Uncategorized

Tubali Book 1 Chapter 13 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Acan B’angaren Daddy kuwa, shida Dr Lukman, da kuma Alhaji Abdu Tababa ne ke zaune, ad’aya daga cikin hall, na Tababa Company.

Wanda kuma gama meeting dinsu kenan, bayan kowa ya watse ne kuma suka d’auko zance akan Rayyern.

K’wafa Alhaji Idi Sale Dakata’n. Yayi, tare da d’agowa ya kalli abokanan makircin nasa.

“Yaron nan Dr. Rayyern ya tsayamin aka, kullum da zancen kawar dashi nake kwana nake tashi, amma Dan iskan yaro har yau ko gidansu na kasa ganewa, yaron yana nan kamar Maye, duk wani motsin da kayi yakan zama tamkar a tsakiyar tafin hannunsa yake, narasa wanni irin yaro ne, nasa abibiyeshi amma ya gane, binciken da yayi akaina kuma saida ya ninka wanda nayi akansa, yanzu shi babu abunda bai sani ha akaina, yasan gidana yasan komai akan al’amurana, ni kuma har yau bansan inane, gidansu ba, nadaisan acikin Nassarawa G.R.A suke, amma bansan Ina ne taka maimai gidansu ba acikin unguwar, duk iya bincikena na gaza ganewa, karfi da yaji.

 D’an karamin tsako yana nema ya zamarmin ciwon ido, ya kuma zama dole na kawar dashi dole na b’atar dashi adoron kasa, dole yabar numfasawa nan bada jimawa ba, Domin Idan ba haka ba zai jawo babban b’arakar da dinketa zaiyi mana matuk’ar wahala.”

Gyara zama Alhaji Abdu Tababa yayi, cikin son kwantarwa da Alhaji Idi’n hankali yace.

“Karka damu Insha Allah, duk yanda zamuyi sai munyi.

Dan sanin duk wani abu daya shafesa, dole zamu kashe sa.

 Domin barinsa araye hadari ne.”

“K’warai kuwa ai dole ne ma sai ya mutu, batun nemo gidansu kuwa, ku barshi a hannuna da kaina zanyi wannan, Domin ni na mafi bukatar mutuwarsa ayanzu fiye da komai, gaba daya duk ya tottosheni, acikin kaso 100 na daga mutanen da suke zuwa hospital dina, yanzu kaso 80 sun koma masa, kullum da bakin cikin abun nan nake kwana.”

Cewar Dr Lukman. 

Dukansu kwafa sukayi, Yayinda kowannensu ya soma tsara irin bak’ar nufin dake cikin zuciyarsa.

Acan gidan su Rayyern kuwa, da matsanancin farinciki, Mamy take Kallon Abba wanda ya gaya mata batun d’aurin auren Rayyern din.

“Alhamdulillah, Alhamdulillah Allah mungode ma, Lallai Tabbas komai nada lokaci, Yau RAYYERN dina ya zama ango, Allah ya basu zaman lafiya, ya kuma saka al’khairi da al’barka acikin auren, ya kade musu duk wata fitina.”

Da.

“Ameen.” Abba ya amsa.

Batare kuma daya jima awajen Mamyn ba, ya tashi kaitsaye ya tafi wajen Baba Maud’o.

Mamy kuwa cikin tsananin farinciki ta fito falo ta zauna, dai-dai lokacinne kuma Ramadan da Riyyam-nsra suma suka sauk’o k’asa.

Riyyam-nsra ne ya karaso wajen Mamyn da sauri, cikin farincikin da yake ciki ne kuma yace.

“Mamy yaufa Auren Hamma Rayyern, gaskiya ya kamata ace mun d’an shashe, duk da ma auren sirrine amma ai dai mukam ya kamata, mu Dan shana ko Mamy.”

Murmushi Mamyn tayi, tare da dan jinjina masa Kai alaman eh.

Saboda tana cikin farin ciki itama yau din.

Riyyam kuwa waka ya kunna awayarsa, tare dayi musu connecting da tv, nan take kuwa sautin wakan Davido Maisuna Jowo ya soma tashi.

Nanfa Yayi starting video awayartasa, tare da soma rawa wayar na shooting d’insa,  Mamy kuwa dake zaune gudun kada ya shooting da ita ne yasa ta tashi ta koma daki.

Tana tafiya kuwa Ramadan shima ya mik’e yana taya Riyyam-nsra din dancewa dan shi farin cikinsa biyu ne auren Hammansa da kuma samun damar nasa. 

Adai-dai lokacinne kuma Rayyern ya bud’e murfin kofar dakinsa ya fito, jikinsa dauke da danshin ruwan alwala, kasancewar adai-dai lokacin ana ta kiraye kirayen sallan la’asar.

Tun kafun ya gama saukowa akan steps din falon, kuwa yake jin kida na tashi.

Da sauri ya dan karaso cikin falon. 

Abunda ya ganine kuma ya sashi tsayawa, tare da dakawa su Riyyam din tsawa, fuska a murtuke yace.

“Mekukeyi haka, wannan wanni irin haukan banzane, ya zaku mayar mana da gida kaman filin gala ko club? Akan meye zaku cika mana gida da kide-kide, saboda meye akan wani dalili??”

Cikin fada sosai ya kare maganar.

Wanda hakan yasa Zakariyya Dan langwabar da kansa.

“Eyyah Hamma Rayyern Dan Allah ka barmu, yau fa ranar farinciki ne ranar auren babban yaya.” 

Harara Rayyern din ya watsa masa, kana cikin takaici yace.

“Nabaku nanda 1mn ku tsaida kidannan, sannan lokacin sallah yayi, kuje kuyi alwala ku wuce masallaci.”

Baki Riyyam-nsra din ya dan turo gaba, dai-dai lokacin kuma Mamy ta fito daga cikin dakinta.

Kallon Mamyn Rayyern yayi, tare da d’an narkar da fuska yace.

“Mamy yaran nan basa ji, wai kida suke kunna mana acikin gida, kuma Mamy kinajinsu amma kika kyalesu.”

Murmushi Mamyn tayi tare da cewa.

