Uncategorized

An Haramta Wa ’Yan Fim Kwaikwayon ’Yan Sanda Fina-finansu

 

Sifeta Janar na ’yan sandan Nijeriya ya gargaɗi masu shirya fina-finai a ƙasar da su guji aibanta aikin ɗan sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ba tare da izinin rundunar ba.

 A wata sanarwa da rundunar ta fitar yau Litinin ta bayyana cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al’umma.

 Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce; “Ka da wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ’yan sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar ’yan sanda.”

 

IG Usman Baba ya ƙara da cewa daga yanzu ka da a ƙara ganin wani mutum sanye da kayan ɗan sanda a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar.

 Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kuɗarsa.

 BBC ta ruwaito cewa masu shirya fina-finai a Nijeriya kan kwaikwayi jami’an ’yan sandan ƙasar, kuma a mafi yawan lokuta ba a nuna su a mutanen kirki.

Back to top button