Uncategorized

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 5

 ZUCIYA DA KWANJI 

BOOK 1___5

Na Maimuna Idris Sani Beli

  Ta muskuta ta kara gyarawa, wanda hakan na bayyana hasken da zuciyarta ke yi, sai dai ba ta son bayar da kai bori ya hau. Ga jarabar dokin da ya ishi zuciyarta na son ganin wannan amaryar mara kuma a idanun Abu Turab. A yangance ta dubi kwayar idonsa ta ce. “Wai fita

zaka yi ne?” 

  Yana yi mata wani tsadadden kallo ya ce, “Eh, uwargida ran gida, ko in zauna akwai abin da za ki ba ni?” Ta yi saurin girgiza kai.

   “A’a sauka lafiya, wai ba zaka gabatar da mu ga juna ba ne a wajen amayar ta ka?” Ba tare da ya ba wa maganarta muhimmanci ba, ya ce “Har sai na gabatar da ku ga juna sadiya, sai ka ce wasu yara? Ku gabatar da kanku ga juna mana, ta zo wajenku ko ku je inda ta ke”.

  Ta dube shi da gefn ido ta ce, “Kawai kuma a matsayina na babba sai na zubar da girmanan

na shiga wajenta ko?

  Ya tuntsure da dariya ya ce,  “Sadiya ke nan uwar son girma. To wallahi ta girme ki, ko wannan kika duba kya ba ta girma”.

  Fuskarta ta cika da walwala ta ce. “Oh tsohuwa ka kwaso mana ke nan?

  Ya gyada kai ya kuma girgiza ya ce “Idan kin ganta idonki ya faɗa miki”. Ya mika mata hannu alamar ta zo gare shi, yana cewa “Wai ba zamu gaisa ba ne?” Ma’ana ya basar da wancan zancen. 

  Ta kawar da kai ranta na kara haske, tana kada idanuwa ta ce, “Ai na sallamawa amarya, idan kwana ukunta sun cika ka kara mata wata daya a nawa”. 

  Ya iso gare ta yana girgiza kai, “Ba zan iya maraicin rashinki ba”. Ya jima suna faranta ran juna, sannan ya yi mata sallama ya nufi dakin hindatu. Yana shiga kicin dinta ya wuce ya barta a falo ya kinkimo fulas da kofi ya zo ya zauna tana faman binsa da kallo ya ce, “To tashi da sauri mana ki kawo min mahadi, kina ganin zan makara”. Murmushi kawai ta yi, ta mike zuwa kicin ta zubo masa wainar shinkafar da ta yi da kyakkyawar miyar albasa, sannan ta kawo masa kayan shayi, sai da ta hada masa komai sannan ta koma gefe tana cewa, “Abu Turab ai ban yi tsammanin zaka fita aiki yau ba. Haba zaka ragewa amaryarka daraja, a kawo ta jiya kuma yau ka barta ka fita aiki”.

  Ya fara taimakon cikinsa yana cewa. “Aljihuna ne babu ko karfanfana dole sai na fita, ko akwai ‘yankudi a wajenki ki sam min aro?”

 Ta yi saurin girgiza kai ta ce, “Ba ka dai kyauta ba. Ai yakamata ka yi tanadi tun jiya”. Bai dube ta ba, ya amsa. “Za a kori gaba”.

 Takawar da kanta daga gare shi ta ce, “Me ye sunanta?” 

  Ya dan zuba mata ido, sannan ya amsa “Sunanta Fadimatu, don Allah anjima ki yi kokarin lekawa dakinta ku gaisa, kar ki duba komai, ki duba ni da na ce ki je din kin ji”. Ita ma ta dan kafa masa ido sannan ta kawar gami da ajiyar zuciya ta ce,

  “Anya ba ka dora min babban aiki ba kuwa Abu Turab? Me yasa ita ba ka yi mata izinin ta biyo mu dakunanmu mu gaisa ba?”

