacin sauri ta nufi waje, dan gab take da haɗiyar zuciya ta mutu.Kamar yadda Dr Kamal ya baiwa Maya files and documents haka Dr James ya baiwa Zinta ta sanya hannu, sannan ya ce tana iya tafiya. Daɗi tamkar ta mutu saboda ya ce a tare zasu yi wannan project ɗin, sai sun kammala project ɗin zata koma aiki a section C ɗinsu, ko a iya haka ta yi nasara, zata samu damar zama kusa da shi, ga shi idan suka shiga project suna iya ɗaukar watanni 6 zuwa 8 kafin su kammala, gwargwadon yanayin project ɗin dai. To kun ji yadda sister Zinta ma ta kare da Dr James, to mu koma kan su Dr Kamal.Suna zaune shiru babu wanda ya yi magana Daidai lokacin Dr James ya shigo ta kofar office ɗinsa, dikkansu daga office ɗinsu suna iya shigowa cikin wajen. So ya shigo hannunsa rike da tarin takardun. Saman sofa kusa da su ya zauna tare da ajiye files ɗin a kusa da shi. Natsuwa suka yi dik suka bashi hankalinsu. Wani document ya ɗauko tare buɗe files ɗin, glass na face ɗinsa ya gyara kafin ya ce. “Information daga ƙasar AVARIS. A dikkan government hospital na 30 states da kasar Avaris take da shi mun gama rarraba files ɗin nan, a cikin ƙasa da 24 hours mun samu mahaifar mata sosai daga asibitoci sama da 20”. Dr Mark ne ya amsa da cewa. “Fin haka ma zamu samu, saboda kowa yana cikin yunwa da buƙatar kuɗi, kowa burinsa ya yi kuɗi, kunga a irin wannan yanayi ko da maginyata basu sayar dan ra’ayin kansu ba likitocin zasu cire masu ba tare da yardansu ko saninsu ba, dan 80 million ba karamin kuɗi ba!”. A natse ya yi maganar, ya faɗa yana sipping drink ɗinsa. Dr Kamal ne ya ce. “Yunwa ya cinye kowa a ƙasar na AVARIS ba dole su sayar ba, gwamnatin AVARIS bata son biyan ma’aikatan lafiyar government hospital ɗinta albashinsu yadda yakamata, basa son sauke hakkinsu, kasar ga yunwa da wahala dole wasu likutocin su yarda sayar ko majinyata basu sani ba”. Cikin kwarewa suke magana, one after the other, yadda zaku san ilimi ya ratsa ƙwaƙwalwalensu matuƙa.Bari in maku karin haske dan zaku fi gane maganganunsu, sayan mahaifan mata suke yi da kimanin kuɗi 80 million a kuɗin Nigeria, to ni kuɗin Nigeria na sani shiyasa da su nine kwatance, kuma shi masu karatu zasu fi ganewa…….😌To sun shigar da buƙatarsu ta hanyar turawa manyan asibitocin gwammanati na kasar Avaris takarda, wani Minister suka baiwa wannan kwangila da makuɗan miliyoyin daloli, shi kuma ya shiga asibiticin gwamnati ya yi zama da manyan gurɓatattun likitoci ya faɗa masu buƙatarsa, su kuwa take suka yi na’am sun ji miliyoyi.Dr James da kansa ya kirkiro wani magani da ya sanyawa project ɗin suna da silent killer, wanna magani ya bawa wannan minister dan a rabawa gurɓatattun manyan likitocin asibitocin, zasu baiwa mata a matsayin wani magani na karin lafiya, ko idan mace ta zo ta ce tana ciwon ciki yayin period sai su bata shi a matsayin maganin warkar da ciwon cikin, idan kin sha zaki yi ta fama da ciwon cikin ne, amma fa a farko in kin sha zaki ji saukin ciwon cikin, daga baya bayan kwanaki sabon ciwon ciki zai ɓallo maki mai zafi, da kin zo asibiti zasu ce maki mahaifarki ta samu matsala sai dai a yanke! Ba zaki kawo komai a ranki ba, zaki aminta a cire maki mahaifarki saboda a rabaki da ciwo. Ministern da aka baiwa wannan kwamgila a kan Miliyan