Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 13 Book 1 Complete Hausa Nove

 

Sassauta murya Ilham tayi sannan tace

“Malam matsala kaman yaya? 

” eh nayi bincike akan yarinyar nan, amma abune mawuyaci asiri yayi tasiri akanta, zanyi kokari inga aikin dazanyi akanta amma kema sekin dage danaki kokarin domin samun nasarar kawar da ita gefe”

Ajiyr zuciya Ilham tayi, 

“to shikenan malam nagode” 

Sukayi sallama Ilham ta yi shiru nawani lokaci sannan tai kwafa

“indai makircine Jalila tasamu daidanta, nasan abunda zanyi” 

Hanan tacigaba da kiran Jalila tana takuramata akan Jawwad, in Jalila taki dagawa tabita what’s app, duk Yadda Jalila taso ta dinga kokarin danne kishinta amma takasa, itakuma hanan kaman Jalila tana zigata, ta dage ita Jawwad takeso. 

Wajen karfe shadaya na safen yau yaya mairo tazo gidansu Jawwad, tunda matar nan tazo gaban Jalila yake faduwa, dan tasan yau ranar cimata mutuncine, tunda yaya mairo bata kaunarta, 

Aikuwa tunda tazo take bakaken maganganu, ita dai Jalila ta makale a daki taki fitowa

    Jawwad sun gama breakfast dinsu, suna hira da Jalal, Nana ta kira Jawwad a waya

“yaya kana ina? Nazo part dinka baka nan? 

“Nana ya akayine? Muna tareda Jalal” 

“Yaya Jawwad, yaya mairoce take nemanka fa” 

Gabansa ne yafadi

“Nana nikuma, me yafaru? Wani abun nayimata?

“wallahi bansaniba, se faman fada take niban san akan me take fadan ba, tace lallai kazo” 

Ajiyar zuciya yayi

“to gani nan, ina zuwa” 

Ya sauke wayar a hankali, Jalal ya kalleshi

“ya akayine?” 

“wai yaya mairoce tazo tana nemana bansan me nayi mata ba, banason fadan  nan nata” 

Tsaki Jalal yayi

“ni wallahi kana  bani mamaki, to dolene sekaje ai ba dole bane,” 

“haba Jalal itama kamar uwa take a gurina fa, ya za ayi takirani naki zuwa” 

“to haifarka tayi, sekayi tayi, tashi muje, akwai abunda zanyi a dakinka” 

Jawwad ya Mike suka fito, suka tafi gidansu Jawwad, Jalal yayi part din Jawwad shikuma Jawwad yai cikin gida, Jawwad yana zuwa ya tarar da Yaya mairo, A palour Maama na kusa da ita, ya shiga cikin palour ya tsaya daga bakin kofa, ya durkusa yana gaida yaya mairo

“shigo mana kawani tsaya daga bakin kofa, kaman mara gaskiya, dama ba gaskiyarce da kaiba” 

Karasawa yayi gabanta ya zauna ya da n risinar da kansa, sannan yace

“Nana tace kina nemana” 

“eh ai naganka, takanas nazo gidan nan domin in maka Jan munne, Mahaifiyarka taje har gida ta sameni akan taga take2nka na shigewa wannan yarinya, yar gidan arniyar nan, to bari kaji kaf zuriarmu babu arna dan haka bazamu hada zuria dasuba jan kunne nake maka, karka kuskura kasawa zuciyarka zamu bari ka aureta, bamu shirya ganinka tsakanin massalaci da coci ba”

Dagowa yayi ya kalli yaya mairo 

“haba Yaya, Jalila fa ba arniya bace kuma koba komai itama kanwata ce, kuma batada wani aibu” 

Maama ce ta kalleshi

“au Jawwad abun har ya Kai ana maka magana kana mayarwa” 

Yaya mairo ta kalleta

“ai shiyasa nace kinyi sake zainab,” 

Jalila kam ga gaji da zaman daki ga shi ko karyawa batayiba, cikinta yafara kullewa ga sauran aikin gida, dazatayi, dan haka ta mike ta fito

Aikam karaf miyagun maganganun Yaya mairo suka fara dira a kunnuwanta 

“muna da ya’n mata a dangi ga su Naja nan da kannenta ka duba a ciki, kasamu matar aure amma ka kiyayi kanka da fara soyayya da wannan yarinyar arniyar ragowar titi, suda basu san abun kunyaba, Allah ka dai yasan mazan da take bi, ni muslincin nasu ma ban yadda dashiba” 

Gani sukayi ya kurawa kofar corridor ido suna juyawa, sukaga Jalila a bakin kofar tana hawaye

Yaya mairo ta tabe baki

“to almira da kika tsaya kina mana kuka ai ba karya nayiba” 

Maama tace “to tama ce karya kike mana, aikowa yasani, nidai fatana a kyalemin yarona, ato bana son wannan shishshigin da ake masa” 

Jawwad yace “haba Maama harda ke?” 

Maama a tsawace tace “dalla rufemin baki,” 

Yaya mairo ta juyo ta gyara zama sosai ta fuskanci Jalila 

“ke ki bude kunnenki da kyau kijimu, gida dai gashi nan kinzo kin zauna, amma Jawwad karki sakawa ranki zamu bari ya aureki dan Zainab tace kusancinku da kuma zakewar dakike yayiwa kashedi nake miki yanzu, kisani ‘yar dangi’ yar cikakkun musulmai zamu aura masa, yar asali yar dangin uwa da uba ba wadda take da raunin nasaba ba, ba wanda yasan uwarki daga ina tazo ya akayi suka…. 

Juyawa Jalila tayi cikin kuka ta koma dakinsu, bazata iya jure wannan maganganunba, dan inta cigaba da tsayuwa za a iya samun matsala, Jawwad yabi Jalila da kallo, yana jin kukan Jalila har cikin ransa ya dawo da kallonsa kan Yaya mairo

“haba Yaya mairo, be kamata kisata gaba kina cin zarafinta ba, babu wanda Allah yayi shawara dashi lokacin da ya shiryamana kaddararmu, meye laifin Jalila anan” 

Maama ce tace “wallahi ka kuma magana sena mareka, mu zaka gayawa abjnda ya dace muyi, kaika haifemu? Koka fimu sanin abunda ya dace da kai” 

Yaya mairo tace

“kyaleshi ya dakeni, se insan kaji haushi” 

Halima tana daga dakinta amma tana jin duk abunda akeyi, ranta ya baci matuka, bataji dadin abunda akayiwa Jalilan ba, cin mutuncin yayi yawa, 

Ita kam Jalila tana zuwa dakinsu da kuka ta shiga, Nana tasan Yaya mairo ce tayi mata wani abun, dan girgiza kai Nana tayi ta Mike ta fito palour

Itama tazo ta tarar yaya Jawwad ya sunkuyar da kai yayi shiru Yaya mairo tanata  surfa masa fada hadi da cin mutuncin Jalila da mahaifiyarta, ita kanta daba ita akayiwa ba seda taji ba dadi, dakinsu ta koma ta tarar da Jalila tana kuka hada sheshseheka zama tayi tana rarrashinta, amma Jalila taki yin shiru 

Seda yaya mairo tayi me isarta Maama tana tayata, Jawwad ko kai bekuma dagoawa ba balle yace zece wani abu seda sukagama sannan yace “Allah yabaku hakuri za a kiyaye Insha Allah” daga nan ya tashi ya fita

Yaya mairo ta dawo da kallonta kan Maama sannan tace “to kema bazama zakiyi ba ki mike tsaye ki tsaya akan yaranki ki tabbattar kin rabasu, ba ruwanku da ita in tagaji ta tattara ta koma inda ta fito, baze yiwuba ankawo miki arniya an ajiye tana mjamala da yayanki ba” 

  Jiki a sanyaye Jawwad ya shiga dakinsa, yasamu guri ya zauna, ya kashingida a jikin kujera ya lumshe ido, Jalal dayasaka systems agabansa yana dannawa ya dan dago kai ya kalleshi ya maida kansa kan abunda yakeyi, Jalal gani yayi Jawwad bashi da niyyar yin magana, Jalal ya dan gyaran murya

“Me yafarune, me kayi mata?” 

Seda Jawwad yaja wasu seconds sannan ya dago ya zauna sosai ya kalli Jalal 

“Jalal narasa me Baby tayiwa Yaya mairo ta tsaneta haka ba” 

Dan tabe baki Jalal yayi “Maybe Rashin kunya take mata” 

“No Jalal, Jalila ba abunda tayi mata ta tsaneta, yanzu ma kiran datakemjn wai Maama taje ta sameta akan wai Jalila tana zakemin, wai kar insa ran zasu bari in aureta, babban abunda ya Kuma bata min rai, kiran Jalila da suke da arniya, me raunin nasaba, kuma Jalila taji, amma matar nan takiyin shiru tacigaba da cin zarafinta, ina jin kukan Jalila a cikin zuciyata”

Dan kurawa Jawwad ido yayi sannan yace

“Wannan matar bata da hankaline? Kokuma bataje Islamiyya ba, ita Jaleeelan shashashar inace ta tsaya, aka dinga zagin mahaifiyarta, Uwa tafi Uwane?” 