 Ya girgiza kai ya ce, “Na fa ce kar ki duba komai”. Sai kawai ta tsaya tana kallonsa yana ta faman cin abincinsa, dama shi mutum ne mara wasa da cikinsa. Can ta nisa ta ce masa. “Wai amaryar ba ta yi girki ba ne, to ita me zata ci?” Ba tare da ya dube ta ba ya ce, “Yanzu zan fita na nemo mata”. Sai ta ji maganar na yi mata yawo a rai. A gidan Abdullahi za a ki dora tukunya, kuma a fita waje a siyo, kuma wai shi ne ma da kansa, anya? Ta dai share har ya gama ya yi mata sallama ya fice, can ta ji tashi motarsa bai fi mintuna ashirin ba ya dawo. Da sauri suka hau lekensa daga ita har sadiya wadda ta ke son sanin abin da ya dawo da shi, yayin da Hindatu ke dokin ta ga kalar abincin da za a tarbi amarya da shi.

 Mai masa share-sharen harabar gidan ya biyo shi da manyan kwalayen sunfi a kirga sun fi kala goma dangin kayan sha, tsotse-tsotse da tande-tande, shi kuma Abdullahi na rike da ledoji biyu na take away mai tambarin wani shahararren restaurant.

 Sai da Ayuba ya gama shigowa da kayan kofar dakin amarya ya fita, sannan Abdullahi ya fara kwankwasa mata kofa. 

  Wani tokareren bakin abu ya tokarewa Sadiya a kahon zuci, kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. Hindatu ma da sauri ta saki labile zuciyarta na wani irin bugawa, tunda ta ke ba ta taba jin zafin kishin Abu Turab irin na ranar yau ba, duk da kuwa Abu turab tuni ya bayyanar mata sadiya ce mai kyallin goshi.

 Cikin magagin bacci Fatima ta ji bugun kofarsa, da sauri ta bude idonta ta dubi agogo, sai ta tarar sha daya har ta gota, nan take kalamansa suka fado mata.

 “…….. Da safe kuma ko ba ranar girkin ba ne zan dinga shigowa mu gaisa……” Ta ture bargo ta dau hijabinta ta zira kirjinta sai harbawa ya ke, saboda fargaba irin cin kashin da ya kunso mata a wannan shigowar, tunda shi dai ya zama annoba, duk haduwa sa ya gadar mata bakin ciki. Sai da ta yi ta gwada irin yadda zata daure fuska da kuma kalaman da zata iya fansar kanta idan ya nemi raina mata hankali, sannan ta bude masa kofar, ta koma makwancinta ta

zauna tana cin magani bayan ta lullube kafarta da bargo. Sai da ya gama shiga da kayan nan a kicin dinta tsab, sannan ya kitsa da ledar take away din, ya ajiye bisa coffe table fuskarsa a daure ya fara nazarin falon da shi wadda ko kayanta na jiya ba ta cire ba ga kuma shaidar a falon ta kwana. Sai daya gama nazarinta tsab cikin sassaucin murya ya ce. “Kin tashi lafiya?”

  Ta kada kwayar ido da kawar da kai ba tare da ta tanka ba. Ya ci gaba da kallonta wasu irin

abubuwa na huda zuciyarsa juriyarsa na shanye su.

 Ya bata murya ya ce. “Ga kayan kwalam din da kika ce min sun ishe ki sati biyun da kike zatarwa kanki a gidan nan, idan akwai wani abu da kike muradi sai ki sanar da ni, wannan kuma karin kumallo ne na yanzu (yana nuna mata take away din) bai kamata na je gidanku na ci abinci mai kyau ke a nawa ya gagara ba”.

  Ta dago a wulakance ta dube shi ta ce, “Nawa ka kashe na biya ka? Ai ba mu shiryo ta zaka yi wata wahala da ni ba”.

 Tana rufe baki ya amsa mata. “Ni ne kawai na shiryo wa kaina, a wani gefen kuma don na nuna miki kudin kawai kika fi ni, amma na ki da shugabanci daga indallah”.

 Takaici ya bayana a fuskarta. “Wa kake shugabanta…..?”

 Ya tare ta da gadara. “Ke!!!!”

 Ta kada kai tana cije lebe ta ce, “Ai na fi karfinka Abdul ya ya zaka yi da ni?”

 Nan ma bai yi kasa a gwiwa ba ya amsa,  “Yadda namiji yake da ko wacce mace musamman jarumi irina, me jarumtar kashi da ta zuciya….. Ni sam ban taba yarda wata mace ta fi karfin namiji ba duk irin kasaitarta….”

