Uncategorized

Maganin Jinnul Ashiq

Aljani mai hana aure ko mai kwanciya da matan mutane

ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ

Idan aka ce Jinnul Ashiq ana nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji.

Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma kokarin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga kokarin kashe mata shi. Su na kuma kokarin hana mace samun ciki, ko kuma in ta samun cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa, ya zamo tun daga haifar sa za a ga alamun jinnu a tare da shi.

Irin wannan nau’in Aljani shi muke kira

JINNUL ASHIQ 

ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷق

Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne mutum yake yi da su, su shiga jikinsa ba tare da wani dalili ba. 

YADDA MUTUM ZAI GANE YANA DA ALJANIN DARE

Ta 6angaren namiji:-

1- Rashin sha‘awar aure ko jima’i sam-sam.

2- ‘Kin mikewar gaba sanda kai nufin yin jima‘i, alhali kuma haka kawai ma yana tashi.

3- ‘Kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana iya zama a cikin marainan mutum.

4- Saurin gajiya, yayin jima‘i da rashin iya komawa

5- Jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in haihuwa yayin jima‘i.

6- Rashin cimma bukatar jima,i.

7- In ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka.

8- Da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo tun kafin ka fara.

9- Komawar gaba da maraina su shige ciki.

10- Yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili, faduwar gaba, da dai sauran su.

11- Haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka.

12- Yawan mafarki kana saduwa da wata mata.

13- Yawan samun matsaloli aduk inda ka je neman aure, sai maganar ta lalace.

14- Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai.

15- Matsananciyar sha’awa da tsoron mata.

Da dai sauransu.

YADDA MACE ZATA GANE ALJANI YA AURETA

1- Yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi acikin.

2- A duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al’adarta bane.

3- Jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida.

4- Suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta ba.

5- Matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.

6- ‘Kin yarda da jima‘i.

7- Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban.

8- Yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da taron suna.

9- Ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa a cikinki ta ya fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki.

10- Yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba.

11- Yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke.

12- Jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana dada girma, amma in likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba.

13- Rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai.

14- Tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha’awar wasu mazan.

15- Jin wari mara dadi yana fito miki ko ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen gaba.

16- Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba.

17- Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi.

18- In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suy mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take musu.

19- Za ta dinga yawan zaman a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane.

20- Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa.

21- Yawan ciwon kai da yin jiri.

22- Faduwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa.

25- Iadan mace ta fara barci sai ta ji an zungureta ta farka.

Da dai alamomi da yawa.

Mafita shi ne ka ziyarci mai Rukiyya don ya dora ka akan tsarin maganin da ya dace da kai.

Kuma ka dinga zama da alwala da addu‘o‘in safiya da maraice.

Idan wannan matsala tay karfi to dole sai an yiwa mutu Ruq’yah, an kama Aljanin an kona shi ko kuma a hada magungunan da za su kashe shi.

Amma dai sihiri da Aljani ba su isa su cutar da kai ba sai da iznin ALLAH.

Daga shafin Sunnah Medicine, masu yin ruq’yah da harhada magunguna na musulunci.

Lambar waya

08162600700

Back to top button