Uncategorized

Don Magance Matsalolin Ma’aurata Amarya Ko Uwar Gida Ga Tsaraba

Abubuwan Dake Ciki:

Idan muka ce gyaran nono akasari ba kowace mace zata gane me muke nufi ba saboda basu dama da gyarawaba, alhali kuma rashin gyaran ba karamar illa yake yi masuba amma su basu sanhakanba, to gaskiya yana da matukar muhimmanci da tasiri ga mace AMARYA ko UWARGIDA, BUDURWA KO ZAWARA, da ku gyara nononku, karki bar nononki hakanan sharaf ba kyan gani, sai kaga mace ta bar nono a zube, in tana shara mai gida yaga sona ta reto kamar anratayo agwagi a bayan keke, idan kuka lura sai kuga matan wadansu yarurrukan wadanda ba hausawa ba (kamar LARABAWA KO TURAWA) matansu sun tsufa ko sun manyanta amma martabar nonuwansu nanan daram ta yadda ko nonuwan wata budurwar a nan baza ka samesu a hakaba, to hakan zai iya rage maki tasiri wajen maigida, hanyoyin da zaki bi don kada nononki ya fadi ko kuma idan ya fadi kuma kina son ya tashi sune zaki samu:

☞ Alkama ki rinka yin kunu da ita kina sha safe da rana,

☞ Ko kisamu garin hulba

☞ Da garin tsamiya

☞ Da zuma farar saka

☞ Da lemun tsami

Sai ki hadasu guri 1 ki rinka shafawa a nonon, bayan awa daya ko (30 minutes) sai ki wanke ki shafa man zaitun, malama zaki sha mamaki.

Karanta>>> Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illah Ga Mata.

 GYARAN NONO GA BUDURWA 

wannan wani hadi ne da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace macema intana bukata zata iya amfani dashi saboda tasirinshi, yanda akeyi shine za a samu.

✧ Garin waken soya

✧ Garin alkama

✧ Garin zogale

✧ Garin bawon lemun zaki

✧ Kunfan maliya

✧ Da zuma

Sai kica kudasu guri daya sai ki rinka shafawa a nonon bayan 30min ko sama da haka sai ki wanke,sannan kuma ki rinka shan kunun alkama zaki sha mamaki.


Karanta>>> Dalilan Dake Kawo Tusar Gaba Da kuma Hanyar Maganceta.

DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA 

Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata samu

✦ Ganyen sabara mai kyau

✦ Da ‘ya’yan alkama suma masu kyau

Sai ki rinka kunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko ko ko duk dai wanda yasamu sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka.


Karanta>>> Yadda Zaku Kula Da Jikin Ku Lokacin Sanyi Kada Ya Lalace.

DON MAGANCE MATSALOLIN MA’AURATA

AMARYA KO UWAR GIDA GA TSARABA

Shi wannan hadin yana da banmamaki musamman wajen karin soyayya tsakaninki da mai gida, da martaba da farin cikin mai gida da nishadin amarya kuma yanasa maigida yaji dadin da bai misaltuwa zaki zama gagara gasar masu gasa, saboda shi wannan hadin manya mata ne;

✎ Ya’yan kankana

✎ Danyar gyada mai kyau

✎ Dabino

✎ Alkama

✎ Garin kumasoriyya

✎ ‘Ya’yan zogale

Sai ki dakesu suyi laushi sai ki rinka shan karamin cokali da madara ta ruwa safe da yamma kuma shima mijin zai iya sha.

TSARABA GA MASU NIYYAR AURE

Wannan wata irin tsaraba ce mai banmamaki musamman ga ‘yan mata masu niyyar aure, ko amarya, kai harma da uwargida sarautar mata, shi wannan hadin yana kara ni’ima da nishadi sannan kuma yana magance matsalolin da ke rage martabar mace yana kuma sa juriya yanda akeyi shine:

➽ Karas sai ki yayyankashi kanana-kanana sai ki shanyashi ya bushe.

➽ Zangarniyar zogale kwara daya1.

➽ Garin jir-jir na asali

➽ Garin dabino

➽ Da rumzali

Sai ki hada su guri daya ki dakesu sai sunyi laushi sai ki hada da mazankwaila sai ki rinka sha karamin cokali da nono dau daya a rana shima wannan hadin yana da kyau.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Kashi Na Daya.


Back to top button