 Ta motsa baki kamar zata yi tsaki, sai ta hadiye shi, nan take kanta ya fara ciwo saboda tsabar takaici, ta dafe goshi kawai.

 Zai kuma dorawa ta dago ta kalle shi rai a bace ta ce, “Abdul wannan hayagagar taka ta ishe ni, idan ka gama abin da ya kawoka ka fice min, kuma daga yau bana bukatar gaisuwarka da bankwananka. Na yarda ba zan fita ba sai da izininka, sai dai ba zan taba neman izinin naka ba ma’ana ba zan fitan ba har wa’adin mu ya cika mu rabu kowa ya huta, isa kuma na yarda ka isa ai ga alama nan tsurut da kai ka ajiye mata biyu kana shirin ta uku ko wannan aka duba sai a sara maka…..” Kuncinsa kunshe da murmushi ya tare ta. “Kin zare kanki daga ciki su ne?” Ta yi fuska ta ce, “Ai dama ba a ciki nake ba”. Ya yi mata wani kallon mai tarin fassarori wanda ita kanta duk hikimarta ta kasa ba shi ma’ana.

 Ya jima yana jan fasali sannan ya kada kai ya ce, “Akwai amanarki a tare da ni, wanda shugabancinki a yanzu ya jaza min, saboda haka dole na shigo na miki bankwana kuma na ga yadda kika kwana….”

 Sai ta yi masa shiru ranta na kara daci. Ya jima a tsaye yana kallonta ta rasa yadda zata yi da shi, ta san neman abin da zai bakanta mata kawai ya ke, kuma ba zai samu ba don ba zata dinga biye masa yana sa mata ciwon kai ba. Haka kuwa bayan ya gama kare mata kallon sai ya bita da Ƙulli, “Wai a nan kika kwana ne? Duk me ya yi zafi?”

 Ko motsi ba ta yi ba bare alamar zata tanka, sai ya kada kai ya juya. “Sai ki tashi haka, ki yi wanka ki dan gyara gurin kada a yi baki su yi miki kallon kazama”.

Haba nan take wasu hawaye masu radadi suka tuntuɗo mata, ba ta iya hadiyewa ba sai da ta ce, “Abdul aniyarka ta bi ka”. Ko a jikinsa don yana dariya ya fice, ta dafe kai a wajen tana maimaita.

“Innalillahi wa inna illahi raji’un” Ta yi kuka mai ishr ta, sannan ta bai wa kanta hakuri ta tashi ta gyara falon, sannan ta fada wanka a gurguje don ta dan fara jin hayaniya a cikin gidan. Ta

shirya a shigar turawa, wando ta saka ruwan wanda ya fito da kirarta, da farar vest saboda zafin da ake a garin duk da na’urar sanyaya daki ta wadata a gidan, amma ji ta ke komai ya yi mata nauyi da zafi, kamar yadda zuciyarta ta ke.. Ta saki ranta ta kwashi abinci don ta tabbatar babu ruwan Abdullahi da abin da yunwa gauraye da bacin rai za su haifar mata, ita kadai wannan asarar zata shafa. Cikin kayan da ya zube mata a kicin ta tarar da abin da ta fiye so, wato yellow peach. Ta balle gwangwani biyu a faranti ta koma falo. zamanta ke da wuya aka kwankwasa mata kofar falo, nan take ta ƙara jin gabanta ya yi mummunan faduwa don ta yi tsammanin dan hayaniyarta ne, tunda tasan ‘yan gidansu babu mai zuwa mata a wannan ranar. Sai da ta leke ta tagar kicin ta ga wasu bakin mata biyu sannan hankalinta ya dan kwanta, sai da ta koma mazauninta ta zauna ta dauki farantin peach dinta ta tsiro da cokali ta kai baki sannan ta yi izinin a shigo.  

  Sadiya da Hibdatu ne, an kullo tsegumi an taho, amma daga tsomo kafarsu numfashinsu ya so ya dauke saboda haduwar falon, sai wani kamshi da sanyi mai rahama ke dukan mutum. A kasaice kamar yadda ya zame mata dabi’a ta ce, “Ku shigo”.

