Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 74 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

Cigaban page 74

Murmushi su ka saki gaba É—ayan su, kafin daga bisani Batul ta rarrabasu zuwa gida uku, Nan fa suka baza cikin toilets É—insu suna neman Æ™ofar nan, Angel tana ruÆ™e da hannun Azeeza saboda makantarta, Uban gumi suka haÉ—a akan fuskokin su, Sun bada himma sosai, wurin neman Æ™opar ba inda basu É—aga ba, hatta tukunyar fulawar da ke a toilet É—insu saida batul da Deeja suka haÉ—a Æ™arfi wurin É—aÉ—É—agota amma basu ga komai ba, Bangon da aka jingine ta dashi ashafe Ya ke haka Æ™asantama Ashafe Yake babu wata Æ™ofa, Kamar zasu fashe da kuka su ka sauke tunkunyar, furennin cikin ta ma duk sun bushe babu mai lafiya, Ko’ina Ciki da bai na sashen toilet É—insu saida suka bincika amma babu Æ™opa, A Æ™arshe sarah Ta hango masu Tagogin nan da ke a saman ceilling waÉ—anda tun farkon zuwan Angel ta yi tozali dasu a garÆ™ame da kwaÉ—o, Kowani toilet akwai tagogin saman ceilling guda biyu, hankalin su gaba É—aya ya karkata akan tagogin ransu ya gama basu cewar Za’a samu hanyar da zata 6ullar da su wajen kurkukun, Sai dai basu san ta yadda zasu Iya kaiwa gare su ba saboda basu da tsauni tsayin su kuma ba zai kai su ba, hatta Sarah Da tafi su tsawo bazata Iya koda É—aga hannu ta ta6a jikin su ba, Bayan haka kuma basu da Makullin da zasu Iya buÉ—e tagogin, daga bisani tunani su ya canza akan Su nemo makullan buÉ—e tagar, A daren ranar basu koma bacci ba, Saboda Aikin neman makulli, Sunci baÆ™ara wahala ga bacci a idonsu amma Sun nace akan neman makullai, wasa wasa har Gari Ya waye suna aikin neman makulli, A Æ™arshe da su ka galabaita, don dole suka haÆ™ura, Ga yunwa suna Ji ga bacci a idanuwansu.

A saman floor na sashen toilets É—insu, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna suka fuskanci juna, Sai haki suke Yi kamar waÉ—anda suka Sha Gudu, Baccin wahala ne Ya É—auke su mai nauyi, duk sun É—aÉ—É—aura kawu nan su saman kafaÉ—un Junansu, Baka Jin sautin komai saina minsharin su.

Daga cikin É—akin su muryar Jamimah ce ke ta Æ™wala masu kira, babu mai jinta, farkawarta kenan daga bacci, Hankalinta atashe ya ke ganin babu su asaman gadajen su, saukowa ta yi daga saman gadonta, tare da nufar Sashen toilet É—in su, shigar ta keda wuya ta yi arba dasu zazzaune suna bacci, Mamaki ne ya kama Jamimah, ganin su anan maimakon saman gadajen su, Æ™arasa shiga ciki ta yi a yayin da ta ke leÆ™a fuskokin su don taga Idan baccin gaske su ke yi ko kuwa tsokanar ta su ke Yi, Kallon Æ™urulla jamimah take binsu dashi, adai dai saitin fuskar Angel ta tsayar da eye balls dinta, muryar ta Æ™asa Æ™asa ta furta”My Genie” shiru bata amsa mata ba, da ta fahimce cewa dagaske baccin su ke yi, Sai ta zauna tare da kwantar da kanta saman laps É—in Angel ta lumshe idanuwanta kamar maiyin bacci, Tsawon Lokaci babu wanda ya farka, Sun saki baki suna bacci.

A firgice Parveen Ta farka tana ambaton”Nagansu wlh nagansu” Sautin muryarta ne Ya farkar dasu Angel a fujajen su ka wawware Idanuwansu masu É—auke da bacci suna kallon Parveen, Har suna haÉ—a baki wurin tambayar Ta”Makullan kika gani? a ina su ke”? Yawu ta haÉ—iya tana faman Zare ido, tare da Æ™are masu kallo, Sam babu natsuwa atattare da Ita, Muryarta AshaÆ™e tace”Kamar mafarki na yi nagan su a cikin Æ™asar tukunyar fulawar nan, Makullan……..”

