Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 12 Book 1 Complete Hausa Novel

 

Jalila na zuwa daidai nan a mafarkinta tai firgigit ta tashi zaune tana gumi, Ta juya ta kalli Nana tana ta baccinta, ita kuwa se maida numfashi take kamar wadda tayi dambe, tanata jujjuya mafarkin nan datayi 

“Tabbas akwai wani abu a boye amma ta Yaya zan Sani, taya zan gane,” gani tayi zaman tunani baze mata magani ba 

Mikewa tayi ta dauro Alwala ta koma kan gadon ta zauna tafara karanta Qur’ani a hankali, a haka har bacci yakuma dauketa wayewar garin yau da Nana da Jalila tareda Ilham sunata hada² shirya abinci domin bakin dazasuzo wato su hanan, suna cikin aikinne, Naja’atu tazo Naja kanwar Sa’ada ce wato “ya’yan Yaya mairo, yayar Maama, daka ganta kasan kanwar Sa’ada ce saboda kamar dasukeyi,

Da Halima ta fara clashing a parlour, ” ke ina Maama take da sauran mutanen gidan naga bakowa?”

“Sunana Halima”

“Bazance Haliman ba, ke zance, kina Yar karere Yar aiki, zan tambayeki, kicemin wani sunanki Halima, koma wace, matsiyaciya kawai mara galihu” Halima tayi saroro tana kallonta, daga baya kuma tace 

“Allah yabki hakuri, hajiya tana bangaren Alhaji, sauran mutan gidan kuma suna dakin girki”

Jalila ce tafito daga kitchen da roba a hannunta

“Ya dai nakejin hayaniya, leemart meya faru” 

“Bakomai bakuwa akayi”

Jalila tana kallon Naja, taga kamanin Sa’ada, tasan Yar uwarsu ce seda gaban Jalila ya fadi

“Sannu da zuwa, bari akira maaman”

“Kekuma daga ina, tambayarki nayi ko gurinki nazo”?, 

Jalila ta dan murmusa

“ai banyi kalarkiba dama balle kice zakizo gurina”

Halima a ranta tace yawwa uwar dakina shiyasa kike burgeni, Jalila ta kalli Halima

“Leemart ga robar ki debo sugar a cikin”

Daga nan suka watse sukabar Naja a parlour, Naja tai kwafa lallai 

“Yan aiki har sun fara samun wannan damar haka a gidan nan”

Dakin Maama Naja taje amma bata ciki, Dan haka tanemi guri ta zauna, bata dadeba Sega Maama tazo 

“Naja saukar yaushe,?”

“Tun dazu nazo”

Download>>> Yar Harka Complete Document

“Amma ban saniba, meyasa Nana bata kirawoniba”?

” oho ni ina na ganta, masu aiki nagani, sukamin rashin kunya a parlour, Maama yaushe yan aikinki suka samu wannan damar,”

” yan aiki kuma? Ai Halima ce kawai Yar aiki “

“A a hadda wata, tanemi tazageni danni bansanta ba, wata Mara mutunci”

” Ke ba Yar aiki bace ba, Yar kanin megidan nan ce Jalila ce fa”

“Wai itace ta girma tazama haka,? Har tanemi ta zageni”

“Ai indai wannan yarinyar ce zatayi fiye da haka”

“To me ta keyi a gidan nan”?

” hmm ta dawo nan da zama”

“Aikuwa zan saita miki ita kafina in tafi, bari inje kitchen din in karemata kallo”

Duk sun maida hankalinsu akan aikin dasukeyi sunayi suna tana hira, Naja ta shigo kitchen din ba ko sallama

“Nana aiki kuke haka”

Waigowa Nana tayi

“Naja yaushe kikazo,”

“Tun dazu nazo, masu aikinku sukayimin rashin mutunci”

“Suwa kenan?”

Nana ta tambayeta, saboda wulakanci seta nuna  Jalila, Jalila a ranta tace “wato hali zanen dutse, yadda mahaifiyarsu Sa’ada ta tsenata har y’ayanta haka suke mata wannan tsanar

Nana ta kalli Naja, lallai ma Naja, Jalila tayi miki kalar masu aiki? To Yar masu gidace me cikakken iko”

“Yar masu Gida kuma?, to ai ya’yan masu Gida mutum biyu nasani, yaushe kuma wannan tazama Yar masu Gida”

Jalila kam tayi kaman bata San da mutum a gurin ba, Nana a hasale tace 

“Kai Naja Wai baki gane JALILA bane”?

Saboda iya gulma secewatayi

” ke haba itace tazama haka, tai wannan kilewar, Yar gidan kiristan nan ko?”

“Kekam Naja wallahi keda Yaya Sa’ada ban San wadda tafi wata rashin hankali ba”

Duk yadda Naja taso  Jalila ta tankamata taki, dan ita yanzu bata ita take ba abubuwan dasuka dameta ma sun isheta, sema karatun Qur’ani data fara a fili, cikin 

kira arta me dadin sauraro (😂😂 Jalila Yar duniyace wato ta maida Naja shaidan, gara tanemi tsari da ita)

Karfe sha biyu da rabi suka kammala, shirya abincikan dasuka yi,

Sukaje sukayi wanka suka canza kaya

  

Yaseera da Ilham sun kule a daki suna tattaunawa, Ilham fuskarta cike da damuwa take magana

“Wallahi yaseera kaina ya kulle nakasa gane ma meyake faruwa, kullum abu kara hargitsewa yakeyi, babu cigaba, kinga rashin mutuncin da yayimin, wai yayi bakuwa namata rashin mutunci namasa krya, waikuma ranan ankkirashi a waya na daga na zagi wadda takirashi, ni abun tambayar wacece, haka hardayake kumfar baki akanta, iya sanina baya shiga sabgar mata, nakasa gane wace ce, da nayi tunanin ko Jalila ce amma kuma naga itama yana kokarin yimata rashin mutunci da kyar nasamu na gudu, Dan rashin mutuncin da nayi masa jiya daya kamani seya kusa kasheni”

Yaseera ta nisa sannan tace

“Abun da daure kai Ilham, amma fa seta yiwu wani makircin Jalila ta hada”

“Anya kuwa Jalila ce tunanina yafara bani ko wata ce daban”

“Ke bar mutum kawai Ilham yanzu abunda ze faru, kama ta yayi mu bigi cikin Jalila maybe mugane wani abu”

“Ta Yaya? Wannan me mugun wayon”

“Da hikima zamuyi ai bada fadaba, amma sekin boye wannan fushin naki, sannan abu na karshe da zamuyi shine, duk yadda za ayi kawai, ayi Auren nan a wuce gurin”

   

Kiran Hanan Jalila tayi, Dan yaci ace sunzo

“Wai yanaji shirune, har yanzu”?

” hh sarkin mita, semu koma, “

“Ke kin isa kukoma, na kagu in gankune,”

“Yi hakuri munkusa, kara turomin address din namanta, na farkon”

Jawwad ya dawo daga masallaci ze shiga Gida shida Jalal, wata arniyar Mota tayi parking a kofar gidan, Dan tsayawa su Jawwad sukayi, Abdallah ne yafara fitowa ya tunkaro su Jawwad da fara’arsa, yana zuwa Jawwad ya ganeshi rungume juna sukayi, Abdallah ya kalli Jawwad

“Aliyu mazan fama dama ana ganinka, tunda muka rabu a school bamu kuma haduwa ba”

Jawwad yai murmushi

“Aikam dai kazama wani babban mutum”

“Kaima haka ai”

Abdallah ya maida kallonsa kan Jalal, sannan ya mika masa hannu sukayi musabaha

“Aliyu wannan brother dinka ne?”