“To Rayyern me kakeso nayi musu, na hanasu nishadi? Bayan ni kaina yau din farin cikin dake zuciyata bazai misaltu ba, yaufa aka daura maka aure, kaga Aikuwa ya zama dole muyi farinciki.”

Fuskarsa yadan narke, kaman zaice wani abu kuma saiya fasa kaitsaye ya fita tare da wucewa zuwa masallaci.

Yayinda su Riyyam-nsra da Ramadan kuwa suka haura sama dan gabatar da nasu alwalan.

Rayyern kuwa Koda yaje masallacin, bayan an idar da sallah, kaitsaye company d’insa ya sake komawa, yayi hakanne kuma saboda kwata kwata bayason zama haka har wani tunani ya dameshi.

Yayinda su Ramadan kuwa bayan sun idar da nasu sallan, suka shiga gari, musamman kuma suka yada zango a Green park, nanfa Riyyam-nsra ya shiga aikin yi musu Video, yana sending direct to Tiktok, daga karshe ma live ya fara yi.

Daga nan masaukinsa Ramadan ya wuce dole yasa Riyyam-nsra kwatso kwamutsansa suka taho gida.

Basu ne suka dawo gidan ba kuma, saida akayi sallan magriba.

Bayan sun dawo dinne kuma suka shirya kayan Riyyam-nsra sukayi al’wala kana suka wuce masallaci.

Rayyern kuwa har saida aka idar da sallan Isha kafun yake dawowa gida.

Anan falo ya samesu dukansu suna dinner.

Shigowarsa ne kuma yasa Mamy sakin murmushi, cike da kulawa tace.

“Yauwa Babana ka dawo ko, yanzu nake zancenka araina, zo kaci abinci.”

Kansa ya dan langwabar tare da Karasowa dining table din, 

“Na nakoshi.”

Ya fad’a akasalance.

Wanda hakan yasa duk suka tsura masa ido, musamman Abba.

Shikuwa Rayyern still sake kwab’e Fuskarsa yayi, tare da dubansu yace.

“Ni baccima nakeji saida safe.”

Yana gama fadin hakan kuwa, baijirayi me waninsu zaice ba kaitsaye ya haura Sama.

Da Kallo Abba ya bisa, Yayinda acikin ransa yake mamakin halin Rayyern din, daga daura masa aure kawai lokaci daya harya sanja, sai kace wani mai aljanu.

Da haka dai suka ci gaba da cin abincinsu, bayan sun kammala ne kuma Abba ya koma dakinsa, Yayinda Ramadan Riyyam da Mamy kuwa suka zauna afalo, suna yar tab’a hira.

11:30 pm.

Gaba d’aya ko ina dake Cikin gidan, yayi shiru babu wani alaman kwakkwaran motsi dake tashi, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar duk wasu mutannen dake zirga-zirga acikin gidan sunyi bacci.

 

Haka ma compound din gidan babu kowa, ko ina shiru.

Daga can gefe kuwa, gaba daya guards din da suke gadin Jannart ne kwance, kowannesu ya sake katon baki da ciki, suna bacci kamar matattu.

Ind daga gefensu kuwa Baba Ado ne zaune, yana rik’e dayar radion sa.

Sai kuma  Ashiru dake bakin gate, yana ta faman lellek’awa tako ta Ina, gudun kada su aikata kifi na ganinka mai jarkoma.

Acan cikin gidan kuwa, Momy ce ta fito daga cikin dakinta, cikin shirin kayan bacci, kaitsaye kuma dakin Daddy ta nufa.

Jannart dake tsaye acikin dakinta kuwa, Idanunta dake zubar da hawaye ta lumshe.

Wani iri takeji, Yayinda acikin ranta kuwa take cewa.

Inama da zata iya bijirewa umarnin Abba Kabir din, da zatace itakam ta fasa, da zata zauna agidansu da dadi ko ba dadi, tayarda kaddarar ta ce tazo a haka.

To amma ya zatayi?  Bata da wani zabi ako da yaushe, tasani zatayi kewar gidansu sosai, zatayi kewar dakinta da kuma yan uwanta.

“Zanyi kewarka Daddy na, zanyi kewar Momy da Abdull, nasani zanyi kewar duk wani abu daya shafeni, Daddyna baya tab’a takuramin, bayayimin komai, kawai dai baya daukan mataki akan duk wani cin zarafi da Yah Junaid zaimin.”

Ta fadi hakan hawaye na ci gaba da zubowa akan fuskar ta.

Cikin sanyi da mutuwar jiki kuma ta d’auki yar jakar da ya hade komai nata na amfani aciki.

Drawernta ta bud’e tare da zaro, wani hijab mai kyau hadi da tsananin taushi ta zura akan, Daguwar rigar, Arabian gown dake jikinta.

Juyawa tayi Ahankali ta nufi kofar fita daga dakin, Yayinda tabar wayarta da goro da kuma sweets din da Abba Kabir ya bata atsakiyar gadon dakin.

Harta Kai bakin kofar fita ne kuma ta juyo, ta sake Kallon cikin dakin nata.

Lokaci daya kuma hawaye ya cigaba da sauka akan fuskarta.

Saidai kuma babu yanda ta iya, haka ta murda handle din kofar, cikin sand’a ta fice.

Fitowar nata ne kuma yayi dai-dai da wulgawan Momy, wanda ta wuce dakin Daddy.

Saurin komawa baya tayi ta labe.

Harsaida ta tabbatar da wucewan Momyn kafun ta fito, cikin tsananin sand’a take tafiya.

 Harta karaso Cikin falon da Kwata Kwata babu yalwan haske acikinsa.

Handle din kofar falon ta murda Ahankali, bayan ta fito ne kuma ta maida kofar ta rufe.

Dai-dai lokacinne kuma Abdull wanda ya fito daukar ruwa, yaji kaman karan rufe kofa, saurin maida kallonsa ga kofar yayi, saidai ko alaman motsi baiga kofar tana yiba, gashi kuma babu kowa acikin falon, hakan yasa yayi tunanin ko kunnuwansa ne basu jiye masa dai-dai ba, kasancewar yana gigin bacci, bayan ya d’auki ruwanne kuma ya juya ya koma dakinsa.