  Sadiya dai donda kunya ne ace ta koma, amma tana dora ido akan Fatima sai ta ji gaba daya falon ya fara zagayawa da ita. Gaba ɗaya ta gama tsinkewa don tasan mijinta dama can ba sauki bane ya sami wannan ‘yar mai kama da gwal. Ko hindatu ta ji babu dadi game da amaryar Abu turab ba zai wuce na kasaita da rashin kulawarta ba, sai kuma ledojin abincin da ke gabanta wanda a arharsa da matsayin resturant din da aka siyo shi ya haura duba uku, kudin cefanen su na kwana biyu a karin kumallon mace daya! Turkashi! Da gaske matsayin mace biyu ta ke amsawa… Ko ma ta haura. Su suka yiwa kansu wajen zama suna mai fuskartarta, sannan ta sami damar matsawa a yangance ta ce, “Ina kwananku?”

 Hindatu ce ta yi kokarin amsawa da murya a bude, amma sadiya kusan a ciki ta amsa ta kuma kasa sake daga ido ta dubi fatima. Sai da fatima ta ci peach yanka biyu sannan ta dire faranti ta mike cikin yauki tana cewa “Bari na kawo muku ruwa”.

 Da sauri Hindatu ta ce. “A’a mu fa yan gida ne ba sai kin ba mu komai ba”.

 Ba tare da fatima ta dakata ba ta ce “To ‘yan gida ba za a karrama ku ba, ina zuwa”. Ta zuba lemon mangwaro biyu a dogon faranti, yellow peach biyu da ruwa faro da tambulan biyu da kuma choculate cake guda biyu. Ta kawo musu ta ja wa kowace coffee table a gabanta, ta bude musu lemo, sannan ta zazzage musu peach ta yi musu bismillah, sannan ta koma nata muhallin. Ko kallon kayan sadiya ba ta yi ba, sai Hindatu ce ta dauki lemon ta kurba sannan ta dube ta ta ce. “Abu Turab ne ya zubar da ladansa bai gabatar da mu ga juna ba, shi ne muka yi karambanin zuwa inda kike tunda ke ba ki nemo mu ba. Ga yaya babba ( ta nuna Sadiya) ita ce uwargidanki, sai ni Hindatu na bi bayanta. 

  A kasaice Fatima ta juyo ta dube su, da dokin ta ga matan da suka fita, ta yi tsaki a zuci kawai ta kawar da kai, haushinsu kuma ya kara turnuke mata zuciya, daman tunda ya ce matansa sun fi ta taji gaba daya ta tsane su, ashe ma burgar banza ce ko kama kafarta ba su yi ba, duk da shi ya ce ba a nan ta ke ba. To amma abu a duhu wa zai dorar? Da kyar ta hadiye tsanar da ta yi musu ta amsa batun da suka zo mata da shi a hagunce. “Wane ne kuma kuma Abu Turab?”

  A kufule Sadiya ta ce, “Angonki!”

  Fatima ta kawar da kai tana kara hadiye takaicinta, kamar dole ta ce, “Au, ban sanshi da wannan sunan ba”.

  “Amma ba ku dade tare ba?” Tamabayar da sadiya ta yi mata ke nan, ita kuma sai ta juyo kawai tana kallonta tana ta faman kokawa da zuciyarta wadda ke wani karatu da ban, sai ta buge da kai peach a baki ta taune ta hadiye, sannan ta dubi talabijin ta ce, “Ba ki da labari ke nan?” 

  A dan zafafe Sadiya ta ce. “Kusan haka ne, don an yi abin ne cikin gaggawa kinga zan iya

tsammanin akwai wani ‘yar burum burum”. Duk da Fatima ba ta iya bakar magana ba, sai ta ji yau kamar an kimsa mata, don sadiya na rufe baki ta amsa. “To ko ma dai odi-di ne ya fice wai tunda ya zama dahir, ko a mafarki dai muka hadu haduwar ta yi amfani tunda mun auri juna, auren da na tabbar a yanzu ya fice gaibu.  

Also Read:

 

 Sadiya ta fara murmushin da ya fitar da sauti ta ce, “Dama ga Abu Turab da aure-aure, shi har kwallon kafa aura yake jiya raba dare ya yi yana kallon kwallo, na yi mamakin yadda kika saki wannan damar”.

