Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 10 Hausa Novel Complete

 

Jawwad ya ja motar yabar cikin gidan, fara zagawa yayi clubs din da yasan Jalal yana zuwa amma be sameshi ba, tun bayan magariban nan yake yawo amma be samu ganinsa ba, Gida ya koma yabar motarsa a bakin layi yakoma part din Jalal ya dakko wayar Jalal ya koma inda yabar motarsa, ya shiga ya zauna cire wayar yayi daga key dayake yasan password din, call log dinshi ya duba yaga kiran Hannah dayawa amma be daga ba lambar Jeje itace ta karshe da aka kirashi dashi kuma shima be amsaba,

Dafe kai Jawwad yayi “ohh my God Jalal ina kashiga ne karka yiwa kanka Illa mana”

Lamabar Jeje ya kira, yai Sa a kuwa Jeje ya daga 

“Ina Jalal yake?”

“Kamar Yaya?” Jeje ya tambayeshi

“Kamar yadda na tambayeka”

Jawwad ya bashi amsa

“Ohhh in ka damu da shi seka zagaya mashayar da yake zuwa kaneme shi,”

Jeje ya kashe wayarsa

Girgiza kai Jawwad yayi ya kuma kunna motarsa ya marasa ina ze dosa Neman Jalal

Haka ya dinga zaga clubs har gurin goman dare, club din dayaje da farko ya koma Wanda nan Jalal yafi zuwa, Jawwad ya duba ko ina amma bega Jalal ba, 

Download>>> Bakar Inuwa Complete Document

Yazo ze fita ya hangi motar Jalal a can wani guri da sauri ya fito ya nufi inda motar Jalal take, bude motar yayi da sauri Jalal yana zube a cikin motar ya fita hayyacinsa sosai, gashi nan dai shiba sumamme ba kuma shiba me bacci ba

Dagoshi Jawwad yayi yana jijjiga shi 

Da sauri Jawwad ya koma ya bada ajiyar motarsa gurin masu gadin club din ya shiga motar Jalal ya jata ya nufi Gida

  Jalila kam tagagara yin bacci tunda Jawwad ya fita tana palour a zaune tana jiran dawowarsa tun suna hira da Halima har Halima ta tafi ta kwanta tabar Jalila a palour

Karfe sha dayan dare taji motar Jawwad ya dawo 

Da sauri ta fito setaga motar Jalal, tana nan tsaye taga Jawwad ya fito daga motar 

“Yaya lafiya kuwa naga ka Dade?”

“Baby da kyar Nagano Jalal, yanzu dare yayi bari inkira Me gadin gidansu Jalal ya kama minshi in kaishi part dina”

“To shike nan”

Jawwad ya juya da sauri, Jalila takarasa bakin motar ta leka, Jalal yana kwance Kamar gawa, ba a dadeba Sega Jawwad sun dawo dame gadi

Suka fito da Jalal suka shiga dashi suka kwantar da shi akan gadon Jawwad 

Jalila ta kalli Jawwad “yaya wai meyasameshi? Bashi da lafiyane”

“Wallahi ban saniba Jalila inaga giya ya sha dayawa”

Dan zare ido Jalila tayi

“To se yaushe ze tashi”

“Se lokacin data sake shi, amma akwai abunda yake damunsa a rai, Wanda bansaniba”

Jawwad yafada cike da damuwa

“Yaya kalli yadda yake numfashi ko bashi da lafiya, kalli jijiyar kansa fa duk sun daga”

Jawwad ya kai hannu goshin Jalal yayi zafi sosai

“Da alama kansa yana ciwo ma”

Kafarsa Jalila ta kalla ta mike da sauri 

“Yaya Jawwad kalli kwalabe sun fasa masa kafa”

Da hanzari Jawwad yazo ya duba kwalabe duk sun shige kafarsa

“Ya salam inaga bari in fita akwai wani abokinmu likitane, bari inga in yana nan yazo ya duba shi inba ya nan kuma, inzo in kaishi asibiti”

Ya Ciro wayar JALAL ya ajiyeta akan side bed

“To kayi sauri danni tsoro nakeji palour zan koma danaga ya taso in zura da gudu”

“Jalila da hankalinsa ba haukacewa yayiba kinji, ki zauna a parlour kiji rani”

Gyada masa kai tayi, ta fito parlour ta zauna shikuma Jawwad ya fita lokaci² Jalila seta leka dakin taganshi a kwance yadda a aka barshi, motsi taga yafarayi a hankali yana yamutsa fuska yana surutai cikin maye

“Hannah meye hakane, bakida hankaline,? Mtseww nace miki bana so fa, bana son yimiki rashin mutuncine amma ba kya ganewa”

A hankali Jalila ta Dan shiga dakin tana kallonsa

“To wace kuma Hannah,”

Jalila tayi maganar a zuciyarta 

Cigaba yayi da surutai idonsa a rufe ya cigaba 

“Nifa Jeje giyar nan yau kaman ba irin wadda nasaba sha bace kamar akwai wani abu a ciki, mtseww, nii ban San meyake damuna ba Jawwad baya son giyar nan danake sha fa”

Jalila ta kalleshi

“Kai ni dalla ka isheni ka cikamin kunne, kayimin shiru, nina aikeka ka sha kalleka Dan Allah, mutum har mutum amma ba hankali, ko kunya bakaji kake shan giya kai ko tsoron Allah bakaji ma bana tunanin kayi sallar isha’i, kana kwance kana maye, kasa Yaya se wahala yake in bakayimin shiruba nida kaine”

Jalila se rashin M takewa Jalal shikam baya hayyacinsa, yacigaba da surutansa

“Ko wace kuma Hannah oho masa”

Wayar Jalal ce tafara ringing ta kalla sunan Hannah ta gani a kan screen din wayarsa,

“Hmm kishiyar Ilham ce Ashe”

Tayi banza da wayar takoma palour, wayarce ta cigaba da ringing ta cikawa Jalila kunne Dan haka ta mike ta koma bedroom din ta kai hannu ta daga wayar

“Dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, me wayar kin ganshi a kwance, tunda kika kira be dagaba ai seki hakura ko, saboda shirme a tsohon Daren nan haba, kinkira ba adagaba sekace mayya duk kincikamin kunne”

Jalila tai tsaki ta kashe wayar ta kai hannu zata aje wyar ya rike hannunta gam ya bude Jajayen idanuwansa fes akan JALILA

Download>>> Yar Harka Complete Document

Kwalalo ido Jalila tayi ta firgita matuka 

“Meye haka kacikamin hannuna”

Ko kyafta idonsa bayayi akanta gashi ya riketa gam ko motsa hannun bata iyawa, idonsa tsoror yake bata 

“Na shiga uku nika cikani, dama ance watakila ka haukace”

Kara karfin rikon yayi mata 

“Wai meye hakane”

Setaga hawaye na bin gefen idonsa can yayi wani yunkuri se yafara amai kumface kawai take fita daga bakinsa, yasaki hannun Jalila a hankali

Zare ido tayi dataga irin aman dayakeyi

“Nikam ina Yaya Jawwad ya tsaya haka”

  Itakam Hannah mamakine ya cikata wace ta dauki wayar Jalal a Daren nan, OK ko Itace kanwar tasa da Jawwad yake fada, to me take masa a wannan lokacin haka?

