Ruwan Zuma Page 5 Hausa Novel
(05) A kan gadon asibiti Laila ta tashi, ko da ta tuno mutuwar mijinta kuka ne mai k’arfi ne ya kwace mata tana tausayin kanta da kuma ‘ya’yanta da suka zama marayu a k’aramin shekarunsu. Washe gari suka koma Kano, gidan Umma suka sauk’a inda ake kar6an gaisuwa. Laila wacce tun farkawanta bata magana ta shiga ciki, tana tuna ranar da ta fara shigowa gidan kanta a lullu6e aka kaita d’akin masoyinta cikin farinciki, yau kuma ta shigo cikin gidan a matsayin mai takaba ga wannan masoyin nata da taci burin tsufa tare dashi. Shigowanta yasa idanun jama’a ya dawo kanta, masu kaico nayi, masu kuka nayi wasu kuma suka fara mata ta’aziyya wanda Laila bata ma iya amsawa sai d’aga kai da take yi hawaye na kwaranya a idanunta. Ajidde ce ta kama hannunta zuwa rumfar Umma, ko da suka iso Umma tashi tayi ta kamo hannun Laila tana gunjin kuka tana girgiza kai. “Aliyu ya tafi ya barmu, Aliyu ya tafi ya barmu. Allah ka gafartawa Aliyu, Allah ka masa rahama.” Shine abunda take ta nanatawa wanda yasa itama Laila kukata ya dawo sabo. “Umma ban ganshi ba, basu barni nayi masa bankwana ba suka rufesa, bai ga ‘ya’yansa ba.” Shine kalmar farko da Laila ta fara furtawa tun da taji labarin mutuwar Aliyunta. “Baza ki so kiga gawar Aliyu ba, yasha wahala kafin Allah ya d’auki ransa, addu’armu Allah yasa k’arshen wahalarsa kenan.” Umma ta fad’a cikin karayar zuciya tana tuno yanda ta ga gawar Aliyu babu dad’in gani, hawaye kuma bai daina sauk’a a fuskarta ba. Hak’uri ake ta basu sannan daga baya aka yiwa Laila jagora zuwa d’akinta in da suka fara zama, shikenan yanzu ita ba matar Aliyu bace ba don ya saketa ba sai don mutuwa ta rabasu? Rayuwarsu ta baya da suka yi a d’akin shi yake dawo mata daki-daki tana jin kamar ana yankar zuciyarta ce sala-sala. Sai a lokacin aka shigo gidan da Abul Khair wanda ke kama da ubansa sak, nan gida ya k’ara rud’ewa da kuka, Umma wacce ganin Abul khair ya k’ara tsananta kukanta ta rungume yaron a jiki tana jin tausayinshi tana kiran sunan Aliyu. Bayan anyi sadakan bakwai mutane suka watse ya rage daga mutanen gidan sai Yanayi (k’anwar Baban Laila) wacce zata zauna da Laila har ta gama takabarta. Laila ta so komawa gida sanin zaman gida ba dad’i zai mata ba amma Baba ya hanata a kan ta zauna har sai ta gama takaba. Tun dawowansu gida, Umma ta rik’e Abul khair bata son abunda zai sa yayi nesa da ita, bacci ne kad’ai ke mayar dashi gurin Laila. Ko fad’a yayi da yaro wanda suka zo ta’aziyya ba abun kunya bane a ga Umma ta fito tana masifa cewa uwar yaron ta kwa6i d’anta, wai Abul khair ba zai rasa uba ba sannan a zo gidansu a dakesa ba. Ganin rasuwa akayi yasa babu mai cewa komai sai hak’uri kawai da ake bata, wasu kuma sun d’auka rasuwan Aliyun ne ya shigeta wanda yasa take aikata hakan. Zaman gidan bai yiwa Laila wuya kamar yanda take zato ba, domin kuwa Umma bata ta6a mata abunda zai 6ata mata rai ba, sai ma tattali da take nuna mata ita da ‘yayanta. (Soyayya bayan rai). Sai dai wani abun da Laila ta lura dashi shine; Umma bata d’aukan Sabrin ko da wasa, iyaka ta tambayi lafiyarta shikenan. Washe garin ranar da Laila ta fita a takaba ta shirya kayansu tsaf domin zata koma gidansu, tuni motar