Jannart kuwa Koda ta fito compound din gidan, cikin sand’a take tafiya, wanda hakan yasa Baba Ado dake tsaye yi mata alama akan tayi sauri.

Yayinda shikuwa  Ashiru ya fita ya lellak’a musu waje,  ganin babu kowa a arean wajenne kuma, yasa Ashirun daga mata hannu akan tazo ta wuce.

Aikuwa cikin sauri, da kuma tarin fargaban da takeji ta zo ta fice daga cikin gidan.

Yayinda Baba Ado shima ya rufa mata baya.

Ganin ficewar nasu ne kuma yasa Baba Ashiru maida kofar ahankali ya rufe.

Jannart kuwa tafiya suke ita da Baba Ado, wanda ya riga da yayi gaba, ita take biye dashi abaya. 

Tafiya kuwa sukayi mai dan tsawo.

Kamar kuma yanda Abba Kabir din ya fad’a, kwana Uku suka shiga, ata ukunne kuma suka hango motarsa.

K’arasawa sukayi da sauri, inda Baba Adon kuma da kansa, ya budewa Jannart din gidan baya ta shiga ta zauna.

Kallon Abba Kabir din yayi, kana yace.

“Barrister Allah Yatsare ya kuma, taimaka akan duk wani abu da kukasa gaba, Allah Ya tono gaskiyar da ake boyewa.”

Da Ameen Barrister Kabir din ya amsa, Yayinda shi kuwa, Baba Ado ya juya Cikin sauri ya nufi hanyar komawa gidan, yana isa gidan kuwa, Baba Ashiru ya bud’e masa kofa.

Sa d’ab sad’ab haka ya shiga cikin mayan guard dinnan ya kwanta.

Barrister Kabir kuwa tada motar tasa yayi suka bar wajen.

Kaitsaye kuma Nassarawa G.R.A suka nufa.

Ita dai Jannart tunda ta shiga motar, ta kwantar da kanta ajikin kujera, hakanan takejin kanta wani iri.

Tafiyar mintuna kadan sukayi, suka shigo Cikin unguwar.

Adai-dai gaban babban gate din gidan, kuma Abba Kabir ya tsaya tare da dan danna horn.

 Ari dake zaune ne ya taso ya bude musu, kasancewar Baba Maud’o karatun Qur’ani yakeyi shiyasa, Arin bai katseshi ba kuma dama Abba da Rayyern sun hanashi ziryar buɗe gate.

Ana bud’e gate din kuwa, Barrister Kabir ya tura hancin motar tasa ciki.

Bayan ya gama dai-dai-ta parking din motar ne, kuma ya bud’e b’angaren da yake ya fito.

Karasowa wajen su Baba Maud’on da yanzu ya shafa addu’a.

Isa garesa  yayi, cikin girmamawa da kuma sakin fuska, ya bawa Baba Maud’on hannu suka gaisa.

kana yace.

“Dan Allah Baba Maud’o ko zaka iya nemamin iso zuwa cikin gidan.”

Murmushi Baba Maud’o yayi, tare da mikewa tsaye yace.

“Babu komai, Barrister bari nayiwa Alhajin magana.”

Kai Barrister Kabir ya jinjina, Yayinda shikuwa Baba Maud’o kaitsaye ya nufi cikin gidan, Koda ya karasa jikin  kofar, kwankwasawa yayi tare dayin sallama.

Abba dake zaune afalo kuwa, Jin muryar Baba Maud’o ne, yasashi mikewa tsaye.

Tare da tasowa yazo ya bude kofar.

 

“A’a Baba Maud’o kaine.”

Abban ya fada.

Inda Baba Maud’o kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa.

”Ni ne Alhaji dama Barrister Kabir ne yace na nemama masa iso.”

Murmushi Abban ya fadada, tare da cewa.

“Masha Allah kace masa ya shigo.”

Da To Baba Maud’o ya amsa, kafun ya juya kaitsaye ya nufi wajen da Barrister din ke tsaye.

“Yace ka isa.”

“To To masha Allah Nagode sosai.”

Barrister Kabir din ya fad’a, yana me bud’e murfin motar, nan b’angaren baya inda Jannart din take.

Wanda kuma tad’an rufe gefen fuskarta, da tattausan hijabin dake jikinta.

Hannunta Abba Kabir din ya kamo, tare da cewa.

“Jannart fito, amma ki fito da kafar dama sannan ki rike addu’a a bakinki.”

Kanta ta Dan jinjina, cikin kuma sheshshekan kukan  da yaso kwace mata ta fito daga cikin motar.

Sosai takejin kirjinta na wani irin bugawa, ga kuma wani nauyi da takeji acikin zuciyarta.

Yayinda hawayen dake cikin idanunta kuwa har yanzu suka kasa tsayuwa,  shin wanni irin kulline acikin rayuwarta da har yasa akayi mata irin wannan auren?

“Masha Allah mu isa To.”

Baba Maud’o ya fad’a, yana me shigewa gaba, shikuwa Abba dake rike da hannun Jannart ya rufa masa baya.

Koda suka isa bakin kofar falon kuwa, Abba da kansa ya taso ya bud’e musu.

Tare da yi musu iso, cikin tsananin farinciki da jin dadi.

Karasowa cikin falon sukayi, Inda Abba Kabir din ya Zaunar da Jannart akan lallausan carfet din dake cikin falon.

Kana ya zauna asaman kujeran dake gefenta.

Abba kuwa Kallon Ramadan  yayi, kana fuska asake yace.

“Ramadan jeka kiramin Rayyern.”

To Ramadan ya amsa, tare kuma da mikewa cikin sauri ya haura sama dan kiran Rayyern.

Rayyern dake kwance yana latsa system d’insa, jin muryar Ramadan dake knocking yasashi bada izinin shigowa.

Bud’e kofar Ramadan yayi ya shigo.

Cikin girmamawa, yace.

“Hamma Rayyern Abba na kiranka.”

Kai Rayyern din ya jinjina,  Yayinda Ramadan kuwa ya juya ya tafi.

Koda ya dawo falon, cewa Abban yayi Rayyern din yana zuwa.

Kai Abba Ya jinjina, tare da cewa.

