Uncategorized

Zuciya da kwanji Book 1 Chapter 1

  ZUCIYA DA KWANJI BOOK 1_______1

Na Maimuna Idris Sani Beli

Kyakkyawar mace matuka gaya! Fara sol, mai kyakkyawan diri na matsakaicin jiki, tsarinta ya bayyana matsayin da kuma matakin da take kai na rayuwa, wato girman nauyin aljihunta, ko kuma na wanda ya dauki nauyinta. Da ganinta mace ce mai kasaita gaske, tare da dabi’ar son mulki da nuna ita wata ce. Ga ta kuma da karamin jiki, sai wannan kyan da yanayin shan kamshinta kan  sabbaba mata wani kwarjini, dake sa wa babba da yaro ke shakkarta, mace ko namiji duk wanda ya kalleta sai ta tsuma shi, a duk lokacin da mutum ya kalleta yakan ji kamar ita ta girmi kowa a idonsa, girma ba na shekaru ba, irin na fada a ji, domin dai shekarunta talatin da biyu ne aduniya. Tana zaune ne akan farar kujera karkashin bishiyar dorawar turawa a wani sashe na gidan zoo da ke kano, tare da wani mutum mai alamun hakuri da fara’a, dan kimanin shekaru hamsin. kallo daya zaka yi masa ka gane inda wannan kyakkyawar matar ta ci ta tada kai. Yadda wajen yake da alamun kadaici haka fuskokinsu ke bayyana damuwa da alamun kewa, shi ya sa wajen tsit yake sai kukan tsuntsaye iri iri, sannan akai akai mutumin kan dubi matar nan fuskarsa cike da alamun miliyoyin kauna wadda ta zarce misali, kamar jikinsa har bari yake, amma wannan matar ko a jikinta, tata fuskar babu abin da take bayyanawa sai gajiya da kuma gundura. Can ya nisa a tausashe cikin ladabi irin na kwararren masoyi ya ce. “Kar fa wannan ya bata ranki Fatima, na sanki da son sanya wa kai damuwa…… Kin sa…..” Sai ya yi shiru yana dubanta kamar zata yi magana, sai kuma ta hadiye abarta, ta kuma kawar da kai. 

     Ya jima yana kallonta, sai kuma ya sake duban agogon hannunsa, ya kara sauke ido a kanta, a ladabce kamar wata gyatumarsa, ya ce, “Ki yi hakuri kin ji Binta?” Nan ma ba ta tanka ba, ba ta Kuna dube shi ba, illa dan muskutawa da ta yi. Zai kara magana ke nan sai ya hango wani matashi yana nufo su, mai kimanin shekaru talatin da uku wankan tarwada mai matsakaicin tsawo da fadi, akwai alamun kan sharafinsa yake, ma’ana yana jerawa da zamaninsa. Yana sanye ne da dakakkiyar shadda ruwan shanshanbale(purple), dinkin boda da tajajjiyar sumarsa ta kara fito da kyawunsa. Shi ma yana da alamun fara’a, sai dai mai dakakkiyar fuska ne ta jarumai kuma irin wadanda kallonsu kawai ba zai sa ka iya yanke musu hukunci ba. Da barin jiki mutumin nan ya dubi Fatima, fuskarsa kamar gonar audiga ya ce, “Kwantar da hankalinki Binta, kin ganshi ya karaso”. 

  Ta dago ta yiwa matashin nan kallo daya, sannan ta kawar da kai gami da karamin tsaki, har ya karaso ba ta kuma sha’awar kallonsa ba. Tana jinsa suna gaisawa da mutumin, sannan ya juyo kanta da muryasa kamar wanda aka yiwa dole ya ce,

“Sunnun madam”

 Ta motsa baki, amma sai ta hadiye amsa sannun tasa ta hanyar kyabe baki da kawar da kai.

Sai  wannan mutumin ne ya wofintar da abin da ta yi da cewa. “Abdullahi har mun gaji da jiran ka san fa ina da sabgogin yi, ita kanta madam ba ta kaunar irin wannan jiran”.

 “A tausashe Abdullahi ya ce. “A yi min afuwa Alhaji, na kai daya daga cikin iyalina asibiti ne, saboda tana fama da ciwon ciki.