tamanin aka sayi kowani mahaifa a wajensa, shi kuma ya cewa likitoci in sun samu mai sayar da mahaifar ya saya miliyan hamsin, su kuma Dr ɗin suna saye miliyan 30 idan kin yarda zaki sayar, kasuwanci kan kasuwanci kuke ji.To wasu matan fa mazansu ake magana da su, wani da ya kawo matarsa asibiti za’a jasa jefe, a shirya a kuma kwaɗaita mashi kuɗin, idan likitocin sun ga ɗan kauyene ma basa ce mashi saya zasu yi, sai su ce ciwo ne, ya aminta a cire maki, wani mijin kuma azzalumi ne, bai gama sauke maki hakkinki na aure ba, zai cutar dake ya sayar maki da mahaifa ba tare da kin sani ba, idan ya shirya da likitocin kan zai sayar masu zai karɓo wannan maganin ya baki, da kinsa zaki fara ciwon ciki, idan zai kaiki asibiti wannan asibitin da suka gama cinikin zai kai, already ya karɓi kuɗin mahaifarki 30 million baki sani ba, sun san komai Doctors ɗin, kina zuwa zaace aiki za’ayi maki, daga nan a cire maki mahaifa ba tare da kin sani ba, sai dai ki ga kin daina haihuwa, kuma ba zai taɓa barinki ki je wani asibitin ba, sai dai ya dinga cewa ki je wannan asibitin da aka maki aiki sun fi kwararrun likitoci, dan bakinsu ɗaya. Ya ilahi, sun fi yi wa matan kauye da basu san komai ba hakan, kun san dai manya matan masu kuɗi basa zuwa asibitocin gwannati ai, a kan mu talakawa abin yake karewa, babu abin da ya fi taɓa mun zuciya irin mazan dake zaluntar matansu su sayar masu da mahaifa ba da izininsu ba, ya ilahi, wlh da babu lahira akwai matsala, amma Alhamdulillahi tin da akwai hisabi, amma bin da ciwo.Meyasa yanzu abu kaɗan mahaifar mace ya samu matsala? Why? Meyasa zata haihu ace ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai a mata Cs? Why? Meyasa ciwon da bai zo a da ba sai yanzu za’a ce mahaifarta ta lalace ba zata sake haihuwa ba gara a cire mata? Meyasa dikka hakan sai a kanmu mata? Me laifinmu? Wani irin cutarwa ne wannan?.Idan an samu miji mara imani ya sayar dana matarsa bata sani ba, wani ma yaya ne mara imani yake sayarwa kanwarsa, matan kauye basu san komai ba haka za’a cutar da su daga zuwa asibiti, ace basu da lafiya sai an masu aiki, daga nan a sace masu mahaifa, AVARIS suna cikin musifa babba, ƴan mata ma ba tsira suka yi ba, wani saurayin mataccen zuciya ne da shi, ya yaudareki ya kaiki a cire maki mahaifa, ya sayar ya yi kuɗi ya gudu ya barki ya nemi wata budurwar wacce take da mahaifar da zata haifa mashi yara in sun yi aure! Ya ilahil alamina, sabuwar musifar dake danno kai a AVARIS kenan.Jama’a ku ji tsoron ALLAH, maza ku tina akwai lahira, akwai mutuwa, meyasa zaku sayar masu da abin da ALLAH ne ya basu ba ku ba? Meyasa zaku cutar da rayuwarsu ta haka? Mata masu sayarwa da kansu ku ji tsoron ALLAH, ku tuna cewa ALLAHN da ya baku a ranar lahira sai ya tambayeku komai da ya baku, wani amsa zaki bawa UBANGIJINKI ranar lahira? Dama ya baki dan ki sayar ne? Kin san me za’ayi da mahaifar ne da kike sayarwa? Kuɗin banza mai karewa, baki san kuɗin haram bashi da albarka ba ko? Maza! Maza! Maza!!.Ni ban ce komai ba, amma shawara da kirana ga mata, dan girman ALLAH dik asibitin da zaki je, kome aka ce za’ayi maki ki ɗauki waya ki kira ɗan uwanki namiji, ya zo ya tsaya maki, duniya ba abin yarda bane, idan kina da wa ko kani ya tsaya a kanki dik abin da