Jalal yai maganar a hasale

“No Jawwad, nasan Jalila kara take mana amma tabbas da a wajene, bazata yaddaba, ni nasan hakan” 

“Ba wata kara Jawwad kadinga gayawa yayar mahaifiyarka gaskiya, dan tana zaune a gidanku bekamata a dinga cin zarafinta ba, koni nan” 

Ya nuna kirjinsa, 

“koni bazan bari wani banza a gari yazagarmin uwaba, dukda abjnda ke tsakanina da mahaifiyata ba, me yasa za a dinga dawo da abunda ya riga ya wuce?” 

“Haba Jalal ya kakeso inyine nayi kokarin nusar da ita amma itada Maama sun rufeni da fada” 

“Mmm ba yadda zakayi, amma Jawwad mahaifiyar Jalila, Mutum ce, ba abar yarwa bace agurinmu, be kamata a ci zarafinta a gabanmu ba” 

“Nasani Jalal, amma ka fahimceni, ba yadda na iya ne, nasani kowaye akayiwa haka baze Ji dadiba, Ina iyajin pain din da Jalila takeji amma ba yadda na iya, da nayi tunanin ko Abba zan gayawa, amma hakan ba mafita bane, ze kuma haddasa fitinane kawai” 

“to wai ma tukuna zuwa kayi kace musu kana sonta” 

Kallon Jalal yayi

“Jalal koban fada ba shakuwar dake tsakanina da Jalila, bata y’an uwanta bace kawai, Jalal ni son Jalila nakeyi dagaske aurenta nakesonyi” 

Wani dogon tsaki Jalal yayi

“Wannan yarinyar mara kunya ita zaka aura, lallai kaci kai,” 

“kaman ya naci kai? Meye aibunta? 

“Babu kam, bayanma bata da kunya ka aurarwa Ummi yarta, wannan matar tazo tana zagin mata mahaifiya, ni danta wannan yarinyar komeyema akmata ban damu ba, amma cin zarafin Mace kaman Ummi be kamata ba, bekamata a cigaba da wulakanta taba saboda kanason yarta ba” Jawwad ya dan gyara zama sannan yace

“Jalal ina fatan komai ze daidaita insha Allah, amma ina son Jalila, so bana wasa ba” 

“to shikenan Allah ya kyauta” 

  Cikin gida kuwa Jalila tayi kuka, har ta gaji, Nana taibata hakuri, se ajiyar zuciya Jalila take, Nana ta tashi ta tafi palour domin dakkowa Jalila ruwa, tana zuwa itama Yaya mairo tafara saukemata nata fadan, itakuwa Nana ta hade rai tana kunkuni 

Jalila tana Cikin kukanne ummi ta kirata a waya, ta dinga kallon screen din har wayar ta katse, kuma kira ummi tayi amma wannan karon se ta Kai hannu ta daga

Ta tattaro nutsuwarta, suka gaisa da ummi 

“lafiya kuwa naji muryarki kaman kina kuka” 

“lafiya kalau Ummi banajin dadiine” 

“meyasame ki?” 

“Ummi ciwon marane fa kawai” 

“Hmm Allah ya sawwake” tafada ba dan ta yaddaba”

Kaman an tsikari Jalila tace

“ummi yaushe zakije garin naku dan Allah ummi kije ki dawo, in dawo gurinki” 

“akwai matsala kenan?” 

“ummi ta tambayeta

” ba wani matsala ni dai kawai sonake kije ki dawo, bazan iya rayuwa ba kya kusadaniba, sannan na kagu inga yan uwanki ummk, “

Jikin Ummi yayi sanyi tasan akwai matsala ne take kokarin boye mata, 

” Baby wayace miki idannaje dawowa zanyi? Bazan kuma dawowa ba nima a cikin ahalina zan zauna”

“haba ummi karkiyimin haka mana, wallahi ko ina kika tafi sena biyoki, bazan iya rayuwa babu ke a kusa daniba” 

Ta karashe maganar tareda fashewa da Kuka, dama kukan take ta boyene dan kar ummi tagane

“is ok my dear, ina nan zuwa jibi Insha Allah, a satin nan zanje gida Nima kidena kukan haka” 

Ummi taita rarrashinta, sukayi sallama

Wunin ranar Jalila a daki tayishi tana kuka, gashi ko abinci bataciba, Nana tayi juyin duniya akan Jalila taci abinci amma taki ci, haka take ma a bangaren Jawwad shi yayi breakfast amma bayan nan beci komai, 

Jalal ya kalleshi

“kai nifa yunwa nakeji, kaje kace ta kawo mana abinci” 

Jawwad ya kalleshi

“wakenan?” 

“kafini sani ai, ni yunwa nakeji” 

“haba Jalal nagaya maka halin da take ciki, ya za ayi ta wani dafa abinci”? 

“Ina ruwana da halin da take ciki? Halin da cikina yake ciki ne ya dameni,” 

Jawwad ya kalleshi

“toni na damu da halin da take ciki, ina ji a jikina har yanzu kuka take” 

“Ko? Da gaske ka damu,? Aini ban saniba, tunda banga kana kukan ba kaima, sharokhan sarkin soyayya, kagani ka tashi kasamomin abinci” 

Wani mugun kallo Jawwad yayi masa, ya tashi yashige bedroom ya bar Jalal a palour 

Jalal yai murmushi ya girgiza kai

  Bayan la’asar Maama ta kira Nana tasata a gaba suka fita, tareda Yaya mairo, sannan ta aiki Halima, akabar Jalila a gida,

Jawwad yaji karar motar Maama ya leka ta window palournsa yaga fitar Maama da Nana da Yaya mairo, Jalal ya uzzurawa Jawwad se ya tashi ya rakashi cin abinci, dan baze bari yjnwa tayi masa illa ba Badan Jawwad yanasoba ya tashi suka fita, 

Fitarsu Nana, hakan yabawa Jalila damar yin kukanta yannda take so

Tabbas da watace ta gaya mata abunda aka gayamata yau a cikin gidan nan to da setayiwa Yaya mairo rashin mutuncin da harta mutu baza akuma yimata makamancinsa ba

Amma kash koba komai yakamata tayi al kunya ko dansu Jawwad, ga nasihar umminta data dingayi mata akan tayi hakuri dazaman da zatayi da mutane, gajiya tayi da zaman cikin gidan, zuciyarta na ayyana mata abubuwa, tasan tunda aka fara haka, lallai Maama zata dau shawarar cigaba da cuzgunamata, kuma yau da gobe se Allah dan wataran zata iya marin mace akan taba mata uwa. 

Tashi tayi ta fito harabar gidan, zuciyarta na saka mata abubuwa dayawa

Ilham ce ta shigo gidan, ta hangi Jalila tsaye a wajen kofar shiga cikin gidan, ta nade hannuwa tayi shiru alamun tana tunanin wani abune, 

Zuwa tayi zata wuce amma Jalila na tsaye a bakin kofar bata fito ba bata shigeba, 

Seda su Jalal suka je karshen layi, sannan ya tuna yabar wayarsa, yace Jawwad yayi parking ya jirashi yaje ya dakko baxe dade ba, Jawwad yayi parking, Jalal ya sakko ya tafi. 

Ilham ta karasa inda Jalila ke tsaye

“Zan wuce” Ilham ta fada tana kallon Jalila 

“basa nan masu gidan, ki koma inda kika fito” Jalila ta fada a takaice

“ke bana son shirme, ba gurinki nazo ba ai” 

“Nasan ba gurina kikazoba, bazaki shiga bane kawai tunda ba kya ganewa nace miki ba sa nan” 

A tsawace Ilham tace

“Ke dakata Malama, karki gayamin magana mana, da kikemin wannan gadarar, aiba gidan ubanki bane, dan nasan ubanki ko taku daya bashi dashi a gidan nan” aikuwa Jalila tayi niyyar sauke fushinta akan Ilham, takuma kallon Ilham 

“Ke daga inda kike gidan naki ubanne ai, saboda tsabar arzkin ubannaki shiyasa naga yabarki kina ragaita tsakanin gidan yan uwa, saboda kwadayi” 

“Hmm Aida tuni gidan ubanane, wasu dalilai suka hana faruwar hakan, amma wataran dukiyar da kike magana zatazama mallakina” 

Kallonta Jalila tayi baki bude

“A matsayinki nawa, dukiyar uban wani zata zama taki kwadayayyiya, aje ai takama da dukiyar uba, bata uban waniba, malama kijuya inda kika fito, 

” Karki gayamin maganar banza malama, kodamene ubana yafi ubanki, tunda nasan kowa kika tambaya ze gaya miki inada Uba, amma ke wayasan naki uban

Wani wawan Mari Jalila ta saukewa Ilham batare data bari Ilham tagama maganar ba

” Karki kuma dukanmin kanwa, inkika kuma sena rama mata”Muryar Jalal ce, suka waiga gaba daya.