“Tabdijan to wallahi da sake akwai matsala”

Jalila ta koma bakin kofa ta zuba masa ido Dan tarasa meya kamata tayi can jimawa Sega Jawwad ya dawo shida wani

“Sorry Jalila kinganni ban dawo da wuriba, seda naje Asibiti na dakko likitan”

“To gashi can dai wani irin amai yakeyi yana surutai”

Da sauri Jalal da likitan suka shiga cikin dakin 

Likitan ya kalli bakin Jalal duk wannan kumfar fara

“Subhanallah” ya furta yasaka abu ya goge masa kumfar yayi masa wasu allurai

Jalal ya dinga aman abunda yaci 

Likitan ya kalli Jawwad

“Jawwad Jalal wasu miyagun kwayoyi yasha Wanda besaba shan irinsu BA, suke nema suyi masa illa”

“Bayan giyar kuma hada kwayoyi”

Jalila tafada cikin mamaki

“To gashi nan dai, kuma da alama ya Dade beci abinci ba”

Likitan yabata amsa, girgiza kai kawai Jawwad yayi, Jalila ta koma palour

Shida likitan suka gyara gurinda Jalal yai aman suka canzamasa kaya zuwa Jallabiya

Kafar Jalal aka ciremasa kwalaben daya taka, sannan yasa masa drip, ya rubuta magunguna yacewa Jawwad da safe yaje ya siyo masa,

“Yaya ni Bacci nakeji seda safe”

“To baby mungode sosai, kiyi bacci me dadi”

“To Yaya kaima ka kwanta haka dare yayi”

Ya gyda mata kai likitanne ya kalli Jalila

“Baby ni baza ayimin sallama ba?”

Dan murmushi tayi

“Seda safe tafada a takaice”

Jawwad kam Dan hade rai yayi, ya kalli likitan “muje in maida kai”

“Jawwad dan Allah wannan babyn fa nifa na faller wallahi, Yar gayu da ita ga iyayi”

“Ina ruwanka da wacece, nifa banason irin wannan abun salis, muje in saukeka ni”

“Tuba nake sirikina amma nikam naga guri”

Fusata Jawwad yayi “kaga wuce muje”

Haka suka tafi ya maida doctor, se bayan karfe daya sannan Jawwad yasamu nutsuwa lokacin drip din jikin Jalal ya kare ya cire masa, sannan ya kwanta

  Bayan sallar asuba Jalila take gayawa Nana a gidan Jalal ya kwana, yanata a man kwayoyin da yasha

“Tab to indai wannan ne sun saba, amma iya sanina baya shan miyagun kwayoyi, sedai giya da taba, watakila Suma yafara watsa abunsa wayasani, kice hadake akai jinya”

Nana tafada Dan Neman magana

“God forbid indai Dan ta shine, yaje ya karata ni Yaya Jawwad ne abun tausayi wallahi”

“Mutane dayawa na mamakin kaunar da sukewa Juna, Allah ne ya hada jininsu”

“Kuma a haka Aminiyarki take sonshi”?

” mhmm kema dai kyafada”

“Hakane, amma Nana Dan Allah wace Hannah”

“Hannah kuma? A ina take”

Se Jalila ta fuskanci Nana batasan zancenba Dan haka tace

“OK don’t mind me kwanta kikoma baccinki, Dan nasan yanzu shiya dameki”

“Aikuwa kamar kuwa kinsani”

Jalila kam mikewa tayi ta tafi kitchen Dan sarrafa abunda za a bawa ciki, Jalila tana matukar son harkar girke²

Tunda sauran duhun asuba ta shiga kitchen zuwa bakwai da rabi ta kammala

A palour ta hadu da halima

“Anty leemat barka da safiya”

“Barka dai sayyada Jalila, naji kamshi yana tashi ba dai kingama girkin ba”

Download>>> Maraicin Nawaff Complete Document

“Nagama, kina bacci ne shiyasa ban tasheki ba”

“Sannu da kokari, ke ba kyajin aiki Sam, amma tun asuba kika fara”

“Eh halima, wallahi kinga Jalal ne ba lafiya za a bashi magani da safe nasan Yaya Jawwad ni ze roka in hada musu breakfast, kinga gara ayi tunkafin yayi maganaa”

“Gaskiya kam, bari inje in karasa, aikin da ya rage”

Zuwan Jalila gidan nan ba karamin amfani yake musu ba Sam batada kyuya, ba ta San kazanta Sam, shiyasa Jawwad yake jin dadin sakata aiki ba kyuya, amma Nana yanzu zata bata rai tana tura baki, ga son jiki a cikin Nana, kuma Maama take biyemata

Ta hado kayan Abincin ta kai part din Jawwad, ta tarar yana zaune a palour da Azkar a hannunsa, sallama datayine yasashi dagowa

Murmushinsa ya fadada

“Sannu da kokari baby, yanzu nake tunanin yaza ayi da breakfast, naga jiya baki kwanta da wuri ba kar in takura miki, nagode da kulawar da kike bamu, sannu da kokari”

Karasawa tayi parlour ta ajiye kayan abincin ta  kalleshi

“Barka da safiya, Dan uwa rabin jiki,”

“Au bazaki amsa sannun nawa ba”

“Ni lafiyata kalau, wancan mutumin na cikin dakinka zakayiwa sannu, shine Mara lafiya”

“Kinganki baby, Jalal dinne mutumi ko? In yajiki ba ruwana, kinsan boss din ba wasa”

“Hmmm lallai boss naga alama”

Sukayi dariya a tare JAWWAD yace

“Jikin nasa da sauki, ya tashi tun dazu yanzuma wanka yakeyi”

“To Allah ya sawwake”

“Ameen baby”

Kallonsa Jalila tayi sannan tace

“Dan uwana”

“Na am kanwata”

“Bakayi bacci sosai ba idonka ya nuna”

“Kema bakiyi bacci ba gashi kuma nasan kin gaji”

“Ni bangajiba”

“Dagaske”

“Eh mana, kasan wani abu”

“A a baby sekin fada”

“Yayana kaina mussamanne a cikin mutane, halinka halin Abba, kanada kirki yayana, Allah yaabamu itaku”

“Baby ni banga wani kirki danake dashi ba, kinfini kirki baby, sedai ince Allah yabamu itaku”

Zumbura baki Jalila tayi

“Nida ake cemin masifaffiya, uwar Neman magana,”

Dariya Jawwad yake sosai

“Wayagaya miki haka”?