“Eh kanina ne”

Jalal ya kalli Jawwad, ya Dan harareshi

“Ko kuma dankaba sukayi dariya gaba daya”

Yarinyar data fito daga cikin motarce tasaka Jalal, da Jawwad sukayi saroro, suna kokarin gane wacece

Jalilace ko wata daban, takaraso inda suke, “Abdallah ka barmu a mota daga ganin abokanka, kamanta damu, nima yakamata inga Yar uwata, daddy ma ya matsu yaga ‘Yar baba”

Takalli su Jawwad

“Sannunku, ina wuninku”

Jawwad ne ya amsa mata,

A yanayin maganar hanan da Jalila akwai Dan banbanci ita Jalila maganarta dauke take da tsiwa, ita kuma hanan da Izza take magana

Ta kalli Jawwad

“If I guess Kaine Yaya Jawwad din namu ko”?

Abdallah yace

” kin canka dai² shine”

Captain Rasheed ne shima ya fito ya karaso inda suke,

Gaisawa sukayi cikin fara a, sannan JAWWAD yayi musu jagora zuwa cikin gidan, JAWWAD yaje yagayawa Abba ga baki nan sun karaso

Hanan se rarraba ido take taga Jalila 

Abba yayi farincikin ganin captain Rasheed suka gaisa cike da girmama juna

Jalila jikinta yabata, kamar sun karaso Dan haka tafito palourn da gudu hanan ta tashi ta rungume Jalila

“Ke in kika karyani fa, matsa inje in gaida Baba”?

Hanan ta harareta

” ni ba kya murnanr ganin se Baba ko”?

Babansu hanan yayi dariya 

“Karaso mu gaisa Yar baba”

Jawwad binsu yake da kallo yana kuma jinjina wannan kama ta Jalila da hanan suke kaman yan biyu

Nana ma fitowa tayi domin ganin Hanan, ita kanta Nana abun yabata mamaki,

Abba yacewa Jalila taje ta kira Maama su gaisa, Jalila ta tafi kiran Maama yayinda Nana taja Hanan dakinsu

Jalal ma Jan Abdallah yayi zuwa part dinsa

Nana na shiga daki da hanan Naja ta kallesu,

“Wai hayaniyar me nakeji a gidan nan?”

“Jalila ce tayi baki”Nana tabawa Naja amsa tareda cewa hanan

” bismillah Hanan”

Hanan ta shiga dakin tareda fadin

“Thank you dear”

Kallo daya Hanan tayiwa Naja tafara kokarin tuna inda tasan fuskarta

Mamakine yadan kama Naja

“Wata tsirfa yaushe kuma ta canza suna zuwa Hanan,”

Basu kulataba, Nana takuma fita don kawowa Hanan abun tabawa

Naja se kallon Hanan take, kamar Jalila kamar ba itaba kuma Jalila dai ba wannan kayan tasakaba

Hanan ta kalleta

“Baiwar Allah banason yawan kallo, kalli gabanki Dan Allah”

Naja ta mata wani kallo

“Uban me zan kalla a jikinki, ina cewa akayi kinyi baki, meye kuma na zuwa ki zauna anan, dukda nasan baze wuce danginkune na arnan ba sukazo”

Hanan ta fuskanci Naja ta dauka Jalila ce

“Ba arna bane cocine sukazo da Kansu, ba arna ba, keba gara arna dakuba, nasan abunda baki saniba, kokuma kinsani amma kuke boyewa, ki kiyayeni “

Sallama Nana tayi da tray a hannunta ta doro ruwa da lemo se glass cup, ta ajiye a gaban Hanan

“Sannu da kokari” Hanan tai maganar cikin kasaita, 

“Bakomai”

“Nana nakasa ganewa, waiba Jalila ba ce”

“Amma gaskiya Naja ba kya ganewa, to ba ita ba ce, abun mamaki ko, suna kama sosai”

Jalila ce ta shigo dakin, hanan ta kalleta

“Wai ina kika zauna kuka barni”

“Ina gurin Baba, ashema tafiya zeyi”?

” Eh zebi jirgin, Karfe 2 zeyi tafiya”

“Eh Su Yaya Abdallah sun tafi kaishi airport”

Nan suka zauna suka kama hira hada Nana, Hanan akwai saurin sakewa da mutane in taga dama, taita basu labarin yadda tayi missing Jalila, da kuma yadda suka cigaba da kawance ita da siyama, sunayi suna dariya

ita dai Naja kallonsu kawai take tana tabe baki ga mamakin maganganun Hanan sun cikata, to me take nufi? Ga kuma kamanin da taga sunayi da Jalila tanaso ta tambaya, amma tsakanin Jalila da Hanan bata San wadda tafi iya wulakanci ba.

Nana tace musu tana zuwa ta fita, ta Dan basu guri, yayinda Naja ta kame a dakin taki fita

Hanan ta kalli Jalila

“Queen kinsan wani abu kuwa”?

“A a sekin fada”

“Ina ganin Yaya Jawwad nagane shi yanada yawan fara’a”

“Ai Yaya Jawwad duk inda yake tauraro ne haskensa ne kawai yake bayyana shine,”

Murmushi sukayi gaba daya, Hanan takuma kallon Jalila, sannan tace

“Kuma kallo daya nayiwa Jalal nasan shine”

Da sauri Jalila ta kalleta

“Ya akayi kikasan Jalal, har kika ganeshi?”

“Hmm nasan komai,kin manta ranar dazaki taho kano keda Siyama kunyi zancensa, Dan haka Siyama na tambaya ta gayamin,”

“Hmm Siyama ko shine tagaya miki, bayan nace mata amana”

“To meye a ciki Dan ta gayamin, nida naganshi, he’s looking so innocent”

“Waye din looking innocent? Amma ba Jalal ba”?

“Shidin Jalila, dukda na gaishesu be amsaba, kuma ban zauna da Shiva, amma yanayinsa miskilanci ma yana matukar damunsa”

Download>>> Bakar Inuwa Complete Document

Jalila ta tabe baki “tab wannan Jarababben”

“Trust me miskilanci yana damunsa, dakuma kadaici Jalila, yanayin yadda Siyama tabani labarin, akwai wani abu a boye game dashi, amma kafin mutafi zaki gane hakan,”

  “Mtseww gulmar banza, munafuncin yabar kan yan Gida harda ya’yan makota” inji Naja

“Kee!! Naga kanki yana wata rawa, this should be the last warning, har in bar gidan nan, kika kuma shiga harkata akwai matsala, Jalila ki gayamata bana bakunta, zanyi ba dai² ba”

Hannan tayi maganar tata cikin isa

“Hmm manta da ita nima tunda tazo nabawa banza ajiyarta, saboda gaba dayanata suffar karyace, da halin Jakuna,”

Bude baki Naja tayi

“Ni kikewa haka Jalila”?

“Wallahi kina kuma cewa tak, zan keta miki rashin mutunci, ba a shiga sabgata”

Mikewa Naja tayi ta bar dakin tana zage²dan taga inta zauna sesu daketa

Hanan ta dawo da kallonta ga Jalila

“Waike dama haka kike zaune a gidan nan ana miki wulakanci duk bakin naki, Tun dazu take wani zage² ta dauka kece”

“Manta da ita yau tazo, taketa wannan shirmen, abunda yasa ban biye mataba abunda yake damuna daban”

“Jalila wai wannan ba kanwar Sa’ada bace ba”?

“Eh kanwarta ce ina kika Santa”?

“Shedanu karuwan banza kawai”

Zare ido Jalila tayi

“Haba Hanan wannan wace irin maganace”?