“Masha Allah to kaida Riyyam kudan bamu waje.”

Babu musu kuwa, duk suka Mike suka nufi steps din sama.

   Suna haurawa kan steps din kuma Rayyern yana sauk’owa.

Kallonsa Ramadan yayi, tare da d’an gumtse dariyar farin cikin dake cinsa na sanin yanzu shine a layi.

Shikuwa Rayyern wani irin masifeffen kallon  ya watsawa Ramadan, musamman alokacin daya sauke idanunsa akan Barrister Kabir da yake Zaune acikin falon.

Hakan yaji wani irin takaici ya cika masa zuciya sabida anfa dameshi matuka an hanashi salama.

Su kuwa Ramadan da Riyyam-nsra neman waje sukayi suka tsaya, Acan saman stairs din.

Yayinda shikuwa Rayyern jiki asanyaye ya karasa saukowa cikin falon.

Inda Barrister Kabir ke zaune agaban Abba, still kuma har yanzu yana rik’e da hannun Jannart wanda ta sunkuyar da kanta k’asa.

Abba kuwa Kallon Barrister Kabir din yayi, cikin tausasa Murya yace.

“Barrister daka koma sama ka zauna, Domin aduk sanda kazo gabana ka zauna akasa sai naji abun yamin nauyi.”

Murmushi Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutum tawa yace.

“Babu komai Alhaji, zamana a k’asan bawai gazawa bace, kuma hakan yana da dalili.”

Kai Abban ya jinjina.

Tare kuma da kai dubansa ga Rayyern wanda ya karasa shigowa cikin falon.

“Zoka zauna anan Rayyern.”

Abban ya fada yana me nunawa Rayyern gefensa, kuma kusa da Mamy dake zaune.

Yayinda Jannart kuwa hawayen Idanunta, kwata-kwata sun kasa tsayawa, saboda yanda kukan ke neman cin karfinta ne kuma yasa har shashshekan kukan nata ya Dan soma fitowa. 

Idanu duk suka zubawa Jannart din da kanta ke k’asa, Yayinda tsananin tausayin yarinyar ke sake lullub’e zuciyarsu, musamman ma Mamy da taji son yarinyar acikin zuciyarta, duk da cewar bata ga fuskar yarinyar ba, amma taji ta kwanta mata.

Rayyern kuwa yanda ya dauke kansa gefe, tamkar ma baisan da wata mai sakin sheshshekan kuka acikin falon ba.

Abba Kabir kuwa gyara zamansa yayi, tare da sake rike hannun Jannart kam, cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace.

“Alhamdulillahi.

 Yau gani na  agabanka Alhaji Bashir, ga y’ata nan Jannart na kawota gareku”.

Sai kuma  ya ɗan numfasa kana a hankali yaci gaba da cewa.

“Bansanku ba baku sanni ba, amma musulumci ya had’a mu kamar yanda manzon Allah yace, Almuslimu ak’ul muslim, musulmi d’an uwan musulmi ne,  na nemi taimako kunyi mini, har lau kuma Ina sake neman taimakonku, akan kulawa da y’ata Jannart, da kuma rik’emin amanarta, Jannart amanace awajena numa kuma nima yau zan baku amana, arikemin Jannart Amana marainiya ce, Dan Allah ku rikemin amanarta, Jannart bata da laifi, jarrabawar rayuwace tazo mata ahaka.

Kana  bata da tashin hankali, Jannart yarinyace mai tsananin biyayya, haka kuma mai tausasshiyar zuciya, Jannart yarinyace mai rauni, yarinyar da maraici ya cika gaba daya rayuwarta, Ina da tabbaci akan biyayyar Jannart.

 Domin yarinya ce da take gudun bacin ran wanda ke kusa da ita, Idan tayi muku ba dai-dai ba ku hukuntata kamar yanda zaku hukunta y’ay’an cikinku.”

Dan tsagaitawa da maganan nasa yayi, saboda yanda Hawaye ke sauka akan fuskarsa.

Juyowa da kallonsa yayi ya kalli Mamy, cikin sanyin jiki yace.

“Hajiya ga Jannart nan na kawo muku Amana, Dan Allah ki rikemin ita, ki dauketa tamkar yar da kika haifa acikin cikinki, Dan Allah ku killacemin Jannart, banason ko k’ofar gida ta l’eka, Idan kuma akwai buk’atar fitar ta wanda ya kama da dalili a gayamin, saboda banason idanun wasu su sauk’a akanta.

Domin fataucin rayuwarta sukeyi, tamkar wanda yaje farauta yagaji bai samu komai ba, haka suke ayanzu, da zaran lokaci ya cika akanta zasu dire, suna son su kasheta, suna tsananin son ganin bayanta, 

Alhamdulillah yau inajin na sauke wani nauyi akaina…”

Kasa karasa maganan nasa yayi, saboda kukan da yakeji na tasar masa.

Yayinda Jannart kuwa tuni kuka yaci karfinta, ba abunda ke tashi kuwa face sautin kukan ta.

Wanda hakan yasa gaba daya su Abba, Mamy, da Baba Maud’o duk jikinsu yayi sanyi.

Shikuwa Rayyern zuwa yanzu ya tankwashe kafafunsa, tare kuma dayin shiru, ya sunkuyar da kansa k’asa.  

Haka kuma yakejin kansa na.

 Dan sarawa, Yayinda yakejin jijiyon dake cikin kannsa nayi masa ciwo.

Badon komai ba kuma saidan saboda yanda yakejin kukan yarinyar na hawa kanshi.

Barrister Kabir kuwa Hannun Rayyern din ya kamo.

Da sauri Rayyern ya ɗago kansa ya kalleshi.

Sai kuma yayi ƙasa da ida nunshi ganin yadda mutumin mai girma yana kuka.

Shi kuwa Barrister Kabir.

 cikin sanyin da jikinsa yayi yace.

“Rayyern ga amanar diyata matarka”.

Ya ƙare mgnar yana mai ɗago hannun Jannart ya saka acikin tattausan tafin hannun  Rayyern din tare dasa nashi hannun ya rumtse tafin hannun Rayyern dake riƙe dana Jannart ya rumtse ya haɗe su…!