Bude kofar bedroom din Jalal yayi ya fito yana dingisa kafarsa Jallabiyar Jawwad ce a jikinsa tayi masa kyau sedai fuskarsa ta rame

Karasowa yayi ya zauna a kusa da Jawwad 

“Sannu Jalal ya jikin naka?”

Jawwad yafada cikin damuwa

“Da sauki, Nagode Jawwad”

Jalal yafada a hankali

“Kasan zamuyi fada ko tom yanzu ga breakfast baby ta kawo, ka karya se inje in gayawa mummy kadawo daga nan in siyo maka magani”

Gyada masa kai kawai Jalal yayi

“Baby bakiwa Jalal ya jiki ba”

“To ai naga ya warke tunda gashinan da kafarsa”

“Jalila sarkin magana yanzu dai jeki kawo mana ruwan dumi Wanda za a gasa masa kafarsa”

“To” ta mike tabar parlour, Jawwad yahada masa breakfast din sannan ya mike “bari inje in siyo maganin, in ta kawo ruwan dumin in bazaka iya gasawa ba kabari in dawo”

Jinjina kai Jalal yayi, har Jawwad ya nufi hanyar fita ya tsaya ya waigo

“Yawwa idan na dawo kuma zaka gayamin meyasa ka fasa kwalabe ka taka seka gayamin meyake damunka”

Still dai bece komai ba

Jawwad seda yaje yagayawa mummy yaga Jalal yanzu haka ma yana gidansu, amma bashi da lafiya

Mummy taita godiya tana sawa Jawwad albarka, Ilham kuwa najin haka ta gashi ta tafi gidansu Nana domin ganin Jalal, Jawwad kuma yatafi  karbo magun gunan

Jalila ta kawo ruwan zafi a flask tai sallama amma yamata shiru tazo ta dire flask dina gefen Jalal 

“Wai ba nace ka dinga amsa sallama ba, 

Gashi nan ruwan zafine in kaga dama ka dumama ka gasa kafar taka in baka ga damaba ka zuba a haka” har zata fita dawo ta tsaya a gaban Jalal

“Saboda wauta waya gaya maka in abu na damun mutum haka akeyi kafasa kwalabe kabi ta kai, kuma kaje ka sha kwayoyi, kakusa kashe kanka daka mutu haka zaka farka a kabari

Ga laifin sabawa iyaye, ga shan giya, ga kashe kanka dakayi da abun yamaka yawa, in abu yana damun mutum a zuciyarsa addu a yakeyi ya koma ga Allah, ba ya aikata wannan shirmen da kakeyiba, duk Wanda be kiyaye salollinsa akan lokaciba haka kunci zeta damun rayuwarsa”

Yana jinta ya cigaba da cin Abincinsa dukda bawani ci yakeba cakala kawai yake, yana tausayawa ranar daze hukunta  Jalila,

se yanzu ta kai duba ga cin abincin dayakeyi, da hannun hagu yakecin Abincin

“Subhanallah Kaikam komai naka na dabanne, komai naka ba irin na mutane ba”

Tasa hannu ta karbe cokalin hannunsa daga hannun hagu ta zira masa a hannun dama

“Shedan ne yake cin Abinci da hannun hagu, Allah yasa kayi bisimillah kan kafara cin abincin”

Dago idonsa yayi yasaka a cikin na Jalila

“Kin manta waye Jalal ko?”

“Eh namanta seka tunamin”

Ilham ce ta shigo palourn ba ko sallama a tare suka waigo suka kalli Ilham

Ilham ce tayi mutuwar tsaye ganin Jalila a tsaye a gaban Jalal shikuma yana kallonta ga abinci agabansa kamar wasu masoya

Watakilama a baki take bashi abincin wani sashi na Zuciyarta ya zigata

“Mezan gani haka? Yaya Jalal menayimaka haka, kake kokarin cin amanata wannan itace sakamakon soyayyar dana dau shekaru inamaka, lokaci daya kayimin haka dama abunda na Dade INA zargine yau Allah ya nunamin”

Saroro Jalila tayi tana kallonta 

Ilham ta dawo da idonta kan Jalila

“Munafuka kina cemin Yar wahala Ashe kece babbar Yar wahala, Ashe hasashena ya tabbata son Jalal kike, to wallahi baki isaba kinyi kadan kiyi takara dani akan abunda nakeso bans…..

” enough malama karkiga nayi miki shiru kicigaba da zagina, mezanso anan” ta nuna Jalal

“Ni abu na kawo nake masa magana akan abunda ya aikatawa kansa banda haka ni babu abinda ze hadani da shi”

Shidai Jalal bece musu uffan ba sema mamakin hakikancewa da Ilham take, yakeyi

“Karya kike wallahi ko duk jikina kunne ne bazan yaddaba kuma wallahi Jalila sekinyi danasanin abunda kikayimin, sena baki mamaki

” ya isheki malama”

Download>>> Dangin Rabi Complete Document

Jalila ta karaso gaban Ilham “bude idonki da kyau, ki bude kwakwalwarki kiga da wacce kikeyi, inkin manta bari in tuna miki  Jalila ce dawo hayyacinki, Dan kinga ina lallabaki ba amin hauka wallahi yanzun nan zan saukemiki abunda yake damunki

Me akai akayi Jalal meye abinso a tareda Jalal wannan makakken Mara tarbiyya, shi kike nufi  Jalila taso, ko ta nuna a matsayin uban yayanta, a tunaninki zan tsaya ina daga murya saboda shi

Yadda yake a maken nan ai se makakkiya Yar uwarsa, badai Jalila ba ni mutumin arziki zan aura Dan babu uban me hankalin daze bawa wannan yarsa a haka

Kema da kike sonnashi kinada manufar hakan badan hakaba yadda yake wulakantashi yaci ace kin hakura useless and hopeless creatures dagake harshi”

Tirkashi

Missing Page

Ja da baya ta dingayi yana Binta, har seda ta kai karshen bango sannan ta tsaya tana zazzare ido

“Kingama gudun?”