Babanta ta kwashi kayan akan Madu yayanta zai dawo ya d’aukesu idan ya ajiye. Kallon k’arshe Laila ta yiwa d’akinta da Aliyu wanda babu komai a ciki sai tarin tarihi. Hawaye ne suka gangaro kan fuskarta da ya rame har ana ganin k’asusuwan fuskar tata. Hannunta tasa ta goge tana furta magana a hankali kamar wacce ke addu’a. D’akin Umma ta shiga ta samu Abul khair na bacci a cinyarta tana shafa kanshi, hakan yasa har Laila ta shigo Umman bata ji sallamar da take yi ba. “Umma mun gama shiryawa zamu tafi.” Cewar Laila tana mai zama a k’asa gurin k’afafun Abul khair. Sai a lokacin Umma ta d’ago kanta tana murmushi tana cewa, “Ha’ah Laila har kin fito?” Ta fad’i sunanta yanda yake ba kamar daa da take kiranta da Lamla ba. “An d’auki kayanmu an yi gaba dasu, Yaya Madu zai kai gida sannan ya dawo ya d’aukemu.” Ta fad’a da d’an guntun murmushi a fuskarta wanda ya fito da kyar domin ta jima bata yi hakan ba. Umma ce ta dakata da shafa kan Abul khair ta dubi Laila cikin tausayawa ta fara magana, “Sai hak’uri Laila, nasan me kike ji saboda nima naji wannan rad’ad’i na rashin miji, duk da cewa sai da muka tsufa tare sannan Allah ya d’auki abunsa. Kar ki manta da Aliyu, kiyi ta masa addu’a domin shi yake buk’ata ba kuka ba, kuka babu amfanin da zai masa, kin ji ko?” Laila da hawaye ya taru a idanunta ya sauk’o kan k’uncinta ta d’aga kai alamar ehh tana gogewa da tafukan hannunta. “Allah ya gafarta masa kurakurensa ya kuma sa Aljanna ce makomarsa.” “Ameen Umma.” Ta amsa tana mai k’ara wasu addu’o’in a zuciyarta. “Ina sauran kayan Abul khair? Naga baki shigo dasu ba.” Umma ta fad’a tana mai d’aga kai zuwa bayan Laila. “Ban gane ba Umma.” Cewar Laila zuciyarta na duka tana addu’a a ranta Allah yasa ba abunda take tunani Umma ke nufi ba. Umma ta k’ara shafa kan Abul wanda ya fara tashi daga bacci ta murmusa tace, “Wannan maigidan nawa ai a gurina zai zauna domin shi zan dinga gani yana d’ebe mini kewar Aliyu.” Ta k’arishe maganan tana share hawaye a fuskarta wanda suka zubo nan take. Shiru Laila tayi amma ko kad’an zuciyarta bai yarda ta bar Abul a hannun Umma ba. Ina ake raba d’a da mahaifiyarsa don kawai mutuwa da d’auki ubansa? “Amma Umma ai baza ki iya rik’e yaro k’arami kamar Abul ba, d’awainiyarsa da yawa zai baki wahala sosai.” Ta fad’a cikin nitsuwa ko hakan zai sa Umma ta canja ra’ayinta. “Ji shashanci, ni da na rik’e ubansa sai rik’onshi ne zai mini wuya Lamla?” Umma ta fad’a cikin fad’a tana mai zaunar da Abul kan cinyarta bayan ya tashi daga baccin. Gyara zama Laila ta yi amma zuciyarta cike take da tsoro da kuma dakewa irinta uwa tace, “Allah ya huci zuciyarki Umma amma kinsan rik’on Abul a hannuna take ni mahaifiyarsa. Don Allah karki d’auki hakan a matsayin rashin kunya amma zan tafi da Abul gidanmu, zan dinga kawo miki su duk sati su kwana miki.” “Zancen banza zancen wofi, har ni zaki kafawa sharad’i a kan gudan jinina? Ina da iko akan Aliyu balle kuma d’an Aliyu, ashe har yanzu baki da hankali? Na d’auka mutuwar Aliyu zai sa ki farga ashe har yanzu sammakal? To a kul d’inki kiyi jayayya dani akan abunda baki da iko dashi.” Sosai ran Umma ya 6aci tana fad’a ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, jin hayaniyar yayi