“Eh ba karya nayiba, yayarta Sa’ada kawar murjace Yar autar su mommy su ukune, group dinsu

Da murja da Sa’ada da Hannah, school daya sukayi, tun daga makaranta suka lalace, duk ina ganin hotunansu a wayar ta, ba inda basa zuwa a Nigeria club² suke zuwa, gurin manyan masu kudi da yan siyasa, daga bayane sukayi fada da Hannah yanzu saura su biyu,”

“Na shigesu ni Jalila,”

“Karki kara yadda wata jaka tacewa danginku arna suma duk gayyar tsiyane, ita batasan nasantaba ai, ita kanta Sa ada bata sanniba amma ni duk nasansu, a wayar murja, manta dasu mucigaba da hirarmu”

Jalila rasa me zatace tayi, se mamakin abunda Hanan tafada ta keyi, Jalila ta nisa “naso ace hada Siyama kukazo, ina cikin damuwa, bata karasa maganar ba 

Nana ta shigo da sallama, tacewa Jalila

“Jalila su Yaya Jawwad sun dawo, yakamata akai musu abinci”

“To bari in kaimusu”

Jalila ta mike, Hanan ma mikewa tayi, tareda fadin “muje in rakaki”

Suna zuwa parlour Maama tana zaune, zata ci Abinci, seda ta Dan bude baki tana kallon Hanan da Jalila

Jalila tace “Hanan ga Maama”

Hanan ta danyi murmushi

“Mamansu Yaya Jawwad kenan”?

“Eh itace” daga tsaye Hanan tace Maama ina wuni

“Lafiya kalau ya hanya”

Maama ta amsa mata ba laifi da faraa a fuskarta saboda ta gaisa da baban Hanan, taga babban mutum ne me Iko

Daga nan Hanan tabi su Jalila har kitchen suka dakko kayan Abinci

Hanan ta kalli manyan kulolin sannan ta kalli Nana

“Ta saku wahala ko? Kalli wannan kayan a wani cikin za a zubasu”

“Wane irin wahala, a cikinku zaku zubasu”

Nana tabata amsa, sukayi dariya gaba dayansu

Suka kwashi kaya se part din Jawwad tunda suka shiga, Jalila taga yadda Jalal yake dariya se abun yabata mamaki, dama Jalal yana dariya kamar haka mutum kullum fuska kamar fuskar shanu ba fara a, amma yasamu Jawwad da Abdallah se dariya yake

Sukaje suka ajiye kayan Abincin, Jawwad yana tayi musu sannu 

Hanan ta kalli Abdallah

“Yaya kalli wahalar da Queen tasa sukayi, kasan niba wani Abinci nake ciba lemo da biscuit ya isheni, kaikuma zaka iya zama bakaciba, tunda in katashi ci na mutum biyar kakeci lokaci daya”

Zare ido Abdallah yayi

“Ke hanan Dan sharri” Hanan ta kalli Jawwad

“Yaya Jawwad ba a zuwa da abokinka bakunta, kunyata mutane yake”

Dariya sukayi gaba daya ciki harda Jalal

Jawwad yace “kalli ikon Allah kamannin Ku har mamaki yake bani”

Abdallah yace “ba kai kadaiba farkon fara ganina dasu nikaina nayi mamaki, Inaga Allah ne yahadasu saboda kamanin dasu keyi”

“Eh amma nasha wuya ba”

Hanan ta fada tana shafa goshi

Jalila ta Dan girgiza kai “mhmm bari inje in dakko plates” ta juya ta fita, Nana ma guri ta nema ta zauna

Hanan ta Dan gyara zama ta waiga taga Jalila ta fita

“Hmm Yaya Abdallah kana Allah ne ya hadamu da Jalila amma nasha wuya,”

“Wuyar me kuma?” Nana ta tambayeta

hanan ta kwashe haduwarsu ta farko a school ta basu labari, Sannan tace 

” Yaya Jawwad wallahi kanwarka kakkarfa ce mari daya nayi mata Dan mugunta tayimin biyu, Wanda kowane mari daya datayimin dai² yake da nawa uku, ai ban gama shiga hankalina ba, seda naga tayi wurgi dani Jini yana bin fuskata, na dago ina dubawa kowanj malaminne yazo rabamu yayimin haka, yai Jifa dani Ashe Queen ce”

Dariya suka kamayi sosai, Yadda Hanan tasaki Miki take zuba kai lace sun Dade tare, kuma tanayi ne Dan monitoring din action din da JALAL ze dingayi 

Jalal yai murmushi sannan yace “ko y’ar gidan bullet ce”

Hanan ta danyi murmushi a ranta, tace hasashena yafara zama gaskiya

Abdallah yace “Jalal Ashe kaima kasan zancen”

Jalal ya nuna Jawwad

“a lokacin ya damu sosai, shi yagayamin”

“Nikam ban San labarin nan ba”

Nana tafada cikin dariya, Hanan takuma gyara zama sannan tace

“Yaya Jalal bakasan wani abuba, tacemin Yar gidan bullet, nazo da daddy ina shirin a casa queen, abun haushi wai Ashe yasanta kwana uku kafin hakan tafaru, Bayan anyi hakan ta dinga like min kaman chewngum kullum setazo inda nake muyi fada ina mata rashin mutunci amma batajin haushi”

Duk abun nan da Hanan ta keyi tana monitoring yanayin Jalal ne, Hanan ta danyi murmushi

“Se dai Queen duk inda taje kokuma Wanda yai tarayya da ita seyasamu wani benefits a tareda ita Wanda mutum baze mantaba, kamar daini ta saukemin rashin kunya, Dan tundaga ranar na nutsu Dan tanada luck a rayuwarta”

Jalila ta dawo takawo musu plates, abun yabata mamaki ita kuwa Hanan metake fada yasa hada Jalal a cikin masu dariya, Jalila ta kalli Nana

“Ku tashi mu tafi muci abincin muma”

Hanan ta kalleta, “Tab anan zamuci anayi ana hira, ni bani da yayye ko kanne a gidanmu masu debemin kewa nikadaice, Abdallah in ya fice koyakoma makaranta sena ganshi, yanzu ga dama ta samu nasamu Yayye” Jalila har mamakin wannan zakewa da Hanan tayi take

Jalila ta kalli Nana sannan ta kalli Hanan

“A gabannasu zamuci Abinci?”

“To meye a ciki ba yayyanmu bane, ko Nana”?

“Aikuwa dai Hanan, gaskiyarki”

“Gaskiya yau ranace ta mussaman Dan tayimin dadi”

Abdallah yafada yana murmushi

“Nima haka Abdallah, kobahakaba Jalal?”

Gyada kai Jalal yayi yana murmushi

Nana ta fara serving dinsu Abinci 

Fried rice ce, da sos se simple salad ga juice nan na kwali da Wanda aka hada

Abdallah yace “Jalila meyasa Baku girka tuwo ba na masar miyar kuka”

“Kutmelesi wallahi da bazanciba”

Hanan tafada tana hararar Abdallah, JAWWAD yace

“Sha kuruminki Hanan Jalal ma da bazeciba, bayason miyar kuka”

“Hh Ashe makiya tuwon dayawa, me fadarma bayaci”

Nana tai maganar tana kallon Jawwad 

Murmushi Jalal yayi, sannan yace “wani abu na tuna, Bros ka tuna lokacin da daddy yake kaimu Maiduguri, abamu biskin shinkafa da miyar kuka, Hajjo tace semunci”

Jawwad yayi dariya 

“Allah sarki rayuwa, kokuma ta dumama tuwo tace shi zamuci, ka wuni da yunwa”

“Mu wuni dai, ai kaima bakaci”

Suka kuma kwashewa da dariya,

Hanan ta Dan taba Jalila sannan tai magana a hankali

“Jalila kin yadda da abunda nagaya miki game da Jalal,?”