Saboda karfin hali irin na Jalila ta dubeshi

“Wallahi kasake ka karaso inda nake sena maka Illa, akan me baza a fadi gaskiya ba, ai duk abunda nake fada ba karya nayimaka ba haka kake”

Daka mata tsawa yayi, Wanda yasa taji hanjin cikinta sun nannade guri daya

“Shut up, akwai wata illa dazakiyimn Wanda yafi miyagun maganganun da kikeyimin, ke badan darajar Jawwad ba da tuni na dade da kakkaryaki na karya banza”

Dagowa Jalila tayi da sauri ta kalleshi, 

“Eh in karya banza mana, in ban mantaba a wancan karon nagaya miki ba ruwanki dani kifita a sabgata kome nake aikatawa babu ruwanki, meyasa kike da taurin kai da shishshigi,?

Dakamata tsawa ya kumayi ba tambayarki nakeba

Banza tai masa ta dauke kanta

” kaga ni ban guri in wuce”

Ba musu yabata hanya, ta sa kai zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa yakamo hannunta guda daya, yai masa wata muguwar murdawa, Wanda in yakuma murdawa ze iya ballata 

Bata San lokacin datayi wani uban zilloba ta fasa kara 

Ya kalleta “da zafine?” 

Kasa magana tayi se wani uban fitsari dataji ya matsota, gashi ko kwakwakwaran motsi takasa balle ta kwace hannunta

Be saketa ba, da daya hannun nasa yasaka yakamo kunnenta, cike da mugunta ya murda iya karfinsa, wannan karon batayi ihunba sedai taji kaman fitsarin yafara fitowa, Allah ya temaketa hawaye yafara zubowa daga idonta, yana daf da ita sosai Dan suna iya jin numfashin juna, ya Dan tsura mata ido sannan yace

“Nikike cewa makakke ko? Kuma Useless and hopeless creature ko, ke gaki wadda ta haifowa duniya rashin kunya, daga yau in kinga Jalal, kikuma kallon ko inda nake sena yi maganinki

Hada cewa kinfi karfin makakke irina, ke meye abunso a gurinki,, yana ina wata mummuna dake, banda rashin mutunci da rashin kunya  baki iya komaiba”

Motsa baki take, tanaso tayi magana amma takasa

Har yanzu be saketa ba, yadan kalleta 

“Ko kinada maganane”?

Girgiza kai tayi, fuskarta tayi jajawur, se ruwan hawaye dayake zuba wani nabin wani,”

Da kyar ta tattaro kalaman dazata fada

“N..Ni kasakeni, zan karye fa”

Yadda tayi maganar cikin kuka da kuma shagwaba, seyaji jikinsa yayi wani iri

“Au bakinki be mutu bako” yafara a hankali

Yasa kafarsa ya take mata yatsun kafarta 

“Wayyo Allah Ummi, ze kasheni, Allah ka temakeni”

Yadda taketa kuka gwanin ban tausayi, Dan zuwa yanzu ji take kamar hannunta ya karye, sannan ta saddakar ya cire mata kunne, ga yatsun kafafuwanta dake wani zugi, kunenta yafara saki sannan yacika mata hannunta

Daya hannun tasaka ta rike hannun dayayiwa muguntar danji take kamar ya karye,

Dan kallonta yayi kamar yayi dariya amma ya dake

“Gobema kikuma sena tabbatar miki ni makakke ne, da giya naso nabaki kisha senaga bake yakamata in bawaba Jawwad zan bawa, in yasha kaman kinsha ne, stupid girl, tafi kibani guri”

Dukda haka be ishi Jalal ba Dan Sam be huce ba akan abubuwan data keyi masa, seda yamata kyakyawan rankwashi a tsakiyar kanta, aikuwa nan take ta tsuguna kasa ta fashe da kuka,

Shikuma yakoma kan kujerar da yataso yai zamansa yacigaba da abunda yake,

Kuka take sosai saboda batason atabamata kai ko kitso bata sonyi setace zafi yake mata, balle wannan katon ya rankwasheta, kuka take sosai hada sheshsheka

“Idan baki tashi kinbar dakin nan ba nazo gurin nan, sena danneki na baki giya, and I mean it”

Bashiri ta mike ta nufi hanyar fita, tana Jan kafa seda ta bude kofar, ta waigo ta kalleshi,

“Allah yasakamin wallahi, mugu kawai, kuma wallahi niba mummuna baceba,”

Shiru yayi mata, “bazata iya yin shiruba, bakinta baze mutu ba”

Tsayawa tayi ta share hawayenta daga waje Dan gujewa tambayoyim Nana, tana daf da shiga cikin gida Jawwad suka karaso shida doctor salis

“Munzo a dai² Jawwad waccan ba mutuniyar bace?”

Doctor salis yai maganar yana nunawa Jawwad Jalila”

Banza Jawwad yai masa yanemi guri yayi parking, Jalila tana kallonsu amma bata tsayaba tayi cikin gida, Allah ya temaketa bakowa a parlour tashiga dakinsu ta tarar halima tana ninkewa Nana kayan sawarta

“Halima ina Nana”?

” hajiyace ta kirata,afiya kuwa”

“Lafiya kalau”

Jalila ta shige toilet Dan kar halima ta dameta kunnenta yayi Ja ga hannunta da ya sage ji take kamar banata ba

Gaskiya Jalal azzalumine, ya iya salon mugunta, babban abunda ya dameta wannan rankwashi da yayi mata Dan tunda yayi mata take jin Jiri har yanzu, kanta har yafara ciwo, lallabawa tayi ta watsa ruwa, ta wanke fuskarta tayi alwala Dan magariba ta gabato sannan ta fito ta canza kaya, bata iya amfani sosai da hannun da Jalal ya murda mata, guri daya takoma ta dunkule lokaci² tana share hawaye

Nana tazo ta sameta a haka

“Lafiya kuwa?, daga zuwa duba Yaya Jawwad kinzauna”

“Naje baya nan yanzun nan ya dawo”

Jalila tabata amsa a takaice

“Wai meya sameki naga yanayinki ya canza?”