yawa yasa Muna ta shigo ta samu Umma na fad’a tana rik’e da hannun Abul wanda ke kuka a jikin mamanshi domin ya ga itama kukan take yi. “Umma lafiya naji maganarki har tsakar gida?” Cewar Muna farin ciki fal a fuskarta saboda ta ji komai. A nan Umma ta mayar mata da zance tana jawo Abul jikinta wanda yake ihu yana tsalle wai bazai je gurinta ba. “Kin ga shima ta asirceshi ko? Ta rabani da Aliyu gashi zata rabani da d’a d’aya tilo daga d’ana.” Da haka ta fashe da kuka tana cewa, “Mutuwa mai tonon asiri, yanzu ni yarinyar nan zaki yiwa gorin d’a don kinga d’ana baya doron k’asa?” Muna dake bakin k’ofa ta fara rarrashin Umma sannan ta maida maganarta kan Laila, “Yoo in banda ke tunda ga Sabrin sai ki bar mata Abul itama ta samu abun sanyawa a ido tana jindad’i. Ai ba rabaki dashi za’a yi ba, rik’onshi ne zai koma gurinta.” “Ni ban damu har auren yarinyar ta rik’eta ba tunda dama mai sunan uwarta ce, amma Abul kam babu mai rabani dashi, shi nawa ne.” Umma ta k’ara akan maganar Muna. Laila dai na zaune ga Abul a jikinta tana kuka bata ce musu komai ba, amma kuwa suma sun gane me take nufi, wato baza ta tafi ba tare da d’anta ba. Sallaman Nazifi a tsakar gida yasa Muna ta fita tana bashi labarin halin da ake ciki, da saurinsa ya shiga d’akin yana ganin ikon Allah, Abul rungume jikin mamanshi suna kuka dukansu yayinda Umma ke rik’e da k’afar Abul d’in tana k’ok’arin jawoshi tana masifa. “Innalillahi Umma menene haka?” Nazifi ya fad’a yana mai kar6e Abul d’in daga hannunsu duka. Kuka Umma ta saka tana fad’in cewa Laila ta mata rashin kunya akan jikanta. “Don Allah Umma ki bar maganan nan, ga Baban Laila a waje yazo gaisheki.” Cewar Nazifi sannan ya fita waje suka shigo da Alh Kashim. Laila da har lokacin tana durk’ushe a gaban Umma ta tashi ta fita zuwa tsakar gida, itama Umma ta bi bayanta bayan ta saka mayafi. Tabarmar da Muna ta shimfid’a a rumfa Baba ya zauna a kai, sannan suka gaisa da Umma yana k’ara mata ta’aziyya tare da mata godiyan rik’e Laila da suka yi har ta gama takabarta. Hankalinshi ne ya koma kan Laila dake tsaye a gefe tana share hawaye, tausayinta ne ya k’ara cikashi a karo na ba adadi tun mutuwar mijinta. “Addu’a Aliyu yake buk’ata ba kuka ba Laila, ki sa dangana da hak’uri a zuciyarki. Allah ya gafarta masa.” Da haka ya fara yin addu’a ya d’aga hannu, saura ma suka d’aga nasu har ya gama aka shafa. Mik’ewa yayi yasa takalmansa yana yiwa Umma sallama amma Laila na tsaye har yanzu a in da take bata motsa ba sai kuka da take yi a hankali jikinta na jijjiga. “Alhaji wai kuka take yi akan Abul, nayi magana kan zai zauna a gurina ta nuna bata yarda da hakan ba. Ban san me na yiwa Laila ta d’aukeni kamar bare ba.” “Laila me nake ji haka? Wannan ba halinki bane, idan tace zata rik’eshi ai baza ki mata musu ba, ko bayan ran Aliyu ita mahaifiyarki ce bata canja ba.” Cewar Baba cikin fad’a yana kallon Laila. “Ki bata hak’uri sannan ki mata sallama mu tafi. Hajiya mu zamu wuce gida, Allah ya bar zumunci ya kuma raya ‘yayan dake tsakaninsu.” “Ameen Ameen.” Umma ta amsa. “Baba don Allah kuyi hak’uri ku bani Abul, Umma don Allah kiyi hak’uri ki bar mini d’ana.” Muryar Laila suka jiyo cikin kuka tana musu magiya. Ran Baba ne ya 