za’ayi a yi a gabansa, ba ruwanki da cewa mijinki da ƴan uwansa suna nan, ke baki da ƴan uwa ne? Idan ta kama an ce lallai sai an cire maki mahaifar ne to idan an cire ki ce su baki kayanki ki tafi da shi, kada ki yarda ki barshi a asibiti, ko sun ce maki jefar da shi zasu yi dan ciwo ne ki ce e su baki kayanki, wlh gara ki je ki tona rami a gidanki ki binnesa kina ganin ramin kullum akan ki bar masu, baki san me suke yi da shi ba, dik abin da aka yi da shi ba zai canza daga sunan mahaifarki bane! Ban faɗa haka dan rashin yarda ya shiga tsakaninku da mazajenku ba! Ku yi hankali ne kawai, kada ki yarda da zuwa asibiti guda ɗaya ana duba lafiyarki, idan an yi maki aiki ne bayan kin samu lafiya jeki wani asibitin daman a maki scanning ki tabbatar da lafiyarki, duniyar yau ta zarce dik yadda kuke tinanin, abin ya fi karfinmu ya fi karfin shuwagabannin AVARIS! Dan abin daga sama yake, ALLAH ne kawai zai iya dafa mana ya kawo mana karshen wannan musifa, amma hakan ba zai faru ba sai mun tashi tsaye, mu kare kanku sai mu nemi UBANGIJINMU da ya taimaka mana. Gabaɗaya WS-HOSPITAL ina typing ɗin labarin ɓangaren ina kuka, wlh har cewa mahaifiyata na yi zan jingine labarin nan saboda tausayin dake cikinsa ya yi yawa, mamana ta ce idan na rubuta zata yi farinciki da hakan, kuma ta umarceni da kada na rage ko A daga cikun ilimi da sanin da ALLAH ya bani, ta ce in daure taimakon alumma zan yi, alƙalami ya fi takobi! ALLAH yana tare dani, ta kara mun kwarin gwiwa sosai, kullum idan ina typing part ɗin sai na ce mata ina jin kamar ba zan iya ba zan jingine labarin, ta ce ta sanni zan iya in dage! The thing is very touching heart, emotional, har tsoron shiga cikin labarin in zayyana komai nike ji! I need your prayers.Mutanen AVARIS suna buƙatar addu’arku, yadda aka horasu da yunwa da wahalar nan kuna tunanin ba zasu karɓi wannan aiki gadan-gadan bane tin da kowa yana son lallai sai ya yi kuɗi? Matan AVARIS yanzu kuma sun shiga uku, mahaifarsu ya zama kuɗi, shikena a kuma, yanzu kowa asibiti ka leƙa za’a ce aiki ake mata, ALLAH ka shige mana gaba ka karemu daga dikkan wata musifa.Wannan shi ne hanyar da su Dr James suke bi dan samun mahaifar mata, tin da kuma kuka ga sun tsuga mashi kuɗin har kimani miliyan tamanin a wajen sayensa fa to ku sani bakaramin abu suke yi da shi ba, ba karamin kuɗi suke samu ba, amma koma menene idan muka shiga cikin labarin zaku sani. Yanzu sai kewaye duniya suke suna raba wannan buƙata tasu ta a kawo masu mahaifa zasu saya, nasan maza masu matattun zuciya tuni zasu karɓa, matanma wasu da basu san ciwon kansu ba da kansu zasu karɓi kuɗin, ni damuwata shi ne idan aka basu mahaifar abin da zasu yi da shi, kun dai san ba zasu zuba makudan kuɗi a ƙan karamin abu ba ko? Babba abu ne!. —————————Dr Kamal ne ya ce. “Yunwa ya cinye kowa ba dole su sayar ba, gwamnatin Avaris bata son biyan ma’aikatan lafiyar government hospital ɗinta albashinsu, basa son sauke hakkinsu, kasar ga yunwa da wahala dole su sayar a”. Sipping na drink ɗinsa Dr Mark ya yi tare da cewa. “Basu da zaɓi ne, dole su sayar”……. Dr James dai rufe files ɗin ya yi tare da ɗauko wani file ɗin….. “Muna da contract har uku fa a shekarar nan, dole mu mayar da hankali, sannan batun project na PC ɗin