“Kainane yake ciwo”

Download>>> Maraicin Nawaff Complete Document

“Eyyah sannu inada paracetamol inkinyi salla seki sha”

Jalila ta gyada mata kai, Nana kuma tayi waje

“Azzalumin banza wainice mummuna makaryaci kawai, wallahi ko makaho yasan niba mummuna bace”

Jalila taita mita tana kunkuni,

Doctor salis ya duba kafar Jalal yace masa babu sauran kwalba a ciki, Dan haka acigaba da gasa kafar da ruwan dumi yana shan magunguna zata warke gaba daya insha Allah

“To mungode sosai salis”

Jawwad yafada yana dafa salis, Dan ture hannunsa salis yayi, ya kalli Jalal

“Jalal a gaskiya Jawwad bashi da kirki, har innemi alfarma a gurinsa yakasa yimin”

Kallonsa Jalal yayi

“Anya zan yadda Dan uwana bashi da kirki, amma me yayi maka?”

“Wai ace inga kanwarsa ince inaso ya hademin rai, yace baze baniba”

Dan murmushi Jalal yayi, yayinda Jawwad yakuma hade rai, Jalal yace wace yarinyarce

“Wadda mukazo muka tarar da ita a gurinka ranar dabaka da lafiya, wata me iyayi, baby sunanta kome? Nidai kaman haka naji Jawwad yana cemata, ranar tana nan har karfe daya, seda kayi bacci Jawwad yatafi maidani sannan ta koma cikin Gida, yau muna shigowa na hangeta INA yiwa Jawwad maganarta amma ya shareni”

Kallon Jawwad Jalal yayi, aransa yace wannan Mara kunyar, sannan a fili yace

“Ba ruwana kaida shi, in yabaka shikenan, ina maka murna”

Doctor salis yadan bude baki

“Au hakaama zakace, bazaka tayani lallabashi ba”

“Niba ruwana”

Jawwad mikewa yayi

“In kungama ni natafi masallaci”

Akayi sallar magariba, da kyar Jalila ta mike tayi salla, tana idarwa ta zube a gurin saboda azababben ciwon dataji kanta yanayi,

Nana takuma shigowa ta tarar Da Jalila ta dunkule akan dadduma, durkusawa Nana tayi ta dafata

“Jalila har yanzu kanne yake miki ciwo”

Jinjina kai kawai Jalila tayi, mikewa Nana tayi ta dakko mata magani ta kawo mata, Jalila ta kalli maganin

“Nana ki bar maganin nan, ni banaso”

“Saboda me haka zaki zauna da ciwo”

“Kibari kawai ze dena, idan na sha maganin nan amai zanyi”

“Ohh my God, sannu amma kina cuta bazaki sha magani ba”?

    Har wajen isha doctor salis yana gidan suna hira jefi², ya zauna ne koda Allah zesa yaga Jalila amma shiru be ganta ba,

Halima tayi sallama, ta kawo musu abinci, Jawwad ya kalli Halima yace

” Halima ina Jalila ne?”

“Bata jin dadine, ta kwanta nikadai nayi girki yau”

“Subhanallahi me yasameta haka”

Jawwad yafada a Dan tsorace

Halima tace “Naji tacewa Nana kanta yana ciwo”

“Ta sha magani ne”?

“Wallahi ban saniba”

“OK jeki, ki kirawomin ita, inzata iya zuwa, tunda salis be tafiba seya dubata”

“To bari inje”

Ta mike ta koma cikin gida, Jalal yana jinsu bece komaiba, 

Doctor salis ya kalli JALAL

“Wace kuma JALILA, naga Dan uwanka ya damu, nidai nasan Nanace kawai kanwarsa”

“Kabari ta zo sekaga wace”

Jalal yabashi amsa

Halima ta koma cikin Gida, ta tarar da Nana tana bawa Jalila tea,

“Jalila yayanku yace kije likita yana nan ya dubaki”

Nana ta kalli halima

“Daga zuwa kai abinci Harkin gaya masa”

“A a tambayata yayi”

“To jeki angode”

Seda Jalila tagama shan tea sannan ta kama hannun Jalila suka fito

Suna daf da Barin palourn Maama ta hangosu

“Me Nana INA zakuje haka”

“Jalila CE bats da lafiya , shine Yaya JAWWAD ne yace taje doctor salis yazo se yadubata

” Allah ya sawwake”

Shine abunda Maama tace tashige kitchen, itakuma Nana suka fito

Nana ce tayi sallama, suka amsa

Jawwad ya mike da sauri,

Download>>> Tubali Book 2 Complete Document

“Subhanallah baby, abin har ya kai haka, sannu”

Jin ance baby yasa doctor salis saurin waigowa

Jalilace fuskarta duk tayi ja hawayene kawai ke fita daga idonta

“Subhanallah Ashe babynmuce ba lafiya”

Doctor salis yafada yana mikewa tsaye

Guri tasamu ta zauna,Nana ta zauna a kusa da ita

Nana takalli Jalal

“Yaya Jalal ina wuni”

“Lafiya sannu”

Hada ido sukayi da Jalila ta galla masa harara, kawai se yayi murmushi yacigaba da latsa wayarsa

Jawwad se jera mata sannu yake

Doctor salis ya kalleta

“Sannu baby dama sunanki Jalila, a very sweet name”

Shiru Jalila tayi masa ta kwantar da kanta akan cinyar Nana

Jawwad ya hade rai

“Kaga cewa nayi ka dubata ba ka dinga yimata shirme ba, in bazaka dubataba zan dauketa mutafi Asibiti”

“To ai dubatan zanyi, kake min masifa”

Doctor salis yakuma kallon Jalila

“Baby kidena kukan mana, kinfiye shagwaba in mutum bashi da lafiya ba kuka akeba,

Yaushe kan yafara miki ciwo?”

“Dazune” tafada a kasan makoshinta

Nana ce tayi yinkurin dagota tareda cewa

“Jalila ki tashi kiyi masa bayani, bayajinki fa”

Jalila ji tayi Nana ta fama mata hannunta da Jalal ya murda da sauri ta furta

“Wayyo Allah Nana hannuna”

Jawwad yakuma rudewa

“Baby mekuma yasamu hannun naki”

Jalal ta kalla, amma shi ya maida hankalinsa kan wayarsa, shi yadda Jawwad ya rudene yake bashi haushi

Wani hawayen takaicine ya zubo mata

“Bigewa nayi da kofan toilet”

“Gaskiya zanyi fama, baby haka kike shagwababbiya komai kuka”

Doctor salis yai maganar cikin zolaya

Wani mugun kallo Jalila tayi masa cikin tsiwa tace

“Sunana Jalila karka kuma cemin baby”

“To yi hakuri na dena, yanzu inane yake miki ciwo”?

