Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 33 By Ayshercool

Jinjina kai indabo yayi, ya ce “Za ayi ba zai gagara ba, zamu dawo idan an kammala aikin, kuma wa’adin da aka ɗibar mana ya cika”.”Shikenan, nasara tana tare da kai, ba yaƙini muke da shi ba, tabbaci nake bakaz duk da akwai ƙalubale a gaba, sai da ba za su gagara ayi maganin ƙalubalen ba, amma a gaba kaɗan ɗin akwai dutse, da zaka yi karo da shi, na buga na duba, duk babu hanyar maganin dutsen nan, sai dai ayi ragas, ko ka kar dutsen ko ya kar ka”P.A ya ce “Kuma babu yadda za ayi da dutsen? Ko wata mafitar?””A yanzu dai babu, Suka tashi suka fito, suna tafe a hanya Indabo ya ce “P.A””Na’am honorable””Bokan nan kullum cikin faɗin ayyuka masu hatsarin gaske yake, ina tsoron tonuwar asirina, kar mu je in sake janyo wa kaina jagwal kana kallon yadda yarinyar nan Naja’atu ta zame mini alaƙaƙai””Mu bi komai a sannu sir, zamu yi nasara kuma samo yarinya ba zai gagara ba, ko cikin ƙauyukan nan aka bincika za a samu, ko kuma Naja’atu ta samo a irin mutanen da ke hulɗa da su” yayi ajiyar zuciya ya ce “Ba zan so ce a samo ta ɓangaren ta ba, amma kai na ɗora maka ragamar samowar””Za a bincika in sha Allah sir””Yayi, ina jiranka, ka ga idan lokaci ya ƙure, aikin da muka yi ya koma baya””Haka ne, da yardar Allah ka ci kujerar nan ka gama, mu je injiniyoyin suna can gida suna jiranka, aje ayi lissafi””Ok to, Aminu haryanzu ya ƙi zuwa ko?””Wallahi yaƙi, Allah da wani wanda zai iya yi mana irin kasadar da yake ɗauka, da mun canza shi, ɗan rainin hankali ne, ko fushi yake saboda wannan karon ba ka fito da shi ba?””Da fushi yake yi, ba zai ɗauki wayata ba, kuma ina son aiki da shi, ba ya jin kasada komai zafinta kuma ba shi da mgana ko kisan kai zaka yi a gaban sa, sai ya ga dama zai ɗaga kai, balle ka ji zancen a waje. Sannan babban abun shi ne, bokan nan ya ce nasarata tana tattare da wanda yake zubar mini da jini, na riƙe shi sosai, shiyas nake shanye iskancin sa”.P. A ya ce “haka ne ya na da amana, ba shi da magana sam, amma shi ya san da hakan ne?”.”Haba dai, hauka nake yi na bari ya sani, ba abun da ya sani, kawai aiki yake yi mini” Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma, manyan injiniyoyi ne zaune a falon indabo, suna ta lissafin ginin plazarsa.Ga wanda zai tattauna da su a kan harkar yaƙin neman zaɓensa, suma su na jiransa.Al’amin yana cikin falon, ana ta lissafi, shikuwa yana hakimce yana kallon tv.Sai da aka gama lissafi, za ayi total ɗin kuɗi, Al’amin ya kalli shugaban engeneers ɗin ya ce “Kayi plusing da kuɗin siminti buhu shida, da tiles carton biyar”Ya ce “Na menene?””Ina ruwanka, ka saka kawai”.Injiniya ya kalli Indabo, Indabo ya ce “Kuɗi ka ke buƙata ne na baka?””Gyaran gidana zan yi nima”Indabo ya ce “Engeneer a rubuta, a bashi”Al’amin ya sake cewa “Akwai yarana mutum biyar, da nake son a saka mini su a cikin aikin ginin nan, su yi su ma a sallame su”P.A ya ce “An gama mai dogon zamani””Zamu zo tare da su, ni ne cikon na shida, da ni za ayi