Uncategorized

Yadda za ki kula da jikinki lokacin sanyi

1=== Idan kinsan jikinki yana da saurin bushewa lokacincn sanyi to, ki rage yawan wanka da ruwa mai zafi sosai domin wasu daga cikin mutane musamman mata suna wanka da ruwan zafi har yana konasu to kisani hakan yana saurin sanya bushewar fata, fatarki ta bushe duk yanda zaki shafa mai, yar uwarki mace kanta bazata yi Sha’awar fatar kiba bare maigidanki.

2=== Yana da kyau ki yawaita shan kayan itatuwa domin inganta ni’imar jikinku, kowa yasan ni’ima tana karanci lokacin sanyi shi ya sa ake son ki kula da jikinki sosai lokacin sanyi. maganin ni’ima kadan zaki iya sha ya gamsar da ke amma wallahi lokacin sanyi sai kin yi da gaske kafin kisamu yalwatacciyar ni’ima irin wacce zata gamsar da ke.

KARANTA: “YADDA AKE DUBA EXPIRED DATE NA GAS SILINDER”


3=== Abu na ƙarshe dazan faɗa shine ariƙayin kunshi lokacin sanyi musanman Jan lalle, kiriƙa kokarin yin kunshi a kafarki domin yana rage kaushi kuma yana hana saurin kamuwa da kaushi musanman na Hausa, sannan a rage yawan yawo cikin ruwa da kafa domin shima yana saurin sanya kaushi da Faso, sannan shikuma leɓen bakinki shima ya kasance kina kula da shi domin sai kaga mace har mace amma idan ka kalli bakinta duk a fashe, saboda haka a yawaita shan ruwa shima yana sanya taushin lebe, 

4=== Yana da kyau a yawaita amfani da man kadanya ana shafawa sannan idan anzo yin brush ariƙa goge sama da kasa na leɓe domin yin hakan zai fitar maki da busheshshiyar fatar baki wacce ke sanya leɓe kaushi

KARANTA: “ABUBUWA 4 DA YA KAMATA MACE MAI AL’ADA TA SAN SU”


5=== Ki kasance mai yawan amfani da safa a kafarki lokacin sanyi sannan ki guji yawo babu takalmi ko acikin falonki, ya zamana kina da takalmi tsabtatacce wanda za ki yi amfani dashi acikin falonki  domin kuwa yawo babu takalmi cikin sanyi yana rage maki dumin jikinki da kuma ni’ima jikinki.

6=== Lokacin sanyi lokaci ne da infection ya ke yawan saurin kama mace, kuma lokaci ne da idan kina da kwantaccen sanyi to fa idan baki tashi da gyara ba tabbas zai taso maki, a guji ywan amfani d ruwan sanyi wajan tsarki sannan a guji yawan shan ruwa mai sanyi.

KARANTA: “SHAWARWARI GA MATA MASU JUNA BIYU”


7=== Koda baki da sanyi ki riƙa yawan amfani d tafarnuwa sosai, kirika hada maganin sanyi dakanki kina ajiyewa lokaci zuwa lokaci kina ɗan sha saboda lokacin sanyi, sanyi yana kama wasu matan batare da sunsaniba, shiyasa ake son karki kasance ba ki da maganin sanyi a gidanki musanman awannan yanayi na sanyin hunturu.

8=== Abu na ƙarshe da zanyi bayani akai shi ne  a riƙa kama ruwa mai dumi da kananfari acikinsa shima yana sanya ɗumi, haka ba a son Hq din mace ya kasance cikin sanyi anfison ya kasance cikin dumi shiyasa muke bada shawara duk abinda za ayi amfani da shi ya kasance mai dumi ne, sannan kuma idan ansamu hali za ki iya yin tsugunno akan rushi d kananfari, idan ba asamu kananfarin bama za a iya tsugunno akan rushi domin samun dumin Hq.

Back to top button