Tun kan ta ƙarasa maganar Zumbur suka mimmiƙe har suna bangaje juna wurin shiga toilet ɗin Saboda tsabar sauri, Jamimah batasan Kan me suke magana ba, binsu kawai ta ke Yi kamar bindi.

A Gaban tukunyar fulawar Su ka zuzzuÆ™unna, Deeja da batul na Æ™oÆ™arin tsoma hannu cikin Æ™asar Angel ta dakatar dasu ta hanyar yi masu magana”Bana so acire furennin nan saboda raine dasu, Ina gudun kada silar cire su su mutu……” Bata kai Æ™arshen maganar ba, Deeja ta tari numfashinta”A halin da muke cikin yanzu bamu buÆ™atar furanni, ganinsu ma Æ™ara tayar mana da hankali ya ke yi, don haka cire su zamuyi” ba tare da 6ata lokaci ba, Mutun Biyar ne su ka tsoma hannayensu Ciki, duk suka tsige furennin tare da jefar dasu Æ™asa.

Hankalin Angel sam ba akwance ya ke ba, Saboda ta yi believing da furannin rai Ne dasu, Ko da su Deeja su ka jefar dasu Ƙasa da sauri ta zuƙunna ta sanya hannu ta ɗauki furen daddynta dana Aunty aneelerh hada ƙaramin furennin nan, Har zata miƙe idonta Ya sauka Akan Dogon furen nan da ganyen shi ya koma baƙi, yanzu ya koma asalin colour din shi, Punch pink Ya ciza sosai, hakanan ta dinga jin gabanta Na faɗuwa, Ayayin da ta ke kallon shi, Kasa miƙewa ta yi har saida ta ɗauke shi ta hada da sauran furennin da ke a hannunta, tukunna taji Hankalinta Ya kwanta.

Fasa ƙara Azeeza Tayi tare da faɗin

“Mun samo shi! Gashi nan Makulli ne” jin muryarta Yasa Angel matsowa kusa dasu, Hankalin kowa Akan hannun Azeeza Ta damÆ™e wani abu dake a nannaÉ—e Cikin Æ™asa, Wani irin farin Cikine Ya bayyana akan fuskokin su, Tun kafin Ta buÉ—e masu tafin hannun nata su ga menene.

A hankali Azeeza Ta ware tafin hannunta, Ta soma kakka6e ƙasar da ke nannaɗe da abunda ta damƙo, ko da ta kammala Kakka6e ƙasar jikin shi, Murnar da su ke yi ta koma Ciki, Ashe jijiyar fure ce, tsabar takaici Yasa kowaccen su ta dafe goshin ta da hannu, Ƙululun bakin Ciki Ya tokare masu maƙoshin su, Ji su ke kamar su rufe Azeeza da bugu, don ba ƙaramin sanya rai su ka yi ba, Kamar masu zaman makoki Haka suka zazzauna Cikin toilet ɗin Abun duniya ya ishe su, Jamimah ce kaɗai a tsaye ta Ruƙe qugu tana kallon su

“Wai ni kun barni aduhu me ake nema ne? Duk kun cire mana furennin mu, Genie Ki fada mini,” hada Æ´ar shagwa6arta

ÆŠago da ido Angel ta yi tare da kallonta kafin ta miÆ™a mata hannu”Zo nan” matsawa ta yi kusa da ita, Ta sanya hannu biyu ta janyota zuwa jikinta

“Yaushe kika farka daga bacci bamu sani ba”? Yatsina fuska ta yi”tun É—azu na farka ina ta kiran sunayen ku babu wanda ya amsa mini, Sai da nazo sashen toilet tukunna nagan ku kuna bacci, ni kun barni a É—aki”

Harara Azeeza ta watsa ma Jamimah kafin ta soma kwaikwayon maganarta, salon jan faɗa, Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba.

“Yanzu fa ba lokacin Yin nishaÉ—i bane, Yakamata Mu nemi mafita, Ni dama tun farko raina bai bani cewar Akwai wasu makullai ba, Mu É—in dai mune makullan, Ƙofa ce kaÉ—ai zamu gano, Saboda a jawabin da tsohuwa Tamira ta yi mata cewa ta yi Mu É—auka cewa mu É—in makullan Wata Æ™opa ce guda É—aya wadda zata sama mana farin ciki, To kunga anan tana nufin we’re the keys da zamu buÉ—e Æ™ofar” Angel ce ta yi jawabin

“Ni kuma aganina akwai makullan, Ma’anar abunda ta ke nufi, Mu zamu haÉ—a hannu don mu gano su, Sa’annan waÉ—annan munafukan tagogin da suka zuba mana ido suna kallon mu, Ina zargin Æ™ofar tana A cikin su,” Deeja ce ta yi maganar, Kowa sai tofa albarkacin bakinsa ya ke yi kamar masu gabatar da shirin wasa Æ™waÆ™walwa.