aikin a biyani”P.A ya sake cewa “Ba ka da matsala”Aka gama aka sallami injiniyoyi, ‘yan jami’iyya suka shigo, duk yana zaune, aka gama meeting.Duk sai da suka gama, sannan Indabo ya mayar da hankalinsa da Al’amin ya ce “Mai zamani” ya ɗaga ido ya kalli indabo.”Akwai tafiya da zan yi ƙaddamar da takarata, a yammacin garin nan, ina buƙatar tawagar ka kai da mutanen ka, saboda ban san ya zata kaya a wurin ba, ‘yan sandan nan gaibu ne wasu lokutan”.”Yaushe ne?””Nan da kwana goma””Cikin azumi kenan?”Indabo ya ce “Eh””Allah ya kaimu, baka da matsala”P.A ya ce “Allah ya ƙara maka nisan zango mahadi mai dogon zamani. Ina matarka kuwa?”Da sauri ya kalli P.A ya ce “Kamar ya ina matata, meye haɗinka da ita?””A’a babu komai, lokacin da kana tsare ne, ta zo ita da Walid, ko da yadda za ayi ka fito, lokacin honorable baya nan”Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba.Wata ƙatuwar mage ce ta shigo, da matasan ‘ya’yanta, fara tas kana ganinta ka san ‘yar waje ce.Al’amin ya tashi ya nufi in da take, ya saka hannu ya ɗauki guda ɗaya ya ce wa P.A “Wannan mace ne ko namiji?””Namiji ne””Zan tafi da shi”P.A ya ve “Ka san kuɗin abun nan kuwa? Ya kai dubu ɗari shida fa, wannan ƙaramin”.”Da gold aka yi shi ne?” Yayi maganar yana nuna ɗan muzurun da yake ta ihu saboda ya ji matsa.Indabo ya ce “A’a ɗan Germany ne””Tun da ba daga aljanna ya zo ba shikenan, kai kawo leda na saka shi” yayi maganar yana kallon mai goge-goge.”P.A ya ce wace irin leda kamar zaka ɗauki masara, kwando dai za a baka.Yayi ƙerere, aka kawo masa kwando, ya saka muzurun ƙato da shi fari, jikinsa cunkushe da gashi mai kyau.Ya kalli Indabo ya ce “Zan tafi”Indabo ya yi murmushi ya ce “Ga abun kuɗi nan ka ɗauka a hannunka, ai ba sai an sallameka ba””Za a sallame ni ko in tafi?””P.A sallame shi”P.A ya buɗe jaka, ya ɗebo kuɗi ya miƙawa Viper.Al’amin yayi masa wani mugun kallo, indabo ya ce “Ƙara masa””Ya ƙara ɗebowa, ya ƙara masa”Ya karɓa ya ce “Na karya wani yaro, yana emergency, babar yaron tayi maganar a kamani, a bi wa ɗanta hakkinsa, yana can a emergency asibitin tsakiyar gari, a kashe wutar, ko ta ƙone yiwuwar aikinka, hankakin nan suka yi ram da ni, ba zan yi aikinka ba” daga haka ya fice daga falon.P.A ya ce “Kai, honorable Mai zamani yana hawa kanmu da yawa wallahi, wai sai abun da yake so za a din ga yi yayi ta yi wa mutane tunƙaho?”Indabo yayi murmushi ya ce “Rabu da shi lokaci ne, bari a ci zaɓen, ai ka ga mutumin can ya ce akwai nasarar mu a tattare da shi, yanzu abun da za ayi, ka koma ka yi waya, ka saka a haɗa wata tawagar ta ‘yan daba, da zasu far mana a wurin taron, yadda za a samu a zubar da jinin shi ma a can. Sannan ka tara mana ‘yan media, idan hakan ta faru a ce abokan adawa ne suka yo hayar ‘yan daba suka far mana”.”An gama honorable, yanzu kuwa zan je na tara su na sanar musu tun yanzu””Yauwwa, idan ka gama da su, a hanzarta ko aike ka yi wurin wanda ya karya ɗin, a rufe bakin babarsa””Ok sir”***Al’amin ya koma gida, ya tarar da Jauhar da