Uncategorized

Fil Hubb Complete Hausa Novel

FIL HUBB Complete Hausa Novel Written By Billy S. Fari

Posted by Ai Hausa Novel
Price ₦500
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 26 Dec, 2022
Upload Time 8:29 pm
Hits 218 Views
Author

Writer Group

Novel Genre

Comment No Comments

      Tunda ta hangosa gabanta ya yanke ya yi wata irin muguwar faɗuwa tayi saurin sadda kanta ƙasa tana jin ƙafafuwanta na sassarƙe mata waje ɗaya, ga wani irin nauyi da suka yi mata da take ganin daƙyar idan zasu iya ci gaba da ɗaukarta balle har su ƙarasa da ita inda ta nufa, yaushe ya Hisham ya dawo kuma? Ta tambayi kanta cikin zuciya tana ji tamkar ta fashe da kuka, iya adadin matsowar da takeyi a kusa dashi iya adadin bugawar da zuciyarta ke ƙarayi, ALLAH ma ya sani bata son ganin wannan bawan ALLAHn don ita kaɗai tasan irin yanayin tsoron da take tsintar kanta aciki, musamman yanda yake yimata wani irin kallo akoda yaushe idan suka haɗa idanuwa, sai taji kamar ta nitse cikin ƙasa saboda tsananin tsoro da tsabar firgita, jikkar littafanta na islamiya ta saka akan ƙirjinta ta rungume ko zata samu ƙwarin guiwar iya ci gaba da tafiya har ta ƙaraso ta gabansa zata wuce, da sauri ta rintse idanuwa sosai tana sake rumƙe littafan dake rungume a ƙirjinta saboda yanda zuciyarta ke halbawa kamar zata fito tayi saurin sinne kanta ƙasa, wata uwar tsawa taji ya daka mata haɗe da cewa “Wai ke wace irin baƙauyar yarinya ce? Ina kika taɓa ganin inda ake tafiya da idanuwa arufe ɓacin mutum na gani in ba sakalci ba?” Ba tare data kulasa ba ta wuce cike da tsoro tana sake ɗaga ƙafafuwan ta da sauri da sauri har lokacin idanuwanta na arufe, ai kuwa bata ankara ba taji ta bugi wata bishiyar icce dake gaban ƙofar gidan nasu, wata irin ƙara ta saki haɗe dayin baya zata faɗi ƙasa saboda wasu irin taurarin azaba data gani sun mamaye mata gaba, jin tayi anyi saurin tare ta tare da riƙota kafin takai ƙasa, wanda hakan ya sa tayi saurin buɗe idanuwa tare da juyowa, karaf idanuwanta suka sarƙe da nashi yana dalla mata wata irin hararar da ta sata saurin maida idanuwan ta rufe haɗe da ƙoƙarin zare jikinta daga riƙon daya yimata jikinta na rawa saboda tashin hankali, dama abunda take gudu kenan kuma gashi ya faru, ta faɗa cikin zuciyarta tare da sauko da hawayen da tun ɗazu suka cika mata idanuwa, ƙin sakinta ya yi ganin yanda take kokuwar ƙwace jikinta har lokacin idanuwanta na arufe tare da ƙarewa kyakkyawar fuskar tata kallo na tsawon sakanni uku ba tare daya damu da mutanen dake wucewa wajen dake kallonsu ba, sai daya rabar data ɗan saki jiki ganin yaƙi cikata sannan ya saketa ta faɗi ƙasa timm…tare da juyawa ya yi tafiyarsa ya barta wajen ƙasa a yashe, cike da jin zafin faɗuwar da kuma gigicewa ta miƙe ta nufi cikin gidan nasu tana maka masa ALLAH ya isa a cikin zuciya, tana ɗaga ƙafarta don ta tsallake kwalbatin dake bakin ƙofar shiga gidan nasu taji tsumbul ƙafarta ta zame ta faɗa ciki, wata irin ƙara ta sake saki da ƙarfi data sashi saurin juyowa daga can cikin gungun abokanansa da yake zaune haɗe da tasowa ya nufo wajen, a hasale ya fisgota daga cikin kwalbatin yana watsa mata wani irin mugun kallo kafin yace.