“Ni ma nafi hasashen acikin su ne za’a samu Æ™ofa, saboda su kaÉ—ai ne hanyoyin da zasu Iya 6ullewa wajen É—akin nan” Acewar Hibba.

“Ku dakata, Kada Mu É—aura buri akan waÉ—annan Tagogin, Har yanzu fa akwai wuraren da bamu Bincika ba, Na farko akwai Æ™arÆ™ashin gadajen mu, Da kuma É—akin tsohuwa Tamira” Yasmin ce ta yi maganar, Rubina tace”Ai babu ta yadda za’ai mu iya buÉ—e É—akin Tsohuwa Tamira, tun da mu ke bamu ta6a shiga É—akin ba, saboda kullum agarÆ™ame ya ke kuma babu makulli ta waje balle muyi tunanin balle shi mu shiga”

Gaddama ce ta 6alle atsakanin su kamar za su yi faÉ—a kowa Ya kafe akan tashi shawarar, Sai tada jijiyoyin wuya suke Yi, Ko yunwar cikin su basa Ji ga Jikinsu da ke ta tsami saboda rashin wanka, Hayaniyarsu ta cika ko’ina, ganin zasu hargitsa mata lissafine yasa ta dakatar dasu ta hanyar daka masu tsawa, Nan fa kowa yaja bakin shi yai shiru, Hankalinsu ya koma kanta, MiÆ™ewa tayi tsaye kamar malami agaban É—aliban sa, A tsanake ta soma magana.

“Idan har mu ka rasa natsuwar mu to kuwa ba zamu ta6a Iya gano Æ™ofar nan ba! Mu kan mu hankalin mu ba a kwance ya ke ba, ta ya ya ku ke tunanin zamu Iya gano Æ™ofar bayan mun Æ™i haÉ—a kan mu, mu sanya natsuwa wurin bincikota”? Ta jefa masu tambayar tana Æ™are masu kallo, duk sunyi Æ™uri da idanuwansu,

“Maganarki gaskiya ce Angel, komai yana buÆ™atar kwanciyar hankali da natsuwa, Yanzu ki faÉ—a mana me ya kamata mu yi? Tun da kinfi mu kaifin basira”

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, Jin an wasa ta, MiÆ™a ma Jamimah furennin dake a hannunta tayi tare da cewa”RuÆ™e mini su My little sis” Kar6ar furannin Jamimah ta yi a hannunta.

“Abu na farko da yakamata Mu fara yi shine mu tsaftace jikin mu, ta hakanne zamu Ji daÉ—in Jikin mu brain É—inmu ta yi fresh, mu samu natsuwar fara yin bincike na hankali, nasan kafin mu kammala Yin wanka Giants sun kawo mana Ganye, Idan mu ka Ci mu ka Æ™oshi Sai mu fara wasan Ƴar 6urun 6urun kamar yarda na tsara mana, don kada ayi zargin wani abu tunda suna kallon duk wani moving É—in mu”

Tun kan ta Æ™arasa yin maganar, murmushi ya bayyana akan fuskokin su, gaba É—aya sun yi amanna da maganarta, without wasting time kowan nan su ya miÆ™e tsaye, É—aya bayan É—aya suka fuce daga cikin toilet É—in, Ya rage saura Angel da Jamimah, Kallon Juna su ka yi atare suka sakar ma Juna murmushi”My Genie, Ƙofar da zamu gudu ku ke nema mana?

ÆŠaga mata kai Angel ta yi alamar eh, Dariyar Farin Ciki Jamimah ta saki har fararen haÆ™oranta sai da su ka bayyana, Bin ta da kallo Angel tayi dariyarta ba Æ™aramin burgeta ta yi ba, sai da ta tsagaita da yin dariyar ta kuma cewa”Genie Zamu Koma Gidan ku da zama ko? Kuma can babu giants sannan ba zamu Æ™ara cin ganye ba ko”? Maganar da jamimah ta yi ba Æ™aramin ta6a mata zuciya tayi ba, yadda suka Æ™wallafa rai akan son zuwa gidan daddynta ba Æ™aramin karya mata zuciya ya ke yi ba, duk idan ta tuna cewa ba lallai bane su samu damar tsira dukkan su ba koda ace sun samu Æ™opar, wata’Æ™il ma babu wata Æ™ofa tunda hasashene kawai suke yi basu da tabbaci akanta.

