Uncategorized

Maciji Ne Page 71-72 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Download>>> Maraicin Nawaff Complete Document

Free book 

Page 71/72

_______________Cikin kuka da rawar murya ,fattu ta fara magana “wa…ce…ce .ma…haifi…….yata?kuma ina ne take ?sannna me ya faru da Hamma na bayan rasuwar momma?”ta fada cikin kuka mai ban tausayi.

Saida Nanny ta share hawayen idanunta kafin taci gaba da fadin” lokacin da labarin hadarin nan ya iske mu,mun shiga tashin hankali bana wasa ba,dan kuwa nan take mai martaba ya yanke jiki ya fadi asume,gaba É—aya faÉ—a ta rikice da kuka da alhinin rashin mutuniyar kirki kamar Momma, wacce ke son talakawa da taimakonsu.

Lokacin da Adeeb suka dawo daga makaranta,ya ji labarin mutuwar Mommansa da kannansa,shima sumansa uku,saida gyar aka samo kansa,tun daga wannan lokacin Adeeb ya kara komawa shiru shiru,bashi da aiki sai tunani haka zaki ganshi zaune shi kadai yayi tagumi yana zubda hawaye,saida aka tashi tsaye akansa da addu’oi kafin ya dan warware.

Mai martaba kuwa,ciwon zuciya ne ya kamashi, saboda tsabar damuwa da tunani.

Yana matukar kaunar Momma,Dan macece mai hakuri da shiga rai.

Tana faranta masa rai,duk abinda yace tayi bata ko musu akan umarninsa.

Bayan sadakar bakwai ne ,aka fara bincike akan abinda ya sami motar tunda  kai tsaye motar ta kama da wuta, kai tsaye aka gano bomb aka sanyawa motar.dan haka wannan hadimin mai kula da harkar motoci shi aka fara kamawa.

Anyi -anyi ya fadi abinda yayiwa motar amma yaƙi,shidai yace tabbas bomb ɗin ne ajikin motar,saidai idan ya fadi wadanda suka sashi,to zasu kasheshi ne.

Dukan tsiya akayi masa tare da kulleshi akurkuku.

Cikin dare muka shirya zuwa gareshi,dan ya faÉ—a mana wadanda suka sa sashi,akan idan ya faÉ—a zamu sakeshi ya gudu.

Amma saidai me?lokacin da mukaje, tuni Ammi ta riga mu zuwa,tana tsaye ita da wani mutum wanda ya nannaÉ—e fuskarsa da bakin gyalle.ta yadda ba wanda zai gane fuskarsa.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

“Wato so kake ka tona mana asiri ko?lallai kayi babban kuskure,dama ko kafada ko karka faÉ—a dole ne ka baÆ™unci lahira, tunda har kashigo hannu, kuma kasanar  dasu da gaske bomb É—inne ajikin motar,to watarana idan kaji azaba zaka sanar dasu mune muka saka ka sanya bomb din Dan haka yau zaka bi su Nazli kaima”Ammi ta fada tana mai dagowa daga sunkuyon da tayi tana yiwa mutumin magana.

“Kuyi min rai, ranki ya dade,wllh bazan ce kune kuka sani na aikata wannan aikin ba,dan Allah karki kasheni” mutumin ya faÉ—a galabaice dan yaci duka dazu.

“Kai!!! sakaran bawa, rufe mana baki, mu zakayiwa magiya mu gyaleka?wllh baka isaba,dole ka mutu dama baka da wani amfani agaremu, tunda kasan sirrinmu dole ka mutu”yana gama faÉ—in haka ya shaÆ™e bawan nan ,tun yana turje turje har ya daina alamun rai yayi halinsa.