 Wani irin raunataccen kuka ne ya kwabcewa Jannart cike da rauni shessheƙan kukan yake fitowa, yana ratsa kunnuwansu.

Banda kukan Jannart dake tashi, shiru gaba d’aya falon ya d’auka.

Yayinda Rayyern kuwa ya sunkuyar da kansa k’asa, tare kuma da rumtse idanunsa gam dan jin fatan saman idonsa nata karkarwa.

Domin kuwa adai-dai lokacin da hannun Jannart din ya sauk’a acikin nasa hannun, wani irin harbawa zuciyarshi  tayi tare da buɗewa da azaban ƙarfi.

Duk da cewar kuwa ba wannan bane first time nasa daya fara tab’a jikin mace, musamman Idan akayi duba da irin yanayin aikinsa, saidai kuma a iya tsawon rayuwarsa, bai tab’a rik’e jikin mace, da sunan wai dan yaji wani abu ajikinsa ba, yana rikewa ne kawai idan takama dole, enfact ma shi baicika son duba mata ba, sai idan abun yayi worst ya kuma zama lallai dole shidin ake da buk’atar ya duba su.

Sam bai tab’ajin wani abu makamancin haka ba.

Tamkar kuma yanda zuciyar tasa ke bugawa haka ma Jannart, da itama takejin wani irin bugun zuciya, badon komai ba kuwa saidan samun hannunta da tayi acikin nasa, haka kuma Wannan shine karo na farko a rayuwar ta, da wani d’a Namiji wanda bata sani ba kuma ba Muharraminta ba ya tab’a jikinta,  domin kuwa Bayan Yah Junaid, Daddy, Abba Kabir, Abdull, sai kuma Dr Lukman wanda ya kasance Dr dinta ne, babu wani wanda ya tab’a kama Koda farcenta ne, sai wannan ayanzu da hannunta yake cikin nasa.

Wanda kuma hakanne yasa taji zuciyarta tayi mata nauyi, Yayinda duk wani rauni dake narke acikin zuciyarta ya sake hauhuwa, lokaci daya taji tamkar wani mafakan kuka ta samu.

Dan tsabar kukan dake cinta har wani seizing numfashinta keyi.

Cikin muryarta da ta dashe sosai, ta saki Sabon kukan da sauti da amonsa ya zarce na baya mai cike da rauni.

 Domin ayanzun kuka take da duka zuciya da gangar jikinta, kukan dake bayyana tsananin tarin damuwa da maraicin rayuwarta, kukan dake bayyana rauninta, haka kuma kukan da yasawa kowannensu matsanancin tausayinta.

Musamman Mamy da gaba daya k’walla ya cika mata idanu. 

Rayyern kuwa har yanzu idanunsa a rumtse suke, saboda yanda sautin kukan nata ke ratsa cikin kunnuwansa, yasa gaba d’aya yaji kansa na juyawa, Sam bayason wani hayaniya ko kuma yawan koke-koke, kwakwalwarsa bata iya jure hakan.

Abba Kabir kuwa wasu irin hawaye masu zafi ne, suka gangaro daga kan fuskarsa,  sake matse hannunsu awaje daya yayi, cikin kuma muryarsa da tayi rauni sosai yace.

“Rayyern ga amanar y’ata Jannart na kawo maka, ayanzu kaine Mijinta majiɓamcin lamuran rayuwata, kaine kuma wanda nakesa ran zaka zame mata Garkuwa, Rayyern Jannart marainiyace, wacce tataso acikin kad’aici da tarin damuwa, Jannart batasan wani farinciki ba Rayyern.

Domin ako da yaushe damuwa da kuma fargaba suke cika zuciyarta, Karikemin amanar Jannart Rayyern, Domin ayanzu duk wani motsinta yana karkashin kulawanka ne da ikonka,  Jannart ta rayu akan wata turba ta daban, sannan an tarbiyantar da ita akan biyyya da kuma karb’an umarni akan duk wani abu da aka sata, ko kad’an bani da haufi akan Jannart, Domin kuwa Ina da tabbaci akanta, nasani Jannart bazata tab’a sab’amaka ba Rayyern idan kuma ta saɓa maka to ajizancin ne da yake halittar ɗan Adam.

Dan Allah ka kula da ita, Koda ace bazaka dauketa awani matsa yi na musamman ba, To Ina fatan ka karb’eta amatsayin k’anwarka, Jannart tana buk’atar kulawa Rayyern, tana kuma buk’atar farinciki, saboda ita din Marainiya ce…”

Ya Kai k’arshen maganan cikin muryarsa dake rawa, hadi da alhinin sark’ak’iyar dake cikin rayuwar Jannart din.

Ahankali kuma ya dawo da kallonsa ga Jannart din, cikin matukar sanyin murya da kuma son kwantar mata da hankali yace.

“Jannart ga Mijinki nan, kiyi masa biyayya kamar yanda kika saba, ki kuma gujewa duk wani abu dazai b’ata ransa, Dan Allah Jannart ki kiyaye kinji, Insha Allah watarana zaki samu ingantaccen farinciki, watarana duhu zaiyaye inda haske zai cika cikinsa, ako wani bayan kunci akwai farinciki,sannan ako wani bayan k’addara akwai sauki, komai da muke yi yanzu da kuma wanda zamuyi anan gaba, rubutacce kuma tsararrene, wanda Allah ya tsara mana,  babu wata damuwa da zata Tabbata Jannart nasan kinyi imani da hakan.”

D’an tsagaitawa Abba Kabir din yayi, cikin kuma hawaye dake zuba a idanunsa, ya zare hannunsa dake saman nasu, tare da tallafo fuskarta, ya sumbaceta akan goshinta.

“Zan tafi Jannart, ki kula da kanki, kada ki sab’awa kowa dake cikin gidannan, Domin ayanzu sune y’an uwa kuma Garkuwarki.”

Abba Kabir din ya fad’a yana me kokarin mik’ewa tsaye.

Jannart da kuka ya riga daya ci karfinta, saurin rik’o k’afafunsa tayi, tare da sake fashewa da kuka.

 Domin hakanan takejin kamar Idan ya tafi bazai dawo ba, tayaya zata iya jure zama amatsayin matar aure?