Murmushi Jalal yai a ransa yace indai wannan yarinyar ce kacigaba dayimata shishshigi, ba karamin aikinta bane ta zageka

Doctor salis yagama yimata tambayoyin daze mata yace a Alluran dayayiwa Jalal akwai guda daya da ze mata sekuma magani daze bata 

Zumbur ta mike zaune 

” Allura kuma, Yaya Jawwad ina tsoron Allura,”

“Yi hakuri a hankali zeyimiki”

Shidai doctor salis wannan shagwabar ta Jalila birgeshi yake

Nana tace

“To ai maganinma ba sha kike ba gara ayi miki allurar”

Aka zuko Allura, Jalila tace sedai ayi mata a hannu, salis yace ta miko hannun, ta mika masa sannan tace 

“A hankali Dan Allah”

“To shikenan a hankali zanyi miki”

Ta mika masa hannun, da kyar akayi allurar nan tana ta kuka,

Shikam goga ko uffan bece musuba dayaga suna biye mata haushi ya isheshi ya tashi yabar musu dakin

Salis yace allurar da yayiwa Jalila ta isa sedai in ciwon kan yaci gaba ai masa magana

Nana takama hannun Jalila suka koma cikin Gida a zaune tayi sallar isha’i saboda ciwon da kan yake mata tana idarwa ko canza kaya batayiba ta haye gado takama baccin wahala, Dan ta manta da batun duba Jarrabawa

(Gaskiya Jalal ya iya rankwashi,)

Da safe bayan tayi sallar asuba takoma baccinta, ranar ko tsinke bata dauke a gidanba balle tayi musu girki

Aikuwa dai Abincin yau da banbanci don Sam be kai dadin na Jalila ba

Har LA asar Jalila bata fitoba, sedai Yaya Jawwad har daki yazo ya dubata ya tarar tana bacci

Salis yakira Jawwad a waya ya tambayi ya jikin Jalila, Jawwad yace masa da sauki,

“Jawwad Dan Allah ka hadani da baby mana in mata ya jiki,”

Jawwad kashe wayarsa yayi, yana mita 

Jalila tana daki da yamma, taji hayaniya a harabar gidan, Dan haka tafito dama wunin ranar bata fito ba, Abbane ya dawo daga lagos, ya canzawa Jawwad dankareriyar mota, duk anje an kewaye motar, yayinda Jalal ya kame a cikin motar sekace tasa 

Murmushi Jalila tayi Abba sannu da zuwa gaba daya suka waigo suka kalleta, ta Dan rame sosai, idonta yayi wani iri 

Abba ya kalleta

“Baby meyafaru ko bakida lafiya ne?”

“Lafiyata kalau bacci nayi”

Nana tai saurin cewa

“A a Abba batajin dadine”

“Eyya Nagani fuskanta ya nuna”

“Abba ciwon kaine fa kuma na warke”

Takalli motar

“Masha Allah, Abba mota tayi kyau Allah yasaka maka da mafificin alkhairi, Allah yakara arziki, amma wa aka saiwa motar naga me motar daban Wanda ya kame a cikin motar daban”

“Lallai yarinyar nan har yanzu bakinta be mutuba ga muryarta har ta dashe saboda kuka”

Jalal yai maganar a ransa

Abba yayi murmushi

“Jalila kayan Jalal aina Jawwad ne, Dan haka tasuce su biyun” Jalila ta kalli Jawwad 

“Yaya congratulations Allah yasa rai da lafiya akayiwa”

“Ameen baby mungode”

“Abba to mu se yaushe za a saimana?”

Nana tai maganar a shagwabe

“Ku tambayi yayanku, shize saimuku, gata mamanku can Ku dinga hawa ko Jawwad yabaku tsohuwar tasa, in kunshiga university seku dinga Ja”

“Abba ta Yaya Jawwad dinfa duk ta tsufa wallahi,”

“Yana jinki dai, in kun gama Ku nabaku naku tsarabar a cikin Gida”

Daga nan Abba yai cikingida yana dariya, Maama tabi bayansa

Jalila ta kalli Jawwad

Download>>> Dr. Eesah Complete Document

“Yaya muje a danamu a motar, dama zamuje duba exams”

“To ku taho muje daga nanma muje shan ice cream”

“Amma Yaya yaushe zaka fara koyamana mota,?”

Nana ta tambaya

“Ku tambayi Jalal seya koyamuku rigimanmun Abba kawai”

“Tabdijan, waye ze koyamana tukin, ba tukin jirgin sama mukeso akoyamana bafa tukin mota Yaya Jawwad, wannan ai tukin jirgin sama yakewa mota”

Jalila tai maganar tana hararar Jalal, yana kallonta ta cikin mudubin motar

“Ba ruwana ke dashi”

Jawwad yafada yana dariya, cikin Gida suka nufa suka dakko hijjabai, da wayoyinsu suka fito

Tunda Jalila taga, Jalal a mazaunin direba taga shi ze tuki jikinta yayi sanyi, Dan tana ganin yanda yake Jan nasa motar.

Nana ta bude motar ta shiga, motar tayi kyau matuka, Jawwad ya kalli Jalila 

“baby shigo mana”

Jikinta a sanyaye ta bude motar ta shiga, Jalal yai musu banza yacigaba da danna wayarsa

Jawwad ya kalleshi “muje ko”

“Ina zuwa” yacigaba da aikin wayarsa sun shafe kusan minti goma shabiyar a zaune sannan yayiwa motar key, aikuwa kamar yadda Jalila take fargaba a guje ya fafari motar nan kaman zasu tashi sama, Jalila se rarraba ido take tana karanta adduo’i daban² a zuciyarta, tabbas Jalila ta yadda sun hau motar Dan giya, yadda yake gudu dasu sekace a Action movies kaman ba mutane ya dakko ba haka yake ratsa manyan motoci yana overtaking

“Wayyo Allah Nikam nashiga uku gaskiya a tsaya in sauka wallahi, na hakura da duba Jarrabawar, ni kadai Ummi ta Haifa baza a kasheni a wannan gangancin ba”

Jalila tayi maganar da karfi

“Yi hakuri baby, Jalal Dan Allah sassauta gudun nan Jalila a tsorace take, guri yasamu yaja wani arnen parking

” ta sauka ta fita in bazata iya zama ba”

“Wallahi bazan sauka ba sedai kai ka sauka ai ba…….” Bata gama ba Jalal ya juyo yana kallonta tai saurin yin shiru