maƙwabta, tana yi musu kitso.Yana shigowa hannunsa riƙe da ledoji, ta tashi tana murmushi, suka gaishe shi, babu wanda ya amsa sai sannu zuwan da tayi masa ya amsa.Ta miƙe hannu za ta karɓi kwandon, ya ce “Banda wannan” ya shiga falo da shi.Ta dudduba kayan, kayan abinci ne wata irin ajiyar zuciya ta sauke, tare da yi wa Allah godiya.Allah ya sa ta gama kitson, ta sallame su suka tafi, ta shiga falon hannunta riƙe da cup ta risuna ta miƙa masa. Ya karɓa ya ga zoɓo mai sanyi, sai ƙamshi yake yi. Ya kafa kai ya zuƙe ya miƙa mata kofin ta ce “Ba ka ce ba”Ya ce “Alhamdilillah” tayi murmushi ta ce “Sannu da zuwa” ya jinjina kai ta ajiye kofin, ya jefo mata muzurun nan a jiki, ta saki ihu tana tsalle, ta ce “Meye wannan?””Shi ma wannan ɗin tsoronsa ki ke ji?””Kamar kare fa?””Mage ne, saboda ƙadangarun da suke damunki, ko shi ma tsoronsa ki ke ji?”Ta ce “Laaa, to ai bai yi kama da mage ba, masha Allah so cute” ta durƙusa ta ɗauke shi.”Master ina ka samo shi dan Allah, kamar ba ɗan nan ƙasar ba. Kai amma na ji daɗi sosai, wani sunan zamu saka masa”Ya ce “Muzuru”Ta kwaɓe fuska ta ce “Muzuru kuma? Sunan gayu za a saka masa, wane irin muzuru?”.”Ba sunansa kenan ba?””A’a, na saka masa suna mai zamani””Ki ka kuma ko?” Yayi maganar yana kallonta.Tayi murmushi tana shafa kyakkyawan jikin muzurun.Ya ve “Da gaske kin je wurin P.A ɗin Honorable lokacin da aka rufe ni?”Ta kalleshi ta sunkuyar da kai. “Ki bani amsa”Ta jinjina masa kai alamar eh.”Ko wani irin hali zan shiga, kar ki sake zuwa wurin wani, mussman gidanmu da wurin ‘yan siyasar da nake mu’amala da su, dan su fito da ni”Ta ce “In sha Allah, ba zan sake ba, amma dan Allah ka daina zuwa wurin da zaka cutu, kaga idan aka rufe ka, nikaɗai nake damuwa ba wanda yake taimaka mini, ni kuma ba zan iya jurewa ba ganinka a tsare” tayi maganar jikinta a sanyaye.Ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi, ya ce “Ungo”Ta saka hannu ta karɓa ta ce “Na menene master?””Ana zubar da kuɗi ne?””Wai bani ka yi? Duka nawa ne?””Mmm ki sha madara”Ta washe baki ta ce “Allah ya saka da alkhairi, Allah ya yi maka jagora, ya ƙara jan dogon zamanin nan”Ya ce “Za ki ga zamani, idan na kamaki”Tayi murmushi ta ce “Wannan kuɗin ya fi ƙarfin shan madara ai”Ta din ga kwarara masa addu’a, tare da nuna tsantsar farincikinta a kan abun da ya yi matan.A daren ya kira guduma a waya, ya sanar masa da batun aikin ginin da za ayi, ya kira Walid da su liti, da wasu daga cikin yaransa, sai dai sai da suka sha wiwi, suka yi bushe-bushen su, domin samun ƙarfi wurin gabatar da aikin.Sai dai tun da Allah ya sa Al’amin ya kawo ɗan muzurun nan, jauhar ta samu nayi, ta tattara nutuswarta da hankalinta a kansa.Duk ranar da babu aiki, sai guduma ya zo gidan Viper, ya tambayi jauhar ko ta na da aike ta kawo ya kai mata, tun ranar da ya ga zata kai markaɗe, ya karɓa ya kai mata, Anty sama Anty ƙasa, kasancewar ta mai kyauta, ya sanya take farinjini a wurin mutane, dan idan yayi mata aike, idan tana da Abinci ta na bashi, ba da abincin