Uncategorized

Tagwayen ‘yan matan Kannywood sun bayyana babbar damuwar su a rayuwa

 TAGWAYEN ‘yan matan Kannywood, Hassana Musa da Hussaina Musa, sun bayyana cewa babban burin su a rayuwa shi ne su samu mazan aure nagari a kowanne lokaci daga yanzu.

Tagwayen su ka ce: “Mu dai a yanzu babban burin da mu ke da shi bai wuce mu samu mazaje nagari mu yi aure ba. Kuma mu na fatan Allah ya kawo mana nagarin.”

Sun bayyana haka ne a lokacin da su ke tattaunawa da mujallar Fim kan yadda yanayin harkar fim a daidai wannan lokaci ya shafi mata.

Jaruman, waɗanda ‘yan biyu ne masu kama kamar an tsaga rama, ‘yan gida ɗaya ne da su ke yin harkar fim tare.

A cewar su, yanzu harkar fim ta zama gida-gida ne kuma sai ka samu gida mai ƙarfi za a riƙa damawa da kai a cikin harkar.

Su ka ce a yanzu finafinai sun sauya ba irin yadda ake yi a ba a da, domin a yanzu daga finafinan YouTube sai masu dogon zango da ake haskawa a gidan talbijin.

Babban burin mu shi ne mu samu maza nagari, inji tagwayen Kannywood

Su ka ce ko da ka na samun aikin, in dai babu wani kamfani da ka ke da kusanci da shi, to wani lokaci sai samun aikin ya yi maka wahala.

Su ka ce: “Amma dai mu sai godiya ga Allah, saboda mu na alaƙa da manyan kamfanoni da su ke yin aikin saboda mun daɗe tare da su, don haka mu na samun shiga cikin manyan finafinan da ake haskawa kamar su ‘Izzar So’.

“Mu a cikin masana’antar ma sai dai mu yi wa wasu hanya, saboda mu kowa namu ne cikin harkar, don mu na zaman lafiya da kowa. Kuma hakan ta sa kowa ya ke neman mu idan ya tashi aikin sa.”

Dangane da yanayin siyasar da aka tsunduma a ciki kuwa cewa, ‘yan biyun su ka ce: “Ai ita siyasa ra’ayi ce, kowa ya na yin tasa, amma duk da akwai namu ra’ayin, idan aiki ya taso to duk wanda mu ke mu’amala da shi a kowace jam’iyyar ya ke za mu je mu yi masa aiki, saboda alaƙar mu da shi ta fi ta siyasa.

“Don haka mu dai a yanzu babban burin da mu ke da shi bai wuce mu samu mazaje nagari mu yi aure ba. Kuma mu na fatan Allah ya kawo mana nagarin.”

Hassana da Hussaina Musa

Back to top button