Uncategorized

Turkashi! Tsohuwar Jaruma Safiya Musa ta bayyana cewa Kashe Ahmad S Nuhu Aka yi ita ma Allah ne yai.

 An dade ana zargin yan film da laifuffuka da suka shafi bata tarbiyya, fidda tsiraici, da sauran su amma ba a fiya zargin su da harkar da ta shafi tsafi ko zubda- jini ko wani abu mai kama da haka haka ba, sai dai yan kanana kananan zarge zargen asiri a tsakanin Su.

Sai dai Wani video da muka ci karo da shi a shafin media hausa da suka kwafo daga shafin tiktok na Tsohuwar jaruma a masa a’antar Safiya musa, ya bayyana Wani sirri da duniya bata sani ba game da mutuwar Jarumi Ahmad S Nuhu, inda take bayyana kashe shi aka yi ba mutuwar Allah da Annabi bace dukda dai dama kwanan sa ya kare.

A cikin videon Safiya musa ta bayyana yadda aka basu makudan kudade da zummar zasu je maiduguri gala, Ahmad An bashi 500k, itama an bata 700k, inda ganin yawan kudin yasa ita safiya ta karbi dubu Ashirin kawai tace bazata je ba ta, bayan tafiyar su sai ji tayi Ahmad S Nuhu ya yi Hatsari ya mutu, wanda tace da itama taje data mutu, ko ta sha wahala.

Sai dai a cikin videon bata bayyana wanda take zargi da kashe Ahmad S Nuhun ba, bata kuma bayyana ta yi kokarin haske kan Wanda take zargi da kashe Ahmad ba, a labarin da aka kira ta aka ce ya mutu bata yi mamaki ba.

koda yake cikin hanzari take bada labarin, kuma ana ta kiran ta ana cewa ta bar maganar jama’a suna jin ta, wanda har kiran ta aka awaya aka yi ana ce mata ta bar maganar amma sai da ta kai aya,

Bamu san dalilin da yasa safiya bata fito da wannan maganar ba tsawon shekaru goma sha biyar ba sai yau, duk da tasan magana ce da zata iya tada hankali ko hukuma da yan uwan mamacin su ce zasu karkade file suci gaba da bincike wanda dole hakan zai sa a so jin karin bayani daga gare ta.

Akarshe tayi addu’ar Allah ya gyara industry din, in kuma baza ta gyaru ba Allah ya tarwatsa ta, tsirarun da suka rage sa gyarta, su amfana ga dai videon hirarda aka yi da Safiya musa a live dinta na tiktok.

Za ku iya kallon bidiyon.

Back to top button