  “Allah ya sauwake”. Alhajin ya fada gami da sauke kallonsa kan fatima wadda ta mayar da idonta kallon wani sashen daban, kamar ba a gabanta suke ba, A tausashe ya ce. Fatima wannan shi ne Abdul da muke magana a kansa”. 

Ta juyo ta dubi Alh a kaikaice, sai dai ba ta tanka ba. Ya kara fadada fara’arsa yana dubanta, ya ce. “Ina fatan ya yi miki?” 

A lokacin ne ta kuma daga kai ta dubi Abdullahi wanda shi ma yake duban wani wajen daban tun shigowarsa kallo daya ya yi mata bai kara marmarin kallonta ba, ko yanzu da jikinsa ya ba shi tana kallonsa sai ya kara yin kicin kicin ya ci magani sosai. Ta kawar da kai daga dubansa cikin tabe baki, har da tsartar da yawu, ta ce.

 “Alh ya yi mana, tunda ba a kafata zan daura shi ba”. 

  Alh ya yi karamar dariya,sannan ya basar ta hanyar duban Abdullahi ya ce. “Abdullahi wannan ita ce Fatima, wadda na fara yi maka bayani rannan, matata ce, shekarun mu goma tare, muna son junanmu kwarai! Wata kaddara mai zafi ta gifta mana na yi mata saki UKU alokacin daya. Rayuwa ta yi wahala a gare mu, domin ba zamu iya rayuwa ba tare da juna ba. Ga shi kuma ba mu da damar kasancewa taren.

  A baya mun dan yi wasu yunkurin na yin auren kisan wuta don mu sami damar mayar da aurenmu, kawunta ya dago mu saboda yanayin wadanda muke gayyatowa suyi mana wannan aikin. Wannan karon sai muka zaboka bayan mun gamsu ka toshe waccan barakar da ta ke sa wa ana dago mu. A  yanzun ina mai gabatar da kai gare ta, shin ka amince zaka aure ta amma ka sake ta cikin wata daya? Ya kamata ka dauka mana wannan alkawarin. Ni kuma na yi alkwarin biyanka ladan kudin miliyon uku, ya ya ka gani?” Alh ya yi shiru yana dubansa, inda shi kuma ya muskuta cikin nuna tsananin girmamawa ya ce. “Kamar dai yarda na fada maka rannan,na amince da muradinka……”

   Fatima ta tare shi tana masa kallon goma ahu. “Ta ya ya zamu gaskata alkwarin ka alhalin yanzu ka gwada mana ba ka san darajar lokaci ba, ka shanya mu kawai kamar wasu kannan yara?” Abdullahi ya yi kasake cikin dakewa da shan kamshi, yana motsa bakinsa a hankali har ya bar abin da yake son fada ya bi ruwa, sai kawai ya bige da kallon Alh wanda yake kallonsu daya bayan daya. Tsarin nasu ya burge shi kamar halayyarsu daya don haka ba zasu taba jituwa a inuwa daya ba. Ya dubi fatima sannan ya kara duban Abdullahi,wanda tuni ya dauki kai, ya ce. “Ai ya wuce Binta ban zabo shi ba sai da na amince da shi. Dan manyan gida ne gidan da aka san kimar amana,kuma bai yi kankanci a ce shi kika aura ba yana da alkibla, yana da sana’a. Ba shi cikin shirgin sawa, duk wadannan makamai ne cikin cimma burinmu wanda za su yi tafiyar ruwa da kwakawar kawu.

    Ba ta ko motsa ba bare ta tanka ,shi ma Abdullahi sai ya ga ba shi da ta cewa. “To yanzu mene ne abin yi?

 Ko motsi Abdullahi bai yi ba, sai fatima ce ta dago ta harari Abdullahi,sannan ashagwabe ta ce. “Gaskiya wata daya ya yi min yawa Alh, don ko sati daya tamkar akan kaya zan yi shi…”

 Ya tare ta cikin tausasawa. “Na sani, amma babu wata mafita wadda ta fi wannan ita zata dauke idanun basaldawa…..” 

Yadda ta yi kicin kicin ya sa ya dakatar da maganarsa da murya nan shi, ya ce. “To yi shuru, Abdullahi ma haka.

