Kannywood: Yadda jaruman Kannywood suka taya yan Nijeriya murnar samun yancin kai a wani salo
Jaruman dai da suka taya yan Nijeriya murnar samun yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka na Ingila sun haɗar da Aisha Humaira, Fati Washa, Rayya Kwana 90, Teema Makamashi, Tijjani Asasi da dai sauransu.
Kamar yadda kowa ya sani 1 ga watan Oktoba ita ce ranar da Najeriya ta samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Ingila don haka duk shekara ake tunawa da wannan rana, To kamar dai kowa sun Taurarin Kannywood sun bi sahun sauran ‘yan Najeriya don tunawa da ranar samun ‘yancin kai na kasar. Hukumomi a Abuja sun ayyana Juma’a, 1 ga Oktoba, a matsayin ranar hutu. Kasar Afirka ta Yamma ta sami ‘yancin kanta a 1960 daga Burtaniya.
An ga taurarin fim ɗin suna sanye riguna kalar tutar Najeriya, wato kalar kore da fari.
A’isha Humaira ta kasance ɗaya daga cikin jaruman Kannywood wanda ludayunsu ke kan dawo, itama ta taya yan Najeriya murnar shekara 61 da samun yancin kai acikin wani salo na burgewa.
Jaruma Fati Washa ita ma ba a barta a baya ba duk da bata saka kaya masu kalar kore da fari ba, amman dai ita ma ta taya yan Nijeriya murnar wannan rana ta shekara 61 da samun yancin kai.
Jaruma Teema Makamashi ma ba a barta a baya ba wajen taya kafatanin yan Nijeriya taya murnar wannan rana .
Rayya Kwana Casa’in itama ba a barta a baya ba wajen taya yan Najeriya murnar wannan rana
Saratu Gidaɗo wato Mama Daso itama ta yi nata shagalin tare da taya al’ummar Nijeriya da cika shekaru 61 da samun yancin kai.
Tijjani Asasi Damisa wanda yanzu aka fi sani da Kanabaro shida ɗansa suma sun taya al’ummar Nijeriya murnar wannan Rana.