Hakan wani rayuwane da bata sanshi ba, batasan wacce irin kalubale ne zata fuskanta ba, Tabbas ta sani acikin rayuwarta gaba d’aya duhu ne, ita da batasan menene cikakken fari ciki ba, tayaya zata iya bawa wani?

Rayyern kuwa cikin takaicin kukan nata dake shirin fasa masa kwakwalwa ya zare hannunsa, tare da kawar da kansa gefe, yana  mejin tamkar yasa hannayensa ya toshe kunnuwansa ko bakinta.

Abba Kabir kuwa kukan da Jannart din keyi ne ya matuk’ar karyar masa da zuciya.

Ahankali ya d’an sunkuyo, tare da kama kafad’un Jannart din cikin tausasawa hadi da rarrashi yace.

“Jannart din Abba ki daina kuka, tafiyar da zanyi ayanzu bawai yana nufin bazan dawo bane, Lallai Zan dawo Jannart, ki saki ranki ki dauka nan tamkar gidanku ne, kuma suma iyayenki ne, kamar yanda muke kulawa dake haka suma zasu kula dake, ako da yaushe Ina miki fatan al’khairi  da nasara Jannart, Allah ya sanya al’barka acikin rayuwar aurenki.”

Cikin matsanancin kukan dake addabarta, ta Dan soma jujjuya Kai.

Ganin hakanne kuma yasa Mamy da ta kasa tsaida ruwan hawayen daya zubo daga cikin idanunta tace.

“Zo Jannart kema y’atace kamar yanda su Rayyern suke yayana, ki daina kuka kinji, Insha Allah zan zame miki  mahaifiyar dake share kukan yayanta,  ki sa aranki kuma cewar kina tare da mahaifiyarki ce, ki kalleni amatsayin wacce ta haifeki, bawai matsayin suruka ba, ni kuma har abada zan rikeki amatsayin y’a, Domin dama Allah baibani y’a Mace ba,.

  To yanzu gashi ya turo min ke amatsayin kyauta biyu, y’ata kuma suruka ta, Insha Allah bazamu bari kiyi kuka ba.”

Mamyn ta fad’a tana me jawo Jannart din jikinta, tare da kwantar da kan Jannart din akan cinyarta.

Hakanne kuma yasa Jannart din, lafewa ajikin Mamyn tana sakin sheshshek’an kuka akai akai.

Abba kuwa da Baba Maud’o duk mik’ewa tsaye sukayi, saboda Ganin Barrister Kabir din da sukayi ya mik’e.

Koda ya soma tafiya, Mara masa baya sukayi, Dan yi masa rakiya.

Suna fita daga cikin falon, kuwa Rayyern da yake jinsa tamkar akan k’aya ya mik’e tsaye, ko kallon inda Jannart din take kuwa baiyi ba, kaitsaye ya haura sama, yana Jin tamkar shi dinma ya fashe da kuka suyi tayi a tare tsabar takaici, haka kawai an takura yarinya.

Tazo da wani shegen kukanta tazo ta saukar masa da ciwon Kai.

Mamy kuwa, hannu tasa ta soma sharewa Jannart din hawayen dake kan fuskarta, wanda kuma saboda tsabar kukan da tayi, har saida idanunta suka zama jajur.

“Kiyi hakuri Jannart, ki daina wannan kukan kinji, haka rayuwar kowacce ya mace yake, Aranar da aka rabata da gidan iyayen ta, saboda haka hakuri zakiyi, da sannu kuma zaki saba da zama damu,

 ba amatsayin surukata kawai kike ba, ke y’ata ce.”

Mamyn ta fad’a tana me shafa bayan Jannart din alaman rarrashi.

Saidai kuma duk da haka Jannart din ta kasa tsaida hawayen dake kwaranya daga cikin idanunta, kukan ya riga dayaci karfinta, duk yanda taso tsaida kukan nata ita kanta ta gaza, amma saidai jin  kanta da tayi ajikin Mamyn, ya d’ansa zuciyarta tayi sanyi ko yanzu tasan ta samu madadin Mom.

Yayinda Acan waje kuwa har bakin mota Abba da kuma Baba Maud’o suka rako Barrister Kabir.

Ganin yanda shi kansa damuwa ke bayyane akan fuskarsa ne kuma yasa Abba da kansa yace.

“Ka kwantar da hankalinka Barrister, Domin kamar yanda ka aminta damu, ka d’auko Jannart ka kawo mana ita cikin gidannan Insha Allah, bazamu bari hawayenta su zuba ak’asa ba, zamu zame mata iyaye na gari, idan tayi rayuwar maraici abaya Ina mai tabbatar maka da ayanzu Jannart bazata sakeyin rayuwar maraici ba, Zamu zame mata Garkuwa da yardar Allah, ka bamu amana kuma zamu rik’e, Jannart ba zata sakeyin kukan kadaici da maraici ba, zamu bata duk wani farinciki.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da kamo hannun Abban yace.

“Nagode kwarai Alhaji Bashir, Lallai Tabbas yanzu na sake gamsuwa da cewar, na kawo Jannart inda ya dace, na kawota inda za’a bata kulawa,  inda bakuma za’a bari tayi kunci ba, Alhamdulillah Allah ya tayaku rik’o”. 

“Ameen.”

Abba da Baba Maud’o suka amsa.

Hannu Barrister Kabir din ya mik’awa, Abba da Baba Maud’o suka sakeyin musabaha.

Bayan yayi musu sallama ne kuma ya bud’e motarsa ya shiga,  Ari ne kuma ya bud’e masa gate din gidan ya fice.

Har acikin ransa yana mejin gamsuwa na abunda ya aikata, Domin yasani acikin abunda ya aikatan Kwata-kwata babu kuskure, Allah yaga zuciyarsa da kuma kyakkyawan nufinsa.

Burinsa shine fito da gaskiyar da azzalumai suka b’oye, wanda kuma yake da tabbacin Allah zai bashi sa’a, akan dukkan komai, Domin Allah ba azzalumin kowa ba ne, saidai wanda ya zalunci kansa.

