Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 45 By Ayshercool

Gaba ɗaya fuskar Al’amin ta sauya takmar ta horo, ta koma Al’amin ɗin sa na ainihi, tamkar bai taɓa sanin wani abu wai shi dariya ba. Wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, jijiyoyin goshinsa zuwa kansa suka miƙe suka kukkumbura, idonsa yayi wani irin ja mai ban tsoro, bugun zuciyarsa ya ƙaru da saurin gaske, jikinsa ya fara ɗaukar wani irin zafi saboda tashin hankali da tsananin ɓacin rai.Ba tare da tunanin halin da Nura yake ciki ba, yayi wa hannun guduma wani irin mugun riƙo, da sai da ƙasusuwansa suka yi ƙara.Nura ya ɗora ɗaya hannun a kan na Al’amin ya ce “Yaya, kai ɗan uwa ne da Allah ya bani rana tsaka a titi, duk wannan abun ka yi ne dan inganta rayuwata, ba ka taɓa yin wani abu da zaka cuceni ba, na san da ka san abun da zai faru da ni kenan, ba zaka bari na je ba, dan Allah ka kwantar da hankalinka, ni na san ba zan rayu ba, abun da suka yi mini ya fi na kowa muni da tashin hankali, ban san yaya zan misalta maka ba, amma dan Allah kar ka yi yinƙurin yin wani abu, idan ba haka ba za su yi maka illa. Na bar su da Allah ka tayani Addu’a Allah ya yafe mini laifukana, idan na mutu dan Allah ka yi mini wanka kar asiri na ya tonu, ba na son a zargeka da abun da mutane ba su san menene ainihin abun da ya faru ba.Wurin bayan gidana ya riga ya ɓaci, kowa ya gani zai gane meyafaru dan Allah kar wani ya je kan gawata idan ba kai ko mama ba”Al’amin ya riƙe hannun Nura gam, amma ya kasa magana sai wani irin numfashi mai haɗe da huci, ya sunkuyar da kai yana sauke numfashi.Yanayin yadda mahaifiyar Nura ta tarar da Al’amin, ya sanya ta gane ya gaya masa.Ta ƙarasa gaban gadon, jiki a sanyaye ta ce “Al’amin, ka kwantar da hankalinka dan Allah, zan iya dafa Alqur’ani na rantse, ba zaka kai mini nura in da za a cutar da shi ba, na san da ka san me zai faru kenan ba zaka yadda ya je ba, a irin yadda yake bani labarin zamanka da shi. Iya ɗawainiyar da ku ka din ga yi da mu kai da matarka ya ƙara tabattar mini da haka. Cuta ce an riga an cuce mu, amma mun bar wa Allah, ni ba zan zargeka ba”Ya saki hannun Nura a hankali, ya tashi ya juya ya fice.Nura yayi ajiyar zuciya ya ce “Allah ya sa kar ya ce zai ɗauki wani mataki, dan mutanen nan sun wuce duk yadda yake tunani, ni dai ku cigaba da yi mini addu’a da fatan cikawa da imani”Duk da juriya da mahaifiyar Nura take yi, sai da ta kasa ta zubar da hawaye, cike da karaya, dan magana kawai Nura yake yi, amma komai sai an yi masa, gashi buni-buni jininsa ya ƙone, sai an saka masa wani, dan bayan bayan gidan, har da jini ne yake zuba daga wurin, jini sosai ba kaɗan ba, a tunaninsa da na mahaifiyarsa ɓoye wa likitocin ainihin abun da ya faru shi ne rufin asirin su, dan babu wanda zai fahimce su, cewa za a yi shi ya kai kansa, saboda kwaɗayi da son abun duniya, dan Nura ya yi girman da ya fi ƙarfin ace dole aka yi masa.Ikon Allah ne kawai ya kai Al’amin gida, dan ko me za ayi masa bai san ya aka yi ya isa gidan ba.Jauhar har ta yi bacci, dan ‘yan kwanakin nan bacci take yi sosai da sosai, duk in da ta ji kwanciya ta yi mata daɗi sai bacci.Ba ta farka ba, sai bayan sha biyun dare, shi ma dan taji ta gaji da kwanciyar ne, a hankali ta tashi jikinta duk yayi tsami, ta kalli ƙofar ɗakin Al’amin, ta tashi ta nufi ɗakin, ta ɗaga labule ta shiga.Yanayin kwanciyar da ya yi, ya tabattar mata da yayi shaye-shaye ya bugu, dan wata irin kwanciya yayi.Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban katifarsa ta zauna a hankali ta ce “Haba master yau kuma?” Dan bai fiye shan abun da zai gusar masa da hankali gaba ɗaya har haka ba, yana yi amma ba sosai ba, ya fi ganewa busa hayaƙi. Kuma kwanakin nan da Allah ya taimaketa tayi galaba a kansa, bai fiye shan abun buguwa ba sai shan sigari, wiwin ma ya rage shan ta sosai, amma ta zo ta tarar da shi a wannan yanayin.Da ƙyar tana haki, haka ta gyara masa ƙafarsa da hannunsa, ta shafi sumar kansa, sai wani irin gumi yake yi, naman fuskarsa yana ɗan yi rawa lokaci zuwa lokaci ga ajiyar zuciya da yake ta yi a kai kai.Ganin ba ya hayyacinsa, balle su yi magana, ya sanya ta tashi ta tafi ɗakinta, cikin zullumi da tunanin me aka yi masa?.Kiran sallar farko ya farka, sai dai zuciyarsa cike da tsananin baƙin ciki da ɓacin rai, ya san ko ya je gida ba zai samu indabo ba yana Abuja, kuma ba zai iya tafiya Abuja ba, cikin fargaba zai tafi kar yana matsawa wani abun ya samu Nura.Alwala yayi ya fice, a hanya yayi sallar asuba, ya ƙarasa Asibitin, maman nura na ta kokowar yadda zata ɗaga shi, ta saka masa pampers, yayi mata girma.Al’amin ya bubbuga ƙofar, ta ce “Waye?”Da ƙyar ya iya magana ya ce “Al’amin ne”Nura ya ce “Mama buɗe masa”Ta buɗe masa ya shigo, Nura ya gaida Al’amin, jinjina kai kawai yayi, suka gaisa da maman Nura, da ƙyar yake iya magana, saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali.Ya taimaka mata, suka canzawa Nura pampers, jinin da Al’amin ya gani a pampers ɗin ya ɗaga masa hankali, gaba ɗaya halittar duburar Nura ta fito waje, babu ƙyanƙyami babu komai, ya taimaka mata suka gyara shi, suka saka masa pampers uku, kamar yadda take saka masa, sai kuma ta kawo zannuwa ta tuttura masa ta toshe ko ina, ta fesa masa turare, ta kunna turaren wuta, ta shiga banɗaki ta wanke kayan da aka cire mas.Al’amin ya rasa me ma zai cewa Nura, abun duniya ya ishe shi, ya ji ya tsani kansa, komai baya yi masa daɗi.A hankali ya kalli Nura ya ce “Zan gaya wa likitoci, su duba idan da abun da za a iya yi, ayi maka babu dabara a ɓoyewa likitoci wannan lamarin”Da sauri Nura ya ce “Dan Allah kar ka yi mini haka, ka rufa mini asiri, wallahi babu wanda zai yadda dole aka yi mini, na san ba zan rayu ba, lokaci kawai nake jira, dan Allah yayana wannan ce alfarmar ƙarshe da zan nema a wurinka, dan Allah kar ka gaya wa kowa”Cikin matsananciyar damuwa Al’amin ya ce “Nura ka yafe mini, wallahi ban san abun da zai faru ba kenan, na zata hakan zai taimaki rayuwarka ne… Sai ya kasa ƙarasawa muryarsa ta fara rawa.Guduma ya ce “Wallahi na sani, kai mutumin kirki ne yayana, dan Allah idan na mutu ku din ga yi mini addu’a, na san sauran jama’ar gari babu lallai su yi mini, saboda ban shuka alheri ba, amma na san kai zaka yi mini kai da mama, da Antynmu. Dan Allah idan ta haihu, idan namiji ne, ka saka masa Nuraddenni ka din ga tunawa da ni” yayi maganar yana murmushi.Al’amin ya haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci, ya