Uncategorized

Yadda Ake Duba Expired na Gas Silinda (Cooking gas) ɗinku

  

Ana samu yawan fashewar bututun iskar gas da yawa kuma idan hakan ta faru, a kan yi asarar rayuka tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin nairori.  Yana da ban tsoro cewa har ya zuwa yanzu, mutane da yawa ba su san gaskiyar cewa silinda gas na da kwanakin ƙarewa ba.

 Lokacin da silindar iskar gas ɗinki ya ƙare, zai fara faɗaɗa saboda matsin iskar gas, wanda ke haifar da fashewar iskar.  A cikin wannan labarin, zan nuna muku yadda ake bincika idan silinda iskar gas ya ƙare don guje wa fashewa ko tarwatsewa, domin shi Bature duk wani abu daya ƙirƙira yana da expiring date.  Kafin nan, a ƙasa akwai matakan kiyayewa da ya kamata ku sani;

 1. In har kun tabbatar da cewa silindar iskar gas ɗinku ya kai shekaru 5 to kawai a haƙura da shi a nemi sabo shi ne ya fi. 

 2. Kada a taɓa siya ko amfani da silinda gas na hannu, domin ba ku san shekara nawa yayi a wajen wanda ya fara siyansa ba, kuma shi a ƙa’idarsa ba a so a haura shekara 5 ana amfani da shi.

 Yadda ake bincika idan Silindar gas ɗin ku ya ƙare ma’ana ya yi expired.

 Bi matakan da ke ƙasa don duba ranar ƙarewar silindar gas ɗin ku;

 

 Ana iya samun ranar ƙarewar silinda gas musamman wanda muke amfani da shi a gidajen mu wajen dafa abinci akan ɗaya daga cikin ɓangarorin ƙarfe waɗanda ke haɗa jikin silinda zuwa zobe na sama.  Ana buga shi ko liƙa a gefen ciki na tsiri ko a gindin silinda, ana buga shi da haruffa da lambobi.

NOTE

Dalilin da ya sa na ce kada ku sayi tsohon silindar iskar gas shine, duk wani ƙarfe idan ya tsufa tsatsa takan yi masa illa kwarai da gaske, sannan idan takarda suka lika za ta iya lalacewa. Anan zan dakata da wannan bayani nawa sai mun haɗu a wani lokaci.

Back to top button