Uncategorized

Addu’ar Neman Tsari Daga Sharrin Aljani Ko wane iri ne da izinin Allah

 

Idan mutum yana karanta wannan addu’ar safe da maraice, to aljani komai hatsabibancinsa sai ya bar jikin mutum koda kuwa tare aka haife ku da shi, haka ma idan wani ciwon ya dameka zaka iya karantawa.

A’uzu bi wajhillahil karim, Wabi kalimaatil lahillati la yujawizuhunna barran wala fajiran, wabi asma’illahil husna kulliha, ma alimtu minha wa malam a’alam min sharri ma yanzilu minas sama’i, wa zara’a fil’ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariƙan yadruƙu bikhairin ya Rahamanu. Wa min sharri kulli dàabbatin Rabbi akhizun bi nasiyatuha inna Rabbi ala siraɗin mustaƙim.

FASSARAR ADDU’AR DA HAUSA

Ina neman tsaruwa da zatin Allah mai daraja kuma da cikakken kalmomin sa, waɗanda babu wani na kirki ko fajirin da zai ƙetaresu, kuma da sunayen Allah kyawawa dukkansu waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba, daga sharrin abinda ya halitta, kuma Ya fitar kuma ya ƙaga, kuma ya kare ka daga sharrin abinda yakan saukar daga sama, da kuma sharrin abinda ya kan hau kanta, da kuma sharrin abinda ya fita daga gareta, kuma da fitinar dare da rana, kuma da masu isowa da dare da rana sai dai mai isowa wanda zai iso da alkhairi.

Ya mai Rahama, ka karemu daga sharrin dukkan dabba wadda Ubangiji ya riƙeta da makwarkwaɗarta, Ubangiji ka sanyamu a tafarki madaidaici.

Insha Allahu duk wanda yake karanta wannan addu’ar ba aljani ba ko mugun mutum sai yayi shakkar sa.

Haka idan mutum nada wata rashin lafiya a jikinsa, idan ya karanta a ruwan Zam-Zam ya tofa ya sha da niyyar waraka Insha Allahu a ƙanƙanin lokaci za’a samu waraka da Iznin Allah.

Back to top button