Gaba dayanmu dagani har Amma kuka muke jikinsu na rawa,tsabar tsoro da razani.wanene wannan wanda ke taimakawa Ammi wajen aikata ta addancinta?ta yaya zamu gane shi ?shine abinda ke ta yawo cikin kwakwalwarmu.amma bamu da amsa. Ganin yadda amma ke kuka kamar ranta zai fice ,gashi jikinta sai rawa yake,yasa nayi saurin janyeta dan barin gurin.

Saidai agarin guduwa muka bigi wani bokiti ya fadi kasa yayi kara sosai.wanda ya jawo hankali su Ammi.

Gudu muka farayi tun karfinmu, dan kuwa akwai tazara sosai tsakanin cikin faÉ—a da kuma sijin É—in.

Suma basu fasa ba kuwa suka biyo mu.

Ganin zasu cimmana yasa Amma ta ce in buya,karsu ganni, ita zata tsaya ayi wacce za’a .

Dan Ni zasu iya kasheni nan take ,amma ita tasan yadda zatayi.

Haka na buya jikin wasu bishiyu.ta yadda bazasu ganni ba,amma Ni ina hango su dajin duk abinda suke fadi.

Koda suka cimma Amma tana zaune tana numfarfashi, tsayawa sukayi akanta suna kare mata kallo.

Ammi ce cikin É“aci rai tace “dama nayi tsammanin kece,dan kuwa nasan ba wani dan kasadar da zaiyi yunkurin bin bayana É—an  ji da ganin sirrina.to kingani, kuma kinji,hankalinki ya kwanta,amma wllh idan naji wata magana akan abinda kika gani na rantse da Allah saina kashe danki da adeeb,kisa mafi muni,kuma na lakamiki kisan, nace ke kika kashesu, kuma kinsan zan iya.

abinda yasa bazan kashe kiba yanzu, ina son kiga yadda zan lalata rayuwar yaranku ,insanya kiyayya atsakaninsu,ta yadda wataran daya shi zai zamo ajalin daya.

Kuma kinsan menene ke nake so kizabi wanda zai zamo ajalin wani acikinsu”Amma ta kare maganarta tana dariya da kallon Amma.

Download>>> Bakar Inuwa Complete Document

Kuka kawai Amma keyi, tana jinjina rashin imani irin na Ammi,mace kamar kafura?sam ba Allah cikin ranta.Amma na kuka take rokon Ammi akan ta gyale musu yara ,taji tsoron Allah,duk abinda take yana kallonta.Amma cikin rashin imani Ammi ke cewa “shikenan Ni zan zaba da kaina,nasan kina son danki,dan haka zan miki adalci yazamo shine zai kashe Adeeb “ta fada tana wani ware hannu da daga gira.

Cikin sauri Amma tace “a’a karki kashe Adeeb,gara Rashad ya mutu amma dan Allah karki cutar da Adeeb Maraya ne,zuciyarsa akarye take karki illatashi na roÆ™eki”Amma ta faÉ—a cikin kuka.

“Wow zabi mai kyau,kin zabi dan kishiya akan danÆ™i ko?lallai kin ciki shashasha,shikenan duk abinda zanyi akan su, naki idone ,daidai da rana daya kika yi min wata magana saina kashe Adeeb kinsan banda asara,bansan ciwon makida ba”tana gama faÉ—in haka ta karasa kusa da wannan mutum da suke tare,wanda dama yana tsaye dan nesa dasu yana kallon hanya.

Saida suka bacewa ganinmu sannan na ƙaraso gurin amma,wacce ke kuka sosai.haka na kamata muka koma cikin fada,zuciyoyinmu sam ba dadi.

Tun daga wannan lokacin Adeeb ya daina yiwa amma magana ,sai harara da bakaken maganganu,masu nuni da cewar  yana zargin tana da hannu wajen kashe Momma.kuma nasan duk sharrin Ammi ne.kuma 

Daidai da rana daya Amma bata taɓa kula Adeeb ba saidai tayi ta kuka.