nan, daga sama an hura mun wuta sosai, yakamata mu mayar da hankali, a nan da wattanni shidda zuwa takwas mu kammala project ɗin nan mu ci kuɗinsa”………………. Miƙewa Dr Kamal ya yi tare da cewa. “We have to go to section D dan duba wancan project ɗin, yanzu ɗayar project ɗin nan zamu kammala, na bawa Maya document na aikin, 24h garesu, dan haka mu bar wannan zancen sai jibi idan mun samu feedback daga garesu”. Na’am suka yi da zancensa, ajiye cup na drink ɗinsa Dr Mark ya yi, kusan a tare suka miƙe suka fito ta kofar office na Dr James, daga nan suka fito izuwa section D. Suna tafiya a natse amma cikin zafin nama. Dik in da suka wuce sai nurses sun duƙa sun gaidasu. Kai tsaye cikin section D suka shiga, rabuwa suka yi, suka fara kewaye a wajen suna duba dashen da suka yi! Suna bi suna ɗaukar rahoto da kansu, komai na tafiya daidai, halittar da suka dasa cikin mahaifar har sun fara motsawa tamkar yaro na motsi a cikin uwa, karku manta sai da ya zama embyro suka dasa shi a cikin mahaifar.Bari in ɗan yi maku karin haske a wannan waje kafin mu wuce gaba dan kada ruɗewar tai maku yawa, naga dayawa sun fara ruɗewa tin ba’a je komai ba, to zan buɗe maku haske kaɗan. Nasan kun fahimci cewa waɗan nan kwayaye da suka dasa a cikin mahaifa a page ɗin jiya kun fahimta yara aka dasa, to yara suke kyankyasa da waɗan nan mahaifa, suna haɗa sperm na ɗah namiji da kwayayen mace su kyankyashe yara. Sai dai kuma idan suka kyankyashe waɗan nan jarirai basa wuce watanni uku a wannan asibiti, wasu jariran a ranar da aka fito dasu daga cikin mahaifar a ranar ba’a sake ganinsu, wasu suna kai wata ɗaya a wajen, wasu suna kai wata biyu har su fara wayau suna shan madara maimaikon nonon uwa, amma basa taɓa haura wata uku iya wuya, kuma abin mamaki kullum suna cikin kyankyasan yaran ne, dik wata suna cire kwan halittar mace ai kun gani, to me suke yi da uban yawan jariran da suke kyankyasar nan? Ina ake kaisu?.Baku yi mamakin yadda na ce maku nurses na asibitin dik shekarunsu ɗaya ba, watau 18 years ba? To ai dik ta wannan hanya aka kyankyashesu, suka renesu, suka basu ilimin likitanci, sannan waɗan nan ƴan mata da ake cire kwan haihuwarsu dik wata ku sani suma a nan aka kyankyashesu musamman aka killacesu dan a rinƙa cire kwayayyensu.Na ji wasu readers suna cewa basu da hankali suka yarda ana cire masu kyan haihuwa, to jama’a a lafa haka nan, suma ƴaƴan kwalbar haihuwa ce da aka kyankyasa ba ƴaƴan mama da baba ba, basu da kowa sai ALLAH, suna dai da azzaluman ubanunsu da suke bada sperm ɗinsu a kyankyashesu, dik namijin da zai bada sperm ɗinsa a wanna harka shi ne babban azzalumi kwai ba zai bada yaro ba sai an haɗa da sperm, to masu bada sperm nasu sun fi kowa laifi, su suna can suna jin daɗi cewa maniyinsa ma saya ake yi a basu kuɗaɗe, a yaudaresa da cewa ai man shafawa ake yi da maniyin, su yarda su yi ta sayarwa, basu san bataliyar ƴaƴa ake kyankyasa masu ba.Sannan dole zaku ga nurses ɗin suna ɗan kamanceceniya, kada ku manta a jikin matan nan dai na page ɗin jiya ake ciro kwayayyen halittarsu, gara maniyin na maza daban-daban ne, amma kunga ana iya ciro kwai goma a jikin mace ɗaya, kunga yara goma kenan! Dole wasu su yi kamanceceniya. Karin wani haske a wannan asibitin, basa kyankyasan