Dukkansu sai numfarfasgin kawai suke, da alama kowa dacin rai na damunsa, sai kawai Alh ya zuba musu ido, a sanyaye ya dubi Fatima sannan ya juya ga Abdullahi a kausashe ya ce. “Wai me ye haka? Ba na son wannan cin maganin da kuke, kun san fa zaku yi ACTING ne sosai yadda da wahala a gane abin da ke binne, kun gane ko?

    Ko motsi fatima ba ta yi ba, sai ma kara hararar Abdullahi da ta kara yi, kai tsaye shi kuma ya yi murmushin da har kumatunsa suka lotsa, yana duban Alh ya ce. “Kar ka ji komai Alh, ai nan ba wajen da zamu yi acting din ba ne, shi yasa duk muke tsaye akan kafafunmu.

     Alh ya sauke ajiiyar zuciya, ya gyara zama ya ce. “Ai shi ke nan,zaka fara zuwa zance .ke ma Fatima ki karbi shi da fuska mai kyau yadda su kawu ba zasu dago ki ba ku yi acting sosai yadda za a zatar muku kaunar juna ya yi kamar zuwa biyu sannan ya tura magabatansa ayi maganar aure, idan an zo sa rana, kar a sa lokacin mai tsawo kamar sati biyu haka sai ta tare”. Ya saka hannu a aljihu ya ciro wasu mabudai samfura biyu,na mota da na kofa, sannan ya fito da rubutaccen cek ya hada ya mika wa Abdullahi yana cewa. “Daya makullin mota ne, ka zo office dina gobe ka dauka,ka fara amafanin da ita tun daga goben, don kawar da idon mutane.wannan mukullin gida ne, shi nake son ta tare a cikinsa tunda nasan ba ka da muhallin da zai dace da ita. Sannan wannan cek ne na kudin dubu dari bakwai ka fara hidimar auren da su dai dai matsayinka ka ji? Idan kana bukatar kari ka zo ka same ni, ladan aikinka kuma ranar da ka sallame ta,ba zaka bar gidan ba sai ta ba ka.kuma muna bukatar ka yi mata saki uku ne, ina fatan kana fahimta?”

 Fuskar Abdullahi ta nuna alamun zurfafa a tunanin,yana faman juya mukullan da cek din sai da Alh ta dure, sannan ya dube shi da kyau,ya ce. “Idan haka ne gaskiya akwai matsala”. Duk suka kara dubansa,har da fatima me shan kamshi,ya dan ja fasali tukunna ya ce. “Mahaifina yana da matukar dora ido akan ‘ya’yansa,abun ne mai wahalar gaske ya ganni da gidan da kuma sabuwar mota bai matse ni na fada masa inda na samo su ba. Kuma wannan dalilin ne da zai kafa min hujjar hana ni auren gaba daya. 

    Fuskar Alh ya bace ya ce. “Ayya! To ya ya za’ayi ke nan?” Abdullahi ya yi kasake sannan ya numfasa. “A bar maganar mota tunda ina da tawa, ko dai ta rainawar ce,maganar gida kuma idan zai samu tunda komai na maneji ne, me zai hana ta yi manejin a gidana? Gidan yana da yalwa dama sashen mata uku ne, sai nawa.yanzu haka matana biyu, kuma ina neman wani auren har an sa min rana,saura wata shida sai ta zauna a sashen amaryar bisa dole tunda ba daukar wani lokaci za’ayi ba, har an yi auren a gama kafin wancan auren ya zo”

     Duk suka yi shiru alamun shakku. Da kyar Alh ya nisa,ya ce. “Anya hakan zai yiwu Abdullahi? Ya ya za a yi ka hada fatima da wasu matan duk matsayinta? Idan a aurena ba ta san bakin cikin kishiya ba, ai bai kamata a naka ta sani ba….” 

     Abdullahi ya yi saurin tare shi. “To Alh ya ya zaa hada wannan auren da naka? Ai bai kamata matana su dame ta ba, tunda babu wani dalili da zai sa ta yi kishi da su….. Amma in ba haka ba….. Gaskiya ina gudun bacin ran mahaifina….”

     Ya mikawa Alh makullan yana mikewa. Alh na nacin kallon fuskar fatima wadda ta kara bata rai, ya ce. “To me yasa zaka dawo min da cek din?”        