Su Abba kuwa ganin tafiyarsa ne, yasa Baba Maud’o wucewa makwancinsa kaitsaye, inda shi kuwa Abba juyawa yayi ya koma cikin gidan. 

Barrister Kabir kuwa kaitsaye gidansa ya nufa.

Koda ya isa cikin gidannsa karfe 12:40 na dare. 

Kaitsaye dakinsa ya wuce, bayan yayi wanka ne kuma Aunty Dijat ta kawo masa Coffee.

Sai-dai ganin yanda gaba daya jikin mijin nata ke sanyaye ne yasa, ta gyara zama tare da kamo hannunsa, cike dason basa kwarin guiwa tace.

“Ka kwantar da hankalinka Abban Hafeez, Domin nasan duk wani abunda ke damunka, ayanzu bai wuce akan Jannart,  meyasa zaka damu Abban Hafeez, bayan kasan cewar wannan auren shine abunda zai kawo sauyi da farinciki acikin rayuwar Jannart, wannan auren shi zaisa Jannart tasan wacece ita, shi ne kuma zai warware mata duk wani k’ulli dake cikin rayuwarta,  Tabbas wannan auren al’khairi ne, kuma Insha Allah akwai lokacin da Jannart zatayi al’fahari da wannan Auren, musamman alokacin da ta gano cewar ka zab’a mata miji, mai nagarta irin wanda bashida saukin samu, sannan ka ceci rayuwarta daga sharrin mak’iyan dake kewaye da ita, way’anda take kwana acikinsu, take tashi batare da ta sani ba.” 

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, Cikin samun karfin guiwa kuma yace.

“Insha Allah Jannart zatayi farinciki, komai kuma zai yaye, ayanzu duniyarta zatayi sanyi, Domin tafita daga cikin magauta, hakika ko ayau na mutu, nasan na mik’a Jannart ga inda za’a tsaya mata, inda babu wani maitsaurin ido daya isa zuwa yaci mutumcin ta, saboda Rayyern ba kanwar lasa bane ba kuma mutum bane kamar kowaba, shi na musamman ne domin naga tsoronshi cikin idanun Magautan nasa da Jannart.

Tun ran forko kuma dana ganshi ya tunomin wani ma irin zarrarsa a tsakiyar su Yaya idi wanda sukayi nasarar kaudashi a duniya.

Sai naketa kamar Allah ya turo Rayyern garesune dan ya tono jiyansu ya tsaida yau ɗinsu ya birkita gobensu yadda yake musu mgna kamar ɗan fansa ne, Insha Allah kuma watarana Jannart sai ta zamo wani sashi na jikinsa.”

Murmushi Aunty Dijat tayi, saboda ta fahimci kalaman da mijinnata ke nufi.

Acan gidan su Rayyern kuwa, Koda Abba ya dawo cikin falon, anan ya sameta zaune ita da Jannart din, da har yanzu ta kasa daina zubda hawaye.

Zama Abban yayi

Tare da tausasa muryarsa cikin aminci yace.

“Jannart”.

Wani irin sanyi taji muryar Abba ya sakar mata.

Shi kuwa a mutunce yace.

“Jannart d’ago kanki ki kalleni.”

Jannart dake sakin shesshekan kuka, sake Jin Muryar Babban mutum acikin kunnuwanta ne yasa ta d’ago kanta Ahankali, da kuma Idanunta wanda sukayi luhu-luhu ta kalleshi.

Kai Abban ya girgiza, kana cikin lallashi da ban baki yace.

“Kada kiyi mini wani kallo na daban Jannart, inaso ki kalleni amatsayin mahaifinki, ni Babanki ne, kada ki ajiyeni amatsayin suruki kawai, saboda na daukeki ne amatsayin y’a, wanda har abada kuma bazan tab’a bari kunci yayi tasiri acikin zuciyarki ba, wannan gidan kada ki daukeshi amatsayin gidan aurenki kawai, ki daukeshi amatsayin gidanku,  kafun yanzu bamu sanki ba, amma ayanzu kedin tamuce, kin zama daya daga cikin iyalinmu, munzama iyayenki ke kuma kinzama y’armu, Ramadan ya zama shak’ik’in d’an uwa agareki, dama kuma duk wani wanda yake tare damu, duk wani damuwa da ya dameki kuwa ki sanar mana.

 Insha Allah zamu magance miki ita, saboda haka ki daina kuka kinji, kisa aranki cewa muna tare dake, kuma Allah Ma yana tare dake.”

Kanta ta d’an jinjina, saboda yanda kalaman Abban sukayi tasiri a zuciyarta, duk da cewar ta kasa tsaida hawayen dake zuba acikin Idanunta.

Cikin sanyi hadi da muryarta wacce bata fita sosai tace.

“Nagode Abba, nagode da karamcin da kukayi min Allah ya kara girma.”

Murmushi Abban yayi, kana cikin jin dadin biyayyar yarinyar yace.

“Ba komai Jannart, Insha Allah zamu zame miki iyaye na gari, Mamyn Rayyern Ina Rayyern din kuma ya tafi.”

Ya ƙare mgnar yana kallon Mamy.

“Rayyern ya haura sama.” Mamy ta fad’a tana murmushi.

Kai Abban ya jinjina, kana cikin kulawa yace.

“To dare na tayi, ki Kai Jannart masaukinta ta kwanta.” 

Ya ƙare mgnar yana nuna mata side din da zata kai Jannart ɗin.

To Mamyn tace, tare kuma da kama Hannun Jannart din suka nufi, wata had’add’Iyar k’ofa dake nan cikin falon, kusa da side din kitchine da kuma dining area. 

Ahankali Mamy ta tura k’ofar d’akin.

“Ki shigo da bismillah.”

Mamyn ta fad’awa Jannart Cikin kulawa, hakan kuwa akayi da bismillah Jannart ta jefa k’afarta ta dama acikin falon.

Falo ne mai kyaun gaske wanda aka k’awata cikinsa, da wasu had’add’un royal cushions masu kyau, sai kuma labulayen da aka k’awata jikin window dana bedroom door dashi,  atsakiyar falon kuwa, wani lallausan carpet ne maikyau da girma, sai kuma babban tv’ plasma’n da aka daurasa akan wani babban tv stand. 