nan ba ƙaramin kankaro mata kima yake yi a. Sai guduma ya mayar da Al’amin kamar yayansa, bashi kaɗai ba, har ‘yan sauran yaran da suke rashin jin, jama’ar guduma, idan suka ga Al’amin, tsakaninsu da shi girmamawa, idan da kuɗi a jikinsa, haka zai bi su mai ɗari biyar mai dubu, hakan ya sa suke yi masa biyaya sosai da sosai.Hatta layin gidansa, idan kwata ta cika, ko ciyayi suka fito, haka za su zo da kayan aikin su, su gyara tsaf.Sannu a hankali, Al’amin ya fara janye matasan, shi dai ba zai hana su shaye-shaye ba, sai dai akwai abubuwan da ya yi musu iyaka da sha.Da sharuɗan da ya gindaya musu, a kan in dai za su zauna da shi, sai sun kiyaye su.Jauhar tana makaranta jarrabawa, biyu suka yi ranar, ta dawo ta tarar an yi plasta a gidan gaba ɗaya, da shi da su Walid da guduma, sun yi kaca-kaca da gidan.Tana tsaka da mamakin ya dawo, ya tarar da ita ta ce “Master, aiki ku ka sha haka? Baka gaya mini ba, balle na kwashe kayan kuma ayi wa masu aikin girkin?”.”Da su mai laya muka yi, ba wani abu”.”Master wai a ina ka samu kuɗi haka? Amma ka yi haƙuri idan tambayar da na yi tayi tsauri”.”Bana sata” amsar da ya bata kenan ya fita.Zata iya shaidar hakan, amma yakamata ace ta san in da ya samu kuɗi, tana tsoron ya ɗaukko musu rigima, sai dai gidan yayi kyau sosai.Da daddare ya dawo, sai dai sai wani share ta yake yi, dan ya ji haushin tambayar da tayi masa.”Master, dan Allah ka yi haƙuri, na san tambayar da nayi maka tayi tsauri, amma ka yi haƙuri dan Allah, Allah Ya ƙara maka arziki da wadata, ya tsare mini kai a duk in da ka ke” yayi mata shiru yaƙi amsawa.”Tuba nake, tare da dukkanin girmamawa kaina bisa wuyana, nake roƙon ayi mini afuwa, ayi haƙuri a yafe wa ƴar madara ranka ya daɗe, Allah ya ƙarawa zamaninka tsayi, ya kare ka ko a gida ko dawa ayi haƙuri ina ƙara bada haƙuri namijin mazaje”Ba ƙaramin fasa masa kai kalamanta suka yi ba, duk da ba yau aka fara yi masa kirari ba, amma sai ya ji nata ya zama na musamman, har cikin kansa ya ji kirarin.Amma kamar wani basaraken zaki, haka yayi shiru ya cigaba da kaɗa ƙafa.”To in dafa ruwan wanka na kai toilet ɗin tsakar gida? Na san an gaji da yawa yau.Ya kalleta ya ce “Ba na so”Ta sakar masa wani ƙasaitaccen murmushi ta ce “Ai na ce ayi haƙuri, manya ba sa fushi fa” ta yi maganar cikin shagwaɓa.A taƙaice ya ce “Kai mini”Bayan yayi wanka, suka zauna a falo, suka ci abincin dare, dama tun a hanya ta sayo wa magenta kifi, ta nutsu tana bashi, tana yi wa master hira.Kasancewar ɗakunan an yi sabuwar plasta, ya sanya suka kwana a falo, sai da ya tabattar ta yi bacci, sannan ya fice tsakar gida yayi shaye-shayensa.Gaba ɗaya washegari jauhar a gidan mai ɗinki ta wuni, ta tayata aikin ɗinki, saboda gidanta su Al’amin suna aiki, hatta ƙofar gidan sai da aka yi wa plasta, gyara ko yaya yake kyau ne da shi, sai ga gida yayi kyau sosai da sosai.