     Abdullahi ya ce “Wai kafin ku yanke shawara”. 

     Da sauri Alh ya ce “A’a ka zauna mu yi komai yanzu mu gama, fatima kina jinmu fa, kina ganin zaki iya ace kin shiga cikin mata biyu,alhalin kin saba da mijinki ke kadai?” Ya karasa da zolaya.

     Ta amsa kai tsaye. “Ko mata goma ne a matsayin na ‘yar ci rani bai kamata su dame ni ba. Ni na fi so a fi jaddada maganar iyakar kwanakin da zan yi a gidan ya sallame ni, sannan ko da wasa ba na so ya rabi dakina da sunan mijina, ya yi harkarsa kawai na yi tawa,ranar alkwari ya miko min certificate kawai”

     Alhaji ya sauke ido akan Abdullahi, ya ce. “Ka ji muradinmu”. Babu alamun shakka Abdullahi ya ce. “Na amsa”. Yana rufe baki fatima da ke kallonsa,kai tsaye ta ce. “Ban ji ka ce ka dauki alkawarin ba, kuma da wacce alama zamu yarda zaka cika?” 

     Ya amsa cikin dakewa ba tare da ya dubeta ba. “Babu wanda zai iya

shaidar abin da zuciya ta boye sai wanda ya kage ta, sai ko in zuciyar ta dan yarjewa mutum ta hanyar bayyana alamu. Amma ku yi min hukunci da auren da na ce zan yi nan da wata shidda, Nasan kun sa so ba karya ba ne, tunda a cikin mayensa kuke, soyayyar da nake wa yarinyar ta kai mizanin da ba zan iya rasata, ta karamin dalili ba, wato aurenki”. 

     Karo na farko da suka dubi juna ita da Alhaji suka yi murmushi,ba tare da ta ware murmushinta ba ta dubi Abdullahi ta ce. “To in dai haka ne,kai dai ba ka san so ba, tunda ka dire mace biyu a gidanka ga ni ta uku zan shiga duk da in na kauce wata zata maye gurbina,na san kuma ba za a shekara ba, ba tare da ka cike gurbin ta 4 ba”. 

     Har yau bai juyo ya dube ta ba,sai dai shi ma fuskarsa da walwala ya amsa mata. “Ai babu wata me maye gurbinki,tunda naki wasa ne, ki kuma sa wa ranki,ina aure akai akai ne don ban dace da kawata ba,amma ita wannan ina jin a raina daga kanta zan kulle kofa, don zata iya amsa sunan mace hudu ma ba biyu ba”

     Ba tare da wani shakka ba fatima ta ce. “To Allah ya sa,don ni ban ga wani burgewa ba wajen tara mata da ya zame muku kamar wata gasa.

     Suna dariya ita da Alhaji shi kuma Abdullahi ya ki share maganarta, cikin karsashi ya ce, “Amin”.

     Alhaji ya magantu “Wai shekarunka nawa?” 

     Ya amsa masa. “On 22nd na wata mai kamawa zan cika shekara talatin da uku”.

     Cikin kada kai Alhaji ya ce “Ka ga ma ‘yan watanin ka ba wa fatima saboda haka ka bata girmanta kamar yadda zaka ba ni, ko babu wannan shirin ai ba sa’ar aurenka ba ce ko? Ko kuwa mutum na auren sa’arsa?”     

     Shiru Abdullahi ya yi, Alhaji ya rufe maganar da cewa “To don Allah ka zama yaron kirki, kar ka sake inji fati ta yi kuka da kai, ka lallabata don Allah ka ga marainiya ce ko a zato ba na son bacin ranta.

TUNA BAYA.

    Mahaifin fatima dukkansu ‘yan asalin karamar hukunmar gwarzo ne a cikin garin Gwarzo, mahifiyar fatima bafullatana ce gaba da baya kusan a wajenta ma ta gaji kashi 70% na kyawunta. A bangaren ginshirya da shan kamshi kuma sai ta gaji mahaifinta wanda ya kasance jinin sarauta. Kakan fatima wanda hakimi ne na wannan karamar hukuma, ‘ya’ya uku kacal ya mallaka, mahaifin fatima sai kannensa biyu, wato Prof. alkasim da karamar kanwarsu Dr. Maryam.