“kin gani ko? Abunda nake faɗa maki kenan amma bakya fahimta, ALLAH ya ƙara maki tunda kunnen ƙashi ne dake”. ya ƙare maganar cikin jin haushi yana kallon ƙafar tata da har ta ɗan gurje jini ya soma fita, runtse idanuwansa ya yi ya kauda kansa gefe haɗe da cigaba da cewa “Ai shikenan sai ki buɗe idanuwan yanzu ki tashi ki shiga ciki tunda kinci riba, in yaso idan Mahmah ta tambayeki sai ki faɗa mata cewa garin kallon samarin waje kika faɗa cikin kwalbati”. fuskarta shaɓe-shaɓe da ƙwalla take sauraren faɗan nasa cike da jin haushi tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa tashi, komawa tayi ta zauna ƙasa tare da fashewa da kuka ta ce “wayyo Abbu..” kafin ta ƙara sa ya ɗaga hannu kamar zai daketa cike da takaicin jin taɓarar da take ƙoƙarin fara yiwa mutane data saba, abunda ya tsana kenan dake haɗa shi da ita akoda yaushe,”ki rufe wannan ƙaton bakin naki kona makeki a wajen, zaki tashi ne ko kuwa sai na makeki a wajen?”

“Wayyo ƙafata, wayoo Abbu”. Ta sake faɗa tana dafe saiti ƙafar tata dake yimata zafi, tsaki ya yi haɗe da duƙawa ya tallabota daga ita har jikkar littafan tata ta islamiya dake gefe ya nufi cikin gidan da ita yana kallon yanda ta wage baki tana kuka sai kace wata ƙaramar yarinya, yana shiga Mahmah dake fitowa daga bayi riƙe da buta a hannun tayi saurin ƙarasowa wajen tana faɗin.

“Me kuma zan gani haka Hisham lafiya? Meke faruwa ne, me sameta?” Jin tambayoyin da mama ke jerowa cike da tsoron yanda taga ya ɗaukota ya sa ta ƙara sautin kukan da takeyi, sai daya ajiyeta saman tabarmar dake shimfiɗe cikin ƴar barandar dake gaban ɗakunan gidan sannan ya ɗago tare da daka mata wata irin tsawa data sata saurin rufe bakin ta sadda kai ƙasa tana yarfi da ƙafar tata dake bala’in yimata zugi, cikin ɓaci rai  yake faɗar “Kar ki rufa mana baki anan kiga yanda zansa yayi maki jini yanzu nan”. Sannan ya juyo yana kallon Mahmah dake ƙoƙarin ajiye butar a inda aka tanada don ajiyeta ya ce “kibar yarinyar nan kawai Mahmah, rashin hankalin data saba yine akoda yaushe yauma ta je ta yi, shine fa ta jima kanta ciwo zata wani zo ta dami mutane da kukan banzan”.

“Ah to ai ya yi kyau, idan shashanci ne taƙamar ta gobe ma ta ƙara, na rasa ranar da zaki girma Madiyam ki dena irin wannan shirmen naki.”

Kallonta ya yi haɗe da jan tsaki sannan ya ce, “Ai gashinan taci riba ta jima ƙafar”.  Ya faɗa yana nuna ƙafar tata dake jini tare da ficewa daga gidan cike da takaici, ya rasa me yasa ko yaushe idan yana son fita harkar Madiyam bazai iya ba, koda yake zai yi maganin wannan shashancin nata da Abbu ya ɗaure mata gindi tana yi sai kace wata marar mafaɗi, kamar jira takeyi ya fita ta sake buɗe baki wiwiwi tana kuka haɗe da cewa.

“Wlh Mahmah bana son shi mugu ne, na tsanesa, shine fa ya sa na buge kaina a waccan bishiyar ta ƙofar gida kuma ya sa na faɗa cikin kwalbati, don ALLAH Mahmah kuce ya koma bana son ganin sa”. Ta ƙare zancen tana riƙe ƙafar tata dake yimata zafi sosai, taɓe baki Mahmah ta yi haɗe da zuwa ta ɗebo ruwa ta fara wanke mata ƙafar dake jini, ai kuwa ta shiga tsala mata ihu kai ka ce da sperit take wanke mata ƙafar, tana kaiwa daga saman ƙafar ta riƙe mata hannu tana faɗin “Wayyo Mahmah da zafi wallahi.”