Adaidai lokacin ne kuma suka tafi Singapore karatu.inda Adeeb yayi karatu bangaren likitanci,tareeÆ™ yayi karatun sa na koyon aikin jirgi,shikuma Rashad injiniya ne.

Bayan dawowarsa daga karatune kuma babban tashin hankali ya samemu, na rasa Adeeb da akayi sama ko kasa, kwanansu uku da dawowa daga Singapore akawayi gari ba Adeeb ba labarinsa.duk inda ya kamata aje nemansa anje amma babushi,lokacin kuma da ya dawo  daga Singapore,yana da tarin dukiya wacce shi kansa baisan adadinta.dan dan kasuwane mai neman na kasan,bai damu da matsayi ko mulkin gidansu ba ,yana da kamfanoni da dama akasashe da yawa,ciki harda nigeria.hakan yasa Adeeb ya iya Yaren Hausa sosai,dan darasi yake dauka na musamman akan bangaren.

Dan haka lokacin da aka rasa Adeeb,tareeÆ™ shine yaci gaba da kula da duk wasu al’amura na  dukiyar Adeeb .har Allah yayi dawowarsa ta silarki,

Ashe kema rabon ki sadu danaki iyayen ne,kuma ba kowa bace mahaifiyarki, face sarauniya suhaimat”

Download>>> Captain Ahmad Junaid Complete Document

Baki buÉ—e fattu ke kallon Nanny ,Tana jinjina kai   cike da jinjinawa Æ™udirar Ubangiji,yanzu dama innar yan biyu itace mahaifiyarta? ashe shakuwar da sukayi ta lokaci É—aya ba banza ba?waÉ—an kyawawan yaran kannantane?wayyo Allah na gode maka Allah mai yadda yaso ga bawansa.

Allah Sarki hammana yaga rayuwa,ya hadu da ƙaidin matar uba.wacce yakewa kallon muguwa itace masoyiyarsa. Ita kuma wacce ya dauka uwa itace ke son ganin bayansa.lallai yazama dole In fahimtar da hammana.

Cikin kuka da sarkewar murya fattu tace “amma waye yayiwa Hamma asiri ya zama maciji?

Ajiyar zuciya Amma tayi  ta fara magana akaron farko,tun zamansu aÉ—akin, tace “wannan ne har yanzu muke son sani,dan bamu da tabbacin Ammi ita tayi masa asirin, saidai muna zargin wannan mutumin da muka kasa sanin ko waye yana da hannu akan al’amarin”Amma ta faÉ—a tana share hawaye.

Hannunta fattu ta kama cikin kuka,tace “lallai Amma kincika mutum mai halacci, kin sadaukar da rayuwar danki,dan ki ceci dan kishiya,nayi miki alkawarin in Sha Allah komai zai dai daita. Hamma zai dawo gareki matsayin uwa da data,sannan rashad zai zamo abin alfahari gareki.

Sai yanzu na gane wannan abinda ya faru dani itace ta shirya komai,dan kuwa ita ta kaini bangaren da kanta,kuma ta kulle Æ™ofofin, sannan ita ta dauke sarkata wacce baffana yace itace shaidar da iyayena zasu gane Ni da ita.”

“Na sani Æ´ata,nasan itace ta shirya komai, sannan tun ganin farko da nayi miki nake ayyana ke yar sarauniya suhaimat ce ,dan kuwa akwai kamar ta atare dake .ina fatan Allah ya bamu sa’a akan abinda muke shirin aikatawa na alkairi “cewar amma.

“Nanny kema kiyi haÆ™uri komai zai daidaita in Sha Allah”fattu ta faÉ—a tana rungume nanny cikin kuka.

Kukan nanny ma keyi,tace “Allah ya amince Æ´ata.

Kallon tareeÆ™ tayi tace” Hamma tareeÆ™ kayi hakuri  in Sha Allah abokinka ,kuma dan uwanka,zai dawo gareka”jinjina kai yayi tare da saurin share hawayen daya gangaro masa,yana murmushi.

