Uncategorized

Yadda ake siyan data mai sauki a layin MTN

 Yadda ake siyan Data 1.2GB akan ₦150 kacal

Assalamu alaikum jama’a barkan da hutun ƙarshen mako lafiya, kasancewar waya ta zama jinin jikinmu, bama iya rayuwa ba tare da ita ba, to amman mahaɗin wayar yana yi wa mutane wahalar siya idan nace mahaɗin waya ba komai na ke nufi ba illa Data, wadda wasu kamfanonin layukan sadarwa ke take da (Data is life). 

Kamfanonin sadarwa na layin MTN kamar yadda kowa ya sani yafi duk sauran kamfanonin arhar Data, kama daga Glo, Airtel, Etisalat dadai sauransu.

To a yau ma mun kawo maku wata sabuwar Data da MTN din suka fitar wadda ba kowa ba ne ya san ta ba. Ita dai wannan Data 1.2GB ana siyanta ne akan ₦150 Kacal.

YA YA TSARIN YA KE?

Yadda tsarin ya ke shi ne, dole mutum ya kasance yana ciki tsarin mPulse, shi ne tsarin da MTN suka yi domin habbaka ilimin yara da suka fara daga shekara 9 zuwa 15 inda sukan taimaka masu da Data don bunƙasa karatunsu.

YAYA ZAN KOMA TSARIN MPULSE?

Hanya mafi sauƙi ita ce ka saka *344# ka dannan alamar kira zai nuno maka irin hoton dake ƙasa, sai ka shiga na farko. Sannan ka tura.

Zaka ga sun turo maka da Congratulation na cewa ka koma tsarin mPulse.

Bayan ka koma tsarin mPulse. Domin siyan Data sai ka sake dannan *344# ka dannan alamar kira. To, anan idan ka ta shi sai ka zabi lamba 2, nan take za su watso maka jerin Data ɗin a ciki har da 1.2GB akan ₦150, sai ka shiga. 

Da fatan wannan muƙalar ta burgeku, daure ka yi sharing

Back to top button