***Yau ɗaya ga azumi, ranar jauhar tana da exams, Al’amin ya ce ta zo ta hau babur ɗin sa ya kaita, babu abun da ta tsana irin yadda yake yawo da babur ɗin babu salansa, ga babur ɗin kamar na ‘yan gwangwani,saman babur ɗin nan duk a ragargaje, kana kallon wayoyin da aka yi wearing ɗin nan da su.Amma dan kar ta watsa masa ƙasa a ido, haka ya karkato babur ɗin, ta rirriƙe shi ta hau, suka tafi.Ko da ta dawo a gida ta tarar da shi, duk idonsa yayi ja, wanda idan ba da ƙwaƙwƙwaran dalili ba, ba za ka ganshi a gidan ba.Ta kalleshi ta ce “Master na dawo”Ya ɗaga mata hannu kawai.Ta shiga ta canza uniform, ta dawo yana kwance yayi wujiga-wujiga.Ta fito ta shiga kitchen, dan ta ɗora musu abun buɗa baki da wuri.”Master wai duk azumin ne, ko magana ta gagara” yayi mata shiru. Kawai ta hau dariya “Wallahi master ranar da babu abinci ban san yaya zaka yi ba, wato ba ka ko azumin nafila, yau ɗaya duk ka fita hayyacinka har haka?” Hararta yayi, yayi mata banza.Ta din ga yi masa dariya, ƙarshe ya koma tsakar gida ya shimfiɗa tabarma, yayi shame-shame kamar gawar sababi.Ko da aka sha ruwa, ba yadda ba ta yi da shi ya tafi masallaci ba, ya ƙi ya shanye lemo jug guda, da uban ruwa kamar amale, kuma ya fara da cin shinkafa, maimakon ya fara da abu mai ɗumi yaƙi.Ta ce “Ohh ni matar master, ya Allah kar ka hanamu abun da zamu ci a kowane hali, ranar da babu abinci akwai matsala master magana ma ta gagara yau azumi ɗaya kamar zaka rasu?” Yayi mata shiru yaƙi kulata.A ɗan tarin da take yi, da kuɗin da ya bata daf da azumi, tayi musu sayyayar kayan tea saboda tanadin azumi.Sai da aka yi azumi biyar, sannan Al’amin yake iya fita idan yana azumi, ya je ya ɗan yi neman kuɗinsa, gefe ga black market ɗin su ta sayar da kayan maye.Yau ya dawo da la’asar ya sheme a falo, sai sauke numfashi yake yi.Ta kalleshi tana dariya, ya kalleta ya ce “Ki ka sake ki ka yi magana ni da ke ne”.Jauhar ta ce “A’a ni ban ce komai ba” tayi maganar tana cigaba da dariya.Tana ta aikinta an kusa shan ruwa ya ce “Anya kina azumin nan kuwa?”Ta ce “Ina yi mana””Gani nayi yau sha bakwai ga wata, ba kya azumi”Ta kalleshi ta ce “To meye da sha bakwai ga watan?”Al’amin ya ce “Period ki ke yi, dan banaba kya azumi” zaro ido tayi cikin mamaki, yaya aka yi ya san tana period, cikin jin kunya, ta ce “Ni ba abun da nake yi, ba wanann date ɗin bane”Kawai ya gyaɗa kai, ya ce “Ai da ki ka gama cin ƙosan a kitchen ki ka cika cikinki, ba ki goge bakinki ba, kuma lemon da ki ka sha ma cup ɗaya kin sha naki, tun da ba azumi ki ke yi ba, sai iya yi mini dariya” ai kamar ƙasa ta tsage ta nutse, ba ta sanin ya ake yi, yake sanin ta aikata wasu abubuwan ta hau goge baki ta ce “Sa ido ba kyau, azumi ka ke yi kar ka zobe ladanka, ko a kwashe ladan naka a bani”Yayi murmushi bai ce komai ba.A wurin shan ruwa faɗa suka yi ta yi, wai ba zata cika kofi da kunu ba, ba tayi azumi ba, kamar sako da sakuwa.”Wai master, dan ban yi azumi ba ai ni na girka, sai ka barbaɗawa duniya ban yi azumi ba? Haba master”Ya ce “Eh ai ba yi ki ka yi ba, dan haka nawa sai ya fi naki yawa, ƙara mini”Ta tura baki ta ce “Aikuwa da gobe in Allah ya kaimu sai dai ka karɓo kunun