Jalala ya karaso inda suke, ya kalli Jalila, “kina kuma marinta kema sena mareki, mara kunyar kawai, Ilham sa’arki ce?”

Wani banzan kallo Jalila tayi masa

“Ilham din banza Ilham din wofi, wallahi ta kuma zagina sena kuma wankamata mari dama Jakace kaima kasaba jibgarta, sha3 Karya banza

Mamakine ya cika Ilham wai ita yake tarewa fada, kallon Jalila tayi

” Kece babbar karya baniba”

Jalila tace “kinga karnuka nan” ta nuna Ilham da Jalal,

Ilham tace “Nida yaya Jalal dinne karnuka”

Tsaki Jalila tayi, ta shige ciki, ta hankado kofa, Ilham ta kalli Jalal

Zatayi magana kawai yai tafiyarsa, yabar gurin dama dan ya kuma kunna Jalila yayi, ba nufinsa ya shigarwa Ilham ba, suka batta a tsaye baki bude

“to me suke nufi da hakan?” 

Babu me bata amasa dan haka ta juya ta koma gida, se bayan sallar isha’i sannan su Nana suka dawo, Nana tai tabawa Jalila hakuri akan sun tafi sun barta ita kadak, Jalila ta nuna mata bata damu ba, tun ranar da Yaya mairo tazo tayi wannan cin mutuncin Jalila bata kuma bari sun hadu da Jawwad ba, ya damu sosai ko wayarta inya kira bata dagawa, ko palourn ma ta dena fitowa se dai ta zauna a daki, 

   

   Yau ta tashi da murnar ummi zatazo, amma haryanzu ba saki jikinta ba abunda su Yaya mairo sukayi mata yana taba mata zuciya, sannan idan ta tuna ummi tafiya zatayi ta barta a gidan, setaji ba dadi, 

Nana da halima ne sukayi wa Jalila kara sukayi girki domin tarbar ummin Jalila, amma ita kam ko san fitowa batayi, seda Abba yasa aka kirata ya tambayeta ko akwai matsala kwana biyu baya ganin gilmawarta, amma tace masa ba komai, Jawwad ma yayi sintiri a cikin gidan amma baya samun ganin ta, gashi yana tsoron yaje dakinsu Jalilan, saboda Maama, in yakira Nana yace tabata wayar se taki karba, Jawwad ya damu sosai

Karfe sha biyun rana ummi ta iso gidan, Jalila kaman ta shige cikin ummi dan farin ciki, tayi murna matuka, Abba yana gidan saboda zuwanta, Maama dai ba yabo ba fallasa ta tarbeta saboda idon Abba, Jawwad ya shigo domin gaida ummi, se lokacin yaga Jalila, ta dan fada idonta yayi zuru2 tana manne  a jikin ummi, tausayinsune yakama shi, suka gaisa da ummi, daga nan ya shantake akayi ta hira, ya tashi ze fita ya waigo ya kalli Jalila yace

“Jalila, dan Allah kawomin coffee” 

Abba yace

“Yayana kafiye takura, tana zaune tana jin dumin ummin zaka sakata aiki, murmushi Jawwad yayi yana dan sosa keya, Maama kam wani mugun harara tayi masa, suna hada ido da Maama ya sunkuyar da kansa kasa, ummi kuma tace

” Ai ba wani takura dan yasata aiki, ai kanwarsa ce, tashi ki kaimasa” 

Jalila ba dan tasoba ta mike taje ta hado masa, ta fita domin kai masa, Maama a ranta tace “lallai Yaron nan, wato beji maganar da mukayi masa ba kenan?, aikuwa sena saba masa” 

Jalila tana kaimasa, ta ajiye ta juyo zata fice Jawwad ya kira sunanta

“Jalila” cak ta tsaya amma taki yadda ta kalleshi, 

Tasowa yayi yazo gabanta ya tsaya, suna iya jin numfashin juna, muryarsa a sanyaye yace, “Baby menayi miki na cancanci wannan hukuncin? Kin kauracewa ganina, tsawon kwana biyu, kinki daga wayata, kinsani cikin damuwa, Baby why?” 

Dan dagowa tayi ta kalleshi, idonta sun ciko taf da hawaye, ta sunkuyar da kai, kallonta yayi ya kuma sassauta muryarsa 

“Ohhh no Baby, nagane, Jalila you are not suffering alone, i also feels what you feel, Baby dan Allah kiyi hakuri akan abunda akayi miki, kar hakan yasa ki kuma, kauracemin kwana biyun nan na shiga damuwa, sannan kidena zubar da hawayen nan, banaso, kuma in Ummi, taganki cikin damuwa bazata ji dadi ba”

Gaba daya jiknta yayi sanyi, duk yabata tausayi, ta gyada masa kai alamun ta gamsu da maganarsa

“Kindena kukan?” 

Ta gyada masa kai, ya ciro handkechief a aljihunsa yabata, ta goge hawayen da yake idonta, ta mika masa, sannan ta fito, ta koma cikin gida, 

Ta tarar ummi tana cin abinci, spoon ta dauka tazo ta zauna, suna ci da Ummi, 

Zuciyar Ummi fal tausayin Jalila, akwai abunda yake damunta, amma taki fada mata, 

Nana ta fito taga Jalila da ummi suna cin abinci tare, ta kalli Jalila

“Wato dan ummi tazo shine, yau bazaki ci abinci dani ba?” 

Dan murmushi Jalila tayi, wanda iyakacinsa lebenta

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“Ni na isa, Nana” 

“gashi nan makuwa nagani” 

Ummi ta kallesu tana murmushi

“kema dakko spoon dinki, kizo muci” 

Haka kuwa akayi, suka zauna suna cin abincin tare

Ummi tagayawa Abba, kwana daya zatayi, ta wuce, 

Maama ta shige daki ta kira Naana, ta hanata fiyowa, karshe ma ta aiketa tabar gidan, ta bar Ummi se Jalila da Halima, dakinsu Jalila taja Ummi, ta dinga mata magiya ta tafi da ita, amma Ummi tace mata baze yiwuba, Yanayin yadda taga Maama ta karbeta, tasan akwai matsala amma Jalila tace komai lafiya kalau suke zaune

Haka Jalila sukai ta hira da Ummi wanda hakan ya rage mata bacin ran da take ciki , 

Rabin hirarsu da Ummi, Nasiha ce take mata akan hakuri da karbar kaddara a duk lokacin datazo mata, 

Da dare yayi ma Maama cewa tayi Nana ta kwana a dakinta, tabar musu can, dan bazata kwana a gurinsuba bata san me za a koyamata ba. 

  Washegari tunda safe Ummi tafara shirin tafiya, tun wayewar garin Jalila take kuka, ko karyawa takiyi, karfe goma na safe, Ummi tagama shirinta tsaf ta fito, Jalila janye da trolley din Ummi tana share hawaye, Nana kuma ta dakko karamin jakar Ummu, hakan yayi dai2  da fitowar Abba wanda shi zeje yasa Ummj a motar garinsu, Abba yace a kirawo Maama suyi sallama da Ummi, Maama ba dan tasoba ta fito, sedan kar Abba yayi mata fada, 

Abba ya kalli Jalila yace “Baby muje, asaka kayan a mota” Jalila tayi gaba ita da Nana, ya bisu a baya, suna zuwa harabar Gidan, suka tarar da Jawwad ya kunna motar ya bude kofofin, suna zuwa yaje ya karbi trolley din hannun Jalila yana kokarin bude boot

  Ummi ta kalli Maama da take tayi mata kallon banza, ta danyi murmushi sannan tace

“Zainab har yanzu ina ganin kiyayyata a idonki, bansan dalilin hakan ba, amma ina rokonki ga Jalila nan amana, kar kiyayyata ta shafeta, ki dubi Allah ki dubi maraicinta, in kikaci amana Allah yana kallonki, badan wasiyyar mahaifinta ba Zainab, babu abunda zesa in bar yata a gidanki, tunda nasan ba kya kaunarta, keda danginki, da da ita zan tafi, ko ina ne” Maama ta katseta ta hanyar cewa

“kinga saurara, amanar yarki a hannun dan uwan mijinki take baniba, dan ba muhada dangin komai dake ba, ni ban hada jini da arna ba balle abani amanarsu in karba” 

Murmushi Ummi tayi me ciwo sannan tace”shikenan Zainab ki fadi abunda kikeso, kema kin haifa, bazan fasa fada ba Jalila amana ce, zan iya yafe duk abunda zakiyi min amma banda cin amanar gudan jinin Aliyu, wato Jalila ” Ummi na zuwa nan a zancenta tayi waje tana share hawaye, tareda tausayin tilon Babyn ta. 

Harabar gidan ta fito, suka koma gefe, da Abba suna magana, Jalal ne ya shigo gidan, ya hangi Ummi yana ganinta ya karaso da sauri yana murmushi, yace

” Ummi saukar yaushe”? 