    Fatima ta taso ne marainiya gaba da baya sakamakon rasuwar mahaifanta duka biyun a ranar da za’a yi bikin cikar shekarunta uku a duniya. Daga nan ne rukonta ya dawo hannun kanin mahaifinta Prof. wanda a lokacin wataninsa uku kacal da aure. Kawu (Prof.) muntum ne mai tsantseni kwarai, kuma masanin ya kamata, sai kuma ya yi dacen mace ta gari kamar shi. Don haka har zuwa yau Fatima ba ta taba dan dana wani dacin da ya yi kama da maraici ba, sai ma da ta mallaki hankalinta sannan tasan cewa ba su suka haife ta ba. Gidan su gidan jama’a ne matuka, don karamcin ma’abotan gidan, don haka duk wanda zai taso a cikinsa sai ka tarar da shi wayayye ma’abocin iya mu’amala, sannan mara kyashi ko kadan, saboda sabo da jama’a”. Kawu na da ‘ya’ya shidda, babba cikinsu Safiyya wadda ta ke kamar sakuwa ga Fatima, tare suka yi fadi-tashin kurunciya, sai maza biyu suka biyo baya, Najib da Abdullahi, sai kuma Nasiba sannan auta Khalid. Don haka duk cikin manyan ‘ya’yansa Fatima yake kallo sannan kuma bai taba bambantata daga cikin ‘ya’yansa ba. Ya bata ilimi mai kyau kamar su, sannan ya jajirce cikin tarbiyyarta iyakar kokarinsa, duk da dai gatan da yake mata saboda maraicinta ya ba ta damar sangarta ta zama wata me murdadden ra’ayi wadda ake shan wahalar canjawa manufa ko da karmatacciya ce.

      Tun fatima na karamarta kowa ya dubeta yasan an sami kyakkyawar mace mai sa numfashin maza sassarfa, koda  kyawun nata ya  hade da ilimi ga kuma kudin, sai ta zama wata zara a cikin mata. Ta yi matukar farin jinin a wajen maza, har ma da matan da Allah ya zare wa kyashi da hassada, don ma kawai miskilancinta. Da wahalar gaske fatima ta fita wani masoyi bai biyo bayanta ba.

     Shekarar da ta kammala sakandire, kawu ya fara koyarwa a jami’ar bayero, sai faduwa ta zo daidai da zama domin a shekarar ta fara nata karatun a nan inda ta karanta (biochemistry) suka tattara suka bar tarauni zuwa gidajen malamai na nan jami’ar. Dai-dai wannan lokacin Alhaji sulaiman karansa ya kai tsaiko bayan doguwar gwagwarmaya wadda kokawar tarar da buri ya haifa. Nasa mahaifin karamin ma’aikacin gwamnati ne, bayan ya yaki jahilci, sai dai mai jar zuciya ne, wanda ko za a kwanta ba a ci ba, ya laminta ya gabatar da bukatar karatun sulaiman sai kuma ya yi dace mahaifiyarsa ta zama mai tawakkali da goyon baya, har ya kai ga hada digiri dinsa a (business administration). 

      Tun tasowar Alhaji mutum ne mai manyan burika, sai dai yana da juriya da jarumtar shanye wahalhalu wajen cika su. Bayan kammala karatunsa, ya yi zaman fiye da shekaru biyu yana neman aiki kasancewar bai sami wanda yake buri ba. A karshe ma kawai sai ya koma makaranta ya yi masters dinsa akan Economic, shekaru biyu ya kuma dawowa ya zauna jiran tsammani, sai ma aikin ya fi tsauri a wannan lokacin, saboda karatunsa ya yi zurfi, guraben da zai shiga sun yi karanci. Shekara daya da wannan karatun ne mahaifin wani abokinsa ya hada shi da wani kwara, wanda harkar kasuwanci ta kawo Nigeria, inda suka fara gwada shi kan shigo da wasu injina, kwazonsa da kwarewarsa akan wannan harkar ya sanya ba a shekara ba sai da suka bude wani katafaren kamfani suka dora shi akai.