sadaka, da ƙosai ka ci, ba zan yi girki ba, tun da ni ba na azumi, ko ka girka abunka”.Ya ce “Eh dan dai girki, ba wuya zan iya, ƙosan nan ma rago shi nan, gandiya ƙatuwa da ke ba kya azumi””Bani da lafiya ne” haka suka yi shan ruwan, ya din ga jin kamar bai taɓa shan ruwa da nustuwa irin wannan ba.Ita kanta tsokanar da yake yi mata daɗi take ji, bayan sallar isha’i ya zauna a falo, ya ɗauka zata yi masa surutun da ta saba, sai dai hankalinta ba ya kansa, yana kan magenta da take cewa boti, tana bashi abinci tana shafa shi, haushi ya ishe shi, shi gashi ba iya hirar yayi ba, balle shi ya fara, kawai ya tashi ya tafi ɗakinsa. Bayansa ta bi da kallo kawai ta yi murmushi ta ce “Master kenan, hukuma sai da rarrashi”.Bakwai ga watan azumi ya kama ranar da za su bi Indabo campaign, tun dare ya haɗa yaransa da wurin da za su haɗu su tafi.Da sassafe bayan Jauhar ta tashe shi yayi sahur, ta idar da sallar asuba ta kwanta bacci, ya silale ya fice.Wunin ranar ba ta ganshi ba, ba ta damu ba sai da ta ga an kusa shan ruwa, ta din ga kiran wayarsa, amma ba ta shiga, sai hankalinta ya fara tashi, dan ta san duk in da ya je da an kusa shan ruwa yake tahowa gida.Al’amin kuwa bayan sun dawo daga campaign, an yi sare-sare sun yi shaye-shaye, an yi wa indabo aikinsa yadda yakamata, Al’amin ya sallammi yaransa, shi kuma Indabo ya ce ya bishi gida, da shi da wasu ‘yan jami’iyya su sha ruwa a gidansa, ya sanya an shirya abun shan ruwa.Al’amin ya ce sai dai su tafi tare da walid.Ƙaton falo ne na musamman, mai ɗauke da haɗaɗɗem dining, kayan abinci aka kawo, na ƙasaita aka din ga jerewa a kan dining ɗin nan, cikin fulasai na alfarma.Walid ya ce “Mu na cin albarkacinka mai zamani, wannan sabga haka?”Al’amin ya bari, aka gama jere abinci, ana ta rawar jiki a fara ci ayi buɗe baki, ya tashi, ya bubbuɗe fulasan.Wani irin farfesu aka yi na kajin gidan gona, ƙosassu, ga flask ɗin dankali dana ƙwai abincin ma har da na almubazzaranci.Al’amin ya ja flask ɗin kaji, ya janyo na dankali, ya haɗe kan kayan shayi madarar gwangwani da milo, ya kalli Walid ya ce “Dafe mini wannan mu ɓace”.Indabo ya ce “Ina zaka tafi kuma, za a ci abinci?””Gida” ya bashi amsa.”To kuma na ga kana harhaɗe kan kwanukan abincin, ya zaka yi da su ga mutane za su ci?”Kai tsaye ya ce ” ‘yar madara zan kaiwa””A’a ya mage zata yi da wannan uban abinci haka?”Walid ya ce “Ba mage ba ce, madam za a kaiwa”Indabo ya ce “Haba mai zamani, sai ka ce a ɗibar mata, amma yaya za ayi mutane na zaune abincin mutum sha biyu duk ka kwashe rabi?”.”Ba zai yiwu da ni da na saka rayuwata a hatsari, da wanda ku ka tsaya a cikin rumfa hankali kwance, ka yi mana sallama iri ɗaya ba, ai kana da kuɗi a dafa musu wani. Ka san son zuciya ba halina bane, a baya ban yi ba ba zan fara yanzu ba. Ba zan ci wannan abincin ita ba ta ci ba, kuma ai ga wasu nau’in abincin nan ku ci. Walid ɗaukko kwandon kayan marmarin nan ma”Indabo ya ce “To fulasan fa? Ka tsaya sai a juye maka a leda, na madam ne wannan””Madam ba ta fi madam