Abdallah ya jefoma Hanan handkchief dinsa

“Kai Hanan kiji tsoron Allah me kike gayamata haka”

“Ina ruwanka sirrine”

Wayar Hanan ta fara ringing, ta mike zata fita ta amsa wayar, Jalila tace

“Kunyarmu akeji dabaza a amsa a gabanmuba”

“Allah ya kiyaye inji kunyarki, inma kunyarce kunyar Nana zanji itace sirikata”

Abdallah yace “ji Mara kunya to wa Nana zata baki”

“Idan ma Nana bata baniba nasan Yaya Jalal ze bani”

“Wa kikeso in baki”

Nana ta tambayeta

“Rabu dasu sirrine se mun kebe da Nana zan gayamata”

Tayi waje abunta

Tafito tana amsa waya turo gate din gidan akayi, yaseera da Ilham suka shigo

Kai tsaye suka nufi inda Hanan take.

Suka karasa inda Hanan take waya, tagama wayar ta juyo ta kallesu, sannan tace

“Lafiya naga kunzo kunsani a gaba”?

Yaseera tayi murmushi

” baki gane niba ne”?

“Eh ban ganekiba, yauma nafara ganinki”

Aikuwa Ilham a fusace tace “kingani ko yaseera tsabar

rainin hankali wai bata ganeki ba, nagayamiki muguwar Yar rainin hankalice”

“Haba Ilham meye hakane? Meye Dan bata ganeni ba seta iya yuwa ta manta ne”

“Kizo shekaran jiyan sannan yau tace ta mantaki”

Hanan ta kallesu

“In Baku da abin cewa, ni ina da abunyi”

Yaseera tace “A a Jalila, Yaseera ce fa, da mukazo shekaranjiya”

Hanan ta fuskanci basu San ba Jalila bace, Hanan a ranta tace wannan ce Ilham kenan, hada ita a cikin labarin da Siyama tabata, na Jalal

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Ta kallesu tai musu kallon tsaf sannan tace “wannan Hanan ce ba Jalila ba”

“Kamar ya?”

“Kamar yadda nagaya muku mana”

Yaseera tace “Dan Allah Jalila a dena Jokes din nan gurinki mukazo zamuyi magana”

Hanan tace

“Maganar Me?”

“Akan abunda yafaru jiya har Jalal ya huce akan Ilham, abunne yabamu mamaki kwarai”

Hanan a ranta tace lallai wannan basu da hankali su nan gaba daya sun yadda Queen ce,.to ni mema zance musu nida bansan meya faruba,

“Nima abun yabani mamaki kam, amma yanzu ina wani abunne, kubari anjima,.semu hadu”

“To shikenan ina Nana?”

Yaseera ta tambaya

“Nana tayi bakine tana part din Jawwad”

“OK mungode se anjima”

Suka juya suka fita

Ilham ta kalli yaseera “ji wani sabon iyayi, ga yadda ta canza magana, tanawa mutane magana da isa sekace wata basarakiya”

“Nima nagani Ilham ai wannan se munbi a sannu”

Suna fita Hanan ta dinga dariya sannan tace amma gaskiya wannan sakarkarune, 

Takoma ta tarar sunata cin abincinsu banda Jalila da take ta tsakura duk a takure take

Hanan ta danyi murmushi sannan tace

“Yaya Jalal kufa ci Abincin nan sosai, inba hakaba Abdallah cinyewa ze ya barku”

Jalal yai murmushi,

“Meyasa kika takurawa yayankin nan haka”?

” Abdallah yace tambayeta dai, ni dai ba kunyarku zanjiba Dan in ban koshiba zan karane”

Hanan tace “Nima ai haka kake min kaita kunyatani a gaban mutane”

Jalila tace

“To suda uwar magana ki zauna kici abinci ni bansan yadda akayi bakinki ya bude hakaba, kika koyi surutu”

“Hh au haba zama dake ne yasa na koya, ni na manta ma kinyi baki fa, yanzun nan”

Jalila tace mata “suwaye”?

” ban sansu ba,.wasu matane su biyu suka ganni a waje sun dauka kece suka faramin surutu, nikuma nace sutafi aiki nake sudawo anjima”

“Dan wulakanci gaskiya baki kyautaba”

Cewar Abdallah, Hanan ta kalleshi ” Abdallah bana son ganin gushewar wannan farincikin da nake gani a fuskokinku, nasan in Jalila ta tashi tsareta zasuyi da surutu, Dan daganinsu ba wani abun kirkinne yakawosuba”

JALILA tace

“Ni mamakima nakeyi suwaye haka?”

Hanan tace “wata fara dai me kwalakwalan idanuwa, se wani kallon banza takemin da wata kuma me surutu, se magana take wai lallai sena ganeta sunzo shekaranjiya ko baseera kowa oho dai”

Jalila ta kalleta “kai Hanan meyasa kikace su tafi”

“To me zasuyi miki, wannan me kwalkwalan idanuwan sewanj kallon banza takemin, shine ya tabbatar min ba abun arziki ya kawosuba”

Nana tai dariya

“Kanwar Yaya Jalal ce fa, Ilham ko?”

Dan zare Ido Hanan tayi, 

“Dagaske amma basa kama, wata Mara.. Sekuma tayi shiru

Jawwad yace ” Hanan kanwar Jalalce cousin dinshi ce”

“Sedai cousin din Dan basa kama, gashi se wani..

Bata karasaba Jalila ta janyota 

” haba Hanan zubar ya isa kici Abinci mana”

“To nayi shiru”

Suka cigaba da cin Abinci

Jalal a ransa yake jin wani nishadi, Wanda rabon dayaji shi har ya manta, a ransa yake jin inama a ce wadan nan duk yan uwansa ne shima yace yau yanada yan uwa amma shikadaine kamar rai

Suka gama cin Abincin sannan su Hanan suka kwashe kayan suka tafi cikin gida

Suka koma dakin su Nana, Nana ta tafi dakin Maama don basu guri Naja se masifa take wai Nana ta rike bare ta manta da ita 

  Hanan ta kalli Jalila “Queen do you believe now Jalila, nagaya miki Jalal yana bukatar kulawane kawai, kadaici yana taka rawa a rayuwarsa”

“Hanan gaskiya nayi mamaki, bantaba ganinsa cikin nishadi ba, koyana dariya kullum fuskarsa babu fara a, kinga wadda sukazo nemana din nan farar, cousin dinsa ce a gidansu take itace take sonshi bakiga dukan dayaake mata ba baya shiga harkar mata, Nima fada muke, yabani mamaki danaga ya kulaki”

JALILA ta kwashe labarin Jalal zuwa yadda suke fafatawa dashi, halayensa dayakewa mahaifiyarsa, har zuwa mafarkan da takeyi dashi”

Hanan ta kyalkyale da dariya

“Jalila ta kalleta, meye haka kuma, Maya baki dariya”

Hanan ta sassauta dariyarta

“Ashe bani kadai rashin kunya ba taiwa ranaba, kut naso inga idonki lokacin daya baki sigari, kut gaskiya Jalal Dan duniyane yayi maganinki”

Tafada tana kuma kyakyata dariya

“Mtseeww nifa bana son wulakanci”

“Yi hakuri queen, let’s be serious, Jalila kiyi wani abu, zaki iya temakon rayuwar Jalal”

“Ta yaya zan iya wannan Jarababben Dan taurin kan”

“Bashi da taurin kai Jalila, he is simple, yanzu dai yakamata kisan meyasa bayason mahaifiyarsa, ki gano wayeshi, Jalila ke Alkhairi ce a duk inda kikaje, kiyi wani abu sannan kidingayi masa addu a kidena yi masa rashin kunya naga alamar bayason rainin”

“Hmm mugun Dan rainin hankaline Hanan bazaki ganeba”