   Maganar ta daki zuciyar Fatima, amana nan da nan sai ta fanshe. “Babu wani abin mamaki akan aurensa don in dai namiji bai yi sa’ar auren farko ba to ya gama shiga garari, ba kwallon kafa ba har kwallon ciki ma wataran sai ki ga ya aura, abin da kuma zai fi saukin yi min ciwo ke nan, wato akan gazarwa da zan janyo a cika min gida da kishiyoyi”.

  Sadiya ta yi masifar kuluwa tamkar ba ita ta fara zunguro fitinar ba, bacin ranta ya kasa boyuwa tana numfarfashi ta ce, “Wata kishiyar ai suna ta tara, kishiyar da zata yi asarar daren farko ai muna maraba da ita. Wallahi ni a kawo min dozen ma” Numfashin Fatima ya yi kamar ya dauke saboda takaici, ta rasa amsar da zata ba wa sadiya ta fashe, sai gaba daya ta tsani kanta ta kara tsanar Abdullahi, wannan babu tantama shi ya janyo mata wannan koma bayan da ya ce sai ta tare a gidansa.

  Ta dinga gyada kai tsawon lokaci, sannan ta ajiye numfashi ta dubi Hindatu ta ce, “Ita ta gabatar min da kanta, ke kin yi shiru ko rakiya kika yi mata?”

  Hindatu ta bude ido ta ce, “A kan me? Igiyarta daban tawa daban, don duk abin da ta fada ita kadai ta sanshi, don ni ban san shi ba…. Ni umarni na bi, don maigidan ya ce na zo mu gaisa, na kuma sauke nauyi……”

  Fatima ta cije lebe cikin girgiza kai ta tare ta, “Kwarai kin sauke nauyi, ina kuma godiya ba tare da na hakkake taki gabatarwar ba tunda tare na ganku…. Ni ban shigo gidan nan don wata ta dinga zuwa tana min haushi ba saboda duk fadin danginmu babu karnuka……”

  “To mun gode”. Abin da hindatu ta ce ke nan, kuma salin’anlin ta tashi da lemonta a hannu ta fice, sai sadiya ma ta ke mata baya bayan ta saki katon tsaki tana habaice-habaice.  

  Fatima ta bi su da kallo kanta na wani irin ciwo saboda bacin rai, yau fa ake yinta, rana zafi inuwa kuna, auren sati biyu mijin babu dadi matansa babu dadi, ita zara’u ina ta tsoma ranta?

*********** *********** *********

 Karfe biyar Abdullahi ya dawo gidansa ya zauna a falonsa da gajiya yana kallon wasan kwallo cikin rabe hankali,fiye ma da uku. Amarya fatima ta debi kason mutum biyu,kwallaon kafa daya, ga kuma iyayen gida wadanda mintuna talatin ke nan da shigowarsa babu wadda ta shigo masa ko sannu bare ta taushe shi game da radadin gajiyar zuciya da ta jikin da ya kwaso. Ya gaji da kaɗaicin don haka ya fara kiran wayar sadiya amma har sau uku tana kin dagawa, sai ya haura ya kira Hindatu, ita kuma tana dagawa don rainin hankali sai cewa ta yi. “

  Lafiya?”

  Takaici ya rufe shi, a zafafe ya ce, “Wacce banzar tambaya ce wannan hindatu? Kuna jina na dawo amma don raini a rasa me bullowa ta gaishe ni?”

  Kawai sai ta kashe wayar tana tsaki. Ashe ya ji ta, ya sauke wayar cike da mamakin mata, mata fa shaidanu ne, kalau fa ya bar su, amma yanzu ya je ya dawo duk sun wani birkice masa, wai ma har hindatu da yake da garantin ba ta salwantar da mutuncinsa da kimarsa. Sai ya ji gaba daya ransa ya kara mugun baci, kawai sai ya tashi ya sa wa kofarsa makulli don ma kar wata ta yi gigin kwaso kafa ta zo masa ya sauke mata nasa rashin mutumcin, don gaba daya haushinsu yake ji. Ya tara lemuka masu sanyi a gabansa, idan ya dure wannan gwangwani ya dauki wannan yana kallon wasan kwallo wai duk don zuciyarsa ta sami sanyi, amma kamar turi don ba abin da ta ke muradi ke nan ba. Fatima ta ke son gani, amma babu wani dalili na ganinta a yanzu, idan ba yana son karyawa kansa tsari wanda Zai iya rushe masa wata katanga a cikin ginin da ya yi nisa a cikinsa ba. Haka ya dinga daurewa har gab da magriba ya yi wanka ya shirya cikin kananan kaya wadanda suka fito da kuruciyarsa a fili, ya fesa turaren five eleven sannan ya kullo kofa ya fice masallaci.

