Uncategorized

Yau Umaru Musa Yar’adua ke cika shekaru 12 da rasuwa

 An haifi marigayi Umaru Babangida Musa ‘Yar’adua ne a ranar 16 ga watan Augustan 1951

 Shi dai marigayi Malam Umaru Babangida Musa ‘Yar’Adua, an haifeshi ne a ranar 16 ga watan Augustan 1951 a birnin Katsina dake arewacin Najeriya. Mahaifinsa shine tsohon ministan birnin Lagos na farko a jamhuriya ta farko, kuma kafin ya rasu shine Matawallen Katsina, sarautar da kuma shi ma marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua ya gada.

 Marigayin ya fara makarantar Firamare ta Rafukka a 1958 kafin a mayar da shi makarantar Firamare ta kwana dake Dutsen Ma a 1962. Ya kuma halarci kwalejin gwamnati dake Keffi daga 1965 zuwa 1969. Sai kwalejin Barewa 1971, inda ya samu takardar shedar karatu ta HSC.

 Tsohon shugaba ‘Yar’Adua ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya daga 1972 zuwa 1978 inda ya samu takardar shedar digiri akan kimiyyar haɗa sinadirai ko Chemistry da Malanta, kafin ya koma domin samun babban digiri duk dai akan kimiyyar ta Chemistry. Marigayin yayi bautar ƙasa a jihar Lagos inda ya koyar a wata makaranta da ake kira Holy Trinity daga 1975-1976.

Related Articles

 

Bayan da ya kammala aikin yiwa ƙasa hidima ya fara aikin Malanta gadan-gadan a kwalejin share fagen shiga jami’a da ake kira CAST dake Zariya a tsakanin 1976 zuwa 1979. A shekarar 1983 marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua ya bar aikin Malanta ya fara aiki da Gonar Sambo Farms a Funtua dake jihar Katsina inda ya zama GM daga 1983-1989.

 Daga shekarar 1984 bayan da Sojojin sukayi juyin mulki malam Umaru Musa ‘Yar’adua an kira shi domin zama wakili a hukumar gudanarwar kanfanoni da hukumomin gwamnati da dama da suka haɗa da hukumar samar da kayan Noma da kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar katsina, Bankin Habib da Hamada Carpets da Madara Limited da kuma kanfanin buga Jaridu da Mujalla ta The Nation wanda ke kaduna kuma wansa Marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’Adua ya mallaka.

 A lokacin da marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’Adua ya shiga siyasa ya yi hannun riga da mahaifinsa wanda a wancan lokaci yake mataimakin shugaban Jam’iyar NPN, inda shi kuma ya zama wakili a jam’iyar PRP ta Malam Aminu Kano mai adawa da NPN. A lokacin da Janar Babangida ya kaɗa gangar siyasa ya zama sakataren jam’iyar SDP a jihar ta Katsina kuma ɗan takararta na gwamna, amma kuma ɗan takarar jami’iyar NRC na wancan lokaci Malam Saidu Barda ya kada shi. To sai dai a 1999 Malam Umaru Musa ‘Yar’Adua ya tsaya takakarar muƙamin gwamnan jihar ta Katsina kuma ya samu nasara a ƙarƙashin jam’iyar PDP, haka kuma ya sake nasara a zaɓen 2003.

 A shekarar 2007 Umaru Musa ‘Yar’Adua ya zama ɗan takakar muƙamin shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP bayan ya samu taimakon tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya zama shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2007.

 To sai dai rashin lafiya da tsohon shugaban yayi fama da ita ta sanya bai samu sukunin gudanar da harkokin mulki kamar yadda yayi fata ba musanman ƙudirorinsa guda bakwai daya tsara na ciyar da ƙasar gaba kafin nan da ƙarni ta 2020.

 Marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’Adua ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2010 da muke ciki a fadar gwamnati dake Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida daga Saudiya inda yake jinya.

 Ya kuma rasu ya bar mahaifiyarsa da ‘yan’uwa da matar aure guda Hajiya Turai tare da ‘ya’ya bakwai da ya haifa da ita da suka haɗa da mata biyar da maza biyu. Haka kuma yana da wasu ‘ya’ya biyu maza da matarsa ta biyu Hajiya Hauwa Umar Radda.

Back to top button