“To kicigaba dayimasa rashin kunya randa yabaki giya, kya kirani kibani labari”

“Allah ya kiyaye”

Halima tayi sallama suka amsamata

Ta kallesu sannan tace “wacce ce Jalilan ne tunda tazo na dena ganeki”

JALILA tayi dariya

“Ya akayi leemart”

“Dama Cewa akayi wai kushirya in anyi sallar la asar, Hanan zasu tafi”

“To shikenan”

Sukayi sallar LA asar Hanan tanata Nanatawa Jalila, ta temaki rayuwar Jalal,.sannan duk abunda ake ciki ta kira ta a waya tagaya mata,

Hanan ta fito tayi sallama da Maama, Maama  tabata kyautar agogo, sannan Sukafito

A harabar gidan suka tarar dasu Jalal Suma sun fito

Abdallah ya kallesu, yace “Yakamata muyi hotuna fa, domin tarihi”

“Gaskiya kam” cewar Jawwad

“A fara yimana nida JAWWAD”

Inji Hanan 

Ta tafi kusada Jawwad akayi tayi musu 

Sannan akaimata itada Jalal, da Abdallah dakuma Nana

Takalli Jalila “Queen come forward”

Ta janyo hannun Jalalila zuwa kusada Jalal,

Kallon Jalila yayi, Jalila kuma ta hade rai

Hanan tace “Haba queen meye haka kiyi dariya mana, kin wani hade rai kamar wata boss”

Dariya sukayi, Hanan tai musu photo, a haka aka dinga hotunan nan, Naja ce ta fito harabar gidan tai tozali da Abdallah gaba daya ta rikice tarasa nutsuwarta, kai Allah yayi Halitta a nan, basu kula da itaba sukaji gaba da hotunansu,

Nana ce suka kuma dawowa da Yaseera suka tarar anata budurin hotuna Jalal kamar bashiba, se fara a

Se yanzu suka gane, ashe dazu ba Jalila suka ganiba tsabar kamace kawai dasukeyi, Jalal na ganin Ilham ya hade rai, suka karaso inda su Jalal Suke, Yaseera ta kalli Jalila tace”dazu munzo gurinki Ashe bake bace” Jalila tayi dariya tace “bani bace Hanan ce”

“To shikenan bari muje naga kunada baki,”

“A a bakomai bari inzo”

“A a ki bari zamu dawo”

Jalila tace”to shikenan “

Ilham, Jalal kawai take kallo da mamaki, ya kalleta, maganar Hanan ya tuna wai fara me kwalakwalan idanuwa

Kawai yadanyi murmushi.

Su Hanan sukayi haramar tafiya har bakin mota su Jalila suka rakasu, Hanan ta kallesu

“Kamar kar mu rabu, haduwar nan tayimin dadi, muna fatan kuma wataran zaku kawo mana ziyara”

“Insha Allah, muma zamu kawo muku ziyara”

Ta kalli Nana sannan tace

“Nana zanyi missing din murmushinsa, Dan Allah kibani shi”

Nana tace “wa kenan?”

Ta kalli Jawwad

“Gashi nan”

Gaban Jalila yafadi, shikansa Jawwad sedaya kalli Hanan,

Abdallah yace

“Aliyu kaga ku kyale Hanan, wani lokacin bata da hankali”

Ya bude mata mota “wuce muje”

Ta rike murfin motar sannan ta kalli Jalal

“Yaya Jalal da Nana da Queen bakinsu daya naga kamar bazasu bani ba, Dan Allah kai kabani shi”

Jalal ya kalli JALILA ya kalli Jawwad yaga duk Jikinsu yayi sanyi kaman Wanda akace za a kashe se yayi murmushi

“Yace indai Jawwad ne nabaki shi,”

Abdallah ya kalleshi

“Tab Jawwad kar ka yadda ka auri fitsararriya wannan, kyanta tsayayyen soja Wanda ze zaneta in tayi ba dai² ba”

Dariya sukayi amma banda Jalila

Hanan ta shiga gaban mota ta sauke glass ta kalli Jawwad,

“I will miss you Yaya Jawwad dina, keep me close to your heart”

Juyawa Jalila tayi ta shige cikin Gida, saboda ji tayi wani abu ya tokaremata a kirji, takasa tsayuwa

Hanan ta jingina da Jikin kujera, tayi murmushi tareda lumshe ido a hankali ta furta “am sorry queen”

Abdallah ya kalleta “ya dai uwar magana”

“Ba komai, ina cikin farincikine kawai”

   

Ilham ta kalli yaseera tace “yaseera Dan Allah mubar batun yarinyar nan kawai munemi mafita”

“Wace mafita Ilham, so muke mu tabbatar da zarginmu tukuna”

“Yaseera lokaci fa kuremin yake, nagaji zanyi abunda naga ya dace”

“Ilham kibi komai a sannu kar garaje yakaiki ya baroki”

“Nasan yadda zan tsara komai ki manta da ita kawai”

“To Allah ya taimaka”

Download>>> Macijine Complete Document

Suna shiga Gida Jalila bata tsaya ko inaba ta nufi dakin su,

Jawwad jikinsa yayi sanyi sosai, Jalal ya kalleshi yaga Jawwad yayi wani iri kaman Wanda yayi wani babban zunubi

Dariya Jalal yai

“Wai meya sameka ne kawaniyi shiru”

“Hmm ba komai,” inni Jawwad

“Dan tace tana sonka shine kawani damu, meye a ciki to, naga dai su biyun duk dayane”

Jawwad ya kalleshi

“Allah ko? Eh ai shiyasa kai gakanan kun jone da Ilham, Dan tace tana sonka, kana sonta kaima”

“Mtseww Dan Allah idan ina magana kadena sakamin maganar banza”

“Ilham dince maganar banza?”

“Ban saniba”

Ya mike yai waje yabarwa Jawwad dakin

Jawwad yayi murmushi “Ashe ba dadi”

  Yana zuwa Gida yaji yanason shan madara, Dan haka ya duba fridge dinsa, bawani lemon kirki a ciki duk se giya, rufe fridge din yayi, ya mike ya tafi cikin Gida, yana zuwa yatarar da Ilham a palour bebi takanta ba ya wuce fridge ya bude ya dau abunda yakeso, yana rufe fridge din ya juyo yaga Ilham tsaye a bayansa

Gefenta yayi ze wuce, takuma dawowa gabansa

Ya kalleta “meye Haka?”

“Abunda kagani mana, Yaya Jalal meyasaka nishadi haka? yau, naganka kana dariya dakuma fara’a abunda ni bakayimin,”

“Zaki bani hanya kosena barar dake a gurin nan”

Hannu ta mika masa “bani in tayaka daukar kayan”

“Jalal dama kana gidan nan, amma baka Neman inda nake”

Suka jiyo muryar mummy, ya juyo ya kalli mummy

“Idan nazo mezan miki? Bani da wani amfani dazan miki, be kamata in dinga zuwa ba”

“Ni kake gayawa haka ko?”

“Yau nafara gaya miki? Kina son maida hannun agogo bayane kawai”

“Jalal kaji tsoron Allah, anya kanaso ka gama da duniya lafiya”

“Mummy ke yakamata kiji tsoron Allah tun a farko ba a yanzuba da aikin gama ya Riga ya gama”

Ilham ta Dan juya baya tayi murmushi, a ranta tace Ashe kana sane da komai, Jalal mahaifiyarka tayi kuskuren da kake karbar hukuncin

Mummy ta kalli Jalal

“Yanzu JALAL….

” Enough mummy, baki da abunda zaki gayamin in saurareki”

Yana zuwa nan a zancensa yai waje, yayinda mummy ta zauna akan daya daga cikin kujerun palourn tafara kuka

  Naja ta shigo dakin su Nana ta tarar da Jalila kwance akan gado Nana kuma tana gyara dressing mirror, kalli Nana “Nana wai bakin sun tafine?”