“My genie kin yi shiru, pls ki amsa mini, inaso inji a Æ™agare na ke,” yadda ta ke yin maganar farin cikine tsantsa akan fuskarta, tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da Æ™walla, sam ta kasa buÉ—e baki ta amsa mata.

“Genie Am talking to u pls ki amsa mini, idan ba haka ba zan cinye furannin da ke a hannuna” Ta yi maganar tare da yin kamar zata cinye su, Nauyayyiyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa”Kada mu 6ata lokaci My little sis, Zan yi maki wanka amma kafin nan ki taya ni mu mayar da Æ™asar tukunyar nan sai mu mayar da furennin” Amsa mata tayi da toh.

Ba tare da ta ƙara tambayar Angel ba, Atare su ka zuƙunna jamimah ta kwantar da furennin a ƙasa, kafin su ka sanya hannu Suna ɗibar ƙasar da ke a ƙasa suna zubawa cikin tukunyar fulawar bayan sun kammala Angel ta ɗauki furennin ta tsirasu Cikin ƙasar, har ta yunƙura zata miƙa Karaf idanuwanta su ka sauka akan wasu furenni guda biyu da ke yashe ƙasa, ƙura masu ido ta yi tana kallonsu Jamimah sai magana take yi mata amma sam bata Jinta,

Wani irin faÉ—uwar gaba taji tamkar zuciyarta zata faso Æ™irjinta, a matuÆ™ar ruÉ—e ta ke kallon Furennin, Ganyen jikinshi ya bushe Æ™asa ya mutu, bakomai ya faÉ—o mata araiba face Majnoon da Unaiza da suka rasu, Zazzare idanuwanta tayi Hannunta É—aya dafe da Æ™irjinta, Nan take ta fahimci cewa furennin su ne suka mutu, Tun da basa araye that mean sauran furennin dukkan su rayukan Æ´an uwansu ne akai, A hanzarce ta É—aura eye balls É—inta kan Dogon furen nan Muryarta Na rawa ta furta”DA…NISH!”

Zungurar hannunta jamimah tayi hakan yasa tayi firgit ta dube ta

Fuskarta a É—aure tace”Kin shanyani Genie, ko ba za ki mini wankan bane? Inje inyi da kaina” Yawu ta haÉ—iya zuciyarta duk ba dadi, Furen Danish ya tsaya mata aranta, musamman da ta tuna da Lokacin nan da ta tarass Ganyayyakin jikinshi Sunyi baÆ™i sosai, tana ji aranta cewa wani mummunan abune ya faru dashi wanda silar hakan yasa furen shi canza launi,

“Genie!!” jamimah ce ta ambaci sunanta da karfi ganin ta Æ™ara shiga zurfin tunani, Numfasawa tayi tare da ruÆ™o hannun Jamimah, Cikin sanyin murya tace”Am sorry Muje inyi maki wankan” Tayi maganar tare da janta zuwa gaban fanfo, Ta cika bokiti da ruwa ta É—auko kwandon soso da sabulu, Bayan ta cire mata kayan Jikinta ta É—aura su saman igiya, wanka ta ke yi mata amma hankalinta gaba É—aya yana akan dogon Furen nan, A shiririce ta gama Yi mata wankan hada sumar kanta ta wanke mata, bayan ta kammala bata mayar mata da uniform É—in jikinta ba, saboda sun yi datti, sai tace mata ta koma É—aki ta Ta lullu6e da bargo kafin kayan da zata wanke mata su bushe saita maida su a jikinta, bayan fitar Jamimah daga Cikin toilet É—in, komawa Angel tayi gaban tukunyar fulawar ta zuÆ™unna tana Æ™arewa Dogon furen kallo, Yayin da zuciyarta ke harbawa da sauri da sauri, Yatsun hannayenta na kerma ta É—aurasu kan furen tana shafa leaves É—insa, Har cikin zuciyarta ta ke jin kamar sumar kan Danish ta ke shafawa, A hankali ta rufe idanuwanta a yayin da Æ™waƘwalwarta ke tariyo mata Rayuwar su ta baya dashi, baza ta ta6a manta Rana ta farko da ta fara Yin tozali da kyakkyawar fuskar shi duk da bata a cikin kwanciyar hankalinta sai da gabanta ya faÉ—i ganin irin baiwar kyan da Allah ya yi mashi, Tana matuÆ™ar Æ™aunar danish, Jin shi ta ke yi tamkar oxygen É—in da ta ke shaÆ™a don ta rayu, taya hankalinta zai kwanta? Bayan ta riga da ta gane furen Masoyinta ne, idanuwanta sun yi maraicin shi, zuciyarta sai azalzalarta ta ke akan ta nemo shi aduk inda ya ke, don taga awani hali ya ke ciki, ya idon shi ya ke? Meya faru dashi da har furen shi Ya canza Launi…………”