“Abdul Jalal haka ka girma, Jalal ka yadani, ka manta dani” 

Ya dan girgiza kai

“ummi wane ni in manta dake ni na isa, yanzu kikazo ne?” 

“A a tafiya zanyi, tun jiya nazo” 

Kallon Jawwad yayi, sannan ya kalli Ummi 

“Ummi Jawwad be gayamin ba danazo mun gais, yaushe rabon da naganki” 

Abba yace “Lallai Jawwad baka kyauta ba tunda baka gaya masa ba” 

Jawwad yace “Abba ba laifina bane jiya throughout ban ganshiba, ban san inda ya tafiba” 

“amma lambar wayata ma baka ganta ba itama ta tafi yawon” 

Jawwad yayi dariya

“Allah yabaka hakuri” 

Jalila mamaki takeyi yadda ya ke girmama Umminta haka, yasan Ummi kenan, amma ranan datayi mata zancen waye JALAL tace mata bata saniba

Ummi tace “Abdul Jalal ina Mummynka?” 

“tana nan Ummi, yanzu nan ta fita”, daddy kuma baya gari,”

Ummi tace Allah sarki, dan Allah a gaishesu

” zasuji Insha Allah Jmmi”

Jalal ya kalli Abba yace “Abba ka bari, semu rakata” 

Abba yace masa “ai ba kano zata koma ba, tasha zasu kaita, zataje garinsu” 

“Ba komai Abba, bari mu kaita” 

“to shikenan yarona, karbi mukullin” 

Jalal yasa hannu ya karba, 

Seda Jalila ta zare ido, ko dai Abba besan irin tukin da Jalal yake ba, yabashi mukullin motarsa

Abba suka gama maganar dazasuyi da Ummi, Jalila da Nana suka shiga bayan motar, sannan Ummi ta shiga, 

Jawwad kuma ya zauna a gaban mota, sekuma Jalal da zeyi tuki

Suna tafe Jalila tana kuka, Nana, da Jawwad suna rarrashinta yayinda Ummi ta maida hankalinta kan JALAL sunata hirarsu, bawai dan batajin kukan Jalila ba sedai kar garin rarrashinta itama tayi kukan, 

Ummi tace “Jalal ya karatu fa?” 

Yace”Ummi kicigaba da yimin addu’a, very soon zakiji labari me dadi”

“to Allah ya tabbatar da alkhairi, yabaku mataye nagari kuyi aure” 

Dariya Jalal yayi “Aure kuma Ummi” 

“Eh mana Jalal, aure ai shine cikat mutum” 

“ko ba hakaba Jawwad” 

“hakane Ummi” 

Jalal yai murmushi, tareda dan girgiza kai, 

Haka suka cigaba da tafiya, har suka je tasha, Jalal hira suke da Ummi, aka samawa Ummi mota, suka saimata ticket, Rirriketa Jalila tayi tana kuka, 

“Ummi dan Allah kidawo da wuri, karki tafi ki zauna Ummi” 

Ummi ta dan goge kwalla tana dan dukan bayan Jalila, alamun rarrashi, sannan ta kalli su Jawwad

“ga sister dinku nan, asaka ido akanta, kuyi hakuri da halayenta, dan Allah,” 

Nana tai saurin cewa “Ummi karki damu, Jalila bata da wani damuwa, lafiya kalau muke zaune” 

Jawwad ma yace “ummi karki damu shagwaba nsme kawai takeji, shiyasa take kuka, amma ba wani damuwa,” murmushi Ummi tayi sannan ta dago Jalila tace 

“Baby na is ok, bazan dadeba zan dawo insha Allah, zamu dinga waya, Baby kiyi hakuri da rayuwa, sannan kizama me hakuri da kaddararki, kizama me yafiya da kauda kai, akan al amuran rayuwa, banda tsokana da neman magana duk abunda yasameki kiyi tawwakali ga Allah kinji baby”

Gyada mata kai Jalila tayi

“Yawwa Allah yayi muku albarka, ya hada kanku gaba daya” 

Jawwad yace “Insha Allah Ummi” Ummi ta kalli Jalal “Abdul Jalal ni zan tafi, Allah ya jishemu alkhairi, in ka koma makaranta, a ko bikin yazo kar a manta dani” 

Dariya yayi yace “Hajiya ummi, kidena batun auren nan fa, zan karbi lambarki gurin Jawwad mudinga gaisawa” 

“to shikenan ku koma haka nagode sosai,” 

Ta dan rungume Jalila tai kissing dinta a goshi

“kidena kuka, addu a zakiyimin” 

Daga haka Ummi ta shige motar

Jikin Jalila a sanyaye, suka koma motarsu suka dau hanyar gida,

Jawwad se bawa Jalila baki, yake kan tayi hakuri amma kaman yana zigata, ta kwanta akan cinyar Nana, se kuka take, 

Kukan Jalila ne yacikawa Jalal kunne, ya samu guri, yayi parking, sannan cikin tsawa  yace “dallah Malama ki rufewa mutane baki, se wani lallabaki ake kina cigaba da kukan, Wani abunne yasamu, Ummin dazaki dinga yiwa mutane kuka haka, in baki rufemin bakiba sena makeki wallahi” 

Yadda yayi maganar seda hantar cikin Jalila ta kada, saboda cikin tsawa yayi maganar, Jawwad yace wa Jalal “dan Allah kayi hakuri ka kyaleta

” Bazan kyaleta dinba Wallahi ta cigaba damin kuka seta sauka, bana son shirme”

Nana tace “Yaya Jalal dan Allah kayi hakuri, tadena, Jalila dan Allah kiyi shiru” 

Banza Jalila tayi musu, amma ta rage sautin kukan, da kyar Jawwad ya lallabashi, yaja motar suka tafi, 

Bayan sun koma gida Jalila kaman wata marainiya, abun duniya duk ya dameta. 

Halima ta lura da damuwar da Jalila take ciki, dan haka  Halima taita rarrashinta

“sayyada Jalila dan Allah ki saki ranki, gidan ba dadi in bakya walwala, Ummi zata dawo fa” 

Jalila ta danyi yake

“leemart baki san yanake Jiba, wallahi zuciyata ba dadi”

“Nasani Jalila, amma kiyi hakuri, damuwa ba shine mafita ba” 

“hakane nagode” 

“yawwa kisaki ranki” 

Jalila taita kiran Ummi tana tambayarta ko ta karasa, Ummi tace mata in taje zata kirata, 

Hakanan Jalila taji hankalinta yaki kwanciya, bayan la’asar ta kuma kiran wayar Ummi amma taki shiga, da farko tayi tunanin ko network ne amma wasa2 har karfe tara na dare wayar Ummi a kashe, hankalinta ya tashi matuka, 

Nana tace “dan Allah Jalila ki nutsu ki kwantar da hankalinki, maybe bata da cajine” 

“Nana cewa kike in kwantar da hankalina, ta yaya? Dazu fa muka gama waya amma ace yanzu wayar bata shiga” 

“To kika sani ko network ne, kinsan hanyar, akwai dazuka, dan haka ba lallai asamu Network ba” da haka hankalin Jalila ya dan kwanta, 

Amma har gurin karfe sha biyun dare, Jalila takasa hakuri trying lambar Ummi ta kumayi, amma still switch off

Jifa Jalila tayi da wayar ta fashe da kuka.

Sosai Jalila take kuka, tareda surutai, 

“Haba Ummi dan Allah ki daga wayata mana, hankalina ya tashi” 

Sam bacci ya gagari Jalila, tayi trying lambar Ummi bata san adadi ba amma a kashe, Nana kam tuni tayi bacci, yadda Jalila taga rana haka taga dare, bacci ko barawo be dauketa ba, ta kagu gari ya waye, 

Da asuba Nana tashi tayi taga Jalila akan dadduma, ta sunkuyar da kai, bata san Jalila batayi bacci ba ta dauka dai ta tashi da wurine, Kamar kullum Nana tayi sallar asuba ta koma baccinta, mikewa Jalila tayi ta fita daga dakinsu idonta ya kumbura, yayi jawur, ga rashin bacci ga kuma kuka da tasha, kai tsaye kofar part din Abba ta nufa, a hankali tafara knocking, tayi ya kai sau hudu, sannan taga an bude, Maama ce ta bude, ta kalleta a wulakance

“Ke! Meye haka zakizo kinamana knocking da safiyar nan” 

Jiki a sanyaye Jalila tace “Kiyi hakuri gurin Abba nazo” 

“ikon Allah yaushe kika zama matar gidan nan dazakizo gurinsa da sassafe haka” 

“A a Maama dama wayar Ummi ne tun jiya da yamma ya dena shiga shine… 

” Shine Me? Fitowa zeyi ya tafi nemo miki ita, Allah ka dai yasan gidan uban data tafi, dalla matsa kibani guri”

Maama ta maida kofa ta rufe, silalewa Jalila tayi a gurin, tacigaba da kuka kuka 

“Kingani ko Ummi dakin tafi dani da koma mene ze faru ina tareda ke” 

Se karfe tara na safe Abba ya fito, yaga Jalila a kofar part dinsa a zaune, tana kuka, “Subhanallah Jalila me yasameki haka,?” 