“Eh sun tafi” ta kuma gyara tsayuwa sannan tace

“Y’an uwansu Jalilane?”

“Eh ya akayi”?

“Naga suna kamane sosai da wannan yarinyar, amma wannan namijin dasukazo tarefa?”

“Yayan Hanan ne” Nana tabata amsa

Jalila tana jinsu tayi musu banza

NaJa takuma cewa

“Yana da aurene”?

Nana ta dan bude baki, ta kalli Jalila sannan ta kalli Naja

“To ai Jalila zaki tambaya bani ba”

Jalila ta kalli Naja

“Kinada damuwa da hakanne, ina ruwanki ne, Suma daga dangin arnan suke, kinada matsala da hakanne?”

Jalila tayi maganar a fusace, da son huce takaicinta akan Naja, ta mike ta shige toilet

Nana kam dariya takama yi, “to hajiya Naja, kinji dai inma sokike seki hakura”

Bayan sallar magariba Jalila ta kira Abdallah, yace mata sun isa Kaduna lafiya tai masa godiya da bangajiya 

Nana ta shigo da katon Leda a hannunta 

“Nima bari in Dana Queen inji Hanan”

“Sarkin tsokana,”

“Ba wani tsokana, zomuje kirakani please”

“Ba inda zani”

“Maama ce fa tace kirakani”

“Ina?”

“Gurin mummy”

“Waike kullum sekinje gidansu Ilham ne?

” to queen ya zanyi Maama ce ta aikeni,”

“Ba sunana queen ba,”

“To Baby Jalila, na dena”

“Kyaji dashi dai” Jalila tasaka hijjabi tabi Nana zuwa gidansu Jalal

Suna zuwa suka tarar da mummy tana kuka a palour Ilham kuma tana kan kujera tana chatting,

Ilham tace “mummy lafiya kuwa?”

Ta goge hawaye, “bakomai Nana bari in dakko miki kudin”

Ta karbi kayan hannun Nana ta wuce dakinta

Nana ta kalli Ilham “Ilham me akayiwa mummy take kuka?”

“Ta tsuniyar gizo ai bata wuce koki, ita da danta ne, yamata rashin kunya ya fita”

Nana ta girgiza kai “kai abun ba dadi Allah ya shiryi Yaya Jalal”

Jalila ce kawai tace Ameen yayinda Ilham ta maida kai kan wayarta 

Jalila tace “yawwa Ilham nikam Neman me kukemin dazu?”

Ilham ta Dan daga kai ta kalleta

“Manta kawai ya Riga ya wuce”

Daga nan Jalila bata kuma cewa komaiba

Mummy ta fito tabasu kudin ta koma dakinta

Ilham ma ta mike tabasu guri Dan zuwa yanzu ba Jalila ba har Nana ma haushinta takeji.

Suka koma Gida Nana ta tafi kaiwa Maama kudi, Jalila kuma ta shiga dakin Halima 

Suketa hirar zuwansu hanan  Jalila take gayamata farincikin datayi,

Tace kinsan wani abu Halima

Halima tace “a a”

“Yau abunda yabani mamaki ganin Jalal yana dariya”

“Naganku kunata hotuna kaman bashiba”

“Wallahi kuwa,Allah sarki mahaifiyarsa ce babban abun tausayi, tanada da kamar Jalal da yakamata ace, tana cikin farinciki amma kullum cikin tashin hankali take”

Halima ta kalli Jalila

“Tab wannan matarce abun tausayi, amma bata taba shukamiki rashin mutunciba”?

Jalila ta kalleta da mamaki

“Me kike nufi Halima?”

Halima ta kalli Jalila sannan tace

“Hmm Jalila kenan abar zancen kawai Allah ya kyauta”

“Amma halima yakamata kigayamin”

“Jalila fadan bashi da amfani, amma kiyi hankali da matar nan”

Daga haka Jalila ta mike ta tafi dakinsu, itakam takasa gane kan wannan al’amari ita dai a haka bataga aibun Mummy, amma meyasa Halima tace bata da kirki, kuma gashi taki gayamata meyasa,

Da wannan tunanin ta shiga toilet tai wanka tai alwala tazo ta tayar da sallar shafa’i da wuturi

Shikam Jalal daya koma part dinsa ji yayi baya kaunar shan madarar Mummy tagama bashi haushi, Dan haka ya kunna sigarinsa ya dinga sha, dayagama kuma ya sha giyarsa iya son ransa, sannan ya baje a gurin

  Jeje ne a gaban wannan mutumin na rannan, mutumin ya kalli Jeje fuskarsa Sam babu alamar tausayi sannan yace

“Jeje nagaji fa, a wannan karon na raina kokarinka, har yanzu abu yaki karewa, har yanzu ace kunkasa aikata abunda nakeso”

“Jeje yace haba Oga KB duk kokarin danayi abaya, se wannan zaka kasa hakuri, aiko iya haka muka kyaleshi nayi maka kokari, balle ma ina kokari fa”

“Hakane amma gani nai yanzu kana nema kayi sanya, a wannan shekarun da kunyi tafiyar nan Dubai da dayan biyu ko akama shi saboda miyagun kwayoyin damuka Sa akayansa, ko kuma da kun tsallake da yanzu munyi arziki fiye da yanzu”

“Hakane Oga abun ne da matukar wahala, wannan Jawwad din shiyake hana ayyukan mu tafiya yadda yakamata, Hannah ma tanata nata kokarin amma hankalinsa baya kan mata, yafi ganewa shaye²”

Wanda aka kira Oga KB ya nisa sannan ya kalli Jeje 

“Bawata yarinyar da za a iya sakawa aikin dole se Hannah?”

“Oga a matan da nasani na bariki a irin taurin kan Jalal inba, Hannah ba ba wadda zata iya,”

“To shikenan amma ka ninninka kokarinka, gaskiya sonake yaron nan ya lalace fiye da yanzu, sonake yazama kaman Dan akuya sabida bin mata, yasha miyagun kwayoyi yayi safararsu, sonake bakin cikin ABDUL JALAL Yayi sanadiyar rasa ran Hadiza sannan ya kare rayuwarsa a gidan yari”

“Kwantar da hankalinka Oga komai ze tafi yadda kakeso mu dai ka Dan karamana lokaci”

“To shikenan ina jira inji kyakykyawan labari”

“Kar kadamu zakajine Oga, kwanan nan ranar zagayowar haihuwarsa zeyi, zamu shirya masa party, a nan zamuyi kokarin ganin komai ya kasance”

“To shikenan ina saurarenku”

Download>>> Budurwar Mijina Complete Document

Da safe Jawwad yaita zuba ido yaga Jalila ta kawo musu breakfast amma shiru, ga Jalal ma bezo ba daga karshe ma Halima ce ta kawo breakfast din, Jawwad ya tambayi Halima, 

“Halima ina Jalila?”

“Tana cikin Gida”

“Meyasa bata kawo Abincin da kanta ba”?