Sosai falon yayi kyau, duk da cewar babu wasu tarkace masu yawa acikinsa, amma komai da komai mai tsada ne.

Sanyin AC da kuma daddad’an kamshin room freshener dake tashi acikin falonne yasa Jannart lumshe Idanunta.

Inda Mamy kuwa kaitsaye ta wuce jin wata kofa dake cikin falon, still kuma tana rik’e da hannun Jannart ta bud’e kofar suka kutsa ciki.

Bedroom ne madaidaici wanda aka zuba masa furnitures na alfarma, bed, drawer, and dressing mirror with bedside drawer then shoe rug. 

Komai dake cikin d’akin kalan pink and white ne, shiyasa haduwarsa yake dajan hankali, kamar dai falon, Domin shima cushions da labulayen cikinsa duk pink and white ne.

K’arasa shigowa cikin dakin sukayi, Yayinda Mamyn ta zaunar da ita bakin gadon daya sha bedsheet na alfarma.

Kallonta Mamyn tayi, kana cikin tausasawa tace.

“Jannart Nan shine masaukinki, zaki zauna ne kuma kafun agama gyara miki asalin inda zaki zauna.

Dan Allah Jannart ki saki jikinki, babu wani wanda zai takura miki, akwai komai na amfani da zaki buk’ata, duk abunda kikeso kuma kiyi min magana, banason kiyi kuka kinji ko Jannart”.

Cikin sharce hawayen ta gyaɗa kai alamun.

Eh taji.

Cikin jin daɗi Mamy tace.

 “Kinga ke amanace agaremu, zubar hawayenki kuma zai zamo damuwa azuciyoyin mu, duk wani abunda ya dameki ki sanar dani, kada kiji shakka ko kuma nauyi na.

Domin bana daukanki amatsayin suruka,  sannan kada ki bari damuwa tayi nasarar tank’wasar da zuciyarki, kowani bawa yana d’auke da irin salon k’addararsa, saboda haka ki kwantar da hankalinki, ke taki k’addarar ahaka tazo, Insha Allah kuma watarana komai zai wuce, babu wani damuwa dake tabbata, kiyi farinciki aduk wani yanayin da kika samu kanki kinji Jannart.”

Kai Jannart din ta jinjina, tare kuma da kama y’an yatsun hannunta cikin sanyi tace.

“Insha Allahu Mamy zanyi duk  abinda kikace.”

Murmushi Mamyn tayi, cikin tsananin jin dadi da farinciki tace.

“Yauwa Jannart, Allah Yayi miki albarka, naji dadin biyayyarki.

Domin duk wani wanda yake daukar maganan na sama dashi, har abada bazai tab’ayin dana sani ba.”

Ta ƙare mgnar tana nufar Bathroom.

Ruwan wanka mai dumi Mamyn ta had’awa Jannart acikin bath, tare kuma dasa mata turaren wanka mai dadin k’amshi.

Koda ta fito daga toilet din, hannun Jannart din ta kamo ta miƙar da ita, tare da cewa.

“Yauwa Jannart kije kiyi wanka ko nasan..”

Sauran maganan Mamyn ne ya mak’ale, saboda yanda taji duk jikin Jannart din ya dau zafi.

“Subahanallah Jannart gashi duk jikinki zafi, nasan kuma hakan bai rasa na saba, da kukan da kikayi, kije kiyi wanka, akwai sabin towels acikin toilet din saikiyi amfani dasu, akwai kuma ruwan dumi dana had’a miki a bathtub.”

“Nagode Mamy.”

Jannart din ta fad’a, Ahankali tare kuma da zare dogon hijab din dake jikinta.

Mamy kuwa murmushi tayi, kana ta juya ta fice daga cikin d’akin.

Koda ta fito nan cikin falon nasu, kaitsaye kitchine ta wuce.

Yar ƙaramar tukunya tasa akan gas, cikin abunda baiwuce.

 15mn ba kuwa ta kammala had’a indomie’n da ta dafawa Jannart din, wanda yaji kayan hadi da kifi, bayan ta juye indomie’n a plate ne kuma, ta had’a tea mai kauri acikin mug.

Bayan ta gama kimtsa komai ne kuma, kaitsaye ta haura sama zuwa dakin Rayyern.

Zaune yake akan gadonsa, inda ya sanja shigar jikinsa, zuwa kayan bacci masu taushi.

Yanayin yanda yayi zaman duka k’afafunsa na k’asa, sannan kuma ya dafe kansa da hannayensa duka biyu.

Idanunsa arumtse suke, kana kuma time to time yake fesar da wani irin numfashi mai kama da ajiyan zuciya.

Mamy kuwa isowarta jikin kofar ne yasa ta d’an soma knocking.

Sai-dai har tsawon mintuna 2 tana knocking amma bataji a bud’e k’ofar ko kuma bata izinin shigowa ba.

Hakan kuwa shi yasa ta murd’a handle din kofar a zayonta ko yana bacci ne, ga mamakinta kuwa sai taga kofar ta bud’u.

Ahankali ta tura kanta cikin dakin tare dayin sallama.

Anan zaune ta hangosa, ya dafe Kai, da dukkan alama kuma yayi nisa acikin duniyar tunanin da yakeyi.

Idanu Mamyn ta Dan tsura masa cike da mamaki, saboda wannan ne karo na farko da taga Rayyern din acikin yanayin zallar damuwa.

Rayyen kuwa da yayi nisa acikin duniyar tunaninsa, Sam baisan cewa Mamyn ta shigo ba.

Gaba daya hankalinsa ya tafi, izuwa sabuwar k’addarar daya samu kansa aciki.

Yayinda har yanzu ya kasa tantance wani irin aure ne aka daura masa, Sam ya kasa tantance marabar auren dana dole, shi ya sani bayason lamarin  mace acikin rayuwarsa, but why za’a takura masa? Yasan meye aure yasan manufarsa yasan hakkokin mata a kan mijinta.

Yasan bashi da lokacin saukesu da reno da tattalin mace yadda ya kamata shiyasa bai kawo mace a rayuwarsa meyasa zasu liƙa mishi ita a dole su lika mata shi a dole.

“Rayyern! Rayyern!!”

Back to top button