ba, sadaki bai fi sadaki ba. Ina fatan ka fahimci lissafin? kuma kuna da kuɗin sayen wasu, ko ba yanzu ba idan kun ci zaɓe zaku samu, dan haka har fulasan mun cinye” Indabo yana ji yana gani, Al’amin ya yarfa shi a gaban jama’a, suka kwashe abinci suka tafi.Jauhar ban da ruwa babu abun da ta sha, har bayan sallar isha’i sai yawo take yi a cikin unguwar tana nemansa, hankalinta a tashe. Ta gaji ta dawo gida da nufin ta kira Walid.Kawai ta dawo ta tarar da shi.”Master ina ka tafi, hankalina ya tashi tun safe rabonka da gida, ba ka gaya mini ina zaka je ba, gaba ɗaya tun da aka sha ruwa na kasa cin komai, ban san ina ka ke ba”.”To kukan zaki yi?” “Baka gaya mini ina zaka je ba, hankalina gaba ɗaya ya ƙi kwanciya haba master dan Allah””Ohh murya kamar tsuntsuwa, yenyenyen, ki din ga buɗe baki ki yi magana sosai” kawai tayi shiru cike da takaici, idonta kawai ya kalla, ya san hankalinta a tashe yake.Ƙeyata ya tura, zuwa ɗakinsa kawai ta tarar da jeren kwanuka, haɗaɗɗun fulasai, da uban kayan marmari.Tayi saroro tana kallon kayan.”Zo ki zuba mana mu ci, ba kayan wani bane, mun je campaign ne muka dawo aka shirya shan ruwa, na ce a gida zan ci na taho da shi”.A ɗan tsorace ta ce “Master duk wannan kuma?””Eh kwaso kwanuka”Iya kajin sai da suka tsorata ta, dan sun kusa goma, fulasai ne na alfarmar gaske.Ta ce “Ai ba zamu iya cinyewa ba”.”Gasu nan dai, ki yi abun da ya dace”.Duk son Jauhar da nama, sai da ya isheta, ta bawa maƙwabta, ta zuba wani ya kira guduma a waya, ya ce masa ya zo ya karɓa.Hatta magenta, sai da ya ƙoshi da ciye-ciye.Haka kurum ya din ga jin annashuwa a ransa, ganin ta ci ta ƙoshi, har abun ya gundureta.Bayan jera masa godiya da ta gama yi, kamar yadda ta saba, tare da addu’oi, ta ce “Master Alfarma zan nema a wurinka dan Allah””Ina jinki”Ta saka hannu ta karɓi wayarsa ta ce “Dan Allah kar ka ce mini a’a, ko ba zaka yi ba”.”To kar ki tambayi abun da ba zan iya ba”.”Zaka iya mai babban suna, kaga naman nan yayi mana yawa, duk da an babbayar dan Allah sonake na ƙara gyara shi, ayi miya gobe in Allah ya kaimu, mu je yi wa su baba sannu da shan ruwa”A take ya tsuke fuska, ya ƙi magana.”Dan Allah Master, na neman albarka mu je mu gaishe su””Wai ke wace iri ce ne? Tun da muka yi aure, bayan su hajiya, kin ga wani ya zo gidan nan daga ɓangarena? Ko Abbun kin ga ya zo? Dama maraba suke nema da ni, har gara mahaifinki ma ya zo”Jauhar ta ce “Kar ka ce haka, dama ba su yakamata su zo ba, mu yakamata mu je, ai su iyaye ba a fushi da su, kai fa ka yi wa wani faɗa a kan haka, bai kamata kai ace ka aikata haka ba, dan Allah ka yarda mu je” An kai ruwa rana sosai tsakaninta da shi, kafin ya amince.Washegari suka shirya, bayan azahar suka fara zuwa gidan su Al’amin.Suka fara zuwa gidan su Al’amin, suka yi sa’a Abbu yana nan, sai dai rahila tayi mamakin ganin Al’amin, yayi wani shar da shi, sai ƙamshin turare yake yi kayansa sun sha guga.Ashe Abbu zuwansa gidan su biyu, ba ya samun kowa, a gidan, gashi Al’amin ya wanke ƙafarsa ya