      Labarin ya canja, Alhaji Sulaiman ya fara cimma wasu daga cikin manyan burinkan da suke binne a ransa, kamar mallakar manyan motoci, kama kudi, da kosassun gidajen da suka yi kama da aljannar duniya, daga nan kuma ya fara hangen kyakkyawar matar da zata dace da shi, don tun yana sakandire ya yiwa kansa alkawarin ba zai yi aure ba sai ya mallaki gida da mota, sannan ya auri kyakkyawar mace…

.

 ********************************* 

Mahaifin Abdullahi wani shahararren malamin ne, kuma alkali ne, mai suna Ustaz Ukashatu Mohammad, mutum mai adalci da yawan dattako, yana da tarin ‘ya’ya maza shidda, mata ashirin da uku, wadanda matansa hudu suka haifa masa, duk da yanzu saura uku, don mahaifiyar Abdullahi Allah ya yi mata rasuwa shekaru biyu da suka wuce. Abdullahi ne dansa na goma, kuma auta cikin mazan nan, kuma a cikin mazan nan shi kadai ne bai gado gida ba, wato karanta shari’a ko koyarwa, sai ya karanci mass communication, amma sai ya buge da aiki a (ministry of rural & community development) ya kai matakin albashi na goma. Abdullahi mutum ne mai hikima da dankaren wayo, hangen nesansa na taimakonsa kwarai a rayuwarsa wajen mallaka masa dukkan burikansa. Jarumi ne kwarai wanda ba’a taba gane lagonsa, ba ya fushi a inda ya fahimci fushi nasa ba shi da ma’ana, sannan ba ya dariya a inda ba a san darajarta ba. Don haka kankantarsa ta tsaya a jikinsa ne kawai, amma zuciyarsa dattijuwa ce, azancinsa kuma tsoho ne mai rankarfe. Matarsa ta fari sadiya, wadda ya aura shekarar da ya kammala karatu ko fara aiki bai yi ba, makociyarsu ce wadda soyayya mai zafi ta shiga tsakaninsu kafin auren, wadda kuma ita ta taimaka wajen amincewar mahaifinsa akan auren sadiyar da shi, kasancewar sadiya ba ta fito gidan tarbiyar da ta gamsar da malam ba, sai dai dole kunyar idon mahaifinta tasa ya amince wanda takanas ya ishe malam din ya ce ya bai wa Abdullahi auren sadiya. Sai dai kash! aurenta Sadiya da Abdullahi ya dinga haifar da matsaloli, matsakaita da kanana, wasu kishiyoyin juna, sadiya mafadaciyar mace mai yawan kuncin zuciya da tsarguwa. Ga kuma Abdullahi miskilin mutum kuma mara daukar raini, sannan mara daukar korafi da muhimmanci, wadannan dalilin suka sa zuciyoyinsu suka canja daga masoya juna zuwa wani abu daban. Kullum su kenan cikin hayaniya, Sadiya ta dauki kafa ta yi yaji, shi kuma ya yi zuciya ya share ta har sai manya sun shigo. Da abin ya ishi malam sai kawai ya nemar wa Abdullahi wani auren. Hindatu kenan matar Abdullahi ta biyu, wadda ya aura ba abisa doron so ba, sai dai ta sami filin karamci a zuciyarsa saboda hakurinta da saukakawa kai buri, tana nuna masa wadatarta akan iyakar soyayyarsa da adalcin da ya yi mata duk da kuwa ba ya iya boye bambancin da zuciyarsa ta ke nunawa tsakaninta da sadiya wadda za a iya kira mowarsa duk kuwa da tambelenta. Shekaru hudu kenan da auren fari, kuma shekarun biyu da auren Hindatu, amma cikinsu babu wadda ta taba ko batan wata, wannan ma sai ya bi layi cikin matsalolin da suka dami duniyar Abdullahi.

****************************************** 

Alhaji sulaiman abokin ne na kud-da-kud ga yayan Abdullahi, mai suna Abdulawahab, sun yi karatun sakandire tare, kuma daga nan abotarsu ta samo asali. Ba za a ce Abdullahi ya yi masa farin sani ba, kasancewar lokacin da ya yi wayo sosai, sabgogin sun yiwa Alhaji Sulaiman yawa, ma’ana ya yi wuyar gani, amma ya waye da Alhaji lokacin da ya kawo wa yayansa xiyara, shi kuma a ranar za a daura masa auren mata ta biyu. Abdullahi na tare da yayan nasa yana sauraron hirarsu. Abdulwahab yana zolayar Alhaji da cewa “Sulaiman burinka fa kamar ya wuce mallakar makudan kudi, gidaje da motocin hawa kafin ka ajiye iyali, me kake yiwa kanka kawa ne?”