mata sai maza, basu cika amfani da sperm mara karfi sosai ba sai idan an basu contracts kan kyankyasar yara mata, amma dik maza suke kyankyasa, waɗan nan nurses ɗin kawai suka kyankyasawa kansu mata, dan ba zasu yarda su kyankyashi maza su renesu ba, dan maza zasu iya basu matsala, mace halitta ce mai rauni, dik a turban da suka ɗaurata zata bi ne, musamman idan bata san komai ba.Amma dani daku dik mun san idan suka kyankyashi maza suka renesu, suka masu ilimin likitanci to fa idan idanunsu ya buɗe suna iya cin ubansu ne, shiyasa suka ki yarda su ɗauki maza, so a takaice basa kyankyansan yara mata sai maza, kansu kawai suka kyankyawa matar nan dake masu aiki, fatan yanzu kun gane?.Yauwa karin wani haske, daga waje wani likita baya zuwa aiki a wannan hospital ɗin, wannan amsar tambayar readers ne, in kara maku haske, babu wani mutum daga waje dake shigowa wannan hospital ɗin, ko sperm suka saya a waje ake ciniki, a ƙasa daban ma ake ciniki, in sun saya su waɗan na. 3D ɗin ne zasu fita su ɗauko sperm ɗin su kawo, dan haka wani daga waje baya shigowa, iya waɗan nan 3D ɗin ne kawai ke aiki a asibitin babu wani likita, fatan kun gane?. Mu je zuwa.Sun jima suna kewaye a wajen, sai da suka tabbatar jariransu suna nan lafiya, suna samun rayuwa daidai da cikin uwarsu, sannan suka fito, kai tsaye office ɗinsu suka koma, dan shiryawa wannan babban project da manyan duniya suka basu aiki a kai mai suna P-C. WANI PROJECT NE WANNAN? SHI NE AINAHIN LABARIN JAMA’A.A gefe guda kuwa sister Lazy tana can tana kuka kan abin da Dr James yai mata, ya koreta a gaban sister Zinta, wannan abu ya tsaya mata a rai matuƙa. To mu leƙa CRYSTAL PALACE mu dawo, na fi son a kowani page ku dinga jin halin da kowani ɓangare yake ciki ko ba yawa ne!. ————————–🔥 CRYSTAL PALACE.Can tsakiyar dare Aryan da ya gagara barci ne ya fito ya nufi room da yake zaton guru na ciki. Ya kuwa same shi zaune daman dadduma yana sallah. A gefen bed ya zauna yana jiransa yana har ya idar, miƙewa ya yi bayan ya kammala addu’a ya nufi Aryan ɗin. A kusa da shi ya zauna tare da cewa. “Brother lafiya?”….. Kai Aryan ya girgiza alamar a’a ba lafiya, amma bai yi magana ba, guru yasan me matsalar, basa iya kwana cikin fushin juna, idan sun yi faɗa kasa barci dikkansu suke yi, su yi ta faman kumbure-kumbure amma ba zasu iya bawa juna hakuri ba. Shiru room ɗin ya yi, can Aryan ya ce. “Brother Lion bai ji ciwo ba ko?”…… Wani irin kallo guru ya wurga mashi kafin ya ce. “Yana second room jeka duba”. Siririn tsaki ya ja tare da gyarawa ta kwanta a gadon na guru. Shiru guru ya ɗan yi yana tunanin yanzu Lion ya bar ɗakinsa fa, shi ma tin da ya farfarɗo daga alluran ya gagara yin barci, shi ne ya zo wajen guru, ya fake da cewa Aryan bai ji ciwo ba ko? Guru da iskanci sai ya ce mashi ya je ya duba, shi ne yaki zuwa ya koma room ɗinsa, yanzu haka yana tsaye a tsakiyar ɗakin, yana son zuwa duba Aryan ya ga yana lafiya bai ji ciwo baz amma girman kansu da nuna isa ya hanasa, ga abin a ransa ta hanasa sakat.Shiru Aryan ya kwanta, zuciyansa ya gagara daurewa, sai ya miƙe game da cewa. “Mu je in duba ko ya ji ciwo”…………. Hararansa guru ya yi game da cewa. “Ku dai kuka sani”. Ya faɗa tare da bin bayansa suka fito waje. Ɗakin da Lion yake suka shiga, yana jin sun turo kofa ya juyo da sauri, ai yana ganin Aryan wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin kuma ya ɗaure fuska. “What brought you here?”