kalli Nura, amma ya kasa magana.Nura ya sunkuyar da kai, yana share hawayen karaya.Maman Nura ta fito ta gama wanke kayan Nura, muryar sa na fita a hankali, ya kalli maman Nura ya ce “Me za a sayo muku ne? Da me zaku karya ba ta tashi ba na taho”Mama ta ce “Kar ka damu Al’amin, ƙanwata suna nan tafe, da wuri za su zo, ai da ƙannensa ma su duba shi, baiwar Allah ai tana ƙoƙari Allah dai ya raba ta da cikin nan lafiya, ta sauka lafiya ƙalau. Ai ta ce tuwon dawa zan yi mata, da miyar ɗanyar kuka da man shanu idan ta haihu, in sha Allah kuma ana ce mini ta sauka, zan dafo na taho kano, yajin daddawa ma ni zan yi mata”.Nura ya ce “Mama ni dai ki tayani roƙo, na ce a saka sunana idan an samu ɗan saurayi”Suna yin hirar ne, dan Al’amin ya kwantar da hankalinsa, sai dai fuskar nan tamau ya kasa yin fara’ar.Ƙarfe takwas da mintuna, wata yarinya ta shigo ɗakin, ‘yar baƙa mai kyau, da siririn billenta, a gefen fuskarta.Babu ko sallama ta faɗo ɗakin ta ce “Mama mun zo””Baki iya sallama ba ne?”Ta ce “Assalamu alaikum, yaya wai da gaske ka je Abuja?” Tayi maganar tana ƙarasawa gaban gadonsa.Nura ya ce “Eh ramma, ya gida ya makaranta?”Ramma ta ce “Lafiya ƙalau, yaya wai to ka ga shugaban ƙasa?” Ya girgiza mata kai alamar a’a.”To idan ka koma zaka ganshi? Ka ce masa dan Allah a gina mana burtsatse, wurin ɗebo ruwa da nisa sosai”Ya shafa kanta ya ce “To zan gaya masa, ina Sani?””Babanmu ya ce ba za a zo da shi ba, ya tafi makarantar Allo, nima da ƙyar ya bar na biyo innar su jafarun muka taho”.Mama ta ce “Ke baki iya gaisuwa ba, balle ki yi wa yayan naki yaya jiki ba?”Ta kalli Al’amin ta durƙusa ƙasa ta ce “Ina wuni?”Ya jinjina mata kai kawai, ta ce “Yaya sannu ya jiki?””Jiki da sauƙi Alhamdilillah””To Allah ya baka lafiya”Wata mace ce tayi sallama, tana faɗin “Ke kuwa ramma an yi ƴar bantan uba, ina can ina bulayin in da aka kwantar da ku, kawai na nemeta na rasa shashasha ba zaki yi hankali ba”Ta zauna suka gaggaisa, Mama ta nuna mata Al’amin ta ce “Atine ga uban gidan Nura, shi ya samo masa aikin nan, yake ta ɗawainiya da mu”Atine ta ce “Allah sarki, ni wallahi kama yake yi mini da mai gyaɗa, yana kama da ‘yar nan ta ta da ta rasu wadda tayi aure a birni, zahra’u” da sauri Al’amin ya kalleta Mama ta ce “Wallahi kuwa, mun yi waya da ita ma, ta ce zata zo duba Nura”.Taɓ yana da alaƙa da Nura ne, ko kuwa kawai dai hasashe ne, ko abun su na mutanen ƙauye, da kowa ma ɗan uwan su ne? saboda tsabar miskilanci bai yi musu magana ba, ya tashi ya tafi.Ya je gidansa ma, ya kasa kawai ya tafi ya samu wani kango, yayi zamansa, abun duniya ya ishe shi, bai ma san ta ina zai fara ba.Bai koma gida ba sai can bayan la’asar sannan ya koma gida, ba ta ce masa uffan ba, tayi masa sannu da zuwa, ita babbar godiyarta ga Allah, dawowarsa lafiya, ba tare da wani abu ya faru da ita shi ba.Sai dai ta haɗa abinci ta bashi, amma ta ga ya daɗe bai motsa ba, daga baya ya ɗauki cokali ya din ga tura abincin da ƙyar, kamar mai tura magani, ya gama ya nemi wuri ya kwanta bai ce mata uffan ba.Duk da yanayin hakan bai yi mata daɗi ba sam, amma ta daure ta ɗan bashi lokaci, amma taga a jere, kusan kwana uku, ba ya ce mata uffan, kuma kullum sai ta yi