“To ALLAH yasa ba targaɗe kika ji ba a wurin, don gashi nan har ya ɗan kumburo” ta ƙare zancen tana kai hannunta wajen, Madiyam na jin haka ta sake saka wani kukan taɓara haɗe da cewa, “wayyo Abbu na boni na lalace, shikenan ya kasheni Abbu, wayyo ƙafata wayyo Abbu wlh ALLAH ya isana ban yafe masa ba..” kafin tarufe baki Mahmah ta kai mata duka a bakin haɗe da cewa, “ke bana son renin wayo da kuma sakalci, yayan naki kike yiwa ALLAH ya isa? To waya kai ki yin rashin ji balle har yasa hakan ta faru dake?”

Cikin kuka take faɗawa Mahmah abunda ya faru cike da ƙuruciya, don duka-duka shekarunta baza su wuce sha huɗu ba aduniya, dariya Mahmah ta saki tana girgiza kai kafin tace,

“Au! Wai kina nufin akan hanya kika rufe idanuwan don kin hangosa? Tirƙashi! Ai kuwa in dai baki dena ba kin dingi faɗuwa kenan kina targaɗe haɗe da bugun bishiyoyi, yo banda abunki ai in da sabo ya ci ace kin saba da halin yayan naki yanzu, ai indai baza kidena wannan sakalcin da taɓara ba shi kuma bazai dena hantarar kiba, ALLAH na tuba kome zai yi maki ai ke kika jawa kanki tunda shi ba mutumne mai hayaniya ba, asalima baya shiga shirgin yara, kema halinki ne ya jamaki kuma inda sabo yaci kisaba tunda ahaka kuka taso tamkar wasu maƙiya, ko da yake na zata yanzu kin girma za kidena halin kiyi murna da ganinsa tunda anjima ba’a haɗu ba, ashe a inda aka tsaya nan za a ɗora, to Ubangiji ALLAH yayi maku magani?”

“Amin” Madiyam ta faɗa tana turo baki kafin taci gaba da cewa “Tab..wa zai yi murnar ganin wancan dodon Mahmah? ni wlh ko ajikina da ma bai dawo ba, meya sha ruwana dashi”.

“Shikenan ai, gaki gashi indai Hisham ne, da sannu zai yi maganinki agidan nan, ba dai har dodo kike kiransa ba? kici gaba ALLAH yasa ya jiki, jikinki ya faɗa maki”.

“Ki dena mun baki Mahmah don wlh bazan dena kiransa da hakan ba matuƙar bai dena cin zalina ba haɗe da wannan kallon nasa dake tsoratani yana sani shiga tashin hankali haka kurum”.

“Ahhh…lallai to ki shirya ziyartar Sadi mai ɗori don bazai dena kallonki ba tunda shi ba makaho bane, haka kuma bazai dena tsawatar maki ba ko kina so ko bakya so”. Mahmah ta ƙare zancen tare da shigewa cikin ɗaki ta ɗauko mayafinta, 

“Tashi muje na kai ki wajen Sadi mai ɗori kafin ayi kiran sallar magrib, don kuwa wannan ƙafar idan ta kwanar miki a haka sai kin gane kurenki”. Cikin sanyin murya irin wacce ke nuna ta gama gajiya da kukan da takeyi ta ce.

“Ni bazan je ba sai Abbu ya dawo na faɗa masa tukuna”.

“Au! kin fiso ki zauna da ƙafar a haka?”.

“To Mahmah ai yana nan waje zaune!”

“Wa kenan?”

“Ya Dodo mana”. Ta bata amsar tana turo baki, “Oh ni faɗimatu, sai aka ce maki kuma bai da aikin yi sai na zaman jiranki a waje don ya saki kuka?, na fahimci har yau baki san halinki ke sa yana yimaki wasu abubuwan ba shiyasa kike ganin laifinsa, Ni dai koma meye tashi muje kada ki ɓata mun lokaci nasan babanki na kan hanyar dawowa yanzu”.

“ALLAH Mahmah ni bazan sake fita ba, kin manta muguntar da yakeyi mun idan ya ganni waje a irin wannan lokacin? ALLAH ko yanzu wata muguntar zai sake yimun idan na fita, ɗazu fa har kadani ƙasa ya yi, gashi ma yanzun bombom ɗina da goshina da ƙafata duka ciwo suke mun”.

“Kai Madiyam! duk wannan iftila’in wake kaɗai?”

“Eh Mahmah, wlh gaba ɗaya ma jikin ciwo yake mun shima?”