Jawwad yace 

“Baby kiyi hakuri babu abinda ze faru lafiya zamuje insha Allah”

“Ni gaskiya tsoro nakeji”

Nana ta kalli Jalila tana dariya

“Runtse idonki ki kwanta akan cinyata zaki denajin tsoron”

Ba musu ta kwanta akan cinyar Nana ta runtse ido Jalal ya Dan kalleta, ya maida kai ya cigaba da bawa sabuwar motar Jawwad wuta

Jalal Ya samu cafe a hanya yayi parking

Suka fito daga motar gaban Jalila se faduwa yake tana fargabar me zata gani a result dinta, Jalal yana zaune a cikin mota be fito ba 

Jawwad yai musu Jagora suka nufi shiga cafe Jalila ta tsaya a kofar shiga

“Ya dai muje mana”

Nana tai maganar tana janyo hannun Jalila

Jalila tayi ajiyar zuciya

“Nana karbi exam card dina ni bazan shigaba abinda kuka duba seku gayamin”

Ta karasa maganar kaman zatayi kuka

“Haba Jalila in kika karaya nikuma ince me, karki damu taho mushiga”

“Nana Allah bazan shigaba, ina nan sekun fito”

Haka Nana ta hakura ta kyale Jalila, tabi bayan Jawwad yayinda Jalila ta tsaya a kofar gurin, kallon da mutane kewa Jalila ne yafara bata haushi Dan ita bata San kallo

Jikin motarsu ta koma taje ta jingina ta tsaya, Jalal ya bude kofar motar ya kashingida a jikin kujerar mota

Jalal ne yake waya tana iya jiyo abinda yake cewa dukda a hankali yake maganar

“Hannah meyasa kike takuramin a rayuwata, kin uzzuramin wallahi,

Ke ko zuciya baki da ita, haba Dan Allah nifa bazan iya wannan shirmen nakiba, kozanyi aure Hannah kinsan bazan iya auren mace kamarki ba”

Jalila ta Dan waiga ta kalleshi,

Taja tsaki

“Mtseeew shirme, sekace wani mutumin kirki, suna zubarwa da Kansu mutunci a gurin wannan Dan giyar, wahalallu dagasu har shi, kowace wannan Hannah oho” ta cigaba da mita daga inda take

Wayarsa yacigaba da yi Dan besan tanayi ba

Jawwad ne da Nana suka fito daga cafen, fuskarsu babu annuri suka nufo inda Jalila take 

Hankalinta ne yai mummunar tashi ganin yanayin fuskarsu, suka karaso bakin motar

“Na fadi ko yaya, banciba, na fadi Jarrabawar ko?”

Mikomata paper yayi sannan yace

“Congratulations my dear u got it, am proud of you”

Yai maganar yana murmushi tareda Jan hancin Jalila, bude result din tayi

A¹ bakwai tasamu B guda biyu

Rungumeta Nana tayi 

“Ina tayaki murna Babyn Abba”

Jalila ta kalleta “Nana me kika samu”

“Nine credits ne”

Murna suka cigaba dayi

Download>>> Goje Sadauki Omar Return Complete Document

“Is  OK murnar ta isa haka, kushiga muje, aje shan ice cream, proud of you all, Allah yayiwa karatunku albarka”

“Ameen suka fada a tare”

Suka bude motar suka shiga, Jawwad ya dubi Jalal yace

“Jalal kaga results din su Nana, Alhamdilillah, result yayi kyau, mussaman na Jalila”

Dan kallon papers din hannun Jawwad yayi yana kokarin kunna motar

“Mmm yayi kyau Allah yasa ba satar amsa tayiba”

Kutmelesi Jalila taso gayamasa bakar magana Dan dai Jawwad yana gurinne, Jawwad ya kalleshi

“Wuce nan bros, duk cikinsu ba wadda take satar amsa”

“How sure are you?”

Jalal ya tambayeshi

“Obviously na yadda da kannena, ranar graduation dinsu Jalila awards din da aka bata sun isa su tabbatar daba ta satar amsa”

“Hmmmm” shine abinda Jalal yace ya fizgi motar a guje yabar gurin

Jalila kuwa se kunkuni take tana magana a ranta, ita kuwa Nana se hira take mata, tana kuma jinjinawa Jalila dangane da result dinta, itakuwa Jalila Kalmar satar amsa ta bakanta mata rai sosai

“Ashe dai ba iya Neman maganar aka iyaba kan yana kawo wuta, shiyasa kike burgeni mutuniyata, baki da wasa”

Nana ta fada tana Jan hancin Jalila

Jalila ta rirrike Nana, saboda gani take a kowane lokaci motar nan zata kife saboda tukin da Jalal yake

A wani joint sukayi parking Jawwad yayi musu rakiya sukaje suka sai abinda sukeso, sannan suka fito suka nufo hanyar gida

Suna cikin tafiya Jawwad yace

“Baby, Nana dai mass com takeso, kekuma fa?”

“Yaya ni nursing nakeso,”

“Wow, u can do it, Allah ya temaka”

Wayar Jalila tafara ringing bakuwar lamaba ce, kamar karta daga, sekuma ta daga tare da yin sallama

“Wa alaikum salam, Jalila Ashe kinkoma kano babu labari?”

Jalila ba ta dau muryava Dan haka tace “wake magana”

“Kai Yar baba, kardai kice baki ganeniba”

“Subhanallah, Yaya Abdallah yi hakuri kasan banida lambarka se yanzu nagane, barka da yamma”

“Yawwa Jalila, yakike?”

“Lafiya kalau ya daddy”

“Yana lafiya, Ashe kinkoma kano, nazo Gida attending birthday Hanan, take gayamin”

“Aikam dai Yaya Abdallah ina kano,”

“Kice zamu dinga haduwa kinsan a bayero nake karatu, na dinga kawomiki ziyara”

“To shikenan Yaya nagode sosai”

“Insha Allah weekends din nan zamuzo, da daddy da Hanan”

“Dagaske Yaya”

“Dagaske nake”

Zuwa yanzu Kishine yake cin Jawwad jin yadda Jalila ta saki jiki tana waya, da wani namiji, Jalal ya Dan kalleshi yaga yadda ya wani hade rai, Dan murmushin gefen baki Jalal yayi yacigaba da tukinsa

Jalila suka gama waya da Abdallah ta kalli Nana

“Nana da weekends insha Allah usainata zasuzo, zasu kawomin ziyara”

“Wa kenan?”