bacci zai dawo, da asubar fari kuma yake ficewa. Idam ya fitan nan, asibiti yake tafiya ya taimakawa babar Nura ta gyara masa jikinsa, sai dai kullum jikin nasa babu sauƙi.Ranar na haɗu, da ya fito zai fita ta tare shi ta ce “Master, wai dan Allah laifin me na yi maka har haka ne? Meyake faruwa yakamata ka sanar da ni”Ya ce “Zan gaya miki idan na dawo” daga haka ya fice ya bar ta.Abun duniya ya ishi jauhar, ta kasa gane meyake faruwa haka yake ɓoye mata.Yana zuwa asibiti ya tarar da mahaifiyar Nura a gefen gadon Nura, ta rufe shi, idanunta sun yi jawur.Cikin matsanancin tashin hankali ya ƙarasa gaban gadon, ya yaye zanin, ya tarar Nura ya cika.”Innalillahi wa Innalillahi raji’un” ya furta cikin matsanancin tashin hankali, ya zauna yayi shiru shiru, ya kasa zubar da hawaye sai wani abu da yake yi masa zillo, tsakanin maƙogwaronsa da ƙirjinsa.Ya saka gwiwoyinsa a ƙasa a gaban mahaifiyar Nura ya ce “Ki yafe mini saboda girman Allah, ban taɓa tunanin abun da zai faru da Nura kenan ba, da na san haka zata kasance wallahi ba zan tura shi ba”Ta share hawayenta ta ce “Wallahi na sani, kuma ni ban zargeka ba, Yanzu fatana Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi, Allah ya yafe masa kai ma ɗawainiyar da ka yi da mu, Allah ya baka lada”.Ya ɗauki waya ya sanar da su liti su samo mota, a asubar su zo a tafi da gawar Nura Allah ya yi masa cikawa.Sun girgiza sun kaɗu matuƙa da mutuwar Nura, da asubar aka tafi da gawarsa gidan mai unguwa, ta ce ita za ta yi wa Nura wanka, Al’amin ya tayata ya ce ban da su biyu, kar wanda ya je kan gawarsa.Mai unguwa ya din ga bala’i, yana yayi asara kuwa, ya rasa wanda zai gayyato kan gawarsa sai ɗan daba.Maman Nura ta ce “Ɗa na bai yi asara ba wallahi, kai ka yi asara, dan da ka kula da shi ka riƙe shi da mutunci da amana, ba zai faɗi haka ba. Kuma ba in da aka ce ɗan daba ɗan wuta ne, ko an haramta masa zuwa kan gawa”.Haka suka yi wa Nura sutura, aka sanar da rasuwar sa.Duk da ana ganin Nura baya ji, amma ya tara mutane, saboda daga baya duk wani aikin gayya na cigaban unguwa da shi ake yi.Sai ƙarfe goma na safe, Al’amin ya dawo gida, yana zullumin yadda zai gaya wa Jauhar mutuwar Nura, ga zuciyarsa da take wata irin tafasa take raya masa kashe Indabo ya huta da baƙin cikin da ya jefa shi a ciki.Cikin matsananciyar damuwa ta ce “Master wai meyake faruwa dan Allah?” “Allah ya yi wa Nura rasuwa”Gaba ɗaya sai ta manta waye ma Nura, ta ce “Waye kuma Nura?”Ya ce “Guduma ɗan gidan mai unguwa” kamar shashasha haka ta bishi da kallo, daga bisani wani irin jiri ya ɗebe ta, cikin azama ya riƙe ta, jikinta ya hau wata irin tsuma, ta saka hannu iya ƙarfin ta, ta toshe bakinta, dan hana kukan da yake ƙoƙarin taso mata fitowa amma ta kasa, iya ƙarfinta ta din ga maimaita “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Innalillahi wa Innalillahi raji’un. Allah ya sa ba Nuran da na sani ka ke faɗa ba”Jiki a sanyaye ya zauna da ita a jikinsa ya ce “Ba kyau yi wa mamaci kuka fa kin sani, ki yi masa addu’a”Cikin kiɗimewa ta ce “To me zan ce?””Ki ce Allah ya jiƙan Nura yayi masa rahama”Tari ta fara yi, ya ɗaga ta yana yi mata fifita, tare da yi mata sannu.Sai da ya tabbatar ta ɗan samu nutsuwa, sannan ya