Uncategorized

Lullubin Biri Complete Hausa Novel

American Hospital Dubai, 2:30pm.

_”hey don’t move, we are us navy seals…God! Damn it…we have a tango in the north wing every week. stop! stop! stop!…great team work guys, yeah we will mark you for the assist on this one.”_

sautin dake fitowa kenan daga cikin ƙatuwar plasma ɗin dake manne a bangon ofishin, cikin wani american film me suna Steel Brigade. dai-dai lokacin da sojojin suka kama mutumin da ke sanye da mask, dai-dai lokacin Yusuf dake juyi akan kujerarsa yasa tafukan hannunsa duka biyu ya shafo fuskarsa tare da fitar da iska daga bakinsa. “ohh dammm it”.

“ai na faɗa maka sai sun kama shi”. Kalid wanda har yanzu bai ɗauke idonsa daga kallon tv ɗin ba ya faɗa a sa’ilin da duka haƙoran gabansa ke bayyana a waje alamar yayi farin ciki da abinda ya faru.

Yusuf ya ƙara juyawa akan kujerarsa zuwa gefe guda sannan yay guntun tsaki yace,”ko waye producer ɗin nan sam bai iya tsara film ba”.

“hhh to ai hakan shine dai-dai, kai kana kallon sojojin nan kasan bana banza ba ne…kuma gwara a kama shi tun a farko, wasan zai fi tafiya dai-dai”.

“kuma wataƙila ya suɓuce masu ba”.

“ta ya ya?, macece fa ai da kamar wuya ta iya ƙwacewa”.

“wannan ai ba mace ba ce”.

“bari su buɗe fuskar zaka gani, ai yanayin gudun kaɗai zaka fahimci macece, itama ba me kamar maza ba”.

shirun Kalid ɗin ya haɗe da sanda sautin maganar film ɗin ta ci gaba da tafiya, nan sukai shiru suna ci gaba da kallon.

_”get the mask!!…there is no harmful in the air we already checked, expect for the thorpe’s breath.”_ ɗaya cikin sojojin yay maganar a tsawace inda a take ya fizge mask ɗin daga fuskar mutumin, kuma lokaci ɗaya zaton Khalid ya bayyana, hakan kuma ya wanzar da dariya a fuskarsa, nan ya juyo ya kalli Yusuf dake aikin jan gajeran tsaki babu ƙaƙƙautawa alamun ba hakan yaso ba.

lokacin da Yusuf ya buɗi baki zaiyi magana lokacin ƙofar ofishin tayi ƙara, aka turota a hankali inda wata matashiyar budurwa ta bayyana hannunta riƙe da wasu takardu, jikinta kuma sanye da unifom na ma’aikatan jinya. ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin ofishin tana ƙarasawa gaban tebirin da Yusuf ke zaune kan kujera yana juyawa gefe zuwa gefe a hankali.

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

cike da girmamawa ta rissinar da kanta tare da aje fayel ɗin hannunta akan teburin tana tura su zuwa gaban Yusuf. “Ranka ya daɗe ga result ɗin da aka samu”. ta faɗa sanda ta ke harɗe hannayenta zuwa baya.

“ta farka ne?”. Yusuf ɗin ya tambaya a sa’ilin da yake buɗe fayel ɗin yana dubawa.

“ehh ranka ya daɗe ta farka wajen ƙarfe ɗaya da minti goma sha biyu, amma bata fi sakan huɗu ba ta koma, da alamu dai har yanzu da saura kamin ta dawo hayyacinta”.

shiru ya biyo bayan maganarta, idon Yusuf ta cikin farin gilishin daya manna na bin rubutun dake cikin fayel ɗin, karantarsu yake da fahimta, wucewar daƙiƙa 1,2 Yusuf ya ɗago kansa akan fayel ɗin, ya kai hannu ya shafo goshinsa sannan ya jinginar da kansa jikin kujera yana mai sauke gajeran numfashi. 

_”huuuuhh”._ hucin iska ta fita daga bakinsa. “EXOGENOUS DEPRESSION”. ya faɗa cikin amon sauti na tausayawa haɗe da kulle murfin idonsa. furucin nasa kuma yasa Kalid maido da kallonsa gare shi.

“tana cikin matakin biopolar kenan?”.

Yusuf ya jijjiga kansa tabbacin hakan ba tare daya ce komai ba, na tsawon wasu sakanni ya ɗaga ido ya kalli Nurse ɗin yace,”kuma iyaka binciken da jami’an tsaro suka yi babu wani danginta a ƙasar nan?”…

WRITTEN BY:   HALIMA H.Z

NOVEL NAME:   LULLIBIN BIRI COMPLETE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         1.5MB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:    12- OCTOBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Lullubin Biri Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button