Uncategorized

Yadda za ki gyara fuskarki kuma fatarki ta yi haske

Yadda za ki gyara fatarki ta dinga sheƙi da kyalli

Hakika mata da yawa na kashe makudan kuɗaɗen wajen fafutukar ganin fatar su tana sheƙi da kyalkyali. Da yawa mata suna faɗawa tasku sakamakon amfani da mayukan da suke da chemicals, wanda a garin kwalliya ta biya kudin sabulu, sai a zo ana da-na-sani. Wannan dalili ne ya sa na kawo maku hanyoyi guda shida yadda za ki lura da fatarki ba tare da kin faɗa wancan tarkon ba. Don haka ga su kamar haka:

1. Ki samu cucumba sai ki yayyankata, ki niƙa ta, sannan ki ajiye ta gefe ɗaya. Ki haɗa ruwan rose da ruwan lemun tsami. Bayan nan kin kammala sai ki kaɗe su da cucumba ɗin da kika markade, ki gauraye sosai. Bayan kin cakuɗe sai ki shafa a fuskarki da sauran fatar jikinki, sannan ki kwanta har zuwa wayewar gari. A lokacin da ki ka zo wankewa, sai ki samu ruwan dumi ki wanke fuskar taki. Hakan zai ƙara wa fatarki lafiya da kuma sheƙi.

2. Hanya ta biyu ki samu madarar shanu mai kyau wacce ba a dafa ba, sai ki samu gishiri ki haɗa da cokali biyu na ruwan lemun tsami sannan ki gauraya sosai. Bayan kin hade su sai ki samu auduga ko tsumma mai kyau ki dinga dangwalowa kina gogawa a jikinki ko kuma fuskarki. Daga ƙarshe shima sai ki wanke fuskar ki da ruwa mai dumi. Hakan zai cire maki dukkan wani dattin fuska da ya maƙale ma ki a ƙofofin fatarki.

3. Hanya ta Uku ita ce, ana gauraya ruwan Rose da kuma Ruwan lemun tsami guri ɗaya sannan a shafa a fuska ko jiki. Yin haka na cire tabo dake ɓata fuska, sannan yana sa laushin fata da danshi.

4. A samu lemun zaƙi sai a yayyankashi, daga nan sai a markada. Bayana an kammala sai a shafa a fuska ko jiki. Shima yana sanya laushin fata.

5. Hanya ta Biyar a samu karas a markade shi, daga nan sai a shafa a fuska ko jiki. Bayan awa kamar biyu sai ki wanke da ruwa mai dumi. Yin wannan yana saka jikin mace ya riƙa haske da kuma daukar hankalin duk wanda ya kalle ki.

6. Hanya ta shida kuma ta ƙarshe ita ce, ki samu kurkum sai ki daka shi, ki haɗa da dakakkiyar alkama, sannan ki haɗa da man zaitun. Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa biyu zuwa uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwan dumi. Hakan na cire kwayoyin cuta da ke maƙale a ƙofofin fata.

Allah Ya sa a dace idan kaji dadin wannan muƙala daure ka yi sharing domin yan uwa su ƙaru

Back to top button