riƙe hannunta, suka tafi gidan mai unguwa, idanunta sun kumbura sun yi jawur, fuskarta ma tayi ja sosai da sosai.Sai dai suna shiga ɗakin da mahaifiyar Nura take karɓar gaisuwa, suka tarar da hajiya a ciki a zaune, a kusa da Maman Nura.Hajiya ta ce “Al’amin, yanzu nake cewa zan kiraka na ga kamar unguwarku ce nan”Maman Nura ta ce “Ai wannan ne ubn gidan nasa da ya ɗauke shi kamar ɗan uwa da nake gaya miki””To ai ɗan wurin Zahra’u ne, jikana ne””Iko sai Allah, Al’amin da kakarka da mahaifiyata uwar su ɗaya uban su ɗaya, Allah bai saka mun san juna ba”Ya zaunar da jauhar, ta zubawa mahaifiyar Nura ido, amma ta kasa magana sai sheshsheƙar kuka, maman Nura ta rungumeta tana ƙoƙarin rarrashinta, amma ta kasa sai suka cigaba da kukan tare gefe ga ramma da ƙaninta sani, da suke uwa ɗaya da Nura, suma su na ta kuka, hakan ya ƙara karya zuciyar Al’amin.Har aka gama zaman makoki, Al’amin yana cikin damuwa da tashin hankali, Hajiya da su ramma, a gidan Al’amin suke kwana, har zuwa kwana bakwai, sai dai kafin a gama zaman makoki, mai unguwa ya fara yada maganganu cewar Al’amin ne yayi silar mutuwar ɗan sa, Allah kaɗai ya san ina ya kai shi, idan abun gaskiya ne, meyasa shi bai je ba ya tura shi.Kafin a ƙare zaman makokin, sai da maman Nura suka yi kaca-kaca da mai unguwa, ta ce Al’amin babu yadda za ayi ya kai shi in da za a cuce shi, idan ma haka ne, ai ɗan uwansa ne ba ruwansa.Aka share zaman makoki, amma Al’amin ya kasa cigaba da walwala, tun jauhar na bin sa na tambayarsa ko lafiya? Ta yi rarrashin tayi ban bakin, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.Zuciyar sa na ta azalzalarsa ya bi Indabo can Abujan, ya halaka shi kowa ma ya huta, amma ya daure ya jira ya dawo.Sai da Nura yayi sati uku, sannan aka gaya wa Al’amin Indabo ya dawo.Gaba ɗaya baya cin abinci yadda yakamata, idan ya fita baya iya zuwa wurin sayar da shayi, sai ya samu wurin da babu wanda zai takura masa ya kwanta yayi ta tunani, ya din ga jin da ma bai san Nura ba a rayuwarsa gaba ɗaya da duk haka bata faru da shi ba, ashe duk abun nan ma suna da alaƙa da juna.Hatta jauhar yanzu ba ta iya samun kulawarsa yadda yakamata, dan ko in da take ya daina zuwa, ba ya dawo wa ma sai ta yi bacci.Gashi ta shiga wata na bakwai, haki ya sakata a gaba, ga nauyin cikin ya fara damunta, da ƙyar take iya tafiya.Indabo yana zaune a falonsa, yana ganin mutane, ya ga Al’amin ya faɗo falon kamar daga sama.Cikin sauri ya sallami waɗanda suke tare da shi, ya miƙe tsaye ya ce “Mai zamani lafiya kuwa? Ya na ganka a haka?”Kafaɗar Indabo ya daka ya hantsila kan kujera, “Me zamani distinguish senator kamar ni ka yi wa haka, dan na sakar maka na ba dama a kaina?””Zuwa na yi na gaya maka shukar da kayi tayi huda”.”Kamar yaya?”Al’amin ya kalle shi da jajayen idanunsa ya ce “Ba na jin magana, amma wallahi ba na cin amana, kuma duk wanda ya ci tawa sai ya biya. Nura guduma ya mutu, na karɓi saƙonka ka jira amsar da za ta biyo baya”.Ras! Gaban indabo ya faɗi, dan ba haka suka tsara ba, ya aka yi ya san Nura ya mutu?.”Ban gane Nura ya mutu ba””Shut up! Ka sam komai, tsohon munafuki algungumi, na san komai, ka lalata rayuwar yaron da nayi niyyar ingantawa. An dawo da shi rai a hannun Allah, na