“To ALLAH ya yi maki magani, ai kuwa ga goshin nan shima ya taso”. Mahmah ta ƙare zancen tana ƙoƙarin kai hannunta wajen, “A a Mahmah kada ki taɓa mun da zafi, ki barshi har Abbu ya dawo yagani” Tayi maganar tana yaƙunar fuska, girgiza kai Mahmah tayi kafin ta ɗan ɗaure fuska tana faɗin,

“Shin zaki tashi muje ko kuwa na koma abina na zauna? ni tausayinki nake ji shiyasa bana so ki kwana da ita haka”.

Sake ya ƙune fuska Madiyam tayi kafin ta shiga ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa har saida Mahmah ta riƙo ta, kallo ɗaya zaka yimata kasan ba wani dogon ciwo bane ajikinta kawai dai don ta riga ta sangarce ne shiyasa duk tabi ta ɗagawa Mahmah hankali, ɗingisa ƙafar ta shigayi har suka ƙara sa ƙofar gida tana faman cuno baki, suna kawowa suka ci karo da Hisham shi kuma zai shigo, da sauri ta noce kanta ƙasa shi kuma ya shiga balla mata harara yana so ta ɗago idanuwan amma kamar ta sani ta ƙi. “Mahmah ina zaku je ne haka?” Ya tambaya tare da ɗauke idanuwan sa dake kan Madyam. 

“Wajen Sadi mai ɗori zan kaita don naga alamun kamar tayi targaɗe a ƙafar.”

“Bari na kaita tunda an kusa kiran sallah, nasan kuma Abbu na akan hanya ya kusan dawowa”.

“To shikenan, ALLAH ya yi albarka, sai kije ku tafi, saura kuma ko yanzun ki sake rufe idanuwan har ki sake faɗawa kwalbatin, kinga sai a guntule ƙafar ki huta.”

Murmushi Hisham ya saki jin abunda Mahmah ta faɗa haɗe da kauda kansa gefe, bayan Mahmah ta ɓuya tana wurgo masa harara ganin yanda yake murmushin haɗe da cewa mugu kawai ai a nan kafi wayau, indai mugunta ce ka ɗauki lamba ɗaya, ta yi zancen ƙasa ƙasa yanda bazai ji ba tare da riƙewa Mahmah mayafi dake ƙoƙarin barin wajen.

“Wai meye haka Madiyam? Ka dani zakiyi? Ni fa nafara gajiya da wannan lallaɓakin da nake yi tun ɗazu kina faman narke mani, don ALLAH Hisham jata ku tafi idan kuma ta ƙi ka karya mata ƙafar a huta tunda tsargaggace” ta fizge mayafinta haɗe da komawa ciki abinta tana mita, 

“ALLAH Mahmah ni bazan bisa ba sai dai ƙafar nan ta ruɓe..” tabi bayanta tana faɗa tare da ɗingisa ƙafar da sauri da sauri tana nem guduwa, kafin tarufe baki ta ji ya wani fizgota haɗe da riƙo shoulder ɗinta ya tasata a gaba yana faɗin, “kika sake cewa wani abun saina ɓallaki awurin, sakaryar yarinya kawai, daga an taimaka maki”.

Wiwiwi ta wuce gaba tana kuka shi kuma yana biye da ita a baya har suka isa wajen sadi mai ɗori, “A’ah ƴar gidan Abbu lafiya?” Sadi ya faɗa yana miƙawa Hisham hannu daya miƙa masa su gaisa, turo baki tayi ba tare data tankasa ba har sai da Hisham ya yi masa bayanin abunda ke faruwa, “subhanallahi, matso to nagani” Sadi mai ɗori ya faɗa yana gyara hannun rigarsa, sharrrr… wasu ƙwalla suka zubowa Madiyam a idanuwa tare da ɗago kai tana kallon Hisham ko zai ji tausayinta amma ya kawar da kansa gefe, muryar Sadi mai ɗori ta ji ya sake faɗar “matso mana ƴar gidan Abbu ankusa kiran sallar magrib”…

FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, idan kuma Vip kike so zaki biya ₦800 ne, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku zukata👏 ga masu buƙatar wannan littafi zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no,  0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode.

Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.

Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com

DOWNLOAD NOW

 

Author’s Contact

  • Name : Billy S. Fari
  • Wattpad Handle : @
  • Nick Name : 
  • Whatsapp Number : 07040402435
  • Nationality : Nigeria
  • Email :
  • Group : Haske Writers Association

The Book is not free

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*

Back to top button