Kuka takuma fashewa dashi

“Abba, Ummi tun jiya da yamma, lambarta ta dena shiga,” 

Tabbas dan shima ya kirata amma taki shiga, cikin sigar lallashi yace

“Kiyi hakuri kinji diyata, yanzu kije kiyi breakfast, zan cigaba da trying lambarta, in be shiga ba zanje tashar motar da kaina inji me ake ciki” 

Gyada masa kai tayi ta mike ta koma palour ta zauna tayi shiru, se hawaye dayake bin fuskarta

Wasa2 har azahar babu labarin lambar Ummi, taki shiga, Jalila fa tafara fita hayyacinta, babu cin, Abinci takasa nutsuwa, Jawwad da Abba suka tafi har tashar da akasaka Ummi a mota, amma aka tabbatar musu da cewa motar taje har garin sun juyo, sedai sunyi tsaye2 sun sauke fasinjojii, amma lafiya sukaje suka dawo, 

Se dare su Abba suka dawo, amma ba wani labarin samun Ummi, Wunin ranar babu batun nutsuwa a tareda Jalila, kuka kam idon harya kafe, babu hawaye se ajiyar zuciya kawai da take yi, Maama ko kallon Jalila ba tayi ba balle wani magana me dadi ta fito daga bakinta, Nana da Halima ne kawai suke rarrashinta, 

Su Abba suna dawowa Jalila ta mike, tana tambayarsu, ya akayi? “

Abba yakama hannunta ya zaunar da ita, sannan yace 

” ki kwantar da hankalinki, kinji, munje tashar motar, sunce mana motocinsu sunje lafiya, sun sauke fasinjojin su lafiya sun dawo, dan haka muna da tabbacin Ummi ta sauka lafiya, watakila wayarta ce tasamu matsala amma sunje lafiya, zuwa gobe Insha Allah nida Jawwad zamu kuma komawa, in takama mu bibiya har can garin nasu zamuje, amma muna fatan komai lafiya ” hankalin Jalila ya dan kwanta kadan,

Abba ya mike, ya koma part dinsa, Jawwad yasa halima ta zubo Abinci ta hado da tea, ya zauna yasaka Jalila a gaba, ya takura mata, amma ta tsakuri kadan tace ta koshi, karbar Abincin yayi, ya dan hade rai, sannan yafara bata a baki, karba take tana ya tsuna fuska, “Yanaga kina bata raine, kiyi hakuri kici Abincin mana” ta yamutsa fuska, muryarta kasa2 tace

“kaina fa ciwo yake” 

“to yi hakuri, ci Abincin, se in kawomiki magani” ta gyada kai 

Yana cikin bata Abincin ne, Maama ta fito, wani mugun kallo tai musu

“Kai Jawwad meye haka, ban isa in gaya maka kaji bako?, meye nawani zama kana bata Abinci, tashi kabar nan malam, tashi kafita sha3 kawai, jiki a sanyaye ya mike yana waiwayen Jalila, yayinda ita kuma ta sunkuyar da kai, Maama ta kalli Jalila sannan tace” Mayya kawai, Mara zuciya” dagowa Jalila tayi ta kalli Maama, ta mike ta bar mata palourn, takoma dakinsu, 

Jawwad ya koma dakinsa abun duniya ya dameshi, yayi wanka yayi sallar isha’i ya dawo ya zauna a palour, yayi shiru yana tunani, 

Jalal ne ya shigo, yazo ya tarar da shi a palour ya samu guri, ya zauna ya kalleshi

“Ina kashigane nazo baka nan, ina ka tafine?” 

Ajiyar zuciya Jawwad yayi sannan yace

“Akwai matsalane Jalal” 

“matsalar mene?” 

“jiya bayan mun kai Ummi tashar mota, tun bayan la asar har yanzu danake maka magana ankasa samunta a waya, lambobinta basa shiga, har tashar motar mukaje nida Abba, amma sun tabbatar mana motocinsu sun isa lafiya sun dawo,” 

“To ya akayi haka tafaru?” 

Jawwad yace “nima ban saniba Jalal, gashi Jalila ta daga hankalinta fiye da yadda kake tunani, ko abinci taki ci, yanzu na tursasata ina bata, Maama ta koreni, kuma hada gayamata munanan magana, Jalal narasa me zanyi, a halin Yanzu Jalila na bukatar me kwantar mata da hankali, ta damu kwarai”

Ajiyar zuciya Jalal yayi sannan yace

“to yanzu wani mataki aka dauka amma da mamaki ace wayarta bata shiga kuma by now, dai nasan ta isa, kwara state, kuma nasan bazata kasa kiran wayaba” 

“Koni jiyan da azahar munyi waya da ita, Gobe in Allah ya kaimu zamu koma tashar, in takama mutafi can garin nasu se muje, ina tausayin Jalila,” 

“Allah yasa komai lafiya” 

Jawwad yace “Ameen” Jalal ya dafa kafadar Jawwad 

“Ka kwantar da hankalinka, karkasa damuwa a ranka, komai zezo da sauki, bana son ka damu” 

Dan murmushi Jawwad yayi sannan yace “to naji” 

Daga haka Jalal ya tashi ya tafi gida, yunwa duk ta ishi Jalal dan ba wani Abincin kirki a cikinsa, saboda Jawwad baya nan, gashi baya son shiga cikin gidansu, dan yasan inya shiga kafin ya fito se an bata masa rai, har ya kwanta, ya tashi ya nufi cikin gida bakowa a palourn, dan haka ya wuce kitchen zuwa yayi yaita bude2, ji yayi kaman da mutum a tsaye a bayansa yana waigowa yaga Ilham a tsaye, da wata yar riga a jikinta, iya gwiwarta, dauke kansa yayi, yacigaba da abunda yake, a hankali ta tako ta karaso cikin kitchen din, ta dan kalleshi

“My star, me kake nema ne?” 

Be amsamata ba balle ya kalleta, 

“Ko kanajin yunwa ne?” shiru yayi mata, ya nufi fridge, bayansa ta kuma bi

“haba star, ka kalleni mana, ka amsamin” 

A fusace ya juyo

“Ohhh God, haba wai meye hakane? Kinyimin magana nayi miki shiru, base ki kyaleniba, kalleki kalli Jikinki, ya dace kizo inda nake a haka, get out from my side” 

Ita a tunaninta shekaranjiya da ya shigar mata fada ko yafara sakkowane, amma yanzu setaga abun bahakaba, shi har yawani san abunda ya dace, ko be daceba, bayan giya yake sha, ga sauran lefuka, amma ta maze ta matso inda yake 

“Yaya Jalal kenan, nasan yunwa kakeji, kawo in dafa maka wani abun kaci” 

“No need” shine abunda yace mata kawai, kuma matsawa tayi daf dashi, yana juyowa suka hade, zuciyarsa ta buga da karfi, 

Ta dan tsura masa ido, 

“Meyasa kullum baka da burin daya wuce azabtar da zuciyata ne, kasan ko yadda nakeji? Please Yaya na, love me too” 

Shiru yayi mata yasa hannunsa biyu, ya tureta gefe, yakama hanyar waje, sauri takumayi tasha gabansa, tana kallonsa, Ajiyar zuciya yayi sannan yace

“bana son yi miki wulakanci, u are pushing me to the wall, meye haka ne? Meyasa bakida kamun kai Ilham, a hakan kikeso in aureki,? Kalli yadda kikemin ba kya tunanin haramcin hakan, kina tunanin ko na aureki zan yadda dake” 

Ta dan nisa

“Yaya Jalal kome nayi kaine sila, meye laifina dan Nace inasonka, da soyayyarka na budi ido why Yaya Jalal? Msyasa baka sona” 

Hade rai yakuma yi “Ana so dolene? Tun farko nagaya miki, niba na 

ra ayinki, kije kisamu wani, ni bani da niyyar aure yanzu, ki hakura mana, nagaya miki gaskiya bazan aureki ba, ” 

“Yaya Jalal agaban idona kake gayamin bazaka aureniba, to bari ingaya maka, kayiwa duk wadda zaka aura Albishir din, ta tari bala’in dabata san karshensa ba, wallahi kowa ka aura, sena hana muku farinciki baka isa ka auri wata baniba indai ina raye a doron kasa, kuma ko bana raye fatalwata seta hanaku sukuni,”

Murmushi yayi kawai yai waje, ya fasa daukar abunda yayi niyya, a ransa yace” lallai yarinyar nan bata da hankali”

Ilham takoma dakin tana jujjuya maganganun Jalal “Wallahi karya kakeyi Jalal, kozan tafi tsirara se nacikawa Mamina burinta, zakaga tsiya, senayiwa Jalila abunda se ta mutu da bakinciki, dan na lura itake kara, batamin aiki, da raina wallahi bazakayi aure ba da wata mace inba niba, if not inyi abinda zan karya asirin kowa ya huta, haka Ilham taita surutai marasa kan gado, 

Shikam Jalal, Ya fita harabar gidan ya tsaya, yana nazari, ya Kalli agogon hannunsa daga baya ya dau motarsa ya fita, Club ya tafi abunsa yaje aka cashe aka sha giya, yai manksa abunsa, yana tangadi  se kawoshi gida akayi. 