“Wallahi bansaniba, kawai tacemin in kawo”

Ya gyada kai

“OK shikenan, Nagode”

Daga nan ya mike ya dau kayan Abincin zuwa gidansu Jalal dan yau be zoba,

Kamar yadda yai tsamanni, Jalal be tashi daga bacci ba, yana kwance a parlour, ko kayan jikinsa be canza ba, ga kwalaban giya da yasha da ragowar sigarin da ya zuke, Dan girgiza kai yai sannan ya  tashi Jalal yasashi yai wanka yai sallar asuba,

Jawwad ya kalli Jalal

“Jalal baza kayiwa kanka fada ba ko? Lafiyarka fa Jalal, zasu iya yi maka illa”

Kallon Jawwad yayi ya sunkuyar da kai 

“Jiya nayi iya kokarina kar in sha matar gidan nan tabata min rai, shiyasa na sha”

“Haba Dan uwa, in rai yabaci hankali baya gushewa, ka dinga hakuri, Mummy mahaifiyar kace, ka dinga hakuri da ita”

“Jawwad kasan komai Dan haka karka kuma batamin rai”

“Shikenan yi hakuri bari mu karya”

  Jalila ta na gyara gadon su dan Nana ta tashi daga baccin ta shiga wanka, wayar Jalila ta fara ringing, tana dubawa taga Hanan setaga bata kyautaba bata kira Hanan tayi mata ya hanya ba, tasa hannu ta daga wayar

Hanan tace “Queen shine ko ki kirani kimin ya hanya ko?”

“Am sorry Hanan nakira Yaya Abdallah”

“Shi daban ni daban”

“To Allah yabaki hakuri”

“Ameen kin temaki kanki da kika bani hakuri, da baki banba ko hmmm”

“To ai ya wuce tunda nabada hakurin”

“To naji, yanzu dai ya Yaya Jawwad dina fatan ya tashi lafiya”

Jimm Jalila ta yi taki cewa komai

“Magana fa nake Jalila, nace ya Jawwad dina, kwana nayi ina mafarkinsa, yanamin wannan kasaitaccen murmushin, kaman inyi tsuntsuwa inzo in kuma ganinsa”

“Mhmmm” shine kawai abunda Jalila ta ce

“Tunda bazaki gayamin ya yake ba shikenan, ni nakirashi inji, ya Jalal dinki”?

“Jalal dina kuma?”

“Eh mana, tunda bazaki gayamin ya, Jawwad Dina ba, se in tambayeki ya Jalal, tunda bakya iya danne kishinki queen”

Dan dabarbarcewa Jalila tayi

“Kin fiye shirme Hanan, wane irin kishi, ya Mummy da Yaya Abdallah”

“Ya kike kokarin canza maganar ne, anyway kowa lafiya, hau what’s app kiga status dina”

“To naji, saura inga shirme”

Hanan ta yi dariya

“Koma dai meye zaki gani”

Jalila ta bude what’s app dinta taga Hanan ta turomata messages, ta bude hotunan dasukayine, hotunan sunyi kyau, tana duba dp din Hanan taga hoton Hanan da Jawwad, gashi be iya hade raiba, yayi murmushi, sunyi kyau shida Hanan, Jalila ji tayi kaman ta buga wayar da kasa

Dagaske kishin Yaya Jawwad nake, “yasalam” status din Hanan ta bude hotunan ne dai akan status din nanma ta rubuta kalaman soyayya, akan hotunanta da Jawwad

“Wai dagaske Hanan Yaya Jawwad takeso ko wasa, Hanan karkimin haka mana”

Tana kuma shiga daya hoton setaga hotonta da Jalal, wanda hanan tasata tai dariyar dole, shikuma Jalal yana kallonta Hanan ta rubuta

“perfect Match, Jalal and Jalila”

“Kutmelesi baki da hankali, kinci kai Hanan, Allah yayi min tsari, da mutum irin Jalal,”

Ta turawa Hanan daga nan ta rufe data dinta ta kashe wayar gaba daya

Sakkowa ta yi ta karasa gyaran gadon 

Sannan tabar dakin gaskiyar Hanan Jalila kishi take, tarasa meyake mata dadi, harabar gidan ta fito, tana son ganin Jawwad, yau ba ta kaimasa abinci ba rabon data ganshi tun jiya da su Hanan suka tafi,

“Maybe ma Hanan ta kirashi suna shan soyayyarsu” wata zuciyar ta raya mata, tsaki Jalila tayi a fili, tarasa abunyi, kawai ta shiga gayaran flowers din harabar gidan, lokaci² tana tsaki

Abba ne ya fito ze fita yaganta tana gyaran flours, yayi murmushi yakarasa inda take yace

“Barka da safiya, yarinyar kirki, da kanki kike gyaran flowers din”

Murmushi ta yi

“Abba barka da fitowa”

“Yawwa Yar albarka, dakanki kike wannan, akin nasaka a nemo wani megadin daze dinga kulada flowers din”

“Abba dan dai gyaran flowers ai ba wuya koni se indingayi”

“A a baza ayi hakaba inkika fara zuwa school fa, wannan ba aikinki bane,

Yawwa munyi waya da umminki, tacemin tana nan tafe next week insha Allah, zatayi tafiyar nan”

“To Abba nima tagayamin,”

“Masha Allah, Allah yakawo mana ita lafiya”

“Ameen Abba”

Abba ya kalleta

“Ina fatan ba wata matsala zamanki a gidan nan ko”?

” babu wata Matsala Abba”

“Masha Allah, in akwai wani abu dai kimin magana”

“To Abba, Adawo lafiya”

“Allah yasa Jalila”

Daga haka Abba ya shiga motarsa ya fita

Bayan sun gama breakfast Jawwad ya kalli Jalal yace

“Am going”

“Where?” Jalal ya tambayeshi

“Gida mana ina son ganin Baby, naga kaman tana fushi dani, tun jiya ban kuma ganintaba, yauma ba ita ta kawo min Abinci ba”

Jalal ya mike kafa ba tareda ya kalli Jawwad ba yace

“Laifin me kamata, zatayi fushi?”

“Nima bansaniba Jalal, zan tambayeta dai, na damu da rashin ganinta”

Tsaki Jalal yayi

“Kafiye abun Haushi,”

“Eh naji, nikam se an nima”

“A sauka lafiya”

Daga haka Jawwad ya tafi Gida a harabar gidan ya Tarar da Jalila  ta na gyaran flowers, tabawa gate bata, dan haka batasan ya shigo ba, a hankali ya karasa inda take, juyowa tayi kawai tai tozali da Jawwad, seda ta dan tsorata

Murmushi yayi mata “matsoraciya ga idonki, am sorry nabaki tsoro ko”

Murmushi itama tayi masa ta girgiza kai, kallonsa take ta tuna maganar Hanan

“Kwana nayi ina mafarkinsa yanamin wannan murmushin”

Dan hade rai Jalila ta yi, wata zuciyar ta ce mata “wata kilama sunyi ways da Hanan” kara bata rai tayi,

Karasowa yayi daf da ita ya kalleta

“Baby laifin menayi miki hakane, kike hademin rai, yau duk bana jin dadi ban gankiba”

Rasa me zatace masa tayi dan kuwa babu laifin da yayi mata

“Yayana bakayimin laifin komaiba”

“Are u sure, naga kina fushi dani”

“Bazan iya fushi da kaiba”

“To shikenan kin tashi lafiya”?

” lafiya kalau,?

“Meyasa baki kawomin Abinci ba yau”? dan sunkuyar da kai tayi kasa

“Bakomai”

Maama ce tafito zata fita unguwa ta gansu tare, kallonsu ta yi ta dauke kai, Jawwad yace “Maama fita zakiyi?”

“Ka aikeni ne?”

“A a Maama a dawo lafiya”

Ta amsa da “Allah yasa”

Jalila ma tace “Adawo lafiya”

Kallon Jalila tayi ta dauke kai, taje ta bude motarta, ta shige tai waje,

Jawwad ya dawo da kallonsa kan Jalila

“Baby me yake damunkine naga baki da walwala tun jiya?”