daina zuwa gidan.Abbu baki ya kasa rufuwa, mamaki yake ganin Al’amin, a nutse da shi ya sako ‘yar matarsa a gaba gwanin sha’awa, sai dai sai cika yake yi yana batsewa yana wani basarwa.Dan tun da suka gaisa da Abbu, bai sake cewa komai ba, jauhar ce take bashi amsa idan yayi magana.Rahila ma sai zuba take ta ce “Ikon Allah, anya ba a canzo wani Aminun ba, kun yi kyau abunku kun ƙara ƙiba, an ce kin yi rashin lafiya kwanaki, To na san dai ba zai wuce laulayi ba, Allah ya raba lafiya”Al’amin ya ce “Amin, tashi mu tafi rana tana yi” kawai ta girgiza kai jin Al’amin ya amsa, idan ma haka ne ai kamata yayi, yayi shiru kawai.Rahila ta sake cewa “To sai ayi ta kula da ita, ka san masu ciki sai ana lallaɓa su, ban da hantara da abun da zai ɓata mata rai, kuma ba zama zaka yi ba, ciki tun yana ƙarami ake fara sayayyar kayan jariri”.Jauhar ta ajiye food flask, da leda ta ce “Mama ga wannan, kwa yi buɗa baki, a saka mu a addu’a”Abbu ya ce “Masha Allah, addu’a kullum cikin yin ta ake, Allah ya yi albarka”Rahila ta ce “Iyee har da su suga da kayan marmari?” Ta buɗe fulas ta ce “Abbu kaza ce fa a ciki, ikon Allah sana’a ka samu ne haka? Ko kuma haryanzu miyagun ƙwayoyi ka ke sayarwa, gara mutum ya san halaccin abun da zai ci”.Al’amin ya kalli jauhar, irin kallon kin ga abun da nake gudu ko?.Ya ce “Ubana na zo gani, kuma banda ‘yar madara ta matsa, da sai dai na je ƙofar masallaci, idan ya fito na ganshi kamar yadda na saba, dan haka ba sai kin san sahihanci da halaccin cin sa ba, tun da bani da alaƙa da ke” ya tashi ya danƙi hannun jauhar a gaban su.Abbu ya ce “Aminullahi tsaya mana”ya tsaya cak yana huci, jauhar sai ƙoƙarin zame hannunta take yi daga nasa, saboda kunya.Abbu ya ce “Allah ya saka da alkhairi, ya yi albarka. ‘ya ta Allah ya saka miki da alkhairi, yayi muku albarka gaba ɗaya”Ta ce “Amin Abbu, a sha ruwa lafiya “A zatonta, zai ta yi mata masifa, sai dai ta ji bai ce mata komai ba, ya wuce da ita unguwar su, ya kaita har ƙofar gida.”Ki yi sauri ki fito mu tafi, mu koma gida”Ta ce “To*Ta sauka daga babur ɗin ta shiga gidan, suka gaggaisa, sai dai baba baya nan, ta ce “Dama ɗan abun sannu da shan ruwa na kawo masa, sauri nake yi na bar shi a waje, kar ya gaji da jirana”Anty Zakiyya ta ce “Lallai jauhar, shi mijin naki ya fi ƙarfin ya shigo ya gaida mu kenan?””A’a ba haka bane Anty, kin san ba ya jituwa da ‘yan unguwar nan, bana son wani abu ya faru ne”Mama ta ce “Haryanzu bai shiryun ba kenan? Sai labari muka ji wai ya fito ai, Jauhar wannan naman kajin, shi ya saya ko ke?”Ta ce “Shi ne”Suryaya ta ce “To a dai yi a hankali, Allah ya sa ba na sata bane ba”.Jauhar ta ce “Allah ya tsare shi, Al’amin ba ya sata”.Anty Zakiyya ta ce “Wato Jauhar ba zaki yi mana Allah ya sanya alkhairi ba ko, ko kishi ki ke yi?”Cikin rashin fahimta jauhar ta ce “Anty na me?””Alhaji mu’azzam ya dawo, tun da kin yi aure yanzu hafsa zai aura, ya bayar da miliyan biyu tayi lefe, dubu ɗari biyar kuma kuɗin aure!”

Ayshercool 08081012143.

Back to top button