  Dare yaraba, Jalila se nafila takeyi, tana addu a Allah ya bayyana mata Umminta yasa tana lafiya, se gefin asuba bacci yasaceta akan daddumar datayi salla, a cikin baccinnata maimakon tayi mafarkin Ummi tunda itace a ranta, setayi mugun mafarkin data saba yi akan Jalal, a firgice ta farka, tana ambatar sunan Allah gaban ta na faduwa, Nana ta taso tazo inda take, ta dafata “Jalila lafiya kuwa?” rirrike Nana tayi ta fashe da kuka

“is ok dear, yi hakuri, Insha Allah komai zezo da sauki, a yau za a ga Ummi Insha Allah” gyadawa Nana kai kawai tayi, seda ta dan samu, nutsuwa sannan ta mike tayo alwala tazo ta tayar da sallar asuba, 

Da sassafe karfe shida Jalal ya tashi yai wanka yai salla, ya dau motarsa ya fita ba tareda wani yasan inda ze tafiba, dan ko Jawwad be gaya masaba. 

Karfe takwas na safe Abba da Jawwad suka hadu a palour zasu kuma fita, Maama ta Kalli Abba

“wai Dan Allah yanzu fita zaku kumayi, ko karya bakuyiba, nasan wallahi wani gurin tai tafiyarta amma duk ka daga hankalinka” 

Abba ya kalleta

“kina tunanin, zata iya tafiya wani gurin batareda sanin yarta ba, bari in tunamiki abunda kika manta, Maryam da Jalila amanar dan uwana Aliyu ce dasu Inna, idan naci wannan amanar Allah baze barniba, dolena innemo abunda yasamu Maryam dan na tabbatar, da taje lafiya, da komai lafiya nasan, komae ake ciki, zata gayamin”

“kai kake ganin hakan amma a gurin su aikata irin wannan ai ba wani abun damuwa bane, ai abun kunyane ta koma garinsu da yarinya bayan basu san tayi aureba, kodayake su ina suka san wata kunya” 

“Ya isheki haka Zainab, Wallahi zan bata miki rai fiye da yadda kike tunani, akan cin zarafin matar Dan uwana, babu bawan da ya isa ya kuskurewa kaddararsa,” 

Jawwad ganin sa’ insa na neman barkewa tsakanin iyayennasa, se ya kewaye ya tafi dakinsu Nana, ya tarar da Jalila ta dora kanta akan cinyar Nana, tana zubda hawaye, yayinda Nana take bata hakuri, karasowa yayi ya tsuguna

“Baby baki dena kukan bako? Dagowa tayi ta kalleshi, sannan ta sunkuyar da kai, kiyi hakuri yanzuma fita zamu kumayi da Abba Insha Allah zamu gano inda take, ki dena kukan nan kinji, ze iya kawo miki matsala” 

Ta dan Jinjina masa kai, ya Kalli Nana yace “Nana dan Allah ki tabbatar taci Abinci” 

“to Yaya Insha Allah” daga haka ya mike yafita cike da tausayin Jalila, 

Yana fitowa palour yaga ba kowa dan haka ya fita harabar gidan ya tarar da Abba a zaune a cikin motar yana Jiransa, Jawwad ya shiga motar ya kunna suka fita, 

Har la’asar babu wani kyakykyawan labari, dasu Jawwad suka samu game da Ummi, kuma har yanzu wayarta bata shiga, haka suka gaji suka dawo gida, koda Jalila taga sun dawo, da sauri ta tashi, ta fita domin sanin me ake ciki, Abba  yasa aka kiramasa Jalila, Jalila tazo, ta durkusa a gabansa

Koda taji Abba yafara dayi mata nasiha ta karaya ta kuma fashewa da kuka

“Shikenan na rasa Ummina, Ummi dama haka zakiyimin, kikayimin wayo kika tafi kika barni, yanzu ba Abee ba Ummi” 

Jawwad yace “haba Jalila duk bagamuba, kuma Ummi fa bacewa akayi ta mutuba tana nan da ranta, kuma mun bada cigiyarta gurin” ‘yansanda, insha Allah za a sameta, kidena kuka”

Daga Abban har Jawwad din Jinsu kawai take, dan bata san me suke fada ba, hankalinta sam baya kansu, dan wani abune yazo saitin zuciyarta ya tsaya, shibe fitaba, shi be komaba, 

har magariba, Jalila kaman wata mara hankali, batun Abinci dama babu shi, dan ko ruwa bata zubawa cikinta ba danba Yadda Nana batayi da itaba amma taki cin komai, banda aikin kuka ba abunda take, ga gefe cikinta da ya kulle saboda rashin Abinci, 

Bayan sallar Isha’i kaman me tabun hankali ta mike ta nufi part din Abba, ta tarar dashi da Jawwad da Maama a palourn sa, tsayawa tayi tana tunanin to intaje mezatace masa, 

Wayar Abba aka kira, yasa hannu yadaga, yayi sallama sannan yadanyi shiru

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ya furta” Jawwad ya kalleshi a kidime “Abba lafiya kuwa?” 

“Jawwad, wai Ummin Jalila wai motace ta bigeta kafin sukarasa garinsu, ta sauka yin salla, kuma wanda ya bigetan yasata a mota ya tafi da ita” 

Da jin haka Jalila ta kwalla kara, sekuma ta kame a tsaye, gaba daya suka juyo suka kalli inda take tsaye, idonta a kafe a kansu, mikewa Jawwad yayi da sauri ya nufi Inda take amma ko motsawa batayi ba, kuma ko kyafta idon batayiba, Yana tabata ta tafi zata fadi, da sauri Jawwad ya rikota, Abba ya taso da hanzari “lafiya kuwa, meyasameta?” 

Idonta a bude kar, amma bata mosti bata numfashi

“Innalillahi wa inna ilaihi raji un Abba Jalila ta mutu” 

Maama na jin haka ta taso da sauri

“kamarya ta mutu?” 

Abba ne yasa hannu ya janye Jalila daga hannun Jawwad, yana jijjigata amma idonta a kakkafe, hannu Abba yasa ya rufe idon Jalila babu alamar tana numfashi, Jawwad ya kalli Abba

“Abba wai mekake nufine, ba dai ta mutu ba,” shiru Abba yayi bece komai ba, Jawwad yakuma cewa “Abba kayi magana mana,” Nana ce ta shigo palourn Abba, “lafiya kuwa Maama inajin hayaniya tundaga palour” hankalinta ya kai kan Jalila dake kwance a jikin Abba, Jawwad kuma, kaman baya hayyacinsa, da sauri takarasa inda suke “Abba meyafarune”

Maama ta kalleta “Ke meye haka ki nutsu mana, mutuwa tayi” zarewa Maama ido Nana tayi, “wallahi karyane” ta cacimo Jalila daga jikin Abba “Yaya Jawwad dagaske Jalila ta mutu, meyasameta, wallahi bata mutuba Abba kajifa ta janyo hannun Abba ta dora a wuyan Jalila, jiyayi alamun jijiyar gurin tana motsawa a hankali, ya kalli Jawwad sannan yace

” tashi maza ka fito da mota, mu tafi Asibiti, da sauri Jawwad ya fita, mintuna kadan ya dawo, ya dauki Jalila kamar gawa yayi waje da ita, kafar Nana bako takalmi tabi bayan Jawwad da gudu, Halima da ba tasan me akeba ganin an wuce da Jalila rai a hannun Allah yasa ta firgice, ga Abba ya fito da sauri shida Maama, Halima ta nufi Maama tana fadin “Na shiga uku meyasami, Jalila ne, Hajiya dan Allah meyasameta?”

“Ke dallah rabu dani, ina ruwanki dame yasameta zakiyi mata maganine, Abba yace” Halima kwantar da hankalinki, suma tayine batajin dadi, amma asibiti zamuje”

Halima a rikice tace “Allah yabata lafiya, dan Allah ku tafi dani Asibitin”

Abba yace “karki damu Halima, kiyi mata Addu a zataji sauki” daga haka yayi waje, itakuwa Maama tasamu guri tai zamanta a palour,

Asibitin doctor salis suka nufa, ba karamin gudu Jawwad yakeba, se kace ze tashi sama, Jalila na kwance akan cinyar Nana, ga sanyin AC amma tana nan yadda take ba wani canji, ko motsi batayi, suna zuwa Asibiti Jawwad ya fita da sauri ya shiga cikin Asibitin ba a dadeba segashi ya taho da doctor salis, Nurses sun turo gado, Abba na tsaye a jikin motar, Jawwad ya karaso ya bude motar ya dakko Jalila, ba wanda zece ba gawa bace, aka dorata akan gadon aka turata, zuwa cikin Asibitin, su Abba suka bi bayansu, suna zuwa kofar emergency suka tsaya, aka shiga da Jalila, su Abba da Nana suka dinga sintiri a kofar emergency tunda aka shiga da Jalila ba wanda ya fito balle su tambayeshi me ake ciki, Nana se kuka take, Abba ya kalleta “Nana kiyi shiru kinji muyi mata addu a zata samu lafiya Insha Allah” Jawwad kam yarasa meyake masa dadi, sam besan mezeyi yaji dadiba, Maama ce ta kira Jawwad “ya akayine naga har yanzu baku dawoba ta mutune”? 