san baka san ya aka yi aka dawo da shi gida ba, bayan ka shirya yayi hatsari idan ya tashi dawowa yadda zaka ɓatar da abun da ka aikata. Wallahi ka ci amanar Al’amin kuma sai ka biya.Ba ka yi mamakin yadda nake yi maka biyayya ba na yi duk abun da ka ke so?, ka zata kawai saboda kana bani kuɗi ne? Bari na tuna maka ni yaron dodo ne, dodo babban sarki doodn da yake ɗauke da makamin tarwatsaka, ka zata ya mutu da sirrin nan a cikin sa ne? Wallahi ma’aruf na sanka fiye da yadda ka san kanka, a Nigeria ko wajen Nigeria wuraren da ka ke tafka tsiyatakunka.Wallahi na buɗe bakina a kanka, ka gama kaɗewa bar ganin kana da rigar kariya, kuma ku ne ku ke juyar ƙasar, dodo ya mutu ya bar ni da babban kundun da zan iya rusa ku.Niyyata idan na zo na kashe ka, sai dai hakan ba zai saka na huce ba, saboda yanzu ba irin da ba ne, na ajiye wanda suke buƙata ta. Akwai dabarun da masu kimiyyar lissafi suke bi, wurin yin solving wato BODMAS. Bracket Open, division, multiplication addition sannan subtraction. To ni upside down nake yi indabo, sai na fara division nake multiplication na yamutsa komai sannan na saka a bracket na rufe.Ka rubuta ka ajiye daga yanzu, ni ne babbar barazanar rayuwarkaDaga yanzu duk motsin da zaka yi, zaka yi shi a tsakanin tarkunan da zan saka maka, ka daina shan ruwa cikin kwanciyar hankali, ni ne magajin dodo kuma zaka biya cin amanar da ka yi mini” ya juya ya fita yana huci.Cikin tsananin tashin hankali, Indabo ya tashi, ya ɗauki wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa.Cikin tashin hankali ya ce “Ya aka yi Nura guduma ya bar gidan nan, garin yaya? Waye ya dawo da shi kano ban sani ba wane munafukin ne ya rusa mana plan?”Jifa yayi da wayar, ya hau safa da marwa, cikin tashin hankali “Kenan kallon biri yake yi mini duk tsawon lokacin da muka yi tare? Amma Allah ya tsinkewa dodo albarka, ya ƙara tsine masa cin amanar da ya yi mana kenan?” Ya kuma ɗaukko wata wayar ya kira P.A ya ce “Maza ka ƙaraso gida ina nemanka”.Ya ajiye wayar ya cigaba da kaiwa yana komowa.Afujajan P.A ya ƙaraso, ya ce “Yallaɓai ya ake ciki ne, meyafaru na ganka cikin tashin hankali?””Dodo”P.A ya ce “Me dodon yayi?””Dodo ya daɗe da kashe mu, kafin mu kawar da shi ashe ya gaya wa mai zamani komai? An dawo da yaron nan Nura kano, ya san komai, na yi waya wai an nemi obi an rasa, ya gudu yanzu ya san komai, na kaɗe idan yayi magana ya gama rusa ni, Allah ya tsinewa dodo albarka””Ka kwantar da hankalinka, honorable wai waye wani mai zamani, me aka yi aka yi shi ne? Mutum nawa ka kawar kan mu zo in da muke yanzu? Ba zai tayar mana da tarzoma ba, bayan mun yi nasara kawar da shi kawai zamu yi”Indabo ya ce “Tayaya wannan yaron mai shegen taurin rai, da ƙarfin tsiya, ashe tsawon lokacin nan kallona kawai yake yi”P.A ya ce “Kwantar da hankalinka akwai abun yi, zan yi maka bayani”.Cikin dare jauhar na zaune tana lazumi, tayi sallar dare, ta ji shigowar Al’amin, ta ɗan jira wasu mintuna, sannan ta bi shi ɗakinsa.