💔PRISONERS💔

Hankalin su Yaƙi kwanciya Jin shiru Angel bata fito daga Cikin toilet ɗin da ta shiga ba, Tun suna saran fitowarta har sun fara tunanin Anya kuwa lafiya? Ita kaɗai ya rage ta fito su fara wasan Ƴar 6urun 6urun, don su gano inda ƙofar nan ta ke, tun ɗazu Giats sun kawo masu Ganye kamar kullum tare da ruwan zafi, babu wanda yasan da cewa An kawo masu abinci.

Jamimah kaɗai ta rage a cikin ɗakin nasu, kwance saman gado ta lullu6e jikinta da bargonta, Jin motsin shigowar Giants, ta yi hanzarin yaye bargon data lullu6a dashi ta yi ɗaurin gaba har yana jan ƙasa saboda rashin tsawonta, Ahaka ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko kwandon abincinsu taje ta zuƙunna agaban dining Carpet ɗinsu, ta kwashe ganyan Ta zuba masu Acikin kwandon, bayan ta kammala kwashewa, Giants suka Ɗauki farantan tare da fucewa daga Cikin ɗakin, Zama Jamimah tayi saman carpet ɗin, ta soma ɗibar ganyen tana Ci yadda kasan ƴar akuya, Kunnuwanta har motsawa su ke yi saboda daɗin da ya yi mata.

“Angel ke fa mu ke jira! Tun É—azu kowa ya fito daga wanka, Saura ke kaÉ—ai kin shige toilet kin garÆ™ame Æ™ofa kin barmu a tsaye” Deeja ce ta yi magnar

Batul tace”Ko dai ta fito daga wankan ne bamu sani ba? ta yi tambayar tare da yin saurin juyawa ta shiga É—akinsu, Jamimah ta hango zauna tana cusa ganye abakinta, babu alamun Angel acikin É—akin, dawowa ta yi sashen toilet É—in tun kafin su tambayeta ko ta ganta, ta riga su cewa Na duba bata a ciki,

Nan fa hankalinsu Ya É—ungunzuma

Sunanta suka dinga kira shiru bata amsa masu ba, Atare suka haɗa ƙarfi wurin bugun ƙofar sai dai ga dukkan alamu An garƙame ta da Jamlock, Tamkar zasu fashe da kuka suka dingayi mata magiya akan tayi masu koda tari ne don su san cewa tana acikin toilet ɗin, saboda su samu hankalinsu ya kwanta amma shiru Angel bata tanka masu ba, kamar zasu 6alle ƙofar saboda Yadda su ke kai mata zazzafan naushi da hannayensu, a ƙarshe da suka Gaji agalabaice suka zuzzuƙunna Haɗi da jingina bayansu Jikin bango, jin motsin shigowar mutun cikin sashen Yasa suka kai idonsu ga mai shigowa,

Jamimah ce ta shigo hannunta ruƙe da kwando ta ajiye masu shi a tsakiyarsu, Bakinta a cunkushe ya ke da kingin ganyen da bata ƙarasa taunewa ba ahaka ta ke yi masu magana,

“Ku ci naku ne na kawo maku” kallonta kawai su ke yi, Ta zumbula bargo ajikinta sai ja da Æ™asa Yake yi, jin sunyi shiru basu tanka mata ba, yasa ta haÉ—e girar ta”Ni ba ruwana Idan ba ku ci ba, Ku yunwa zata kama, Sannan Ina GENIE É—ina ta ke? Ko haryanzu bata fito daga wankan bane?

……………….. WHERE’S ANGEL ????

Ku duba page 75 in kun gama wannan, Da anjima zan daura sauran

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

(Mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button