” A a Maama bamu saniba, sun shiga da ita emergency tunda mukaje ba wanda yace mana komai” 

Daga haka ta kashe wayarta, Halima se addu oi take, tana yi wa Jalila adduar samun sauki, sun shafe awanni a gurin nan kafin doctor salis ya fito, yana share Gumi gaba daya suka nufi inda yake

Abba cikin zakuwa yace “Ya ake ciki” ya kalli Abba sannan ya kalli Jawwad

Jawwad yace “Dan Allah kayi magana mana” 

Doctor salis ya nisa sannan yace

“ku kwantar da hankalinku, Alhamdilillah mun samu nasarar ceto rayuwarta cikin ikon Allah, Blood pressure dinta yayi high fiye da tunani, wanda yasa tasamu stroke, yanzu Alhamdilillah tana iya numfashi, kuma bugun zuciyarta yazama normal, sedai har yanzu bata farfadoba, zamu ajiyeta a ICU tukuna muga abunda hali zeyi, 

Dan murmurshi Nana tayi tareda fadin “Alhamdilillah, Allah yabaki lafiya Jalila”

Doctor salis yace “Abba kubiyoni office akwai magunguna dazan rubuta” Abba yace to shikenan muje, suka bi doctor salis office dinsa, akace Nana ta tsaya a waje, Abba da Jawwad suka shiga, doctor salis ya kalli Abba

“Muna bukatar Jini koda leda dayane zuwa gobe insha Allah , zamu kara mata, mun gwada PCV dinta shima yayi kasa, kaman ta dade tana rashin lafiya, ya akai condition dinta ya zama worst haka lokaci daya,? Jawwad ya gaya masa komai, yayi rubuce2 yabasu magungunan da ake bukata su siyo,

Jawwad yace “doctor zamu samu ganinta kuwa” 

Doctor salis yadan girgiza kai “No bazaku iya ganinta yauba gaskiya, zaku iya tafiya, in yaso gobe in Allah ya kaimu seku dawo, daga nan a duba Jinin da za asamata,” Abba yace “Kana ganin ba komai in an barta anan” 

“Eh Abba ba wani matsala, za a kula da ita Insha Allah, ko wani ya zaunama bata hayyacinta bacci take, ba lallai ta farfado a yauba” 

Sukayi sallama da doctor, sukaje suka biya bill dinsu, daga nan suka taho gida, a palour suka tarar da Halima, ta sha kuka, tana ganinsu tafara tambayar Abba, “Ya jikin nata” 

“Ki kwantar da hankalinki ta farfado, tana baccine, an kwantar da ita” 

“Allah yabata lafiya” 

Abba ya amsa da Ameen, dama Nana bata tsaya ba dakinsu ta wuce, jin dakin tayi babu dadi, ta kalli gurin kwanciyar Jalila, da yanzu ta kwanta kokuma tana salla, Hawaye yazubowa Nana, “Allah yabaki lafiya Yar uwa”daga nan taje tayo alwala, tai sallar Isha’i, ko kayan jikinta bata canzaba ta haye kan gado tayi shiru tana tunani, har bacci ya dauketa, 

Koda Abba ya shiga part dinsa Maama tayi dai2 akan gado tana baccinta, ko a jikinta, wanda da yartace da bataga tayin bacciba, shigewa yayi yai wanka, yafito ya dakko sallayarsa ya dawo palour dukda ya gaji matuka yau, wuni sukayi yawon neman bayanin inda zasu samu Ummi, ga wannan abu daya samu Jalila, 

Bangaren Jawwad ya dakko wayarsa ya kira Jalal amma bata shigaba, dan haka ya tashi yatafi gidansu Jalal, da mamakin Jawwad, Jalala baya nan, yasan baze wuce yana mashaya ba, dan haka ya hakura, ya koma gida ya rama sallolinsa ya kwanta, se dai bacci ya kauracewa idonsa, se tunani

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Doctor salis ya koma inda aka kwantar da Jalila, ya dan tsura mata ido, ta rame sosai akan lokacin daya fara ganinta, idonta a rufe ga oxygen da aka samata, a hankali numfashinta yake sauka, sedai bugun zuciyarta ne har yanzu be daidaita ba, kallonta ya cigaba dayi, dukda ta rame amma setayi kyau, goshinta kwance da gashi, ga girarta itama a cike take da bakin gashi, doctor salis y shagala sosai da kallonta, tareda tunani2 daban2 akan Jalila, yaji an taba shi waigowa yayi, yaga Abokin aikinsane, wanda zeyi night, suka gaisa 

“Salis har yanzu baka tafi ba? ai nazata katafi tun dazu” 

“A a doctor ban tafi ba,” 

“Dare yayi sosai fa, yakamata ace ka tafi” 

“eh anan zan kwana” doctor Khalid ya kalleshi

“naga kai kayi dutyn yamma” 

“Eh, ina da patient ta mussaman” Salis ya nunamasa Jalila

Gyada kai doctor Khalid yayi, yai gaba abunsa

  Da sassafe Nana ta tashi ta kintsa, Halima ta dama kunun gyada dan Jalila na matukar sonsa, har Abba ya tashi ya shirya Maama bacci takeyi, suka kintsa suka tafi Asibiti, Jawwad ya kira lambar Jalal har ya gaji amma Jalal be daga ba, yaso yaje ya kuma dubawa ko yadawo, amma da wuri suka fito, dan gari da sauran duhu, dan haka be samu damar komawa yaduba ko Jalal ya dawoba,

Suna zuwa asibiti, Jawwad ya nemo doctor salis, doctor salis yace su kara hakuri har yanzu bata farfado ba, amma za a gwada Jinin Abba kona Jawwad wanda yayi zasu dauka, domin sakawa Jalila, aka duba jinin Jalila da nasu, amma babu wanda yazo daya dana Jalila, cikin damuwa Jawwad yace “to yanzu meye abunyi?” 

Doctor Salis yace ” A yanzj gaskiya mu   a lap dinmu bamu da irin Jinin ta, sedai inmaka kwatancen Asibiti wani abokina kaje can, in akwai kace nina turoka sesu baka,” 

Abba yace “to hakan yayi kyau,” doctor salis ya dakko wani takadda yayi rubutu, yabawa Jawwad, Abba yace “

salis, baze yiwu muganta ba ne?” 

Doctor yace “Abba ka kara hakuri tana, karkashin kulawa ta mussaman bazaka samu ganinta ba amma insha Allah zuwa anjima in akasamata Jinin zamu fito da ita” 

Abba yace “to shikenan, Jawwad muje ka ajiyeni, zan yi wani abunne, kai seka wuce ka karbo jinin, insha Allah anjima kadan zan dawo” 

Suka tashi suka fito, Jawwad yace Nana tazo su tafi tare ba yanzu za a fito da Jalila ba, 

Maama ta tashi, ta duba bataga Abba ba, taji gidan tsit, ta fito palour taga halima tana aiki, “Ke halima Abban Jawwad ya fitane” 

Halima ta dan risina

“Eh hajiya sun fita gaba dayansu, sun tafi asibiti” 

Wani dogon tsaki Maama tayi, ta koma dakinta

Halima tabi bayanta da kallon mamaki, tacigaba da aikinta, 

Karfe tara Jalal yai parking motarsa a kofar gidansu Jawwad ko daga ina yake oho, da sauri ya nufi part din Jawwad, amma yaje ya tarar Jawwad baya nan, gashi kuma wayarsa ba caji balle ya kirashi, yana fitowa yaga halima tana gyaran harabar gidan

“ina Jawwad ya tafi”? ya tambayeta, cikin isa

“Suna Asibiti an kwantar da Jalila” 

Kallonta yayi sannan yace “me yasameta” 

“Nima bansaniba amma a asibiti ta kwana” 

Daga haka yafita waje ya hau motarsa, ya nufi asibitin, dan yasan asibitin dasu Jawwad ke zuwa, yana zuwa ya tafi office din doctor salis, Jalal yayi sa a, doctor salis yana nan be tafiba, 

Ya mika masa hannu suka gaisa, Jalal ya kalli doctor salis 

“Wani patient su Jawwad suka kawo?” 

“haba kacemin baka saniba? Kanwarku ce fa, wadda Jawwad ya hanani ce Baby” 

“me yasameta?” 

Jalal ya kuma tambayar sa

Doctor salis ya gyara zama, ya zayyanewa Jalal rashin lafiyar ta ta, Jalal yace “Yanzu ina Jawwad din yake”? 