Ƙwayoyi ta tarar da shi ya haɗa zai sha, cikin azama, ta durƙusa ta kwashe ƙwayoyin, ta dube shi ta ce “Akwai abun da ka ke ɓoye mini master, ba iya mutuwar Nura ce take damunka ba, akwai wani abu a ƙasa ka gaya mini. Baka saba ta’amalli da ƙwayoyi haka ba”.Yayi shiru bai ce komai ba.”Master ka yi mini magana dan Allah ka gaya mini ” tayi maganar cikin matuƙar rauni.”Ki yi haƙuri ki je ki kwanta, dare yayi””Ka san kwana nawa nayi bana iya bacci, saboda damuwar da ka ke ciki? Kallonka kawai nake yi kar na takura maka ina jiran ka yi mini bayanin menene amma shiru, haba master ka gaya mini dan Allah”Ya juyo ya riƙe hannun jauhar, yana murzawa cikin matsananciyar damuwa, ya sunkuyar da kai ya ce “Duk da abun a ɓoye ne, amma bai kamata na ɓoye miki ba, bai kamata na bar abun a raina nikaɗai ba”.Sai a lokacin ya gaya wa jauhar abun da ya faru.”Innalillahi wa Innalillahi raji’un” tayi ta maimaitawa cikin matsanancin tashin hankali.”Master, ka ga irinta ko? Yana ɗaya daga abun da ya sa nake ta fatan ka nesanta kanka da mutumin nan, ya cucemu amma kansa ya yi wa. Baka yi da niyya ba, Allah ya jiƙan Nura ya saka masa”Al’amin ya kifa kansa a kan cinyar jauhar, sai a lokacin ya ji wasu irin hawaye suka zubo masa.”Sadik ya mutu a sanadina, Nura yayi wulaƙantacciyar mutuwa a dalilina, na zama annoba kenan? Mahaifiyar Nura har ta mutu ba zata manta, ni na kai yaron ta, in da ka yi dalilin gurɓata masa rayuwa ba”Jauhar ta girgiza kai ta ce “Dan Allah ka daina faɗar haka master, kowa abun da Allah ya rubuta masa yake riska ba kaine sila ba” tana kuka tana rarrashin sa.Tun da Allah Nura ya mutu, Al’amin ya ƙara nutsuwa, babu abun da yake yi masa daɗi. Ita kanta jauhar ta kasa daina jin ɗacin rashin Nura, dan tun da Al’amin ya ce masa an samo masa aiki a Abuja yake murna, yake bata labarin shi wata yarinya ya gani yake so, kullum sai ya je ƙofar makarantar islamiyyar su idan an taso su ya ganta, yanzu yana fara aiki, idan ya ginawa mama gida a cikin kano, ta dawo sai ya nemi auren yarinyar, amma kar ta gaya wa master.Take yi masa dariya ta ce masa ai mamansa aure take yi sai dai ya haɗo da mijinta, ya ce ya fasa zai yi aure ya ɗaukko ramma ta dawo cikin gari, ta baro ƙauye.Ta ce “Ban da abunku Nura haryanzu fa da sauran ƙuruciyarka, ɗawainiyar aure da yawa fa”.Ya ce “Ni dai kawai ki yi mini addu’a, da na dawo, zan fara zuwa wurin yarinyar nan zance”Da haka tayi ta tuna ire-iren hirarsu, da barkwancinsa, ta kasa mantawa da shi.Al’amin har tofa ya sake zuwa, ya yi wa mahaifiyar Nura gaisuwa, ya kai mata abun alkhairi, ya biya ya gaida Hajiya ya dawo gida.Jauhar cikinta yayi girma sosai, kamar kana fita ka dawo zaka tarar ta haihu, ƙafafuwan ta duk suka kukkumbura, saboda girman cikin, aka ce yana shiga wata tara ayi inducing ɗin ta ta haihu ta huta, dan bayan nauyin cikin kullum cikin haki take, a haka kuma take lallaɓawa ta je makaranta.Wurin shayin Al’amin kuwa, wasu irin kuɗi ne suke shiga suna fita, dan tun safe ake aikin ɗorawa da saukewa, ya zama chamber matasa sosai da sosai, duk da suna sayar da kayan shaye-shayen su a wurin, ba sa cutar Al’amin shi kuma ba ya yi musu mugunta.Da safe su yi shayi, da rana indomie shayi, taliya haka suke wuni saye da sayarwar abinci.Juahar sun gama haɗa kayan haihuwa, dan washegari ne ya kama ranar da za su je ayi mata inducing, tana ta jin tsoro yana kwantar mata da hankali.Ta ce “Master”Ya ce “Mmm””Ka ji sai motsi yake yi, kamar