“Amma kibi komai ahankali yata,hammanki ya aminta da Ammi sosai ,ta yadda baya ganin laifin ta ko kaÉ—an”amma ta faÉ—a tana shafa kan fattu.

Jinjina kai fattu tayi tace “In Sha Allah Amma zan kula”

Adeeb  kuwa,gaba É—aya ya duba ko ina baiga fattu ba ,hankalinsa ya tashi sosai,ina kuma taje?ko wani abune ya faru da ita?”ya Salam”ya faÉ—a yana mai fitowa daga part É—in nashi cikin sauri. Kicibis sukayi da fattu tana shirin komawa bangaren nashi,dan Nanny ce tace ta koma kar Adeeb ya ganta anan yayi wani tunanin,

Kallonta Adeeb yayi idanunta sunyi mugun jaaa, cikin hanzari ya kamo kafaÉ—unta yana girgiza kai,gabanshi na faduwa”me yasameki? Wani ne yayi miki wani abu? Ko Rashad ne ?”ya faÉ—a cikin ruÉ—u yana duba jikinta.

Download>>> Tubali Book 1 Complete Document

Ita kuwa fattu kallonsa kawai take cikin tausayawa,yana cikin matsala babba,amma shi Sam baigani,zuciyarsa da idanunsa sun rufe,ya rike azzulamar uwa matsayin mai kaunarsa.jikinsa ta fada tare da sakin wani sabon kukan mai tsuma zuciya.

Hankalin Adeeb gaba É—aya ya tashi,jikinsa har rawa yake ,tana rungume ajikinsa ya bude part dinsa suka shige ciki,sai kuka fattu keyi harda shashsheka.

Kai tsaye  cikin daki ya wuce da fattu,bakin gado ya samu ya zauna tare da rungumeta ajikinsa ,yana jin damuwarsa na kara yawaita,zuciyarsa kamar zata fashe .

“Am sorry Hulwa ki sanar dani abinda ke damunki zuciyata na  min zafi,bazan iya jurar ganinki cikin damuwa hakaba “Adeeb ya faÉ—a kamar zaiyi kukan shima.

Fattu dai taki cewa komai sai kuka take tare da kara kankameshi.ganin irin kukan da takeyi  ne ,kuma baisan me zai mata tayi shiru ba ,ya sanya Adeeb É—ago kanta,ba tare da bata lokaciba kawai ya haÉ—e bakinsu guri É—aya.É—iff kukan fattu ya dauke,sai ajiyar zuciyarsu kake ji,cikin Æ™ankanin lokaci suka lula wata duniyar ,kasancewar Adeeb yana cikin damuwa da rashin nutsuwa,hakan ya kara ingiza shi cikin tsantsar bukatuwa da son kasancewa da fattu.

Ita kuwa fattu,tsabar tausayinsa da tashin hankali,yasa ta sakarmasa jikinta yake sarrafa ta yadda yaso.

Gaba ɗaya sun fice daga hayyacinsu,tun abu yana karami harya girmama, dan takai ga Adeeb ya raba su da kayan jikinsu banda rawa ba abinda jikinsa keyi,ita kuwa sai wani ƙara rukunkumeshi take tare da kiran sunansa cikin wata irin murya.

“Hamma ka bari ,Hamma! hammana!!kawai take iya fadi tana kara shigewa jikinsa.

Cikin murya mai cike da tsantsar bukatuwa da ficewar hankali Adeeb yace”h….uul…wa ki….n.amin..ce…dani…..matsayin ……. Abo…kin rayuwa?

Kin amince na kusanceki……..

Danƙari!!! masu karatu ya kenan?Hulwa kuwa zata amince ?

Me zai biyo baya ?

Muje zuwa Mrs babi ce 💘💘💘

Share and comment fisabilillah.

Download>>> Wata Rayuwar Complete Document

More comment 

More typing.

Back to top button