“eh sun tafi neman jinin da za a saka mata, daana Abba dana Jawwad duk beyiba, nima nawa baze mataba dana wa zansaka mata,” Jalal ya kalleshi ya dan tabe baki, sannan yace “Meye blood group dinta? ” 

“Meyasa kake tambaya” 

Hade rai Jalal yayi, 

“Meye kuma na tambayata, kaima kasani patient din Jawwad nawane” 

Doctor salis yace “Allah yabaka hakuri, O+ ne” 

Jalal yace “irin nawane, a dibi nawa akai lap, inba matsala a saka mata” doctor salis yace “to shikenan muje lap din” 

Sukaje aka duba, jinin Jalal, irin natane, kuma anyi gwaje2 amma jininsa lafiya kalau, 

Kafin a dibi Jinin ya kalli salis yace “Wannan sirrine tsakanina da kai, ko Jawwad bana son yasan nina bada jinin, dukda nayine saboda Allah, kuma saboda Jawwad, amma bana son yasani, kace masa kawai wanine yazo yabada jininsa sadaka” 

“To shikenan, bazan gaya masa ba Insha Allah, yanzu ka zauna se su diba” 

Jalal ya zauna aka dibi jininsa, suna gamawa ya mike, aikuwa jiri ya debeshi, yakusa faduwa, lap attendants dinne suka rirrike shi, aka maidashi ya zauna wani ya tambayeshi

“Kaci Abinci kuwa?” 

Jalal ya girgiza kai, dan rabonsa da Abinci tun jiya da safe, youghurt akasamo aka bashi ya dan yasha, ya dan huta sannan ya mike, shi yanzu so yake ya tafi, bayason Jawwad yazo ya tarar dashi anan, Doctor salis se sannu yake jerawa Jalal, Jalal ya kalleshi “Muje ka kaini inganta” 

Doctor salis yace “A a Jalal tana karkashin kulawa ta musamman, baze yuwu ka gantaba” 

“kamar yaya, ganinta zanyi nace ba wani abuba” Jalal ya fada a tsawace, ba shiri salis yayi masa Jagora zuwa inda Jalila take, 

Jalal ya dan tsorata da ganinta, ta rame sosai, ga oxygen a hancinta, gefe kuma ga drip, a hankali numfashinta yake fita, dan girgiza kai Jalal yayi, yai waje dan ko sallama beyiwa Salis ba yayi waje abunsa, motarsa ya nufa ya hau ya tafi gida,

Jawwad suka dawo Asibiti shida Nana, sun samo Jinin amma doctor yasanar dasu an samu Jinin, wani yabada nasa sadaka, kuma yayi dai2 dana Jalila an samata, Cikin damuwa Nana tace “wai har yanzu bata tashiba?” 

Doctor Salis yace, “kiyi hakuri zata tashi ne, ana samata jininne, Insha Allah, zuwa magariba zaku iya ganinta” 

Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace “to shikenan, magungunan ban samosu duka ba, sedai in nafita inkuma dubawa” 

Doctor yace ba matsala, daga nan su Nana suka tafi gida, 

Jalal kam kwanciya yayi, ya kama bacci, dan ya gaji matuka, dukda yunwar da yakeji, gajiya ta hanashi neman Abinci, baccinsa yake sosai, Jawwad ya shigo yaje part dinsa ya tarar Jalal na bacci, se yazata ko giyar ya sha, ya nemi guri a dakin Jalal yayi sallar azahar. 

Nana koda ta koma gida, batabi takan Maama ba ta shige tayi wanka tai sallar azahar, sannan ta nufi kitchen, ta dakko Abinci, tana zuwa palour ta tarar da Maama zata fita unguwa, Nana ta kalleta “Maama fita zakiyine?” 

“Eh zanje kasuwane zan karbo kaya,” 

“Adawo lafiya” 

Daga nan Maama bata kuma cewa komai ba balle ta tambayi yame jiki, ita kanta Nana abun setaji ba dadi, taga Sam Maama bata kyauta ba, haka ta wuce ta zauna ta fara cin Abincinta a palour, Halima ta fito daga dakinta tace “Nana ya jikin Jalila kuwa” Nana tace mata da sauki, daga nan tacigaba da abunda take. 

Jawwad yana nan yana zaune, har Jalal ya tashi daga bacci, becemasa komaiba shima be kulashiba, ya shiga toilet yai wanka, sannan ya zo ya zauna ya kalli Jawwad 

“ya akayine ina ka tafi, da sassafe?” 

Jawwad yace “kai zan tambaya ina ka tafi, tun jiya ban ganka ba, wayarka kuma bata shiga” 

Jalal ya gyara zama “mmmm to na danje wani gurine,?” 

“wani gurine? , bashi da suna” 

“Eh bashi da shi” Jalal ya bashi amsa, 

Jawwad yace “Shikenan” 

Jalal yace “Kai yunwa nakeji, zomuje inci Abinci, ban karyaba, ga rana tayi banci abincin rana ba, nasan gidanku an gama Abinci” 

Jawwad ya kelleshi

“Can inda kaje basu baka abincin ba”? 

“Eh basu banba, dan Allah ka tashi inajin yunwa sosai fa” 

“Me dafawar an kwantar da ita a asibiti” 

“Wa kenan?” Jalal ya tambayeshi kaman besan meyafaruba

“Baby mana an kwantar da ita a asibiti, a can ta kwana” 

“Allah ya sawwake, ya labarin Ummi fa?” 

Jawwad yai ajiyar zuciya, “shine dalilin dayasa ta kwanta a asibiti, Abba aka kira, aka gaya masa wanine ya bige Ummi, kuna ya dauketa ya tafi  da ita, tunda taji haka ta fadi, mu mundauka ma ta mutu a jiyan nan” 

Jalal ya gyara zama, ya dakko sigarinsa ya kunna, ya busa hayakin sannan yace “waye ya kira Abban yagaya masa?” 

“nima bansaniba ina tunanin, ko daga tashane da yabada lambarsa yace in ansamu bayani a kirashi” 

Jalal yace “Hmmm” yacigaba da shan sigarinsa, Jawwad ya kalleshi 

“anjima kadan zan koma semuje tare ka ganta,” 

“inga wa?” 

“ka duba Jalila mana,” 

“da kyar ne inje, ai nace Allah ya sawwake” 

“haka zakace?” Jawwad ya tambayeshi 

“yeah” yafada tareda busa hayakinsa sama Jawwad yaji haushi, dan Jalal ko a jikinsa, ya mike ya fice ya barwa Jalal dakin, yana fita Jalal yai murmushi

Jawwad kenan dan uwana na kaina, wani lokacin akwaika da rashin hakuri 

Jawwad yakoma gida, yasamu abinci yaci, ya tambayi Nana wai ina Maama, ta gaya masa ai ta fita kasuwa, abun yabatawa Jawwad rai amma yai shiru bece komai ba. 

 Seda akayi sallar magariba sannan Maama ta dawo, lokacin Abba ma yadawo, yakuma bibiyar report din daya kai gurin yansanda, ko ansamu wani labari akan wanda ya bige Ummi, amma wunin ranar yagama yawonsa ba wani labari, 

Maama salla tayi kawai, taje ta dauki Abincin Abba ta kaimasa part dinsa, taje ta ajiye masa, amma bece mata komai ba ta kalleshi 

“Abban Jawwad ka dawo bana nan ko? Wallahi fita ce ta kamani” 

A fusace Abba ya dago “dole fita ta kamaki Zainab, tunda ba yarki ce a kwance a Asibiti ba, yarinyar nan tun jiya an kwantar da ita a Asibiti, babu tabbacin zata farka daga suman da tayi, amma koda wasa baki taka kafa inda take ba, ina sane da duk abunda kikeyi, ni bazanci amana ba, dan uwana ya nunamin soyayya, bazan iya wulakanta masa yaba, amma kema kin haifa, Wallhi zainab akan Jalila zan iya rabuwa da kowaye, bakeba har yayan cikina, ita nake kallo inji dadi, Aliyu baya raye amma har yanzu Alkhairinsa muke mora, kije kiyi harkarki inyi tawa, ko kije ko karkije dubata hakan baze sauya komai ba, ki dauke Abincin ki, ki fita karki kara zuwa inda nake!!! “

   Jawwad yai sallar isha i ya koma Asibiti yasamu, doctor salis yana tambayarsa ya jikin Jalila, ya gayamasa sunfito da ita, an bata daki, daga yanzu zuwa kowani lokaci zata iya farfadowa, amma a tanadi Abinci, dan in tafarka a samu a bata, daga nana yagayawa Jawwad lambar dakin da aka kai Jalila, yana zuwa dakin da mamakinsa yaga Jalal a zaune, a can gefe yana shan sigarinsa, gefe kuma ga Jalila a kan gado ana samata ruwa, tana kwance. 

Jalal ya kalleshi yai murmushi

“Sarkin fushi, ya akai na rigaka, zuwa” 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button