  Sai da ya sallaci isha’I sannan ya nemi gida dauke da take away din amarya, zuxiyarsa cike da sakar yadda za su bullowa juna a yau. Yana shiga ya yi karo da sadiya a tsakar gidan, wanda babu dalilin ganinta a tsakar gidan a wannan lokaci, kawai sai ya yi murmushi don yasan kwannan zancen, ta fito ne kawai don ta sanya masa ido ta sami abin yi masa korafi su hau rigima. Ya share kamar bai san Allah ya tsireta a wajen ba, idanunta kyam kan ledar hannunsa, ya share ya fara kwankwasa kofar fatima. Ya shafe fiye da mintina goma yana bugun kofar ba tare da jin a ransa zai gajiya ba koda kuwa zai  shafe sama da awa daya yana bugawa. Can sai gata ta zo ta bude tana sanye da after dress, fuskarta na bayyana shirin ko ta kwana, ta koma baya zuwa tsakiyar dakin tana sauraron karasowarsa. Ta gama zuwa wuya ba zata yarda Abdullahi ya jona mata ciwon zuciya babu dalili ba. Ya karaso ya ajiye ledar kan table sannan ya zuba mata ido, tun ma kafin ya yi magana ta riga shi.

 “Ka ga malam! Matukar rashin arziki ka kwaso ka shigo min ka juya da tarkacenka, don ni ma na shaki kamarsa ina ji kum a raina ba zata yi mana kyau ba…..”

  Ya dan yi galala yana kallonta cikin murmushi, sannan ya taussa harshe ya ce, “A’a, arzikin na kwaso,ba ni hanya na wuce, amma ke ma ki shaki irinsa”.

 Ta yarfe hannu ta wuce kujera ta zauna tana tsaki, ya kara rage nisan da ke tsakaninsu idanunsa a kanta, sai huci ta ke kamar wadda ya kashewa dan fari.

  Ya dora kafa kan table yana ci gaba da kare mata kallo, sannan cikin muryar zolaya ya ce “Sannu”

  Ta kada ido ta kawar da kai

  Ya kuma zungurota da sassaukar murya. “Ki daina fushi Fatima, sam ba ya yi miki kyau wallahi….. Ina ganin kamar ba ki saba ba……” Nan da nan ta kara cika ta ce, “Ai na ga wadanda fushin ke yiwa kyau, wadanda babu tantama ka dace da su suma sun dace da kai. Idan kana nan, ka muzguna

min, idan ba ka nan ka turo min wakilai, sai dai na yi mamaki da ba ka hada wannan kwangilar da su ba, ko kuwa kyashin ba su nasu kason kake? Na ga suna yi min gorin asarar daren farko alhalin dama can na gaibu ne……

  Ya ji tamkar ta daba wa zuciyarsa adda, wato rashin mutunci su Sadiya suka zo suka yi mata? Ya ji ciwon abin fiye da duk wani bacin rai da ya riske shi a ‘yan watannin da suka shude, sai dai juriyarsa ta hanawa fuskarsa bayyanawa, amma muryarsa a sanyaye ya amsa.

  “Ni ban turo kowa ba, duk kuma abin da wani ya yi ra’ayin kansa ne ba nawa ba……in kuma kishi ne ya sa ki fadar hakan, to ki tuna babu wani dalili da zai sa ki yi kishin matana”.

  Sanyin muryarsa ya sa ta dan dube shi a tsanake, sannan ta kawar da kai ba tare da ta tsira da wani abu a cikin kallon nasa ba.