ya san gobe in Allah ya kaimu za a fara inducing ɗin nan”Ya ce “Ya ƙagu ya ga daddynsa, Nuradeenin daddy, in sha Allah sunan Nura zan saka, kamar yadda na yi masa alƙawari”.Ta ce “Allah ya jiƙan Yaya Nura ya sa ya huta”Ya ce “Amin”.Cikin shagwaɓa ta ce “Amma a gabanka zan haihu master, tsoro nake ji, an ce haihuwa akwai wahala fa””Ba wata wahala in sha Allah, ina kusa da ke, ina yi miki addu’a zaki haihu, Ni zai fara gani kafin ya ganki ” yayi maganar yana sumbatar cikin nata.”Ni dai na fuskanci ba a so na, ta babynka kawai ka ke yi” tayi maganar cikin shagwaɓa.”Ni na isa? Dukkanku ina sonku madarata””Ba wani, ni baka taɓa cewa kana so na ba”.Yayi murmushi ya ce “Amma kina gani a aikace ai”.”Baka taɓa faɗa ba”Yayi dariya ya ce “Ai ke da ruwan zinari aka rubuta sunanki a zuciyata. Ina sonki madarata, ina ƙaunarki ƙauna mai tsanani ya fi ubban shadidan”Ta ce “Wayyo Allah daɗi. Wallahi har cikin tsakiyar zuciyata na ji kalaman nan, ba ka taɓa gaya mini ba, ka cigaba da gaya mini, da daɗi”Ya ƙara rungumeta ya ce “I love you madarata””I love you too babyna, kuma baban babyna, masterna abun ƙaunata”Har mamakin irin kalaman soyayyar da suka din ga musaya take yi, da ba ta taɓa tsammanin jin su daga bakin mastern ba.Cikin matsanancin shauƙin so da ƙauna, suka kasance cikin farin ciki. Suka yi wanka, ya rungumota daga toilet tana takawa a hankali da ƙaton cikinta a gaba.Ya taimaka mata, ta saka rigar bacci, sannan suka kwanta, ta kwanta a jikinsa, tayi balance da ta motsa sai yayi mata sannu.Wani irin nannauyan bacci ne yayi awon gaba da ita.Ji tayi kamar ana kokowa a falo, ta laluba ba ta ga Al’amin ba, ga wani irin ƙaurin taba ya cika ko ina.Hasken fitila ta hango an kunna ƙwan falo, ta saukko ta fito falon tayi arba da wasu matasa hannunsu riƙe da miyagun makamai, madaki ta fara ganewa gabanta ya faɗi.Sun rirriƙe Al’amin, suna shaƙa masa wani abu, jikinsa ya saki yana ta layi.Madaki ya bushe da dariya ya ce “Ka ce baka ji, dama ka ce da ni da kai sai wani ya kawo ƙarshen wani, to ni zan kawo naka ƙarshen yau ina dodon da kake taƙama da shi? Duk da zuwan ba nawa bane ba, na uban gidanka ne Indabo, amma ya jaddada mini in tabattar ka tafi da wani mugun miki a zuciyarka”.Cikin tashin hankali jauhar ta janyo jikinta ta nufi in da Al’amin yake tana kiran sunan sa “Al’amin me ka yi musu ne? Dan Allah ku yi haƙuri mana”.Al’amin ko harshensa ya kasa motsawa, balle wata gaɓa ta jikinsa.Madaki ya riƙo gashin jauhar, ya kalleta ya ce “Yanzu kin zama ragowa, ni kuma ba zan ɗana abun da yake ragowar maƙiyina ba, gashi kin zama cuus” ta riƙe ƙasan gashinta da Madaki ya riƙe.Cike da mugunta, ya saka ƙafa ya kawashe na jauhar ta gaba ya saketa, ta faɗi a kan cikinta, ta ƙwala wata irin razananiyar ƙara ta ce “Ya Allah, Ya Allah, Ya Allah” ta faɗa sau uku, take jini ya fara malala daga jikinta, harshen ta kawai take motsawa a hankali tana kiran sunan Allah, ta din ga ɗaga hannunta tana son kiran sunan Al’amin. Ya ƙura mata ido yana kallon ta, cikin buguwa da mutuwar jiki, tun tana ƙoƙarin magana a hankali har ta daina motsi.Madaki ya samu wani ƙarfe ya bugawa Al’amin a ka, shi ma suka sake shi a wurin.

Ayshercool 08081012143.

Back to top button