“Hanan mana”

“Dan Allah dagaske”

“Wallahi Nana”

Jawwad ya Dan gyara zama 

“Baby da wa kike waya?”

“Yaya Abdallah ne”

“A ina yake?”

“Abokin nan nakafa, Dan gidan captain Rasheed”

“Hmm nagane”

Daga nan be kuma cewa komai ba harsukaje gida, lokacin ana kiran sallar magariba,

Suna zuwa gida suka tarar Maama tana salla Abba kuma ya tafi masallaci, Dan haka suka tafi dakinsu, halimace ta biyosu a baya, tana fadin

“Jalila ya akayi,? Ya jarrabawar kuwa?” Jalila ta tsaya tana murmushi, Nana kam bata tsayaba ta wuce dakinsu

“Leemart jarrabawa Alhamdilillah, kinga results dinmu” Jalila ta mikamata result din

Karba halima tayi ta duba

“Masha Allah, Jarrabawa tayi kyau kam, Allah ya sanya alkhairi, Yasa a ci gajiyar karatu”

“Ameen my leemart, bari inje zanyi salla”

“To shikenan”

Bayan sunyi sallar magariba suka tarar da Abba a part dinsa Maama ma tana part din, suka bashi result din yayi murna sosai yai musu addu a, da fatan alkhairi

Sannan ya dauki kayan da yakawo musu tsaraba yabasu, na Jalila harda brown din Teddy da kayan sawa na alfarma, sukayi masa godiya 

Nana se tsokanar Jalila take wai ta ci sunanta baby ta girma amma tana wasan teddy

Maama ta tabe baki

“Nima haka Nagani, yarinya da girmanta amma kana sai mata teddy, wannan ai sangarta ce”

Murmushi Abba yayi

“A ganinkine sangarta, ni a gurin kyautatawane”

Da Jalila taji haka ta mike ta bar part din gaba daya ta koma dakinsu

Suturar da Abba yabasu manyan suturune masu tsada matuka

Bude trolley dinta tayi ta debo wasu kaya masu kyau kala hudu, ta Dora turare body spray da roll on, ta bude kayan dasuka siyo, dazu dasuka fita ta dakko ice cream roba daya ta hada ta fito, sukayi clashing da Nana ta kalli kayan hannunta

“Wannan kuma fa? Me zakiyi dashi”

” Halima zan bawa”

“Saboda me”?

“Nima Allah yabani wasu, ba tare da yayi shawara daniba”

“Kudi fa ake biyanta meyasa zaki dauki kayanki masu kyau kibata”

“To meye a ciki Nana, naci jarrabawa Alhamdilillah Abba yamin kyautuka, yakamata mu farantawa wasu muma”

Dan tabe baki Nana tayi ta wuce daki yayinda Jalila ta nufi dakin halima

   Ilham tarasa abinda yake mata dadi yan kwanakin nan takasa gane inda Jalila tasa gaba shin da gaske Jalila tana son Jalal, kokuwa, amma in tana sonshi ya za ayi tagaya masa wannaan miyagun maganganun,

Amma kuma ya akayi Jalila take gaya masa maganganu son ranta amma be dau wani mataki akanta ba, Wanda ta tabbatar ita  bata  Isa tayi masa haka ba,

Kenan shima yana son Jalila, tunda take gaya masa maganar data ga dama amma ya kyaleta

“Kan uba karyane wallahi ina wani shirmen hakan ze faru”

Tai maganar a fili

“Ko mami zan kira in gaya mata abinda yake faruwa, yanzu ina gaya mata ni zatayiwa fada tace laifinane, kuma baze yiwu in gayawa Nana ba tunda Yar uwattace za a iya hada kai da ita a cuceni, yanzuma watakila bakinsu daya”

Tayi nannauyar ajiyar zuciya to ni yazanyine?

Ko gidan malamin nan zanje da kaina innemi yaseera ta rakani(kawar Ilham ce) hakama za ayi inje inji ya za ayi aimin maganin wannan tantiriyar

Da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta samu nutsuwa

Halima ta kalli Jalila 

“Jalila inani inasaka wannan kayan masu tsada”

“Leemart to meye a ciki, ba wani kaya masu tsada, sedai in abun hannuna ne bazaki karba ba”

“A a Jalila ba haka bane,”

“To in ba hakabane kawai ki karba”

“Nagode Jalila, Allah ya faranta miki kaman yadda kikayimin”

“Ameen leemart”

Jalila ta koma daki ta kira Ummi a waya tagaya mata abinda tasamu a result dinta Ummi tayi murna sosai, sannan tace

“Jalila ya yanayin zamanki a kano? Naji muryarki cikin farin ciki ina fatan komai lafiya?”

“Komaiafiya Ummi, bakiga Mayan da Abba ya siyo mana ba,”

“Masha Allah, haka nakeson ji, yacigaba da hakuri da rayuwa Jalila,”

“To Ummi insha Allah, Ummi da weekends insha Allah Hanan zasu kawomin ziyara”

“Dagaske baby”

“Dagaske Ummi, dazu Yaya Abdallah ya gayamin”

“Allah sarki gaskiya suna kaunarki Jalila, Nima next week insha Allah zanzo, daga nan zan wuce garinmu”

Haka nan se Jalila tayi jikinta yaysanyi 

“Ummi tafiyar tana nan Ashe zakiyi,?

“eh tana nan zanyi insha Allah”

“To Allah ya kaimu, next week din”

“Ameen ki gaida mutan gidan”

“Zasuji insha Allah” 

Nana ta Dan kalli Jalila

Download>>> Tubabbiya Complete Document


“Yanaga jikinki yayi sanyi”

“Nana banason tafiyar nan da Ummi zatayi”

“Haba Jalila, Ummi yakamata tayi tafiyar nan yana da kyau taje taga danginta”

“Hakane Nana”

“Yawwa to kidena tayarda hankalinki, kiyimata addu a kawai”

“To Nana”

“Yawwa babyn Ummi”

  Daren ranar Ilham batayi baccin kirkiba se tufka da warwara kawai tekeyi, kamar ta janyo safiya tayi domin taje gurin malamin nan

Washe gari da safe wajen karfe goma Ilham ta shirya tacewa mummy zataje gidansu

Ummi tace seta dawo, tana fita ta tafi gidan su yaseera, suka gaisa da Maman yaseera sannan ta wuce dakin yaseera, ta tarar yaseera ta shirya ita take jira ko zama Ilham batayiba suka fita ita da yaseera sukayi gidan malamin nan.

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button