Rasa mezatace tayi kawai setace masa

“Yaya Jawwad, meyasa abokinka bashida kirki? Jiya munje gidansu da daddare Mummy tanata kuka saboda shi Yaya ka dinga yi masa nasiha, ni a ganina tarayarka dashi bata da amfani”

Dan kurawa Jalila ido yayi na wasu sakanni, ya dan sunkuyar da kai sannan ya kuma kallon ta

“Jalila” ya kira sunanta

“Na am Yaya Jawwad” ya mike tsaye sannan yace mata

“Biyoni”

Ba musu ta bi bayansa, har palournsa sannan ya nuna mata guri ta zauna

“Jalila rabuwata da Jalal ba mafita baneba, ina tareda shima kalli halin da yake ciki, inaga inna rabu dashi, babu wasu abokan arziki a rayuwarsa kowa yayiwa dansa kashedi akan mu amala dashi, babu wasu mutanen kirki da yake rayuwa dasu, ko ransa ya baci sune mutanen da suke tarairayarsa, kowa yana kyamarsa shiyasa abune mawuyaci ya rabu da shaye² indai mutanen kirki sukayi karanci a rayuwarsa”

“To Yaya meyasa bazaka masa fada ba ya canza rayuwarsa haka yaga kowa yana yi, babban abun damuwar yadda yake treating mahaifiyarsa, Sam be dace ba” Jawwad yayi ajiyar zuciya

“Abunda yake tsakanin Jalal da mahaifiyarsa sirrine na rayuwarsa, amma dai a da mutumin arziki ne, bahaka yake ba, wani azzalumin aboki ya hadu dashi waishi Jeje shine silar lalacewar Jalal nayi iya kokarina ya rabu dashi, amma yaki, akwai wani mummunan kuduri da Jeje yake dashi akan Jalal Wanda ni kaina ban saniba, yanzu ga wata shedaniyar yarinya data shigo rayuwarsa, wadda nake kyautata zaton bakinsu daya da Jejen wai ita Hannah”

Dan dagowa JALILA tai ta kalleshi “Hannah kuma?”

“Eh Hannah, ta shigo rayuwar Jalal, iatama, Jalal kaman Wanda akayiwa asiri, gashi cutar dashi suke amma baze iya rabuwa dasuba, duk lokacin da nayi yinkurin yi masa nasiha, idan yayi kaman ze dauka seya birkicemin ya dingamin tsawa jijiyoyin kansa su kumbura, wani lokacin seya suma, shiyasa na barwa Allah komai nake masa addu a”

Shiru Jalila tayi wato Jawwad yasan Jalal yana wannan abun

Jawwad yabata labarin nan a dukunkune bata wani gane komaiba amma waye Jeje she needs to know him

Jawwad ya kuma dubanta

“Yana daga abunda yasa bazan iya rabuwa da Jalal ba halaccin mahaifinsa Jalila bayan Abba da Abee, daddyn Jalal yana cikin mutanene daba zan mantaba,Jalal ya kaunaceni tun ina dan talaka na, Jalilalokacin ina zuwa gidansu Jala, y’an fashi suka shigo gidan da daddare, tashin hankalin daddyn Jalal karsu yimin wani abu da sukaga haka se sukai kokarin harbina, Jalal ya taremin harbi, aka sameshi a memakona, Jalal seda yayi jinya a kasar waje, badan ya tureni ba ya tsaya.dani zasu samu “

Zare ido Jalila ta yi, ya gyada mata kai

“Da gaske Baby, idan nafara gaya miki halaccin da yayi min dayawa, dan haka idan na gujeshi nayi butulci, naci amanar kauna da soyayya da yayi min, kitayani yi masa addu a komai ze zama dai² insha Allah”

Nannauyar Ajiyar zuciya Jalila tayi “zan dinga yi masa addu a insha Allah”

“Yawwa baby in kakayi haka kingama min komai”

Daga nan JALILA ta tashi ta koma cikin Gida

Tunani ya hadu yayi mata yawa, Yaya Jawwad be bayyana mata komai sosai ba, yagayamata abubuwan a takaice kuma a dukunkune, ko wazata tambaya

Yana da kyau tasan waye Jejen nan, amma to kuma meya kawo Hannah cikin lamarin nan akwai kanshin bakinsu daya da Jeje kenan

“Kai JALILA karki bari kwakwalwarki tayi bindiga mana kin takurawa kanki akan wannan sha³ dabe masa ciwon Kansa ba mutumin da giyarsa tafiye masa komai inyi rayuwata mana, haka Jalila ta cigaba da takura kanta, seta dena wannan tunanin son sanin waye Jalal”

Download>>> Jiddertul Khair Complete Document

  Maama kuma tunda ta fita zuciyarta ke tafasa kan wannan kusanci da shakuwa dake tsakanin Jawwad da Jalila, saboda gani take abun nasu na shirin komawa soyayya, idan kuwa tana Raye bazata taba bari hakan tafaru ba, dama gidan wata abokiyar kasuwancinta zataje dan haka tana zuwa a gurguje tai abunda zatayi ta fito ta tafi gidan yayarta mairo

Tana zuwa kuwa tayi Sa a tana Gida dan gantalalliya ce ta innaniha dillaliyace yau tana nan anjima tana can

Ga ta da ‘yan mata manya irinsu Sa ada da Naja da sauran mannensu amma har shabiyun rana ko wanke² ba suyiba

Daki suka shige da Maama da Yaya mairo, suka gaisa sannan

Yaya mairo ta kalleta “lafiya dai Zainab naganki haka?”

“Inafa lafiya game da wannan yarinyar ne”

“Wace yarinyar?”

“Jalila mana”

Yaya mairo tayi mutmushi

“Kice Jalila ta gurin arniya, ai jiya Naja data dawo tabani labarin komai, yarinya ta samu sakewar yin abunda taga dama,wai ta dawo gidanki da zama, narasa wace irin macece ke Zainab, ya akayi kika bari ta dawo miki Gida harta samu wannan yancin? Ashe kinshirya ganin ya’yanki sun fara binta coci”

Maama tai ajiyar zuciya

“Ni duk ba wannan ba Yaya, yaron nan fa Jawwad alamu sun fara nunamin kamar Santa yakeyi”

Zare Ido Yaya mairo tayi “ita wa din?”

“Haba Yaya mairo ya zaki dinga tambayata kaman baki San akan Wanda nake maganaba”

Yaya mairo ta jinjina kai

“Tirkashi, se yau na tabbatar da Zainab baki da wayo kina me hakan ke shirin faruwa garin Yaya?”

“Kedai bari duk yadda na kesa musu ido amma alamu sun fara nunamin hakan”

“To yanzu wani mataki kika dauka?”

“To Yaya mairo da na dauki wani mataki ai da banzo nanba”

“Gaskiyane, yanzu abunda ze faru zanzo gidan naku, zan zo in samesu, nasan abunda zanyi”

“To shikenan har na danji sanyi,  wallahi”

“Karki damu kibar komai a hannuna”

Da haka sukayi sallama Maama ta koma Gida

Jeje ne ya kalli Hannah,

“Hanna akwai bukatar kara himma akan Jalal, idan mukace zamu cigaba da bin komai a hankali muna lallabashi to aikin nan base yiwuba”

“Nima nayi tunanin hakan amma me kake gani za ayi?”

“Birthday Jalal saura wata daya, a wannan lokacin nakeson mu kaddamar da komai, ko ya rayu yayi abunda mukeso, ko kuma……………….

   

  Ilham tana kwance ta lumshe ido, da alama tana son yin baccine, wayarta ta fara ringing, yamutsa fuska tayi takai hannu da niyyar yin rejecting kiran taga sunan malam Wada a jikin screen din, da sauri ta tashi zaune taje tasawa kofar dakinta key ta dawo ta daga kiran

Suka gaisa, sannan yace

” dama batun Yarinyar nan da kikayi min magana akanta ranan ne”

“Nagane Jalila kenan”

“Yawwa ita nayi bincike akanta amma akwai Matsala…………

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button