6aci sosai ya fara mata fad’a kan tana son koyan rashin kunya. Daga baya da kanshi ya tisa k’eyarta zuwa mota sai kuka take yi. Tana ganin Abul a hannun Nazifi ya shige cikin gidan yaron yana zillo yana mik’a hannunsa zai zo gurinta. Dafe kanta tayi da dukkan hannayenta tana kuka tana jin zafi da kuma zogin rabuwa da Abul. Madu dake zaune a mazaunin direba ya juyo yana kallonta sannan ya fara bata hak’uri a tsammaninsa kukan mutuwan take yi. Sai da suka fara tafiya sannan Baba yake fad’a masa rashin kunyar da tayi a gabansa a kan d’anta. Shiru Madu yayi amma yaji haushin abunda Laila ta yi, dama tun da ba wani shiri ne tsakaninsu ba saboda dukanta da yake yi akan wai kwalliyarta tayi yawa. Daa Baba baya kusa ne zai mata fad’a kaca-kaca tunda dama shine mai kareta. Har suka iso gida Baba fad’a yake yiwa Laila daga baya kuma ya koma rarrashinta, “Ban ji dad’in musun da kika yi da ita akan jikanta kuma a gaban ‘yayanta ba. Haba Laila, don tace zata rik’eshi ai ba rabaki dashi zata yi ba. Shima kuma zai ji dad’in zamanshi kusa da dangin mahaifinshi. Ki bar kukan nan haka, duk in da yake zai samu kulawa.” Gyad’a kai kawai tayi tana goge fuskarta amma zuciyarta na mata kukan rabuwa da gudan jininta. Tunda mutuwa ta rabashi da mahaifinsa ai bai kamata kuma Umma ta rabashi da mahaifiyarsa ba, rashi biyu a lokaci d’aya yaron ba zai d’auki hakan da sauk’i ba. Tana shiga gida da Mas’ud ta fara cin karo wanda aka hanashi zuwa d’aukota, kamo hannunta yayi zuwa d’akinta yana fad’a mata cewa shi ya gyara komai ya kuma kimtsa mata kayanta da aka kawo d’azu. “Ga can Sabrin a d’aki tana bacci, tun lokacin da Iya Yanayi ta dawo da ita na goyata.” Da haka suka shiga d’akin yana mata hira duk don ta sake amma sai gani yayi tayi zuru tana kallon gefe. Sai a lokaci ya tuna da bai ga Abul ba, “Kalti ina Abul khair, ko yana gurin Baba ne?” Ya tambayeta yana mai ta6a hannunta don ta dawo da hankalinta kanshi. Kuka ta fashe dashi sannan ta 6oye fuskarta da tafukan hannunta. “Umman Aliyu ta rik’e Abul tace baza ta bani shi ba, sun rabani da d’ana alhali ko rashin mijina bai fita daga zuciyata ba. Ina zan sa kaina Mas’ud? Ga rashin miji ga rashin d’a duk a kaina kuma a lokaci guda, don Allah kace su tausaya mini. Ina k’ok’arin d’aukan nasiharsu bana yiwa Aliyu kuka, amma rabuwa da d’ana ne bazan iya ba. Su tausaya mini su barni na rik’e ‘yayana su taso guri d’aya. Don Allah kace su tausaya mini.” Zan tsaya a nan don ina rubutu ina kwatanta d’acin da Laila take ji wanda hakan yasa I can’t write more. 😢 Wasu dangin mijin suna raba yara da mahaifiyarsu idan d’ansu ya rasu. Sai kaga yaro ya taso ba uwa ba uba ba don ya rasa uwar ba. Meyasa muke haka? Ruwan Zuma littafin kud’i ne a Naira dari kacal N100. Zaku turo kud’inku ta bank 5139579011 FCMB Suwaiba Babagana, ko kuma katin waya Zain/Airtel ta wannan number 09023713064, Zaku yi amfani da wannan number dake sama domin nuna shaidarku na biyan kud’in Ruwan Zuma. Ga maza masu son shiga, kuma zaku turo kudinku sai ku yiwa wannan number magana 0903 662 1442 a sakaku a group na maza zallah. Sannan Ina wad’anda basa son hayaniyar group? Zamu iya tura muku ta private a farashin N300 mace ko namiji. Sai na jiku.