  “Ba na bukatar ka yarda da ni, don haka ba zan yi kokari goge duk wani fenti da zuciyarka ta kagi goga min ba. Amma kishin matanka Allah ya tsare ni, sai dai abin da nake musu ya fi kishi, domin kuwa ba na kaunarsu, na kuma raina musu wayo fiye da yadda kuka raina nawa kai da su.

   Ya kara tausasa murya ya ce. “Yanzu don Allah me ya kawo wannan maganar? Ko don kawai na yi raddi akan kin ce na miki rashin arziki?”

   A kufule ta amsa. “Idan ma zaka yi rashin arzikin ai na shirya masa…. Kai ban ki ba fa a ce a yau na bar gidan nan ba, domin DUHUNSA ya fara munan a idona”.

  Ba tare da wata shakka ba, ya ce “Ga shi kuma kin yi masa shiga sojan badakkare”.

  Ta yunkuro a birkice ta ce, “Me kake nufi?”

  Da karfin gwiwa ya share tambayar tata, cikin kara kyautata murya ya ce, “Ya ya kadaici? Na damu da yawa da kadaicin da nake hasashen kin wuni cikinsa, sai komai ya gundure ni a office na matsu na zama abokin dauke kewa gare ki ko da hakan na nufin ba zan miki abin burgewa ba”.

  Ta yi sukuti kirjinta na bugawa tun kafin ta shirya, ta kalubalance shi “Wannan dogon zancen naka yana bukatar tambihi a nawa lissafin, inda hali ka fito fili ka wanye min domin in dorar da inda fahimce ka”.

  Ya girgiza kai cikin dariya “Duk abin da zan furta a matsayin tambihi ba zai canza da wanda kika bukaci na fassara miki ba, don ni ne din dai ba canja ni aka yi ba”.

  Da ta rasa abin da zata ce masa kawai sai ta nuna masa kofa ta ce, “Idan ka gama abin da ya kawo ka, ka fita Allah ya tashe mu kalau”.

  Ya dan jima yana nazari, sannan ya murza yatsu ya juya ya fice yana cewa “Ga abincinki nan. 

*********************************

Dare da wuni suka dinga dauki ɗai-ɗai, har suka samar da lissafin da za a kira kwanaki bakwai na kwanan fatima a gidan Abdullahi. Sai dai yadda al’amura ke faruwa a gidan sun zarce a kiyasta su, musamman a ma’auni irin na ZUCIYA, zuciyar ma irin ta Fatima da Abdullahi wadanda dukkansu abubuwa masu girma ke yiwa kudirinsu barazana.

  Fatima dai tana yiwa nata kallon sauki, domin gab ta ke da cimma buri ta idan mai duka ya rayata sati daya ne a gaba, kawu dai ba zai dafata ba kuma ba zai la’ance ta ba, idan mai afkuwa ta riga ta afku, matsalar ta daya shi ne, banjin da aka samu tare da Abdullahi, daga wani kungurmin makiyi zuwa wani mai sadaukar da komai a kanta ko da kuwa bakin tsanyarsa bai mutu ba.

  Abdullahi ba ya yi wa nasa kudirin kallon matsala wadda zata ɗaɗa jarumi da kasa, amma a zahirance jarumtar tasa ce kawai ta kai ga hakan domin shi kadai ne tilonsa ba shi da mai goyon baya, kuma yana yunkurin ne a inda ba a san yana yi ba, hasalima ba a damu da yunkurin nasa ba, sannan a gefe ɗaya ga ma sa idonawa da sana’ar korafi da hakkinsu ko babu.

  Cikin sati dayan nan da za a kira Abdullahi da gwauro to, zai iya amsawa, domin ko wacce ta zare wukarta akansa. Don me? Kwanakin fatima uku wanda shari’a ta ba ta a matsayinrta na bazawara ba su sauya da kwana dayan da ya karantu ba. Ba ta cas ba ta as, saidai Abdullahi ya shigo mata da abinci daga waje ba na kudi kadan ba, banda kayayyakin kwadayi iri iri hatta ruwan sha ba ya ma baya dosarta da pure water sai dai na roba, kuma ko baki tayi abin da zasu ci ke nan.

Zamu dakata a nan sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Also Read:

Ga masu bukatar Audio kuma za su iya saurara ta hanyar taɓa wannan hoton dake ƙasa. Mun gode da ziyarar Aihausanovels.

Back to top button