Shin ko kunsan dalilin yin kidnapping din Sumayya a Labarina kuwa?
LABARINA.
A haƙiƙan gaskiya wasu sun sani wasu kuma basu sani ba dan haka ayau a kuma yanzu zamu sanar da ku ku dai kawai ku danna mana Subscribe sannan ku taɓa karrawar sanarwa domin sanar da ku da zarar mun ɗora sabon shiri.
To, kamar dai yadda na ambata zan faɗi dalilin kidnapping din Sumayya ta Labarina, kai harma dalilin da yasa Mahmud ya mutu a cikin shirin mai farin jini, ba wani abu ba ne ya faru face ƙarin wasu maƙudan kuɗi da jaruman suka buƙata a wajen babba director, inda shi kuma ya ce ai sam bazai ƙara masu adadin kuɗin da suka buƙata ba, hakan ne yasa jaruman suka fara tutsu, wanda cikin gaggawa director ya yi yunƙurin canza jaruman da wasu jaruman daban saboda kada su kawo mai cikas a cikin shirin nasa mai farin.
Ya yi yunƙurin canza jarumi Mahmud wanda aka fi sani da Nuhu Abdullahi da jarumi Sadiq Sani Sadiq ya yin da yayi yunƙurin canza Sumayya wadda aka fi sani da nafisat Abdullahi da Fati Washa. Sai dai bayan dogon nazari da shawarwari daga masu ruwa da tsaki kan harkar director ya gano cewa indai yayi haka to Film din nasa mai cike da farin jinin jama’a gami da ganɗoki zai yi faɗuwar baƙar tasa, ma’ana zai rasa kasashinsa da masu bibiyar Film din sau da ƙafa, to wannan ne dalilin daya sanya ya canza shawara ya kashe Mahmud ɗin, duk da ba haka aka so ba wai ƙanin miji yafi miji kyau, yayin ita kuma Sumayya ta zama karfen ƙafa, domin ita bazata mutu ba saboda kasancewar gabaɗaya Film itace Babbar tauraruwa, kenan idan har aka ce ko aka nuna ta mutu to labarin yazo karshe shi yasa director ya yanke hukuncin yin garkuwa da ita domin a samu a shawo kan lamarin.
Also Read: Cikakkiyar Hira Da Akayi Da Aminu Saira Akan Mutuwar Mahmud Na Shirin Labarina.
SHARHIN LABARINA SEASON 4 EPISODE 7
Marubuci: Yakubu M Kumo.
Salo mai burgewa da ban sha’awa, siga mai fuzgar zukatan masu kallo. Tabbas a wannan shirin a na yin zube-ban-ƙwaryar basira tsakanin marubutan, shi ya sa shirin ya bambanta da saura. Yanayin sigar bayyanar ƙwarewar jami’an tsaro ya nuna cewa marubucin na wannan makon masani ne a harkar ƙabli da ba’adin tsaro. Hakan kuma ya zo a daidai gamar da matsalar tsaron ta addabemu.
1. Samun labarin ɓatan Sumayya da Presido ya yi, ya sake haifar riciki wajen neman lafiyar shi. Hakan ya sa bai da sauran burin ci gaba da zama a ƙasar waje dole ya dawo gida.
2. Makauniyar soyayya na haukatar da Lukman, ta yadda ya ke shiga hurumin da ba nasa ba, musamman harkar jami’an tsaro. Matakin da Al-Amin Buhari ya ɗauka a kansa shi ne daidai, ta kamata ma ya haɗa da zabga masa marin da sai ya gigice.
3. Ya kamata Rukayya ta sanar da jami’an tsaro ziyarar da Sa’a ta kawo mata da kuma irin alwashin da ci wajen ganin bayan Sumayyan. Duk da dama a baya ba ta ji tsoron jami’an tsaron ba ta faɗi kalamai son ranta. A wannan gaɓar ita ce babbar abar zargi lamba ɗaya, bai kamata a yi wasa da ita ba.
4. Kiran wayar da masu garkuwar suka yi, zai tallafawa jam’an tsaro wajen bin diddigin layin domin gani maboyar tasu.
5. Jinkirta bayyanar Sumayya, wani salo ne na kara jan zaren labarin zuwa gaba.
Za ku iya kallon cikakken Bidiyon