Alhaji na dariya ya ce, “Wallahi har yau na kasa samun matar da zata da ce da gida na, watanin baya na so auren wata balarabiya wani abokina ya dinga kwabata, wai tatike maza suke su tsere, dole na hakura tunda an ce mutum ba ya kin ta mutane”.

 Abdulwahab ya ce, “Haka ne, amma ya kamata ka yi taka tsantsan a cikin sha’anin mata, sun fi kowacce kawa hatsari, musamman kyawawa don yawancin su nagartasu ba ta kai masu karamincin kyau ba, sai ka zauna da matarka mai karancin kyau ka dinga sarrafa abarka son ranka, amma awajen kyakkwayawar mace ka yi kadan, komai kudinka da mulkinka, wuyarta ta kalli kanta a madubi sai ta ji ta girme idonka, kuma ko yau kuka rabu zata sami wanda ya fi ka, don haka ba ka isa ka sa ba, balle ka hana”. 

Kamar a sanyaye Alhaji Sulaiman yace “To, Allah ya zaba mana na gari.”

 

Alh sulaiman ya hadu da fatima ne ranar bikin kammala karatunta, gaba daya ya sasusuce, don fatima ta kusan zarce tanadin da yake wa kansa game da mace. Sunanta ya nuna masa daga inda ta fito, sai ta kwanar masa gidan sauki, domin kawu malaminsa ne tun a sakandire, sannan ya koyar da shi a digiri dinsa na farko, sun shaku matuka suna ganin mutumcin juna kasancewar kawu mai son jarumin namiji mai hazaka da juriyar cimma burin abin da ya sa a gaba. To Allah ya horewa sulaiman wannan, mutum ne mai kaifin kwakwalwa, wanda duk abin da aka zuba masa sai ya kwashe, shi yasa yake ji da shi tun a sakandire. Kwana uku da ganinta ya wanke kafa ya tafi gidan prof. bayan ya nemi izininsa a waya. Prof. ya karbe shi cikin mutumci kafin ya shiga rudanin abin da ya zo masa da shi, wato neman auren fatima. 

“Ko akwai matsala ne?” Alhaji ya tambaya saboda ganin yadda kawu ya shiga damuwa.

 Prof. ya sauke numfashi ya ce, “Sulaiman Fatima ta dade tana dauko min magana wallahi, manyan mutanen da nake jin kunya ba zan iya kirga maka wadanda suka zo da kokonbararsu gare ni na son auren fatima ba. Amma sai ta watsa mana kasa a ido ni da su, na rasa inda yarinyar nan tasa gaba, kowa ya zo ba ta so. Abayanta fa kanwarta ta biyu ake shirin aurarwa, amma ita ko a jikinta….maraicinta ke sani tausayamata, amma tabbas da ni na haifi Fatima da na tilasta mata aurenka”. 

Wannan togaciyar ba ta sa sulaiman ya dauke kafa ba, sai ya ci gaba da kawo gaisuwa da rokon iri har aka kai matakin da kawu ya ba shi damar bayyana kansa ga fatima. Amma kash! Sai aka yi rashi sa’a cikin masu son ta ba ta taba tsanar wani sama da Alh sulaiman ba, ba ta kaunarsa ko kadan kuma ba ta iya boyewa kowa ma ya sani.

Shekarunsu biyu a haka, Fatima ta kammala service, ta kuma nemi izinin kawu na neman aiki. A nan ne kawu ya yi ta maza ya ce sam bai san wannan zance ba, ya ma ba ta wata guda ta fito da miji, idan ba haka ba sai dai ta ji taron daurin aureta. Fatima ta dauke maganar kawu wasa, har ta bari watan ya share a wasa, sai rana tsaka ta ga taron jama’a a gidansu, labarin ya zo mata an daura aurenta da Alhaji Sulaiman.

Zamu dakata a nan sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Ga masu bukatar Audio kuma za su iya saurara ta hanyar taɓa wannan hoton dake ƙasa. Mun gode da ziyarar Aihausanovels.

Back to top button