. Ya faɗa har da nuna irin bai damu da su ɗin nan ba….. Banza da shi Aryan ya yi tare da wucewa ya kwanta a gado yana satar kallonsa, shi kuma guru ya shigo ya hau tausan Lion ɗin. Da yake abin da yake so kenan su yi sulhu sai ya yi saurin hakura, da haka suka wuce saman gado in da Aryan yake, babu wanda ya ce da ɗan uwan uppan, suka kwanta shiru, ba jimawa barci ya kwashesu.Washegari suna sun mance da sun yi faɗa, suka koma kamar da, a tare suka yi sallar asuba kamar yadda suka saba, suka dawo, wanka kowannensu ya yi suka sanya hoodie iri ɗaya fari tas, sannan suka faɗa ɗakin aikinsu dan tsawaita bincike kan AVARIS.A gaban computers ɗinsu suka zauna, Lion ne ya ɗauki cube yana jujjuyawa yana ƙoƙarin haɗawa. Su Aryan dake kokarin duba aikinsu ne suka samu sakon binciken Lion da ya tura masu.Buɗe saƙon suka yi, a natse suka fara karantawa, batu ne kan dalilin da yasa ake ta faman tashe-tashen hankula a arewacin AVARIS, dik jerin tattalin arzikin da arawacin ta mallaka ya rubuto masu ajere, albarkatun ƙasa sama da 28 arewacin AVARIS ta mallaka, ciki har da uranium da ake haɗa su nuclear, arzikin gold, fetur, coal tantalite, tin, granite, asbestos graphite nickel, dik arewacin kasar tana da shi, ma’adanai masu balain tsada, batu ake na makaman nuclear fa, arzikin da manyan ƙasashe basu da shi, shiyasa abin yaiwa Avaris yawa wai shege da hauka.Bayan sun karanta sun gama ne guru ya ce. “To tin da ma’adinan sun yi wa kasar yawa, shuwagabanninta basu iya amfanar da ƙasar da ita ba why not ba zamu shiga siyasar kasar ba? Ma’ana mu tsayar da waɗan da za su iya kwato ƙasar daga hannun ƴan sarin da ta faɗa?”. Cigaba da jujjuya cube ɗin Lion ya yi tare da cewa. “That’s impossible!”. Ya faɗa idanunsa a kan Aryan da gabaɗaya ya mayar da hankalinsa a kan waya, his attention isn’t there. Yana can yana kallon Seraphina dake ta faman neman hotonsa da ta ɗauka jiya dan ta turawa Rimsha, a tinaninta she’s smart, bata san da IRON FIST take tare ba, yama za’ayi ta ɗauki hotonsa ba zai sani bane? Ko da yake bata san gabaɗayanta ma a tafin hannunsa take ba, wai ita ma ta yi wayau. “Rimsha i didn’t see this pic, but why not ki turo mun pic na uncle ɗin naki, idan shi ne zan gane ai”. Ta yi typing ta tura mata. Shi dai Aryan ganin gudun ruwansu kawai yake yi, yana son jin karshen wasan……… “Seraphina you are out of your sense! Uncle Aryan ɗin ne zan samu pic ɗinsa? Don’t you that ni makiyarsa ce? Idan yana waje ma bana fitowa”. Ta turo mata amsa. Miƙewa Seraphina ta yi, zarya ta fara yi a cikin ɗakin tana tinanin yadda aka yi hoton daddyn nata ya goge a wayar, ta san dai ta ɗaukesa Unexpected Aryan ya ji an kwace wayansa, a zabure ya ɗago kai, four eyes suka yi da Lion dake tsaye a kansa. Wani irin harara Aryan ya dallah mashi kafin ya ce. “Give me phone malam, ka wani tsaya mun a kai kamar sojan gona”. Cike da fargaban kada Lion ya duba wayar ya yi maganar. Juya gaban screen na wayar Lion ɗin ya yi dan ya ga me ya ɗaukewa Aryan hankali suna irin wannan zama kan mission ɗinsu mai muhimmanci, ai yana juyo da wayar sai……….



